Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da nan zaibita dayake an dace da kudi ahannun dankane saiya yarda da wannan shawara ya siwo kiya-kiya sannan duniya na kwance Fam Biyar ta isa tayiwa mutum aure batareda kowa yaji ba balle anemi gudunmawa.

Ba samun duniyar ba ga dan tsako inda zai tsugunna yaci nan ne aiki. Dankane da kudi ba dama duk da ya na samu amma ko yaya zai kashe su sai ya auna yaga lalle in su fita zasu dawo don haka dayaga yasai mota da kudi dayawa saiya gwammace yadora yaro akan harkar saida shayin shigo ya rika bin motarsa ya zama karan mota yazama shine mai tara kudi. Duk da dankane shine mai mota saiya zama sune irin fitsararrun yaron mota wanda aka fi sani da Kwandasta.

Lamarin dankane babu mutunci acikinsa shidai kudi kawai babu maganar tausayi in mutum dattijo ne kokuma dattijuwa baya daukarsu wai zasu bata masa lokaci kamar shi bazai tsufa ba. kuma ko yaya mutum ya rike kunshin kaya sai an tsawwala masa kudi mai yawa da idonsa zai raina fata kuma yayita kyarar masu shiga motar.

Kuma ya rika shigar da wasanni acikin sana'ar sa musamman in har ta hada da mata saiya nemi ya zake.SUDA-15

DANKANE DILLALI

Musamman in har ta hada da mata saiya neemi ya zake koda macen bata tanka masa ba.

Zanceen batsa da cin mutunci da rashin albarka wajeen dankane don haka kullum sai jafa'i ake masa anayi masa mugun baki dankane dai bai farga ba saida yaga yaran daya dora akan saida shayinsa zasu karya shi saiya rufe saida shayin.

Yana cikin sana'ar mota sai ta tsaya domin duk kudin da ake samu ba'a gyara ta sai idan yazama dole.
Don haka mota ta tsufa da wuri dankane dayaga mota tafara shiga rigima saiya saida ita ya koma kamasho in dillanci ya samu ya taba kuma da yake tsohon kwandasta ne saiya koma gwangwan yana saida tsofaffin kayan mota zuwa babur da keke shaho maganin dankwai.

Dankane ina yasai abu da arha saiyayi kokarin kwankwance shi da wuri ko danyan kaya ne za'a biyo baya shidai yagama masa aiki. Kuma ga shi duk yadda kuke da dankane bashinsa baya ciyuwa dole ka biya shi amma shi ko in ya karbi bashin mutum saidai ya hakura don lalatar da yakee jeka ka dawo zai tayiwa mutum har ya gaji kuma kullum baya rasa kudi a aljihunsa in mutum ya zo neeeman biyan bashi sai yai tai masa hanya hanya ya hanashi daya tafi sai dankane yayita dariya ya leka aljihunsa inyaga kudin aciki saiya sake sa hannunsa ya kyakyace ya taba kudin yace Nagode muku da bakwa magana. Kuyi zamanku bamai rabani daku da an jima zan kawo muku yan uwa sannan saiya sake kyakyacewa.

Dankane yana cikin kirikiran sa ya rakito wannan kaya ya siyar yakuma rakito wanda yake na halali dana haram ba ruwan shidai kudi kawai.
Dankane yana wannan sana'a ta gwangwan sai wani saurayi lalatattun gari yashiga asibiti wurin marasa lafiya saiya yaga wani mutum ya ajiyee sabon kekensa da wani kwali abayan keken wannan mutum saiya kafe keken yakoma inda yafito kafin wannan mutum ya fito daga dakin daya shiga saiyazo ya tarar an dauke masa keke.

Wannan mutum daya fito yaga babu kekensa saiya rasa wane irin bakin ciki zaiyi domin matarsa ce ta haihu dan ya mutu shine aka bashi jaririn yasa acikin kqali don ya koma gida ayiwa yaron sutura a binne shi to da yaron da keken ansace sai mutumin yasa hannu aka yayita kuka jama'a nabashi hakuri.

Shiko wannan saurayi lalatacce daya saci keken saiya kaiwa dankane ya siyar masa da arha shiko dankane bai bincika ba ko don arahan da keken yayi sai yayi sauri ya biya barawon kudinsa dama baya maganar takarda yasan baza'a samu ba saidai ya tambayi yarin inda keken yafito yaron yace masa daga asibiti.

Dankane yayi dariya kawai dankane dayaga wannan keken yanada kyau sosai saiya yanke shawara azuciyarsa yaje ya boye shi agida in an kwana biyu yafito dashi ya rika hawa abinsa koya siyasa da tsada dankane ya dauko keke yahau ya zaga ta baya damma kar yabi hanyar dayakee zaton za'a ganshi akama shi. Dankane yayi wajen sabon gari sai masu kaman lasisin keke suka kamashi don keken babu lasin wani dansanda garin karambani saiya bude kwalin dayake kariyar keken saiyaga jariri a mace shi ko dankane baima san meye aciki ba.
Koda dansanda yagani saiya dakawa dankane tsawa yace masa yafadi inda ya samo wannan mataccen jaririn shiko dankane baisan dashi ba ganin wannan jaririn sai dankane ya rude ya rasa inda zaisa kansa dansanda ya kwashe shi da mari sai dankane yace shi ba barawon jariri bane amma sato keken yayi a asibiti kuma yaga keken da wannan kwalin wannan amsa ita dankanee zai bayar kawai ya kare kansa daga tafiya lahira yadda mutane sukayi caaa akansa. Duk da dai bashine barawon daya dauko keken daga asibiti ba aka iza keyar dankane sai asibiti da jama'a koda mai keke ya hango kekensa saiya karaso da sauri wajen kekensa yayi bayani nasane kuma jaririn ma nasa ne yafadi yadda akayi har aka sace keken.

Sannan dankane yakubata daga satar mutum yakoma satar keke duk da haka aka iza shi zuwa ofishin yan sanda da suka bincika sosai sai aka gane dankane barawon zaune ne akai masa tara mai tsanani. Da dankane yakubuta saiyabar garin saboda surutun mutane jama'a da aka dame shi dashi koda dankane ya yanke shawara yayi gaba sai ya rasa wacce wainar zai toya duk abinda aka jarraba indai na ha'inci ne saikaga abin baiyi tasiri ba shikuma dankane zuciyarsa taki karkata kan gaskiya.

Dankane dai yataho yanata kulle kullen wacce zata fishshe shi dayake dankane yasan doki kadara ce kuma duk wanda ya mallake shi yana da martaba idan masu ganinsa musamman ma duk da ba'a sanshi ba don haka dankane ya ratsa wata kasuwa ya sayi doki da ragowar kudinsa.

Dankane ya sake siyan doki dan yasan rikonsa kadara ne yana cikin tafiya akan dokinsa saiyakai garin MAGAGA yana shiga ya tarar an idar da sallah limamin garin yafito daga masallaci dankane na ganin wannan mutum yasan ba mutumin banza bane ba saiya sauka yaje suka gaisa yayi masa bayani shi bakone yanason masauki ne. Liman yacee to ai sai mu tafi suna zuwa aka nuna masa inda zai sauka liman yasa aka tafi da dokinsa cikin garken shanunsa aka daure dokin shi ko dankane daya sami inda zai kwanta sai yayi bacci har yamma ddaya tashi yayi wanka ya huta aka kawo masa abinci yaci ya koshi saiya fito waje saiya tarar liman yana bada karatu sai shima ya zauna ya sami wani littafi ya bude yana dubawa har liman yagama da jama'a yatashi ya shiga gidan yayi alawala yatafi masallaci.
Bayan anyi sallar isha'i dama al'adace awajen liman yafita su gaggaisa da jama'a kuma suci abinci ayi hira har zuwa wani lokaci sannan kowa ya tafi makwancinsa don haka da lima yafito sai dankane shima ya fito sukayita hira a irin hirar da liman suke da dankane saiya fahimci lallai dankane ba jahili bane saidai akwai wargi cikin al'amarinsa
Amma KASHSUDA-17

DANKANE DILLALI

Kwatsam sai wazirin garin ya mutu sai sarki yayiwa dankane wazirin garin Magaga tunda dankane yasami wazirin magaga sai yayi kicin kicin a harkokin garin yakuma dace ya sami sarki ahannunsa dayake ya iya munafurci duk wata harka baza'ayi ba in dankane baiga dama ba dole duk maison kansa da arziki ko mai neman shima atafi dashi dole yabi dankane ko yana so ko baya so. Attajirin bafulatanin nan da dankane ya kwacewa mata saikuma ta tasamma karya shi saiya sa aka kwace masa bujiminsa ko wata saniya mai mai ajikinta shi ko ya sha dabge kuma ba dama bafulatanin nan yayi magana dan dankane sune da garin ahannunsu lokacin da akaiwa dankane waziri yan majalisar sarki da hakiman sa su arba'in ne harda sarki amma dankane ya kai saida duk yaga bayansu ya cire su sarki kadai ya rage duk wanda aka nada daga baya mutanen dankane ne.

Munafuki ne yahana mumuni sarki ya gama yarda da al'amarin dankane don haka yake saurara masa duk shakiyancin da dankane yake tafkawa liman yana dai ganinsa tun yanayi masa magana har yazama dankane yafi karfinsa don ya sami rana sai shanya yake yadda yaga dama akuma inda yaga dama munafunci dodo ne yakanci mai shi duk lalatar da dankane yake sarki ne yaba shi wannan damar don haka babu mai ja da shi dankane baya ganin zarau saiya tsinka ganin kamar ya karbu agari saikuma shakiyancin nasa ya koma kan sarki wai yana so ya cire shi ya nada kansa sarkin magaga daya fahimci inda dankanee yasa gaba sai ya dage da rokon Allah akan wannan masifa data taso masa shiko dankane yanata kulle kullensa rannan kwatsam sai dankane ya bada sanarwar ya cire sarkin magaga.

KOWA YA SAMI RANA.
Kowa ya sami rana sai yayi shanya abu kamar wasa dankane ya cire sarkin magaga ya kuma ciru kodayake hausawa sunce in anbi ta barawo sai abi ta mabi sahu sarkin magaga shi yake sake har dankane yayi masa sakiyar da babu ruwa don shi yabashi dama har yafi karfinsa.

Ran sarki ya dade dankane sarki ne mai karfin iko lokacin da dankane yake sarki sarautarsa dai dai yake da kowanne irin shugaban kasa na yanzu domin duk arzikin kasar da al'ummar kasar da ita kanta kasar ahannunsa take banda wannan karfin ikon da dankane yake dashi gashi kuma kasar sa yanada girman gaske domin al'ummar kasar sunfi miliyan dari.

Kuma an dace kasar dankane kasa ce mai albarkar noma ga kuma arziki wannan dama da dankane ya samu ya kece raini yayi yadda yake so wannan kasa ta dankane an daure wa jari hujja gindi fajirai sun mike kafa cin hanci da bada rashawa da karbarsa wannan an halatta shi akarkashin mulkin sarki dankane.

Sarki ko wani dodo sarki dankane yadda al'ummarsa take jin tsoronsa kuma suke bin dokokin sa da sunajin tsoron Ubangijinsu daya halicce su da kowa sufi ne ko wali agarin. Amma abanza duk biyayyar da talakawan kasar sukewa dankane amma sune suke shan wahala ga tsadar kayan masarufi da talakawan sukee fuskanta ga kuma rashin kwanciyar hankali da suke fama.
Abin takaici ga tsarin mulkin dankane shine ga talakawa nashan wuya amma dankane da yan koransa sai bushasha suke suna ta gine ginewa yayansu sannan kuma sunata gina gidajen holewa inda suke fajircin su ran sarki ya dade dankane in yai hawa da jama'arsa sai kace zai tada garin saboda kayan shiri dakuma tarin barade da suka kewaye shi suna tafe ana masa kirari in kuma dankane yana zaune afada duk wanda ya kwan yatashi saiyazo gaisuwa fada duk runtsi don gudun fushin sarki.

Sarki ran duniya dankane sarki ne mai jin nishadi da annashuwa don haka in ya zauna afada sai aita barkwanci in kuma lalatarsa ta motsa yaita daure mutane yana keta musu haddi babu yadda zasuyi dubu jiran mutum daya sarki dankane ya samu yadda yake so kuma ya rike albarkar garin da jama'a duk harka indai da wasa acikinta dankane yana bada muhimmanci don alokacin dankane al'ada tafi addini saboda yana shigar da son ransa.

Sarki dankane ya shirya mulkin kama karya yadda yaga dama kuma babu wanda ya isa yai magana sarki dankane yana wannan hali mutanen gari tura ta kai bango da abu yai tsamiri sai jama'a sukayi bore suka tasamma kashe dankane kafin masu boren nan suyi karfi sai dankane ya gudu gidan liman don shine kadai yake da ragowar mutunci a idon jama'ar garin dan shi baya shiga huldar dankane kuma abinda yasa dankane bai cire shi ba dan shine ubangidansa na farko.
Koda dankane yaje gidan liman yayi masa bayanin abinda ake ciki sai liman yayi ta masa fada don yasan dole ne ta auku. Liman da dankane suna cikin bayani sai kawai sukaji duk jama'a nata kuwwa akofar gidan liman wasu nacewa ai sai mun shiga wasu kuma nacewa a'a ai saboda girman liman adai bari yafito ko nan da can bazai daraba zan fille masa kai wasu kuma nacewa kada ai saurin fille masa kai sai an kaishi kasuwa kowa ya tofa masa yawu dankane dayaji wannan saiya rungume liman yana kuka sai liman yace ai abu ya riga ya lalace kuka bashine magani ba yanzu hikimar da za'ayi bara na tashi iyalaina in tura su gidan na'ibi saikai ma ka shigar mata kabisu da kaje saika kasa na'ibi ya daurama sirdi ka gudu kabar garin nan ayau in yaso daga baya in abu yayi daidai daga baya na tura anemo ka.

Dankane yayi shigar mata ya shiga cikin mata ya saje suka fice yana zuwa gidan na'ibi yayi sauri ya daura sirdi ya hau ya gudu liman kuwa daya tabbatar dankane ya samu kubuta saiyafito ya sami mutane makil wasu masu ragowar kunya suka gaishe shi wanda kunyar su ta bace suka dake duk halin da liman ya same su aciki saiya nemi yai musu nasiha sai suka ki yarda sai wasu daga cikinsu suka tambaye shi ina dankane yake sai yayi musu bayani ai tuni ya tsallake ya guduSUDA-16

DANKANE DILLALI

A irin hirar da liman sukee da dankanee saiya fahimci lallai dankane ba jahili bane saidai akwai wargi cikin al'amuransa.

Dama dankane tun yana karami yayi karatu daidai gwargwado kuma gashi zama ya hadashi da liman ya sake karuwa yin ilmi awannan marra ba ya cikin tsarin dankane amma dole tasa yanayi.
Zama da madaukin kanwa shike ka saka ka farin Kai.

Lokaci mai tsawo dankane suna tare da liman har azumi yazo dama liman shiyake tafsiri agarin da liman ya fuskanci dankane yasan baki sai yasashi yana ja masa baki tunda dankane yafara aiki har yagama babu wani kuskure.

Dankane dai suna tare da lima har zuwa wani lokaci da alkalin lardi ya mutu sarki yace yayiwa liman alkalanci shikuma liman dayaji haka saiyaje wajen sarki yayi gaisuwa yayi kuma godiya amma yace shi dai yanaso sarki ya dauke masa wannan nauyi danshi yanzu girma ya gama shi da sarki yaji maganar da liman yayi sai ya yarda da hanzarinsa yace bakomai an sauwake masa amma liman yabada wanda yake ganin ya dace.

RASHIN SANI YAFI DARE DUHU.
Rashin sani yafi dare duhu liman baisan lalatar dankane ba rana tsaka ya tsince shi kuma ance tsitacciyar mage bata mage. ganin yadda dankane yake binsa sau da kafa saiyace da sarki Allah ya taimaki ai ina ganin wannan bawan Allah da mukee tare dashi zai iya sarki yace to ai shikenan dama ai cancanta ake dubawa ba wani abu ba.

Abu kamar wasa sai akayiwa dankane Alkalin lardi da dankane ya kwana biyu akan karagar alkalin lardi sai ya murmure yakuma fahimci yadda abubuwa suke da in zaiyi abu saiyaje yayi shawara da liman daga baya saiya daina yasa mu wasu wazirai yan zamani suka kewaye shi. Alkalin lardi dankane mai tauna tsakuwa don aya taji tsoro koda dankane ya mikee kafa saiyaga duk hukuncin da yaga dama ya yanke ya yanku sai dankane ya rufe idonsa babu sani babu sabo kuma mutum ko yanada gaskiya in yakawo kara shima sai anci tararsa sannan kuma mai laiifi ai masa tsatstsauran hukunci.

Kuma dama hukuncin dankane tarace ta kudi in ka kasa biya ya kwacewa mutum kadara ko yana so ko baya so in kuma babu kudin ba kadara to mutum yasha dauri dankane duk irin hadarin da yake cikin kayan marayu shi ya take domin shi har murna yake in anzo rabon gado don biyu yake rabawa rabi na bitalmali rabi na magada kuma babu wata bitalmali don aljihunsa zai zuba.
Tara kuwa dama kowace irice rabi tasa ce.

Munafuki ne ya hana agane mummuni da tsakani ga Allah dankanee yake aikinsa daya samu ladan don duk wani shakiyi saida ya daina sakarci don ya dinke bakinsu kaf babu wani ja'iri mai sauran sakarci garin MAGAGA saida ya zama kamar babu jama'a kowa ya shiga taitayinsa saboda tsoron tara ko dauri.

Kowa ya samu rana sai yayi shanya wannan kujera ta dankane tabashi dama yayi abinda yake so in in shari'ar kisan aure ce indai matar ta kuruciyarsa to babu maganar daidaitawa ko sulhu komai kankantar maganar saiya mai da ita babba ya kashe auren yayi amfani da matsayinsa ya aure matar in an kwana biyu kuma in cuta ta samu ya saki mai tsautsayi ya sake shigar da wata.

Dankane yana cikin wannan hali wata shari'a tafado gabansa da wani bafilatani mai dukiya. Don garke guda ne dashi na shanu kuma wannan bafilatani yanada mata guda daya kuma duk yadda za'a kwatanta mace wajen kyau itama tana da daidai nata. Wannan bafilatani sai suka samu sabani da matarsa akan ya karomata kishiya ita kuma saitaki zama saboda tanada zafin kishi shine tsautsayi ya kawota gaban dankane don araba su da mijinta saboda tasan bazata wulakanta ba don tana budurwa wannan mijin nata mutum tara ya kasa don haka wannan mata ke son bujurewa mijinta don samin lafiya yaki sakinta.

Koda wannan magana tazo gaban dankane aka gabatar da ita yaga wannan mata mai kyau saiya kwallafa zuciyarsa akan matar nan da nan yatashi daga camba saiya nufi gida saiya aka kirawo masa Muhutin alkali koda muhutin alkali yazo sai dankanee ya tambaye shi labarin wannan mata don sune suka san matar garin. Da muhuti yaji wannan magana saiyace da alkalin lardi dankane Yallabai ai rigani kayi dama inata sauri naje gida na barwa iyali abin kalaci sannan in dawo in maka tsegumi sai dankane yayi dariya ya tafa kafa akasa yace ashe kaima ka na lura? Muhuti yayi dariya yace ai yallabai sawun giwa ne ya taka na rakumi ai yanzu abinda naga yafi duk da dai mijin nata mai sukuni ne amma tunda ba mai mulki bane ai talaka ne kada mage ba mai wuya bane kuma yanka ta ma bazaiyi wuya ba agurin mu don haka atura akira mijin yabata takarda.

Dankane tun agida sun yanke hukuncin da zasuyi gobe gari na wayewa dankane yasa matar tazo kuma alokacin ya aika sammaci akazo ta mijinta aka tilasta shi ya saketa dankane saiya shiga sahun zawarawanta duk mutumin da aka sami labarin yaje wajenta sai su dankane shi sa ai masa sharri da safe akamoshi a dauree irin mutanen da dankane ya daure a sanadiyyar wannan mata harda saurayin da tun wannan yarinya tana karama shima yana karami suke soyayya da yarinyar duk duniya babu wanda wannan mata take so kamar wannan saurayi dama auren da tayi iyayenta ne suka bada ita ga mai kudi kawai ba don tana sonsa ba ta zauna ne kawai don dai yarinyace mai biyayya ga iyayenta.
Wannan saurayi RABE dankane ya daure shine don don hankalin yarinyar yakoma kansa don haka da dankane yaga zai kawo masa cikas saiyasa aka daure shi ya manta dashi harsaida ya auri matar ta haihu sannan ya tuna da yaron yasa aka sake shi da yaran da aka sake shi tunda yabar garin dama maharbine saiya shiga daji kawai.

Shi ko dankane anata yin yadda ake so da makarrabansa kwatsam sai wazirin garin ya MUTUSUDA-18

DANKANE DILLALI

Wasu daga cikinsu suka tambayeshi ina dankanee yake sai yayi musu bayani ai tuni ya tsallake ya gudu sai wasu sukace basu yarda ba sai liman yabasu dama yacee su shiga su duba nan aka sami wasu tsageru suka shiga har cikin gidan suka duba sukaga dankane baya nan sai suka bazu ko zasu ganshi.

Shi dankane tunda ya samu ya kubuta saiyayi gaba duk inda ya sami garin dagaci saiya tsaya ya sami wani abu sannan yayi gaba dan su basu san abinda yafaru akan saba sun dai dauka shine sarkin su har wannan lokacin daga baya da labari ya bazu ako ina da ina aka sami labari kuma aka bada sammancin duk inda dankane yake akamo shi da dankani yaji wannan labari sai yayi kokari ya gudu daga yankin kasar dokin ma da yake hawa ya sayar dashi yakara guzuri tsakanin garin magaga da wani gari DANDA akwai wani dan karamin daji da mafarauta kan taba farauta acikinsa.
Wannan dan karamin daji hanya ce ta dankane yana cikin tafiya sai sukayi karo da yaran nan Rabe wanda dankane ya daure shi akan bafulatanar nan daya kashewa aure kuma ya aureta wannan saurayi na ganin dankane saiya biyo shi aguje ya sha gabansa dankane bai gane shi ba sai rabe ya dube fuskar dankane yaga hakika shine ba idonsa bane yayi zagi sai ya kwashe dankane da mari sai dankane yafadi agaban saurayi danshi ya zaci dan fashi ne.

Rabe yabi dankane har kasa ya haushi da duka yana cikin dukansa saiyaga wasu yara abookan rabe suka tambaye shi lafiya yake dukan wannan mutumin rabe yace ai ba mutum banee tunku ne ya rikida bayan ya harbe shi da wayannan samari sukaji sai sukace karka kashee shi zo muje garin DANDI akwai wanda yabamu cigiya yana son kansa zaiyi magani dashi koda dankane yaji ance ana son kansa za'ayi magani dashi sai cikinsa ya kada sai zawo duk da halin da dankane yashiga yana gudawa wannan samari basu kula ba saicewa suke ai dama ance tunku ba irin shakiyancin da bayayi idan ankama shi amma ance baya son yaji nan da nan wani daga cikinsu ya dauko yaji suka gabzawa dankane a ido yayi ta tsalle yayi ihu yafadi ya tashi.
Wadannan samari da suka kama dankane sukayi ta ja har suka isa garin dandi suna zuwa sai suka sami wani attajiri dayace anemo masa tunku suka kai dankane. Wannan alhajin ya dubi dankane da kyau yace anya tunku ne wannan ba mutum ba? Kuna ganin wannan mutum harda gemu da gashin baki ya tsaya sai rabe yace ai lokacin dana ganshi adaji su biyu ne mace da namiji da na harbi mace ta gudu shine na sami namijin yanzu in ba wahala yasha ba ko kuma ya mutu ba zai koma tunkunsa ba. Alhaji mai sayen tunku yace yanzu abinda nake so kar akashe shi kuma kar ace za'a bashi wuya kuma ya mutu agarin haka amma yanzu adauke shi akaishi gidan namun daji da ake kiwon dabbobi nan da wata daya in ma tukunnee zai koma tunkunsan wannan attajiri shida su rabe sukaje suka shaidawa mai gari.
Mai gari yace akaishi aka kai dankane gidan namun daji ga dakinsa gana wani gwaggon biri shi kadai don ya rinka sabo da kirarsa aka ware shi guri guda kuma daga gafe ga dakin wasu aladu daga bayan dakinsa kuma dakin wani tsohon kwadone bididdigi mai tsohon tarihi haka aka bar dankane daya waiwaya yaga wannan abubuwa sai ya fashe da kuka musamman in ya tuna shine mai cewa ayi ko abari in kuma yaga dama ya daure ko ya saki yanzu gashi agidan kiwon dabbobi.

Jama'ar gari kuwa wanima yafi shekara dari amma labarin tunku yakeji bai taba ganinsa ba don haka birni da kauye sai kallan tunku ake zuwa agidan dabbobi duk mutumin dayasan dankane yakuma san irin shakiyan daya aikata duk da haka mutun in yaga halin da dankane yake ciki zai tausaya masa saboda irin tururwar da jama'a sukeyi masa dakuma mugun kangin da yake ciki ga jama'a suna nema su wuce makadi da rawa ko ba komai surutu da kallo yana neman ya hana dankane cin abinci ga bacin rai duk yabi ya lalace ya kanjame wanda ya shekara kawai da sanin dankane idan ya ganshi bazai gane shi ba saboda ya gama canjawa.

Wahala da wulakancin jama'a idan sunje kallansa ma ya ishe shi don jama'ar har tsinke suke soka masa kokuma ajefe shi da hoge ko atofa masa yawu don wai jama'a sunce wai tunku baya son wulakanci da wahala da an matsa shi zai koma tunkunsa idan ma yakoma kamar mutum.
Wannan dali da dankane yashiga na wulakanci da wahala sai duk kamannin nasa yakoma kamar bama na mutum ba shidai gashi nan ba mutum ba kuma shi ba dabba ba kima shi ba aljani ba yadai zama jemage kawai. Da maigari yaga abin ya baci nema yake ya kazanta saiyasa aka dauko dankanee daga gidan zoo ya tura aka kirawo sarkin maharban garin baushe yai masa bayani ga halinda ake ciki da baushe yaji yadda lamarin yake saiyace to bara zaiyiwa dankane hayaki idan tunku ne ko gwanki ne to zanganee dan duk taurin kansa da kwarinsa zai koma surarsa ta da.

Maigari dayaji wannan magana saiyace da baushe to a jarraba agani mai

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment