Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka dawo, sannan 'yan fashi suka tare su, suka karbe kudin suka kashe mutum uku cikin su, sannan ragowar ma kowa ya sami nasa kason Harbin. Kwanan su ne kawai a gaba.

Su Aliyu suna tsaye har sai da suka daina ganinsu, sannan suka juya suna dariyar abin da ya faru.

Wasa ya koma sabo aka yi ta shan shagali karfe biyun dare, Aliyu ba dan ya gaji ba ya nemi makwanci, tsoronsa daya kar ya shanke a waje wani ya lallaba can ya kashe masa Rahma.

A ka kai shi wani kuntataccen daki mai wata mitsitsiyar raga a sama, wai nan ma an zaba masa ne, an dire masa katuwar katifar da aka saka amaryar kabiruwa ta ciro daga gadonta aka shimfideta da darduma irin wadda suke sa wa a bango.

Aliyu ya hada nazarin dakin da duban kabiruwa.
"Ina Rahma?"

Kabiruwa ya kara mutuwar tsaye, ya ce.
"Na zaci an bar wannan maganar tunda sun tsorata sun gudu."

Aliyu ya kawar da kai.
"Sun kuma yi maka alkawarin ba zasu dawo ba ko?"

Kabiruwa ya yi shiru yana kallonsa, ganin Aliyu bai yi ko gezau ba sai shi ma ya baro masa.

"Yanzu kai dan fitsararka ta kai fitsara sai ka taba yarinya a gidan surukai?"

Aliyu ya juya baya alamar ko kadan maganar ba ta Dada shi da kasa ba, ya na cewa.

"Ko a gidana ta ke ba ta isheni tabawa ba bare a nan ko haka na fada maka? Alhalin idan hakan ne niyyata ba zan kasa fada maka ba, na ce maka tsaron lafiyarta zan yi, don me kake son matsa min?

Kabiruwa ya dade a tsaye, cike da tsabar mamaki, a kashe ya kada kai ya wuce ya na cewa.
"Za a rakota, kuma kannenta biyu zasu kwana tare da ita."

Aliyu ya dan daga murya ya bi shi kulli.
"Idan ma kai zaka tayata kwanan ka zo."

Yana tsaye tsakiyar dakin yana binsa da kallo kuncinsa ya yi yawa, duk da zanyi ake amma ya san iskar shaka sai ta yiwa mutum kadan ko da kuwa shi kadai ne a dakin, kofar dakin kanta guntuwa ce, sai mutum ya duka ya ke shiga. To ga labile ga kofa an tura daga waje, kuma ga asabari an saki duk a wannan dakin mai kama da na tantabaru.


Ya na nan tsaye ya ji 'yan maganganu. Da sauri ya ja kofar yana budewa Rahma, yaran biyu ne suka fara shigowa, sannan wata gyatuma ta shigo rike da hannun rahman da aka dakawa uban lillibi. Aliyu ns rike da kofa labile ya amsa gafara dai din tsohuwar yana binsu da kallo, sannan ya ganta a tsaye zunubin da suke giemamawa ke nan tamkar na Wanda ba ya sallah, dan haka ma ta ki amsawa ta ce masa.

"Kai dan kaniyarka ni yayar mahaifinta ce."
Ya fara tartare labilen yana kullewa tare da kare kofar dakin da wani dan buta yana karamar dariya, shaidar dai korafin bai sami karbuwa ba har ta gaji da mamaki ta fara shimfidawa Rahma keson da ta riko, ta sa mata filo, ta ce.
"Kina gurin kwanciyar ki, kinji dai gargadain da akayi miki ko? To wallahi ki tsare mutuncinki kwanta, ku ma mandala ku zo ku kwanta."


Sai da ta ga kwanciyarsu sun saka Ramata a tsakiya sannan ta nufi hangar fita tana cewa.
"Mu kwana lafiya"

Dariya kawai Aliyu ya ke, ya kasa tanka mata. Sai da ta fita sannan ya bi Rahma takure tsakiyar yara da kallo, abin da ya bashi takaici shi ne kodaddiyar atamfar nan da ya ganta da ita dazu ce dai a jikinta, shaidar ko ruwa ba ta gani ba, kanta ya yi him! Alamar an tsefe shi, bai tashi firgita ba sai da ya dubi kafafu da hannayenta ya gansu nade da Leda da wani tsumma kamar mai karaya. A rikice ya dalleta da tourchlight ya ce.

"Rahma mene ne wannan a kafarki da hannunki?"

Rahma ta yi luf da kirjinta na bugun sittin-sittin, shi kuma ya zo ya hau taba kafar yana jinjinawa, daya yarinyar ta tashi zaune murya a sanyaye ta ce.

"Kunshi ne fa".
Ya dubi yarinyar da sauri bayan ya saki hannun Rahma, yace.

"Wane irin kunshi?"
Ta nuna masa hannayenta da kafarta ta ce. "_irin wannan, ita ma idan ya kwana aka cire haka zai yi ja da baki."

Aliyu na haska kafafun yarinyar, ya mike tsaye da sauri, ya debo wata katuwar ashar ya dire da cewa.

"Tab! Rahma tashi ki fire shi!"

Duk su ukun suka tashi a tsorace, bakin Rahma sai rawa yake ta kasa magana. Kawai sai ya durkushe a gabanta yana kici-kicin sabule mata amma tamau a daure, sai ya dago kai fuska a bace ya dubi ta, muryarta na rawa ta ce.

"Don Allah ka bar shi...
" Don me? Wallahi ba na sonsa, cireshi zaki yi."
Kawai sai ta fara Jan azargin tana warewa ta ce.

"Talle zo ki katse min."
Yana tsaye yana haska musu suka yi bakin katse kunshin yana kallonsu cike da kyankyami, Abu sai ka ce kashi, suka kwashi lallen suka fito waje, shi da kansa ya zuba mata ruwa ta wanke har ya fara dan ja, ya dinga sa ta tana dirjewa, amma a wofi, har ya hakura suka dawo daki yana ta faman mita.


"Ku hau waccan shimfidar ku kwanta."

Ya fada lokacin da yake kokarin shimfida sallaya dab da kofar dakin da ya bude kofa, su kandala na rige-rigen hawa katifa, Rahma kuma ta yi sararo a tsaye tana son tambayarshi in da zai kwanta tana cike da kunya da fargabar su mandala su yada ta, har Aliyu ya biyo a tausashe ya ce.

"Rahma ki kwanta mana, ni kings in da zan zauna ba na son zafi ne, kuma ba wai bacci zan yi ba."
Babu halin ts tanka, kawai sai raba cikin su mandala ta kwanta. Shi kuma ya zauna ya jingina da bango ya ajiye bindiga gabansa, ya fito da wayarsa ya shiga cikinta ya kasa hankalinsa da yawa.

Gundumemen son Rahma, da train matsalolin da suke baibaye Rahma., ba wai da na San in aurenta yake ba, amma yanzu ne ya kara tabbatarwa, lallai *BAMBANCIN*tsarin rayuwar da ke tsakaninsu Wanda ya kwana da sanin sa sai ya girgiza shi.

Abu biyu ne mai dadi a auren Rahma, su ne son da ya ke mata da kuma wata maganar da mahaifinsa.

_ina jin babu wani abin kirki da zaka tsira da shi a yarinyar nan illa ladabinta, na yarda da cewa za ta barka ka yi komai ba tare da ta saka maka ido bare ta yi maka birni ba_
_ sannan zaka iya yi mata tsawa, ta yi maka barin jiki, bayan wannan duk wani Abu na bangaren dadawa da nishadantar da zuciya ban saka maka ransa ba Ali, kai a bangaren shimfidar baccin ku ma sai ka kusa ciwon zuciya, dan zaka kirata ta zo da kyar ne, kuma idan ta zo tabarka da kida da rawa kai kadai....


Ya tuna wancan ranar haka ya ce ma haifinsa.
*NA SAN DA BAMBANCIN*
Shi kuma ya ce masa. "Ba sanin kawai kake bukata ba, zaka iya tanadin juriyar."

To tun daga yau ya fara samun somin tabi kunshin tsohuwa ta fada kwata, rashin wanka da tsabta, ga uwa uba gargadin da tsohuwa ta yi mata...
"Ki rike mutuncinki."
Sai ya rasa da wanne kwakwalwarsa zata ji son nata. Lissafin BAMBANCIN da ke tsakanin su ko kuma himmar tanadin juriya da dabarun da zai shafe bambancin?

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment