Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dana siyo maki ice-cream."
Zahra ta kalli kud'in gami da zaro idanu tace"nidai banaso,ki'aje kud'inki bene kawai nakeso kihau dani,indingayin sululu."
Mamaki yacika dr.ru'kayya aranta tana riyawa ashe duk wautar zahra tanada tarbiyya?
Lallai zasuji dad'in zama da'ita lokacin da 'kuruciya ta barta.
Babu yanda batayi da zahraba,amma 'kememe ta'ki karbar kud'in dole ta mayar a jaka.
Tanamasu umma godiya dacewar zata aikoma zahra da sweet tunda ta'ki karbar kudin.
Har zaure umma tarakata itakuwa tari'ke hannun zahra tace taje taraka mota.
Sunfito bakin lungun isha'q yana bud'e mota,idanun zahra yasauka akan jabiru wanda jiya ya 'kalamata sheri wai taje kwad'ai gidansu ummilolo,
Bata tsaya tabi takan dr.ru'kayya ba,tafincike taruga da gudu tayi wajen jabiru wanda ya d'auko ni'kan gari akai.
Tana zuwa ta hankad'ashi garin ya zube a kwata,sannan ta cukumi rigar jabiru tafara 'kuli-'kulin kubura dashi Dr.ru'kayya tana daga nesa ta hango yara harsun fara zagayesu suna wa'kar"bamu rabawa sai dai mu'kara zigawa bugi cikin."
Subhanallah cewar dr.rukayya wadda tuni tanufi inda zahra take dambacewa,
Dasauri tarike hannu zahra wadda take yayyafa ruwan bala'i,
Jin anri'ke hannunta yasaka batare data waigo ba tace "wlh kowaye yasakeni inba hakaba najuyo saina yima mutum wanka da ruwan kwatar nan,
Dr. Ru'kayya tace"oh oh zahra haka kike ashe.
Zahra tawaigo suka had'a idanu da Dr Rukayya,
Tace"shinefa jiya wai yace naje gidansu ummilolo naci garin kwaki,alhalin karya yakeyi ni aigidanmu anmafi cin dad'i abbanmu kullum da dare yanama siyomana kifi itakuma umma saitayi wanka taje can d'akin abban mu har....."
Dr. Ru'kayya tace "ya'isa zahra nasan kunacin dad'i ai,amma kiyi hakuri bakiga kin sakashi kukaba."?
Tace"aima wlh danban shillirashi nayi mashi fad'an y'an chanis ba,dasaikinga nafasa mashi baki.
Rannan ma damukayi fad'a da hinde saida nakusa 'kwa'kulo mata kunne,itakuma irin fad'an sharuhkan nayi mata."
Dr. Ru'kayya ta jinjina kai tana kallon isha'q wanda yayi tsuru,baiso mummy tagane halin zahra yanzu ba.
Yasanta dasakama ranta damuwa dayawa,
Tajuya ga zahra dake cema yaron"yaro zan kamaka,zamuje lungun bata kashi saina gurje maka baki da kashin kaji ha'koranka sun zube,banza latas karas kabeji masu kwana abakin titi d'an kabewa mai..."enough pls."
Dr. Ru'kayya tafad'a ranta a'bace"kewai waccce irin yarinyace,ahaka kikeson inje dake gidan bene kina dakarmun d'iyan ma'kota.tonikam ba'a haka dani,idan bazaki sake haliba lallai zan 'bata dake sam banason masifa kin ganni nan."
Zahra tayi tsit,sannan tace"nadena ai."
Dr. Ru'kayya tayi murmushi dacewa "gud girl"
Tashafi gashin kanta,
Tayima yara y'an kallo tsawa kowa ya kama gabanshi.
Itama mota tashige tana d'agama zahra hannu,lokacin gaf da magrib.
Motarsu na 'bacewa zahra ta hango su ummilolo da sauran 'kawayenta,taje suka kashe "tace yara albishirinku?"
Duka suka kasa kunne dacewa"goro fari 'kal"
Tarage murya sosai"amanatun amana wa'azabatun azaba,idan kuka tona taciku,kun yarda?"
Duk sukayi tsuru,
Tace "inbaku yardaba shikenan."
Sukace "munyarda zahra,"
Zahra ta tafa hannaye dacewa"yara kuka gayama wani saina dirji baki ehe."
"amanatun lauratun 'kwan kiyashi,yara ankusa yimun aure.
Duk suka zaro idanu waje suna kallonta sun sandai 'karya ba halin zahra bace,don sam tsage gaskiya take komai d'acinta.
Ummilolo tayi karfin halin cewa"mai 'karya"
Zahra ta'amsa da "d'an wuta abishi da duka har wuta lantarkin babalo da an kyasta sai wuta."
Duk suka ce"yeeeee dagaskene.
Nanfa aka zauna ana labarin aure,ummilolo tace "tab ashe zahra ke zaki dinga dafa abinci kiyita ci dayawa cikinko yayi 'kullumeme saimuga zahra ta haihu."
Sauran yara suka kwashe da dariya,
Zahra ido ya raina fata tace"ai sai in'ki cin abincin,inyita shan ruwa kawai."
Uwande tad'an fisu wayewa tace"kai wlh ance bacin abinci kesa mutum ya haihu ba."
Duk suka zaro idanu sukace "to menene"?
Tace inkun yarda amana,
Sukace sun yarda.
Tace"wlh yara idan kuka yarda namiji ya ri'ke maku hannu ya luliya tafin hannunku saikuga ciki yafito 'katoto,"
Zahra data gama tsorata tace"lalalala aikuwa Allah yasoni ban wasa da maza."
Daga nan aka rufe cafta,akace atafi satar kifi,wajen y'an kifi.
Haka kuwa akayi xahrace gaba sungama tsara plane na yanda zasu saci kifi,
Suna zuwa saitin wani mai kifi yakasa a faranti yana tsaye gaban kifinshi,
Zahra nazuwa wajen saitin kifin ta yanke jiki tafad'a akan farantin kifi,
Sauran yaran duk sukayi fuskar tausayi"wayyo zahra sannu,"
Mai kifi ma fad'i yake subhanallahi sannu yarinya.
Zahra ta bala riga akan kifi ta dumbuji uku,
Sannan tari'ke ciki"wayyo cikina ummilolo zoki tadani.
Ummilolo itace mai hijabi,dan haka tana zuwa zahra ta 'kunsa mata kifin a hannu,
Tasaka ariga,
Suka mi'ke suna kakka'be jiki zahra na d'angyashi.
Kamar ance maikifi ya kalli kashin kifinshi yaga anyimashi rani,
Yabisu aguje yana 'kwala masu kira,
Sukuwa 'kafa menaci ban bakiba,
Tuni sun sata.
Maikifi saida yayi Allah ya'isa saboda balagaggun kifayen suka d'auke,gashi ranar ba ciniki.
Awani lungu suka ma'kale zahra ta'amshe kifin ta finfincinar masu,tana la'kume sauran.
Uwande ta kalli d'an nata,taga na ummilolo yaninka nata biyu,tace"gaskiya anyi son kai,na ummilolo dayawa namu kad'an".
Zahra takaima bakin duka tana harararta"sannu mara gode Allah,da kud'in babanku aka saya kifinne,"?
Uwande tayi gum tana mamular kifin da aka bata kai da bindi.
Nan sukayi gaba,
Dai-dai kwalbatin y'an ganda suka hango wata budurwa da saurayi ana tafe ana rangaji suna gogar kafad'un juna,
Ummilolo ce tafara gani ta lakaci zahra,duk suka ware idanuwa suna mamaki.
Zahra tace"aje ajanye gyalen tsinanniya,"
Nanfa kowa tacire takalmi suka ma'kala a jijiyar hannayensu,suka d'age zani sama.
Saida budurwanan tazo saitin majalisar masu ganda,zahra tayi wuf ta fizge gyalen dake kafad'ar budurwar,
Suka auna aguje,budurwar tarasa yazatayi,ta waiga dacewa"honey dallah kabisu ka'amso man gyalena,kaga kayan jikin rabin 'kirjina duk awaje yake."
Saurayin yace"tabd'i,sarai nagane yarannan masu gudu kamar barewa,nida rannan gaban idanuwana suka janyema wata budurwa zani,yaseen da rarrafe tashige gida,camon ki kare wajen kawai mutafi asfa gayu d'innan kingane ai "
Ran budurwar ya 'baci kawai saita tsugunna ta fashe da kuka,
Me mutane zasuyi banda dariya da ihu...
*Nima nadara,nabi bayan zahra balbali zahra bala'i ta'ba d'aya kaga goma*

KUNA TARE DA MAMAN MEENAT, INSHA ALLAH
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀

BY MAMAN MEENAT

EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN FAROUQ, HYDR)

Muna miqa saqon ta' axiyan Hamma umar Allah ya jiqan shi yayi mishi rahma yasa mutuwa ta xama hutu a garesh, muma in tamu taxo Allah kasa muyi mutuwar shahada)




Chapter9.


Daga wajen tonon fad'a su zahra basic zame ko'inaba sai gida,saboda lokacin tuni angama sallar magirb,
Da sand'a tale'ka cikin gidan tace "inshigo'"
Umma dake ninke kayan da abba yacire dazu ta harareta dacewar "dawwama anan,har mahadi ya bayya,"
zahra taahigo kanta tsaye,tad'auki buta tafara alwalar magrib umma bata tankataba.
****************
Hadadd'en saurayin dake sanye cikin 'kananun kayan riga shirt dakuma wandon jeans kirar kamfanin Gucci,akwai kwatsetsen takalmin kafarshi mai shegiyar tsada gordon rush,
Face dinshi manne da space na Prada,watch na hannunshi dolce jikinshi manne da mayen turaren American crew.
Sumar kannan nashi ka rantse na macene saboda gyara da kula kai infarct isha'q 'karshene akan tafin hannayenshi kawai yakan kashen kud'i masu yawa,ha'koranshi kuwa akoda yaushe suna walwali da daukar idanu saboda time daya ware musamman domin su yakan je wajen wankin hakora lokaci zuwa lokaci.
Hatta da tafin kafar isha'q baya barinta face ya tsaftaceta da mayukan dake tsaftace 'kafa dasakata taushi.
Yanda yake wana steering kadai abin kallone,duk inda ya gifta mutane kan bishi da idanu musamman motar dayake tu'kawa new modern ce kirar mazda mx-miat abin saiya bada wani styles na daban.
Adai-dai kofar gidan sadiq ya matsa horn mai. gadin yale'ko dakai lokaci guda ya wangale get din yanama isha'q barka da zuwa,
Yafaka mota inda aka tanada don hakan,lokaci guda yazaro wallet d'in dake manne abayan aljihun jeans dinshi,yafiddo 2thousand yamikawa mai gadin,baijira sauraren godiyar damai gadin keyiba yayi gaba abinshi yana wana keys na motarshi.
Dai dai shiga harabar gidan yahad'u da hindu matar sadi'q da tsohon cikinta tana ganinshi tasaki murmushi"yau makuwa kayine isha'q yau agidan,"
Yasaki simple smile nashi kafin yace"yakike ya jiki kuma."
Tayi gaba tashige falo tana fad'in"banacin mi'ke,"
Bayanta yabi ya nitse cikin manyan kujerun dasuka zagaye falon yadauki remote yana canja channel daga Bollywood zuwa dstv yana searching 'kwallo,
Hindu tuni tacika gabanshi da kayan sanyi tasani yafi shan hollandia ko malt sune best drinks nashi.
Ya fincine hancin malt na gongoni yana zubawa a glass cup yana tambayar"ina mutumina ne."?
"yana jinka yanzu zaka ganshi yafito wankane yana shiryawa."
Isha'q yad'an dara,dacewa kice nazo asa'a dama tad'i zai rakani."
Idanu hindu ta fiddo waje"to gaskiya bari yafita ba,haka kawai wata budurwar ta kwaceman shi."
Tafad'a tana turo baki da alamar fushi.
Isha'q dariya sosai yakeyi yanacewa"aigara kishirya don mutumina hudu zaiyi,"
Maganar sadiq ta katseshi"a'a banganeba,wato kai ka'ki aure shine zakazo ka 'killen dannawa auren ko,"
Yafad'a yana dariya lokaci guda yana zaunawa kan hannun kujerar da isha'q yake kai.
Yami'kama isha'q hannu suka tafa duk suna dariya
Isha'q yace albishir fa nazo inyi maka,
Duk suka bishi da idanu sunason jin abinda zai fada masu,
Yasake kora maltina yana kallon sadiq wanda ya tsareshi da idanu,
"anbani zahra abokina,daga yau nakoma angon zahra "
Wata zabura hindu tayi"nice to hear isha'q seriously pls dagaske kasamu zahra?"
Isha'q ya saki dariya lokacin da sadiq yakai mashi duka yana fad'in abokina bakada mutunci wlh,wato saida ka rikita masu yarinya da salon wankanka ko?"
Amma duka sati biyu da had'uwa ace har anbaka saikace kaza,koda yake nasanka gwanin iya sarrafa soyayya but natayaka murna sosai abokina aikawai daga wannan wankan muwuce inga amaryar nan."
Hinduma fad'i take "nayi murna isha'q kaga nasamu 'kawa,"
Isha'q ya sauke numfashi.
Headache wlh typin din bayamun dad'i kuyi hakuri pls,
Tun d'azu nakeson typing amma kaina yana matsamun dafatan zaku gafarceni.

Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀

BY MAMAN MEENAT


EDITED:AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ)


Wannan shafin naku ne masoyan mijin kwaila, sai daku xamuji dadin cigaba da rubutawa in baku bamu hadin kai rubutun baxamu ji dadin yiba. Maman meenat nayi muku fatan alkhairi, t. Fulani ma baa barta abaya ba��


Chapter 10.



Isha'q yad'an murmusa yana shafar sumar kanshi,
Sadiq yace "Allah am serious abokina,yakamata inga wannan zahran tauraruwar mata.
Isha'q dake mi'kewa tsaye yana tafiya abinshi yana bashi amsar"zaka ganta very soon but not today,"
Hindatu tasakeyin dariya"isha'q bani phone number nata my be mu saba kafin tazo gida,idan dai tanada son jama'a."
Gaba yayi abinshi yana bata amsar"kidaice zaki koyamata gulma da kitififi kawa,"
Duk sukayi waje da sadi'q suna mata dariya.
Ajikin motar isha'q suka tsaya,sadi'q yana tambayar"abokina kamata yayi ashirya komai harkar girma kasan y'ammatannan yanzu suncika saka bidi'a a al'amarin aurensu."
"Banda zahra itakam batada wannan halin,"
Cewar isha'q wanda yabude motar yana kokarin tayarwa,
Sadi'q yabishi da kallon mamaki sam isha'q yawani canja kamar bashi ba,yatuna lokacin wancen auren yanda yaketa rawar jiki kusan koda yause maganar kenan yakeyi,koda yake watakila hakan nada alaka da rasa zahra dayayi akaro na farko yana tsoron rasa wannan zahran akaro na biyu.
Da sallama yashiga falon mummy tana zaune da hisnul muslim a hannunta,ta ajiye littafin bayan ta tsura mashi idanu fuskarta babu walwala,
Kusa da ita yazauna,lokaci guda yana matsa kafafunta"barka da yammaci mummy yau kindawo aaibiti da wuri hope lafiya dai".
Yatambaya dukkan hankalinshi gareta.
Tayi kokarin kauda damuwar dake kan fuskarta dacewa"banmaje asibitin ba yau banajin dadin jikina,nayi handling komai wa dr.aysha nasan zataji da komai "
Isha'q ya gyad'a kai yana kallon zalla damuwar dake fuskarta,
Yajuya ga hanan wacce take buga game hankalinta kwance yace"jeki d'akinki kiyi wasanki inason kadaicewa da mum".
Tamike abinta duka kanta yanaga game,
Yasake duban dr.rukayya akaro nabiyu yace"mum akwai zalla damuwa akan ni'imtacciyar fuskarki mai kwarjini pls mum sanar dani matsalarki i will save it insha Allah."
Kai ta girgiza mashi''banida wata damuwa isha'q kawai ina nazarin yanda zakaji dad'in rayuwar aure da yarinyar da kwata-kwata batasan me kalmar aure take nufiba,ina tunanin yanda zakaci gaba da rayuwar tazuranci alhalin kanada mata,ina nazarin yanda zaka zama *mijin kwaila*kuma mijin dazaiyi zaino,ina hango maka matsalar kada zahra tagirma ta gujeka bayan ta fahimta who you are.isha'q inajiye maka ka rainar ma wani mata".Kalamanta sun d'aga hankalin isha'q wanda idanunshi suka kad'a jajawur yana kallonta cikin idanu yawani koma kalar tausayi,musamman idan katuna duk soyayyar dayakema zahra saboda wata zahrance ba wannan fake zahran ba,
Ya sauke numfashi murya a raunane yace"pls mum don't say that,bana tunanin zahra zata gujeni bana fatan insake rasa zahra bayan tadawo gareni,kamata yayi kiyi courage d'ina akan zahra but kema nasan u feel loved her,nasani zahra tayi kankanta amma wata rana zata girma mum. Bajikin zahrane yake 'kayatar daniba da Zahra ko babu zahra zan iya kame kaina bazanyi abinda nasan addinina da al'adata bazasu soba."
Dr. Ru'kayya ta danyi dumm kafin tami'ke tadawo da littafin addu'o i tace"kaje kayi isthakara isha'q,nakuma saka malam babba yatayamu da rokon Allah akan zabin damuke so.amma nikaina inajin son zahra har cikin zuciyata sai dai halinta nake gudu wanda kowa yake kuka dashi"
Isha'q dake duba littafin yace"komai mai wucewane mum,kada ki kalli wannan ki hango alkairan dake tare da ita ba sharrintaba."
Mum tace hakane Allah yayimaka albarka,
Ameen yace gami da mi'kewa yahaye upstairs abinshi.
***************
Lala..la.la..lah.. ubanka ta tsinke mata azo asai nama sauran 'kashi da y'ar tsoka....muryar zahra data karad'e kaffatanin unguwar ce ke rera wa'kar zagi bayan d'an sabo ya kwasheta da mari,lokacin data jima 'kaninshi wankan gawayi.
Abinda yafaru kuwa shine hamid 'kanin d'an sabo,dayake gidansu dukansu fararene,shine yake tsokanar zahra dacemata wankan baqi asarar ruwa ko yayima kamar baiyiba,zahra dai tasan ko giyar wake tasha hamid yafi 'karfinta don garjejene zahra tarasa hanyar dazatabi tayi ramuwar gayya,hakan yasakata kama 'kanin su d'ansabo mesuna dady taje dashi gidan anty bilki wata makwafciyarsu datake shiri da zahra kamar me,don ita zahra dariya ma take bata.
To shinefa anty bilki tana bacci batasan shigar zahraba,tasamu gawayin da anty bilki take girki dashi tadaka a turmi lu'kwui ta yima dady wanka dashi tas duka jikinshi,bayan anmashi wanka da fararen kaya,
Yaron yafito waje yana kuka karantse aljanine.
Koda d'an sabo ya tambayi ba'asi yaro yace zahra ce,
Hargida d'an sabo yaje yakai kashedi wa umma,umma takama zahra tayimata dukan tsiya.
Dalilin dayasaka tatara duwatsu sunkai cikin fanteka ta tattaro basawanta wato su ummilolo suka dinga yima gidan ruwan duwatsu,zahra itake bada common datace "ajefaa"zakaji duwatsu nasauka bisa kwano kamar aradu.
Ashe d'an sabo yana bayansu shine ya lalla'bo ya cafke zahra ogar tasu,sauram suna ganin haka suka ranta ana kare,sukabar zahra wadda d'an sabo yake kwashewa da lafiyayyun mari har biyu.
Agabanshi tadinga ro'konshi yayi ha'kuri bazata 'karaba,mutane suna bashi hakuri yana sake d'uramata ruwan ashariya.
Aiko yana sakinta tafara antaya mashi style d'in zagi sunfi kala d"ari tun yana girgiza kai saida takai yakasa jurewa,babu irin kiran da umma batayima zahraba amma inaa zaginta dayafi bama d'an sabo haushi shine da'akace bananar
babanshi ta tsinke mata suzo susai nama .
Sai da hawaye suka zubo mashi,musamman dayaga abokananshi sunata kwasar dariya hada masu ri'ke ciki.
'kwafa yayi duk randa yakama zahra kashetane kawai bazaiyiba. .
Zahrama tahad'a mashi plane cewarta aitasan gidan budurwarshi saitaje ta kunyatashi...

Kuna tare da maman meenat, Aisha T. Fulani Insha Allah
[12:03, 24/11/2017] hm: *MIJIN KWAILA*����‍♀




by maman meenat

editing (maman faruq)

Chapter 11.




Saida ta tabbatar d'an sabo yashige gida sannan tayi 'kwafa dafadin"yaro tunda kataboni kata'bo bala'i kuma marin dakayimun ban yafeba har kabarinka na balbala da wuta."
Tajuyo danufin tafiya d'aga d'aya tahango motar anty lubnah tana fakawa da gudu tabi motar tana ihun"ga antin mu ga antinmu,anty lubnah tafaka mota tafito sa'be da ammar da yusra dake tafiya zahra tana zuwa tacafe anwar tana juyashi sama sosai,anty lubnah tace"a'a bani abina kada ki kayar mun dashi,zahra ta batashi bayan ta dungure kan yusra data tsaya tana kallonta dacewa"miye kike kallo dawani 'kwalakwalan idanu kamar na mage",
Yusra tasaka kuka anty lubnah ta harareta "zaki fara ko,jarababbiya uban me ta maki"?
Zahra bata tankaba ta aunkuce jakar anty lubnah tana tsalle"Allah yasaka kinzomun da alewar kano mai dad'innan."
Anty lubnah datayi gaba tana cewa"ahakan zanbaki alewa kina makarmun yara,"
Suka shiga gidan da sallama,umma tagama jefa dan wake tamike"lale marhaba da ba'kin kano."
Anty lubnah tashige kafad'ar umma dafadin"nayi kewarki mamana,
Umma sai murmushi takeyi y'ar farice shiyasa bata cika janta ajiki ba.
Ta amshi ammar tana mashi wasa, yayinda anty lubnah tashige daki tafara bude kwanoni"ummanmu mekika ajiyemun",
Umma tace"oh oh nida bansan da zuwanki ba, ai babanki kadai kika sanarwa shima baidade dakirana awaya ba yake sanarmun."
Dariya antyn tayi"kedai kawai umma donba hafsa ko mirja bane aida kinyi masu dambun nama",
Umma tace"ah to kema basai babanki yasayo makiba."
Anty lubnah dake rage kayan jikinta don zafi tace"ai umma naki nakeso ina missing girkinki mai rikitan tunani,gaskiya umma keta daban ce".
Umma tayi dariya "kyaji dashi ai."
Zahra kam tuni atsakar gida tagama yakicema jakar anty lubnah albarka wai tana neman alewar kano,
Umma taganta tana kiciniyar bud'e zif din baya tace "mezakiyi?"
[9/30, 1:50 PM] mum meenat: Bata dena 'kokarin bud'e jakar ba take bama umma amsa "alewar kano zan dauko,ai tace zata zo man dashi,"
Umma tace "shikenan kuma don tace zata zo maki dashi saiki kama binciken mata sirrin jaka wacce irin yarinya ce kene zahra.meke yawo cikin kanki haka wai",
Zahra ta turo baki gaba saiga hawaye,umma tayi tsaki"kyaji dashi shagwa'babbiyar banza magana ba magana ba kin iya hawaye amma idan masifarki ta tashi zakice sam bakisan wani lamari waishi kuka ba."
Zahra dai tayi gum,bata tankaba.
Anty murja ta kwad'a sallama suna tare da anty hafsat, umma tace "lale marhaban kamar kun had'a baki ga 'bakin kano can ma sunxo,anty hafsa tace ai umma tunjiya mukasan dazuwan ta baba yayimana waya cewar yanason magana damu musameshi gida da yamma".
Umma tari'ke baki"halin malam sai shi,nadaisan bazata wuce akan auren zahra bane,"
Duka suka kalli umma darashin fahimta dai dai lokacin da anty lubnah tafito daki ta rungume kannen nata"oyoyo my sisters yakuke."
Sukam yaranta suka amshe suna cirawa sama,anty murja nacewa"gaskiya anty lubnah yarannan kara kyau kawai sukeyi kinga yara kamar wasu jinsin larabawa."
Anty lubnah dariya take sosai"kedai murja bakya rabo da shirme "
Duk suka saka dariya,
Anty lubnah amsar hinan tayi daga wajen hafsat tana mata wasa duk suka shimfid'a tabarma waje saboda zafin garin.
Sai lokacin anty hafsa takula da zahrah wacce tayi kicin kicin darai kamar bata gansu ba.
Kamota tayi"oh my sister waya ta'bamun ke,halan umman muce ta bugeki?
Zahra ta idasa saka kuka hada turza kafafu akasa"ba anty lubnah bace taki sayoman alawar kano,kuma umma batayimata fad'a ba"
Anty lubnah dake zuge hand bag ta jefeta da alewar dake cikin ledar "amshi fitinanniya kada ki taramun makwabta."
Zahra tasoma tsalle tana godiya,don duk abinta tasan ka kyautatamata tayi maka godiya.
Tashi sukayi suka kamama umma aikin gidan tas aka gama,lokaci guda umma tana d'an tsegun tamasu yanda zancen aurar da zahran yataso.
Duk sukayi shiru kowacce da abinda take sakawa acikin ranta,can dai hafsat tagaza ha'kuri tace anya umma kunyi tunani wajen yanke wannan d'anyen hukuncin?
Zahra haryanzu yarinya ce karama koma baga hakaba halinta yasha banban dana sauran yara sa'anninta gaskiya batada natsuwar daza'ayimata aure yanzu,sannan shi isha'q meyake nema jikin zahra dayake rawar jikin auren ta umma."
Anty lubnah ta amshe"ato tunda sunyi alkawarin bazai kusanceta ba harsai takai munxalin hakan gud and fine,nadai san zaiyi *auren reno*ne,kuma atleast umma taji saukin bari-bari,nasan dr.ru'kayya inada labarinta asibitinta 'kanwar abban ammar take aiki gaskiya matar so simple umma batada matsala sannan zansaka asake bincike akanta dama family dinta gaba daya,tunda akwai wadda tasanta."
Umma ta gyad'a kai cike da gamsuwa"hakan yayi allah yamaku albarka".
Duk suka amsabda amin,
Itadai anty murja bata tsinka ba,
[9/30, 2:08 PM] mum meenat: Tunaninta yafi karkata akan yanda zaiyiyu ace zahra za'ayima aure tab bazata mance abinda zahra ta'aikatama jamil d'inta ba,lokacin yana zuwa zance wajenta.
Tasauke numfashi dacewa"umma na tabbata isha'q dakanshi zai maido zahra gida batare da ansakashi ba,cox zahra tawuce dukkan tunanin mai tunani yarinyar nan bataji umma,saita sakama isha'q hawan jini watakila."
Umma ta harareta"bakinki dai ya tsaya can,kidena mana wannan fatan cewa akayi zahran bazata kimtsu bane ta tabbata a mai wauta da masifa? Haba ku sakarma autata mara tayi fitsari mana."
Anty lubnah takwashe da dariya tace "uhm..uhm..umma
,zahrafa karshe ce,gashi kiri kiri zahra ta hana abban ammar zuwa kaduna idan ba kwakwaran daliliba,"
Umma sai alokacin ta kwashe da dariya tana girgiza kai,"abar tada maganar data riga tawuce dai."
Wuf anty hafsa tayi tace pls sister halan me zahran ta aikatama abban ammar ne,umma kam mikewa tayi tana murmushi"badani za'a maimaita wannan abun kunyar ba."
Cikin dariya anty lubnah take basu labari"ina lokacin da'akayima ammar shayi(kaciya)duka suka ce eh" taci gaba,kunsan nan kaduna na dawo saboda shine d'an farina bansan yaya'akeyi ba,
Duk sun za'ku sukace munsani mana haba,
Anty lubnah taci gaba da kwasar dariya tana cewa"abban ammar yazo dubashi,ranar wata weekend,ga abbanmu zaune akan kujerar umma,itakuma umma tana bakin gado zaune nikuma ina kusa da abban ammar gefenshi yayinda zahra take zaune tajingina jikinta da nashi .
Shikenan sai bayan angama gaisawa sai abbanmu yakada baki yace"ammar an girma allah ya raya,
Abban ammar yana jin kunya ya'amsa da amin.
Nakira ammar na d'age mashi riga abbanshi yaga kaciyar,yace aikuwa ta warke Allah yakaro lafiya duka muka amsa da amin.
Zahra dake gefe saitayi caraf tace"aikuwa abban ammar baka ganiba kaciyarshi ta warke kuma tadena jini,
Yace mata nagani mana.
Saita sake kada baki tace dashi"abban ammar kaima anyima kaciya?,
Anty hafsat da murja suka kwashe da dariya sukace kai zahra batayi ba.
Anty lubnah tace,aimu dake zaune saimuka daskare awajen saboda kunya,
Shikuwa abban ammar kasa d'aga kanshi yayi saboda kunya,
Umma tanama zahra tsawa amma ina sake tambayarshi takeyi "kaji anmaka kaciya?
Cike da jin kunya yace mata"anyimun zahra."
Zahra ta gyad'a kai cike da rashin yarda saikuma tace"me 'karya"?
Abban ammar yabata amsa "d'an wuta,
Kanshi yana 'kasa.
Abba dake zaune baisan sanda yakaima zahra dukaba,
Amma dayake batada wayo saitace "abbanmu naga kanata dukana menayi maka.?"
[9/30, 2:25 PM] mum meenat: Taci gaba da tambayar abban ammar"to kaciyar taka ta warke?"
Yad'aure fuska kamar zaiyi kuka yacemata "eh ta warke,"
Amma zahra bata 'kyaleshi ba, saida tace "to indai da gaske kake ta warke bud'e ingani .....
Abban ammar tuni zufa tagama rufeshi,yari'ke hannayen zahra dake 'kokarin kwance mashi zariyar wando,wai zataga kaciyarshi idan tawarke ,
Gaba d'aya dariya suke she'kawa,cikin dariya anty hafsa tace"thanks god,lokacin dana kawo nawa habibin zahra tana islamiyya thanks Allah".
Anty lubnah tace kinsan Allah saida umma tazaneta sannan ta 'kyaleshi amma duk da haka,saida tala'be abakin kofa tana cewa dama ashe ba'ayimashi kaciya ba yace anmashi .
Ke ranar baiyima su umma sallamaba,yasa kai baisake zuwa kaduna ba har yau.
Suma su umma ranar kamar zasu nutse don kunya.
Anty murja tace to itadai zahra watakila aljanunta nason ganin meke cikin jiki gareta,hakafa tayima jamil yazo wajena fira allah yasaka ba'agaban su umma bane,
Shida abokinshi na shimfid'a masu tabarma azaure tazo har zata wuce jamil yakirata irin ga 'kanwar budurwa d'innan yace wai tazauna suyi fira.
Zahra tazauna kusa dashi tanata wasa da duwatsun hannayenta shikuma yana tsokanarta.
Can idanunta suka sauka akan abokin jamil wanda yasaka dogayen kaya,gashi riga ta tattare sai gaba d'aya halitar jikinshi ana ganinta.
Zahra ta lura don haka ta kalleshi lokaci guda takai hannunta idanunta waje alamar mamaki tace"yaya menene acikin wandon abokinka, ,
Gaba daya su anty lubnah suka saka salati,anty hafsa tace dama kince 'kaniyarkice aciki ,
Murja tace "anty ina nake da bakin magana,wlh gida nashige nabarsu zaure suma suka sa'be babu shiri.
Har yau abokin baya iya hada idanu dani
**************
Bayan sati guda aka saka ranar auren zahra da isha'q watanni biyu masu zuwa...
Zahra itace mai raba minti,duk inda taje akace na menene saitace nice za'ayima aure,ummana tace kuzo mata biki......
[12:03, 24/11/2017] hm: MIJIN 'KWAILA ����‍♀



BY MAMAN MEENAT

EDITED :AISHA ABDULLAHI T. FULANI (UMMUN HYDR, FAROUQ) ��


ALHAMDULILLAHI ALA KULI HALIN

Chapter 12.







Acikin kaf dangin umma dama na abba babu wanda baisan da maganar auren zahra ba,
Kowa mamaki yakeyi nayanda abba zai aurar da kankanuwar yarinya kamar zahra abun saikace a film kokuma a novels.
Maganganu kam umma da abba suna shansu amma dayake abba kaifi dayane saiya saka tsumma ya toshe kunneshi daga maganar mutane yariga ya'amsa cewar yabada zahra tokuwa bazai mayarda hannun agogo baya ba.
Wannan kenan..
Zaune take cikin office dinta,gabanta akwai tulin files na patient wanda take dubawa sai dai azahiri kallo daya zakama kawayar idanuwanta kagano tsintsar damuwar dake makale cikin dattijuwar fuskar tata.
Fara tattara files din gaban nata takeyi bayan tamanna dan glass din idanuwan nata,
Gafe guda tana makala hand bag dinta a hannu,
Jin kwankwasa kofa yasata dakatawa lokaci guda tazubama kofar idanuwa bayan umarnin shigowa data bayar.
Kyakyarwar macen tashigo itama kamar dr.ru'kayya sam babu uniform na asibiti jikinta,farace tas da ita,doguwa sosai tanada manyan idanuwa dakuma yalwar gashin kai.
"dr.aysheh ",
Dr.ru'kayya takira sunanta idanunta fes akan fuskarta,
Matar ta karaso bayan tasamu matsugunni a kujerar dake fuskantar ta dr.rukayya,
Atare suka sakarma juna murmushi kafin dr.aysha tafara gaida dr. Ru'kayya,
Duka suka danyi jumm suna duban juna,
Dr.aysha ta kawar da shirun dake tsakaninsu tahanyar tambayar dr.ru'kayya damuwar datake yawan gani kwance a fuskarta cikin kwanakinnan.
Numfashi dr.ru'kayya tasauke kafin tace"abokin kuka shi'ake gayama mutuwa aysherh hakika ina cikin damuwa dangane da aurennan da isha'q ya jajibo,anawa ganin kamata yayi isha'q ya natsu,yasamu macen dazata kwantar mashi da hankali amma zahra kam tayi kankanuwa dayawa a matsayin matar isha'q wanda yakeda akalla shekarun dasuka tayarma talatin."
Saida tadan tsagaita dr. Aysherh tad'ora dafadin"nifa ru'kayya sainake ganin duka laifin abinnan yana akan wuyankine,bayag
a haka nisam banga dalili kokuma hujjar dazaki biyema isha'q akan aurennan ba,yaso zahra kuma yarasa zahra kamata yayi

Please Login or Register in order to submit comment