Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganarmu rigima Basma, kin ga nan office ne ba gida ba, sannan muna da magana ne ta fahimta, bai kamata ki ce ina miki karya ba. Idan ina son bata miki rai me zai hana na fada miki? Zan ma iya bata miki ran kai tsaye babu yadda zaki yi a kaina."
Ta mike cikin fushi ta fara hada masa kaya tana cewa. "Mu bar office din muje gida."








Mum Abdoul
[2:53PM, 2/24/2018] ‪+234 703 300 1537‬: ♦🔸♦🔸♦🔸♦🔸
*NA SAN DA BAMBANCIN*
Page 28


*KAINUWA WRITERS ASS*
®






*NA*
*Shopiee*
*Ummu shukran*







Ya mike ya na kallonta, ya ce. "Ayyukan da ke gabana na yi ya ya da su? Kuma kina tsammanin akwai abin da zan kasa fada a nan na fade shi a gida? Kin manta kawai ni ne a nan din, a can gidan ma ba sauya ni za a yi ba."



"Naji." Ta fada da karamar tsawa tana miko masa gilashinsa ta rike jakarsa ta ce.

"Mu je."
Ya ba ta hanya yana tsuntsura dariya, ya ce

A'a muje dai, kin saka ni a gaba ne kamar Wanda ya yi sata zaki kai ki tsare?"

Ta wuce ya bita, ya bige da ba wa masara lafia hakuri, ma'aikata kuma ya yi musu bankwana suka dinga binsa da kallo ya na wucewa, musamman Nurse din da ya cewa.


_ko wane ne kar a barshi ya zo ya samin ciwon kai_

Cikin ranta ta ce.
"Munafiki kawai."


Da yake direba ya kawo shi, kawai sai ya shiga motar Basman suka tafi.

Duk yadda ta ke son maida abin rigima a tsakaninsu sai ya ki, har suka isa gida ya yi wanka suka ci abinci da mai girkinsa, ya shirya musu.


Ya wuce bedroom dinsa ya yi tsaye kawai ya na duban agogo, karfe tara, amma Basma ba ta nemi gidansu ba.


Yasan akwai 'yanci a nasu gidan, amma bai kai nasu Basma ba, mahaifinsu ne ya fi kawar da kai, amma innarsu tana da mugun saka ido babu yadda za'a yi zainab ta kai karfe tara a waje ba ta binciki daga inda ta ke ba, kuma ko zainab ta sha giyar wake ba zata ce mata daga gidan saurayi ta ke ba, amma Basma ta sha kwana a gidansa ba zai kirgu ba.


To a yau ba ya butakarta da kwanan nata, ya kuma rasa ta hanyar da zai kore ta. Ta gayyato shi wannan gida domin su yi maganar da ya ke fatan ta yanke wannan alakar tasu mai kama da mummuna, amma kamar ta manta ma ta bige da binsa da sharholiya.


Bai kai karshen tunaninsa ba sai gata ta shigo, ba ta bashi sararin magana ba, ta fara masa abin da yake gudun ba, dan ya bayar da kai bori ya hau, wannan ne kuma ya ba ta karfin gwiwar zatar masa da karya yake ba zai iya barinta ba.

Tana wasa da faratan hannunsa, ta ce masa.

"Ali wannan farin cikin kake son raba mu da shi?"

Ya yi shiru ransa ya na dan baci, sai dai bai ce mata komai ba.

Taci gaba da magana
"Akwai wata yarinya da kake nutsuwa a tare da ita kamar ni? Na sani ba ka taba son wata mace sama da ni ba Ali, amma ina mamakin yadda kake son karyata zuciyarka Ali."


Ya gyara mata kwanciyar kanta a kirjinsa, a nutse ya ce da ita.

"Duk wadannan da kika lissafa ba su kadai ne farin ciki ba Basma, aure da kike jinsa ya wuce duk yadda kike tsammani, wannan farin cikin da kika lissafo sai ki ga ya kasa samuwa idan ba a yi taka tsan-tsan ba, shi yasa tun farko ba na yaudarar mace na ce zan aure ta. Dai dai gwargwado ina gudarwa aurena kuskure, kamar kwayar zarra na ganin idona."


Jikinta a sanyaye ta ce.
"Ali ina da matsala kenan ko....?


Ya tare ta cikin tausasawa.
"No, ni ne nake da matsalar, saboda dukkan tsarina da tsantsenina na nauyaya shi akan matar aurena, ciki har da cika zuciyata taf da kaunarta fiye da yadda nake da tasiri a tata zuciyar.

Wannan shi zai ba ni damar da zan Kore mata dukkan aibuna, wanda hakan zai alkhairantu rayuwar 'ya'yana, wadanda na sha fada miki tun yanzu nake share musu fagen rayuwa mai kyau, dan ina jin ba ni da abin alkhairin da ya wuce su...."


Basma ta gaji da toshe kunnenta daga jin maganganun da suke neman fasa mata zuciya. Ta tare shi da neman yin kuka.


"Takaita min manufarka Ali, na gaza ne dan na cika sonka, na gaza ne dan bazan iya cike guraben da ka hakawa matar aurenka ba, ko kuma na gaza ne dan akwai wadda ka fi so a kaina...? Buds bakinka dan Allah ka fada min gaskiyar magana."


Ya yi shiru ya na shafar kanta a hankali ya na nazarin maimaita amsoshin da ta riga ta amsa, ta ke son goga masa bakin jinin ya fada da nasa harshen ta ga bakinsa. Can da ya fahimci jiran amsarsa ta ke, sai yace.



"Ni ban san abin da zan ce miki ba Basma, ba mu taba alkawarin aure da ke ba, bai kamata yanzu ki daga min hankali a kansa ba. Ba na so nayi ta yi miki laifin cewa ba zan aure ki ba, sannan ke ma bai kamata ki damu ba idan na fadi hakan, wanda kamar rashin auren nawa gareki ma ya fi..."


Ta kwace kanta cikin bacin rai da fita hankali.

Ta janyo bargo tana rufe jikinta, muryarta a kausashe ta ce.


"Ka ga malam! Na gaji da wannan yaudarar da kwane-kwanen, ka fito fill ka fada min wata ta hure maka kunne. Yaya kake neman mayar da ni karamar yarinya, ko kuma an fada maka dai dai nake da mutan kauyen da ka baro....


Ya tsura mata ido ya na daga kwance, ya yi fuska, ya ce.


" To Basma na sami matar aure, shi kenan! Na fada miki bana son bata miki rai."


Kamar tashin hankalin fuskarta ya ragu, amma na zuciyarta ya ninninku matuka, shi ne kuma ya tunzura wuce gona da iri a kalamanta.

"Na rantse ba ka isa ba Ali, an fada maka an haifi shegiyar da zata Shiga tsakanina da kai..."


Fuuu! Ta mike ta fada bandaki kamar mintina sha Biyar, ta fito cikin fushi sai faman kumburi ta ke tana munfarfashi, shi kuma ya na daga kwance ya na binta da kallo.


Ta na tsaye gaban madubi tana daure gashinta, ya jefa mata tambaya, hankali kwance.

"Dams munyi da ke zaki damu rayuwar aurena ko kuma ni zan damu da taking?"

Ta table baki ba tare da ta juyo ta dube shi ba. Tace


"Idan ka ga dama ka damu tawa rayuwar amma na rantse maka ni zan damu taka da son ranka ko babu..."

Ya yi karamar dariya ya na kokarin tashi zaune.

"Da zaki shawartu da na shawarce ki katse bata lokaci a kaina. Ba zaki wani iya damuna ba, domin dukkan kawaicina da hakurina bai shafi lamarin iyalina ba."

Wannan karon kamar ta fara sabawa da takaicinsa, dan ko juyowa ba ta yi ba ta ce.

"Duk mun fadu, sauranmu aikatuwa."

Ta day wayarta sannan ta dube shi da kyau, ta ce.

"Bari na dawo maka da tambayar da ta bata maka rai rannan, tunda yanzu neman bacin ran naka nake, wacce jakar ka bi da gudu rannan?"

Kuncinsa cike da murmushin da ya ke dadewa bai yi kamarsa ba. Ya ce


_She is my fianceee_

Ta dafe baki tana zaro ido, kawai kuma sai ta tsuntsure da dariya har da kwanciya a sofa. Ta yi dariyarta ta isheta, sannan ta mike zaune da ragowar dariyar tana nuna shi da hannu.






Mum Abdoul
[2:54PM, 2/24/2018] ‪+234 703 300 1537‬: ♦🔸♦🔸♦🔸♦🔸
*NA SAN DA BAMBANCIN*
Page 29


*KAINUWA WRITERS ASS*
®





*Na*
*Shopiee*
*Ummu shukran*




*Ban manta da ke ba Rahinat saboda irin kwarin gwiwar da kike ba ni Allah ya saka da mafificin alherinsa ameen*







"Ali, daga yau na dauke maka shaida biyu da na yi maka, zamowarka mai cikakken tsari, da kuma kasancewarka mutum mara karya dan a so shi..."


Ta ci gaba da dariya sannan ta dora.

"Bafulatanar kauye, Empty brain a ilimin boko da na addini, balle na ce sahabbai kake son kwaikwayo.... Hahahaha! Ali !! Bukatunka ga mace ka ke tsammanin jaka ce zata iya dauka? Ali, qwallinka da tsantseninka kake tsammanin matar daji zata iya dauka...? Na rantse Ali ka fadi babu nauyi, kuma ka rage digo da yawa na kason kallon kimar da nake maka."


Har yanzu yana dariya.
"Kalma daya ce ba ta yi min dadi ba cikin maganganunki. Da zaki janje ta ni sai na kara miki digo a taki kimar kiran matata JAKA, duk runtsi ko muzuru ba zan iya kiran mijinki haka ba."


Ta kara tuntsurewa da dariya, tana tafa hannaye ta ce.
"Ka kira shi mana! Ai babu wani mijin bayan kai, jaka kuwa mafarkin ido biyu ce, yanzu ne kuma nasan ba da gaske ka ke ba. Ta idan gundurarka na yi bari na baka hutu, ko shi yasa ka ce na rage sonka ba na cire sonka gaba daya ba?"

Ya tare ta cikin raha.
"Ni kuwa ba na so ki yawaita cika baki Basma, kamar kin manta ban cika zolayarki ba, ko ina yiwa kowa karya ke dai banayi miki, saboda haka ki dauki maganata da muhimmanci."

Ta zabga tsaki ta yi gaba tana cewa.
"Na barka lafia, sai na ga goron auren."
*******************


Ya kwana ya wuni da farin cikin ya sabule Basma daga rayuwarsa, saboda haka da yamma ya shirya ya nufi gidansu, dan tuntsurar da ta maryam ma wadda ta dami mahaifiyarsa da zancen.

Abin da bai so ba, tare da maryam din akayi masa oyoyo, ita da zainab suka riki hannunsa suka isa har gaban kyakkyawar innarsa wadda ta ke zaune sanye da farin gilashi a idanunta.

Ya fada kan kujerar kusa da ita yana fadin.
"Hii mum."

Ta kara fadada fara'arta tana dubansa.
"Ali, mun yi kewa fa, sati biyu ba mu saka a idanu ba, amma ka kwana biyu ba ka leko na ganka ba, sannan ka kashe wayoyi...wai mene ne hikimar kashe wayoyin da kake kwana biyu."

Ya saci kallon maryam da ke hidimar zuba masa lemo, sannan ya maida hankali ga innarsa cikin sakewa ya ce.

"Momi zuciyata ce ta bude kofarta, wasu abubuwa masu tauri da korar sauran lissafi suka cikata, su suka da min son kadaici."

"Ko" inji momin fuskarta na bayyana farin ciki idonta a Kansa. Ta ce.

"To sha lemon ka ba ni labari, a kawo abinci?"

Ya girgiza kai lokacin da ya karbi lemon a hannun maryam, sannan ta zauna kusa da shi kamar 'yar uwarta mace, sai kallonsa ta ke sai ka ce wata tsohuwar mayya. Ya ajiye tambulan, sannan ya mokada kafada.

_"Surprise mum_watan aurena ya tsaya."

Momi ta zare gilas cike da farin ciki da mamaki, ta ce da shi.

"Ka shirya karrama mu kenan? Gaskiya na yi farin ciki, maryam din ce ko Basma, ko wata daban?"

Ya kara satar kallon maryam ya ce.

"Wata 'ya marainiyar yarinya ce mai tsada na ga ana yiwa kokawa, shi ne nima na shiga aka yi da ni. To na sami sa'ar tsigo furen soyayyarta, yanzu kokawar da ta rage min ta yadda zan kwaci kaina daga mafiyancin masoyanta..."

Momi sai dariya ta ke tana kallonsa da kayen yadda yake bata labarin. Ta ce

"Wacce tsadaddiyar yarinya ce haka? Gaskiya ina tayaka murna da sonta. A ina ta ke?"

Cike da karsashi ya ce .
"Sunanta Rahma, kuma a kauyen da na kai ziyara ta ke...."

"Ita ma ziyarar ta kai?" Inji momi da ta tare shi cikin doki. Ya girgiza kai.

"Haifaffiyar can ce, a can din kuma ta girma."

Momi ta rage walwalar fuskarta zuwa hade girar rashin fahimta, ta kada kai ta ce.

"Ali ban fahimce ka ba, 'yar kauye mai tallan fura da nono, ko kayan Gina zaka auro...?"

Kai tsaye ya amsa.
"Ba ta tallar nono, sai dai kiwon shanu."

Fuskarta momi na cika da jimami, amma maryam sai ta debo dariya irin wadda Basma ta yi masa, ita had da kwanciya a kasa tana faman nuna shi da yatsa, sai dai ita ba ta tanka ba.

Momi ba ta iya hasala komai ba, illa juya hannu kawai ta ke, ta ce.

"Ban ga hikima a wannan azancin naka ba Ali, me yasa ba zaka yi auren dazaka yi farin ciki ba kamar mutane masu daraja irinka? Me zaka tsinta a karamar yarinya yar shekara sha bakwai, kuma 'yar kauye wadda ko aji kila ba ta taba gani ba, Ali zaka rusa farin cikin 'ya'yanka."

"A'a momi."
Ya fada yana duban agogo ba tare da damuwa ba, yace.

"So ya hanani ganin aibun da ke kika gani, farin cikin 'ya'yana kuma ba zai sha ruwa ba, zan shirya masa ta duk hanyar da karfi na zai iya, ki yiwa daddy maganar, shi ma zan same shi gone."

Sai ta kasa tanka masa, ta ni shi da kallo kawai tana ficewa, kuma da gayya ya take kafar maryam da ke kwance tana dariya, ta na kara ko waiwayowa ya dubeta bai yi ba.
*******************


Washe gari ya dauki yammaci ya koma gidansu. Daga can filin wasan gidan ya hango mahaifinsa tsakiyar karnukansa uku yana wasa da su, sanye yake da farin wando _three quater_ da farar singileti. Cike da farin ciki ya nufi shi, da farin cikin suka rungume juna, sannan Aliyu ya sunkuya yana wasa da wani kare, mahaifinsa na binsa da kallo cike da kauna. Ali ya dago cikin sangarta yace.

"Daddy ka sami labarin na sami matar aure ko?"

Daddy ya rungumo kafadar Aliyu ya ja shi suka nufi kujerun hutawa. Ya zaunar da shi, shi kuma ya dora kafa kan tasa kujerar da ya ja, ya sunkuya yana dafe da kafadarsa ya ce.

"Na ji Ali, kuma na kwana da shakkar kai da kanka ka tsarawa kanka ganganci irin wannan."

Aliyu ya dan yi fuska, sai dai bai ce komai ba, ya ci gaba da shafar kan wani kare da ya dafe masa.

Mahaifinsa ya ci gaba da kallonsa cikin murmushin yake, sannan a tausashe ya ce.

"Ka gane gangancin da ka ke shiryawa kuwa Ali, wanne farin cikin kake tsammatarwa kanka ga matar da ba ta da ilimin boko da na addini, kila ko mota ma ba ta taba hawa ba, duk ci gaban zamani da wayewar da ka yi da ita ko yarda akwai su ba ta yi ba, bare ka ji dadin ka gama da matakin farko na matsalarta...."

Aliyu ya kara yin fuska, ya ce.
"Haba Daddy, wannan ai mugun data ne..."
Mahaifinsa nasa ya tare shi cikin dan bugun kafadarsa, na alamar rarrashi.

"A'a ba mugun fata ba ne Ali, bambancin da ke tsakaninku nake son nuna maka. A matsayina na mai son farin cikinka sama da kowa, kuma mai kauna da fatan matarka ta samar da gagarumar gudunmowa a nishadinka da farin cikinka.

Ali wanne farin ciki ka yiwa kanka tanadi a yarinya mai shekaru goma sha bakwai, sannan ga duhun kan kauyanci da jahilci?"

Aliyu ya sauke ajiyar zuciya, amma ya kasa cewa komai. Mahaifin nasa ya kara tausasa murya.

"Ina son ka fahimce ni da kyau Ali, ai ba ka kawo Abu m na tankwabe wannan ma dan na ga da tsabar ganganci a ciki ne ya sa zan kasa goyon bayanka, kai da kanka ya kamata ka zauna ka yi tunanin *BAMBANCIN*da ke tsakaninku, wanda zai iya hana muku zaman lafiya idan kunyi sure.

Tazarorin da ke tsakaninku kamar sama ce da kasa, kana da kudi ita 'yar talakawa, kai boko mai digiri uku, kila mota ba ta taba hawa ba bare ayi maganar ta taba ganin alli. Abincin da kake ci daban, Wanda ta ke ci daban. Duk maganar da zakayi cikin ilimi zaka yi ta, ita kuwa zata fadi abin da ya zo bakinta ne kawai, yadda ake shirya gida da yi masa kwalliya bata sansu ba, dan ta saba rayuwa karkashin rufin bunu....ta ko ina _life style_ din Ku ya bambanta Ali, bambancin kuma shi ne haske a gidan aurenku ba wai dan ba kwason juna ba, kuma na fi tausaya maka don zata tawaye ka da yawa."

Ali ya dafe kai cikin runtse ido da girgiza kai, ya sauke numfashi ya dubi mahaifinsa da kyau.


*"NA SAN DA BAMBANCIN*Dad, na kuma yi duk lissafin da ka yi, sai dai na kasa rinjayar da nauyinsa akan nauyin son Rahma da nake ji a zuciyata. Ina son yarinyar kwarai fiye da duk wani so da ka taba samun labari daddy."

Daddy ya kawar da kai da dan kyabe baki.

"Amma ka yi asarar wannan so mai daraja tunda ka aza shi a muhallin da ba zaka sami raddi ba, ko da a fatar baki yarinyar nan ta taba cewa tana sonka?"

Aliyu ya dago a sanyaye ya dubi mahaifinsa ya na girgiza kai.

"Ba ta taba ba dad, duk da haka na kasa da zuciyata ta ga laifinta."

Daddy ya fara dariya cikin ka da kai.
"To ina tabbatar maka _I love you_shi ne mafi karancin gatan da zaka rasa daga gareta, ka ke kayi nazari, dan ba zan matsa maka ba."

Aliyu ya yi shiru tamkar mai son zurfafa tunani, sai dai Rahma ce kawai ke yawo a zuciyarsa cikin watsar da aibunta..
[2:54PM, 2/24/2018] ‪+234 703 300 1537‬: ♦🔸♦🔸♦🔸♦🔸
*NA SAN DA BAMBANCIN*
Page 30



*KAINUWA WRITERS ASS*
®






*NA*
*Shopiee*
*Ummu Shukran*






*Shafin na yau naki ne Ameeratu ummyn Nihlah Allahu ya saukar mana da ke lafiya alfarmar fiyayyen halitta Annabin rahama(S.A.W)*





Rashin amincewar daddy ya nuna bai rage komai a cikin son Rahma da shiryawa kai aurenta ba.

Yana ji a ransa kawai kauyacin Rahma da jahilcinta kawai kowa ya sani, amma ba su San amfaninta gare shi da zai iya danne jahilcinta da kauyancin nata ba, ko da kuwa zata dauwama cikin kauyanci da jahilcinta.


Ranar juma'a ya gama komai na shirin kai kansa ga neman auren Rahma ba tare da ya sanar da kowa ba. Tun yammacin juma'ar ya yi tanadin, komai ya adana cikin motarsa _jeep_kamar kudade, tsarabar Rahman, su Musa da Dagaci, sai kuma zuciyarsa da ya korar mata dukkan tsoro da fargabar yadda zata iya rutsawa da shi.

Da sanyin safiya ya cusa bindiga a aljihu ya shige mota yana bata wuta, direbansa da ke masa bangaren ya cimmasa a guje daga shi sai singileti da dogon wando. Ya rusuna cikin haki yana gaishe da shi, ya ce.


"A yi hakuri oga, ban san da wuri zaka fita ba.... Shi ne... Oh naga sai tara kake fita ranar asabar."

"Ai komai daurowa ta ke."
Ya fada lokacin da ya ke shirin ta ke giya, ba tare da ya dubi direban ba a ladabce direban ya ce.

"Mai gida ina zuwa? Idan...."
Ya tare shi da kallonsa fuska a bace.

"Ko ina zauna akwai aikin da zan yi maka?"

A ladabce Balarabe ya girgiza kai.
"A'a, ina nufin idan na yi wanka sai na biyo ka."

Aliyu ya yi murmushi ya fara Jan motar yana cewa.
"Idan ka yi wankan sai ka tafi biyan bashin zancen da ba ka je jiya ba, ko kana nufin ban fahimci yadda kake yamutse min fuska jiya ba? Da na rike ka har dare na hana ka zuwa hira."

Balarabe ya bige da bin motar da kallo yana murmushi cike da kaunar ogansa tunda bai bashi damar raddi ba, maigida na da sakin fuska da daukar mutum da daraja, ko ya yi fushi bai cika tsawaita shi ba, in yaso kuma yana wasa da su tamkar abokansa.

A bakin _get_ ma haka suka yi da maigadi yana daura _belt_ yake cewa maikudi maigadi.

"Ranka ya Dade ayi mana addu'a."
Maikudi ya rusuna da fara'a ya na cewa.

"Allah ya taimake ka, Allah ya dawo mana da kai lafiya, Allah ya ba ka dukkan abin da kake nema."

Aliyu ya ja mota yana dariya, ransa na yi masa haske game da fatan maikudi.
_Allah ya baka abin da ka ke nema_


Kamar dama ya San zai je neman muhimmin abu a duniyarsa.

Ya dagawa maikudi hannu yana cewa.
"A kula da kyau, kar a bar kowa ya shigo min gida, duk yadda na ke da shi."

Maikudi na masa Allah ya kiyaye yana tuna Basma a zuciyarsa, yasan da ita maigida yake. Haba yarinya kamar ta hada dangi da mayu, ya fada a ransa yayin da a fili ya dora.

"Allah idan ta zo yau zan nuna mata kalar rashin kirkina."

Lafiyar mota da kwarewar gudu da mota ya sanya Aliyu isa Rugar Gulu cikin awa uku daga Kaduna. Ya tsayar da mota dab da bigiren da aka tashi tantinsa satin da ya wuce yana bin wajen da kallo. Wata sabuwar kaunar Rahma na kara cika kirjinsa, dan babu abin da Rugar da duk wani abu a cikinta ya ke tuna masa sai soyayyarsa da Rahma.

Dai-dai sannan lokacin Rahma na kwance kan bishiyar kanyar da ta hango Basma a kirjin Aliyu ranar da zai tafi, a yau tana cikin damuwar da ta zarce ta wancan ranar. Dan kuka ta ke sosai, amma zuciyarta ta kasa sanyi kamar mai shirin babbakewa. Duk fadin duniyar nan ita sai ta yi mata kunci tamkar wadda aka saka cikin kura tandu.


Kamar almara ta hango silalowar bakar motar Aliyu, kukanta ya dauke, hawayenta kuma suka tsaya cak! Ta kurawa motar ido cikin bugun zuciya da fargabar ta ga sannan matar ta fito tare da Aliyu, ko Aliyu tare da wani, sai ga kyakkyawa Aliyu mai kamshi ya fito. Nan take ya kamshinsa ya karade wurin iskar ta dinga ratsa zuciya har kwakwalwa tana rikida zuwa halittar son sa, har sai da halittar son nasa ta cika zuciyar ta ta fal! Sannan ta fara sauyata wasu hange hange masu tsauri.

Rasuwar Halliru, aurenta da ake shirin daurawa ga mai rabo nan da bayan sallar azahar, yadda zata rasa Aliyu da yadda zata dauki rashin, sai kuma yadda zata iya nasarar samunsa duk cikin wadannan dakiku da ba su fi cikin luddai ba.



Wannan ya sanya kukanta dawowa sabo fil!
Mai ciwo fiye ma da na dazu, tunda yanzu tana kallon kyakkyawar fuskar Aliyu da ke son zame mata kila wa kala duk da zuwan nasa a yanzu ya shayar da ita mamaki kwarai, don kafin wannan lokacin ta fitar da rai da zuwansa.

Fitarwa da ya yi awon gaba da saka ran farin ciki a rayuwa iyakar zamanta a duniya.

Aliyu ya gama da kallon muhallin tantinsa da zagayensa, zuwa turbar da yake bi zuwa wajen motsa jiki da kiwon rahma. Ya bi ganinsa nisan wajen gadarsu Rahma da hakan ya sa shi matsanancin jin kishin ganinta. Da sauri ya kai ganinsa ga bishiyar hanyar da ya hangeta rannar da zai tafi, kamar almara sai gata a bishiyar.

Cike da wani irin nishadi ya karasa gare ta har da hadawa da gudu. Jiki a sanyaye ta diro daga bishiyar tana kokarin goge hawayenta Wanda tun kafin ta sauko ya kula da su.

Ya dubi ta run daga sama har kasa, ta na sanye da kodaddiyar atamfa zani daban, rigar daban, dankwali daban, daurin kan ma ta wani tamke shi, ga urban murjani da dankara a wuya, kunnenta kuma da wanj yararin yari.....wannan shigar tata ta ishe kawar mata da kai ya tsartar da yawu, amma sai sam ba su Dada shi da kasa ba, sai ya fi damuwa da tarin hawayen da ya gani a idonta. Bai kuma yarda idonsa ke gizo ba, ta rame matuka! Cikin Barin jiki ya dafa kafadarta yana dubanta a rikice.

"Rahma me ke faruwa?"

Ta ja da baya a hankali dafe da gurin da ya rike a kafadarta tana kallonsa kai tsaye. Hawayenta na kara gudu. Hakan ya sa ya kuma shan gabanta ya rike kafadunta duk biyun, kuma ya rike da kyau yadda da ta yi yunkurin kwacewa sai ta kasa. Da murya kasa-kasa ya ce.

"Fada min Rahma, mene ne ya faru?"

Tana kokarin tsayar da hawayen ta ke kokarin bambare hannunsa daga kafadarta, fatar jikinsa kamar auduga, amma nata hannun da ta ke kokarin hukunta shi da shi wani tattaura har da kaya-kaya, hakan ne yasa da ya saki kafadarta sai ya riko tafukan hannayenta yana kallo, sannan a hankali ya dago ya nacewa kallon fuskarta, zuciyarsa cike da wani irin rauni dalilin so da kaunarta. Da wannan damar kuma ta yi amfani ta kwace hannayenta ta ja baya tana kuka da girgiza kai har ta furta."

"Ni na

Please Login or Register in order to submit comment