Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nemi abawa dankane hakkinsa tunda haka akeyi wanda yayi kaye ya debi kashi uku bisa hudu wanda aka kayar ya debi kashi daya bisa hudu dayaje wajensu wannan dan tsigigin araba abawa dankane nasa sai dan tsigigin mutumin da mutanen sa sukace basa haka saidai in dan ba'agale ya isa ya tube shima. yayita basu baki har yagaji sukaki sai ransa ya baci yace a dawo filin daga zai karbar masa kudin.

Dan haka afagen kokowa sai wasa ya dawo sabo dan ba'agale ya kwace rigarsa ya yar wata mata na tallan ruwa atulu yayi wuf ya dauke tulun ya shanye ruwan gaba dayansa yaga wani katon daro cike da funkaso ya dauko ya cinye ya sake waiwayawa yaga wata tsohuwa dauke da wani sanho cike da zogale shima ya dauka ya cinye duk abin nan da dan ba'agale yake ci acikin dan kankanin lokaci yakeyinsa don haka sai kallo yadawo wajensa kuma shi duk abinda yake ci ba'a cikinsa yake zubawa ba acikin wannan dan tsigigin mutumin yake zubawa don haka wannan dan tsigigin mutumin saiyaji cikinsa yayi masa kabe kabe kamar ta zai tafi lahira kafin wani lokaci saiya rasa a inda kansa yake. Shi ko dan ba'agale dayaga haka saiyaje ya cafe shi yayi sama dashi ya buga da kasa wannan dan tsigigin mutum duk wanda yake wannan waje ya zaci karshen rayuwar sa kenan don haka duk wanda yake wurin hankalinsa yayi duba ya tashi saboda tsorata da sukayi da dan ba'agale nan da nan aka kawo duk kudin aka bawa dan ba'agale.

Shikuma daya karba ya bawa dankane rabi yace subar wurin nan da nan suka bace suka shiga yamma dasu kai yi nisa sai dan ba'agale yayiwa dankane sallama suka rabu
Koda suka rabu sai dankane yaje rumfar mai saida goro ya makale yasayi abinci ya kwanta ya huta da taro yaci ya cinye sai kowa ya rinka nade kayansa yanayin gaba don haka sai dankane shima yayi yan saye sayen sa ya canja kaya yayi gaba.

HANYA MAI HADIN ZUMUNTAR DOLE.
Hanya mai hadin zumuntar dole koda dankane yayiwo gaba sai tafiya ta sake zame masa sabuwa don baisan inda zai nufa ba can dankane ya hanga saiya hango wasu mutane ayari guda ana tafe ana kida nan da nan yakara taku yakai garesu shima ya shiga yana zuwa saiyaga ashe masu wasa da kura da biri ne suma suka dau hanyar su ta zuwa babbar kasuwar GUJUNGU.

Dankane yashiga cikin wannan ayarin yayi kicin kicin kamar dama tare suke wadannan mutane kafin su karasa wannan babbar kasuwar ta gujungu saida sukayi kamar kwana biyar dayake akasa suke tafiya kuma duk inda suka tadda wani babban gari ahanya sai sun taba wasa sannan suyi gaba duk wannan tafiya da suke dankane yana cikinsu kuma duk irin alherin da suke samu dankane yana gani nan da nan sai wadannan mutane suka karya masa zuciya yaji yana da sha'awar wannan sana'a domin shi duk hanyar da zata kawo kudi da wuri yana santa.
Dan haka sai dankane ya saki jikinsa dasu sosai SAIDAI......SUDA-11

DANKANE DILLALI

Dan haka sai dankane yasaki jiki sosai awurin wadannan mutane sai suka saba sosai dama wannan ayari da dankane yabiyo sun kasu kashi biyu akwai masu wasa da wani namijin kure akwai kuma masu wasa da biri sai suka canza shawara aje aci kasuwar wudil tukun in yaso daga baya azarce Gujungu shikuma mai wasa da kura yace shi kam yagaji dan so yake yaje kasuwar gujungu idan ya taba wasa sai ya sayarwa da masu maganin gargajiya su yanka ta su rika bada lakanin ta idan ana nema shikuma ya koma gida ya huta ya rika tsakurar abinda ya tara.

Da masu wasa da birirrikan nan sukaji bayanin mai wasa da kura sai sukayi sallama dashi yayi hanyar gujungu sukuma sukayi wudil wadannan mutane sun kasawa dankane hankali sai ya rasa suwa zaibi yayi dawurwura daga can saiya yanke shawarar yabi mai wasa da kura don shi kadai ya dau hanyarsa don yana ganin in yabi shi zai samu wani abu nan da nan sai dankane yakara sauri yaje ya sami wannan gardi mai wasa da kura suka sake gaisawa yace masa ai gani nayi ka taho kai kadai shine na biyo ka don tafiya mutum biyu tafi dadi sai gardi yace da dankane amma nayi murna kuwa saidai ni tafiyata gajeriyace don so nake na sayar da kurar zan koma gida.

Dama dankane tun ahanya yaga yadda sukayi ta wasa kuma yaga yadda sukayita samun alheri da dankane yaji gardin yace zai saida kurar saiya tambaye shi yace dan uwa in ranka bazai baci ba don Allah kafin ka shiga wannan sana'a kayi wani shirine ? Da gardin yaji wannan tambaya saiyace wa dankane ai yawanci masu irin wannan sana'ar ba wani shiri muke dashi ba kafin mu shiga saidai in an shigeta ake kokarin yin shirin don ka ganni nan daga fara wannan sana'a zuwa yanzu ban taba daura guru ba da sunan maganin kura saidai mutum ya kiyaye da ba ta abinci kawai dan in tana jin yunwa komai na iya faruwa don inda tsautsayi sai tayi ta'adi.

Dankane dayaji duk wannan lamarin taurin kaine baya bukatar wani shiri saiyace da wannan gardi dan uwa naji kace sayar da ita zakayi dana baka dan wani abu mana nima naje na nemi abinci daga ita tunda ni nan yanzu banida wani tudun dafawa gardin nan dayaji bayanin dankane kuma yaji zai rabu da kurar acikin ruwan sanyi saiyace da dankane toh ai wannan mai sauki ne bani abunda ya samu.
Dankane yasa hannu ajihunsa ya debo kudi ko kirgawa baiyi ba ya bawa gardi shikuma ya karba yasa aljihunsa ya mikawa dankane igiyar kurar shikuma ya karba don ciniki ya fada.

Rigimar duniya da mai rai akanyi ta hakika ko ba komai dankane mutum ne mai taurin zuciya don bashida tsoro kuma duk abinda yasa kansa zaiyi don duk inda kure ya rika na wajen dankane ya wuce nan don daga nesa in mutum bai matso kusa ba sai yayi zaton saurayin jaki ne saidai in ya matso kusa aga namijin kure ne kai ko acikin kuraye ma kurar da dankane ya saya yakai kure.
Amma shi dankane duk girman kuran nan baya bashi tsoro sai Allah-Allah yake suje kasuwa yafara cin ribar abin. koda su dankane sukaje kasuwa sai gardin nan yayiwa dankane sallama suka rabu dankane kuwa saiya shiga kasuwa da kure ahannunsa duk wanda ya kalle shi saiya sake kallonsa saboda girman kuran shikuma dankane da yake yaga yadda gardin nan yake yiwa kuran tun farkon haduwarsu sai shima yafara zungurin kuren yafara gunji ga kuran da wani gunji mai ban tsoro nan da nan sai dankane ya fara bin rumfuna duk rumfar dayaje sai an masa kyauta saboda girman kuran.

Abu kamar wasa kafin kasuwa ta tashi saiga dankane ya sami ninkin kudin daya sayi kuran nan kamar sau goma daya huta yaje ya sami wani wuri ya daure kurar. Duk da kuran nan yayi sanadiyyar da dankane ya sami kudi sai ya kasa saya masa abinci sai kashi yaje ya samo masa irin kashin nan da za'a zubar ya kawo masa kuran nan ya dan ci wanda zai iya yabar wanda bazai iya ci ba dankane ya kwashe ya zubar.

Dankane yana cikin hutawa akasuwa saiga sarkin kasuwa yana zagawa yana zuwa inda dankane yake sai ya tsaya suka gaisa yaran sarkin kasuwa sukayiwa sarkin kasuwa bayani shine bakon mai kura sarkin kasuwa yace da dankane yabaka zo mun gaisa ba? Naji dadi da zuwanka don duk wanda zai kawo mana ziyara muna murna da zuwansa. Da dankane yaji an bashi fuska saiyacee da sarkin kasuwa ai dama yallabai zanzo wajen ka ko saboda masauki dan irin mu bakuntar mu tanada wuya sai sarkin kasuwa yace ai ba komai kazo muje anuna maka inda zaka sauka dankane yaja kurarsa aka nuna masa masaukinsa.

Yaje ya nemi waje mai kyau ya daure kurensa tunda kuran nan ya shiga hannun dankane yasan ya shigo mugun hannu kota wajen abinci don sau daya ake bashi abinci kuma bama ya isarsa kuma gashi dankane yayi yanka akan gaba yashigo gujungu da kafar dama don mutanen gari sai zuwa wajensa sukeyi suna karbar kashin kura don lakani wasu kuma yaro suke kawowa adora su wai maganin Danshi ne wasu kuma ruwan da kuran yasha ya rage dashi suke hada nasu lakanin kowa dai da irin abinda yake tafe dashi nan da nan acikin kwana bakwai kafin ranar kasuwa ta sake zagayowa dankane ya sami abinda zai fitar da zakka amma duk da irin alherin da yake samu kuran nan baisan anayi ba saidai hawa yake sha awajen yara har ma manyan don maganin danshi.
Ana gobe ranar kasuwa ta zagayo kuran nan saboda yinwa da wahala sai ya kwanta yayita murkususu yana neman mutuwa dankane hankalinsa yayi dubu ya tashi dan gari na wayewa yasan zai sami alheri a kasuwa don haka sai dankane yayi sauri yashiga gari yayi cinikin wani katon rago ya biya idonsa ya rufe shi yasa ya sayi irin wannan rago bai tsaya neman karami ba daya sawo ragon yayi sauri ya kawo shi gida yana zuwa ya yanka rago dama kuran yasha mugun dauri irin da ake masa yanaji yana gani za'a iya babbaka shi babu yadda zaiyi Ɗanƙane na zuwa saiya cire masa takunkumi ya jefa masa rago wannan kuran yana ganin tarin ragon nan sai yaja shi gabansa yayita ci kuran nan babu abunda ya bari ya cinye dankane yakawo masa ruwa yasha koda kuran nan yayi koto ya koshi ya kwanta sai barci ya debe shi bai farka ba saida gari ya waye.

GARI NA WAYEWA SAI...SUDA-12

DANKANE DILLALI

Gari na wayewa sai dankane yashiga gari ya siyo masa nama mai yawa yabashi kuran nan ya sake ci yabashi ruwa ya sake sha nan da nan sai karfi ya zowa kuran nan sai wata mika yake da rana tafito sai dankane ya kwanto kuran nan ya nufo kasuwa. Jam'a ko suka dafo masa baya tun daga yadda kuran nan yake takawa dankane yasan ya canza dan wani lokacin maimakon dankane yaja kuren sai ga kuren nan yake jansa. Amma haka ya lallabo shi suka taho kasuwa don yasan alherin da zai samu dankane ya iso kasuwa ya yini yana zungurin kuren nan yana gunji jama'a ko nata bashi kudi don haka shi dankane akan kansa ma baya tunawa da abinci balle kuran da yamma tayi sosai sai kuran nan ya sake neman abinci don dankane ya tara masa yunwa da gajiya dakuma kishirwa don kuran sai gumi yake kamar mutum.

Da kuran nan yaga babu sarki sai Allah kuma ya fuskanci dankanee manufarsa ta ya halaka shi ce da yunwa da azaba yayinda sukaje layin yan kolu dayake wajene da ya tara dattijai al'ada na tasiri awurin don haka sai ruwan kudi sukewa dankane sunje gaban wani dan koli kenan kuma anyi musu dammun fura fal koko dankane ya zunguri kuran nan yayi gunji dankane yayi wani doro da kuren nan yaga yabishi ya turmushe shi jama'a suna kallo suna dariya sun dauka wani salon wasan dankane ya canja can sai dankane yafara ihu
AKAWO TAIMAKO JAMA'A.

Dan kolin nan sai yayi zumbur ya tashi aguje garin gudu duk furar nan ya juyeta afuskar dankane jama'a kuma da suka farga sai suka fara gudu shikuma kure yanata yakushin dankane ba don takunkumi ba da tuni labari ya sha bamban don halaka shi zaiyi dankane dai na kasa yana yunkurin kufcewa garin ya kwace sai dankane ya cirewa kure takunkumi jama'a da sukaga babu takunkumi ajikin kuren nan sai gudu cikin dan kankanin lokaci kasuwa ta yamutsee.
Shidai kuran nan dayaji babu takunkumi abakinsa saiya daga dankane yabazama cikin kasuwa can daya hango kara sai kuran yayi wajen yana shiga kuren nan duk ya hargitsa wurin duk dabbar data ganshi ko tana daure saita tsinkee tayi wani waje in ma ahannun mai ita take saita kufce duk waje ya yamutse kamar tashin duniya jama'a kuwa sai tambayar mai kuren suke don su halaka shi don barnar dayayiwa mutane da asara daya jawo koda numfashin bazai iya biya biya. Don haka da dankane yaji duk jama'a na nemansa sai ya bi kuran aguje shikuma kuran yayi dawa da gudu da wani dan kankanin rago sabon haihuwa abakinsa shikuma dankane yanata binsa aguje koda sukayi nisa dankane ya canza hanya dama fakewa yayi dabin kuran ya gudu ba kamashi zaiyi ba. Kuran nan daya hanga saiya gano dankane saiya bishi.
Dankanee garin gudu saiya buge wani mutum akan jaki shi da jakin sun taho kasuwa. Cilakowa mai cinikin lalata koda dankanee yayi wannan badda bami sai yayi dawa da gudu ya bacewa mutane wannan rana dai mutane sunci bakar kasuwa don duk wanda ya halacci kasuwar asara yayi maimakon riba.

Dankane yana cikin tafiya a daji saiya tadda wani karamin gari ya tsaya ya huta yaci abinci yana zaune suna hira da mutanen saiyaji suna cewa zasu taho kasuwa wani daga cikinsu yace zaikai dokinsa ya sayar da dankane yaji kalamin wannan bawan Allah saiyace ko hutar dakai zanyi na saye dokin indai baifi karfina ba da mai doki yaji ya sami mai saye acikin ruwan sanyi saiyace da dankanee mai zai hana in sayar ma in rabonka ne.
Sai yaje ya jawo doki dankane yagani sukai ciniki aka sallamawa dankane ya biya a irin kudin daya samu albarkar kuran nan nasa.

SAMU YAFI IYAWA...
Bayan ciniki yafada tsakanin mai doki da dankane sai yayi.....SUDA-13

DANKANE DILLALI

SAMU YAFI IYAWA
Samu yafi iyawa bayan ciniki yafada tsakanin dankane da mai doki sai yayi harama ya dorawa doki sirdi ya hau yayi gaba yana tunanin wata lalatar da zaiyi kuma.

TSUMMA MAKUNSHIN CUTA
dankane yayi nisa yayi girman dabbobi dawa yana girma yana kara bata duk da lalatar da dankane yayi da kuma isharar da aka nuna masa akansa ta zahiri amma bai saduda ba. Yana cikin tafiya sai ya karaso wani babban gari mai suna MAGAGA.
Ya karya linzamin dokinsa ya shiga garin kafin ya karasa saiya tsaya ya sauka daga kan dokin sa ya karyi itatuwa kuma ya debi ganyayyaki ya kunshe abinsa. Shi kansa dankane baisan irin itatuwan daya diba ba amma koda ya shiga gari ya nemi abinci yaci ya koshi yabawa dokinsa shima ya koshi yayi masa ban ruwa saiya sake jefa masa sirdi.

Dankane saiyayi cikin garin Magaga ana zare idanu da wata katuwar bulala ahannunsa yana cewa kai mayu yau karyar ku ta kare duk inda kuke ku fito da kanku kafin na bayyana ku kuma idan masu wata lalura suzo ga magani. Yau Allah ya kawo sarkin mayu da kansa. Dankane yanata faman ihu agari bakinsa har kunfa yake. Jama'ar gari kuwa da sukaji kurarin dankane sun dauka da gaske yake su kayi ta fitowa siyan magani ko ta ina sai zuwa ake gashi kuma karfafa masa gwiwa sun ganshi akan ingarmar doki.

Hakika dankane baya ganin zare saiya tsinka ya wuni yana abu daya kuma kudin daya samu ko kuran nan bai tara masa masa ba. Amma da yamma tayi yaga ya samu karbuwa agarin har zagin mayu yake yana cika baki duk mayen da bai bayyana kansa ba zai kamo shi ya nunawa jama'a dankane yanata yin wannan kurarin saiya biyo ta wata hanya inda wata mata take soya kosai wannan mata kowa yasan maiyace agarin kuma kowa yana shakkar ta jama'ar gari dama sun gama tsorata da wannan mata kuma gashi dankane yanata cika baki yabiyo ta hanyar don haka jama'a suka biyo wajen aguje don suga yadda sarkin mayu dankane zai muzanta wannan mata.

Dama kuma jama'ar gari sun tsani wannan baiwar Allah musamman makotanta saboda duk mutuwar da akayi su dama basa cewa Allah sai suce ai wannan maiyar ce. Wannan maiya Allah ne kadai zai iya yi mata sakayya don ko aiki mutum yayi yaji yagaji saiyace wannan maiyar ta kamashi balle mutum yaji kansa na ciwo ko wani bangare na jikinsa koda dankane ya karaso wajen wannan maiya saiya tsaya yanata zage zage yana cika baki wannan baiwar Allah jama'a sun kewayeta suga yadda za'ayi dankane yana cikin wannan kurari saiyaji cikinsa ya kulle yayi wata kara jama'a sun zaci duk firgita wannan mata yake sai jama'a sukaga dankane yafado kasa sharaf kamar kayan wanki yana amai yana gydawa koda jama'a sukaga haka kowa sai kafarsa takai shi ko da dankane yayi sharaf sharaf acikin najasa koda mai gari ya sami labari saiya tura a dauko dankane baisan inda kansa yake ba mai gari ya tura aka baiwa wannan maiyya hakuri sannan dankane ya samu kansa. Duk mutunan gari suna al'ajabi yadda reshe ya juye da mujiya da yamma tayi wannan masifa ta fadawa dankane koda dare yayi dankane ya samu ya taba kalaci yayita bacci da gari ya waye dankane ya farka maigari ya sake sawa aka kai masa kalaci ya taba dankane yagama tsorata da wannan gari sai yayi kokari ya sallama da mai gari duk zalama da son abin duniya irin na dankane saiya manta da dokinsa don ta kansa yake baya ta dokin.

Rigar da dankane ya kwanta da ita yatashi ya kade abarsa ya shafa yaji babu komai sai hankalin dankane yatashi don bashida kudin da zaiyi guzuri don haka saiya sake dukawa awajen mai gari ya nemi ya taimaka masa da abinda zaiyi guzuri mai gari ya taimakawa da dankane yayi godiya zai wuce maigari ya tuna masa da maganar dokinsa da dankane ya tuna yanada kaddara sai yayi ajiyar zuciya saiya nemi maigari ya sai dokin mai gari dayaga dokin yanada kyau sai ya biyasa kudin da dankane yasamu isassun guzuri baya farin ciki sai Allah Allah yake yabar garin yai sallama yayi gaba.

JA DA BAYA GA RAGO
Dankanee ya sami kansa da kyar don haka yayi gaba tunani mai zai kama gashi yaga damfarar saida magani akwai ci amma yanaji yana gani zata kaishi ga halaka dankane yana cikin tafiya yana tunaninsa sai yaga wani mutumin kasar nijar yaga an tara masa korai yana dinkewa anata bashi kudi nan da nan sai dankane ya raba suka gaisa da wannan mutum dayaga ya rabe shi yakuma bashi fuska saiya tambayeshi sirrin sana'ar gyartai.
An dace wannan gyartan bashida mugunta nan yaja dankane ya nuna masa wannan sana'a ta gyartai. Abari ya huce shi yake kawo rabon bako dankane dayaga ya koyi sana'ar gyartai saiya shiga gari yana cewa GYARTAI GYARTAI GYARTAI
Duk inda yazaga wanda sukeda bukatar yayi musu aiki su bashi inyagama yayi gaba dankane yana cikin tafiya acikin wani lungu yana fadin gyartai gyartai wani yaro da babansa suna zaune sai dankane ya wuce koda yaro yaji ance gyartai saiya zaci wani abinci ne saiyace da babansa BABA ZAN CI GYARTAI. Koda dankane yaji yaro yace zaici gyartai saiya zura da gudu dan ya zaci yaron maye ne shikuwa harka ta mayu yagama tsinkewa da ita wannan gudu da dankane yayi sai ya sake yowa wajen KANO ya sauka wata unguwa wajen Dala da gwauron dutse dankane ya rasa tudun dafawa shikuma duk sana'ar da zata kawo kudi da wuri ita yake so koda gaskiya ko babu gaskiya acikin lamarinta.

Dankane yataba yin lebura asibiti lokacin dayake aiki a asibiti shi aikinsa tattare kayan marasa lafiya yakai wajen wanki amma jama'a har dakta ake ce masa yana bawa mutane magani yana kuma musu allura. Awannan lokaci ya samu kuudi har ya watsar da aikin yashiga duniya saboda zara irin tasa. Don haka da dankane yadawo kano saiya tuna da cewa..SUDA-14

DANKANE DILLALI

Dankane ya taba aikin lebura a asibiti lokacin dayake aiki asibitin shi aikinsa tattare kayan marasa lafiya yake wajen wanki amma jama'a har dakta suke ce masa yana bawa mutane magani yana kuma yi musu allura. Awannan lokaci ya samu kudi har ya watsad da aikin shiga duniya saboda zara irin tasa. Dan haka da dankane yadawo kano saiya tuna da cewa shi fa dokta ne saiya sayi allura da kwalaban magani shi kansa baisan amfaninsu ba yana yiwa mutane.

Wasu mutanan da batan basira suke duk wanda kansa na ciwo ko bayansa maimakon ya tafi asibiti sai a atura akirawo dakta dankane yayi masa allura. Shi kansa baisan amfanin alluran da suke wurinsa ba awannan lokacin irin mutanan da dankane ya nakasta bazasu kirgi ba wasu ya lalata musu hannu wasu kuma kafarsu ta shanye ko inna da ake zagi bata yi bannar da dankane da yayi ba.

Abin mamaki jama'a sun kasa ganewa masu tsautsayi sai zuwa sukeyi ya zuba musu lalura ana cikin wannan hali sai dankane yayiwa dani mutum allura ba daidai ba atake awurin mutumin ya mutu koda jama'a sukaga haka sai suka rike dankane masu duka nayi masu zagi nayi iyalan mamacin sukace abarshi kar a kashe shi saboda yansanda na nan suka iza kyeyarsa saboda irin rikon da akayi masa kafarsa ko kasa bata takawa sosai wani ya rike kugun wandonsa koda aka iza keyar dankane sai ofishin yansanda can yaje ya gama shan wahalarsa iyalan mamacin suka yafe masa daga baya.

Dankane daya samu kansa saiya yanke shawara aransa ya chanza sana'ar magani bata karbashi ba dankane kogin jakara ne idan an zubar da shi a birni a sha shi a kauye. dankane daya gama yanke shawara aransa saiyabar unguwar dayake sai yayi wajen FAGGE

Fagge matattara ce ta yan birni don haka masu sana'ar abinci suna samun alheri awurin.
Dankane saiya kafa tebur na saida shayi in ya fara daga magariba sai gari ya waye yana ta samun ciniki abu kamar wasa dai dankane ya kafu sana'ar tayi karfi yan birni suka daure masa gindi dankane yagama karbuwa awajen yan birni duk tsukin fagge babu inda ake shayi mai kyau kamar nasa awannan lokaci kuwa fagge itace kano don duk wani wanda yake ganinshi dan birni ne ko kuma yanaso yaci abinci mai kyau sai ya dangana da Fagge domin fagge wajene da abokai ke saduwa suyi zumunci musamman ma wanda suke ganin sun fahimci rayuwa ta zamani.

Jama'a kance duniya budurwar wawa dankane ba'a iya cin duniya da tsinke ba koda dankane yaga yadda yan birnin kano suka karbe shi sai kuma ya shiga shakiyanci ya zama wai shayin ma ba kowa da kowa ake sayarwa ba sai wanda ya goge yadace da zamanin da suke ciki. Ganin yadda kasuwa ta budewa dan dankane ido sai yan birno ko kuma shakiyai suka kewaye shi nan ne gurin hirar dayafi ko ina cika ana hira in mutum baya shan shayin dankane gani ake kamar kansa bai waye ba.

Samun wuri barawo da sallama dankane saiya zama ya kafa doka wai in mutum zai sha shayi awurinsah ba dama ya gutsiri burodi ya tsoma acikin kofin shayi wannan kauyanci ne don in mutum yayi haka daga wannan lokaci har abada dankane ya daina siyar masa da shayi. Dankane ba dama da aka kwana biyu yan birni sun yadda da wannan dokar ta dankane.
Ganin yan birni sun ji sun gani sai dankane lamarin nasa ya wuce gona da iri sai yazama duk mutumin dayazo shan shayi ya gutsuri burodi ya tsoma kafin yakai bakinsa saiyaji an kwashe shi da mari ana mari mutum saikaji yan birni sun rude da kuwwa gaba daya da shewa suce ya tsoma anata dariya wanda aka mara haka zai tashi ya kade riga babu abinda za'ayi don in mutum yace zaiyi rigima ganin yadda shakiyai suka kewaye dankane ba wani tasiri da mutum zai samu ba.

Dankane ya samu dama saidai baiyi amfanida ita ba wajen neman arziki saiya shiga wasa. Al'amari irin na birnin kano idan ana bawa mutum labari ga wanda baisan kanon ba saiyaji abin kamar al'amara don lokacin da dankane yake kan sharafinsa akwai inda abirnin kanon mutum zaije siyan danwake baza a bashi ba ko kuma asiyar masa ba saiyace abashi (Kodin) kokuma yace abashi magani sannan za'a siyar masa inda yayi siriri ta nan yafi tsinkewa da wuri dankane yanata fantamawa yadda yake so kuma yana shegantaka daban daban.

Amma kasuwa kamar shi kadai yake saida wani abu abirnin kano don da an dafa shayi zai kare tun safe yake fara dafawa har gari ya waye babu sassautawa. Wannan kasuwa da dankane yake samu sai wasu daga cikin yan birni suka bashi shawara ya sayi mota arikayi masa haya duk wata hanya da zata kawo kudi da wuri dankane ya santa indai zai iya to nan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment