Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fasa sonka wallahi."
Shi ma ya ja baya yana tuntsura dariya dan yasan laifin da ya yi ta fasa son nasa. Ya sha gabanta yana ci gaban da dariyarsa, yace mata.

"Wai me yasa daga na yi Dan karamin laifi kike cewa kin fasa aurena? Idan kuma mun ji auren idan na yi laifin me zaki dinga fasawa?"


Ta fara kokarin goge hawayenta tana kau da fuska. Ya kuma kasa kai yana dariya ya ce.

"Rahma kar ki bari na saba da kukanki har ya zame min jiki, ki daina cutar min da kanki ta hanyar damuwa da abinda bai kamata ya same ki ba. Ina muka kwana, ya ya Halliru?"

A nan ne ta kara fashewa da kuka cikinsa ta ce.

"Yau kwanan sa biyu da rasuwa!"
Aliyu ya yi mutuwar tsaye, amma zuciyarsa ta tsayar da aiki ne bayan ta rasa abin da zata yi, KUKA KO DARIYA?


Dariya zai yi domin Halliru ya mutu ya saukaka masa dawainiya da fafutuka, ko zai iya kuka ne dan sabo da Halliru da kirkinsa, ko kuma kukan kishin kukan mutuwar Halliru da Rahma ta ke zai yi? Ko kuma tasa mutuwar zai wa kuka kafin ta zo.

Da ya yi dabara duk sai ya kori kuka da dariyar da fuskar jimami ya ce.

"Ayya! Allah ya yi masa Rahma, me ya kashe shi?"


Furtawa kawai sai ta kuma fashewa da kuka. Takaici duk ya cika zuciyarsa, amma haka ya zura ido yana kallonta har sai da sonta ya raunana zuciyarsa da tausayi sannan ya katseta a sanyaye.
[2:54PM, 2/24/2018] ‪+234 703 300 1537‬: ♦🔸♦🔸♦🔸♦🔸
*NA SAN DA BAMBANCIN*
Page 31


*KAINUWA
®






*Na*
*Shopiee*
*Ummu Shukran*







*Ya zama dole na gaishe ku muta ne na kainuwa writers Allah yabar kauna har karshen abada muna tare for ever🤝*





"Ya isa, wannan kukan ya isa, kuma nasan ba zai dawo miki da halliru ba."


Ta kokarta cikin kukan tace. "Shi tasa ta kare, kaina kawai nake tausayi, ina jin a raina da wuya idan rayuwata ba ta kare cikin kunar rai da bakin ciki ba."


Ya yi dira-dira a rikice kamar zai rungumeta, sai kuma ya nutsu cike da tausayi ya ce.

"Tsayin rayuwatazan kare duk wani abu da zai kona ranki Rahma, kar ki yanke kauna, idan dai kina tare da ni, iyakar karfina ba zan barki ki yi bakin ciki ba."

Ta fara girgiza kai da murmushin yake.

"Ban San da yadda zata kasance har na sami farin cikin da kake tanadar min ba, Wanda yake-kashen mutane a kaina ya bayyana,dan sarkin dorin rugar sama da mu ne, shi kuma ya kashe halliru ya danna shi ruwa a kogi, har sai da ya mutu.


Asali shi ne Wanda ya fara fitowa ya na sona tun ina karamata, ya yi ta min toshi har tsawon shekaru, amma rashin tarbiyyar gidansu ya sa Baffanmu ya hana shi aurena, kowa ya yi zaton zai yi tawaye a wannan lokacin amma sai aka ga salin alim ya janye jikinsa ko duriyarsa ma ba a cika ji ba a rugarmu.

Ashe shi ya dinga bin dare ya kashe sale, da Tanimu, babu wanda ya ko zarge shi sai da layin kisan sa ya zo kan Halliru suka yi a gaban mutane cikin bacin rai da cika baki kuma ya fadi abinda ya yi.

A washe garin ranar ne kuma aka tsinto gawar Halliru a kogi."

Aliyu ya jima cikin nazari, sannan ya ce.

"Me yasa ba za'a mika shi ga hukuma ta hukunta shi ba?"

Ta karkada kai tana tabe baki.
"A yanzu ya bar garin, na tabbatar kuma sati daya ya yi yawa zai dawo, kuma idan ya dawo sai ka ga an rasa wanda zai yi masa ko mugun kallo.
Ai sun saba ko musu ba ayi da yan gidansu sai su illata mutum da mugun asiri..."

Aliyu ya debo wani dogon tsaki, ya katse ta.
"Dan Allah bari yi min maganar banza, duk jarumtarku ku dinga shakkar mutun daya......"

Ta yi sakare tana kallonsa, ta ce.
"Sihiri gaskiya ne..."

Ya tare ta da fadin.
"Allah ma gaskiya ne, ina tabbatar miki mutum na karshe ya kashe a masu son aurenki, ko ya sha giyar wake ba zai iya zuwa muhallina ya kashe ni ba, ke ko muhallinsa naje na rantse miki ba zai iya kashe ni ba, kuma ko da shaidan yake bautawa ba Allah ba akan tsafi, kar ki kara yi min maganarsa.

Yanzu me ake ciki?"
Ta kalli gidan Dagaci da hawaye, tana nunowa da hannu.

"Jiya na ji rade-radi a gidan Dagaci ya yi kiran baffanmu ya tabbatar masa zasu hukuntashi idan aka kuma rasa rai a kaina, saboda haka lallai zuwa yau ya aurar da ni ga wani.

Dazu kuwa Dagaci ya aiko har gidan aka kira shi, nan da nan kuma naga an tashi harkar biki a gidanmu, ba zan yaudari kaina ba, na sani ana fitowa masallaci sallar azahar za a daura min aure da duk wanda ran mahaifina ya kawata masa."

Yana saurarenta sannan zuciyarsa na shirya masa mafita,dan haka tana direwa ya bi turbar gidan Dagaci da kallo, sannan ya kama kafadarta yace.

"A can ke nan kike tunanin za a daura auren?"
Ta janye jiki.


"Ina tsammanin haka, musamman idan an yi gudun rigima tunda shi Dagaci ana ganin kimarsa ba za a tashi hayaniya a gidansa ba."

"Ok, yanzu maza ki koma gida, in Allah yaso zaki sami labarin da ni aka daura."

Bai jira cewarta ba ya nufi motarsa da sauri ya bude bayan motar ya dauko keken da ya kawosa Musa yana faffarke ledojinsa, sannan ya rufe bayan motar ya dauko makullin keken a cikin mota ya rufe komai ya matsa _security_ na motar, sannan ya hau keken ya waiwayo ya dubi Rahma da ke tsaye rungume da hannu tana dubansa.

Ya dago mata hannu da dan daga murya.
"Ki tafi gida mana, kar ki kara fitowa kin ji?"

Ta daga kai sannan jiki a sanyaye ta gangara ta dauki hanyar gidansu.

Aliyu ya sami Dagaci da baki kamar yadda ya yi hasashe wato dangin Rahma, mahaifinta da kannensa, sai wasu dattawan gari. Dagaci ya nuna mamakin ganin Aliyu kwarai, sai dai bai cika masa tambaya ba, ya karbe shi da mutunci da girmamawa, shi kuma Aliyu ya dinga bin dukkan dattawan nan har da mahaifin Rahma yana ba su hannu suna gaisawa, duk sun ga tsaurin idonsa, domin duk wajen babu Wanda bai haife shi ba, amma ba tare da shakka ba ya ba su hannu, sai dai wasu a ciki sunyi masa uzuri, musamman wadanda suka yarda rayuwarsa daban, tasu daban.


Aliyu ya nemi guri a tsakiyarsu ya zauna, Dagaci ya dube shi a tausashe, ya ce.
"Lafiya dai ko?"
Aliyu ya kada kai.
"Lafiyar ke nan, amma akwai abin da ya kawo ni."


Cikin kulawa Dagaci yace.
"To ko zasu bamu wuri."
Aliyu ya girgiza kai da Sauri.
"A'a, ka gama da su mana."

Dagaci na dariya, ya ce.
"Wadannan nan ZANU wuni da su, wani rikici ne ya ki ci ya ki cinyewa Muke son cinye shi yau."

Aliyu ya yi dariyar basarwa, yace.
"Shi ke nan sai a cinye shi da ni."
Duk aka yi dariya aka mayar da abin raha, Aliyu kuma ya dora da cewa.

"Rikicin shanu ne ko na gona?"
Dagaci ya amsa kai tsaye.
"Wata yarinya ce samari ke kashe juna a kanta, ka san yadda al'adarmu ta ke ana fitar da gwani ne wajen shadi. To wannan ya gagara, daga an fitar kafin auren sai a kashe manemin, shi ne a yau muke son yinta ta kare, a fitar da wani ba tare da gwada kwanji ba kawai a aura mata idan aka ganta da aure kowa ma zai hakura."

Cikin dakewa Aliyu yace.
"An taba kama Wanda ya yi kisan?"
Dagaci ya amsa.

"A'a, yanzu dai an sami wanda ya yi har da kirarin wadancan kashe-kashen, sai dai us tsere daga zarar ya dawo kuma za a kama shi da izinin Allah.
Kaga mahaifinsa nan ma zaune."
Dagaci ya nunawa Aliyu wani mutum dattijo, kansa fari tas! Yana sanye da shudayen kayan saki.

Aliyu ya bi mutumin da kallo cikin tsana a ransa, ba tare da shakka ba ya ce

"Oh, wacce irin shari'a kuke? Me yasa ba za a kama mahaifin nasa ba, in ya so shi sai ya nemo dan nasa?"

Gurin ya yi tsit, kowa na kallon Aliyu, sai mahaifin Halliru da ke wajen be ya rausayar da kai alamar (nima haka na gani).

Nan take dattijon nan ya fara hararar Aliyu da wani irin kallo, Aliyu kuma ya dubi kwayar idonsa kai tsaye yana karanta masa( nafi karfinka).

Dagaci ma akwai alamar shakkar mutumin yake, domin nan da nan ya turbude maganar.

"Haka ne, amma mu yanzu abin da ke gabanmu shi ne, kawar da yarinyar daga Datsa, idan mun gama da batunta sai mu shi ga wan. Ga mahaifan samari uku na nemawa 'ya'yansu, ga kuma waliyyanta."
[2:55PM, 2/24/2018] ‪+234 703 300 1537‬: ♦🔸♦🔸♦🔸♦🔸
*NA SAN DA BAMBANCIN*
Page 32


*KAINUWA WRITERS ASS*
®







*NA*
*Shopiee*
*Ummu Shukran*
Dagaci na nunawa Aliyu su daya bayan daya, kannen mahaifin Rahma biyu Madu da Nakuri da kuma mahaifinta Malam Shehu, kana ganinsu duk ka ga jinin Rahma.

Aliyu bai dade yana nazari a Kansu ba, ya kara gyara zama, idonsa cikin na Dagaci ya ce.
"Mene ne sunanta?"
A sanayaye Dagaci ya amsa.

*"RAMATA*"
Aliyu ya kara gyara zama muryarsa fes ya ce.
"To ga ni na zama na hudu cikin masu neman aurenta, kuma ina wakiltar kaina ne."

Gurin ya kara yin tsit tamkar mutuwa ce ratso wajen, sai kallon-kallo ake.. Da kyar Dagaci ya kokarta ya ce.

"Da gaske ko da wasa."
Aliyu ya ce.
"Da gaske nake, dama can abin da ya kawo ni ke nan.
A zuwan da na yi na ga Ramata, son ts kuma ya sami muhalli a zuciyata na tafi da kunar ran asarar soyayyarta da zan yi. Da zuciyata ta gagara jurewa shi ne yau na dawo da zumar neman salama da Halliru ya fansar min da sayayyarta. To kuma cikin ikon Allah ina dira a rugar nan sai na sami labarin Allah ya yiwa Halliru rasuwa, shi ne na nufo nan dan na zantar da kai kudirina."

A'a! Wajen ya kara daukar tsit, kirjin kowa yana bugawa, sai mahaifin kalla makashin Halliru ne ya ke kule da Aliyu ya muskuta ya ce.

"Kai amma jama'ar garin nan kullun kara shahara suke da tsegumi...."

Mahaifin Halliru ya tari numfashinsa a sike.
"To mutum ya yi abin kirki ma ake tsegumi bare ya yi mugun Abu?Ai dole a yada kowa ya yi tir!"

*************
Dagaci ya tsawatar ta hangar dakatarwa da hannu, shi Kansa ya rasa ta inda zai kwaso maganar da ta kamata, ya yi shiru sai sauke numfashi ya ke tsawon lokaci.

Mahaifin kalla ya mike ya debi takalma a hannu yana fadin.
"Dama ai karshen alewa kasa, idan an hana dan gari mai asali, ai sai a ba wa mai sana'ar yankan mutane yana kudi da su."

Ya fice yana ta faman mita da maganganu bakake. Wajen ya kama shiru fiye da sakanni talatin, sannan Dagaci ya nisa yace.

"Ku yi hakuri dan Allah, ku dai ba bakin sanin halin mutumin can ba ne, sai dai kawai mu ci gaba da kai kararsa wajen Allah."


Wani a cikin su ya ce.
"Ga dan banzan karfin hali, wai shi tsakaninsa da Allah ya zo neman a aurawa mugun dansa, sai ka ce daga turu aka kwanto mu...

Babu mai karfin halin amsawa mutumin nan, sai Dagaci ya dubi malam Shehu ya ce.

"Kana jin batun malam Aliyu, me za ka ce?"
Malam Shehu ya muskuta kai a kasa yace. "Ranka ya Dade, da dai a taimaka a bar wannan maganar..."

Dagaci ya tare shi. "Don me?"
Malam Shehu ya dukar da kai kawai, kafin ya yi magana mahaifin Halliru ya dan rusuna ya ce.

"Ranka ya dade a yi afuwa na koma wajen zaman makokin can."

A sanyaye Dagaci yace. "To shi ke nan, amma ba zaka tofa albarkacin bakinka akan maganar da Aliyu ya zo da ita ba, kamar yadda aka faro maganar 'ya'yan su umaru da kai?"


Mahaifin Halliru ya yi kasake cikin nazari, sannan a nutse yace.

"Da ina daga cikin mashawartan malam shehu, to tabbas da na bashi shawara muddin yana son rayuwar tasa diyar ta dore, to ya aurawa Aliyu Ramata ta bar garin nan ta bace daga idanun mugayen mutanen nan, dan ban fitar da rai ita ma zasu nemi ganin bayanta ba idan ta auri wani ba dansu ba. Kun fa san halin wannan mugun mutumin ...ku kuma ku gafarce ni."


Ya na nufin sauran mutane biyu da ke son a aurawa na su yaran. Ya ce.
"Idan fa tsakani da Allah za a yi, kuma idan mun kwantanta a kanmu cewa idan Ramata 'yar mu ce."


Kowa ya yi tsit, Dagaci na kallon malam shehu yana masa umarnin magana da ido. A dan rikice mahaifin Rahma yace.

"Idon akayi haka ai an gudu ne ba a tsira ba, me na sani game da asalinsa da tarbiyarsa? Kuma me na sani dangane da yadda zai iya rikonta? Sannan kun taba ganin aure irin wannan, ace yaro da kansa zai zo neman aurensa, kuma a bashi aure ba tare da waliyai ba?"


Dagaci ya sauke idonsa ga Aliyu, ya ce. "Kaji batun mahaifin Rahma, me za ka ce?

Aliyu ya gyara zama yace. "Idon ana son sanin asalina, ai bincika za ayi, akwai Musa ku nemo shi dan uwansa masinja ne a kamfanin abokin mahaifina, sai a kawo muku sama'ila kuji daga gareshi, maganar yadda zan rike ta kuma tunda ba gwada ni aka yi ba babu wanda zai dorar, ban taba aure ba bare a binciko gudun ruwana, sai dai kawai idan za a yi shahada a ba ni.

Maganar zuwa neman aure ni kadai kuma, wannan akasi ne tunda takanas ba dan na nemi auren na zo ba, idan kuma an gamsu za a ba ni, to awa biyu ma ya yi yawa zan gayyato waliyan nawa su karba min.


Dagaci ya kara duban malam shehu, wannan karon Nakuri ne ya yunkuro ya dubi Aliyu ya ce.


"Misali idan mun kawar da kai akan komai, da wacce fuskar zamu gane ribar da ka hango a neman diyarmu, tana 'yar kauye fitik! Kana dan birni kuma mai kudin da ya ci ya tayar da kai. Akwai tazara mai nisan gaske a tsakaninku, ina tsammanin zaman zai zama kamar na doya da manja ne."


"Ina tsammanin idan akwai cutuwa a tsakaninmu, to tabbas ni zan fi cutuwa, dan ita zata gaza da yawa daga muradaina, na tabbatar ita ba zata ci karo da sauyin da zai taba ran zama da ni ba. To amma duk da haka ni bansan komai ba, sai sonta. Na yarda kuma na rasa komai na tsira da ita."


Kowa ya sauke numfashi a wajen, Madu ma ya katse murmushin da biyu da yake.

"Ita ma akwai bangaren da tata cutuwar ta ke, Ramata na da alkunya, kai kuwa da Sauki, Ramata na da gwargwadon tarbiya, babu munafinci tarbiyarka ba ta yi mana ba."

Kai tsaye Aliyu ya amsa.
"Kowa a cikin nan da salon tasa tarbiyyar, ta gidanmu daban, ta naku gidan daban. Idan kun ba ni ita ma, tarbiyyar gidan mu ni da ita sai ta bambanta da naku gidan da kuma namu gidan ko ba ni kuka aurawa ba kuma hakan ce zata kasance."

Duk suka saki baki kawai suna kallonsa, mamaki da al'ajabi duk ya ishe su, ba ya magana cikin shakka, sannan bai yi nadamar kallon Mara kunya da suka yi masa ba.

"A ba mu lokaci mu yi shawara."
In ji malam shehu yana rusuna ga dagaci. Ya yin da dagaci ya yarje musu mintina talatun, suka duk suka fice, mahaifin Halliru ma ya yi sallama da su ya tafi, aka bar Aliyu da sauran mutun biyu, shi ma Aliyu ya dubi, Dagaci ya ce.

"Ka yi min izini na kira waliyaina su zo dan ina jin nasarar auren Rahma a jikina."

Dagaci ya yi dariya ya kada masa kai, don shi kansa girman fitsarar Aliyu ta ishe shi.
Aliyu ma ya mike ya fita, ya kebe ya kira mahaifina a waya ya kwashe masa dukkan labari ya kada masa.

Mahaifinsa bai so ba ko kadan, amma haka ya danne ya amsa masa da muryar murna, tunda bai kamata ya tauye masa 'yancin rayuwa da abin da yake so ba. Yace masa.

"Ok, zan Sanar da uncle muktar yanzu su biyo jirgi zuwa kano, sai su dauki motoci su shigo.
Kamar nawa zasu taho maka da shi, ko baka bukatar kudi masu yawa?"


Aliyu ya ce da shi.
"Daddy kawai su zo da kudi masu tsoka, dan Allah su yi Saudi."

Bai ma jira cewarsa ba ya zuge wayar ya koma fada. Bai jima ba su malam shehu suka dawo. Madu ya fara zano sharuddansu biyu.


"Wanna tabbaci muke d shi na cewa, ba salwantar da rayuwar 'yarmu zakayi ba?"

Aliyu ya amsa masa.
"Ai ba ku da wayo ko dabara a kanta, sai abin da ubangijinta ya zabar mata. Idan fa bana son yaba muku kaina ke nan ko kuma fadar abinda idan ba ku gamsu ba zaku karyata."


Madu ya gyara zama yace.
"Akwai tarin kudade da zasu hau wuyanka na biyan dukkanin samarin da suka yi dawainiya da ita..."

Nan ma ya tare.
"Babu matsala a tara jumullarsu kudin zan biya."

Aka kara daukar shiru a wajen. Sai can jumawa Nakuri ya motsa ya ce.
"Zamu aura maka Ramata bisa sharadin idan mun ga cutarwa daga gareta zamu dawo da 'yarmu gida, yallabai ka shaida wannan?"

Nan ma Aliyu ya ce.
"Ku ba ni amanarta, zaku same ni mutum mai nagarta da rikon Amanda."
[2:55PM, 2/24/2018] ‪+234 703 300 1537‬: ♦🔸♦🔸♦🔸♦🔸
*NA SAN DA BAMBANCIN*
Page 33



*KAINUWA WRITERS ASS*
®





*NA*
*Shopiee*
*Ummu Shukran*










*Yan uwa Rabin jiki ban ga kamar ku a fadin duniyar nan ba*
*Anty binta*
*Anty samira*
*Nabila*
*Badiya*
*Mamy*
*Ummy*
*Zainab*
*Hadiza*
*Aisha*
*Allah ya bar zumunci duniya da lahira*







Sai karfe biyar Rahma ta matar Aliyu, gari ya dauki dumi da zugugun wannan aure fiye ma da na rikice-rikecen auren, musamman na ganin Aliyu kamar ba musulmi ba.
Nan da nan aka hau zugugun yadda yake hannu da surukansa, maimakon durkusawa kasa ya gaishe su, shi ya nemawa kansa auren kai har ma da masu rantsewa shi ne waliyyin kansa, saboda tsabar zakewar da ya yi akan auren.

Babu laifi su uncle muktar sun yaba da karbar da aka yi musu, tamkar auren shir, haka suka dinga hatuna da vedio coverage, ranar marokon garin har kasa godiya suka yi saboda kudin da suka dinga zuba musu, kai har wanda bai gaji rokon ba ranar ya yi haye.


Mutan rugar nan ba su gama yanke kauna da fitsarar Aliyu ba sai da yamma dab da magriba da danjin Aliyu suka tashi komawa, ya nuna fau-fau ba za shi gida ba sai gobe, ga kafarsa ga ta Ramata tunda ance ba za basu ita yau ba.


Babu wanda ya nemi matsa masa a dangin nasa, suka kama hanya suka yi tafiyarsu.

Har karfe goma Aliyu na tare da su Musa da wasu da yawa matasan garin kofar gidan su Rahma, ana ta wasannin gargajiya na murnar aure iri-iri, kowa cikin nishadi sai haba-haba suke da Aliyu, musamman saaboda barin kudin da take musu.

Can rade-radi ya fara tashi, ga zugar 'yan rugar su kalla can sun yi shirin farauta,
irin wanda suke fakewa.

Labarin na zuwa kunnen Aliyu ya dubi Musa da kabiru wa yayan Rahma yace.
"Wannan ne dalilin da yasa na ce ba zan tafi gida ba, saboda kar na yi biri boko, na saki baki a can nayi bacci, wani ya lallabo ya kashe min mata."


Musa da suka saba wasa da shi, yace.
"To yanzu da ka zauna, ina zaka ganta bare ka ce kana gadinta?"


Aliyu ya amsa da karsashi yana duban kabiruwa.
"Kabir a gidan ku akwai jarumin da zai yi kwanan zaunen tsare min Rahma? Idan babu to tun wuri ka je ka fada kar a raba mana makwanci."


Kabiruwa ya dauki abin wasa, saboda cikin dariya ya yi maganar. Ya ce.

"Waye zai hana idonsa bacci ya yi wani gadinta? Wai me kake tsammanin?"

A nutse Aliyu ya ce.
"Dazu a gaban dagaci wani ya yi batun da yake nuna, kalla zai iya kashe Rahma kowa ya rasa, wannan yasa na ji bazan iya sakaci da ita ba."

A sanyaye kabiruwa ya ce. " kowa ma yasan da wannan, sai dai da kyar wasu zasu fahimce ka, fitsararka kawai za a gani, saboda haka ma ka bar wannan maganar...."

Aliyu ya tare shi da riko kafadarsa da kyau.
"Me yasa zan barta? Dan kar a ga fitsarata? Wa ya fada maka ni ina gudun bakin mutane? Idan aka kashe min ita akwai wanda zai dawo min da ita da surutunsa ne? Saboda haka mayar da hankali da gaske nake, ka je kawai ka sanar musu, idan kuma ba haka ba, ni da kaina zan sami Baffa."


Musa ya shigo maganar shi ma jiki a sanyaye.
"Aliyu, sai fa kana dan sassautawa, dabi'armu ta bambanta da taku...

Kawai sai Aliyu ya yi tafiyarsa ya ba su guri, sunyi zaton wajen baffan nasu zai tafi, kabiruwa ya biyo shi da Sauri ya na cewa.

" A'a bari zan je na yi musu maganar."
Kabiruwa ya je da wannan ga wata yakumbonsu, saboda tsabar tsorata sai da gudawa ta tsuke mata, haka suka dinga kumbiya kumbiya da maganar a tsakaninsu dangi, har dare ya fara tsalawa ba su sami madogara ba.

Ana cikin haka ne labari ya cimmasu ga tawagar farautar rugar kalla can ta doso wajen shagalin bikin shading da ake a halin yanzu a kofar gidan su Rahma.

Hayaniya ta kaure kwarai a wajen sai guje-gujen shigowa gida daukar makamai matasa suke suna ficewa. A cikin gidan kuma hankalin mata ya yi mugun tashi.

"Ka ga Aliyu kawai ka shiga cikin gida."
Iro ya fada lokacin da samarin suka hada kai suka shawarta zuwa tarar su kalla kawai ayi kare jini biri jini. Aliyu yana tsakiyarsu sai ya fara magana cikin karfin gwiwa.

"Suna amfani da bindigar farauta?"
Wani daga cikin su yace.
"Matsiyata ina suka ganta, ban da wukake da sanda ba su ajiye komai ba, sai mugun Abu fal ciki da kurin su sun fi karfin farauta da bindiga."

Aliyu ya yi murmushin nasara, ya ce.
"To ku yi zamanku, kar ku tare su, ba na so wani ya rasa ransa ta dalilin aure na, ina fatan sun san bindiga?"

Aka ce, "sun sani " Aliyu ya ce.
"To ku barni da su, tsorata su kawai zanyi, mutum uku su zo mu je."

Bai jira cewarsu ba ya kutsa ya fito, kusan kowa ya taka zai bi shi amma da yake suna da tunani da hadin kai da Kansu suka dinga rage Kansu har sai da suka rage mutum ukun da suka take masa baya. Ba su yi wata tafiya mai nisa ba, suka yi kicibus, matasa ne guda tara, ciki har da kalla da ake maganar ya gudu, suna dauke da sanduna da takubba, ga karnuna kusan ashirin. Ya zaro bindiga daga aljihunsa ya daga ya harba sama, kararta ta karade gaba dayan dajin, karnuka suka tarwatse suna haushi, masu su ma duk sun gigice, sai dai babu wanda ya yi kokarin gudu, illa sun daskare waje daya kawai suna tsuma. Aliyu ya kara kusantarsu ya bude murya ya ce.

"Duk wanda ya yi kokarin yi mana ta'addancin ko wallahi zan fasa cikinsa."

Ya kuma sanin bindigar sama ta kara gauraye dajin, ya fara zagaye, su duk suna tsaye.

"Da na sani na farko da zaku farayi a duniya idan ma ba ku taba yi ba, shi ne ku ce zaku kashe ni, ina shawartarku kar ku fara domin Ina da gatan da idan kun kashe ni to kafatanin zuriyarku ba zasu biya fansata ba na rantse. Ban shigo cikinku aure dan in ina makaskanci kamar ku Ba, sai dan amfani da damata kawai ta mallakar duk abin da na so.
Ina kalla?

Ya fada da tsawa da kausasshiyar murya.
Duk suka yi tsuru tsuru sai dai babu wanda ya nuna shi, Aliyu ya dora cikin bacin rai.

"Idan mahukuntan garinku sun kasa hukunta ka game da kashe-kashen da ka yi, to ni zan kawo jami'an tsaro daga birni, sai sun bi hakkin jini halliru dan na zan yafe shi ba, kowa ya bace min da gani!"


Ya kare cikin tsawa, sannan ya kara sakin harbi.


Ai ba bu wanda ya tanka suka juya gwiwa na rawa, su kalla sun fi kowa sanin sharrin bindiga a gamuwarsu da 'yan fashi, wata fitarsu ta farko zuwa kudu sai da shanu mota guda da wani mai ido a can ya yi musu jagora sai da suka kullo kudin

Please Login or Register in order to submit comment