Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

memartaba, tana shiga parlour dada ce kawai nan sumayya taduk'e k'asa tare da fashewa da sabon kuka.

Dada rud'ewa tayi tace lafiya sumayya me yake faruwane? Bakida lafiya ne?


Sumayya girgiza mata kai tayi tace kod'aya dada, yarima ne yasakeki.

Dada dafe k'irji tayi tace Innalillahi wa'innah ilaihiraji'un, saki fa kikace?

Memartaba da yake ciki yana shirin fita jin hayaniya yasa yafito yana cewa hayaniyar me nakeji haka?

Sumayya duk'awa tayi tagaishesa cikin girmamawa,
Saida memartaba yazauna sannan ya amsa mata tare da cewa lafiya sumayya kike kuka?

Dada girgiza kai tashiga yi tace ranka yadad'e wlh yarima baya da mutunci yanzu saboda Allah ace ya saki 'yar uwarsa?

Memartaba cikin d'aga murya yace saki kuma? Anya kuwa sakinta yayi dan bana tunanin yarima zai zartas da wannan hukuncin batare da na saniba.

Dada tallabe ha6a tayi tace wlh indai yarima ne zai aika.

Memartaba kallon sumayya yayi yace ke kallanni nan fad'amin me kikayi masa yasakeki?

Sumayya rage sautin kukanta tayi sannan tace banyi masa komai ba daga matarsa ta ja ni fad'a har da cemin juya marar haihuwa, shine nikuma nabiye mata nan mukayi fad'a shine yakamani yai min duka,tafad'i hakan tare da d'age hijab d'inta su memartaba salati suka shiga yi da suka ga kwanciyar bulala a jikinta.
Cikin sheshek'ar kuka tace bayan ya gama dukana shine yasakeni.


haushine yacika memartaba yace banyi tunanin hakan daga wajen yarima ba banta6a tunanin zai iya min cin mutunci irin hakaba ammah bari inkira iyayenku suzo asan yadda za'a 6ullo ma lamarin.

Memartaba wayarsa yad'auka yakira mahaifin yarima da na sumayya yace duk suzo da iyalansu susamesa.


Bayan kamar minti goma sai gasu su duka sunzo harda Aunty husna da rahma da suke gidan basu koma gidajensuba,

Lokacin su memartaba suna zaune suna tattauna al'amarin gabad'ayansu suka duk'a suka gaishesu, kowa da mamaki yake kallon sumayya.

Bayan su memartaba sun amsa gaisuwa, gyaran murya yayi yace wani ya aika akira min yarima dan na kira wayansa a kashe.

Abban sumayya ne yace toh ranka yadad'e nan yamik'e yaje ya aiki wani dogari yace yaje yakirasa.



Yarima bayan ya baro part d'in sumayya nan yakoma 6angaren zarah yanayinsa kawai zaka kallah kasan ba k'aramin tashin hankali yake cikinsaba, kallon zarah yayi da take kwance ta zuba ma waje d'aya ido tana kallo, daga gefen gadon yazauna tare da dafe kansa yana tunanin lamarin sumayya dan gabad'aya ta gama ficce masa a rai, wayoyinsa yakashe gabad'aya dan ya san dole sai memartaba ya nemesa dan dama gudun kar amaido masa aurenta yasa yaimata saki ukkun.

Zarah ruk'o hannunsa tayi cikin muryarta da tadashe saboda kuka tace tunanin me kakeyi?

Kallonta yarima yayi cike da tausayi yace in kaiki asibiti adubaki ko?

Girgiza kai zarah tayi tace babynka lafiyarsa lau dan basu samu sun ta6asa ba nikuma ciwon jikine kuma nasan zan warke insha Allahu.

Yarima d'aura hannunsa yayi saman fuskarta sannan yace ammah kina buk'atar asa miki drip kuma jikinki akwai zazza6i.

Zarah maida idonta tayi talumshe, yarima zuba mata ido yayi yana kallonta.

Knocking d'in k'ofan da akayine yasa yamik'e yaje yabud'e kuyangar zarah ce cikin sauri taduk'a tagaishesa, yarima batare da ya amsa mataba yace ya dai.

Jikinta yana rawa tace ranka yadad'e daman dogari ne aka aiko daga turakar sarki yace yana son ganinka.

Yarima baiyi mamakin hakaba, dawowa yayi yakalli zarah da take kwance ta ji duk maganarsu, janye idonsa yayi daga kallonta sannan yace bari indawo sai muje hospital.

'Daga mai kai kawai zarah tayi, nan yarima yajuya yafita yanufi turakar memartaba.


Lokacin da ya isa baiyi mamakin ganin family d'insa da suka hallaraba, bayan ya yi sallama, waje yasamu k'asa chan gefen Aunty husna yazauna, cikin rashin damuwa yagaishe da su memartaba.

Ciki-ciki memartaba ya amsa masa nan d'akin yad'au shuru kowa saurare yake yaji memartaba ya fara magana.

Gyaran murya memartaba yayi sannan yakalli yarima da kansa yake sunkuye k'asa yace wannan taron ba dan kowa nayisaba sai dan kai yarima.
suhail ka bani kunya ban ta6a tunanin hakan daga garekaba koma menene ai ana son sasacin a cikin aure, wace irin zuciyace ta d'ibeka har kasaki matarka.

Gabad'aya 'yan d'akin sukace saki!! Nan aka fara kallon kallo.

Memartaba nuna sumayya yayi da take kuka har Lokacin Sannan yace toh gatanan dai ya saketa, ke kifad'a musu dalilin sakin suma suji.

Sumayya saida takalli yarima da kansa yake sunkuye sannan tamaimaita abinda tafad'a ma su memartaba.

Da mamaki yarima yad'ago yakalleta jin k'aryar da tadage tana shararawa, wata uwar harara yawurga mata nan Sumayya tafara dabarbarcewa.

Yana hararanta karaf a idon dada cikin fushi tace kikwantar da hankalinki kiyi bayaninki dan babu abinda ya isa yayi miki tunda kina a gabanku,
Nan Sumayya tacigaba da bayani.

Bayan ta gama d'akin yad'au shuru kowa yana jimami a cikin ransa, dadyn yarima ko kunyace takamasa ganin abinda d'ansa ya aikata ma d'iyar d'an uwansa, ummi ma jin abun take wani iri dan bata ta6a tunanin hakan daga garesaba.


Gyaran murya memartaba yayi yace kunji jawabinta, kunga abin kunyar da yarima ya aikata kan bare yarabu da 'yar uwarsa, toh yanzu ba sai anja maganar da nisaba na umurceka kamayar da ita d'akinta.


Sai a Lokacin yarima yad'ago yakalli memartaba cike da girmamawa yace ranka yadad'e kagafarceni, bata fad'a muku saki nawa nayi mataba? Ko daman idan anyi saki ukku ana komawa.


Nan d'akin yarikice da salati memartaba yace da hankalinka zakayi ma matarka saki ukku yarima? Sakin da ubangiji bayaso ana yi, ina iliminka da tuninka suke.

Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa.

Memartaba yace inji a lokaci guda kayi sakin?

Sumayya tayi karaf tace eh ranka yadad'e gabad'aya yayimin.

Toh Alhmdllh tunda gabad'ayane kuma cikin fushine zamu iya d'aukansa a matsayin saki d'aya kaga sai kamaidata d'akinta yanzu....cewar memartaba

Yarima k'ara duk'ar da kansa yayi sannan yace kagafarceni ranka yadad'e na riga da na haramta ma kaina k'ara auren Sumayya,

A firgice kowa na d'akin yakalli yarima, nan Sumayya tafashe da kuka tace na shiga ukku dan Allah kutaimaka min yamaidani d'akina.


Memartaba kallon yarima yayi yana jinjina kai dan ya ma rasa abinda zai ce masa,

Dada ce tashare kwallar da tazubo mata saboda tausayin Sumayya sannan tace ranka yadad'e ka gani ko? Lokacin da nake fad'a maka wulak'ancin da yarima yake ma Sumayya ba ka yarda, duk wulak'anci da cin mutuncin da matarsa takeyi mata bai ta6a tankawaba sai ita da suka d'an samu sa6ani shine yadank'ara mata har saki ukku.


Ummi kallon yarima tayi kallon mamaki, yarima cike da jin kunyar ummi yaduk'ar da kansa k'asa.

abban Sumayya ne yai k'arfin halin cewa kuyi hak'uri yanzu haka wani haukan ne Sumayya tayi masa kuma ba a ji daga garesaba.

Memartaba murmushin takaici yayi sannan yace bana buk'atar jin komai daga garesa, nagode sosai suhail ni kawulak'anta tunda ni na aura maka Sumayya yanzu ka maido min abuna ka ce ban isa inyi maka abinda bakasoba,
Saboda ganin kamar ban kyauta makaba yasa nabarka kaje ka auro za6inka bayan shekara d'aya da aurenku da Sumayya, duk labarin da ake bani akan abinda kake ma Sumayya ban ta6a yardaba sai gashi yau na gane ma idona abinda zai d'aga min hankali abinda d'ana nacikina bai aikataba sai gashi jikana namiji tilo d'aya ya aikata ma 'yar uwarsa.

Yarima d'ago kai yayi yakalli memartaba yace kagafarceni ranka yadad'e nima ba a son raina na aikata hakanba, wlh Sumayya ba gaskiya tafad'a mukuba.

Memartaba d'aga masa hannu yayi yace dakata bana buk'atar jin komai daga wajenka abinda idona yagane min ya isheni.

Daddyn yarima kallon yarima yayi cike da takaici yace suhail ka ban kunya kana gani yadda nake zaune da d'an uwana lafiya ammah karintse ido kakarta min rashin mutunci har haka, yanzu da wane ido kakeso ink'ara kallonsa.


Girgiza kai yarima yashiga yayi yace kayi hak'uri daddy wlh nima ba a son raina hakan takasanceba.


Memartaba a hankali yafurta innalillahi wa'innah ilaihiraji'un, kallon kowa yayi d'aya bayan d'aya sannan yamaida kallonsa ga dada yace kin gani ko? Ni yanzu banma san wane hukunci zan yanke masaba ko zan samu d'an sauk'i a raina.

Dada kallon yarima tayi sannan tace ma memartaba ranka yadad'e kaga ita tagaban goshin tasa tana chan tana hutawa babu abinda yadameta bata ma san wainar da ake toyawaba ita ga 'yar gaban goshi me ciki.


Jinjina kai memartaba yayi sannan yace nasan abinda zanyi, kallon Rahma yayi da take kuka yace ke jeki kisamo min takarda da biro, mik'ewa Rahma tayi tafita.

Nan kowa yayi jugum yana jira yaji hukuncin da memartaba zai yanke.


Bayan kamar minti biyar sai ga Rahma ta dawo rik'e da takarda da biro, tsugunnawa tayi gaban memartaba tamik'a mai,

Kar6a memartaba yayi yace yauwa, sannan yakalli yarima da yake zaune har Lokacin bai d'ago kansa mik'a masa memartaba yayi yace kar6a.

'Dago kai yarima yayi yakalli takardar sannan yamaida kallonsa ga me martaba, a karo na biyu memartaba yace kar6a mana.


Hannu yarima yamik'a yakar6a tare da tsare memartaba da ido yana jira yaji abinda zai ce.

Shima memartaba kallonsa yake sannan yace inaso karubuta ma wacchan matar taka itama saki ukku.

Gabad'aya d'akin d'agowa akayi aka kalli memartaba cike da mamakin kalmar sakin da ya ambata.

yarima ko gabansane yayi wani irin fad'uwa saida biron takubce daga hannunsa, tashin hankaline k'arara yabayya a fuskarsa.

har a lokacin memartaba kallonsa yake fuskarsa ba alamun wasa yace indai kana son cigaba da zama a gidannan toh dole kasaketa saboda hakan shi zaifi dacewa karabu da kowace d'aya daga cikinsu.

Dada gyad'a kai tayi tace tabbas ranka yadad'e ka kawo shawara mai kyau inma cikin da yake jikintane yake ma rawar kai toh taje gidansu da abinda tacigaba da raino zamu dinga aika mata da duk abinda take buk'ata har sai ta haihu, intaso tashayar da abunta inkuma batasoba tabamu abunmu a haka zamu sami wacce zata kular mana da shi.


Ummi ita kanta saida gabanta yafad'i dan ita jin abun take kamar a mafarki tabbas ta san d'anta akwai dalilin da yasa ya saki sumayya saidai miskilanci da zurfin jikinsa bazasu ta6a barinsa yafad'aba.



Abban sumauya ne yaduk'ar da kansa yace ranka yadad'e ataimaka a sassauta ma yarima wannan hukuncin yai masa tsauri.

Sultana sadiya da take gefe takaici duk ya cikata tana ji kamar tashak'e yarima yamace kowa yahuta, jin maganar da mijinta yayi yasa tawurga masa harara, sai a lokacin tace ranka yadad'e tabbas wannan hukuncin da kayanke shine daidai dan yarima ya tozarta min d'iya,,,, d'aga mata hannu sultan abbas yayi yace ke banason hauka na san duk abinda yaima sumayya toh tana da laifi a ciki dan na san sumayya bata ji.

Sultan Ahmad ne yai k'arfin hali yace ma sultan Abbas kadaina cewa haka domin yarima bai kyautaba.



Memartaba gyaran murya yayi nan kowa yanutsu, sannan yace duk naji k'orafinku saidai inaso kusani babu wanda ya isa yasa incanza maganata dan ku kanku kunsani ni kaifi d'ayane bana magana biyu.

Duk'ar da kansu sukayi sukace Allah yaja da ran sarki me adalci.

Memartaba kallon yarima yayi da duk sanyin A-C d'in da take d'akin ammah bai hana yayi zufaba, murmushi Memartaba yayi sannan yace suhail ina saurarenka dan kaji abinda nafad'a.

Aunty husna ce tad'auki biro d'in da tafad'i tamik'a mashi.

Cikin sanyin jiki yarima yak'arfi biro d'in yad'aura saman paper, nan kowa yazuba mai ido ana jira yarubuta.

Ido yazuba ma paper tare da d'aura biro d'in kamar zaiyi rubutu nan gabansa yashiga dukan ukku-ukku jinsa yake wani iri gabad'aya komai ya kwance masa, yarasa cikin biyu wane zaiyi shin sakin zarah zaiyi ko kuma ya amince yarabu da family d'insa, runtse idanunsa yayi yana jin wani irin k'unci a ransa........





_Shin yarima zai amince yasaki zarah?_

_Ko zai amince yarabu da family d'insa kamar yarda memartaba yafurta?_



_*Muje Zuwa dan jin yadda zai kasance*_





_Comment_
*nd*
_Share_







_Sis Nerja'artโœ๐Ÿป_๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘

_*YARIMA SUHAIL*_

๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘



_*Written By~Sis Nerja'art*_



_*DEDICATED TO MY DAUGHTER ZARAH*_


https://m.facebook.com/Intelligent-Writes-ASSO-294634797868361/

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION ยฎ*
*[onward together]*
*{ we give the readers of ours the best out of the bests,,our inks are melodious and dropping a kinda lights to readers }*
THE PEN OF LOVE ๐Ÿ˜˜ HEART TORCHING โค TEARS OF SORROWS ๐Ÿ˜ญ CURDLES ๐Ÿ™‚ GIGGLES ๐Ÿ˜ AND MARRIEGE THINK๐Ÿ’‘
*JUST GIVE US FOLLOW....*โœ”


_*Nagode Sosai da kulawarku agareni masoya, gaskiya naji dad'i dan naga k'auna zallah daga gareku, banda abinda zanyi inbiyaku saidai ince Allah yabar k'auna da dank'on zumunci๐Ÿ˜˜*_


*PAGE* 5โƒฃ7โƒฃ


Ahankali yabud'e idanunsa da gaba d'aya suka canza launi, ji yake kamar yarubuta ma zarah saki sai kuma yaji bazai iya aikata hakanba dan shi kansa ya san idan yasaketa bai mata adalciba.

'Dago kai yayi yakallesu d'aya bayan d'aya har a lokacin idanunsu suna a kansa,,,Yarima kallonsa yasafke ga memartaba cikin sanyin jiki muryarsa tana rawa yace kagafarceni ranka yadad'e bazan iya rabuwa da matataba.

Gabad'ayansu a firgice suke kallonsa hatta shi kansa memartaba yayi mamakin furucin da yafito daga bakin yarima.

Murmushi memartaba yayi sannan yace suhail idan na fahimceka toh kana nufin ka za6i matarka akanmu ko?


Cike da damuwa yarima yagirgiza kai yace ranka yadad'e ba haka nake nufiba kawai dai... katseshi memartaba yayi yace kawai dai me!!! Toh bara kaji indai har bazaka iya rabuwa da itaba toh mu yazamar mana dole murabu da kai, dan haka kaje kawai na cireka daga cikin masarautata yanzu ka fita daga cikin iyalaina dan haka na baka awa d'aya kaje duk wani abu da kasan mallakinane kaje kakawo min sannan kafita kabarmin masarauta, inkuma ba hakaba zansa a fitar da kai a wulak'ance.


Gabad'aya d'akin shuru sukayi kamar ruwa ya cisu dan sunsan tunda har memartaba yafurta toh tabbas ba wanda ya isa yacanza.



Yarima runtse idonsa yayi yana jin yadda maganar memartaba take dukan dodon kunnansa wani irin d'acine yakeji a ransa

Ummi ko rufe fuskarta tayi da alkyabbarta tana goge hawayen da suka taru a idonta, gabad'aya lamarin ya rikitata.

Daddy ma shikad'ai yasan abinda yakeji a ransa game da maganar da mahaifinsa yafurta, kawai dai ya dakene bai nuna ba.


Dada ce takalli memartaba tace ammah ranka yadad'e ba... d'aga mata hannu memartaba yayi yace banason jin maganar kowa daga cikinku dan ni nariga da nagama magana yanzu lokacin da nabaka zai fara aiki.


Yarima har ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yafasa, ahankali yamik'e jiki ba k'wari kamar wanda kwai yafashe mawa a ciki haka yake tafiya har yafita daga d'akin.


Rahma da Aunty husna ko kuka sukeyi ahankali, inda sumayya take kuka akan mutuwar aurenta.


Yarima ahaka ya isa part d'insu, bakin gadonsa yazauna yadafe kansa shi kad'ai yasan abinda yakeji gashi an hanasa yai magana, tunani yashiga yi shin in ya bar gidansu ina zaije? Tunowa yayi da maganar memartaba da yace ya fara cin lokacin da yabasa, dan haka yajanyo wayarsa yakira wata number bata dad'e tana ringing ba akayi picking,

Yarima k'ok'arin saita nutsuwarsa yayi suka d'an gaisa sama-sama sannan yace Dr Mu'az kana gari?
Daga chan 6angaren wanda aka kira da Dr mu'az yace eh ranka yadad'e.
Ohk, please kaje kasamar min hotel maikyau yanzu zan shigo Abuja.
Cikin jin dad'i Dr mu'az yace angama ranka yadad'e Allah yakawoka lafiya.

Ameen yarima yace sannan yakashe wayar,
Sannan yakira yasa ayankar masa ticket na mutum biyu yace yanzu yakesonta, kasancewar sanannene nan suka amsa masa, bayan sungama wayar yai musu transfer d'in kud'insu, bayan ya gama Dr khalil yalalubo bai wani 6ata lokaciba yai picking

Yarima ko gaisawa bai bari sunyi ba yace Dr khalil kana ina yanzu?

Daga chan 6angaren Dr khalil yace ranka yadad'e ganinan wajejan anguwarku gidan Auntyna.

Ohk, please kazo yanzu akwai inda nakeso kakaini.

To ranka yadad'e ammah ya naji muryarka haka? Lafiya dai ko?

Yarima kashe wayarsa yayi batare da ya bashi amsaba,,,,mik'ewa yayi yaje yafara had'a duk wani abu da yasan ba mallakinsa bane yaware ma daddy da memartaba nasu sannan yad'auki nashi, wajen wardrobe d'insa yaje yabud'e nan yafara fitar da kayansa yana sawa a trolly, cikin trolly guda yazuba duk wani abu da yake buk'ata sannan yajawo,

Tsaye yayi yana k'are ma room d'insa kallo yana jin k'unci a ransa, janyo trollyn yayi yafito cikin sauri guards d'insa suka zo suka kar6a nan yace suwuce masa da shi waje.
Cike da ladabi suka amsa masa.


Daga nan part d'in zarah yawuce kallonta yayi har lokacin tana kwance, ita kanta zarah yanayinsa kawai tagani tasan yana cikin tashin hankali,

Yarima batare da ya janye idonsa akantaba yace tashi kihad'a kayanki,

Zarah saida gabanta yafad'i tace na'am.

Shareta Yarima yayi yawuce wajen wardrobe d'inta yabud'e nan yafara zuba mata a trolly duk abinda yasan zata buk'ata saida yazuba mata a ciki, bayan ya gama juyowa yayi yakalli zarah da tatsaresa da ido yace tashi muje.


Zarah k'wallah ce tacika mata ido tace ina zamuje?

Tsawar da Yarima yadaka matane yasa tamik'e ba shiri tajanyo veil d'inta tayafa nan Yarima yawuce gaba tana biye da shi, wata kuyangarta ce cikin sauri takar6i trollyn da yake hannun Yarima

Zarah tana biye da yarima gabad'aya kanta ya d'aure gashi yarima bai bata fuskar da ma zata iya tambayarsaba ahaka har suka fito harabar gidan, da mamakinta sai gani tayi sun nufi turakar su memartaba.

mamaki bai ida kamataba saida suka shiga d'akin taga gabad'aya family d'in yarima suna a ciki, bata lura da yanayin da suke cikiba, dasauri tatsugunna tagaishesu, gabad'ayansu babu wanda ya amsa mata,

Ta d'auka basujiba nan tak'ara gaishesu, dady da abbah ne kawai sukayi k'arfin halin amsa mata,

'Dagowa tayi takalli ummi da talullu6e kanta da alkyabba, sai kuma takalli su Aunty husna da rahma da suketa kuka, nan jikinta yak'ara yin sanyi, daganan tamaida kallonta ga sumayya da take gefen dada tana ta rusa kuka, inda dada tabuga uban tagumi, sultana sadiya ko ta cika tayi fam.

gani tayi yarima ya wuce wajen memartaba nan yarussuna yamik'a masa wasu files, a wulak'ance memartaba yakar6a sannan yace ina fata komai ne nan kakawo min.

Ahankali yarima yace eh ranka yadad'e,

Jinjina kai memartaba yayi sannan yace yarima ka bani mamaki yanzu saboda mace ka amince karabu da kowa naka, inaso kasani dangi basu canzuwa ammah ita mata a kowane lokaci zaka iya canzata, tunda ka za6i mace akan danginka toh sai katashi kutafi.

Zarah cikin sauri tad'ago kai takalli memartaba da yake maganar dan kwata-kwata bata fahimci inda maganarsa tadosaba,

Dada ce cikin damuwa tace ammah har a yanzu suhail idan ka amince zaka rabu da ita toh bismillah dan kasan memartaba yana nan akan bakansa,,,tak'arashe maganar tare da mik'a masa takardar.


girgiza kai yarima yayi yace kugafarceni har yanzu ina akan bakana nima yana fad'in haka yamik'e

Sumayya ce tasake fashewa da kuka tace yanzu saboda waccan jakkar kasakeni saki ukku yarima, wlh bazan yardaba sai ka maidani d'akina, duk inda kaje zaka dawo kataddani.


Zarah sai a lokacin ta fahimci abinda ake tattaunawa gabantane yashiga dukan ukku-ukku a firgice takebin kowa na cikin d'akin da kallo,

Rahma ce tayi saurin mik'ewa dagudu taje tafad'a jikin yarima, cikin kuka tace dan Allah bro kar katafi kabarmu dan Allah ka amince karabu da matarka kazauna cikin danginka.

Yarima idanuwansa ne suka kad'a sukayi jawur kallon daddy yayi da ya janye fuskarsa gefe, a 6angaren abbah ma gefe d'aya yake kallo,

Yarima har ya bud'e baki zaiyi musu magana sai kuma yafasa, janye rahama yayi daga jikinsa, kallon umminsa yayi da taketa k'unshe kukanta, wani iri yaji a ransa gudun kar yaimata magana yaja tayi kuka saisa baice mata komai ba yawuce yanufi inda zarah take tsugunne tana hawaye.

Kallonta yarima yayi yace tashi muje.

Girgiza kai zarah tashiga yi dak'yar tabud'e baki muryarta tana rawa tace please yarima kar karabu da danginka ni yafi dacewa karabu da ni dan danginka sune komai naka, mik'ewa tayi tare da fashewa da kuka had'e hannuwanta tayi waje guda tace dan Allah yarima na rok'eka kacika umurnin memartaba kasakeni kawai, cikin sauri taje takar6o takardar hannun dada tadawo inda yake tsaye tamik'a mashi tace please karubuta min sakina, kar katafi kabar su ummi, neman tura mashi tankarda tayi a hannunsa ganin ya k'i kar6a yasa tawuce inda ummi take zaune tatsugunna cikin kuka tace please ummi kisa baki yarima yarubuta min sakina bana son yasamu matsala da kowa dan ku kune farin cikinsa.


Ummi kasa 6oye kukanta tayi nan tafara sheshek'ar kuka, zarah ganin ummi batada niyar cewa komai yasa tamik'e takoma wajen yarima tace kaduba kaga ummi da 'yan uwanka kuka suke yanzu ka amince katafi kabarsu cikin....wani gigitacce mari yarima yakwad'a mata wanda gabad'aya 'yan cikin parlourn saida suka kallosu, yarima cikin 6acin rai yace zarah kidawo hayyacinki.

Nan zarah tashiga hankalinta tare da kife kanta a k'irjin yarima tarushe da wani sabon kukan, yarima jin kukan nata yake har cikin ransa, janyeta yayi daga jikinsa nan yarik'e mata hannu suka fara tafiya, memartaba janye idonsa yayi daga kallonsa inda su daddy daman basu d'ago ba dama.

Aunty husna ce cikin sheshek'ar kuka tace yarima na rok'eka kar ka aikata hakan dan Allah kadawo,

Jan hannun zarah yayi suka ficce daga parlourn Aunty husna har ta mik'e zata bi bayansa nan taji muryar memartaba ya ce kar wanda yasaki yabi bayansa.

kan dole takoma tazauna.


Yarima yana fita nan yatarar da Dr khalil tsaye yana jiransa, wajen motar dr khalil yanufa.

Cikin sauri Dr khalil ya iso inda yake yace yarima ya naganku haka?

Yarima kallon guards d'in yayi yace susaka masa kayansa a boot, cikin sauri suka cika umurninsa.

Nan suka bud'e masa motar yashiga, zarah da take tsaye fuskarta rufe da mayafi itama aka bud'e mata baya tashiga.


Dr khalil da yake tsaye zuwa yayi yashiga motar tare da kallon yarima yace ranka yadad'e ina muka nufa?


Yarima batare da ya kallesaba yace airport.

Cikin sauri Dr khalil yatayar da motar, lokacin da zai fita daga masarautar yarima runtse idanunsa yayi yana jin wani iri a cikin ransa,


Tafiya suke ammah gabad'aya babu wanda yayi magana,

Dr khalil juyowa yayi yakalli yarima da yazuba ma titi ido cike da damuwa yace ranka yadad'e wace irin tafiya ce ta gaugawa takamaka haka? Ina zakaje?

Yarima batare da ya juyo ya kallesaba yace Doctor ga amanar hospital d'ina nan na damk'a a hannunka domin nasan zaka kularmin da shi kamar yadda zan kula da shi ammah ban saniba ko nan gaba za'a kawo wanda zai maye gurbina, koma mekenan nidai na aminta da kai.



Kiiittt yaja burki yatsaya tare da juyowa yakalli yarima, cike da damuwa yace please yarima kaimin bayani yadda zan fahimta dan gabad'aya ka d'aure min kai, wace irin tafiya ce zakayi haka? Ina zakaje please kafad'a min.




Yarima duba agogon hannunsa yayi sannan yace please kayi sauri flight d'in da zamu bi ya kusan safka.

Tada motar Dr khalil yayi dagudu yafigi motar.

Yarima ta mirror yakalli zarah da tabuga uban tagumi, jingine kansa yayi a kujeyar da yake zaune tare da k'ura mata ido ta mirror d'in, zarah ko bata ma san yanayiba dan gabad'aya ta yi zurfi cikin tunani.


Suna isa flight d'in yana safka, Dr khalil cikin sanyin jiki yakalli yarima yace Dr toh yanzu sai yaushe zaka dawo?

Murmushin k'arfin hali yarima yayi sannan yace kar kadamu ba wani dad'ewa zanyiba.

Jinjina kai Dr khalil yayi sannan yace ammah zanyi kewarka dayawa,

Yarima kallon abokin nasa yayi yace nidai fatana karik'e min amanata kacigaba da tafiyar da komai daidai kamar ina nan.


Murmushi Dr khalil yayi yace karkadamu insha Allahu zanyi kamar yarda kace,
Nagode sosai abokina,,, yarima yafad'i hakan cikin jin dad'i, sannan yabud'e k'ofar yafita,

Nan shima Dr khalil yafita, yarima dakansa yabud'e ma zarah k'ofan, dak'yar tasafko k'afanta tafito, nan yarima yana rik'e da ita yai waya akazo aka kawo masa komai nasa, kayansu aka fitar aka saka a cikin flight d'in.

Dr khalil har wajen jirgin yarakasu nan suka k'ara sallama da yarima cikin rashin jin dad'in nisan da zasuyi da juna.

Zarah ko saboda tashin hankalin da take ciki baisa tayi murnaba koda wannan shine karo na farko da tafara shiga jirgi.


Daga gefen yarima take zaune har jirgin yatashi, wani irin kunci da bak'in ciki yaziyarci zuciyan yarima a lokacin da suka fara tafiya, bak'in space d'insa yajanyo yadad'e idonsa, zarah cikin rashin k'arfin jiki takwantar da kanta a saman k'irjin yarima.

Rungumeta yayi cike da tausayinta, ahaka zarah tayi bacci.


Cikin k'ank'anin lokaci suka isa garin abuja.

Jirginsu na dira yarima yakira Dr mu'az yace gamu mun safka.

Dr mu'az cewa yayi ranka yadad'e ai gani nan tun d'azu nake jiran safkarku.

Tada zarah yayi da take bacci nan suka fito.


Wani mutum ne wanda bazai wuce tsaran yarima ba koda ma zai girmi yarima toh dakad'an ne, nan ya iso inda suke fuskarsa d'auke da fara'a.

Yarima koda yana cikin damuwa ammah hakan baihana sa nuna jin dad'in ganin abokin nasaba,

Dr mu'az cike da jin dad'i yace sannu da

Please Login or Register in order to submit comment