Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mumina ba dabi"a mai kyau bane.domin babu wanda yasan tsakanin Ubangiji da bawansa...


_Allah ka shiryemu kabamu ikon sarrafa zuciyarmu ta hanyar mai kyau_





_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *MALIKA MALIK* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *09069067488* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488

*Shakira*

*MALIKA MALIK...!*
_(Sai na rama..)_

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ📚*

*_Mallakar:Janafty_*😘

*8*

  "Yana zaune cikin Office dinsa aiki ya kacame mai Sargent musa ya shigo agabansa ya tsaya hannunsa asaman kansa yana Fadin"Weldone sir...."

Bai dago ba ya amsa da cewa"Weldon..Arm ya"aka yi ne Sargent musa..? Baya yaja yana Fadin"Yallabai kayi bako ne,yana waje yana son ganinka,ya shigo ne..?"Shuru yayi kafin ya dago yana Fadin"Bako kuma? Who...? Sargent musa yace" I don"t know sir buh kamar naga na gida ne"Tsaki yaja kafin yace"Let him in,buh dagashi bazan kara ganin kowa ba gaskiya a hv alot to do,koda wani ne yazo yana son ganina matukar iz not imfortant,plz tell dem bani nan ok..."saramai yayi kafin yace "Yes Sir..." Ya Fice da Hanzari,shiko yamaida hankalinsa kan karamar syestem din dake gabansa wanda da alamu dai Abunda yake yaja ra"ayinsa.

Sargent musa bai dade da Fita ya Turo kofar office din ya Shigo yana kwarara sallama."Assalamu Alaika..."Aka Fada ana yar dariya,Dago kansa yayi ya Jefa cikin na mai sallaman,kai tsaye bayan ya dauki hannunsa wanda ke rike da pen yana sosa gemunsa dashi yana kara kallonsa kasa kasa,shiko Sadiq dariya Abun ya bashi ammh sai ya doje, ya karisa yana Fadin

"Haba Friend kuma shikenan don kazama Mijin hajiya sai azubamu akwandon shara,kuma ma don katon Wulakanci bayan Rejecting din call dina dakakeyi na baro uzirin gabana nazo inda kake ba mirmishin maraba balle abani wajen zama, ko..? Yafada yana zama cikin daya daga cikin kujerun da suke Fuskar Saleem din.

Wani bad look yamasa kafin yace"Ammh wlh kai kam indai aka leqa Wuta baka to kila ka makaleni,😝gulma da munafunci suna cin gindinka shege Bawan mata kawai..."Dariya Sadiq ya sheke dashi yana Fadin"Uhum sai ba kai ba,wai meyasa kasama rayuwata ido ne,badama nayi magana sai kace na cika gulma,kuma in an bibiya wlh gaskiya nake Fada.."Yafada yana kara saka dariya,

Tsaki Saleem yaja kafin ya tashi ya isa ga karamin Frigde din dake office din ya dauko Ruwa mai sanyi yazo ya ijiye agaban Sadiq,yana mai zama kujerar dake kusa dashi yake Fadin"Naji mallam,yanzu dai lafiya Tunda ga Abia ka bugo sammako,ko kana  bina bashi ne...? yafada Fuska Daure,dariya Sadiq yayi kafin ya dauki Ruwan daya ijiyemai ya bude ya kurba kadan kafin ya ijiye yana Fadin.

"Nazo yimaKa Allah sanya alheri ne,naji Abun alheri,ance ma ansaka ranar aurenka kai da Diyar Dankasuwan nan Alhaji Abdulmalik,wama take da suna...? Yafada yana Rike haba,kuri Saleem yamasa da ido kafin yace"Ok nagode yaushe kazo garin..? ya fada yana basar da zencen,Shiko Sadiq ya gyara zama yana Fadin"Jiya na iso,kuma yau nace kai zan dakama sakkko naji dadin ratayeni dakayi baka daga kirana,ko kafarama irinmu nisa ne Tun yanzu..."Mirmishi Saleem ya saki kafin yace"Eh duk yadda ka dauka hakane,ya aikin..?

Sadiq yace"Normal,ya shirye shirye...? tabe baki Saleem yayi kafin ya mike yana Fadin"Babu wani Shirye shirye daga wajena kabaro wajen da"ake Shirya komai ma"ana gidan Abbi..."Dariya Sadiq yayi kafin yace"Friend nazo ne muyi Serious tok dakai,wai don Allah meye ka gani jikin wannan watsatsiyar yarinyar da har ka makale sai ka aureta...? yafada Shima Fuskarsa nasa na rage Fara"a,ko kallonsa Saleem bai yi ba yace"Me ruwanka Allah yasa Tambadaddiyace ba watsatsiya ba,ni naji na gani,so plz and plz Sadiq stay out indai akan wannan mgananr ne, matukar kanason mu cigaba da zama a mtsayin abokai...",Yafada babu wasa amganarsa.

Baki Sadiq ya rike yana Fadin"Haba Friend ina laifi don na gaya maka gaskiya,karka manta Ance mu zabama ya"yayenmu uwa tagari...."Cikin hargowa Da Fushi Saleem yace"Plz Sadiq i said stay out of it ko? kada ka Tunzarani nayi Abunda banyi niyya ba"Yafada idonsa yakada yayi jajir,kuma muryansa a kausashe,Shuru Sadiq yayi yana kallonsa kafin yayi ajiyar zuciya yana Fadin"Is ok,yanzu meye Shirinka akan shagalin bikin,bawani event ne,ko daga bangaren Amaryan...?

Saleem yayi kasake aransa yana Fadin"Kai Sadiq maye ne wlh,...? Fuska ba Annuri yace"Nifa ka ganni nan babu Abunda zanyi ko gayyata babu wanda nabashi aikin balle yazo ya wahala Saboda ni kai infact ma ni banda ku na gida babu wanda zai san da wannan auren nan,so plz mu chan wata hirar.."Yafada yana zama bisa kujeransa Fuskarsa kuma taki bada dama balle har Sadiq ya Fahimci wani Abu.

Duk yadda yaso ya bugi cikin saleem shiko yaki bashi dama,dole ya hakura suka shiga wata hirar,sai wajen la"asar kana yayi mishi sallama yakoma Abuja,bayan sun rabu kan gobe zai koma bakin aiki sai kuma Lokacin bikin na saleem in ya samu dama zaizo Daurin aure,shiko saleem yana mirmishi yacemai in bai samu lokaci ba kada ya takura kanshi,Abun yabama Sadiq mamaki,nan da nan kwalkwalrsa tashiga Tunanin akwai lauje cikin nadi,game da wannan auren na Saleem,ammh duk da haka zai cigaba da bibiyan al"amarin har ya gano gaskiya duk da Shi saleem din ya ki bashin damar Fahimtar hakan.

  _____________________

*BAYAN SATI BIYU*

Shirye shirye ta ko"ina ya kamkama,Abbi da kansa ya kira mutanen Kumo ya sanar dasu,tare kuma da sanar dasu lokacin biki,Hakama Ummi ta sanarma duk wanda yakamata yaji,ammh bata bada Fuskar wata mgana ta shigo ba,duk ba kasafai take iya sanar da wacece Shi Saleem din zau aura ba.daga ita har Abbi suna ta gayyan mutane da yan"uwa da Abokan arzuka ayayinda da ango da amarya basu san wainar da,'ake toyawa ba,Shi saleem bai yarda ya sanar da kowa ba,sai inspector sale,domin shine kadai yasan Shirinsa,ammh shikanshi baisan me yake Shirin aikatawa ba,kuma Tun bayan tafiyarsa baiji yanama sha"awar zuwa gida ba.

Shiko Alhaji Abdulmalik,Tuni ya kira chan Malumfashi ya sanar dasu,hakika sunji mamaki tare da al'ajabin jin wannan sangartattaciyar yarinyar zata yi aure? Abun tambaya wani dan asaran ne zai kwasan ma kanshi,haka kowa ya rayawa aranshi,Fatan alheri sukayi da murna,shima anashi barayin Shiri yake na mussaman Domin ana Saura sati biyu biki ya buga kayatattun katina,nashi dana Abbi wanda Direba guda ya tasa yakaima Abbi Abuja,akallon Farko kanama katin zaka Fahimci Abun na manya ne,mai fara fasa Abun Aduniya ba,saboda kada lbri yakai kunnann Malika komai ya tawarwatse.

Ana Saura sati daya bikin, kayatattacen ginin da Alhaji Abdulmalik ya sanya ayimai a anguwan GRA katsina ya kammallah wani gida ne upstair mai kyau da tsari bayan yaji makeken haraban mai dauke Da Fulawowi masu dadin kallo da ban sha"awa,wanda akallah zasu ji motoci fin ashirin basu san an ijiye komai ba,Tsarin gidan ko akasar Turai albarka,duk Abunda maleka ke so an ginamatashi acikin gidan,kama daga wajen wasanni,da kuma wajen wanka Swimming Fool,domin kusanta akwai shiga ruwa kamar kwado,Sai Tsarin kayan gida wanda kamfanin MAHARBA tazo ta baje kolinta acikin wannan gida kafin lokaci sun kawata gidan da kayansu na alfarma kalan Red and black duka kayan gidan komai da komai kalansa kenan,domin best colour ne na Malika,mai gayyah mai aiki,dakinta kuwa fadar yadda aka tsarashi bata baki ne,hatta da wasu ubansu sabbin kayanta wandanda take sakawa an Jeramatasu cikin wani makeken wardrope,mai kunshe da gilasai Abun sai wanda yagani.

Daki guda aka ware aka jeramata akwatunanta guda 40 wanda Mahaifinta ya dagi kirji ya bada kudi Hajiya binta taje Dubai tahado mata komai da komai na bukarar rayuwa,sai dai kash gabadaya kayan daga Atamfofi da lesuka sai material da kuma dogayen Riguna,babu Zabin Malika ko daya aciki,saboda ana Tunanin zata shiga kwaryan manya,Sauran akwatunan cike suke da kaya shake kama daga takalma,Jakukkuna,Kayan make up,sleeping dress,agoguna da Yan kunnaye Banda Zinare da Azurfa babu Abubda ke ciki,Abun fa sai wanda ya gani,daki ne guda ne aka ware musu suma kalansu Red and black ne,an jerasu gwanin ban sha"awa.

Shikanshi dakin Uban gayyar Acp Saleem kumo,kenan wanda ke upstair kusa da jerin dakunan Malika,An tsaramai shi,bayan yaji kayan more rayuwa shima Wardrope guda aka Cikamai da kaya kama daga Shadodi,da yadina babu na banza daga gezner sai yadi mai daukan ido,American Suit kuma na kowani kamfani akwai kama daga Hilfiger,Tommy,Armani,louls,Button Dolce,and Gabbana Bersace,DKNY,dukkansu kalan Bakake da masu Ruwan kasa.

Bangaren Turareka da lation kuwa Abun sai wanda yagani kamar za"a budemai shago,balla aje ga bangaren Takalma,gasunan ajere Reras,Kama daga sawu ciki zuwa Rufaffu na Fatar damisa ga jerun agogun nansa na Fata dana karfe na kamfanin Rado,Babu Abunda mutum zai nema ya rasa acikin wannan Dakin,domin duk Abun jin dadin Rayuwa da bukata akwai acikin dakin.

Daga haraban gidan kuma ya Faka musu Tafkakan motoci guda biyar Biyu na saleem,Uku na Malika na saleem Daya prado ce,sai dayar kuma matrix ce,sai ta malika Komferesor ce,607  kirar piagion,sai Accord,motocine na gani na Fada,kuma dukkansu sabbi ne, daga kwatano aka shigomai dasu diret kuma nan aka killacesu domin ma mallaka motocin sune zasu Shiga wanna kayatattacen gidan mai kama da Aljannah Duniya.

Lbrin Auren bai Fita waje ba,saboda tsoron kada lbri yakaima Malika tun tana chan,kuma jin hakan zai iya sakata taki dawowa gida ta Shiga Duniya yasan halinta sarai,shiyasa bai yarda gidajen Yan jaridu da sauran kafafan yada lbrai sunji batun baba,so yake sai bayan an daura sai afasama Duniya taji komai,Shiyasa Tun sauran kwana biyar da bikin Sukayi waya da Malika wacce daga Amurka,Babban birnin America ta Wuce U.S Taje kaima abokan karatunta ziyara,dagachan kuma england ta wuce wajen Dangin mamarta,Da sukayi waya sai ya sanar da ita tadawo gida nan da kwana biyu saboda akwai Suprise din daya Shiryamata bata kawo komai ba ta sanar dashi Visarta take jira,tana bisa hanyar Dawowa.

Ana gobe biki gabadaya duka bangarorin biyun gudajensu ya cika da yan"uwansu,na kusa dana nesa, Gidansu Saleem Tuni yan kumo suka hallarta mata anata shagali,ayayinda katsina kuma yan malumfashi kwansu da kwarkwatansu sun hallata mata da maza,saboda bikin dai zahirin batu za"a yi wadaka da abubuwa domin komai mota ke saukeshi kama daga ababen sha,da kuma snacks da sauran Abinci kuwa tun ana saura kwana uku da biki wani kayatattacen restaurant ke yo odar suna kawowa gidan,Abun sai wanda yagani

Joda ma ta iso Tun jiya domin Amminta na sanar da ita tayi alqawarin kallo bazai Wuceta ba,so take ga shin waye mijin na malika,kuma ya malika zata kare matukar taji Abunda mahaifinta ke kulla mata? duk ta anada tambayoyinta ne shiyasa ta tadawo daga mkranta da hanzari domin ganema idonta Abunda ke Faruwa koma nace yana kan Faruwa..

Daga Amaryar har Ango sai daren Daurin Auren suka iso gidajensu,wanda suka tararshi cike da jama"a Saleem bai damu ba domin yana da masaniyar komai,Sadiq ne Maye Tun safe ya iso ya dinga jeramai wayar Shuru haryanzu bai ganshi ba,Shiko yayi niyar daga zamfara su hadu aktsina ne,Ammh ya kama damunshi yasa har Abbi na kiransa,Wani Abun mamaki bai dade da zuwa ba,sai ga ya marwan ya kariso shima,wanda kwata kwata saleem bai so ba,yaso ne kowa yayi zamanshi don zuwan fa harga Allah baida wani amfani,saleema dai tace ayi biki lafiya ammh bazata samu zuwa ba haka ta gayama Saleem shiko yace Gaskiya tayi Dabara don baya gayyatan irinsu dama.

Malika ko koda adawo taga dangin Abbanta bata wani damu kanta ba, domin tariga ta raina musu arxiki duk azatonta anzo Maula da cin arzikin da"a ka saba ne,shiyasa bayan sun gaisa da Abbanta ta Shige dakinta bata kara lekowa waje ba don bata son hayaniya sam,kuma ko aranta bata kawo wa ita aka taru ba, domin ko amafarki batata zaton hakan zai Faru da ita ba.


*WASHEGARI..*

  _RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA..._… Ayau Jumma"a 17/1/2020 Dubban Mutane suka Shaida Daurin Auren *MALIKA ABDULMALIK DANKASUWA* Da angonta *ACP SALEEM KABIR KUMO* Akan sadaki Naira Dubu Dari Hudu da hamsin wanda mahaifinshi ya biya da hannunshi ayayinda wani Baffanshi dake kumo ya karboma Saleem Auren,Itakuma malika Kawun mahaifinta dake Malunfashi ya bada aurenta,wanda ya gudana Ababban masallacin jumma"a dake garin katsina.

Daurin Auren daya samu hallartan manyan mutane,kama daga kusoshi agwannati,yan kasuwa manyansu da kananansu,kungiyar direbobi,kungiyar Kwadago ta kasa baki daya,Sevil defence,yan mofal,Yan sanda manyansu da kananansu sun samu katin gayyata zuwa wajen wannan Daurin Aure,sai bayan da"aka Daura aure ne, kana Alhaji Abdulmalik Dankasuwa yabama yan jaridu,da kafar yada lbria sanin Abunda ke Faruwa,ko kafin kace kwabo Tuni lbri ya zaga duniya ta ko"ina Kowani Shafi ka bude na wasop,instergram ne,Fbuk,twitter,duka lbrin zaka gani yana yawo da cewa" *WANI ABUN MAMAKI AYAU MUKA GA TARON DUBBAN JAMA"A WANDA SUKA HADA DA KOWANI MUKAMAI AFALIN JAHAR NAN ANA GUDANAR DA DAURIN AURE BAYAN AN SALLAME SALLAR JUMMA"A ABABBAN MASSALLACIN JUMMA"A DAKE  LAYOUT,SAI BAYAN KAMMALLAH DAURIN AURE NE, MUKA SAMU LBRI DAGA BAKIN SHAHARARREN DANKASUWAN NAN WATO ALHAJI ABDULMALIK DANKASUWA INDA YAKE SANAR DAMU DAURIN AUREN DIYARSA CE WATO MALIKA MALIK,TARE DA ANGONTA ACP SALEEM KUMA,WANDA D"A YAKE GA INSPECTOR GENERAL OF POLICE NA KASA GABADAYA WATO IGP KABIR KUMO,SHIN YAYA MUTANE ZASU DAUKI ABUN,ACE DAURIN AURE YA"YAN MANYA KAMAR IGP KABIR KUMO DA ALHAJI ABDULMALIK DANKASUWA BABU LBRI SAI BAYAN AN DAURA AUREN,SHN BAKU TUNANIN AKWAI LAUJE CIKIN NADI..*? Haka kowacce jarida ke wallafawa asaman Shafinta kama da leadership,Dailytruth etc.

Shiko Saleem yana gefe shida Sadiq da ya marwan,wanda dukkansu suke sanye da shadda fara taji kyau harda manyan Riguna da hulansu zannah bukar suna ta hannu da mutane,shiko ango tunda aka daura auren yaji wani Faduwar gaba da kasala duk karkashinsa,da wani zumarshi na ramuwa yaji ya Fitarmai aka,yana jin wani Abu mai kama da nadamar Abunda zai aikata ammh kuma bashi da yarda zaiyi domin bakin alkalami ya rigaya daya bushe,Bai ji faduwar gaba sai daya dinga samun waya ta ko"ina da sakonnin Fatan alheri,da kuma tsiyan yayi aure babu lbrin hatta abokan karatunsa da abokan aikinsa lbri yaje musu,Ya marwan ne yake sanar dashu lbri yazaga duniya don harda hotunanshi da Malika ansamu masu hadashi waje daya an dorashi bisa media akasa an saka *COUPLES OF D YEAR* Shi ahoton yana sanye da kakinsa na yan sanda ne,sanda Sadiq ke numai hoton wanda aka watsashi a Twitter,ya tuna sanda akayi hoton sanda Tsohon Inspector general ke sanya mishi Rank din karin girmanshi ne sanda ya zama ACP abuja akayi hoton,shine aka yanke IGP na lokacin aka hadashi da malika wacce ta ke sanye cikin riga da wando black and white kanta babu dankwal gashinta ta saki jelan ta baya,bayan ta tamke samanshi da band,kunnenta makale da waya,alamar kamar ma tana Tafiya ne,aka yanke hoton aka hadasu, sharrin Na"ura ace tare suka dauki hoton.

Kanshi gabadaya ya dau zafi,barin ma sanda yaga Abbi cikin mutane yana ta gaisawa dasu bakinshi har kunni saboda murna da Farinciki,suna wajen har mutane sukafara watsewa,yan jarida ko sunan suna haskawa abubuwan dake Faruwa awajen kai tsaye harshi sun so suji ta bakinsu ya daure Fuska yaki basu dama,Shiko Alhaji Abdulmalik bayan sungama Gaisawa da mutanen da suka gayyata sai gasu sun jero shida Abbi hannunsu sarke dana juna kowannensu yaci Farar shadda harda malum malum,Fuskarsu na bayyanar da Fara"a da kuma Farin cikin dasuke ciki.

Haka suka kariso wajensu,wanda dukkansu suka zube suna gaishesu,ammh banda saleem don Fuska yayi yaki bude baki gabadaya domin Gabadaya yanzu kowama haushi yake bashi,Alhaji Abdulmalik ne ya Umarcesu kafin su wuce Abuja zai gabatar musu da wani Abu,nan da nan suka shishshiga mota suda tawagarsu sai Gra.


Koda megadi ya bude musu get suka sulala ciki,da mamaki suka firfito suna bin gidan da kallo da alamun dai komai sabo ne kama daga motocin gidan yadda suke lullibe cikin tamfol,Daddy bai yi wata wata ba ya damko hannu Saleem ya zuramai makullaye har guda uku,Tsaye yayi yana kallonsa,shiko kafadansa ya daka yana Fadin"Kowa ya Shaida,Wadandan makullayen naka ne halak malak,daya makullin wannan gidan ne, inda zakuyi rayuwar aure kaida malika,Sauran biyun kuma keys din sabbin motocin dana siya maka ne Gift din Aure amatsayina na Uba gareka..."Gabadaya sai su Sadiq da marwan da sauran mutanen wajen,suka dau kabbara,Shiko saleem suman tsaye yayi aranshi yana Fadin"Kash kayi gaggawa Alhaji,inda kasan Abunda nake shiryama yarka dabaka Bani wadanan kyaututtukan ba..."Ammh Afili ko fadawa jikin Daddy yana matse hawayen karya yana mai godiya,Bayansa yake dafawa yana dariya haka Abbi ma yayi ta godiya,ammh sai da ya nuna dawainiyar tayi yawa gaskiya.

Nan suka isa ga motocin aka bude suka gani harda na Malikan,jinjina kai kawai Sadiq yake aransa yana ayyana Dalilin daya sanya Saleem auren Malika saboda kudi ne,Ai basu saki baki sai da suka shiga gidan,daki by daki suka dinga shiga suna ganin Uban Dukiyar da"a Narkama gidan,basu tsinke da al"amarin ba sai da sukaga lefen dayayima Malika boutique Guda ne,aka tara,shikanshi Dakin Saleem din ya basu tsoro,kai Ai nan da nan Sadiq ya yarda da zuciyarsa na dama kwadayi ne da Auren jari yakai saleem ga auran malika Kai,babu shakka ya tsinci dami a akala.

Bayan sungama gani suka sanya albarka nan Daddy yake sanar dasu basai Saleem yazo daukan Amarya ba,shida kanshi zai kawo malika har dakinta,kana bai hanashi bayan sungama cin amarcinsu ba ya dauki matarsa zuwa wajen dayake aiki ba,in kuma zai barta nan ne,duk yadda yagani.


Saleem yaji dadin haka dama kuma Shirinsa kenan,domin adaren yau yake son dukkan wani Shirinsa ya kammallah zuwa waye garin gobe sai Dai aji bom din ya fashe shikuma kafin lokaci yayi nisa da jaharsa,kilama harda Kasar gabadaya.

Daganan gidan hanyar Abuja suka dauka,shikuma Alhaji Abdulmalik da danginsa suka koma gida,ko acikin motar,daga sadiq har marwan Zence suke tare da mamakin uban Dukiyar da aka batar suke,shiko Saleem ko baki bai tsoma musu ba illah danne dannen waya dayake tayi,ammh bayan lokaci kuma ana turomai sako ta waya kuma ya na maida reply batare daya bari wani cikinsu ya ankare dashi, ba Gabadaya zuciyarsa ta kekeshi,ba kamar dazu data nemi ta karaya ba,Abbi na gaba shida tawaganshi da sauran motocin yan uwa da sukazo daga kumo,suma lbrin arzikin da Saleem yatako kawai suke kowa aranshi yanajin dama shine saleem.


____________________

Malika ko tun daren jiya data Shiga dakinta bata Fito ba har gari ya waye,akayi ta hada hadar biki da kuma zuwa daurin aure batasan wainar da,"ake toyowa ba,tana kwance tana barcin gajiya sallar asuba ma,sai wajen 10 tayi bayan tatashi daga barcinta na asara,wanka kawai tayi,dama already Breafast dinta su Dose sun gama jera mata komai,Falo ta Fito daga ita sai wata yaloluwar riga Red colour,wacce da Kadan ta Wuce gwiwanta ,Wayace ahannunta wanda Tun jiya bata bi ta kanta ba,sakonni ta tarar bila adadin tare da kuma da kiran mutane,duk yawancin kiran na abokan kasuwancin Abbanta ne,na kasashen ketare,Abunda ya dauremata kai Shine sakonninsu ,mai dauke da *HAPPY MARRIAGE LIFE MRS SALEEM KABIR KUMO*

Abun ya Dauremata kai sosai,har ta zauna bisa daya daga cikin kujerun Falon tana sake cigaba da karanta sakonnin,Abun yabata mamaki ammh sai bata daukeshi wani Abu ba,tana tunanin kila kuskure ne,bata ji jikinta ya saki ba,sai da ta shiga shafinta na Twitter taga hotunanta dana Saleem Rututu ana Dorawa ,Friend dinta suna ta mata Happy marriage life.

Jikinta ne ya soma rawa,tafara Zargin wani Banza ne ya nemi bata mata suna aduniya kawai dare daya ya hada hotonta da wani kazami kazamin ma,wai wani Dan sanda,wanda basu iya komai ba sai lalacewa da shaye shaye,wai kuma da sunan mijinta,Kutumar uba ne,lalle kowani Wulakantattace ne, ayau basai gobe ba take son saninshi,taji dalilinshi na bata mata suna,da kuma yimata karya Aduniya

Fuuu tatashi ta Fice daga dakin dauke da waya ahannunta Falon Alhaji Abdulmalik dake sama Ta nufa tana kwalamai kira bata damu da Dimbin jama"ar dake falon kasa suna kallonta ba.

_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *MALIKA MALIK* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *09069067488* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488



*Shakira*

*MALIKA MALIK...!*
_(Sai na rama..)_

*ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ📚*

*_Mallakar:Janafty_*😘


_Dedicated To my Uwar Room, *ZM CHUBADO* Na sadaukar da wannan bautifull Chappy,gareki Ina so ki sani na *YARDA DAKE* kuma nima nasan Tuni kin gama bani Dukan *YARDAN KI* Son so Fisabillah_ 😘


*9*

    "Tana Shiga Falon ta tarar da babu kowa ciki sai wasu baki goggoninta na malumfashi dasuke zaune bisa lumtsuma lumtsumar kujerun Falon suna hira...

Kallo Daya tayi musu ,bata kara ba bayan taja musu uban dogon tsaki ba wanda tacema kala ta tsallakesu zuwa bedromm din Daddynta tana kwalamai kira,anan ma wayan Fitowa tayi a hargitse daga Falon tayi Falon kasa bibbiyu take hada Steps saboda yadda Ranta yake amatukar bace,gana Abunda tagani  ga kuma na ganin wayanan zugan yan kauyen da suke zaune musu agida basu Tafi ba.

Tana saukowa Falon Tashiga kwalama Hajiya kira muryanta akaushe..."Hajiya...?Hajiya...? Take Fada tana takowa zuwa tsakiyar Falon Fuskarta babu Annuri tana bin mutanen dake zaune da wani wulakatattacen kallo....

Joda ce ta Fito daga dakin Hajiyar tana Fadin"Anty Malika lafiya,...? Kallonta tayi tana wani mele baki a sangarce tace"Bai shafeki ba,juz ina hajiya...? Ta bude baki tayi mgana sai ga Hajiya ta Fito daga wani bangare na gidan tana Fadin"Lafiya malika,ina wanan kiran fa..? Baya taja tana Fadin"Ina Daddy shi nake nema banganshi ba...?

Kada kai Hajiya tayi tana karema malikar kallo,da ita da rigar jikinta tace"Bayanan ya tafi daurin aure,ammh nasan yana bisa hanyar dawowa.."yamutsa Fuska Tayi kan tajuya tana kallon mutanen Falon tana fadin"Toh su kuma wadanan me suke jira basu tafi ba,sun zo sun share kafa kamar wadanda aka gayyata wani sha'ani plz nidai su tararra su Tafi ko ni na bar musu gidan...

Wata goggon Alhaji Abdulmalik dataji haushin mganarta kai tsaye tace mata",Mu tafi ?muje ina Amarsu ta ango? ai muda tafiya sai mun mika ki gid..."Kai Goggo Baraka don Allah kiyi Shuru..."

Hajiya ta katseta da hanzari jikinta na rawa,domin Alhaji Abdulmalik sai da ya gargadeta datayi taka tsan - tsan ko Malika ta Fito kada ta kuskura tabada damar da zata Fahimci Abunda ke Faruwa,shi zai sanar da ita da kanshi,to gashi goggo Baraka Tayi baram barama.

Malika dataji mganar bata maida kai ba,Saima mele baki datayi wanda ga duk alamu ya zamanto mata jiki,ta juya gabadaya duwawukanta na wani rawa ,da alama ma ko pant bata saka ba,ammh sai me Abun ne ya shiga mata yawo akunne _Mu tafi muje ina Amarsu ta ango? Ai muda tafiya sai mun mika ki gidan ki.._ Toh me hakan ke Nufi..? Tafada tana kara kallon hotunansu dake yawo A Twitter,da sauran sakonnin Jama"arta.
.

Hajiya binta harta Fara murna,sai kawai taga Malika ta juyo cikin mamaki tana kallon Goggo baraka kafin tace"Kikace me? sai naji kamar kin ambace ni da Amarsu....? Tafada tana kure ta da ido,Tuni Hajiya binta tayi saurin tarewa da cewa"Tafiyarki Malika bada ke take ba,kawai tana zencenta ne..."Tafada bakinta na hardewa saboda tsoro.

Malika bata samu zarafin mgana ba mazan yan Daurin aure suka fara Shigowa,wani kawun Alhaji Abdulmalik ne ya Shigo yana Fadin"Kai yau naga jama"a Bura ube,😂alqur"an harda wandanda banta tsammani ba,duk na gansu,yau gani ga Shugaban yan sanda na kasa gabadaya mukayi hannu dashi duk dalilin Auren Malika,kai babu Abunda zance sai Allah ya basu zaman lafiya kawai mallam".. yafada yana saba babban rigarsa bakinsa har kunni.

Turus kowa yayi domin Tundaga shigowarsa har mganarsa Kaf akunnan Malika,wacce Tunda taji zencensa lakkan jikinta ya saki tayimai kuri da ido tana binsa da kallon mamaki,shi da fari baima Lura da ita ba,sai da yaga anyi Shuru ana kallon  barayin datake kana ya kallah,ganinta tsaye yasa ya nufota yana Fadin"Wai ga yar cin Durin uwa"Wani irin banzan dabi"a ce haka kina amarya ammh babu wani kwalliya,sai Fito da wannan banzar Shigar,ke binta kuna me baku Shiryata,ayi amikata gidan mijinta Tunda An Daura aure kuma ai babu jira..."Yafada yana kallon Hajiya binta wacce ta jike da zufa,Shiko ko ajikinsa domin bashi da masaniyar Malika batasan Abunda ke Faruwa ba.

Kawai bai ankara

Please Login or Register in order to submit comment