Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farka a tsorace tana kuka.
.
Za ta dai iya tuno kamar suna tafiya su biyu ita da Ma'aruf... kamar sun ga wani rami a gabansu wanda basu san da shi ba." qafar Ma'aruf ta fada cikin ramin ya yi iya qoqarin sa ya ciro qafar amma ta qi ciruwa. xuwa can kuma sai wuta ta tashi daga cikin ramin, ta fara kamawa Ma'aruf qafar sa.
.
Ilham ta fara 6urari a cikin mafarkin tana kiran mutane don wani ya zo ya taimakesu. Ta bar Ma'aruf a inda wutar take cin qafar sa a cikin rami, ta fara taran-taran tana neman wanda zai zo ya ciro mata mijinta daga cikin ramin da ya fada.
.
Sai daga baya ta ga wani tsoho a zaune a bakin hanya yana barci ya tasa qaramin qoqon sa wanda babu komai a ciki. Ilham ta durqusa a gaban Tsohon ta fara yi masa magiya ya taimaketa ya zo ya ciro mata mijinta daga rami wuta ta kama masa qafar sa. Tsohon ya kalleta cikin tausayawa. Ta ji ya kira sunanta kamar dama ya san ta sannan ya ce da ita,
.
"Ki yi haquri Ilham. Rayuwar mijinki ta zo qarshe, ki tafi gida ki barshi a cikin ramin nan da ya fada. Sbd babu wani abu da zaki iya yi masa a halin ynxn sai dai ki yi masa addu'a."
.
Ilham ta ji maganar Tsohon ta saki xuciyarta. Ta ce dashi a fusace
.
"Qarya ka ke yi babu abin da zai samu mijina sai alheri. Kana so ne ka tsorata ni, baka isa ka rabani da mijina ba." ba zan tafi gida in barshi a nan ba." ba zan yarda da abin da kake fada mani ba."
.
Ilham ta tashi ta bar wajen Tsohon ta garzaya ta koma wajen Ma'aruf mijinta tana kuka. Kafin ta yi nisa ne ta ji Tsohon ya yi magana muryarsa cike da tausayawa ya ce....'
.
"Ban ce dole sai kin yarda da magana ta ba yarinya. Amma ki sani cewar mutuwa tana kan kowa..."
.
A lkcn ne Ilham ta farka daga barcin tana kuka.
.
Khairat ta fara jin ana qwanqwasa qofar gida. Ta tashi ta bar falon ta garzaya dakin mahaifiyarta Ilham don ta shaida mata cewar wani yana qwanqwasa qofa a waje.
.
Khairat ta samu mahaifiyarta a zaune akan gadonta tayi tagumi. Da yake shekarunta basu kai na yadda zata fahimci halin xullumi da rudanin da mahaifiyarta take ciki ba, sai Khairat ta ce da ita kai tsaye.
.
"Mama ana sallama a waje."
.
Ta yi sauri ta juya don ta koma falo ta ci gaba da kallon wasannin tseren da ake nunawa a wata tashar wasanni ta tauraron dan adam. Ilham ta yi ajiyar xuciya ta fito daga cikin dakin nata, ta zo falo ta sami 'ya'yanta biyu, Aiman yana wasa kwance akan darduma. Khairat ta qurawa tangamemen tibin su idanu ko qiftawa bata yi fuskarta cike da fara'a.
.
Kafin Ilham ta fito ne ta dauko (remote) ta rage sautin tibin ya dawo kadan-kadan ake iya jin maganar. Ta fice ta bar 'ya'yanta suna cike da farin ciki a falo. Ta tafi xuwa inda zata ci karo da wani labari wanda har abada ba zata iya mancewa dashi ba....tare da mutumin da yazo ya fada mata.
.
Ilham ta je qofar gida ta zare sakatar qofar ta bude ta, tana tsammanin ganin wata mace a cikin qawayenta da suke yin adashi a layin. Ko kuma wadanda suke xuwa makarantar islamiyya ta matan aure. Ta yi sauri ta ja baya da ta ga wani mutum ne dake a layin su mai suna malam Haruna wanda gidan sa yake a can kan kwana
.
Ta mance bata sako lulli6i ba ko hijabi da zata fito. Sbd xuciyarta a rude take, to amma bata koma ba, tunda dai tana sanye da doguwar rigarta baqa wacce ta kai har qasa, ta hade da kallabinta.
.
"Sannu, ina yini?"
.
Ilham ta gaishe da malam Haruna tana dafe da qofar gidan. Tun kafin ya amsa mata ta yi saurin cewa.
.
"Ai kuwa gashi mai gidan baya nan, ya tafi Katsina tun safe, sai anjima zzai dawo da yamma."
.
Ilham tana qoqarin mayar da qofar ta rufe kenan don ta koma ta ci gaba da begen mijinta wanda bashi nan.....mijinta wanda take sa ran dawowarsa nan ba da jimawa ba." malam Haruna ya dakatar da ita ya ce....'
.
"Nazo ne in fada maki cewar mijinki ya yi hadari akan hanyarsa ta xuwa Katsina."
.
Maganar ta daki xuciyar Ilham. Wanda ya sa ta bude baki ta kasa cewa komai. Idanunta suka furfito bakinta ya bushe tana dafe da qofar gidan. Tun kafin malam Haruna yazo ya yanke shawarar zai fada mata komai kai tsaye sbd yayi sauri ya tafi. Don baya son ya tsaya yaga halin da zata shiga a dalilin abin da yazo fada mata.
.
Malam Haruna ya sake cewa da ita.
.
"Ki yi haquri matar Ma'aruf, ki yi wa mijinki addu'a, Allah Ya yi masa rasuwa a sakamakon hadarin. Ynx haka gawarsa tana nan a wajen 'yansanda zamu je da mai unguwa mu amsota. Na biyo ne in sanar dake don ki sanarwa 'yan uwanki da 'yn uwan mijinki, su zo ayi jana'iza tare dasu. Allah Ya jiqan Ma'aruf ."
.
Malam Haruna ya juya ya fita cikin sauri, ya barta a nan tsaye a bakin qofar gida ta kasa motsawa ta kasa cewa komai. Tsoro da razanar abin da mutumin nan ya fada mata ya sa ko'ina a jikinta ya bushe. Kunnuwanta basa tuno komai, sai 6ur6ushin maganar maqwabcin nasu lkcn da yake cewa.
.
L....ki yi haquri....mijinki addu'a.....a a sakamakon wannan hadarin mota....gawarsa.....'yansanda muje mai unguwa......"
.
Maganar ta zo ma a daburce. Maganar ta rikita dodon kunnenta ta kasa fahimtar sahihiyar ma'anar abin da mutumin ya fada mata. Ilham ta saki qofar gidan ta batra a bude. Ta kasa rufe ta, sbd yn jikinta ba qarfi. Ta koma cikin gida idanunta basa iya ganin komai, ta shiga falo ta wuce 'ya'yanta suna kallo bata dago kai ta kalle su ba. Xuciyarta tayi nisa a cikin firgici da rudani, ya yin da xuciyar yaran ta yi nisa akan abin da suke kallo.
.
Ilham ta shiga dakinta a rude ta fada kan gadonta. Ta sake qoqarin tuno abin da malam Haruna ya fada mata. Babu shakka mijinta ne ya rasu. Dama tun daxun ita ta ji a jikinta. Dama tun safe ta ji ta rasa me yake yi mata dadi kamar bata da lfy. A lkcn ne Ilham ta fashe da kuka jikinta yana kyarma sbd tsananin kaduwar da ta yi. Yn shi kenan Ma'aruf ya tafi....shi kenan ba zzata sake ganinsa ba a duniya?....shi kenan ba zata sake jin muryarsa ba idan yana sanar da ita wani abu yana murmushi?....shi kenan ba zasu sake yin wasannin su ba na soyayya....? Ba zasu sake zaunawa tare da 'ya'yansu ba su yi barci.... Su tashi.... Su ci abinci tare....su tafi unguwa....su yi bankwana in zai yi tafiya....?
.
Ilham ta ji juwa ta dauketa, duniyar ta fara juya mata. Bata san lkcn da ta sulmiyo daga kan gadon ba ta fado qasa. A nan...a yashe a tsakar dakin ta xube ita kadai tana kuka da alhinin begen mijinta.
.
.
.
Lp=5%?%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 5
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ba ta san lkcn da ta silmiyo daga kan gadon ba ta fado qasa. A nan a yashe a tsakar dakin ta xube ita kadai tana kuka da alhini tana begen mijinta. A lkcn ne ta fara tuno baya. Ta fara tuno abubuwan da suka faru a rayuwar ta...tun farkon haduwarta da Ma'aruf masoyi ne na gsky kuma jarumi a cikin maza sbd ya yi mata halacci mai yawa a rayuwar ta... Ilham ta fara tunani.
.
.
.
BABI NA DAYA
*
*
An haifi Ilham a cikin birnin Katsina a unguwar Filin samji. Mahaifinta Alh. Ayuba Tsohon ma'aikacin gwamnati ne wanda ya dade da yin ritaya ya dawo ana hada-hadar siyasa tare da shi.
.
Ilham ba ta girma tare da mahaifiyarta ba tun tana qarama 'yar shekara uku mahaifinta ya rabu da mahaifiyarta, kuma ya hanata tafiya da ita. Ilham ta taso kamar marainiya a gidan su tare da yayyenta su takwas uku maza biyar mata, wadanda duk mahaifiyarsu daya wato Haj. Kubra.
.
Faraira ita ce mahaifiyar Ilham. wata bafillatanar jihar nassarawa ce a cikin garin Lafiya. Wacce Alh. Ayuba mahaifin Ilham ya hadu da ita a wajen yawace-yawacen canjin aikin da aka sha yi masa, bashi a wannan gari bashi a wancan.
.
Ilham ta dauko kamannin mahaifiyarta sak, bata bar komai ba." wankan tarwada ce wacce take da kafar gashi a jikin ta...gashin idanunta da girarta da kuma yalwataccen gashin kanta, da wasu baqaqe sirara wadanda suka fito mata a hannuwanta, sun isa su sa kowa ya fahimci akwai wani jinsi dake tattare da ita na wasu mutane ko wata qabila, wacce ta sha banban da na mahaifin ta Alh. Ayuba.
.
Ilham tana da kyakkyawan jiki, ba ramammiya ba ce, duk da yake ba zai yiwu a sakata a layin masu qiba ba." lkcn da tana makarantar firamare a unguwarsu mutane da yawa sun ce idanunta sun fi komai basu sha'awa. Duk sanda aka tashe su tara idan Ilham tana wasa da yara ko in zasu dawo gida, wani mai tireda dake a layin su wanda yake da budurwar xuciya ya kan kirata ita kadai ya bata kyautar cingam ko alawar tsotso don kawai ta kalleshi ya ga idanunta.
.
Amma da Ilham ta je makarantar kwana gashin kanta da qananun gashin da suke fito mata a haanu yafi burge qawayenta wadanda suke daki daya. Idan Ilham ta fito wanka kafin ta bushe ta kan sa hannunta ta riqa kwantar da gashin kanta ya kwanta ya yi ta sheqi a bayan. Qawayenta suna kallo daga kan dagajensu suna ji ina ma sune suke da gashin Ilham
.
Da Ilham ta gama karatun sakandire ta dawo gida ta zama cikakkiyar budurwa komai dake tattare da ita yana burge mutane. Shigarta, maganarta' fara'arta, dabi'unta da kuma uwa uba kamun kanta da jan ajinta, sbd a duk fadin unguwarsu ba za a samu maza uku wadanda take yiwa magana ba." idan ma har za a samu to sai dai wadanda take mutunci dasu. Ko dai inda take sayen katin waya ta bayar da caji. Ko kuma wani matashi dake sayar da kankana da lemu a bakin qofar gidan su." Ilham bata kula mutane barkatai. Ba maza ba, hatta 'yan mata yawanci sai wadanda ta san sun yi karatu tare. Duk fadin unguwarsu bata da qawa ko daya.
.
Mahaifin Ilham yana sonta sosai, kuma hakan shi ya jawo mata baqin jini da tsana a wajen sauran 'yan uwanta. Duk lkcn da Alh. Ayuba zai yi wa Ilham wani abu, to qura ta taso kenan a cikin gidansa. Mahaifiyar manyan 'ya'yansa wato Haj. Kubra, ata taso ita da 'ya'yanta su nuna atafau!! Basu yarda ba." idan kuma wani abu ne wanda za a yiwa kowa da kowa, to sai 'yan uwanta sun san yadda suka yi mata kutunguila da bi-ta-qulli suka karkatar da ra'ayin mahaifinta ya fasa yi mata nata abin da take so.
:
Tun a wajen makarantun da Ilham ta yi ta ke samun matsala da 'yan uwanta. Lkcn da zata je sakandire aji daya, makarantar 'yanmata ta Gwamnatin tarayya (Federal Government Girls College) da ke Funtuwa Ilham ta ce da mahaifinta tana so ta je. Kafin ya nemar mata makarantar ne, sai ya kira yayyenta su uku maza wadanda suka gama karatu suke zaune a gida ba aikin yi ya fada masu abin da da Ilham ta ce tana so.
.
Babban yayansu Auwal ya ce da mahaifinsu.
.
"Baba ai Ilham ta yi qanqanta da xuwa (Boarding school) a dai samu wata (Day) nan kusa dake a gida a kaita."
.
Yayansu na biyu wanda ke bin Auwal mai suna Mustafa ya ce da mahaifinsu.
.
"kuma ga nisa baba. Ko hutu aka yi sai an sha wahala kafin a je a dawo da ita."
.
Qaramin yayanta a maza wato Jamilu ya ce....'
.
"Bayan nan kuma kaga ba wani qoqari gareta ba Baba. Yawancin yaran da ake dauka a irin wadann makarantun masu qoqari ne....! Amma gsky Ilham ba zata iya ba."
.
Suka rushe maganar xuwan Ilham makarantar da ta ce tana so. Mahaifinta don a zauna lfy a gidan don kada Haj. Kubra ta ce an fi son Ilham akan 'ya'yanta sai ya bi shawarar da su Auwal suka bashi. Aka sa Ilham a wata qarammar makarantar sikandire jeka-ka-dawo dake a layinsu. A haka ta yi karatun tsawon shekaru uku cikin fushin rashin cimma buri.
.
Da ta kammala aji ukun farko zata je babbar sakandire a nan ma sai da aka kai ruwa rana. Ilham ta yi sha'awar xuwa makarantar kudi ta 'yanmata. Amma Auwal ya yi ruwa ya yi tsaki akan dole sai sai dai idan makarantar kwana take so ta za6i wata amma ba dai wacce take so ba." a qarshe Ilham ta je makarantar kwana dake a Kabomo, qaramar hukumar Bakori. Anan ta gama karatunta na sakandire. Ta dawo gida cike da burin zana jarrabawar share fagen shiga jami''a.
.
Duk sauran 'yanmatan da suka taso yayyen Ilham da suka yi aure. Babu wacce ta wuce sikandire. maza ne kawai su Auwal da Mustafa da Jamilu suka yi difloma, suma babu wanda ya je jami'a a cikin su." Da labari ya riskesu cewa Ilham tana so a biya mata jarrabawar share fagen shiga jami'a (jamb) sai duk suka yo mata caaa!!
.
Auwal ya ce da mahaifinsu.
.
"Me Ilham zata iya yi a jami'a Baba? Muma da muke maza kuma yayyenta mun haqura mun yi diploma ita sai ta ce dole sai ta yi digiri....?"
.
Mustafa ya qara da cewa.
.
"kamata yayi kawai ta fito da miji a yi mata aure Baba, ba wani karatu da zata iya yi a jami'a."
.
Jamilu ya ce a qarshe.
.
"To yaushe ma zata gama karatun, abin da Kodayaushe ba a rabuwa da yajin aiki a jami'o'in qasar nan? Gsky Baba ka qyale maganar jami'ar nan a dai nemo mata wani abin..."
.
Mahaifinsu ya dauki shawarar 'yan uwan Ilham duk da yake cewar ya san ya hana Ilham abin da take so fiye da komai a rayuwarta. Daga baya ya kirata ya ce da ita ta yi haquri ta shiga (FCE) TUNDA 'YAN UWANTA Basu goyu bayan xuwanta jami'a ba." Ilham ta ce da mahaifinta ta haqura da karatun baki daya, Ta tashi ta koma dakinta tana kukan baqin cikin wannan qiyayya da tsana da 'yan uwanta suke nuna mata.
.
Gashi kuma mahaifiyarta wata irin mace ce wacce Ilham ta kasa gane ta. Sai ta shekara uku cur bata zo taga ilham ba a Katsina. Tunda suka rabu da Alh. Ayuba ta koma jihar Nassarawa, ta mance da Ilham kamar ba ita ta haifeta ba." bata ta6a niqo gari takanas-ta-kano ta zo don ta ga Ilham ba, sai dai idan wani abu ya kawota Katsina ta biyo ta ganta a gurguje ta tafi ta ce sauri take yi.
.
Ilham tana so duk sanda mahaifiyarta ta zo su zauna ta fada mata inda danginta suke. Tana so ta sansu ta riqa xuwa inda suke komai nisan garuruwansu, sbd da su kadai ne zata yi alfahari, tunda dai 'yan uwanta da suke uba daya basu damu da ita ba, kuma sun tsane ta...tun
.
Furaira ba ta ta6a fadawa Ilham inda wasu 'yan uwanta suke ba." da Ilham ta tambayeta to wa take aure ynx bayan rabuwarta da mahaifinsu? Sai ta ce da Ilham har ynx bata sake yin wani auren ba. Ilham ta fahimci mahaifiyarta zaman kanta kawai take yi. Sb ko a wani xuwa da ta yi Katsina wani qaton baqin mutum mai kudi ya kawota a mota, wai sun zo wajen wani taron siyasa da ake yi na jam'iyyarsu.
.
Tun daga lkcn Ilham ta tsinke da lamarin mahaifiyarta ta daina xumudin ganinta. Don kuwa ta fahimci bata kama kanta ba. Ta riqa jin kunyar yadda mahaifiyarta take gudanar da irin wannan rayuwar ba aure.
.
.
.
Lp=6%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 6
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Tun daga lkcn Ilham ta katsa da lamarin mahaifiyarta. ta daina xumudin ganinta domin kuwa ta san bata kama kanta ba." ta riqa jin kunyar yadda mahaifiyarta take gudanar da irin wannan rayuwar ba aure. Kuma bata damu da kowa ba sai kanta kawai, da abubuwan da take so a rayuwar ta...tun
.
Ilham ta rasa da wa zata zzauna ta ji dadi a duniya? Ba tare da mahaifiyarta. mahaifinta kuma yana tsoron ya nuna mata so. Sbd kada matarsa uwar manyan 'ya'yansu ta ji haushi. Su kuma yayyenta sun tsaneta, gashi kuma ita kadai mahaifiyarta ta haifa a gidan, ta tafi ta barta.
.
Ilham ta fasa karatun ta zauna a gida tare da sakamakonta na sakandire kadai...tare da kyakkyawar surar jikinta wanda a Kodayaushe yake jawo mutane ta ko'ina xuwa gareta suna kawo mata farmakin soyayya ita kuma Ilham tana gocewa makamin soyayyar namiji. Bai ta6a fadawa kanta ba. Ba ta ta6a yin soyayya da kowa ba."
.
A zamanta haka nan a gida ma bata tsira ba." mahaifin ta ya ce da yayyenta ya kamata a samarwa Ilham da sana'ar da zata riqa yi kafin tayi aure, tunda dai babu karatun. Sanda Alh. Ayuba ya kira 'yan uwanta zasu yi wannan shawarar, ba a kira Ilham ba, ta dai zo wucewa ta falon mahaifin su ta ji suna magannar. Alh Ayuba ya c masu. Zai saya mata babban injin saqar kaya ta koyi saqa don idan tayi aure ta dogara da kanta.
.
Auwal ya ce da mahaifinsu cikin damuwa.
.
"Gskyr magana Baba Ilham ba zata iya yin saqa ba." wannan san'a ce ta masu kazar-kazar, ba san'aa ce ta masu son jiki irin Ilham ba, 6arnar kudi kawai za'ayi ko an sayo mata injin don kuwa ba zata iya ba."
.
Mustafa ya ce....'
.
"in haka ake so ai yafi ma a saya mata keken dinki, amma yaushe Ilham zata iya yin wani saqa?"
.
Jamilu ya ce....'
.
"irin wadannan kayan ma Baba ko an saye su ba dadewa suke yi ba, nan da nan suke lalacewa. Kawai ka barta tunda dai ba ita ta ce tana so ba."
.
Ilham ta girgiza kai ta yi tafiyarta. Ta bar 'yan uwanta a falon tare da mahaifinsu suna ta kushe abin alherin da mahaifinsu ke son yi mata. Shi kuma ya riga ya saba' bai ta6a yi mata wani abu ba sai ya kira su yayi shawara dasu' matsayin manyan 'ya'yansa.
.
A haka rayuwar ta ci gaba da xuwar wa Ilhamm ta yi haquri ta ci gaba da zama tare da 'yan uwanta wadanda suka dora mata karan tsana, akwai abubuwa da yawa da ta rasa a rayuwarta. Akwai abubuwa da yawa da take so, amma da yake ta san ko ta tambaya ba zata samu ba, sai ta riqa yin haquri tana barin abin a xuciyarta. Kuma da yake Ilham tana da haquri da zurfin ciki, bata ta6a fitowa waje ta fada ba." kadan ne daga cikin mutanen da suke makwabtaka dasu suka san abin da yake faruwa da irin zaman da Ilham take yi a gidansu tare da 'yan uwanta wadanda ba mahaifiyarsu daya ba."
.
A ranar wata alhamis...tabbas ranar alhamis ce da yamma, Ilham ba zata ta6a mancewa da wannan rannar ba mai dumbin tarihi a rayuwarta. A ranar ne Ma'aruf ya fado cikin rayuwarta ba zato ba tsamman.
.
Ilham ta fito kenan daga gida tazo shagon sayar da katin wayar dake kusa da gidan su a kan layin nasu. Ta iske samari kusan biyar a zazzaune a kan benci tare da mai shagon suna labarin qwallon qafa. Ilham ta yi sallama ta ce da Khalid mai sayar da katin ya bata (MIN) na dari biyu. Ta miqa kudin. A sanda tazo wajen kowa yayi shiru a cikin matasan da suke zaune a bakin shagon. Ilham bata daga kai ta kallesu ba, ta san ita suke kallo. Ta hadefuskarta har lkcn da Khalid ya ciro latin ya bata. Da ta juya ta tafi ne ta nufi gidansu ta ji wani a cikin samarin ya ce da Khalid mai shagon.
.
"wannan kuma wace ce a nan layin Khalid? Kune 'yan gari mu baqi ne....! Don Allah wace ce?"
.
Ilham ta ji Khalid ya yi dariya amma bai cewa wanda ya yi masa tambaya komai ba akanta.
.
A sannan ne Ilham ta tabbatarwa kannta duk da bata waigo ba, babu shakka wani a cikin samarin ya kamu da sonta....a nan take daga kawai ta zo sayen kati.
.
Kamar yadda mutane da yawa suka sha kamuwa da sonta amma har ynx bata hadu da wanda ya ji ya yi mata ba ranta.
.
.
.
***
.
.
Da qarfe takwas na dare bayan ann idar da sallar Isha'i ya zo har ggidansu ya aiki yaro ya kai mata wasiqa har gida. Ilham tana kwance a katifarta yaron yayi sallama ya miqa mata takardar.
.
"Gashi in ji wani ya ce wai a baki."
.
Ilham ta kalli takardar cikin rashin kulawa.
.
"wane ne ya baka ya ce ka kawo min?"
.
Yaron ya ce....'
.
"nima ban sanshi ba, yana nann a tsaye a waje."
.
Ilham ta amshi takardar, a yayin da yaron ya fita ya bata wuri. Ta warware taga rubutu ne bai wuce layi hudu ba bashi da yawa, ta fara karanta.
.
.
Assalamu alaikum.
Ilham suna na Ma'aruf. Daxu na ganki da yamma a sanda kika zo sayen kati a shagon Khalid ina so ne in fadi maki wata magana, ina so ki fito ina qofar gidanku ina jiranki ynxn nan.
na gode.
.
.
Ilham ta dubi takardar bayan ta gama karanta ta. Ta sha cin karo da irin wadannan saqonniin ba sau daya ko sau biyu ba. Ta sa hannu biyu ta keta takardar, ta watsa ta a kwandon shara dake bayan qofar dakinta.
.
A lkcn ne ta sa qafa ta tura qofar ta rufe, ta jawo mayafinta ta rufa sbd ana sanyi. Ta rufe idanunta. Bata yi minti ashirin a baka ba ta fara barci.
.
A daren sai da Ma'aruf ya kai awa uku a zaune yana jiran fitowarta. Da ya tabbatar ba zata fito bane ya tafi ya rabu da ita.
.
A rana ta biyu tun da safe ya zo gidansu don ya ganta su sake yin ido da ido. Ya nemi lambar wayarta kamar gwal a ruwa amma duk fadin layin bai samu wanda yake da lambar Ilham ba. Shi kanshi Khalid mai sayar da kati duk da yana mutunci da Ilham bata ta6a bashi lambarta ba." shi yasa tun farko bai ba Ma'aruf qwarin guiwar xuwa ya sameta ba." don ya san da wahala ta amince masa. Ilham ba kamar sauran mata ba ce.
.
Da fitowarta zata shiga gidan dake hade da nasu kenan sai Ma'aruf ya taso sameta yana fara'a. Ilham ta samu kanta tana fuskantar wani farin saurayi dan kimanin shekaru talatin da haihuwa. Sanye da baqin wando da rigar masu bautar qasa. Ilham ta tambayeshi da taga ya tsaya mata a hanyar wucewa.
.
"Lfy malam..?"
.
Ma'aruf ya ce da ita.
.
"ni ne Ma'aruf din da na aiko miki da takarda jiya da daddare ki qi fitowa. Shi ne na sake dawowa ynx da safe, sbd na qosa mu hadu in fada miki abin da yake raina."
.
Ilham ta ce dashi cikin fushi.
.
"Dakata malam, kaga bana son irin wannan, kada ka sake biyoni gidan mu. Kaga kai ba qaramin yaro ba ne, bana so in yi maka wani abu ka ce nayi maka rashin kunya. Don Allah ka rabu da ni bana so, kawai ka rabu da ni, na gode.
.
Ma'aruf ya rage fara'ar dake a fuskarshi ya ce da Ilham
.
"na gode sosai da kika fada min gsky tun ynx. Ban san cewar na takurawa rayuwarki ba a dalilin biyoki da nayi har gida ba. Li yi haquri Ilham."
.
Ta kauce ta bashi wuri ta shiga cikin gidan da zata shiga ta barshi a tsaye a waje cikin damuwa.
.
.
.
Lp=7%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 7
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ta kauce ta bashi wuri, ta shiga cikin gidan da zata shiga ta barshi a tsaye cikin damuwa. Da yake Ilham ta san Khalid ne ya fadawa mutumin ko ita wace ce? Ba a dade da yin haka ba da rana ta taka ta je har shagon wayarsa ta same shi babu kowa yana zaune yana gyara wata waya akan teburi. Ilham ta ce da Khalid a fusace.
.
"wajen ka nazo

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment