Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ๏ปฟ * ๐Ÿ‘‘YARIMA SUHAIL.๐Ÿ‘‘*

_STORY,WRITTEN &EDITED BY._
*SIS NERJA'AT.*

_COMPILATION BY._
*HAWWA M.U (ยฎEAL $MASHER).*
?๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘

_*YARIMA SUHAIL*_

๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘



_*Written By~Sis Nerja'art*_



_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_




_Jinjina agareki my hafnan ina tayaki murnar fara new novel d'inki *HIBBATULLAH* akowane lokaci kina a โค๐Ÿ‘ˆ๐Ÿป d'ina_




_~Sak'on gaisuwata agareki my blood sis *Aufana* sonki a cikin jinin jikina yake๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜~_


*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ยฎ*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE ๐Ÿ˜˜ HEART TORCHING โค TEARS OF SORROWS ๐Ÿ˜ญ CURDLES ๐Ÿ™‚ GIGGLES ๐Ÿ˜ AND MARRIEGE THINK๐Ÿ’‘
*JUST GIVE US FOLLOW....*โœ”



_Wannan page d'in nakine Sainah Ummun Meenal uwa tagari Allah yabar mana ke๐Ÿ˜_


page 1โƒฃ


garin gazban garine mai albarka da yawan mutane yana d'aya daga cikin garuruwan da ake alfahari da su.


sun kasance suna da babbar Masarautar da babu kamarta wajen girma da kyau sarkin garin ya kasance sarki mai adalci duk kud'in mutum bai isa yazalunci nak'asa da shi ba indai har yazalunta labari yazo ma sarki toh sai yad'auki mataki,


sarki umar yana son talakawansa sosai suma suna sonsa abun mamaki wannan sarki ya manyanta domin zai kai shekaru 76 ammah indai ba ka saniba sai kad'auka d'an shekara 50 ne, domin babu alamun tsufa a tare da shi idan dukiyarce ya tara, idan sarautarce yana d'aya daga cikin manyan sarakuna kai intabbatar muku wannan babbar Masarautar ko da me kazo anfika.


Sarki faruk matarsa d'aya dattijuwa dada, saidai abun mamakin duk mulkin nasa ammah 'ya'yansa biyu dukansu maza ne Ahmad shine babba sai k'anensa Abbas sun taso atare sun kasance suna son junansu.



saidai a tsarin mulkin garin indai sarki yahaura shekaru arba'in (40) saman karagar mulki toh d'ansa ba zai ta6a gadon mulkinba saidai babban jikan gidan, saidai idan babu jika namiji shine d'an sarkin yake hawa mulkin



lokacin da 'ya'yansa suka tasa yaza6a musu mata inda Ahmad ya auri d'iyar sarkin agadaz wato sultana Bilkisu, shi kuma Abbas sarki ya aura masa d'iyar d'an uwansa da yamutu yabari wato Sultana Sadiya.


A cikin babbar Masarautar kowa aka fitar masa da 6angarensa.


Suna zaune lafiya da matansu, inda sultana Bilkisu takasance macece mai hak'uri da tawakkali ga ta macece mai kyauta ta kasance mai son jama'a,


inda Sultana Sadiya takasance akasin haka domin bata son talakkawa suna ra6arta dan ma mijinta a tsaye yake sun d'auko hali irin na mahaifinsu, ammah duk da haka taci alwashin ita take da burin tafara haihuwar d'a namiji.



saidai kash sultana Bilkisu ita tafara samun ciki, hankalin sultana Sadiya ya tashi sosai ganin ita ko 6atan wata bata ta6a yiba,


Bayan wata goma sultana bilkisu tahaifi d'iyarta mace murna wajen iyayen ba'a magana hatta ita kanta sultana Sadiya tayi murna ganin ba namiji bane ta haifa.


ranar suna anyi shagali sosai kud'i sunyi kuka tsakanin masarautar gazban da masarautar agadaz anzuba naira sosai a inda yarinya taci sunan dada wato Asma'u ammah ana kiranta da husna.



Bayan shekara ukku Sultana bilkisu tak'ara haihuwa inda tasamu d'anta namiji kyakkyawa domin ita yabiyo kamar antsaga kara murna wajen su sarki ba'a magana hatta su kansu jama'a sun shaida wannan haihuwar domin sarki sadaka yadinga yi da dukiya sosai,

akasin sultana Sadiya da takasa 6oye bak'in cikinta turakar mijinta taje tasameshi a zaune yana ta kiran waya yana fad'a ma mutane, zama tayi gefensa tana kallonsa cike da takaici har yagama wayar sannan yakalleta fuskarsa d'auke da murmushi yace sultana akwai abinda kike buk'ata ne?

sultana sadiya d'auke fuskarta tayi daga kallonsa tace ranka yadad'e meyasa kake murna dan matar d'an uwanka ta haifi namiji kar fa kamance shine zai hau karagar mulki bayan ran sarki,

da mamaki sultan abbas yake kallonta yace sultana ba dai bak'in ciki kike ma d'an uwana ba dai ko?

d'aure fuska sultana tayi tace bak'in cikin me zanyi masa, naga kana ta murna ne mukuma kaduba kaga ko 6atan wata ban ta6a yiba bamu da d'a ko d'aya kuma kyau ace d'an kane zai gaji masarautanan.


sultan Abbas sakin baki yayi yana kallonta har takai aya sannan yace sultana inaso kisan wani abu wlh da zuciya d'aya nake son d'an uwana ban damu da sarautar da d'ansa zai hau ba domin nima d'ana ne sannan da kike magana akan rashin haihuwa inaso kisani Allah shi yake badawa ga Wanda yaso kuma yahana Wanda yaso ban cire rai ba idan da rabo nima zanga tsatsona, dan haka kar ink'ara jin kinyi wannan maganar, kibinneta daga nan da kika yi ta.

Mik'ewa sultana tayi cikin fushi tace daman nasan ba zaka ta6a fahimtaba ammah nan gaba dakanka zaka fahimci abinda nake nufi. wucewa tayi fuuu tafita tabar d'akin.


Sultan Abbas binta yayi da kallo har tafita sannan yagirgiza kai cike da takaicin abinda matarsa tayi yace Allah yashiryeki sadiya.





Ranar suna yaro yaci suna Umar sunan maimartaba ammah suna kiransa da suhail,


suhail yataso cikin gata domin yana samun kulawa sosai a wajen iyayensa da kakanninsa hatta shi kansa sultan Abbas yana ji da d'an nasu,

akasin sultana sadiya da ta tsanesa bata d'aukarsa sai idan gaban su Dada ne nan take nuna tana sonsa sosai, ammah a cikin zuciyarts ji take ina ma ace yamutu.


ahaka yataso cikin gata tun yana shekara ukku maimartaba yakesawa ad'aukosa akawo sa fada yazaunar da shi kusa da shi saisa suhail yataso ya shak'u da kakansa sosai.


Bayan shekara biyu sultana sadiya tasami ciki murna wajensu da wajebnsu sultan Ahmad ba a magana,


kulawa sultana sadiya take samu sosai daga wajensu maimartaba da mijinta hatta ita kanta sultana bilkisu tana bata kulawa sosai.
inda sultana sadiya take addu'a akan Allah yasa tahaifi d'a namiji.

inda itama sultana Bilkisu take d'auke da d'an k'aramin cikinta.



bayan wata tara sultana sadiya tahaifi d'iyarta mace ta yi bak'in ciki sosai ammah daga baya tahak'ura, murna wajen su maimartaba ba'a magana kowa ya nuna farin cikinsa,


ranar suna yarinya taci suna sumayya, anyi shagali sosai anci ansha.
inda sultana sadiya taci alwashin ta kowane hali sai d'iyarta ta auri sarki mai jiran gado .



bayan wata ukku sultana bilkisu tahaifi d'iyarta mace inda taci sunan mahaifiyarta wato Rahama,


tun daga lokacin babu wadda tak'ara ko da 6atan watane, sumayya da Rahma sun taso a tare komai nasu d'aya bacci kawai yake rabasu.



Yarima Suhail duk halin maimartaba yad'auko yatashi mutum ne mai tausayi kuma mai girmama na sama da shi saidai ya kasance bai da son hayaniya miskiline na sosai baya shiga abinda bai shafesaba baya da yawan fara'a sosai saidai ga wanda bai sansaba zai masa kallon mutum mai girman kai.

In ko kagansa a fada toh maimartabane yasa yaje ammah shi kwata-kwata baida burin yin sarauta, ko da dakagansa komai nasa irin na sarauta yakeyi.


tun da yataso abokinsa d'aya d'an waziri wato shahid tare suka taso tun suna yara sunyi makarantar arabi da boko a garinsu.


bayan sun gama secondary yarima suhail yanuna yanaso yafita waje yayo karatunsa, anyi daga sosai da maimartaba afin ya amince domin cewa yayi shi da zai gaji sarauta mezaisa yafita waje karatu, daga baya dai dakyar aka samu maimartaba ya amince inda yarima yaje india yayi karatunsa na likitanci inda yakaranci surgeon.


bayan shekara biyu akasha bikkin Gimbiya husna inda ta auri d'an chairman d'in garin anyi shagali sosai anyi bikkin da ba a ta6a irinsaba a garin, inda husna tatare a gidan mijinta
yarima suhail yaso yazo ayi bikkin da shi ammah iyayensa suka hana sukace yazauna yayi karatunsa.



Gimbiya Sumayya da Gimbiya Rahama sun shak'u da juna sosai saidai suna da banbancin halayya sumayya tana da wulak'anci sosai kuma ta tsani talaka yara6eta bata abota da kowa sai wanda yakasance jinin sarauta ko d'an wani attajiri.

akasin Gimbiya Rahama da takasance mai son jama'a kuma bata da wulak'anci kowa natane abinda yake had'ata fad'a da sumayya kenan ko a school.







Bayan shekara hud'u yarima suhail yakammala karatunsa yadawo k'asarsa ta haihu ya k'ara girma da kyau miskilancinsa ya k'aru da kagansa ka ga jinin sarauta,
murna wajen maimartaba da iyayensa ba a magana hatta kansu jama'ar gari sunyi murnar dawowarsa.
ba kamar abokinsa shahid da yayi missing d'insa sosai.


gidan sarautar hidima akayi sosai inda dukkan ma'aikatan gidan suka had'u adafa wancan asafke ad'aura wancan,

walima akayi ta azo agani hatta kansu talakawa sun ci sun sha,


Sumayya tun da tad'aura idonta akansa tace ai tayi miji ba zata auri kowaba sai shi ko da taje ma mahaifiyarta da maganar itama tayi murna sosai domin itama burin da take da shi kenan a rayuwarta inda tabata shawara akan taje tasanarwa dada.


sumayya ta d'auki shawarar da mahaifiyarta tabata dan haka tawuce tanufi 6angaren su maimartaba lokacin da tashiga d'akin dada zaune take saman kujera gefenta dama da haggu duk kuyangine suna ta mata hidima,


sumayya bisa kujerar da kaka take zaune taje tazauna tace ranki yadad'e 'yar tsohuwarmu Allah yak'ara miki tsawon kwana,

dariya dada tayi tace Ameen gimbiya ganinki da nayi haka nasan bakinki yana d'auke da magana,
sumayya murmushi tayi tace tabbas hakane ranki yadad'e akwai abinda yake tafe da ni.

kaka sallamar kuyanginta tayi duk suka fita sannan tatattara kallonta ga jikartata cike da kulawa tace ya ke sumayya inaso kifad'a min abinda yake tafe da ke nikuma indai baifi k'arfina zan taimaka miki.

sumayya duk'ar da kanta tayi cike da kunya tace dada daman akan yaya suhail ne,
murmushi kaka tayi jin an ambaci nagaban goshinta tace ina jinki me suhail d'in yayi?


sumayya tace babu abinda yayi saidai nice wlh dada tun tuni nakeson yaya suhail kuma ina tsoron intaresa da maganar dan nasan zai iya min wulak'anci saisa nace bari infara samunki da maganar wlh dada ina sonsa har cikin raina.


dada tunda sumayya tafara maganar kasa rufe baki tayi saboda jin dad'i, saida sumayya takai aya sannan dada tace masha Allah gaskiya naji dad'in labarin nan da kikazo dashi domin daman nima ina da burin hakan a raina ammah tunda har kikafurta da kanki toh ai shikenan.


sumayya kallon dada take cike da jin dad'i tace toh dada shikuma yaya suhail fa idan yace baya sona?


dada tace kikwantar da hankalinki zai ma soki domin babu yadda za'ayi nagida bai k'oshiba aba na waje ke dolene mane yasoki dan haka kikwantar da hankalinki shalele kamar kin zama matarsane kibari zamuyi maganar da shi da maimartaba.



sumayya cike da jin dad'i taduk'a takwashi gaisuwa tare da yin godia sannan tayi ma dada sallama tafito tanufi 6angarensu duk inda ta gifta tun kan ta ida isowa inda bayi da ma'aikata suke ake zubewa kwasar gaisuwa kowa tsoronsa kar tace yayi badaidaiba domin sunsan halin gimbiya sumayya da mahaifiyarta yi musu laifi abune maisauk'i, kowa yau yana mamakin yadda fuskarta take a sake sa6anin da dakullum take a d'aure.


dada ko da tasamu maimartaba da labarin shima yayi murna sosai inda yace zai gana da su gobe.





yarima suhail ne kwance saman makeken gadonsa inda shahid yake gefensa yana ta zuba masa surutu shi dai yarima daga uhm sai uhm-uhm bai cewa komai sai ma dannar wayarsa da yakeyi.

shahid ya k'ule sosai tsaki yaja yace kai fa matsalata da kai kenan sai ana yi maka magana kadinga share mutum kamar ba dakai akeba.

shuru yarima yayi yacigaba da dannar wayarsa takaici yakama shahid dan haka yafizge wayar, ganin haka yasa yarima yamaida idanunsa yalumshe.

shahid baiyi mamaki ba domin yasan halin abokin nasa tun suna yara.

knocking d'in k'ofar da akayine yasa shahid yabada izini da ashigo, wani dogarine yashigo tare da zubewa k'asa yana k'wasar gaisuwa shahid ne kawai ya amsa masa,

dogarin kansa yana k'asa yace Allah yaja da ran yarima mai jiran gado daman Maimartaba ne yake kiranka ya ce kasamesa a turaka,

yarima batare da yabud'e idonsaba yad'aga ma dogarin hannu alamun yatafi.

tashi dogarin yayi yace nabarku lafiya sannan yaficce daga d'akin.

shahid kallonsa yayi yana murmushi yace yau sarautar ta motsa kenan.....





_Comment_
*nd*
_Share_





_Sis Nerja'artโœ๐Ÿป_
๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘

_*YARIMA SUHAIL*_

๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘



_*Written By~Sis Nerja'art*_



_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_




*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ยฎ*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE ๐Ÿ˜˜ HEART TORCHING โค TEARS OF SORROWS ๐Ÿ˜ญ CURDLES ๐Ÿ™‚ GIGGLES ๐Ÿ˜ AND MARRIEGE THINK๐Ÿ’‘
*JUST GIVE US FOLLOW....*โœ”


_Sak'on gaisuwata agareku intelligent writer's Allah yabar k'auna๐Ÿ˜˜_



_My k'anwa janaf Allah yabar min ke๐Ÿ˜˜_




_*Wannan page d'in nakine Asma'u Yusuf Beji kiyi yadda kikeso da shi ina godia da kulawarki agareni๐Ÿ˜*_



page 2โƒฃ


Yarima suhail saida yayi kusan minti biyar yana a kwance sannan yabud'e idonsa ahankali yamik'e yasafka daga kan gadon, alkyabbarsa yajawo yasa batare da ya kalli shahid ba saida yataka yakusan zuwa k'ofa sannan yace kajirani bari indawo, shahid cike da tsokana yace toh ranka yadad'e


yarima baice komai ba yafita yana tafiyarsa ta k'asaita, dogarawan da suke zaune k'ofar d'akinsane suka zube suna kwasar gaisuwa sannan suka tashi domin sutake masa baya, yarima batare da ya kallesuba yad'aga musu hannu.


ganin haka yasa duk suka tsaya, yawuce yacigaba da tafiyarsa shi kad'ai duk inda yagifta kwasar gaisuwa akeyi, d'aga ma mutane hannu kawai yake idan da sabo sun saba da halin yarima ahaka har yashiga turakar mai martaba da mamakinsa yaga har da iyayensu a zaune,


waje yasamu gefen maimartaba yazauna a k'asa tare da kwasar gaisuwa wajensa da wajen iyayensu nan duk suka amsa masa,


maimartaba gyaran murya yayi yace toh Alhmdllh nasan duk zakuyi mamaki akan dalilin taraku nan da nayi ammah ba abun mamakibane alkhairine muke tafe da shi, ba akan kowaba sai akan yarima suhail,


maimartaba cigaba yayi da cewa domin na riga na yanke hukunci saboda nasan zai kar6i abinda nake tafe dashi na alkhairi, bakomai bane sai akan dubawa da cancantar da naga yayi dan haka naza6a maka matar aure bakowa bace face 'yar uwarka sumayya.


yarima gabansane yaji ya fad'i dasauri yad'ago kai yakalli maimartaba har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa dan haka yasunkuyar da kansa k'asa tare da runtse idonsa cike da takaicin za6in da maimartaba yayi masa, nan iyayensu sukaita murna suna tofa albarkacin bakinsu akan maganar.

shidai yarima saurarensu kawai yake,

muryar maimartaba ce yatsinkayo yana cewa toh kai uban gayyar bakace komai ba,

yarima suhail kamar ba zaiyi magana ba sai chan yace ranka yadad'e na amshi za6in da kayi min hannu bibbiyu Allah yak'ara tsawon rai.


cike da Jin dad'i maimartaba yace masha Allah, naji dad'i sosai tabbas nasan daman bazan samu matsala daga garekaba wlh ka faranta min nima Allah yakawo lokacin da zan faranta maka,


gaba d'ayansu sukace Ameen, yarima suhail nan yak'ara kwasar gaisuwa sannan yamik'e yafita


umman sumayya kamar tazuba ruwa k'asa tasha saboda murna domin ko bakomai tasan burinta ya kusan ciki ko da taje ma d'iyarta da labarin sumayya har da rawa tataka saboda murna dagudu tafita taje 6angarensu rahama tashaida mata, nan rahama tatayata murna.




yarima suhail yana komawa d'akinsa saman gadonsa yafad'a tare da lumshe idonsa cike da bak'in ciki domin an 6ata masa plan saboda shi baida burin yin aure a yanzu ko ma da zaiyi sumayya bata daga cikin irin tsarin matan da yake da burin aure saidai kawai zai amince ne saboda maimartaba domin baya iya jayayya da shi,


shahid ganin yarima acikin wannan mood d'in yasa bai tambayesa abinda yake damunsaba domin yasan ko da ma ya tambaya toh ba zai samu amsaba saidai idan shi yaso yafad'a masa toh dakansa zai basa labari dan haka yasharesa yacigaba da kallon ball d'insa.



yarima ya dad'e a kwance sannan daga baya yatashi yashige toilet.




bayan sallar isha'i yarima turakar iyayensa yaje inda yatadda mahaifiyarsa kishingid'e wata baiwarta tana mata tausa inda wasu biyu suke gefenta suna mata hira.


suhail yana shiga yatsaya bakin k'ofa ganinsa yasa duk suka zube suna kwasar gaisuwa sannan daga baya suka tashi suka fita suka basa wuri domin yagana da mahaifiyartasa,


sultana bilkisu tashi tayi daga kishingid'en da take nan suhail yataka yaje inda take yazauna sannan yagaishe da mahaifiyartasa cike da fara'a ta amsa masa.



suhail duk'ar da kansa yayi k'asa baice komai ba, ganin haka yasa mahaifiyarsa tace yarima me yake faruwane? kafad'a min damuwarka domin bakada wata uwar da tafini,


suhail d'ago fuskarsa yayi cike da damuwa yace ummi yanzu Sumayya ita zan aura?

murmurshi ummi tayi tace toh menene dan ka aureta ina ce 'yar uwarkace kuma ta cancanta da hakan,
dan haka kakwantar da hankalinka kakoya ma zuciyarka sonta insha Allahu zakuji dad'in zaman aurenku.


cike da damuwa suhail yace ammah ummi kinsan halin Sumayya ko kad'an halinmu bai zo d'ayaba,

ummi tace injiwa yace maka haka? duk abinda kaga tanayi harda yarinta, nidai burina kakwantar da hankalinka tunda ita kaga bata tada hankalintaba kakoya ma zuciyanka sonta insha Allahu zakuji dad'in zaman aurenku.


yarima suhail yace toh ummi nagode, nabarki lafiya.

ummi tace toh my son dan Allah kar katashi hankalinka tunda kaga an amince da aikinka yanzu haka mahaifinka ya sa afara maka ginin hospital d'inka.

murmurshi yarima yayi yace nagode ummi sannan yafita daga turakar yakoma tasa.



Bayan kwana biyu aka tsaida maganar aurensa da sumayya nan da wata biyu masu zuwa, yarima yaso asa lokacin dayawa ammah maimartaba yace a'a, ,sumayya farin ciki tayi sosai agaban kowa take nuna murnarta,


yarima ganin dagaske ake yasa yad'an saki jikinsa har suna d'an ta6a hira da sumayya shima d'in kafin yayi magana d'aya tayi biyar, in ko kaga sunyi waya toh itace takirasa shima daga gaisuwa yake kashe wayarsa.


Bayan wata biyu akasha bikkunsu anyi shagali sosai ak'allah saida akayi events kusan guda biyar ammah dakyar aka samu yarima suhail yaje d'aya daga ciki shima saida ummi tasa baki, ammah sauran duk k'in zuwa yayi k'arshe idan yaga za'a takurasa sai yakashe wayoyinsa yace kar abari kowa yashigo sashensa,


ranar asabar aka d'aura aure, auren da dubban mutane daga nahiya dadama suka hallara,

amarya ta sha kyau har ta gaji, inda amarya tatare a part d'in yarima da aka fitar da shi a cikin gidan sarauta, k'arshen gata an nuna mata babu abinda ba a zuba masu na amfani ba.


kowa yazo sai ya yaba tsarin gidan domin babu wanda zai ce acikin gidan sarautane saboda part d'in yarima antsarasa kamar a turai inda aka fidda ma sumayya 6angarenta sai na yarima sai wani part d'in da aka fara ginawa aka aje sai kuma part na ma'aikata da bayinsu maza da mata.




da daddare saida shahid yayi dagaske sannan yasamu yarima suhail yayi wanka yashirya suka fito suka rakasa gidansa.

suna ta tsokanarsa shidai yayi shuru yakyalesu saboda wani irin haushi da yakeji, hatta su kansu haushinsu yakeji tunda su suka matsa masa sai yaje.
saida suka rakasa har part d'in amaryarsa sannan sukayi masa sallama suka tafi.


yarima suhail 6angarensa yabud'e da mamakinsa yaga dogarawansa zaune a k'asa suna ganinsa suka zube suna kwasar gaisuwa, yarima suhail batare da ya amsaba yace kun iya tafiya ,

k'ara kwasar gaisuwa sukayi sukace toh ranka yadad'e sannan sukace atashi lafiya sai suka tashi suka fita


bedroom d'insa yashiga komai na ciki very need da mamaki yakalli yadda aka shimfid'a masa farin bedsheet mai kyau a saman gadonsa d'auke kansa yayi yawuce yashiga toilet yawatsa ruwa , bayan ya fito yayi shirin kwanciyarsa yahaye gadonsa.



A 6angaren gimbiya sumayya bayan ta gama shirinta su jakkadiya suka take mata baya zuwa turakar yarima, da sallamarsu suka shiga ganin baya parlour yasa suka kwank'wasa masa bedroom,

yarima da yake kwance yabada izinin ashigo, da mamaki yake kallonsu sumayya da suka shigo, nan su jakkadiya suka zube k'asa suna kwasan gaisuwa, ita dai sumayya zuba masa ido tayi tana kallonsa cike da son mijinta,


haydar bai damu da kallon da take masaba yace lafiya kukazo man d'aki?

jakadiya da take durk'ushe tace ranka yadad'e yarima mai jiran gado daman dada ce tace mukawo maka amarya,


yarima suhail shuru yayi baice komaina yamaida idonsa yalumshe.
ganin haka yasa su jakadiya sukace mun barku lafiya gimbiya da yarima Allah yaja da ranku atashi lfy.


Gimbiya sumayya tace idan kun fita sai kurufe mana k'ofan,

yarima suhail yana jinta mamakine yakamasa domin bai ta6a ganin amarya hakaba.



suna fita sumayya tatako ta iso bakin gadon tazauna gefen da yarima yake kwance, suhail batare da ya bud'e idonsaba yace kije kid'auro alwallah,

sumayya turo baki tayi sannan tatashi tashiga toilet d'insa tad'auro alwallah,


lokacin da tafito yarima yana shimfid'a darduma nan yajasu sallah raka'a biyu sukayi sannan yakama kanta yayi mata addu'a.


bayan ya gama yayi mata tambayoyi akan addininta baiyi mamaki ba da yaga bakomai take iya basa amsaba, wata amsarma ba daidai take basaba nan ya Ida tsurewa da lamarin sumayya ammah kuma

Please Login or Register in order to submit comment