Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kwanta ya tada kai dashi yana numfashi dai-dai dankani yagama kintsa kayansa ya dau kayan tsiren nan nasa sai ya juya ya tambayi mahaukacin yace bani kudin sai mahaukacin ya fashe da dariya yace mai tsire Kabani dariya sai dankani yayi dariya shima yasake cewa bani kudin sai mahaukacin yace mai tsire kana bani dariya.

Dankani dai yaga abin kamar wasa tun yana dariya har ransa yafara baci don baya son wasa da kudi shikuma al'adar wannan mahaukacin duk abinda yaci baya biya shikuma ba abin ka kai shi karaba bashida hankali dayake gaba da gabanta aljani ya taka wuta wannan mahaukacin ya hadu da gabansa dankani mai naci sai faman tambayar sa yake yi mutane suka zo suka same su suka tambaya yayi musu bayani sai sukayi ta dariya suka yi masa bayani saidai ya hakura mahaukaci ne kuma al'adarsa ce haka baya biya.

Da Dankani yaji wannan bayani sai ya kasa magana don bacin rai gashi kuma bai yadda da asara ba ko ta yaya tazo masa yana cikin tunani can sai ya hango wata bulalar danko ya sami mahaukacin nan yayi ta dukansa saida mahaukacin nan ya gudu yabar wani tsumma da wata jakar filo tayi Dauɗa ya kulle wani abu acikinta dayake dankani baya barin ta kwana saiya dau jakar matashin kan yana dubawa saiyaga kamar da wani kaya aciki don haka saiya dauka don ya rage asara yayi gaba ya duba saiyaga wata matacciyar mage ce aciki harta bushe yayi jifa da jakar filon yatafi yana sambatu.

Da aka kwana biyu dankani ya goge a fagen fawa sai ya koma saida kan dabbobi da wadannan sana'o'i dankani ya aiko aka saya masa gida a birnin Kano kusa da kofar fada.

Kwadayi mabudin wahala duk wannan sana'o'in da dankani yayi da kuma alherin daya samu saiyaga yayi masa kadan.

WANDA BAIJI BARI BA YAJI AJIKINSA.
Kowa ya debo da zafi bakinsa duk abinda dankani ya samu sai ya rinka hangen wani babban attajiri agarin sai dankani ya dinga bincike akan yadda ya sami kudinsa.

Dankani yagama bincikensa daga karshe ya yanke hujjar cewa wannan mutum KWAYA da HODAR IBLIS yake sayarwa shiyasa ya sami kudi haka don haka sai dankani yasamu wasu yan zamani yan gari wai a nemo masa wannan hoda wadannan yara sukaiyo yan kulle kullen su suka kawo masa irin farin maganin nan da kwayoyi barkatai na banza da wofi dankani ya kunduge kudinsa ya saya yayi wajen kwatano zai tsallaka kasa koston suka kama shi da suka bincika sai sai sukaga bawasu miyagun kwayoyi bane wanda shi yake nufi yaran da suka sayar masa cutar sa sukayi nan masu tsaro sukayi masa duka suka koroshi..SUDA-23

ƊAN ƘANI DILLALI.

Wanda baiji bari ba yaji hoho da dankani ya kubuta sai yayi wajejen SOKOTO saiya sake neman wadannan miyagun kwayoyi ya samu saiya yi wajen wani malami ai masa addu'a kada asirinsa ya tonu dayaje wajen wannan malamin yaga abubuwan ban mamaki amma sai ya danne kwadayinsa saida yadawo daga fataucin kwayarsa yayiwa malamin bayani zai tafi Makka ne da ita dankani yayi rashin sa'a wannan malamin bamai wasa bane sai malamin yayi masa nasiha yabar wannan mummunar niyya tasa.

Dankani da yaga malamin bashida niyyar taimaka masa ta wannan hanyar sai yayi masa sallama yafita dankani yakoma yagama kunbiya kunbiyarsa saida ya shirya tafiya yana zuwa aka kama shi a filin jirgin sama masu tsaro sukayi gaba dashi wasa wasa saida dankani ya doke kimanin shekara biyu a tsare acikin tashin hankali na kurkuku sannan yafita.

Dankani yagama wa'adinsa sai ya koma wajen malamin nan yayi masa bayanin karya yace ai tunda suka rabu yana kwance bashida lafiya shiyasa bai sake lekowa ba malamin ya tausayawa dankani saboda ganin yadda rayuwarsa ta gigita ya dada chanzawa duk ya yamutse.

Dama zuwan dankani yaga abubuwa masu girman gaske wajen malamin nan na karama kuma dama yanada labarin sa don haka yaje ya taimaka masa.
Malam Suna hira dasu dankani da ragowar manyan almajiransa sai wani daga cikin almajiransa yace da malam Allah ya gafarta malam nidai yau sai yadda Allah yayi damu da malam yaji haka sai yayi shiru daga can yace to Allah ya sauwake kuma Allah ya kara rufa mana asiri.

Da lokacin yin sallah yayi sai wannan Shehun malamin yace da jama'ar da suke wurin kowane ya daga karkashin buzun dayake kai yayi bismillah yasa hannunsa na dama ya Debi kudi.

Duk jama'ar da suke wurin sai suka buda suka dantsa da hannunsa na dama suka zuba a aljihun sukayi godiya suka tashi.

Shi ko dankani saiya matsa kusa da Shehun malamin ya gurfana da kansa kasa yace Allah ya gafarta malam inason ayi min izni na saka hannuwana biyu ni hannuna ƙarami ne sosai da malam yaji haka sai yayi murmushi yace ai ba komai ba yawa ake nema ba albarka ake nema sa hannu dayan kamar yadda yan uwanka sukayi dankani yasa hannu jikinsa na bari ya dantsa har wasu na zuba yabi ya tattare kayan sa ya zuba a aljihunsa.

Tunda dankani yaga wannan shaihun malamin yayi haka a gabansa saiya dage sai malamin nan yabashi wannan lakanin tun yana tambayar sa a boye har idonsa ya rufe ya rinka tambayarsa acikin jama'a har wasu in sun ji sai su rinka kwabarsa acikin irin almajiran malam akwai wani gardi da bashida gudun duniya kuma ba wani karatu yayi sosai ba duk irin yan surkullen gardawan nan ya iya dayaji dankani ya damu malam da a bashi fahamin kudi saiya ja dankani gefe guda yace zai bashi na RAUHANAI indai kudi yake so kuma in ba zaiji tsoro ba zai samu.

Koda dankani yaji wannan batu sai ya rude saboda farin ciki nan yayi ta matsawa gardin nan har saida yabashi wani lakanin da za'a kwana arba'in anayin sa kullum wannan aikin ana farawa daga bayan sallan isha'i zuwa assalatu kuma a tsaye duk wannan sharadin dankani yace yaji ya gani ya karɓa yafara kamar wasa saida yayi kwana talatin da tara ranar da dankani zai gama wannan rana azaune mutum zai karasa wuridin.

Wajen karfe uku na dare sanyin asuba yafara hurawa sai barci ya kwashe dankani can sai ya bude idonsa yana budewa saiyaga wani gabjejen rakumi ya koshi girman sa ya zarce girman giwa wannan rakumi ya naɗa wani rawani a kansa ya nade kansa ya fidda kunnuwansa kamar kunnen rawanin.
Dankani na farkawa sai ya kalli rakumin.
Rakumin ya kalle shi yace da dankani bawan Allah menene bukatar ka. Dankani ya kalli rakumin jikinsa na rawa yace ni bukatata kawai itace ka koma inda ka fito.

ƊANƘANI na fadin wannan kalma sai wannan rakumi ya bace shi ko dankani ya dunkule anan har barci ya kwashe shi saida rana ta bude sosai ya farka yaje yayiwa wannan mutumin daya bashi wuridin bayani koda yaji saiyace da dankani da nasan Zakayi wannan sakarcin da ban baka ba ai da kace ga abunda kake bukata da yanzu labari ya sha bambam don in duk garin nan kace ya cika maka da kudi haka za'ayi.

ƊANƘANI dayaji wannan rashin da yayi sai bakin ciki ya kama shi har hararwa yayi saboda bakin ciki hawaye na zuba sai wannan malamin yayi ta bashi hakuri yace bakomai akwai wani lakanin da bai kai wannan wuya ba zan baka kasake jarrabawa. da dankani yaji akwai wata damar sai yaji saukin bacin rai ya kalli malamin yace dashi shi kuma wannan yaya yake?

Malamin sai ya bawa dankani wani wuridin na kwana guda jal.

ƊANƘANI MAI KWASHE KWASHE

KU BIYO NI
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment