Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Khalid."
.
Ya dago kai ya kalle ta...tun
.
"ya aka yi ne Ilham?"
.
Ta ce dashi
.
"Kaga ina jin kunyarka Khalid, na daukeka kamar yayana a layin nan, amma shi ne zaka je ka na fadawa mutane suna na da gidanmu suna biyoni suna takura mani tunda sassafe? Gsky ban ji dadi ba, don in banda kai ne har ga Allah sai an jimu. Idan mutum ya yi min haka. Gsky bana so Khalid kada ka qara yi min haka."
.
Khalid ya tsaya da gyaran wayar ya tattara hankalinsa waje guda ya ce da Ilham
.
"da farko zan fara da baki haquri Ilham, ki gafarceni don ban san haka abin zai kasance ba da ban fada masa ba. Kin san kin zo nan jiya kin sayi kati. To a sannan ne ya ganki. Baqo ne yazo (service) dakinsa na can gaban 'Yaryara. Shima dan nan jihar ne, a Matazu yake. Ya ci sa'a ne an turo shi nan Katsina, duka-duka yau kwanansa shida da xuwa. To kin san halin Baqo musamman in aka ce mutum yayi karatu, zaki ga yana qoqarin shiga mutane a san shi, ni kaina ban so na fadiwa Ma'aruf sunanki ba' to ya matsa mani ne, yana sonki sosai Ilham, tunda ya ganki jiya ya rude, amma ki bari idan yazo anjima zan fada masa ya bari, kin ce bakya so."
.
Ilham ta dan sauko daga fushin kadan. Ta ce da Khalid
.
"shi kenan ya wuce."
.
Ta koma gida tana tunanin...sai yaushe irin wadannan samarin masu nacin tsiya zasu barta ta huta da fushi? A ranar da yamma wani yaro ya shigo ya kawo mata wani faffadan katin saka muhimman saqonnin soyayya da gaisuwa wanda aka yiwa rubutu a samansa kamar haka:-)
.
Please forgive me.
.
Ma'aruf ne ya aiko mata da saqo yana roqonta tayi haquri. ta bude cikin katin ta ga qaramar takarda a nannade ta cirota ta warware. Ta ga ya rubuta mata qaramar wasiqa kamar haka.
.
Ilham
Ki yi haquri da abin da ya faru a tsakanina da ke. A wani lkc da dadewa na ta6a jin wani ya ce, duk wanda ciwon so ya kama baya iya ganin komai. Na dauka ba gsky bane, amma ynx na yarda da maganar a dalilin haduwata da ke. Ki yi haquri....
Na gode, daga masoyinki Ma'aruf.
.
Ilham ta kekketa wasiqar ta xubar da ita a waje. Ta kira wata yarinya wacce tazo gidansu 'yar wata yayarsu ta miqa mata katin ta ce da ita.
.
"gashi idan kina so basira ki yi wasa da shi."
.
Yarinya ta amsa tana murna ta fita waje dashi. Awa daya bayan haka har Basira ta fara wasan qasa da katin ita da yara a qofar gida.
.
Bayan kwana biyu Ma'aruf ya sake aiko mata da wani katin wanda yafi na farko kyau da ban sha'awa jikinsa an rubuta.
.
I hope I'm forgiven.
.
Wato yana fatan ta yi haquri ta yi masa afuwa bisa fushin da take yi dashi sbd kawai ya ce yana sonta. Sai dai a wannan karon bai sako wani saqo a rubuce ba." ya dai hado mata da wani zobe ne na azurfa wanda zai burge Ilham da ace tana son Ma'aruf
.
Ilham ta rasa me yake yi mata dadi. Ta cire zoben ta sake ba yara katin ta ce su yi wasa idan suna so. A ranar ta ba wani almajiri zoben kyauta. Wanda yake debo masu ruwa a gidan. Ta ce a xuciyarta.
.
"idan har bana son mutum to kayansa ma bana so."
.
Tun daga ranar, kusan Kodayaushe sai Ma'aruf ya aiko mata da kyaututtuka irin su kayan kwalliya, sarqoqi da turaruka masu tsada. Ilham bata ta6a yin amfani da ko daya ba a cikin su." a ranar da suka zo itama a ranar take kyautar dasu. Ta san idan ya gaji wata rana zai bari don kanshi, zai rabu da ita... Indai ba shi ne sarkin marasa xuciya ba."
.
Wata rana Ilham ta je sayen katin waya wajen Khalid maqwabcinsu, sai ya ce da ita.
.
"Ilham duk da dai baki son ayi maki zancen mutumin nan, yau dai ya cika mani fuska ya bar min saqo wai in kin zo in baki.
.
KHALID YA miqo mata wani abu a cikin leda. Ilham ta amsa ta duba ta ga wani hadadden takalmi ne a cikin kwalinsa dake kama da gilashi. Takalmin ya burgeta, sai dai kuma wanda ya aiko mata da takalmin ne bai ta6a burgeta ba, kuma tana zaton ba zai ta6a burgeta ba." ta ce a xuciyarta.
.
"lkc ya yi da ya kamata in dakatar da wannan shashashan."
.
"ka ce dashi na gode, kuma idan ya zo ka ce ina son ganin sa anjima da daddare a gidanmu. Ya zo da qarfe takwas."
.
Khalid YA amsa mata cikin murna.
.
"zan fada masa Ilham. zan je ynxn nan in fada masa. Na san tukuicina mai tsoka ne."
.
Ya yi dariya. Ilham ta tafi gida da takalmin a cikin baqar leda. Da xuwanta dakin ta ta jefar dashi ya hadu da bango.
.
Bata sake waiwayen inda yake ba."
.
Da qarfe takwas daidai na daren ranar ko minti daya Ma'aruf bai qara ba." ya zo gidan su Ilham. ya aiki yaro ya ce, ya shiga ya fada mata Ma'aruf yana kiranta.
.
Yaron ya fito ya ce dashi.
.
"ta ce tana xuwa."
.
Ma'aruf ya tsaya cike da farin ciki, ya qosa Ilham ta fito. Sbd tana sa ran haqarsa ta cimma ruwa. Ilham ta amshi soyayyarsa da hannu biyu. Yarinyar da yake so fiye da komai. Wacce yake kwana yake tashi da radadin begenta, tun ranar da ya fara ganinta.
.
Ilham ta fito dauke da takalmin da ya aiko mata dashi a hannu ba ma a cikin ledar da ya sako takalmin ba."
Ma'aruf ya fara yi mata fara'a, kafin yayi mata magana ne ta watso masa takalmin suka fada a jikinsa suka xube a qasa.......
.
.
.
Lp=8%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 8
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
TAre da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Kafin ya yi mata magana ne ta watso masa takalmin suka fada a jikinsa suka xube a qasa..akan qafafuwansa. Ma'aruf ya bude baki cikin razana yana kallon abin da tayi masa. Ilham ta nuna masa yatsa ta ce dashi cikin kakkausar murya.
.
"ina so wannan ya zama gargadi na qarshe a tsakanina da kai.... Kada ka sake aiko min da komai, bana buqata, kamar yadda bana son ka sake xuwa inda nake. Ina fatan zaka kiyaye, idan har kana so ka karewa kanka mutunci."
.
Ilham ta juya zata shiga gida kenan sai Ma'aruf ya kira sunanta.
.
Ilham dakata."
.
Kamar ba zata tsaya ba, sai kuma ta juya ta ce dashi.
.
"na tsaya' mene ne kuma?"
.
Ma'aruf ya dan sake matsawa inda take, da yake akwai haske a qofar gidan, Ilham ta ga yadda fuskarsa ta koma, akwai alamun qunci da nadama a ko'ina a fuskarsa. Duk da haka sai ya yi mata murmushi ya ce....'
.
"laifina ne duk abin da ya faru Ilham. Baki da laifi sbd na san ba a soyayya dole. To amma ba yadda zan iya yi, ni kaina na san abin da nayi bai cancanta ba, ba zan iya hana kaina sonki ba." ban san yadda zan yi in hana kaina sonki ba. Ba zan iya dakatar da xuciya ta ga barinn begenki ba."
.
Ya dan saurara sannan ya ce da ita.
.
"Amma tunda baki sona, nayi maki alqawarin daga yau ba zan sake xuwa inda kike ba, kuma ba zan sake aiko miki da komai ba." ina fatan zaki gafarceni a bisa 6ata miki ran da nayi na saki fushi, a yayin da kike zaune cikin kwanciyar hankali tare da iyayenki da 'yan uwanki. Ki yi haquri Ilham na shiga rayuwarki."
.
Ma'aruf ya sake mayar da numfashi kafin ya sake cewa.
.
"kafin muyi bankwanan qarshe, zan so ki ara min minti daya domin in fada miki dalilin da yasa har kika ga na nace akan sonki naqi yin fushi akan abin da kike yi min.
.
"Ilham a rayuwata ni maraya ne....! Na taso cikin rashin kula. Babu wanda yake sona. Iyayena sun rabu tun ina jariri dan wata uku, mahaiffiyata ta barni a wajen mahaifina a sakamakon zazzafar rabuwar da suka yi. Mahaifiyata ta tsaneni sbd irin wulaqancin da mahaifina ya yi mata. Haka shima mahaifina ya tsaneni a cikin 'ya'yansa, sbd tsanar da yayi wa mahaifiyata. Bai barni a gidansa ba, da na rayu ban mutu ba tun ina jariri, mahaifiyata ta barni a tsumma ta yi tafiyarta, sai ya kaini Matazu wajen mahaifiyarsa wato kakata. A hannunta na girma, cikin rashin kula da quncin rayuwa.
.
Ilham ta bi Ma'aruf da kallo tana saurarenshi, jikinta a sanyaye. Tarihin rayuwarsa da yake fada mata, kamar yana tuno mata da kwatankwacin nata Tarihin rayuwar ne. Itama da irin wannan azabar rashin kulawar ta taso a rayuwarta.
.
Ma'aruf ya ce da ita.
.
"mahaifiyata ta dade da rasuwa, ni kaina sai daga baya na samu labari. A lkcn ina a makarantar firamare, bana iya xuwa garin da take, ita kuma bata iya xuwa wajen kakata don ta ganni."
.
Ilham ta tuno yadda take damuwa idan mahaifiyarta ta dade bata zo ba." ta tuno irin maganganu da take fada mata.
.
"Mama me yasa baki son xuwa Katsina in ganki? Gashi kin qi nuna min 'yan uwanki, ban san kowa ba a danginki mama."
.
Ma'aruf ya ci gaba da cewa Ilham
.
"mahaifina yana da 'ya'ya da yawa. Amma ganin bai damu da ni ba." suma basu damu da ni ba. Basu kulawa da ni, suna daukata kamar wani bare ba dan gidansu ba."
.
"Baba Ilham ta yi qanqanta da xuwa makarantar kwana. A rabu da ita kawai a samu wata (Day) a nan kusa..."
.
Ma'aruf ya ci gaba da fada mata cewa.
.
"ina da qoqari a makaranta Ilham. Dana gama sakandire a MATAZU naso in je jami'a, amma aka hana mahaifina ya biya mini. Dole sai dai nayi ta fadi-tashi na samu kudin da na shiga (Federal polytechnic) dake a KADUNA. A can nayi (HND) na gama. Duk da haka sauran 'yan uwana dake tare da mahaifina a halin ynxn basu ta6a yi mani fatan alheri ba. Ban ta6a yin wani abu da na burgesu a duniya ba."
.
"me Ilham zata iya yi a jami'a baba..?"
.
Ma'aruf ya sake cewa.
.
Xuwa da nayi garin nan nazo bautar qasa ne....! Na hadu da mutanen arziqi wadanda suka nuna mani qauna. Kuma na gode. Ina son a nuna min qauna sbd ita ce abin da na dade ina nema ban samu ba." na taso cikin wata irin rayuwa mai wahala Ilham. Mutanen duniya kadai suke ganin mutuncina da darajata. Amma mahaifina da 'yan uwana basu yarda zan iya zama wani abu ba a duniya."
.
"gaskiyar magana Ilham ba zata iya yin saqa ba, ba sana'a ba ce ta masu son jiki irin ta..."
.
Ma'aruf ya sake cewa Ilham
.
"ganinki sa na n a karo na farko, sai naji haka kawai Allah Ya sa min sonki a xuciyata Ilham. Da ace na samu kulawa a rayuwata, na san ba zan yi ta binki ina roqonki ki soni ba." to amma kiyi haquri daga yau nayi miki alqawarin ba zan qara takurawa rayuwarki ba. Dama wannan shi ne dalilin da yasa kika ga na qwallafa raina a kanki, na san ynx ba zaki ga laifina ba, kuma zaki daina daukata a matsayin mahaukaci, na gode Ilham, ina yi maki fatan alheri a rayuwarki."
.
Ma'aruf ya juya zai tafi, ya duqa zai kwashe takalman da ta watso masa a jiki.
.
Ilham ta ji xuciyarta ta sosu sosai. Bata ta6a haduwa da namijin da ya yarda da ita ba, ya dauketa da muhimmanci har ya fada mata gskyr rayuwarsa babu yaudara irin Ma''
.
Ta ji ma' ya zama kamar dan uwanta a nan take. Sbd duk wani abu da ya fada mata a cikin Tarihin rayuwarsa irin qalubalen nata rayuwar ne....!
.
.
Lp=9%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 9.
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ta ji Ma'aruf ya zama kamar dan uwanta a nan take. Sbd duk wani abu da ya fada mata kwatankwacin abin da itama take fusksnta ne a rayuwar ta. Ba wani dalili dama da yasa Ilham take qin amsar soyayyar samarin da suke sintirin sonta ba, sai kawai don kawai don taga rayuwar ta cike take da damuwar rashin kulawar da ake nuna mata, tana jira ne har sai ta samu saurayin da zai fahimci rayuwarta ya riqe ta amana domin idan har ba ta samu miji na-gari ba wanda zai riqe ta amana ba, to tabbas rayuwarta da ta 'ya'yanta da zata haifa tana cikin garari.
.
Ilham ta ji Ma'aruf ya zama kamar dan uwanta, kamar wani babban amininta. Ta ji xuciyarta ta gamsu dashi sbd shi ma yana cikin irin rayuwar ta. Shi kadai ne namijin da ta fara haduwa dashi wanda ya dandani abin da ta dandana a rayuwarta. Shi kadai ne zai tausaya mata yayi mata adalci akan duk wata mu'amulla da zasu yi, sbd ya san irin matsalar da ta sani a rayuwarta.
.
Bayan Ma'aruf ya duqa ya dauke takalmin da ta watso masa ne kafin ya tafi sai ta ce dashi.
.
"Ina zaka tafi min da takalmina da naga ka duqa ka dauka Ma'aruf, ko ka fasa yi min kyautar ne?"
.
Ma'aruf ya dubeta cikin kaduwa da mamaki ya ce....'
.
"ke ce fa kika watso min su kika ce baki son kyautar da nayi miki. Nima kuma baki sona."
.
Ilham ta ce dashi cikin nadama.
.
"ka yi haquri Ma'aruf, na san nayi maka abubuwan da basu dace ba." amma ka gafarceni ynx komai ya wuce."
.
"kada ki damu Ilham, baki yi min laifin komai ba."
.
Ilham ta matso
Inda yake ta miqa hannuwanta ta ce dashi.
.
"ynx dai fara bani takalmana tukuna kada in mance dasu."
.
Suka yi dariya tare ita da Ma'aruf. ya miqa mata takalman ta amsa cikin ladabi.
.
"na gode da kyautar da kayi min, da kuma duk sauran kyaututtukan da kayi min a baya Ma'aruf. Allah Ya saka da alkhairi."
.
Ma'aruf ya kasa magana sbd farin ciki, abin yazo masa a ba-zata. Bai san yadda akayi Ilham ta canza ra'ayin ta ba a cikin lkc qanqani. Duk qiyayyar da ta nuna masa kwana da kwanaki, ynx ta rikide ta zama gagarumar soyayya. Ma'aruf ya tambayi Ilham cikin wasi-wasi.
.
"ynx kina nufin kenan kin dawo kin amshi soyayyata Ilham? kin amince da ni in zama masoyinki?"
.
Ilham ta kalleshi har cikin idanunsa ta ce
.
"wacce soyayya kuma zamu fara yi, ai har mun yi ta mun gama a cikin dan abin da ka fada mini na minti biyun da suka wuce. Ynx ina so gobe kazo mu je wajen Babana ya ganka. Tun yau zan fada masa na samu mijin da zan aura."
.
Ma'aruf ya rufe idanunsa ya sake budesu. Bai ta6a yarda ba mafarki yake yi ba, sai da ya bude idanunsa yaga Ilham a gabansa tana yi masa murmushin soyayya riqe da takalmin da ya bata a hannunta.
.
.
.
*** *** **
.
.
.
Babi na biyu.
.
Duk wanda zai ce ya ta6a ganin soyayya ta gaske....soyayya ta ban mamaki a duniya indai ya ta6a ganin soyayyar Ilham da Ma'aruf to labarin ta zai fara bayarwa.
.
Ba a dade ba duk wani mutum dake a layinsu Ilham ya san tayi wani saurayi wanda ake sa ran shine zai aureta. A wajen Ma'aruf Ilham bata tsaya kawai a masoyiyarsa ba." ya dauketa tamkar 'yar uwarsa ce ta jini, duk wani mutum da Ilham zata nunawa Ma'aruf ta ce dan uwanta ne, a wajen Ma'aruf shima dan uwansa ne. Bai ta6a mance sunayen mutanen da Ilham ta ta6a fada masa sunayen su ba a gidansu da 'yan uwanta na nesa da na kusa. Sbd ya daukesu da muhimmanci
.
Ma'aruf ya kan je gidansu Ilham ko tana nan ko bata nan. Idan tana nan yayi hira da ita, idan kuma bata nan sai ya zauna tare da yayyenta a qofar gida suyi hira, a nan zai wuni ya kai har dare, sbd ko'ina ya je in har baya kusa da Ilham baya jin dadi.
.
Ita kuwa Ilham sanin kowa ne cewar ko a cikin qawayenta idan har ana zancen samari da wahal ta tsoma bakinta tayi magana, amma tun haduwarta da Ma'aruf, tun sanda ta fara sonshi ta fara bada labarin shi a duk inda ta zauna. Qawayenta da ba unguwa daya suke da ita ba. Suka qosa su ga kowanene wannan Ma'aruf din, wanda Ilham ta dame su da zancensa, har sun fara gajiya da jin sa.
.
A wani bikin auren da wata qawarsu zata yi a 6atagarawa Ilham ta gayyaci Ma'aruf ta ce tana so yazo don ya gaisa da qawayenta. Ma'aruf ya yi mata alqawarin zai je. Yawancin qawayenta sun yi zaton Ma'aruf wani miloniya ne wanda yake hawa manyan motoci, sbd a yadda suka san Ilham bata kula kowa, ba qaramin mutum zai iya shiga xuciyarta haka duk ta rikice da soyayyarsa ba tayi ta zancensa a ko'ina
.
Sai da yamma da Ma'aruf ya je wajen bikin a qasa, yana sanye da kodadden shudin wando da takalmi (sandal) sai rigarsa mai dogon hannu. Da Ilham ta gabatar dashi a wajen qawayenta sai duk kunya ta kamasu.
.
Kowacce ta riqa mamakin me Ilham ta gani a wajen wannan saurayin. Me zai bata a rayuwa? Ta yaya ma zai iya riqeta? Don kuwa sun san mutane da yawa masu kudi sun dade suna son Ilham, bata amince masu ba." ta yaya kuma zata amshi soyayyar Ma'aruf wanda bashi da komai?
.
Ilham tana cike da farin cikin ganin Ma'aruf yazo wajen bikin. Bata damu da ganin samarin qawayenta da suka xo a manyan motoci ba." kuma bata ji kunyar gabatar masu da Ma'aruf ba tana murmushi.
.
"ga masoyina Ma'aruf da nake baku labarin sa, wanda nake so ki tayamu addu'a, Allah Ya cika mana burinmu mu zama mata da miji."
.
Qawayenta sukan kalli juna su rasa abin da zasu ce, sbd abin yana basu kunya.
.
.
.
Lp=10%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 10
.
Daga alqalamin
Shafi'u dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska).
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Qawayenta sukan kalli juna. Su rasa abin da zasu ce sbd kunya. Bayan Ma'aruf ya tayasu farin ciki da zai tafi sai Ilham ta rakashi har bakin titti inda zai hau mota ya koma gida kafin Ilham ta dawo gida idan sun gama bikin da daddare
.
Bayan Ilham ta dawo wajen qawayenta ne cike da farin cikin xuwansu masoyinta Ma'aruf' ta same su sunyi tsam' a tsaitsaye suna mamaki ta ce dasu
.
"bari ku ji wani abin dariya da ya faru tsakanina da Ma'aruf ynx nan da muka tafi na rakashi. na tambayeshi ne ya ya yaga bikin nan da muke yi? Me zai ce, shi ne sai ya ce da xuwansa ya ji ina ma da ace bikinmu ake yi ni dashi? Wai idan an tashi (engagement) dinmu, kwana uku kawai za a sa a daura aure."
.
Ilham tayi dariya
.
Babu wacce tayi dariya a cikin qawayenta
.
.
Duk abin da Ilham take so a rayuwarta shi Ma'aruf yake so. Haka itama tana son duk abin da yake so. Idan Ma'aruf yazo gidan su wajenta, Ilham ta kan bude falon mahaifinta su zauna suyi hira idan baya nan. Sau da yawa idan Ma'aruf yazo sun fi yin kallo. Ilham tana son fina-finan indiya fiye da kowanne irin fim. Shi yasa ba ta da wata tashar da take kamowa fiye da (Zee Aflam) indai ita kadai zata yi kallo.
.
A ranar da ta fara shiga da Ma'aruf falon gidan su suka yi hira da ta kunna kallo sai ta tambayeshi
.
"kana kallon fina-finan indiya kuwa?"
.
Ma'aruf ya dubeta
.
"me yasa kika yi min wannan tambayar?"
.
Ilham ta ce dashi.
.
"sbd ina sha'awarsu fiye da duk wani abu da zan kalla na debe kewa. Ban sani ba ko kai baka sha'awarsu."
.
A qa'ida Ma'aruf bai ta6a zama ya kalli fim din indiya ba sbd basu yi masa ba." in har kallo zai yi yafi son ya kalli (Wrestling) ko wasannin qwallon qafa.
.
Bai fadawa Ilham baya so ba." ya ce da ita.
.
"nima ina sha'awarsu...suna burgeni."
.
Ilham ta kunna musu kallo, aka fara nuno 'yan wasa. Ta fara sanar da Ma'aruf ra'ayinta akan jaruman da take so. Maza da mata, ta ji yayi shiru ya kasa magana sbd bai sansu ba." Ilham ta yi dariya ta bar abin a xuciyarta, ta fahimci Ma'aruf baya kallon fina-finan indiya, yaqi fada mata gsky ne, don dai ya goyu bayanta kada ya kushe mata abin da take so.
.
Washe gari da Ma'aruf yazo gidansu suka zauna a falo suna hira, sai Ilham ta kunna masu kallo har ta kamo tashar qwallon sai ya ce da ita ta canza tasha ta kamo masu fim din indiya suyi kallo. Ilham ta dubeshi ta yi murmushi
.
L"Ma'aruf na fahimci baka kallon fim din indiya, me yasa zaka 6oye min abin da baka so, don kawai Kaga ni ina so?"
.
Ma'aruf ya ce da ita.
.
"wa ya fada maki bana kallon fina-finan indiya? ina kallon su sosai."
.
Ilham ta yi dariya ta ce dashi.
.
"zan qure ka fa, kada mu fara kallo in tambayeka sunan wani ka kasa fada min."
.
Ma'aruf ya ce da ita.
.
"duk wanda kika tambayeni zan fada maki sunansa."
.
Ilham ta kamo tashar tana dariya, ta san cewar Ma'aruf bai san kowa ba a cikin jaruman indiya. tana kamo tashar suka iske ana tallar sabbin fina-finai masu fitowa. Jarumar da aka fara nunowa tana rera sassanyar waqa a cikin sahara, iska na kada dogon gashin kanta da kuma gyalenta mai shara-shara, tun kafin Ilham ta tambayeshi ya ce da ita.
.
"wannan ita ce Kareenah Kapoor, wacce 'yar uwarta itama tsohuwar fitacciyar jaruma ce wato Karishma Kapoor. Kareena tana daga cikin manyan jarumai mata a fagen fina-finan indiya. tayi fim din Bewafaa tare da Akshay kumar. Tayi Asoka, tare da Sharukhan. Tayi Khabi Khushi Khabi Gham tare da Hirthic da su Amita Bacchan."
.
Ilham ta yi mamakin yadda akayi Ma'aruf ya san wannan jarumar haka sosai, bayan ta san bai ta6a kallon fim dinta ba." xuwa can bayan ta gama waqar sai aka sake nuno wata jarumar tana wasa da shuke-shuke a wani qayataccen lambu. Ma'aruf ya ce da Ilham
.
"ita kuma wannan ita ce Aishwariya, wacce ta kasance tauraruwa sha kallon duk wani fim da zata fito sbd daukakarta. Ta yi fina-finai tare da duk wani jarumi dake tashe. Tayi fim da Devdas tare da Sharukhan. Wanda fitaccen daraktan nan ya bayar da umarni wato Sanjay Leela Bansalay. Sannan tayi fim din jordan Akbar tare da Hirthic. Fitaccen fim dinta wanda ake ganin babu kamarsa shine Aor Pyar Hogaya, wanda ta fito tare da Boby Deol."
.
Ilham ta bi Ma'aruf da kallo cikin kaduwa da mamaki. Ita kanta bata san duk wadann fina-finan da yake fada mata ba." aka sake nuno wani jarumin akan babur Ma'aruf ya ce da ita.
.
"wannan shi ne Abishek Bacchan shine ya auri ita Aishwariya, kuma shine dan tsohon jarumi Amitab Bacchan. Abishek yayi fim din Run ya yi fim din Drona, da kuma Doom 1 da Doom 2 ya fito a fim din Dus tare dasu...."
.
Ilham ta dakatar da Ma'aruf ta tambayeshi
.
"Ya akayi ka san wadann fina-finan da jaruman Ma'aruf? na tabbatar jiya da kazo nan baka san kowa ba a cikin jaruman fim din indiya. ba ka ta6a kallon fim dinsu ko daya ba." ya akayi ka sansu daga jiya xuwa yau?"
.
Ma'aruf ya dubi Ilham ya ce da ita.
.
"gsky ne Ilham, ban ta6a kallon fim din indiya ba ko daya, kuma ban san sunan ko daya ba a cikin jarumansu. Jiya ne da nazo wajenki na fahimci kina so, shi yasa nima naji ina so. Duk abubuwan da kika ji na fada maki, da kuma wadanda ma ban fada maki ba, nayi bincikensu ne a wajen mutane daban-daban na sansu daga jiya xuwa yau. A ynx ina sha'awar indiyan fim sbd naji kina sha'awarsu. Duk abin da kike so a rayuwarki Ilham nima shi nake so a rayuwata."
.
Ilham ta kasa magana. Ta qurawa Ma'aruf masoyinta ido. A lkcn ne ta tabbatarwa kanta cewar ba zata sake samun masoyi kwatankwacin Ma'aruf ba a duniya.
.
.
Lp=11%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 11
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ilham ta kasa magana ta qura wa masoyinta Ma'aruf ido. A lkcn ne ta tabbatar wa kanta har abada ba zata sake samun wani masoyi a duniya kwatankwacin Ma'aruf ba."
.
.
A zamantakewarsu Ma'aruf ya saba ko me ya samu tunanin shi na farko shi ne me zai yiwa Ilham wanda

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment