Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gari ya ware wani daki aka saka dankani aciki baushe ya kulle shi ya dauko wasu garin magani ya zuba a wuta aka budee dakin da dankane yake ciki aka saka duk inda akasan iska zata fita sai aka tottoshe can zuwa wani lokaci sai hayaki ya ratsa dankani yayita ihu don hayaki yana nema yayi masa illa har dankane yagaji da ihu yayi shiru can baushe yasa aka bude dan yana zaton ya koma tunku ko gwanki da aka bude sai aka tarar dankane ya suma baushe yana kokarin ya hada wata wutar maigari ya hanashi don da da'ace akwai tsautsayi da tuni dankane ya mutu maigari yace ba'a kyale shi kada ayi gangancin akashe mutum babu hakkinsa baushe ya dage sai akyale shi ya karasa ladansa maigari ya sallami baushe yatafi dankane kuwa yana kwance rai ahannun AllahSUDA-19

DANKANE DILLALI

Baushe yatafi dankane kuwa yana kwance rai ahannin Allah yanata numfarfashi maigari yasa aka zuba masa ruwa ya bude idonsa jama'a sun kewaye shi maigari ya kori jama'a aka bar dankane nan dayaji sanyi ya ratsa shi na ruwan da aka zuba masa sai yayi ta barci har gari ya waye.

Gari na wayewa sai maigari yasa aka kawo masa abinci yaci ya koshi sai barci sannan yasake tashi maigari daya fuskanci duk zancen tunkun nan zancen banza ne sai hankalinsa ya tashi don tausaywa dankane saboda mawuyacin halin daya shiga.
Dankane yatashi maigari yasa aka tafasa masa ruwan zafi aka bashi yayi wanka ya dan dawo hayyacinsa yana zaune wuri guda yai zuru kamar wanda maye yakama yana jiran mutuwarsa mai gari dai tun da ya tabbata dankane mutum ne saima ya rika jin kunyarsa.
Su kuma yara da suka kamo dankane sai rabe ya dage shi daga baya ne ya rikide ya koma mutum don haka shi abashi kayansa yatafi dashi. Attajirin bafulatanin nan da dankane ya kwacewa mata kuma yaso ya karya shi ya durkusar dashi wannan bafilatani ashe aminin mai garine tun suna yara kuma wani lokacin yakan ziyarce shi. Lokacin dasu rabe da abokansa suka dage akan sai sun tafi da dankane mai gari yadage saiga wannan attajirin bafilatanin yayi sallama ya shiga sukayi ido hudu da su rabe dama kuma garinsu daya kuma abokan adawar juna ne saboda sun hada nema akan wannan yarinyar da dankane ya kwaceta ahannun wannan bafilatani koda wannan attajirin bafilatanin yashiga sai suka gaisa da mai gari kuma ya tsaya yana sauraren wadannan yara da kuma abinda suke cewa. Kuma mai gari na faman basu baki gakuma dankanee can kwance kamar an jika wanki don haka wannan attajirin bafilatani ko gane shi baiyi ba da dai yaji cacar bakin tayi yawa sai yayi kiran mai gari gefe guda yace abiya su don daukar alhakin yayi yawa maigari yaje ya sami yara yace nawa zasu fansar da tunkunsu sai sukace mudai dayake kaine yallabai zamu iya fansar dashi fam goma da mai gari yaji sai yayi dariya yace amma kun tsauwala kuna ganin abu rai ahannun Allah zakucee fam goma.
Da bafilatanin nan yaji saiya dauko fam goma ya mikawa mai gari shikuma ya karba ya mikawa su rabe suka karba sukayi godiya sukayi gaba. koda wadannan yara sukayi tafiyarsu sai mai gari yayi kiran dankane ya taso da kyar yazo wajensu da bafilatanin nan yagane dankane sai ya sake dubansa saiya gane shi don shi ya kwace masa mata lokacin da yana alkalanci kuma daya zama waziri ya tasamma karya shi har yayi sanadiyyar guduwarsa daga garin dama kuma duk halin da dankane yake ciki na korarsa da akayi daga kasarsu wannan bafilatani ya sani da wannan bafilatani ya sake kura masa ido sai yace da wannan bafilatani ya sake kura masa ido saiyace da dankane bawan Allah inayi maka kalloon sani kamar sarki dankane.

koda dankane yaji wannan tamvaya saiya dago kansa saiya gane wannan attajirin bafilatani sai ya sake sumewa saboda kunya da fargaba na dai suka sake shafa masa ruwa afuska ya farfado da attajirin bafilatanin nan yaga hankalin dankane yatashi daya ganshi saiyace da dankane bawan Allah tashi ka kuma kwantar da hankalinka mu ma su taimaka maka ne bada zimmar mu cuce ka ba ko wulakanta ka ba saidai nasiha da zamma wannan wata jarrabawace don haka akiyayi gaba kuma ai taka tsantsan da duniya.
Bafilatanin nan har ya gama yiwa dankane nasiha sai yayiwa maigari sallama ya sake yiwa dankane kuma yakare zamansa da maigari baigaya masa tsakaninsa da dankane ba kuma da irin sharrin da ya kulla masa shidai yayi shiru da bakinsa da yayi sallama zai tafi ya deebo kudi ya bawa dankane yace bawan Allah ga wannan ko abukaci wani abu.
Dankane kansa na duke yasa hannu ya karba yayi godiya maigari yace madalla da maigari yaga sun rage saura su biyu shida dankane saiyayi ta bawa dankane hakuri kuma yana lallashinsa don ya kwantar da hankalinsa ya saki jikinsa ya rike cin abinci don saboda bakin cikin abinda akayi masa ko abincin baya ci kuma saiya zauna yayi guri dashi kamar wanda mayee yakama.
Su kuma jama'ar gari duk labari ya kewaye gari dankane ba tunku bane kuma ba gwanki bane mutum ne kamar kowa don haka wasu sukanje kallansa don suna jin tausayinsa wasu kuma don su je suyi dariya don irin muzuntar dayayi tun muntane na rurumar abin har ma suka gaji suka daina bayan kwana biyu dankane ya sami kansa saiya samu ya rika fita kasuwa tun mutane in sun ganshi suna dariya harma suka daina abin ya zama jiki duk da halin da ya shiga amma zuciyarsa batayi sanyi ba ya komaga Allah ubangijinsa ba. Zuwan da dankane yake kasuwa saiya sama da wani dan daudu dattijan biri girma ya fara hawansa amma shima bai saduda ba shi wannan dan daudun anace masa HAJIYA BAKUWA. Sabon dankane da hajiya bakuwa saiya zama sun fahimci juna abu kamar wasa dankane saiya kwashe kayansa daga gidan maigari saiya koma gidan hajiya bakuwa dama kuma hajiya yanada yara da ya lalata su ya maida su yan daudu dakuma karuwai agidansa duk da wajen rashin mutuncine kuma bai rasa ci bai rasa sha ba agidan maigari amma sai dankane ya gwammace yakoma gidan hajiya bakuwa dan daudu saboda wajen yafi daudu sosai. Kuma shima yana da sha'awar irin shaidancin da akeyi awurin duk da girma yafara hawa kansa.

MAGEDUWA LALURA AKAFA.
Abu kamar wasa sai dankane yakoma wannan gida a unguwar da ake kira MAGANGARAR SHAIDANU mai gari daya sami labarin inda dankane yakoma yayi iya kokarinsa ya hana shi abin yaki yiwuwa daga karshe maigari ya kyale shi yace da mutanensa su rabu dashi dama asalinsa ba mutumin kirki bane shiyasa aka jarrabe shi da wannan bala'i amma don ya gane bai lura ba.
Shi ko dankane da aka kwana biyu sai yaSUDA-20

DANKANE DILLALI

Dama asalin sa ba mutumin kirki banee shiyasa Allah ya jarabce shi da wannan bala'i amma don yagane bai lura ba amma.

Shi ko dankane da aka kwana biyu ya sami sake ya sakankance ya sake sabon salo acikin dan lokaci kalilan sai yafi mai kora shafawa duk da hajiya bakuwa ne yajashi ajiki don ya rika debewa jama'a kewa suna dariya in sun ganshi sai dankane ya zama har ya danne hajiya bakuwa dayake dankane tsohon najadu ne sai ya zama ya ma daina saka riga saidai ya daura zani akugunsa maimakon rigar kuma duk garin idan an sami sabuwar yarinya data lalace dankane ne yake koya mata yadda zata shiga duniya kuma har tafiya da magana mai dadi wacce zataja hankali duk dankane ne yake koya mata agarin.
Wanda yayi nisa bayajin kira ana kwana biyu dankane saiya canza suna yakoma HAJIYA DELA ya cika bakinsa da hakorin maka na tasa duk da gidan da yake na hajiya bakuwa ne kuma shi hajiya bakuwa yafi shekara ashirin agarin duk jama'a sun san shi amma dankane bai shekara ba saiya danne hajiya bakuwa gidan ma dasuke ciki jama'a basa ganewa sai ance Gidan Hajiya Dela.
Wannan lamari na shakiyancin dankane yayi dumu dumu acikinsa ya zama shima ya rikide sai kace wanda ya shekara hamsin yana wannan lalata in dankane yana tafiya sai mutum yayi zaton wata yarinya ce yar shekara goma sha shida wace bata shiga daki ba.
Saboda raye raye da yake ahanya ana tafe ana kashe ido ga fuskarsa ta dau hoda yakuma shafa jan baki duk inda furfura ta fito masa ya shafe ta da shuni yana kuma tafiya ana jefa makulli sama ana cafewa ana gada mutan gari in an ganshi sai atsaya ai batsa ai shegantaka awuce in zance yayi masa dadi har guda yakeyi yayi shewa kuma ya wuce ana dariya. Hadiya dela yagama karbuwa agarin da safee yasa yara su toya waina da kaji asayar da rana ayi abincin sayarwa da naman rago da daddare nan ma haka ga farfesu nan iri iri na kaji dana danshila da kayan cikin rakumi dana shanu dana rago don haka wajensa yazama matattarar yan birni dakuma shaidanu wasu ba abincin suke zuwa ci ba shakiyanci ne yake kaisu. Wani lokaci wajen dankane hajiya dela ya cika sai wasu alhazan birni sukazo da wasu yara yan mata su uku awata babbar marsandi sabuwa suna zuwa sai alhazzan suka nemi wuri suka zauna su ko wadannan yara yan mata duk da hajiya dela uba ne abarikin suna zuwa sai suka zarvee wajensa wata daga cikin su ta kalli dankane tace dashi kafi zuru gamu mun iso dayar kuma ta dubi tsakiyar kansa tacee kai dan magyazo ban hankalinka nan dayar kuwa ta kalle shi tace kai tsohon najadu bara na gaya ma wani sirri ta kama kunnensa da karfi ta sunkuyo kansa zatayi masa rada saita masa aman giya akansa da fuskarsa.
Shiko hajiya bakuwa dayake dama kishi ya fara shiga tsakaninsa da dankanee yazo ya danne shi sai ya dauko wani ruwa da ake wanke hannu acikinsa kuma idan anyi kuskurar baki aciki ake zubawa sai hajiya bakuwa ta dau ruwan nan ta kuzawa dankane wai zai wanke masa wannan aman giyar da akayi masa aka.
Nan da nan waje ya rude da kuwwa da ihu anayiwa dankanee shegantaka saboda bacin rai yaji kamar ya hadiyi zuciya ya mutu don yaran da sukayi masa haka duk kansu basufi kamar jikokinsa ba kuma gashi cikin dubban jama'a
Saboda bakin ciki dankane yatashi zai shiga gida ya canza kaya idonsa a rufe baya gani sai yayi tuntube da wani katon daro na miya. Waje ya sake rudewa da kuwwa wasu daga cikin yaran dankane suka zo suka dauke shi suka tafi dashi gida suna zuwa wajen katuwar randa suka yarda shi akasa ragaf. Kamar mataccen jaki wani ya dauko wani babban koko ya kamfato ruwa zai zuba masa sai dankane yace dan Allah kada ka kashe ni sai ya yarda kokon yai ficewarsa.
Dankane ya lallaba ya tube kayansa ya debi ruwa ya shiga bandaki yayi wanka ya sake fitowa waje har ya zauna daya gaji da shegantakar da akeyi masa tayi yawa saiya koma ciki ya kwanta da dare ya tsala su hajiya bakuwa sun gama sayarda kayansu sai suka shigo suka sami dankane ba barci wata yarinyar karuwa tana zuwa ta ja gemun dankane tace kai gawa taki rami tashi ka tayamu lissafi dankane ya tashi yana tari maimakon ayi masa sannu wani na daga bayansa sai yayi masa dundu yacee fitar dankane ya fitar da wani dunkulen goro da yake tauna sai wannan goron ya zuba a takalmin wata yarinya tana ganin haka saita dauki takalmin ta shafe akuncin dankane suka sheke da dariya hajiya bakuwa tayi guda yace kai wannan yara zakuci gidan ku karku kashe min kanwata wa'adinta baiyi ba.
Mai rai baya rasa motsi da dankane yaji abinda hajiya bakuwa yace saiyace aini kowa yaci tuwo dani miya yasha wadannan kananan karuwan in naga dama sai na kashe musu kasuwa zaman garin yafi karfinsu kuma ni hajiya dela mai kwanciyar daukan rai lalatar danayiwa mata arayuwa harna mutu bazasu rama ba don kafin ma nayi aure saida na nemi yan mata dari ba daya kuma kowaccensu ban taba bata sisin kobo ba sai su danake tsiyatawa da dai na gaji da cikon ta darin ce na aura amma itama sadaki kawai na bayar dankane yana magana yana tari da suka hada ido da hajiya bakuwa saiyayi guda yace sai ni hajiya dela ta hajiya bakuwa mageduwa lalurar kafa bani jin magani sai dace hajiya bakuwa dayaji abinda dankane yace saiyace amma kawata kin iya tsiya saikace mai jan carbi suka tafa da hajiya bakuwa wadannan yara yan mata da sukaji bayanin dankane sai jikinsu yayi sanyi suka tabbata goggage ne sai suka rinkayin dari dari dashi. Da aka kwana biyu sai hajiya bakuwa yaga dankane ashe shakiyin duniya ne sosai maganar da yafada saida ya aikata yaran nan yan mata duk saida yasa bariki ta wulakantasu suka koma kamar almajirai.SUDA-21

DANKANE DILLALI

Yan matan nan duk saida yasa bariki ta wulakanta su suka koma kamar almajirai dankane da hajiya bakuwa suna hira sai hajiya bakuwa yace amma dela kin ban mamaki da kika so ki sakee yara su kwacee miki zani a kasuwa sai dankane yace ba sakaci bane lalata ce da iya shege basu san an fisu iyawa ba ko da yake ishara ce ake nuna min wannan abu da mukeyi ba mai kyau bane amma mun take mun ki gaskiya.

Bayan an kwana biyu sai dankane yayi wata rashin lafiya kamar ya mutu abokan watsewar tasa tun suna kula dashi har suka gaji suka watsar ba mai bashi abinci ko ruwa ballantana su kai masa magani yagama shan wuyar tasa ya mike yakai da kyar dayaga ya samu sauki saiya canja shawara aransa wannan rayuwar bazata fishshe shi ba babu sallama ya tattare inasa inasa zakara ya bashi sa'a ya yi gaba.

KARYA FURE TAKE BATA 'YA'A
Karya fure take bata ya'a koda dankane ya shura takalmansa sai yayi wajen kasar Katsina yana tafiya sai ya tadda wani babban gari funtua wadannan bayin Allah matunan kasar funtuwa mutane ne masu karrama bako da sanin yakamata koda dankne ya isa garin sai ya zarcee babban masallacin juma'ar garin yayi alwala yayi sallah ya koma gefe ya rike carbi kamar gaske koda yake ya sani ya take.

Dankanee yana cikin lazimi sai lokacin sallar la'asar yayi liman yazo akayi sallah dankane ya shige sahun gaba da aka idar suka gaggaisa da mutane jama'a suka fara fita daga masallaci sai yayi nazarin mutanen da suke wurin dayaga wani mutum abisa alamunsa duk inda yafito kasan mai sukuni ne wannan bawan Allah daya yunkura zaifita sai dankane yatashi yabishi suna fita suka gaisa dankane yayi yanka akan gaba ya dace wannan bawan Allah yana daga cikin manyan attajiran garin kuma mutum nee mai kyawawan halaye da suka gama gaisawa da dankane sai yayi masa bayani shi mutum ne daya fito daga wajen gabas amma yanada sani daidai nasa don haka yakan danyi tafiye tafiye duk inda ya samu sarari yakan yada zango in an kwana biyu yayi gaba.

Wannan attajirin dayaji haka sai yayi murna yacee ai ba komai zo muje abaka masauki ya wuce gaba dankane na binsa har gida kafin su karasa sai ga wasu karti akofar gidan zaune suka taho aguje suka kwashi gaisuwa sukayi sauri suka bude wata babbar taska da suke zama da mutane shi kuma dankane da wani yan kunshin kayansa ahannu wadannan karti suka karba aka shigar masa dasu cikin wannan taskar dankane yanaganin haka sai yayi ajiyar zuciya yaga al'amura zasu wakana.

KARA DA KIYASHI
Daukar mara sani dankane na zama awata kujera ta alfarma sai yaji yayi kasa saboda taushin ta sai farin ciki yasake kama shi da ya waiwaya gefensa sai yaga wani karamin tebur an daura wani karamin juzu'i an rubuta suratul Waki'a sai dankane ya dubi wannan attajiri yace alhaji wannan ayar da ansan lakaninta da rayiwa ta duniiya angama. Alhajin naji saiya fuskanci dankane yace algafarta malam ai abinda muke ta nema kenan sheekara da shekaru sai dankane yayi dariya yaga tarkonsa ya kama saiyace haba alhaji ba'a dai nema ba ai in an tashi neman abu sai aneme shi a inda za'a samu ba'a shiga har magaga ba amma yanzu tunda kanada bukata za a baka amma idan naga lakanin zai zame ma fitina saidai a taimaka ma da wasu abubuwan.
wannan attajiri dayaji haka sai yayi murna kuma yayita iya kokarinsa yaga ya kyautatawa dankane shikuma dankane karya yake bashida wani lakanin surar yadai san ta kawai.

Tun dankane yana kwana awannan babbar taska sai attajirin ya ware masa wani gida da ba'a gama aikinsa ba yakai shi can babu kowa daga shi sai mai masuyi masa hidima.

Yau da gobe sai mutane suka rika samun labarin danakne attajirai da mata sai suka rinka lekawa wajen don taimako ya zama ganin dankani ma yana neman ya zama aiki saboda jama'a abin nema ya samu dankane da wannan dama ta samu sai ya zama bashida aiki sai kawo rago ko kaza shi kuma kullum yana diban dabgee nan da nan ya canja ya murmure.

Dantsako sami ka ki dangi ba samun duniyar ba inda za'a tsugunna aci duk da daular da dankane ya samu yaransa masuyi masa hidima su basu san anayi ba sai wahalar kawai suke sha baya basu komai kuma shi dankane kuda ne bashi haram babu tausayi acikin lamarinsa da mai karfi da mara karfi duk baya sassauta musu.

Acikin irin mutanen da suke zuwa wurin dankane akwai wata mata da mijinta ya mutu take zuwa dan ataimaka mata akan ta samu wani mijin duk dan abin da ta samu a gado saida dankane yaga ya tatuke ta yazama babu komai awurinta sai rabon wani jariri nata da aka bar masa rago da tunkiya ragon dole matar nan babu yadda zatayi ta kawo ragon haka.
Koda ta kawowa dankane rago saiyaga ragon mai kyau ne bazai iya yanka ragon ba saiya bar shi yana kiwo ragon nan ya girma ya zama kato duk wanda yaga ragon sai ya tanka saboda kyaun ragon. Shikuma dankane yayi sabo da ragon ya zama ragon ko daure shi ba ayi saboda sabon da sukayi da dankane kullum yana kusa dashi akwance ajikinsa.

Rannan dankane yana zaune saiyaji motsin wasu mutane suna tafe koda ya leka sai yaga attajirin nan ne da ya sauke shi tare da wasu mutane manyan alhazai suka kashe mota suka shigo kafin su karaso wai dankane dan ace mai himma ne babu alwala kawai saiya tada sallar karya yanatayi. Attajirin nan ya shigo ya same shi yanata fama suka koma gefe suna jiran ya idar shikuma dankane dayaga haka daya idar sai ya sake mikewa ragon dankane yanata kiwo yana cin abinci sai yaga sunkuyawar da mikewar da dankane yake kamar tsokanarsa yake da wasa dankane bai kula ba sai ragon yaja da baya da baya dankane ya sunkuya yazo ya kara masa akai ragon ya sake ja da baya ya sake dukan dankane nan aka dauki dankane a sume jini ta hanci ta baki aka ruguntsuma asibiti duk jama'a sun bayar ya mutu daga baya akace bai mutu ba da likita ya duba shi.

BAYAN KWANA BIYU.......SUDA-22

ƊAN ƘANI DILLALI

Bayan dankani ya kwana biyu a asibiti sai aka sallame shi mutane na zuwa gaishe shi agarin akwai wani dan damfara dama yana jin haushin dankani ya danne shi duk jama'ar sa sun koma wajen dankani wannan dan damfara sai yazo wajen dankani don ya duba shi ya tarar dankani yana tsakar gida a kwance shi kuma dama wannan Ragon tunda ya daki dankani sai aka rinka daure shi anan tsakar gidan dan damfarar na shiga sai yayiwa dankani sallama Ya amsa saiya kalli Ragon saiyace da Ragon
MALAM AUTA MAI YA KAWO KA NAN??
Sai dankani ya kalli mutun Yakuma kalloli rago yaji Ragon yace GA WANDA YA DAURE NI ZAI HALAKA NI DON HAKA NAKE SON NA HALAKA SHI KAFIN YA HALAKA NI.
Da Dankani yaji haka sai hankalinsa ya tashi ya zaro idanunsa yana neman fita aguje dayaji abinda Ragonsa yace.

Shikuma wannan dan damfarar da yaga hankalin dankani ya tashi saiya tabbata ba wani cikakken malami bane irin su ne masu wasa kawai saiyace da dankani Allah gafarta malam wannan ai ba abin tada hankali bane amma amma me ya Kaika zama da aljani kuma ma bakin aljani irin wannan mai hadari dankani yace dan Allah bawan Allah inda yadda za'ayi ataimaka a rabani da wannan tashin hankalin.

Duk abinda ake wannan dan damfara tare suka shigo da wani amma wacce yayi rufa ido dankani baya ganinsa shine yaje ya tsaya kusa da Ragon yake magana amma shi dankani azatonsa Ragon ne yake magana wadannan yan damfara wanda ya fito fili ya sami dankani a razane duk abinda dankani ya mallaka saida ya karbe kuma yace aljanin yabashi kwana uku yabar garin.
Su kuma suka janye Ragon suka fice dashi.

Cikin dare yayi ta shiri gari na wayewa yaje yayiwa attijirin daya sauke shi sallama zai tafi attijiri baisan dalili ba yayi da dankani ya zauna dankani yagama tsorata yaki kuma gayawa kowa dalili da dai yaga attajirin zai hana shi tafiya saiyace ai mako guda zaiyi yadawo kawai.

Sannan attajirin ya hakura ya kyale dankani yatafi bayan dankani yatafi masu yi masa hidima da basu ga Ragon sa ba sai suka zaci sacewa akayi don haka da Sukaje kasuwa sai suka ganshi akara za'a sayar suka nemi masu saida Ragon kamar zasu saya sai yan damfara suka yunkuro don ayi ciniki dasu sai sukaga yaran dankani saika zaci ganewa yayi ya turo akama su basu tsaya wata maganar rago ba sai suka fita aguje sai suka bisu suka kama su suka kaisu gidan alkali yasa aka tsare su agidan sarka.

Wadannan yan damfarar sai sukace sunada magana aka kaisu wajen alkali sukayi masa bayanin yadda suka sami rago dakuma yadda suka razana dankani har yabar garin alkali yasa aka kirawo attajirin nan yayi masa bayani yayita dariya.
Da matar nan ta samu labarin yadda abu ya kasance saita zo tayiwa attajirin nan bayanin Ragon nan nata ne shikuma attajirin dayaji haka bayan yasa an yanka Ragon tuni anyi sadaka dashi sai duk ya mayar mata da dukiyar data yi asara kuma dayaji burinta aure take so saiya aure ta.

TA LEKO TA KOMA

Ta leko ta koma shidai dankani da yayi gaba sai yayi ta sauri don kar ya sake haduwa da wannan aljanin dayayi gaba sai ya yi wajen ZAZZAU dayaje garin Zazzau ya shiga gari ya nemi abinci yaci ya sake neman masauki ya samu ya kwana ana biyun sai ya sake tambayar yan garin wacce sana'a ce take ci ne agurin sai wani yace masa ai babu sana'ar da bata ci saidai a jarraba aga wacce ake da nasibi aciki.

Dankani ya tsaya yana tunani sai mutumin yace bawan Allah tunanin me kake kaida ka sauka agidan makera a jarraba mana da dankani yaji agidan makera ya sauka saiya koma ya sami maigidan yace masa yana son ya rika aiki dashi.

Maigidan yaji dadi suka fara fita da dankani har ya koya masa ya saba aciki wannan sana'a saida dankani ya sayi gida da wannan sana'ar ta ƙira.

Dankani mutum ne mai zari da ya kwana biyu yana kira saiya hango JIMA saiya ga fata na tafiya sai ya watsar da kira yakoma jima sai da yayi aure da amfanin dayake samu yana cikin jima sai hango SAKA saiyaga kamar tafi saiya koma sana'ar saka sai yakara sayen wani gidan kan dankani kamar kan mage yake duk inda ya Cusa kansa saiya shiga.

Dankani yana cikin yin saka ta karbe shi sai ya bari yakoma rini da sana'ar rini ya sake gina filin daya saya.

Lamarin dankani yazama kamar wasa sai ya koma fawa tunda yana saida kan akuya daya biyu har ya zama yadaina yanka akuya da tafiya tayi tafiya sai yazama har shanu yake siyarwa da ransu ko wayo yasan naki dankani yazama guguwa mai kwashe kwashe saboda san Banzar dankani har mahaukaci zai daki hancinsa wata rana dankani ya gasa tsire yana talla sai wani mahaukaci yayi kiran dankani ganin mutumin mahaukaci ne sai dankani yakara kudin tsiren mahaukaci yace ya sauke dankani ya sauke mahaukaci yarika dauka yana ci har saida ya koshi.

Shikuma dankani sai wata giggiwa yake don ya hadu da mara hankali zai cuce shi da yagama cinye tsiren yaji ya koshi sosai saiya jawo wani katon dutse

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment