Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin Abun ya ishesa Din nan, dankawafar da wayar yayi yana tsaki bayan naga sunan mai kiran *FRIEND* ne da manyan baki,Idanuwansa ya kankance aransa yana Jin in ya hadu da saleema sai yaci ubanta,Bakin yarinyarnan kamar sikat,saboda rariya jikinta narawa komai akayi agida sai ta kira sadiq ta sanarmai kamar wata Sakarya,Abunda ya lura dashi daga shi har ita Tsofaffun munafukai.

Tun jiya daya dawo Sadiq keta kiran wayarsa yana kin Dauka,domin yasan Tatsuniyar gizo bata wuce ta koki,Mganar malika ne yake so yamai,shikuma haryanzu bai shirya Amsa wata tambaya ba,ko kuma ya budi baki yayi bayani Abunda ke gabansa kawai Sai ya rama ne,shiyasa yake ganin kiran yana kin dauka.

Wayar nasa ne takara dauka Tsuwa wannan karon dogon tsaki yaja ya mike daga kwance ya dauki wayar yayi niyyar ya dagane ya danna mai ashar sai yaga sunan Abbi na yawo asaman Sreen din wayar tasa,jikinsa na rawa ya daga kiran yana Fadin"Barka da Safiya Abbi.?

Dagachan bangaren Abbi ya amsa da cewa"Lafiya lau Acp,ya aikin? ya karba da"Alhadulilallah Abbi ya gida dasu Ummi...? Abbi yace"Gida dukkansu suna lafiya,jiya kuma sai ka tafi ba sallama ko? Kunya takamasa sai ya kama sosa bayan keyanshi yana yar dariya yarasa tacewa,yar dariya Abbi yayi irin nasu na manya kafin yace"Mu bar wannan mganar,yanzu dai dalilin kiranka danayi dama juz na tambayeka tsakaninka ga Allah ne,Shin meye dalilinka nason Auren Diyar Alhaji Abdulmalik Dan kasuwa..?

Gaban Saleem ya Fadi nan da nan zufa tashiga ketomai ta ko"ina azahirin gaskiya bazai iya sanar da Abbi dalilinsa na Son auren malika ba,kuma bazai iya sanar dashi don Allah yakeson aurenta,kada Allah yakamashi da laifin karya,gashi Abbi ya daureshi da cewa ya sanar dashi tsakaninsa da Allah.

Kame kame yafarayi Muryansa na Rawa Abbi ya katsesa da cewa,"Kaga Ka natsu ni ba ina Turke ka bane naji dalilinka,ni Abu dayane nakeson ji,Allah yasa ba zargin danike akan ka bane,..? Saleem ya aro baki dakyar yace"Abbi wani zargi kake akaina..?

Kai tsaye Abbi yace"Ina tsoron ko saboda kudin mahaifinta kakeson auren ta..?Ajiyar zuciya ta kwacema saleem ya saukarya yana jin wani sanyi aransa kai tsaye yace!Wlh Abbi Waye Allah..? shine Shugaban halittun duka Duniya ko? Toh Tallahi ba saboda kudin mahaifinta bane,haba Abbi kafi kowa saninmu,mu har wani kudi ne zai Rufemana ido,me muka nema muka rasa agidan Duniya.."

Mirmishi Abbi ya saki kafin yace"Alhamdulillah,Naji dadin jin haka,dama Fargaba na daya kada wannan ne dalilinka daga baya azo ana jin kunya,Masha Allah jiya naje katsina na hadu da mahaifinta,dayake munada kyakyawan alaqa dashi na sanar dashi komai,kuma shima ya nuna murnansa kuma yayi na"am da mganarka.."

Washe baki Saleem yayi kafin yace"Nagode Abbi Allah kara girma..."Abbi ya Murmusa yana Fadin"Ameen,ammh yanzu yace yana son ganinka,so in kasamu lokaci sai kaje ku gana ko? gyada kai yayi yana Fadin"To shikenan Abbi babu damuwa ko gobe ne sai naje ya ganni.."Abbi ya jinjina kai yana Fadin"To babu mtsala zan kirasa na sanar dashi zuwanka,kai kuma zan Turamaka nombarsa kaji ko.."Amsawa yayi da cewa,"Naji Abbi Allah ya biya bukata ngd sosai..."Daga haka sukayi sallama.

Saleem ya tashi da sauri ya daka tsalle yana Fadin"Game din ya kusa karewa fa..."Malika malik ganin nan zuwa gareki.."Yafada yana wani Cije baki bayan ya datse lebenshi na kasa,yana wani juyi kamar wani zakin daya dade bai ga abinci ba.


___________________


Shiko Abbi koda yadawo koda wasa bai sanar da kowa Abunda yake Faruwa ba,kama bakinshi yayi ya tsuke yana jiran Saleem yaje katsina ya dawo komai kenan daga baya kowa yaji,ko Hajiya data matsamai sanar da ita yayi sunyi waya da Alhaji Abdulmalik ya sanar dashi baya gari ammh da zarar ya dawo zai sanar dashi,toh dahaka ya kashe bakin Hajiya.

Itako Ummi bata kara marmarin karamai mganar ba,yasani ta sakamai ido ne taga iya gudun Ruwanshi,shiko yafi kowa karantarta tana da saukin kai,koman Turjiyanta kan Abu,da zarar ya tankwasata tana tankwasuwa,saboda yadda suke da Fahimtar juna,shiyasa bai damu da shariyanta ba,kuma mganar gaskiya duk wata uwa tagari bazata so Danta ya hada Zama ko Aure da Malika ba, domin kwata kwata bata cika sharudan zama mace tagari ba,Marwan ko Tun ranar litinin din yakoma,shi bai wani damu ba,don yana daukan mganar Saleem amatsayin Shirme ne kawai.

Shiko Alhaji Abdulmalik Ranar bai iya Runtswa ba saboda damuwa da Tunanin mafita,duk Farkawar da Hajiya binta zatayi sai ta ganshi zaune ya jingina da gado idonshi biyu ya Shiga zurfin Tunani,in ta tambayeshi yace mata bakomai takoma ta kwanta Kawai,Farkawanta uku tana ganinshi cikin wannan Halin,Na karshen ne tatashi tashiga tiolet ta wanko Fuska tazo ta zauna kusa da kafafunsa tana Fadin"Haba Alhaji,wai meke Damunka ne,Tun dazu  dana farka sai na ganka zaune ka zabga Tagumi,kuma na tambayeka kace bakomai,Bakomai ne zaka kasa barci Fisabillah...?

Tafada cikin kulawa Tana kallonsa,kur da ido,ajiyar zuciya ya sauke yana Sauko da kafafunsa kan lallausan Cafet din dake malale abedroom din,Dukar dakai yayi yana Jin Damuwa tayimai yawa,yana da bukatar Abokin shawara,Kuma yanzu bashi da kowa akusa dashi sai Binta,dalilin daya sanya ya dago yana kallonta kafin yace"Binta akaro na Farko Tun bayan aurenmu zan sanar dake damuwata ina Fatan zaki bani shawara don Allah..?

Gyada mai kai tayi tana Fadin"insha Allahu Alhaji,dama amfanin zaman tare kenan..."Kada kai yayi kafin ya shiga zayyanamata yadda sukayi da IGO KUMO,har zuwa karshe ya karishe da Fadin"Ya kike ganin za"ayi Binta wlh ina tsoron sanar da Sweetbby wannan al"amarin bansan da wani Fuska zata kalli Abun ba infact ma ni banison Abunda zai bata ranta ,ammh mganar gaskiya inason Malika ta auri Dan wajen Kabir kumo,ko don samu ingantattacen tarbiyan dani mahaifinta na gaza bata..."Yafada cikin Raunin murya.

Hajiya tayimai zuru tana kallonsa cike da mamaki kafin tace"Tabdijam babban mgana Alhaji,ammh azahirin gaskiya najima malika murna,domin ko ba komai Aure wani Nau"i ne na Bautan Ubangiji,da kuma Fatan Rabauta ranar gobe kiyama,ammh kuma wani hanzari ba gudu ba Alhaji a yadda ka bata yarinyarnan bana jin ko kai dakake mahaifinta zata saurareka balle kuma wani,..."Tafada tana jinjina Abun.

Dafe kanshi yayi yana Fadin"Shine babban damuwana,Binta yanzu menene mafita..? Ajiyar zuciya ta saka kafin tace"Mafita dayane Alhaji,sai dai aboye wannan mganar kada asanar da malika sai bayan an daura auren kana,koda zatayi borinta na dan lokaci ne Tunda anrigaya da an Daura auren.."

Kallonta yake yana jinjina kai alamun gamsuwa da shawaranta yace"Shawara mai kyau Binta,kinga yadda ma Tafiye Tafiyen kamfafoninnan suka gabato zata kashashe biyu ina jin kwanannan,Allah barshi sai ansanya lokacin bikin daidai lokacin da zata dawo..."Hajiya binta tace"hakan ma yayi Alhaji Allah dai ya Shigemana gaba...Da Ameen ya amsa kafin ya cigaba da sanar da ita sauran Shirinsa ammh zai ijeye komai sai yaron yazo su Tattauna.


_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *MALIKA MALIK* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *09069067488* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

09069067488




*SHAKIRA*

*MALIKA MALIK...!*
_(Sai na rama..)_

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ📚*

*_Mallakar:Janafty_*😘


_Masu tambayan *MALIKA MALIK* ko yakoma Free ne,No bai koma ba,yanan Ana saidawa kan Farashi mai sauki gamai bukatar Siyan Malik malik zai iya Turamin 200 kachal👌ta wannan account Nombar 0552179550,bayan kin Turonin hoton sreenshoot din payment din ta wannan nombar wayar 09069067488,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar wayar shima 09069067488,kai tsaye bayan an dauki hoton katin_


*Ina maraba daku masoyan gaskiya*😘



*7*

   ""Washegari da misalin karfe 10 da wani Abu na Safe Saleem yadau hanyar katsina bayan ya kira Abbi yasanar dashi,shikuma yakira Alhaji Abdulmalik ya sanar dashi ga saleem nan zuwa.

Shi ya tuka kansa,shiyasa  ya isa akan lokaci domin dama Saleem akwai gudu amota kamar zai tashi sama,koda ya shiga cikin garin katsina bai sha wahalan gane gidan ba,sakamakon gidan Alhaji Abdulmalik Dankasuwa ba boyayye bane a katsina,cikin lokaci sai ga motarsa ta tsaya abakin makeken gidan,wanda yake kama da wata al'karya guda.

Hon ya zuba Kafin megadi ya leko yana Tambayansa sunansa kai tsaye yace"Saleem kabir kumo..."Bai yi watawata ba ya wangalemai kofar get din motarsa kirar 4matic ta sulala ciki domin dama Tuni an san da zuwanshi.

Aparking space ya Faka motarsa kafin ya Fito yana bin haraban gidan da kallo,wanda wasu tafka tafka motoci iya kallon ka mallam,sukama gidan kwanya gefe daya kuma excorts din Malika keta zagaye suna wani Mazurai Dan ware ido yayi yana bin benen gidan da kallo yana jinjinama fasahar bazanin da maginin harda wanda aljihunsa yayi kuka,domin duk Abunda yake zato,toh ya ganshi Fiye da Tunaninsa.

Komawa yayi ya jingina da motarsa Yana wasa da key din motarsa,sanye yake da Shadda mai Ruwan kasa wacce taji yarari da maiko,dinki tazarce ne yayi matukar amsansa,gefe daya kuma ya dora wata hula zanna bukar itama mai alaman zanen Ruwan kasa,hannunsa sanye da agogon Fata na kamfanin Rado,shima mai kalan Ruwan kasa,bayan takalminsa shima Rufaffafe ne na Fatar damisa,shima kalan Ruwan kasa,kallo daya zakamai kaji kakasa kara kallonsa saboda yadda kwarjinsa da haibansa ke tasiri a idon wanda ya kallesa

mace kuwa komin Girmanta da ajinta,da isarta da takamarta da duk Abunda take takama dashi,in ta kalli saleem sai taji ta raina kanta da duk Abunda ta mallaka.

Bai Dade da tsayuwa ba,yaji muryan wata mace cikin hadadden Turanci wanda dagajinsa kasan mutum ba haye yayi ba,ya kware ne,daga gefensa kamar bazai daga  kai ba,sai yadaga idonsa ya Fada kan Malika wacce ke Tahowa daga bayan gidan Daga ita sai wani karamin mini sikat,da wata riga kai breziya ce ma,domin banda kokon nono bata tare komai ba gashin kanta ajike yake da karamin Towel akanta tana gogewa da hannu daya,dayan hannu kuma tana mgana awaya,fararen kafafunta da cinyoyinta awaje suna kyalli,bayan kafarta na sanye da wani Takami flat mai taushi.

Bayanta Merry ne da Dose,merry na Rike da robar Ruwansha,ita kuma Dose tana rike da wani karamin Towel din,dukkansu suna biye da ita kamar rakumi da akala,bai gama mamaki ba sai da yaga tabiyo ta gabanshi cikin wannan banzar Shiga ko ajikinta ta kuma ratsa ma,'aikatan gidan,wadanda suka kame mata kamar wata matar Shugaban kasa,Bayanta yabi da kallon Tir,yana jin wani takaichi aransa ganin yadda gabadaya idon kardawan arnan samudawan ke kan Hips dinta wanda ke Juyawa kamar wanda ake controle dinsu.

Saurin Kauda kai yayi yana kiran Sunan Allah,wani Siririn tsaki yaja yana Fadin"Lalle yarinyarnan ta Wuce da Tunanina,ashe tsinanniyace ta karshe bansani ba....'Yafada yana rike haba,yana bin Kofar data bi da kallo,Bai gama mamaki ba,sai ga Alhaji Abdulmalik ya Fito da hanzari cikin Fararen kaya yana saba babban Riga ya kariso wajen Saleem yana Fadin"Am srry na barka awaje ko..?

Yafada yana kokarin mikasa hannu ammh sai Saleem yaki bashi hannu sai ya rankwafa yana Fadin"Ina Wuni Daddy..."Yafada yana sadda kai,Dagosa Daddy yayi yana Fadin"Ash Tashi Tashi mana,Saleem ko..',?Yafada cikin Fara"a,

Gyada kai Saleem yayi yana Sadda kai,kafadansa Ya kama yana Fadin"Masha Allah..."Yana kallonsa murna da Farinciki sun cikashi ganin Saleem amtsayin Surikinsa koshi dayake Namiji kwarjinsa ya dakesa sosai,Yana Rike dashi Har zuwa Babban Falonshi na saukan baki,ya zaunar dashi bisa kujera,wanda Saleem din yayi saurin zamowa kasa yana dukar dakai.

Yar Dariya Daddy yayi yana Fadin"A"a Haba Saleem,maza tashi ka zauna da kyau nan ma fa gidanku ne,nima Abbanka ne ko Kumo bai sanar dakai bane..?"Yana duke ya murmusa yana Fadin"Ya sanar dani Daddy kayi hakuri kabarni anan..."Dariyan Farinciki Daddy yayi yana Fadin"Toh indai ka dauke ni a mtsayin Daddynka toh na baka Umarnin katashi ka koma bisa kujera kaji.."ba yadda ya iya,sai tashi ya koma bisa kujeran yana Kallon Cafet din daya karama Falon kyau.

Kallonsa Daddy yake ransa na Fari,Aransa yana ta Fadin masha Allah,waya ya daga ya kira Hajiya binta yace akawoma Bako Ruwa da lemo,ai ba'a dauki muntuna ba,sai ga Atika da Tire niki niki da lemuka da Ruwa ta ijiye gaban Saleem bayan ta duka ta gaisheshi,ya amsa bai kalli ma inda take ba idonsa na kasa.

Mikewa Daddy yayi yana Fadin"Bari na barka kasha Ruwa ka huta kafin nazo muyi mgana ko..? Mirmishi Saleem yayi baice komai ba har Dadddy ya Fice daga Falon jikinsa na rawa,Da kallo mai kama da harara Saleem ya bisa kafin ya saka hannu ya dauki Ruwan swan ya tsiyaya akofi yasha,Ajiyewa yayi yana sakin ajiyar zuciya Lokaci daya yana bin Falon da kallo Yana mele baki

Bai jima ba,sai ga Daddy ya dawo yana ganinsa yayi kasa da kai kamar wani na gari,nan ko zaginsa kawai yake aransa,domin hardashi abada Gudummuwar Wulakancin da Malika tayimai,kusa dashi Daddy ya zauna yana Dafa kafadansa kai tsaye yace"Sannu da zuwa,hop kazo lafiya..?

Saleem ya amsa da cewa"Alhamdulillah.."Alhaji Abdulmalik yace"Masha Allah nasan dai mahaifinka ya sanar dakai komai ko..",?Gyada mai kai kawai Saleem yayi,kafin ya cigaba da Fadin"Toh naji dadin hakan,yanzu Abunda nakeso dakai kamar yaushe ne kake bukatar ayi auren ...?

Saleem yaji ransa Fes,ammh sai ya basar yana Kara sadda kai yace"Daddy duk yadda kuka tsara ni awajena Daidai ne.."girgizamai kai Daddy yayi kafin yace"A"a ba ahaka Saleem ai kaine zaka zauna da ita,kai ya kamata ka sanar damu zuwa yaushe kakeson ayi komai agama.."Shuru yayi kafin yace"nan da Wata daya yayi Ko...,?

Daddy yace"Yayi sosai ma,Allah ya nunamana yanzu kana wani aiki ne...? Saleem yace"Ina aiki a zamfara ne,karkashin wata headquter,a mtsayin Acp..."Washe baki Daddy yayi yana buga kafadansa yake Fadin"Wow Bravo...Ashe magajinn kumo ne,gaskiya am so happy to hear dat,Allah ya taimaka.."Yana mirmishi ya amsa da Ameen.

Gyara zama yayi yana Fadin"Kana da muhallin ma"ana wajen da zaku zauna...? gyada kai Saleem yayi kafin yace"Eh inada dan madaidaicin gida anan zamfaran..."Shuru Daddy yayi kafin yace"Toh babu laifi,ammh akwai Abunda nakeso na sanar dakai,bawai don zaka auri yata ba A"a don kaima kana mtsayin Dana ne ko ba malika zaka aura ba,zan maka dukkan Abunda yakamata.."

Saleem ya jinjina kai yana Fadin"Hakane Daddy..."Yace "Toh Abu na Farko Shine bani son ka kashe sisinka amganar auren nan bayan sadaki,duk wani Abun bukata,kama daga lefe da gidan da zaku zauna duk zan tanadar muku kaji.."Mirmishi Saleem yayi kafin yace"Ayi haka Daddy...'Kafadansa ya dafa yana Fadin"Karka damu Dukkanku ya"ya ne,so yanzu sauran mganr zamu tattauna da mahaifinka kaji ko,Allah yayi maka albarka yakuma baku zaman lafiya.."Afili ya amsa da Ameen ammh cikin ransa ba Ameen ba yake fadi ba,yana ayyana yadda rayuwarsa zata Cutu matukar Allah yabasu zaman lafiya da wanchan tantiriyar yar iskan.

Mikewa Daddy yayi yana Fadin"Yanzu zaka Wuce ne,ko akirama ita ku gaisa ne?."(Shima dai kawai ya Fadane kada Saleem din yagano ita malikar bata sani ba...) Saurin Girgiza kai saleem yayi yana mikewa yace"A"a Daddy rabu da ita,zan dawo insha Allahu,yanzu ma ina Sauri ne aiki yayiman yawa a office ni zan koma..."Daddy yace"Haba ka tsaya kayi lunch mana!Saurin girgiza kai yayi yana Fadin"ngd daddy..."

Bai hanashi ba illah Shiga ciki dayayi ya kira Hajiya binta suka gaisa,wanda itama ta yaba da Saleem din,kuma aranta tana ganin Malika ta samu daidai da ita,har bakin mota Daddy ya rakasa yabashi rafar kudi yan Dubu ammh Saleem yaki karba sai da yaga ya nuna baiji dadi ba kana ya karba,har ya Fice daga gidan yana dagamai hannu da Fatan Allah ya kaishi lafiya.

Saleem na tuki yana cin dariyan Ladabin karyan dayayima su Alhaji Abdulmalik,domin harga Allah baya wani ganin mutumcinsa,kawai yana mai na yan Duniya ne,ammh ina Abun girmawa anan wajen,yana babba ammh sam baida Tunani yabar yarinya na Abunda taga dama,ammh no wahala karshenta ya kusa zuwa,domin dama yace wata daya ne don ayi komai a Wuce wajen,Yaci burin yadda Adare daya malika ta chanzamai rayuwa,shima yayi al"kwarin chanzamata shi awannin goma ne bama sai an kai ga cikar dare ba,kudin daya bashi yake kallo yana harara,yana fadi afili,"Dole mana kabani kudi,Tunda za"a Tusa min Ragowar arna,yaga yaro shar zai makalamin tsohuwa,yo tsohuwa man wanda naba shekara daya,ai ta tsufa..."yafada yana sakin tsaki yana cigaba da hararan kudin kamar sune Alhaji Abdulmalik din.

   *****************

Saleem bai kira Abbi ya sanar dashi Abunda ya wakana tsakaninshi da Alhaji Abdulmalik dan kasuwa ba,shi da kanshi ya kira Abbi ya sanar dashi komai kuma yana kara yabawa da Saleem din,Ada Abbi yaso yayi Turjiya game da Cewar dayayi sadaki kadai yake bukata,ammh sai shi Alhaji Abdulmalik Dankasuwa ya nuna daga Saleem din har Malika shi uba yake garesu,saboda yana da hakkin yimusu dukkan Abunda ya kamata,nan yake sanar dashi ya tsaida mganar auren nan da wata daya,.

Abbi yaji dadin karamcin Alhaji Abdulmalik har ya nuna yana so yan"uwanshi baffanninshi da suka rage akumo zasu agabatar da neman aure,Alhaji Abdulmalik ya dakatar dashi da cewa basai sun zo ba ai duk Abun na gida ne,su bari Ranar daurin Aure sai suzo tare da Sadaki,babu komai shi ya riga yaba saleem malika har Abada,da wannan mganar sukayi sallama cike da Farinciki.

Abbi baya da zabi illah sanar dasu Ummi halin da'a ake ciki,wanda Hajiya ce kadai ta nuna murnanta Afili ,ammh Saleema da Ummi Kamar su fasa ihu saboda bakinciki,Saleema ta bude baki tana Fadin"Haba Abbi yanzu Fisabillahi in yaya Saleem baida hankali da Tunani sai ka biyemai,yanzu don Allah duk matan Duniya yarasa wazai aura sai Wannan yar iskar...?

Tafada idonta cike da kwallah,hararanta Abbi yayi yana Fadin"Kul na sakejin kina kiranta yar iska,iskancin me tayi miki toh zan sabama miki wlh in bazakima dan"uwanki Fatan alheri ba juz keep ur mouth shout tunkafin na saba miki wawiya kawai...",Yafada cikin Fushi.

Saurin mikewa tayi tana kuka ta Wuce zuwa dakinta,Ummi dake zaune batace komai ba,Hajiya ce ta kalli Abbi tana Fadin"Wai ni kabiru Meye dalilin da yaran nan basu son Auren nan,kodai ba diyar kirki bane...? Ummi tayi Saurin taran hajiya tana Fadin"Wlh bs diyar kwarai bace Hajiya,Yarinyar kwata kwata batayi kama da..."

"Aisha....."Abbi ya katseta da tsawa yana kallonta,shuru tayi da bakinta tana Jin wani daci aranta,Bai kara mgana ba ya tashi ya haye sama ammh daga yanayin kallon da yayimata Jikinta yayi sanyi,tashi tayi tabi bayanshi batare data kara cema hajiya komai ba,.

Hajiya tabe baki tayi ta mike tana Fadin"Allah ya kyauta..."Daga haka ta shige dakinta Ranta fes Domin Dama babban burinta shine su Saleem suyi aure tagaji da ganinsu haka ba iyalai.

Shiko Abbi yana Shiga daki sai ga Ummi ta biyo bayansa tana Shigowa ya tasomata yana Fadin"Haba Aisha meyasa kike haka? ke yanzu Abunda kikayi Yayi kama da Abunda uwa tagari zata aikata,kada kimanta kema kinada Diya mace,in aka aibatata zaki ji dadi? kada ki manta Allah shi ke shirya wanda yaso ya batar da wanda yaso,nasan kuma kina da sani kan hakan bayan karatunki na Shari"a low kina da karatun Addini daidai gwargwardo,why kika aikata haka?


Yafada yana kallonta kur da ido ganin yadda jikinta yayi sanyi ne yasa ya juyamata baya yana Fadin"Kin bani mamaki Aisha,wlh ayadda na sanki mai hankali da hangen nesa banzata zaki ki bada goyon bayan Saleem yayi jihadi ba,baki Tunanin in ya aureta ya natsarta da ita,dani da ke dukkanmu munada lada? Gaskiya ban zan boye miki ba u already disoppoiting me Aisha..."

Yafada Yana jadda  kalamansa,Kukane ya kwacemata ta isa gareshi ta rumgumosa tana Fadin"Kayi hakuri yallabai,wlh nakasa sarrafa zuciyata ne na ganin Saleem ya auri yarinyar nan, da Duniya tagama saninta afannin rashin tarbiya da kamewa mezan cema yan'uwana da kawayena? wlh Abun kunya ne babban Amtsayinka na mai mutunci aji mun hada zuru"a dasu,sai ma afara zargin kila kwadayin Dukiyar mahaifinta ne ya Tsolemana ido...

Tana Fada tana Sheshshekan kuka waigowa yayi yana rikota gefen gado ya zaunar da ita yana Fadin"kalle ni nan Aisha.."kai tsaye ta dago tana kallonsa hannunsa ya mikamata ta kama kafin yace"Tun sanda kika zamo mata nake mika miki hannuwa na domin ki kama,yazama bango da majingini gareki,kuma har gobe zan cigaba da mikamiki ,Toh yau gashi na kara mika ,mi ki ki kama ki damke yazama kariyarki har gobe kiyama ki kuma saka aranki indai Dan dani Kabir na haifa tare da Aisha ne bazai zamo gafalalle ba,sai da ikon Allah,na yarda da zencenki na za"a ce ko muna hangen Dukiyar mahaifinta ne,yes Alhaji Abdulmalik yana da tarin Dukiyar da baisan yawanta da karshenta ba,ammh wlh tallahi Aisha Dukiyarsa bata taba tsolenmun ido ba,mena nema na rasa,akwai Abunda bazan iya mallaka bane anan Duniyan...?Babu shi to kisa aranki Da zuciya daya na yarda da wannan auren,ki kuma toshe kunnuwanki daga zencen mutane,dama wasunsu dayawa basu son akullah alheri,ki kuma yi kyakyawan zato ga Danki,kinsan Abunda zai aikata da wanda bazai aikata ba,don Allah ki Cire wannan Tunanin azuciyarki kisama auren nan albarka kuma ki Rufe kofar da wani zai kawo kushen wannan Auren don Allah....,"

Yafada yana kara damke hannunta hawaye ne suke shatatamata kawai sai tafada kan kafadansa tana Fadin"Na yarda kuma na saka musu albarka...Allah ya sanya alheri,ka yafemin yallabai,Akullum ina alfahari da samun miji gwarzo kamar ka,lokacin da na nemi kauce hanya sai kayi saurin dawo dani,Allah yabani ikon Yima biyayyah har karshen Numfashina,Allah kuma ya Shiryamana Zuru"a...."Da Ameen yayi ta karba bayan ya sanya hannu yana Sharemata hawaye yake Fadin

"Toh bar kukan hakan,Fushi ya kare ko..."Yafada yana dariya Kirjinsa ta fada tana Rufe fuska wai ita kunya,yar dariya yayi yana Fadin"A'eesh dita har gobe bani da kamar ki AISHATUL HUMAIRA..."Yafada yana Mata rada akunne,Rumgumeshi tayi itama tana mai rada akunni,nidai nayi waje Tunda dai naga ma"auranta sun daidata kansu dole na ja Siraran kafafuna zuwa waje😂


___________\_________

Tundaga Ranar Ummi ta fauwalama Allah komai ta karbi Auren saleem da hannu biyu,wanda harshi sai da takira tana mai Tsiyan yana Fushi da ita kwaso rantsuwa yayi yana bata hakuri,dariya kawai tayi tana sanyama auren albarka,aransa bai amsa da Ameen ba,don cewa yayi ai dama baki sakko ba Ummi,don ba auren gaske bane,na Ramuwa ne kawai na awannin kadan,ammh duk da haka bata makara ba😂

Saleema ko kwana uku takara takoma mkranta bayan taga gidan gabadaya anhada kai babu mai goyon bayanta,Ummi ce toh itama yanzu tabi bayan mijinta,Hajiya kuwa batama sauraran mutum indai ta Fahimci zai kawo wata sukane game da auren Saleem,shiyasa ta tattarara kayanta Takoma mkranta,kuma tayi alqawarin ko bikin yatashi wlh bazata zo ba,indai da wannan Jinin Turawan ne.

Ita ta kira ya marwan ta sanar dashi,wanda yaji Abun kamar almara,nan da nan ya hau Shafin instergram,ya bude shafin Malik malik,nan yaga badala kala kala nata,Tunda abokan aikinsa sunsha Tuka jirgin data ke ciki ita da Amintattun Escorts dinta,ammh shi bai taba katari da shegiya ba,duk da yasan lbrinta ba boyayyiya bace,anan nema yake ganin Jiya da misalin karfe 2:00pm jirgin daya tashi daga Abuja zuwa Amurka tana ciki wai tatafi tarin karama yan kasuwa sani da Duniya gabadaya ta Shirya akasar ta Amurka,irin hotunan data daura da shigarta Abun ba kyan gani,nan da nan zuciya ta debi Marwan ya daga waya ya kira Ummi yana Kumfan baki tana gani Saleem zai auri wannan Shegiyar yar iskan yarinyar.?

Ashe Abbi na kusa yako karbi wayar yayima Marwan din Fata fata daga karshe ya bishi da Nasiha mai kashe jiki,shima din jikinsa yayi sanyi Domin yasani Shi da Allah ya Shiryar dashi bayafi sonshi bane,haka Allah yake Abunshi shi zai raya wanda yaso,kuma ya kashe wanda yaso,shi zai Shiryar da wanda yaso,Allah shike da ikon Umartan Faruwan Abu nan take kuma ya Faru ko ya kasance,ya sanar dashi ko ya manta kissan Annabin Allah Annabi Yunus wanda yayi Fushi da mutanensa ya baro garinsu zaiyi hijira ya Shiga jirgi sai aka ga jirgi na tangal tangal,nan masu jirgin sukace akwai wanda yayima Allah laifi acikin Jirgin,nan suka ganoshi suka jefasa cikin kogin,shikuma Allah nan da nan ya Umarci Kifi data hadiyeshi,ya sanar dashi Allah yace acikin alqur"ani mai girma ba domin Annabi Yunus yanemi gafarar Allah ba da ya dauwama acikin cikin kifin nan har ranar tashin kiyama.

Hakuri yayi ta bama Abbi,domin Hakika duk Abunda ya Fada gaskiya ne, domin sau nawa zamu dunga aibata yan"uwanmu da jifansu da  munanan kalamai a maimakon murika musu Fatan Shiriya tunda munsan babu mai batarwa,kuma ya Shiryar sai Allah,kuma hadisi ne ingantattace sau tari Mutum zai Fara aiki irin na yan Aljannah sai yana gabda mutuwa aikinsa ya juye yakoma na yan Wuta kuma ya mutu ya shiga Wutan,ALLAH YA KAREMU...Kuma sau tarin mutum yana ta aiki irin nan yan Wuta kwatsam sai yakoma aikin yan aljannah,kuma ya mutu alokacin ,sai kuma ya Shiga Aljnanah,to mai zamu ce da haka? musani Aibata wani

Please Login or Register in order to submit comment