Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

E-book Creator
Bashier Sardaunah
08066046091



*💦MALIKA MALIK💦..!*
_(Sai na rama..)_

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ📚*

_MALLAKAR:Janafty😘_

*14 January 2020*

•WARNING: ŃO PÁŔŤ OŦ ŤĤĨŚ PÚßĹĨČÁŤĨOŃ ŚĤOÚĹĎ ßĔ ŔĔPŔOĎÚČĔĎ,ĎĨŚŤŔĨßÚŤĔĎ OŔ ŤŔÁŃŚMĨŤŤĔĎ ĨŃ ÁŃŶ ŦOŔM OŔ ßŶ ÁĹĹ MĔÁŃŚ,ĨŃČĹÚĎĨŃĞ ŔĔČOŔĎĨŃĞ OŔ ÁŃŶ OŤĤĔŔ ĔĹĔČŤŔOŃĨČ MĔŤĤOĎŚ ŴĨŤĤOÚŤ ŤĤĔ PŔĨOŔ ŴĨŔŤŤĔŃ PĔŔMĨŚŚOŃ OŦ ŤĤĔ PÚßĹĨŚĤĔŔ,ŚO ßĔ ŴÁŔŃĔĎ!!!*

_*Bismillahir rahamanir rahim,in The name of ALLAH The most Beneficient the most mercifull praise be to Allah lord of The words*_

_Gabadaya Littafin *MALIKA MALIK* Sadaukarwane ga duk wani *D''AN SANDA* dake Fadin kasarnan,kama daga *IGP,DIP,AIG,CP,DCP,ACP,CSP,SP,DSP,ASP,INSPECTOR,SERGENT,AND CORORAL P.C*...Allah ya karemana ku Da ikon Allah_


*1*

Free Fage

  _KATSINA_

     """Da misalin karfe 11:20pm na daren Ranar jumma"a Akan Titin dake tsakanin Dutsenmah da katsina wacce take gabda shiga katsina.

Adaidai kan Titin akwai yan Sanda wadanda suke patrole awajen,Suna tsatsaye ne Gefe kuma ga motocinsu guda biyu akallah yan sanda zasu kai su Biyar kowannesu, sanye da uniform dinsu bakake,da ganin kayan jikinsu basai ka tambayesu ba,zaka gane dukansu inspector ne,domin basu da kowani Rank ajikin kakin nasu,dukkansu fuskarsu sanye da Hula p-cap,da bakaken safan hannu sai manya manyan Tociloli masu bala"in haske kamar ta yan fashi,wanda in aka dallareka dasu, sai ka dakata saboda bala"in haskenta,Duk motar da tazo wucewa sai sun tsaidata sunyi bincikenta saboda tsaro  dakuma bincike, wanda daga sama suka sameshi saboda masu shiga da fita da mugayen makamai wanda ake Shigo dasu daga  bodar katsinar aboye.

   Motocine jere guda goma sha biyu dukkansu 11 din iri daya ne Corollahx sai babban ciki wacce tafita dabam itace Range cover baka ce gabadaya motar Tinted ne gaba da bayanta kowacce mota bayan motan an saka musu Nomba mai dauke da Tambarin *MALIKA MALIK1* har zuwa na 12,gudu suke ta shararawa bisa Titin Dutsenma zuwa katsina,Tundaga nesa Yan sandan suke Dalle su da fitila Tunda sukaga yadda suke gudun ganganci bisa Titi.

     Sai da suka kawo gab kana suka fara slow,motar Farko Tana tsayawa Suma na baya suka tsaya,Wani inspector ne ya karisa kusa da motar yana kwankwansa glass din motar,sai da aka bata lokaci kana aka zuke glass din motar.

Wani Inyamuri ne zaune a mazaunin Direba sanye da wasu kaya brown colour Riga da wando da alamu dai kamar Uniform ne,Kallonsa yayi daga sama har kasa kamar yadda Dan Sanda ke karemasa kallo,Cikin gadara ya furta"Lafiya mallam.?."Dan Sandan yayi mamakin jin Hausa abakinshi don akallon Farko bai yi kama da wanda yakejin Hausa ba.

  Gyara tsayuwa yayi yana fadin"Zamu bincika duka motocinku ne,daga ina kuke da tsohon daren nan? kuma kuke gudu ba bisa ka"ida ba..?."Yafada yana leka motocin dake bayansa Dan ware ido Direban yayi yana fadin"kai kana ko da hankali kasan motocin waye ka tsare kuwa? dariya Dan Sandan yayi yana fadin"Wannan bashi ne Abun da na Tambayeka ba,tambayanka nake daga ina kuke,? bai mai mgana ba kawai sai ya kada kai yana fadin"Zaka shiga mtsala matukar *MADAM* Ta fahimci meke Faruwa.."Yafada kai tsaye.

  Tana kishingide abayan motan Tana Karanta jaridar Dailytruth bata ma Fahimci meke Faruwa ba,sai zuwa chan Ta fahimci motar da suke ciki ta tsaya cak,cikin mamaki ta dago da kanta bayan Ta kauda jaridar lokaci daya take fadin"Joy Har mun iso gidane..?daga gaban motan ya amsa mata da fadin""A"a madam yan Sanda ne suka tsaidamu wai zasu binciki motocinmu..."Wani zabura tayi tana fadin"What...? wani banzan Dan sanda ne ya tsaidamin motoci,i swear sai na koya masa hankali sai ya gane ba"a yima *MALIKA MALIK* wargi.."

Tafada cikin Fushi kafin ta balle murfin motan ta fice,Doguwa ce  sosai kirarta irin kirar Cocacola ce,Tana sanye da Riga da wando blank and white,tayi Stoking ta ciki ta Kama gashin kanta da band daga tsakiyar kanta bayan ta saki jelan Ta baya,Kafanta sanye da wani takalmi sawu ciki mai tsini sosai blak colur ne,shima Doguwar Fuska gareta wanda kusan Rabinta yake rufe dawani bakin glass,mai kyau da tsari,yadda ta fito cikin Fushi ya sanya duka bodygourd dinta suka Firfito,suna take mata baya cikin Fushi Tanufi wajen Dan Sandan da suke Rigima da Direnba Tun Farko.

Ganin yadda suka nufosu ne yasa yan sandan dasuke gefe suka kariso daidai lokacin data kariso Gabansu ta tsaya suma Bodygourd din nata,sukaci burki abayanta Gilashin idonta ta cire tana fadin"Waya sakaku ku tsare ma mutane motoci,?kuma don Rashin kunya harda motocina,cikin shashancin ku,Uban waya sakaku,waye shugabanku C.P ko IGP  gayamin Shiyace ku tsare motocin *MALIKA MALIK..*? tafada cikin Tsawa Tana binsu da wani matsiyacin kallo.

Jin sunan da tafada ne yasasu mamaki dama sun dade suna jin lbrinta da irin Rashin mutumcinta gashi yau sun gamu da ita,saboda kwarjinta da haibanta dukkansu sun kasa maida mata da martani balle wani cikinsu yayi magana.

  Yana cikin motar yan sand'an Ta patrole video call yake Shida *YAYA MARWAN..* Hira suke sha suna dariya,ta madubin motan yake hango Abunda ke faruwa,saurin yima Marwan sallama yayi Shiko yana tsokanarshi da *INSPECTOR..* Cikin hanzari ya katse wayar lokaci daya yana bude murfin motan ya fito,dogon Namiji ne,sanye da bakaken kaya Riga da wando harda wata rigar sanyi wacce takaimai har zuwa gwiwansa,ba"a iya ganin Fuskarsa saboda ya sanya p_cap ne kuma ya sauko da ita ta Rufemai rabin Fuska,cikin takun isa ya nufi wajensu ammh duka hannuwansa suna,coge a aljihun wandonsa ne.

Tana ganin ya Fito daga motan Ta nufeshi tana fadin"AU shine wannan yabaku umarnin ku Tsaremin motoci ko,toh yau zan koyamasa Hankali in yana neman na goro ne,ko na Sigari bazai kara yunkuri sawa Atsareni ba..."Tafada Tana karisawa garesa Tana zuwa batayi wata wata kawai ta kifesa da mari jikake Kau...!Saboda zafin marin saida ya fito da duka hannuwansa daga aljihu har wayarsa ta fito ta fadi bai sani ba,Hannu biyu ya sanya ya dafe Fuskarsa yana binta da kallon mamaki,miyau ta tsirtamai kafin tace"U Stupid kai ne kasa wadan nan kananun karnukan naka su tsaremin motoci ko,Dama ku yan sanda ba mutane bane,all of u,are Monkey and bakusan komai ba sai tsaida motoci kuna karban na goro dana Sigari Tunda daman ba Abunda kuka iya sai shaye shaye da yima mata Fyade ko,?Toh as From Today bazaku kara tare wata mota ba, joy bring d box Now..."

Tafada ciikin Tsawa Da hanzari wanda aka kira ya nufi mota ya dauko wata yar karamar akwati yazo gabanta wani abu kawai ya danna sai Ga kudi suka bayyana dollars ne Shimfide batai wata wata ba ta dumbuza ta watsamai Afuska tana fadin"Take d money ayi na goro dana Sigari banzaye Yan"iskan kan hanya kawai,wlh i hate aikin yan sanda hardama Uniform dinsu all of dem basu da wani amfani a akasarmu sai lalacewa,Next time ka sake sakawa Atsare motocin *MALIKA MALIK..*Kagani wlh sai na saka an batar dakai Rubbish..."Tafada tana juyawa kamar walkiya Sukuma suka take mata baya.

   Tunda ta kifamai mari da wadandan mugayen maganganun datake fada suka daskaran dashi gabadaya Tunaninsa da zuciyarsa ta tsaya lokaci guda,wani bakin ciki da takaichi tare da wani Fushi suka lullubeshi,kowacce kalma in ta fada sai yaji kamar saukan aradu,tacima kakin yansanda mutumci tayi jam"i gabadaya ta hada kenan harda mahaifinsa mafi soyuwa garesa,wanda yabada komai nasa domin Taimakon kasarsa,yan sanda da basa barci domin kare dukiyan al"ummah da lafiyansu sune take kira basu iya komai ba sai shaye shaye dayima mata fyade,kakin dayake burin yaga ya sanya ajikinsa Shitake kira Rubbishi...Ina!Da sake Tuni wani Bakin ciki  mai hade da wani Tarnakin hawaye suka kwaranyomishi tana gabda da Shiga mota ya daga murya cikin Fushi da amo mai Sauti yace"" *MALIKA MALIK...!SAI NA RAMA...* ..."yafada cikin wani irin amo,waigowa tayi kafin tayi danyi dariya tace"Ok start d game young police man.."Tafada kan Tafada mota,dukkansu kowa yakoma motarshi Suka tadasu suka wuce da gudun bala"i kamar zasu bankesu.

  Suna Wucewa ya nufi mota yana fadin" Inspector Saleh take me to home now..."Yafada muryansa ya fara rawa  saboda bacin rai lokaci daya ya bude gaban motan ya shiga,da hanzari Inspector saleh yayi mgana da sauran yan Sandan kafin shi ya nufi motar ya shiga mazaunin direba yaja sukahau kan titin da Sauri,Suma din dai cikin katsinar suka nufa adaren.

____________________

Anguwan *LAYOUT* suka nufa daya daga cikin anguwannin masu hali dake cikin katsina ta dikko Dakin kara,kofar wani makeken gida motar patrole ta yan Sandan tayi parking Tunkafin motar tagama tsayawa ya bude murfin motan, ya Fita da Sauri yarda yake tafiya kadai zaka gane yana cikin Fushi ne da Fusata.

Inspector Sale ya kalleshi yana kada kai,bai Fito daga motar ba, yamata kwana ya juya lokacin agogon dake hannunsa yake nuna karfe 1:00am na dare,shiko yana zuwa jikin get dinsu yasaka hannu ya shiga bugawa da karfi kamar zai tashi sama,megadi dake zaune gefe gyangyadi yafara dibamshi kamar amafarki yaji bugun get,da hanzari ya mike sanye da yake da uniform irin na yan mopal,koda yaji bugun bai razana ba,Nufar get din yayi yana Fadin"Who iz dis..?

Tsaki yaja kafin yace *AM SALEEM FREEKING KABIR KUMO..* Yafada ransa na kuna,da hanzari jikinsa na rawa da bari yabudemai karamar kofar yana Fadin"Am sorry sir did know...."Baigama Rufe baki ba ya wucesa Fuu kamar iska baki ya rike yana binsa da kallo,domin a iya saninsa Saleem baida dabi'ar shariya.

Maida kofar yayi ya Rufe yana Fatan Allah yasa koma miye ya Faru mai dadi yadda yake alfahari da wanda zai gaji Yallabai.

Babbar kofar da zata sadaka da babban falon gidan Abude take,sakamakon ansan komai dare zai dawo yana Shigowa Falon babu kowa yadda yake tafiyane zai ankarar da mai kallonsa kamar agauce yake.

  *CP KABIR KUMO* dake tsaye kofar dakinsa ya kuramai ido yana kallonsa yana neman Shiga dakinsa ne yasa yayi kiransa.."Saleem...."Yafada cikin datattako,Waigowa yayi da sauri yana kallon Abbin nasa,saurin sadda kai yayi saboda kada Abbin nasa ya fahimci halin dayake ciki kakalo mirmishi yayi yana Fadin"Na dawo Abbi..."

Gyada kai yayi yana Fadin"Ai na ganka,ammh why naganga kamar azafafe..? Saurin Washe hakora yayi yana Fadin"la babu komai Abbi,barci nakeji dat why na dawo da Wuri.."Yafada yana Jin takaichin karyan dayayi,kallonsa kawai Abbi yayi kafin yace "Ok sai da safe.."Yafada yana kuresa da ido,da hanzari yace"Sai da safe Abbi..."Yafada yana tura kofar dakinsa ya Shige da sauri,Yana sauke ajiyar zuciya.

Yana Shiga yayi tsaye yana karema dakin nasa kallo,hannu ya dungula ya daki bangon dakin,bayan kunnuwansa suna jiyomai amom muryanta,fuskarsa tana jin zafin karan Tafinta kana idanuwansa suna kallon sanda ta Tofamai miyau,ta watsamai kudi,kana kunnuwansa na jiyomai sanda tace yan sanda basu da wani amfani,sai yima mata fyade da shaye shaye? kenan harda Abbinsa tayi jam"i ? yazama dole ya binciko ko wacece wannan yarinyar domin yayi Saurin ankarar da ita kuskurenta.

Kan gado yafada yana dukan katifan kota ko"ina Yana fadi da karfi..* WLH SAI NA RAMA..."!* yake Fada yana jin wani tukuki daga kasan ransa,har sai da wasu hawaye suka zubomai,yasaka hannu ya sharbe kafin yace"No saleem kuka bana ka bane,juz stand up kayi karatu tukuri domin ka zama DAN SANDA,ka nuna mata cewa ita bata karfin kowa ba,ammh duk hakan bazasu samu ba sai yafara gano ko  *WACECE ITA*..."

  _*Tirkashi....Salon na dabam ne,haka Jimarin na mussaman ne,wannan karon Abun zai taba zukata,wannan karon Abun zai taba kowa ne,Kada Abun ya daure muku kai Abu daya zaku nemo Wacece MALIKA MALIK.!? kuma waye wannan Dan MATASHIN SAURAYIN? miye alakarshi da Aikin yan Sandan? Duk ku biyoni Zan warware muku Zare da Abawa*_

_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *MALIKA MALIK* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0552179550* JAMILA UMAR GT BANK,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *09069067488* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyi KISHIN MATA na hafnan,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488,am srry a karshen Aliyu gadanga nayi mistake wajen Rubuta nombata maimakon na saka 69 sai na saka 60😂Fata zakuman izuri jikin tsufa ne😂👌🙋



*#Janafty..#*
*#Intelligent writers asso...#*

*💦MALIKA MALIK💦..!*
_(Sai na rama..)_

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ📚*

*_Mallakar:Janafty_*😘



*2*

_NIGERIAN POLICE FORCE-BIRNIN RUWA ZAMFARA STATE_

  """Wata babban Headquater ce mai dauke da haraba mai girma da Fadi,da ban sha"awa,ginin wajen gini mai kyau da tsari domin da Duste aka gina wajen.

Daga haraban Compound din Motocin Police sunfi guda goma Fake,awajen kana ga wasu yan sanda nan na shawagi awajen daga Inspectors sai su sargent suke yawo aharaban wajen Fuskarsu kwata kwata babu Annuri.

Daga cikin Babban ginin, akwai tarin Afisoci kafin kayi gaba karatsa wani dogon lungu ka isa kofar Office din Shugaban Headquater wanda Sunansa yake makale jikin wani dan Anini daga saman kofar Office din, *ACP SALEEM KABIR KUMO* naga an Rubuta da manya baki,ban tsinke da al"amarin ba,sai da kofar Office din ta wangale kanta,Cak na tsaya ina bin kayatattacen office din da kallo azahirin batu an tsara wannan office din,daga yammah wasu kujeru ne guda uku ga wani karamin center table mai kyau da tsari atsakiyar wajen,kana daga gefe ga wani karamin frigde,mai kyau da tsari,daga kudu,kuma kofar wani daki,wanda yake akulle,daga gabas,kuma wani katon Tebur ne mai dauke da Takardu da kuma Laptop,sai wasu kananun hotuna wanda suke sanye cikin Frame,sai daga chan sama kuma Hotuna ne,Farko na Shugaban kasa ne,sai daya na gwannar Jahar Zamfara,sai guda daya na Shugaban Yan sandan NIGARIA,IGP NA POLICE GABADAYA wato *IGP KABIR KUMO*.."

Ashe duk wannan Abun kalle kallen danikeyi ma mallakin office din na zaune akan kujeransa irin mai juyawan ne,ta juya dashi yabama kofar Shigowa baya,juyo da kujeran yayi Idanunsa duka suna Rufe ne,kuma dukka hannuwansa suna kan kirjinsa ne,da alamun yayi Zurfi cikin Tunanin dayakeyi,baki na sake ina karemai kallo cike da mamaki da al"ajabi.

Shiba fari bane Bakin mutum ne,ammh Ganin farko zakamai ka zata cewa Fatarshi batayi kama da yan Nageria ba,sai dai tafi chanchanta na yan kasar maroco,saboda yadda tahade tabada wani choculate,na kyau da tsari,doguwar Fuska gareshi sai dai tana  da dan Fadi kadan,Hancinsa dogo ne,wanda ya hade da bakinsa karami mai dauke da bakin Sajensa,wanda yakara ma Fuskarsa kyau lebensa Pick ne,yana Fitar da maiko kamar yasanya Man baki,giransa tana cike da gargarsa wanda taso ta hade da yar"uwanta haka gashin idonsa,Bude idanunsa dayayi ne yasa nayi baya ganin yadda Fararen idanunsa suka bayyana awaje,farare kal dasu gasu basu da girma na azo agani ammh suna cike da wani Sirri,mikewa yayi cikin azama yana goya duka hannuwansa abaya yafara zagaya office din yana cije baki,Ashe dogo ne sosai ammh yana da murjewa ta wadanda sukaji dadi da hutu sosai Wadanda ake kira giant,matashin Saurayi dan kimanin Shekaru 28 Aduniya,wanda akallo daya in kayimai zakayi mamakin yadda Yaro matashi mai kananan shekaru kamar sa zai iya taka wannan mtsayin,yana sanye da Uniform dinsa bakin wando da Rigarsa mai launin Ruwan Bula ammh light dinshi,daga hagu dan aninsa ne,mai dauke da Sunansa ajikin bayan gefen duka kafadunsa suna sanye da duka rank dinsa ma"ana amtsayin dayake kai ayanzu.

  Komawa yayi yazauna yana Dora kafansa daya kan Daya,wayarsa ya zaro wata faskekiyan wayar Kirar Samsumg,yana latsawa kafin hotonta ya bayyana,tana sanye da Riga da wando black and white,kayan sun dameta bayan sun Fitar da duka Surarinta waje,kanta babu kallabi,illah dogon gashinta wanda ta daure atsakiya da band,ta saki jelan yayi kasa,fuskarta sanye da wani bakin glasa,yacikamata rabin Fuska,kafarta kuma wani takalmi ne,mai tsini wanda har ya Wuce misali lokaci da aka dauki Hoton tana saukowane daga matattakalan benen Jirgi,wasu Exscorts suna biye da ita su biyu kowanne sanye da Court sun saka wasu galasai Abun sai wanda ya gani,daya yana dauke da Brief case,sai daya yana dauke da wata karamar jaka na mata,kunnanta yana sagale da waya tana mgana sanda aka dauketa hoton da alamun ma bata da masaniyar sanda akayi hoton.

  ""Kuramata ido yayi zuciyarsa na bugawa,Tuni hoton Abunda yafaru Shekaru biyar baya ya Shiga dawomai daki daki,har saida ya dafe kuncinsa ba dama inda ta shararamai mari,,har sai da ya Runtse ido,kamar alokacin take marin nashi,matse bakinshi yayi yana Shafawa,daidai inda ta tofamai miyau,idanunsa ya Runtse yana Sauke ajiyar zuciya yana tuni sanda ta watsamai kudi ajikinshi tana kiran aikin yan sanda da Rubish,Saurin bude ido yayi yana wani Zare ido,tsoro naji saboda ganin yadda gabadaya jijiyoyin kansa suka Fito radau,ga idanuwansa sunyi jajir kamar barkoni bayan gabadaya muscle din hannuwansa sun bayyana suna wani motsi daga cikin Abun tsoro wlh..😥

Wayar ya kifar akan teburin kafin ya mike azuciye kamar tana gabanshi yasaka hannu ya daki gaban Teburin yana huci yake fadin", *MALIKA MALIK..Sai na rama.."Nayi alqawarin sai na wulakanta rayuwarki sai na nuna miki ke ba kowan kowa bace,sai na miki matsayi tare da zati,jarumta da sadaukanta yafi komai muhimmaci,wlh tallahi sai na nuna miki mtsayin kakin yan Sanda yafi uwarki yafi ubanki da duka danginku da dukiyar dakuke takama...!!!!"Yafada yana Fitar da huci Shikadai kafin yakoma yazauna jagab yana Ajiyar zuciya.

Duk tsawon wannan Shekarun daidai da Rana daya baitaba barin Abun yafita daga Ranshi ba,barci yake,cin abinci,wanka yakeyi karatu yake,driving yakeyi,komai in yana yi sai Abun ya fadomai,zuciyarsa taki barinsa sukuni daya Runtse ido ita yake gani tana tsaye gabansa tana aibatanshi tare da wulakanta martaban mahaifinsa bayan ta hada ta shararamai mari,kamar wani sa"anta yarayu cikin wadannan shekarun cike da zumar da zati na Ramuwar gayyah ga malika malik,duk iya tsawon wannan Shekarun daya kwashe baitaba yarda yabar bibiyar Rayuwar Malika ba,duk wasu bayananta da hallayanta da komai nata yana dashi kuma ko"ina zata yana da ido kanta,bai ta bari koda ta minti daya yarasa wani Abu game da ita ba,saboda ita ya chanza burinsa na zama *ENGNEARING*,saboda ita ayau yake zaune awannan mtsayin domin ya nunamata Wutsiyar Giwa tayi nesa dana Rakumi,kuma tsakanin shi da ita kamar tazaran sama da kasa ne.

Da hanzari ya mike yafara tararra kayansa,Wayarsa ya maida aljihun kafin ya maida laptop dinsa ama"ajiyarsa key din motarsa kawai ya dauka ya Fice da hanzari,yana Fitowa suka dinga kamemai suna Fadin"Sir.."ko kallonsu baiyi ba iilah jefama wani daya daga cikinsu key yayi yana fadin"Close d office,..Kai kuma Sargent musa follow me,Abuja zamu yanzu.."Gabadayansu suka amsa da ok sir Safe landed.."Har yafara taku ya waigo yana kallon Sargent musa yana Fadin"Bring d key back to me sargent musa,i will drive my self juz take care, komai kenan zamu waya sai Monday,zan dawo ok.."Da kai suka amsa kafin sargent musa ya mikamasa key din motar,da sassarfa ya fice suka mara mai baya,sai da suka rakasa har wajen motarsa 320 kirar Toyota,Sargent musa ya budemai gidan gaba ya Shiga,sai da ya daura belt kafin ya bama motar Wuta rufemai kofar motar sukayi suna dagamai hannu,mirmishi yayi musu yana kara jadaddamusu su kula sosai,ribas yayi yana danna hon da hanzari megadi yazo ya wangalemai babban get din waje ya sulala zuwa waje da gudu,sanin dayayi akwai Tafiya agabanshi yasanya yasakarma mota Wuta,duk da yasan ko atsarin doka hakan ya haramta,ammh bashi da zabi dole ce tasashi yin haka domin yana bukatar isa Abuja kafin duhu ya shiga,sanda yake duba Rantsatsen agogon Fatan dake hannunsa Hudu saura kwata,jinjina kai yayi bai Fita daga garin zamfara ba,sai da ya tsaya awani masallaci yayi sallar La"asar kafin ya dauki hanyar Abuja.

   ________________

_GARKI ABUJA_…

  Karfe 8:30pm na dare yasaka Hancin motarsa Cikin Rantsatsiyar anguwan nasu tamasu hali,wato GARKI,wani tamkamen gida naga yana ta zuba hon,inda megadin gidan yazo da hanzari ya wangalemai get,Koda ya sulala ciki,parking space ya nufa inda ga motocin nan birjit,afake akaton haraban gidan,gidan gabadaya dauke yake da Security yan mopal,sukai su goma suna zagaye gidan,megadin da kanshi yazo ya budemai yana Fadin"Barka da zuwa yallabai.."Amsawa yayi yana Shafa kanshi Motar Ummi dake fake a haraban gidan ya kallah ajiyar zuciya ya sauke,Thank god Tunda Ummi tana gida yafada aransa,Wayar dake aljihunsa yafito dashi daidai lokacin da kiran *YA MARWAN* yafito daga wayarsa da hanzari ya daga yana Fadin"

"Wai nikan Yaya marwan,bazaka iya kwana bane, batare da kaji muryata bane..? yafada yana dagama Mopal din dasuka sarama hannu,,hanyar dazai sadashi da Falon gidan,ya nufa yana dariya jin Abunda Ya marwan ke fada"Kai kai..lallenema yaron nan,daga ina kula da Amanan Abbi,sai na murdema kunni in nadawo malalacin Acp kawai"Dariya ya kece dashi daidai yana Shiga falon,tsaye yayi yana Fadin"Kai ya marwan,kullum haka kake cewa,ammh kaki dawowa u know  we all miss u ko.? yafada yana kokarin zama a daya daga cikin Royal chair din dasukayima Falon Kwanya,kawai yaji kikam ta fadomai tana Fadin

"Oyoyo Ya saleem...."Take Fada Tana ihu,saboda yadda ta fadomai harsai da wayar hannunsa ta subuce tafada kan kujeran da yake kokarin zama,dagowa yayi yana riketa dakyau kunnanta ya murde yana Fadin"Yarinyar bakijin mgana ko? Baki ta bare da karfi tana Fadin"wayyo Allah kunnena Abbi,Ummi ku fito ya saleem zai karyamin kunni na, yarage min sadaki.."Take Fada tana kware baki harda buga kafa,shiko da gangan yakara murdemata kunni yana Fadin"Har yaushe ne,zan ce kidaina fadomin ajiki kai tsaye,ke bakisan kin girma bane.."? yafada yana dalle mata baki da dayan hannunsa,yana dariya yace"Dallah yima mutane shuru,ai babu mai zuwan cetonki..."Gum...!Yaji an makamai Filon kujera a keyarsa lokaci daya da Fadin"Sakarta don mai garinku kumo.."Tafada tana tsaye tana hararansa,dafe keyarsa yayi bayan ya saki *SALEEMA* wacce takoma gefe tana Fadin"Yauwa hajiya,ramamin..? tafada tana murza kunnanta saboda zafin dataji bana wasa ba.

Da Kallo yabi *HAJIYA BABBA* wacce ke tsaye da Filon kujera tana Fadin"Ai Tunda naji ihunta nasan Azzalumi ya dawo,wlh duk kakoma dukanta sai naci kaniyarka acikin gidan nan,yarinya tazama budurwa ko yanzu aka kaita daki zata zauna,ammh kana jibgarta kamar kasamu jaka..? Tafada tana Hararansa again,Bata Fuska yayi yana kallon Saleema wacce hajiya ta karisawa wajenta tana fadin"Muga Fuskar da kunnan,wlh indai naga Shaidan yatsu sai yabiyamu,kowani yatsa dubu daya ne,dubu biyar dinmu

Please Login or Register in order to submit comment