Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai sarki yafito duk waje ya sake rudewa mutane sukayi ta kai gaisuwa fada can sarki ya tura sarkin baki da sarkin sharifansa aje ataho da sarkin sharifai dankane yana ta jan carbi kamar gaske suna isa sukayi masa sallama ya amsa cikin farin ciki suka gaisa sannan sukayi masa bayani sarki na nemansu gaba daya akofar fada. Dankane yace ai sai muyi harama ya tashi cikin hanzari da gaggawa ya shirya suka nufi fada ana hango su dankane mata sai guda maza na tafi don za'a raba gardama tsakanin mutan gari.

Su dankane na isa suka kai gaisuwa wajen sarki ya amsa sannan sarki yace da dankane gashi yanzu Allah yakawo mu wannan rana ta farin ciki yaya alkawari ko kanada damar cikawa sai dankane yayi dariya yace da sarki ai mu bama magana biyu da sarkin sharifan wannan gari yaji haka saiyace ai sai mu karasa wajen da za'ayi wasan sarki ya yunkura duk jama'a suka mikee aka dunguma gindin wutar da aka hura inda aka hura wutar za'a iya daure dawakai dari masu fitina su zauna lafiya. Kuma yadda wutar take toroko ko mao girman gini da tsahonsa ta hadiye shi tsaf.

Suna zuwa wurin sai sarkin sharifan garin aka hau masa kirari sarkin sharifan yaji kirari da ake masa sai ya kunna kai cikin wutar yayi kamar rabin sa'a saiyafito daga cikin wutar daya kulle ko ganinsa ba'ayi yana fitowa sai waje ya rude da ihu da kuwwa mata sai guda ake shikuma dankane yayi dariya ya shafa kasumbarsa ya kwance rawaninsa ya jefa cikin wutar.
Sannan ya kalli jam'a hagu da damansa sai ya kunna kai cikin wutar da jama'a anyi tsit ana kallansa duk inda dankane yake bi ta cikin wutar sai wutar ta mutu dankane yaje har karshen wutar ya dawo kafin yafito ya nado rawaninsa aka yafito da shi waje babu abinda ya same shi ko hayaki bai bata masa kaya ba yana fitowa sai waje ya rude da kuwwa masu tafi nayi.

Yana karasowa in da sarkin yake da jama'arsa duk sai aka dare aka bashi waje ya tsaya kusa da sarkin sharifai da maigari ga kuma manyan gari agefensa tsaye. Daga can dankane ya kalli sarkin sharifan yace yanzu tunda garinku nazo zansa wuta ta kama mai gari kaikuma ka hanata ta tashi duk jama'a da sukaji wannan batu sai suka dare suka bar mai gari atsaye shi kadai. Maigari dayaji wannan al'amari za'ayi wasa da ransa saiyace da dankane jadda jikan rasulu ayi hakuri don Allah kada afara wannan abu mu munyi hakane daman don al'ada ce agarinmu in mun sami baki irin ku mu girmamaku sarkin sharifai dayaga hankalin sarkinsa ya tashi kuma baisan irin karamar da dankane yake da ita ba sai shima yayi ta bawa dankane hakuri daga can dankane yace ba komai yayi tsawa sai duk wutar nan da aka kwana ana hurawa ta mutu.
Duk jama'ar da suka taho sai....

DA SAURAN RIGIMA FA BAWAI INJI YARIMA BA

NAZO ZANYI CIGABAN WATA BAIWAR ALLAH MAI SUNA Muhmar Othman
TA KWACE LITTAFIN

SO DUK MAI SON CIGABAN SAIYA TUNTUBE TA CIKIN GAGGAWASUDA-07

DAN KANI DILLALI

Shima yayita baiwa dankane hakuri daga can dankane yace bakomai yayi tsawa sai duk wutar nan da aka kwana ana hurawa ta mutu duk jama'a sai aka taho anata gaisuwa ga dankane don asami tubarraki.

Bayan antashi daga wannan kasaitaccen biki sai sarki da dankane suka shiga gidan sarki tare sukayi kalaci sannan suka sake hutawa tare afada duk jama'ar kasar suka sake zuwa aka zauna anata mubaya'a da juna daga can sai dankane yace da maigari Yallabai ai gara nayi harama in koma gida gobe in Allah ya kaimu sai sarki yace haba jikan rasulu ai mu so muke kayi kamar wata uku anan sannan azumi yazo sai muyi bikin salla tare saika koma gida.

Sai dankane yace ai ba komai wani lokacin in ba wani abu muhimmi daya sha gabana sai in bullo na zauna sosai. Sarki yace ai babu komai wannan bullowar dakayi ma mun gode Allah ya saka da alheri maigari ya aika aka kirawo ma'aji aka bashi kudi da tufafi masu yawa jama'ar gari kuma sukayi tayi masa kyauta don neman tabarraki duk yan kudin da dankane ya samu aka dauka aka kai masa masauki yayi bankwana da sarki ya taho jama'a aka rako shi masauki don da asuba zai tafi da dare yayi duk jama'a kowa ya koma mahallinsa don abaiwa dankane dama ya huta shikuma dayaga sawu ya dauke saiya kwanta asuba na kawo kai saiya tashi ya yiwo waje sai ya tafi gidan babban sharifin nan da ya taimaka masa wato sharu abubakar yana isa ya tarar yana waje yana alwala yakarasa da sauri yayi sallama suka gaisa sai yayi masa godiya kuma ya debo kudi zai bashi sharu abubakar yacee a'a nagode ya barshi yayi guzuri tunda tafiya zaiyi sukayi sallama.

Bayan anyi sallama sai sharu abubakar yace na manta bari na dada baka shawara don Allah anan gaba kar arika wasa saboda gaba kar ashiga halaka.
Dankane yacee haba ai wannan ma kuskure ne amma baza'a sake ba nagode. Shima sukayi bankwana ya wuce

Daya isa masaukinsa sai yayi sallah yanata lamizi saiga sarkin sharifai nan yazo suka gaisa sukayita hira har zuwa wayewar gari sai dankane yayi shiri suka taka masa sai ya yiwo gida da wannan kayayyakin daya samo.

Da dankane yayo gida bayan kwana biyu saiya sami nutsuwa ya huta sosai saiya zama kullum sai asako babbar riga ana tafiya ana takama in kuma yamma tayi sai yafito waje ya shimfida karaga ya zauna yana shan lofe sukuma mutanan garinsu wasu dayawa akan idon su dankane yashiga wuta agarin daya samo kayayyaki kuwa ba taima masa komai ba sai duk gari aka rika batun dankane sudai sun san iyayensa da kakanninsa ba sharifai bane. Wanda basu ganewa idonsu ba cewa suke ai duk maganar ma karya ce in gaske ne ya shiga wutar agabansu suko yawancin makotansa dayan uwansa baya kyauta musu da mutum yayi magana saiya sa yan doka suci zarafinsa. Suma sai suka rika yi masa hamayya suna cewa watakila yashiga yin aiki da aljanu ne kawai su ba ruwansu da shi tunda ya bata ya kauce wa hanya.
Gari banza a farau faran banza yake karewa dankane yana cikin wannan hali akayi wasu baki yan damfara bakin tunn kafin suzo suka sami labarin dankane saboda haka da suka iso gari sukayi tambaya aka nuna musu gidan dankane sukaje sukayi sallama dashi jim kadan yafito da katon carbi ahannu yana muzurai suna gaisawa da wannan bakin sai suka zube akasa suka gaishe shi ya amsa ana muzurai ya nuna musu waje suka zauna.

GARIN BANZA A FARAU FARON BANZA YAKE KAREWA.
Bayan wadannan baki sun zaina sun huta sai sukace da dankane jadda jikan rasulu munzo muyi wasa ne amma aikin mu mukanyi rufa idone don babu gaskiya cikin lamarin mu shine muka zo mu gaishe ka kuma muna roko duk abinda mukayi muna fatab za'a kauda kai.
Abin nema ya samu matar falke ta haifi jaki ko da dankane yaji wannan bayanin mutanen saiyacee kai samari wane irin wasan kukace yan damfara ne kawaio kuyi abinda zakuyi amma ina so ku bani fan ashirin in kuma kun ki yanzu nasa wuta ta kama ku macutan wofi.
Da wadannan yan damfara sukaji wannan batu sai sukace tuba muke Wallahi bamuda wannan kudi da kake bukata kuma dudu du in munyi wannan wasa baifi mu sami fan biyu ba ballee muyi alkawarin zamu kawo ma wani abu. Amma yanzu tunda abin hakanee zamu koma sai mu dawo da shirin mu sosai. Dankane dayaji haka saiyace ku tashi ku tafi mutanen banza tun kafin raina ya baci ya tashi ya shiga su kuma suka tashi suka tafi jikinsu a sanyaye suka tafi suna tattaunawa akan cikas din da dankane yakawo musu.
Daga can wani daga cikinsu yace kai ni ban yarda wannan mutumin sharifi banee don ko ruwansa irin namu ne na yan damfara sai sauran sukayi dariya sukacee sharifi ne sosai don jama'a sun shaida saidai kace ko ya kauce hanya. Wanda yayi maganar saiyacee tunda ko ya kauce hanya muma sai miin latsa shi sauran sukace karfa mu jawowa kanmu sai wanda yabada shawarar yace haba ai tunda yake irin wadannan kalamai har yanaso mu hada kai dashi ai kunsan ya shagala kudai ku zuba ido ku gani sauran sukayi dariya sukace to ga filin nan ga mai doki mudai yan kallo ne wadannan bakin yan damfara suka nemi masauki suka sauka wanda ya dagee sai sunwa dankane wani abu ya shirya makircinsa yayi duk wani suddabaru da zaiya iya yan uwansa suka taimaka masa.
Shi kuma dankane yama manta da wata magana da sukayi da wadannan yan damfara tunda yaga babu wata mammora ajikinsu. Da yamma tayi yafito waje yana shan iska da yan birni sun kewaye shi wanda suke zuga shi yana ciwa mutanee mutunci yana zaune akan kujera sukuma suna kasa sun keqaye shi anata hira. Sai kawai sukaga wani katon kadangare mai girman gaske ya keto aguje ya nufo dankane gadan gadan yana zuwa sai kawai ya huda babban dan yantsansa ya....SUDA-08

DANKANE DILLALI

Sai kawai sukaga wani katon katangare mai girman gaske ya keto agujee ya nufo dankane gadan gadan yana zuwa sai kawai ya huda babban dan yatsansa ya shiga yayita tafiya bai tsaya ba saida yaje tsakiyar bayansa ya tsaya duk jama'ar dake wurin da sukaga haka sai suka watse aguje suka bar dankane yanata tsalle shi kadai duk ya zubar da rawaninsa da rigarsa har saida ya cire amma abanza don ga shatin kadangaren atsakiyar bayansa.

Dankane dayaga haka sai ya shiga cikin gidansa aguje yana ihu matarsa ta rike shi da kyar aka shawo kansa ya kasa magana sai daga can yayi bayani ya nunawa matarsa wannan kadangaran ta gani sannan taje ta nemo yan uwansa dayake ci musu mutunci sukazo kansa aka kama dankane sai gidan mahaukata akai masa alluran barci yayita fama babban likitan ya duba ga hoton kadangare abayan dankane amma likita daya duba sosai babu komai ajikinsa saidai hoton kadangaren aka rasa yadda za'a shawo kan matsalar labari kuwa ya kewayee birni da kauye ya zama ko ina ba inda labarin dankane baije ba jama'a sai tururuwa suke wajen zuwa kallonsa.

Ana cikin wannan hali sai yan damfarar nan da sukai wa danakne wannan bita da kullin sai suka canja kama suka zo wajensa dankane ya bude faggen karbar masu magani dan haka kowa yaketa zuwa karbar nasa rabon suma wadannan yan damfara da sukazo sai sukace sunada maganin wannan cuta zasu gwada in an yarda amma saidai abasu duk abinda dankane ya mallaka araba shi biyu abasu rabi.

Dankane dayaji za'a rabashi da wannan alakakai saiya yarda wadannan yan damfara ba tareda ankai ruwa rana ba sai sukacee duk wanda yake wurin yaja da baya duk jama'a suka ja da baya can daya daga cikin yan damfarar nan sai ya daga wani kara sama saiya juyar da karan kasa ahankali sai akaga kadangaran nan daya shiga jikin dankane yana motsi yana fitowa ahankali daga can da karan yagama kallon kasa sosai sai kadangaren ya biyo ta wajen kafar dankane yafito aguje jama'a suka dare aka bawa kadangaren waje yayi can da kadangaren ya tsaya sai akaga ya zama bawan kara mutane sukaje aguje don su shaida sukaje suka gani da idonsu suka kuma tabbar da bawan kara ne da dankane yaga haka sai ya tabbata damfararsa za'ayi saiya tada alkawarin dayayi na bada rabin dukiyarsa yace ba zai baiwa yan damfarar nan ba.

Duk jama'a kuma kowa sai fadin albarkacin bakinsa yake gameda abinda ya sami dankane.

Yan damfara kuwa da suka nemi abasu hakkinsu dankane yaki sai suka yanke shawarar su bar wurin da wuri kar a farke musu laya. Don haka sai suka tattare nasu inasu suka bar wurin sun fara tafiya kenan sai bawan karan nan ya sake zama kadangare ya yiwo kan dankane aguje baki bude.

Dankane na ganin haka saiya mike ya nufi wajen yandamfarar nan aguje jama'a na mamakin wannan al'amari wasu kuwa suka gudu don kada kadangare yayi musu yadda yayiwa dankane. Masu taurin rai kuwa suka tsaya suna dariya dankane dai ya mike aguje kadangare na binsa yana zuwa wajen yan damfarar nan sai ya rungume daya acikinsu kadangaran ya tsaya baki bude yana kallan dankane.

Shi kuma dankane yana haki yace don Allah ku rufa min asiri ku rabani da wannan masifa daya daga cikin yan damfarar yace ai masifa ka hadu da ita tunda ka saba mana alkawari dankane yace kuzo muje duk abinda na mallaka in baku. Nan dankane ya shawo kansu suka juyo duk dan kudinsa ya kwashe yabasu wadannan yan damfarar da suka karbe wannan kudi ahannun dankane sukayi tafiyarsu.

Wadannan shakiyan yan damfarar da sukaga sun sami yadda suke so kuma dama duk garin dankane suka tsorata don shi suke jin labarinsa sai suka fasa tafiya sukace tunda mun sami baraka mu tsaya muci abinci dukkan su suka yarda da shawarar da sukayi. Bayan sun yanke shawara sai sukaje suka sami wata babbar hanya da zata bulle kofar maigari sai suka zubar da wasu tarin karare duk mutumin dayaga wannan kara saiyaga kamar macizai duk gari ya dauka ai wasu macizan iska sun fito zasuyi barna da sarki yaji wannan labari saiya rasa abinda yake masa dadi saiyasa aka kirawo manyan malaman garin da yan majalisar sa akai shawara yada za'a rabu da wannan masifa don duk jama'a sun gama razana.

Sarki da yan majalisarsa sukace a samo masu maganin macizai don su kwashe wadannan tarin macizan da akai shela ana neman wanda zasuyi wannan aiki da yan damfarar nan sukaji shela sai suka rantayo aguje sukace zasuyi wannan aiki nan da nan aka shigar dasu wajen sarki.

Sarki yace a kaisu su gani idan zasu iya taimakawa su taimaka.
Bayan sun gama adawo dasu wadannan yan damfara da sukaji sun sami damar da zasuyi shakiyanci sai sukaje suka debo kararransu suka kawo gaban sarki suka zube duk jama'a suka ga macizai azahiri da sarki yaga haka yayi musu godiya yace da ma'aji aje a sallame su.

Acikin wannan fada ta sarki akwai wani masani mai asararu. Amma shi ba kasafai yake magana ba amma dayaga rainin hankalin wadannan mutane yayi yawa sai ransa ya baci yakasa magana yana kallansu kawai.

Yandamfarar nan da samun sake sai sukace da sarki Ai Allah ya kiyaye amma badon haka ba da yanzu duk garin an halaka don macizan bana garin bane sun fito ne daga garuruwa daban daban can wani daga cikin yan damfarar ya fito waje afadar sarki ga duk yan majalisar sarki na kallansa sai ya dauki damin macizan saiya daga daya sama yace KAI KWAURE MAZA KOMA SOKOTO.

Sai akaga maciji ya tafi sululu yayi inda aka nuna masa can kuma sai ya dauko wani yace kai DUNA maza tafi borno macijin yayi inda aka nuna masa saikuma ya daga wani yace kai DUMUJI maza tafi IBADAN haka dai duk macizan da sukazo dasu suka tarwatsa su.

Duk abin nan da ake wannan malamin yana kallo. Sai ya fusata ya Mike tsaye a fusace ya...........

MUCI GABA KO MU BARI HAKA ?SUDA-09

DANKANE DILLALI

Duk abin nan da ake wannan babban malamin mai lakani da ya zauna a fadar sarki dayaga rainin hankalin yaran yayi yawa saiya tashi duk da yan damfarar nan rufa ido suke suna yadda kara amma mutane na ganin kamar macizai ne da gaske sai ya daka musu tsawa yace kai yara karya kuke nan garin ya wuce kuyi mana wannan shegantaka sai ya kirawo duk sunayen macizan da suka fada duk sai macizan suka dawo yace da macizan ku kama su sai macizan sukayi kan yan damfarar nan.
Su yan damfarar sun san ba macizai suka kira ba sunsan kara ne kawai amma sai sukaga macizan gaske sunyo kansu sai suka rude da ihu suka matsa gaban sarki suna cewa ran sarki ya dade don Allah kai mana rai mun tuba da sarki yaji haka sai yasa wannan dan majalisa nasa ya kyale su sai wannan malami yace da macizan kowanne yatafi makwancinsa sai macizai suka tafi makwancin su.

Duk jama'a sunata mamakin wannan abin al'ajabi sai sarki ya tambayi wannan malami mai yasa yayi haka sai malamin yayiwa sarki bayani cewa wadannan mutanen yan damfara ne ba masu gaskiya bane sunzo ne suyi yaudara su tafi.

Da sarki yaji haka saiya tambayi wadannan mutane ko su waye su yan damfara suka bashi labarin yadda sukazo garin da yadda suka nemi izini wajen dankane dakuma abinda ya nema ahannunsu da kuma yadda sukayi ta wahalar da shi abanza da jama'a sukaji haka sai sukaita dariya sarki yasa aka kwace duk yan kayan da suka damfaro mutane awannan wuri yasa aka zuba a baitilmali.

Su kuma sarki yasa aka hore su duk gari da akaji labarin shakiyancin da sukayiwa dankane sai akayi ta dariya harda baya son fitowa waje saboda shegantakar da ake masa musamman in ya sami abokan wasan sa.

MAI RAI BAYA RASA MOTSI
Wannan hali da dankane ya shiga sai abin yayi masa yawa ga dan abinda ya tara sun kare gashi kuma bai zauna da mutane lafiya ba don haka sai abin duniya yayi masa zafi saiya sake yanke shawara yabar garin yasake nutsuwa duniya ko za'a sake dacewa.

Ɗanƙane ya yanke shawara azuciyarsa nan ya sake yin sallama da iyalansa. Mai rai baya rasa motsi da dankanee yagama yanke shawara saiyayi sallama da duk wani wanda yakamata yayi masa sallama saiya fito daga gidansa a kas baisan inda ma ya nufa ba kuma baisan wace wainar zai toya ba yataho yanata tunani har ya baro gari. Dayayi nisa da gari sosai saiyace aransa tunda wancan karon yamma yayi to bara yanzu ayi wajen gabas don haka sai dankane yasa kansa gabas yayita tafiya yana cikin tafiya saiyaga wasu tarin jama'a azaune amma abisa alamu su matafiya ne sai dankane ya matsa wurinsu yayi musu sallama suka amsa masa ya mikawa na kusa dashi hannu duk suka gaisa bayan sun gaisa ne ya sami wuri ya zauna suka bashi ruwa yasha kuma suka bashi abinci yaci sai ya kishingida sai barci ya debe shi don ya gaji can zuwa wani lokaci ya farka bayan ya rintsa yana farkawa saiyaga wadannan mutane da ya tarar suna kinkintsa kayansu zasu tafi saiyace dana kusa dashi tafiya zakuyi ne na kusa dashi yace ai tafiya zamuyi don muna so mu isa dandalin gabas gobe in Allah ya kaimu don zamuyi wasa mu daga arewa muke wannan wasan shekara hamsin baya ba'ayi irinsa ba don haka muke so muje da wuri.

Dankanee dayaji lamari ne na holewa saiyace to ai nima saina biku in ganewa idona irin wannan abu da za'ayi don wannan lamari idon mutum bai gani ba ansha dashi wanda suke hira da dankane yace ai tunda hakane gara ka shirya muyi gaba don tafiya cikin jama'a tafi dadi dankane yatashi ya dan wanke jikinsa suka dangana da wajen sai suka tarar wajen ya dinke babu masaka tsinke don wajene da ake al'adu daban daban akwai masu shadi akwai yan kokowa kuma ga makada ga kuma masu sauran wasanni nan na gargajiya daban daban wannan waje dai abu biyu ya hada akwai wasanni wasu wasane ya kaisu wasu kuma cinikayya ce ta kaisu. Kowa dai da abinda yake gabansa.

Ayarin dasu dankane suke ciki sai kowannen su ya zaga inda yafi dacewa dashi dankane kuwa na tare da wannan mutum daya bashi shawara su taho tare koda yake dankane baisan sunan sa ba amma yasan ba'agale ne dan haka yake ce masa DAN BA'AGALE in sunga wani waje ya rude da ihu saisu zaga aguje don suma kar abasu labari irin wannan biki dama al'adace ta mutanen wurin sau uku ake a shekara da bukukunan salla guda biyu sai kuma na takutaha to wannan lokaci ne na karamar salla dan haka duk wanda zaizo wurin da zimmar wasa saiya shirya kansa kuma shiri bana wasa ba don har duk wata al'ada sukanyi da kuma canfe canfensu.

Dankane da dan ba'agale suna cikin kewayawa ganguna na tashi sai suka zago inda ake kokawa suka tarar da wani dan tsamirmirin mutum kamar akife da kwando gashi babu jiki kuma babu tsawo gashi kuma kamar yaron daya tashi daga ciwon kyanda.
wannan bawan Allah gashi da karfin hali duk da irin kirarsa ya cire rigarsa daga shi sai wani wando ya daura kafa kamar mai wasan bori kuma gashi anata yi masa kirari ga kuma maroka da makada sunata fama kuma gashi atsaye kamar ahure shi yafadi an tara kudi masu yawa agabansa anata shela duk maiso yazo ya dauka wannan kudi da aka tara sun isa mutum akira shi mawadaci in har ya mallake su.

Ashe wannan dan tsigigin mutum ba haka kawai ya shigo fili ba hujjarsa mai karfi ce don yanada mugun asiri shiyasa duk jama'a suka kauda maitarsu daga kan wannan kudi dayake gabansa.

Shi ko dankane koda ya kyalla idonsa yaga irin tarin wannan kudi saiya kasa hadiye kwadayinsa saiyace da abokin tafiyarsa nifa zanje na dauki wancan kudin don inada bukatarsu.

Shikuma dan ba'agale ya zaci dankane shima ashirye yake amma duk da haka saida dan ba'agale yace da dankane wancan tsakon fa da kake gani...SUDA-10

DANKANE DILLALI

Shikuma dan ba'agale ya zaci dankane shima ashirye yake amma duk da haka saida dan ba'agalee yace da dankane wancan tsakon fa ba kanwar lasa bane. Dankane dai tunda yaga kudi duk ya rikice hankalinsa yatashi sai tsima yake zaije ya dauka daga can da abin ya ciwo shi sai yayi zanbarwa ya shigo fili aguje yayi wajen wannan tsigigin mutum yana zuwa yasa hannu zai dauki kudin sai wannan tsigigin mutum ya rigashi dauka su kuwa makada da sukaga haka sai suka zo suka kewaye dankane sunata faman yi masa kida ana zuga shi dan gashi da alamun karfi kuma gashi basu san shi ba dan haka sai suka zaci ko shima ya taki wani abune sai kallo ya koma kan dankane can zuciyarsa ta buga sai ya kaiwa wannan tsigin mutum cafka shiko dayaga haka sai ya yarda kudin. Yana zuwa saiya shafa kan dankane koda ya tabawa dankane kai sai dankane yaji babu abinda yake masa dadi aduniya yaji duk jikinsa yayi sanyi kuma bashida kuzari.

Shi ko wannan dan tsigigin mutum saiya zo ya kama wuyan dankane ya kuma cafi tsakiyar bayansa ya daga shi sama yayita hajijiya da shi asama duk wuri sai ihu akeyi shiko dankane yafita daga hayyacinsa. Don tun yana gane gabas da yamma har ya daina da dan tsigigin mutumin nan ya tabbatar dankane ya shiga wani hali babu wani sauran kokari da zai iyayi sai ya riko kafufuwansa ya sako shi kasa. Dankane yana zuwa kansa ya daki kasa yafadi ragwaf gaba daya da fara kokawar da gamata da irin faduwar da dankane yayi kamar mutum ne da sabuwar adda ya sare gwanda koda dankane ya fadi sai wannan dan tsigigin mutum ya hau bayansa ya tashi tsaye akansa mutane na yi masa kida jama'a ko sai kallo ake.

Sauran jama'a ko masu dan tausayi aransu sune suka debo ruwa sukayi ta zubawa dankane har ya fara farfadowa shiko abokin tafiyar dankane wato dan ba'agale duk da dai ahanya suka hadu da dankane harya zama kamar dan uwansa don haka dan ba'agale ransa yayi dubu ya baci sai yazo yana kokarin ya daga dankane can dankane yayi motsi ya yunkura ya mike sukayi ido hudu da dan ba'agalee shidai dankane arude yake saiya ya tambayi dan ba'agale shida wannan tsigigi wa aka kayar ne shine ya kayar ko shi aka kayar ne akawo masa kudin daya ci

Wannan tambaya ta dankane mai sa zuciya ta canza farar daya ga ban haushi ga ban dariya sai dan ba'agale yace da dankane tafi can sullutun wofi shawaraki kai da kake neman tafiya lahira kake wannan zance dan ba'agale kuma ya kalli dankane saiya fashe da dariya ganin yadda yayi muzu muzu kamar wanda ciwon kwalara ta kamashi lokaci guda ya canza kuma gashi garin juyashi da ake asama duk yan kudinsa sun zube.

Dan haka sai dan ba'agale yace da dankane bara naje na karbo maka naka kasan dankane ya tsaya shidai kansa sai juyawa yake baisan a inda yake ba shida kawai sai jin kida yake kuma ana iho ihoi shiko dan ba'agale dayaje ya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment