Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hore masa ya kawo a daura aurensu, ita shi kawai take so ba kudinsa take so ba."
.
Ilham bata san lkcn da ta daga wayar mijin nata Ma'aruf ta makata da qasa ba ta tarwatse bayan ta gama karanta saqon, ta fara yi masa kuka wiwi tana cewa ya kasheta ta huta.
.
"Ba sai ka yi wahalar tsayawa jiran baqin ciki ya kashe maka ni ba, ka sa hannunka ka sa hannunka kaqareni in yi sauri in mutu tunda haka kake so. Duk alqawarin da ka yi mini a baya cewar zaka riqe ni amana ashe yaudarata ka ke yi Ma'aruf?
.
.
.
Lp=19%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 19
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
"ba sai ka yi wahalar tsayawa baqin ciki ya kashe maka ni ba' ka sa hannunka ka maqareni in yi sauri in mutu tunda haka kake so. Duk alqawarin da ka yi min a baya cewar zaka riqeni amana ashe yaudarata ka ke yi Ma'aruf? Duk murnar da nake yi a dalilin samunka da nayi ashe akwai ranar da zata zo ka gujeni ka koma wajen wata 'yar iska a can waje?"
.
Ilham ta rude... Ta riqa 6urari tana fadawa Ma'aruf duk irin kalmomin da suka zo bakinta. Ya yi iya qoqarin sa ya bata haquri amma ta qi fahimtar sa...ta qi yin shiru. Tana kuka tana fada masa magana
.
Ta fara hada kayanta a cikin akwati ta ce zata bar masa gidan sa, zata koma Katsina ya auri wacce yake so tunda ita ya gaji da ita. Ma'aruf ya yi wa Aliya matar manajansa waya, dama ita ce babbar qawar Ilham, ya fada mata abin da yake faruwa ya ce ta zo ta ba Ilham haquri ta ce zata tafi Katsina, daga kawai sun dan samu sa6ani.
.
Kafin Ilham ta gama shiri ne Aliya ta zo gidan ta sameta a falo tana kuka. Ma'aruf ya fita waje ya basu wuri. Bai san yadda aka yi ba har ya yi kuskuren baiwa wannan bazawara dama tana kiransa a waya, tana turo masa da saqo ba, gashi tazo suna zaune lfy ta girgiza masu aurensu na soyayya. Ma'aruf ya yi alqawarin ba zai sake yadda koda wasa ya saba da wata mace ba a waje, an yi na farko an yi na qarshe.
.
Da Ilham ta ga Aliya ta shigo gidan nasu ne, ta share hawayenta ta daina kukan' suka zauna a falo suka fara magana ta fahimta. Ilham ta ce da qawarta.
.
"ki bani shawara Aliya, ni kawai ina ganin rabuwa zan yi da Ma'aruf, ba zan iya jure abin da yake shirin yi mani ba." gara in bashi dama ya auri wacce yake so idan bani a gidan."
.
Aliya ta ce da ita
.
"shawara daya kawai yafi dacewa in baki Ilham."
.
"ina saurarenki Aliya, me ya kamata in yi?"
.
Aliya ta yi ajiyar xuciya ta ce da ita.
.
"ki yi sauri yau din nan ki je asibitin mahaukata a duba maki lafiyarki."
.
Abin ya basu dariya su duka biyun. Suka yi dariya. Ilham ta kaiwa Aliya duka a baya. Ta riqe hannunta.
.
Tun daga nan rigimar ta zo qarshe. Ilham ta dawo cikin hankalinta. Ta haqura ta yafewa Ma'aruf' don kuwa abin da Aliya ta fada mata gsky ne....! In ba hauka ba ta yaya zata yi tunanin rabuwa da Ma'aruf mijinta? Har ynx Ma'aruf yana nan da matsayinsa na jarumi a gare ta, wanda yake yaqi da matsalolin rayuwarta, wanda yake kafa harsashin gina duk wani abu da zai kawo mata ci gaba a rayuwarta.
.
Suka dawo suka shirya, suka ba juna haquri
.
Kowa ya ce shi yake da laifi.
.
"baki yi laifi ba Ilham kome ya faru ni na jawo."
.
Ilham ta ce ba haka bane.
.
"ni ce ban fahimceka ba Ma'aruf, ka yi haquri da maganganun da na fada maka, na yi kuskure ka gafarceni."
.
A tarihin zaman aurensu wannan shi ne sa6anin da suka ta6a samu sau daya kawai. Tun daga ranar da abin ya faru Ma'aruf ya fahimci a yadda suka ba juna amanar rayuwarsu shi da Ilham, ba zata iya jurewa ya karkata koda kashi daya a cikin kashi dari na soyayyar da yake yi mata ba xuwa ga wata macen, kamar yadda shima ba zai iya jurewa ba idan ta ce zata tafi ta barshi.
.
Da cikin Ilham ya isa haihuwa ne ta haifi 'yarsu ta farko Khairat. A daidai lkcn ne lkcn ne kuma suka tashi daga gidan da suke zaune wanda dama ba nasu ba ne, suka koma gidan da Ma'aruf ya gina. Ba a kammala gyare-gyaren ba a cikin gidan, haka nan suka koma sbd qosawar da Ma'aruf ya yi su shiga nasu gidan
.
Sa'ar da Khairat ta kai wata biyar ne da haihuwa aka yiwa Ma'aruf canjin wajen aiki, aka mayar dashi Katsina. Ma'aruf bai so wannan canjin da aka yi masa ba."
.
Ya saba da mutanen da yakee zaune tare da su a Malumfashi, ga sabon gidan sa da ya gina, inda suke zaune. A ranar da yazo da takardar gida ya nunawa matarsa Ilham, sai ta fara murna, domin kuwa ta san lkcn da zasu koma Katsina ne ya zo." Ma'aruf ya juyo ya kalleta tana dariya, ya ce da ita.
.
"dama kin daina wannan murnar, ba zamu tashi daga nan garin ba, na gwammace in riqa xuwa ina dawowa a qarshen kowanne mako."
.
Ilham ta tsaya da murnar da take yim ta hade fuskarta ta matso wajen Ma'aruf, don ta ji dalilin sa na qin amincewa su tashi su koma Katsina tunda an mayar dashi can da aiki. Wannan ne lkc na farko da damuwa ta fara kawo ziyara a zzamantakewar auren su."
.
Lkc ya riqa xuwa yana wucewa da gudu, wasa-wasa har suka yi shekara biyu...shekara uku. Bayan Ilham ta yaye Khairat ta samu wani cikin ta haifi Aiman dansu na biyu...shekara idan Ma'aruf ya koma Katsina 'ya'yanta sune abokan zamanta. Khairat tana da saurin girma da kuma wayo, da ta shiga cikin shekararta ta uku ne aka sa ta a makaranta. Ba nisa daga makarantarsu xuwa gida, tun Ilham tana kaita har Khairat ta fara xuwa ita kadai. Idan an taso daga makaranta ta dawo gida, sai Ilham ta zaunar da ita ta koya mata karatun addini.
.
Ma'aruf yana son 'ya'yanshi, idan ya dawo gida duk inda ya sa qafa a cikin garin Khairat tana nan biye dashi, wani lkcn ya kan dauki Aiman duk da qanqantarsa ya kai su shagon daukar hoto shi da Khairat a yi masu hotuna. Wani lkcn tare da shi ake yi msu.
.
A shekara daya kawai Ma'aruf ya cika falonsu da dakin Ilham da hotunan 'ya'yansa, wani lkcn ma sai an cire masa wasu hotunan a jikin bango ake sake kafe wasu sababbi. Idan daya daga cikin 'ya'yansu bashi da lfy, Ilham bata so tana fada masa. Sbd ko a ina yake idan ta fada masa zai yi sauri ya dawo gida a rude. Ma'aruf baya sake samun ssukuni sai yaga sun samu sauqi sun fara walwala.
.
Aiman ya ta6a yin zazza6i lkcn da ya kai wata biyar, Ma'aruf ya dawo a qarshen sati ya ga yadda aim ya rame. A ranar ko abinci bai iya ci ba, ya zauna ya yi tagumi ya dauko magungunan da Ilham ta zo dasu daga asibitin da ta kaishi, ya bude su ya riqa ba Aiman a baki yana rarrashinsa, don kada ya yi kuka.
.
Da dare ya yi sun kwanta su duka akan faffadar gadonsu. Da misalin qarfe biyu na dare da Ilham ta farka ta ga mijinta a zaune yana kallon dansa Aiman ya kasa yin barci ta ce da shi.
.
"kai dai ka cika son 'ya'ya. Don Allah ka yi haquri hakan ka kwanta ka yi barci."
.
Kafin Ilham ta gama abinci da rana, musamman idan a ranakun qarshen sati ne Ma'aruf wuni yake yi a gida suna wasa shi da 'yarsa wacce itama ba ta gajiya da guje-guje, in har abokin wasanta ya dawo gida. Akwai wani qaramin daki da babu komai a ciki sai kayan wasannin da yake sayo masu' Khairat ta kan debo su tazo dasu falo, idan sun karye Ma'aruf ya kan zauna da kanshi ta gyara mata.
.
Aiman zama kawai ya iya yi' sai dai a bashi qaramar mota mai danjoji, ya yi ta qoquwa da ita. Idan ya fara kuka sai Ilham ta shigo falon inda Ma'aruf yake tare da Khairat tana hawa bayansa shi kuma yana hanata suna kokuwa...suna dariya
.
Ilham ta kan dauki Aiman ta tafi dashi dakinta.
.
"Allah Sarki Bawan Allah, kana ta kuka ba ta kai suke yi ba."
.
Idan sallah ta zo Ma'aruf ya kan bata isassun kudin da zata sayi kayanta da kuma na 'ya'yansu. Ana dawowa daga masallacin Idi, baya tsayawa ko'ina zai zaqulo motarsa ya dawo wajen iyalinsa.
.
Kowa zai ci kwalliya da sababbin kayansa....abokansa suna kawo masa ziyara suna yiwa 'ya'yansa wasa. Ana yiwa juna barka da sallah! Bayan an gama gaisawa da abokan arziqi sai su shirya ya daukesu a mota su tafi Katsina da MAtazu su gaishe da iyaye da 'yan uwa. Komai dare basu kwana a can Malumfashi suke dawowa su kwana a gida, su zauna a cikin far ciki. Tun suna su biyu, gashi yau wani zamani yazo sun zama su hudu. Idan suna zaune a falo tare da 'ya'yansu hayaniya takan cika gidan. Aiman yana kuka ana bashi haquri. Khairat tana ta faman surutu, Ma'aruf yana bata amsar duk tsokanar da ta yi. Ilham ta kan yi dariya, idan ta tuno maganar da Ma'aruf yake fada mata a lkcn tana amarya, idan zai tafi wajen aiki. Zai barta a gida ita kadai.
.
"idan kika yi haquri Ilham, watarana zaki wayi gari ki ga xuri'armu cike fal a gida nan sun kewayeki."
.
Har Ilham ta kai shekaru hudu da yin aure sau biyu kawai mahaifiyar Ilham tazo gidan.
.
.
.
Lp=20
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment