Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai faranta mata rai da shi? Ma'aruf ya saba ya yi ta kashewa Ilham kudi da saye-sayen kayayyakin kyaututtukan soyayya. To amma Ilham ba ta san yaya yake qoqarin yi mata irin wadannan hidindimun ba a matsayin sa na wanda yake aikin bautar qasa.
.
Ilham tana so ta tambayi Ma'aruf amma tana jin kunyarsa. Sai da abokinsa Khalid ya ta6a bata wani saqo da Ma'aruf ya aiko shi sannan Ilham ta tambayeshi, ko ya san yadda Ma'aruf yake samun kudaden da yake kashe mata haka?
.
Khalid ya ce da ita.
.
"gsky Ma'aruf bashi da wata hanyar samun kudin da ta wuce dan alawus din da ake basu a inda yake aikin sa na (Service) sai kuma wata makaranta da yake xuwa yana taimaka masu a ranakun litinin da talata amma su bana jin yana amsar kudi. Kyauta yake yi musu."
.
Tun daga ranar Ilham ta fahimci duk abin da Ma'aruf yake samu a rayuwar sa akanta kawai yake qarar dasu baki daya. A lkcn ne tayi alqawarin ba zata qara amsar duk wata kyauta da Ma'aruf ya yi mata ba."
.
Tun daga ranar kome ya kawo ya bata, bata amsa, kuma duk sanda irin haka ta faru a tsakanin su sai ta fada masa ya daina yi mata dawainiyar komai. Ta gode! Ta gode!! Ta gode!!!..amma ba zata amsa ba."
.
Don kada ta riqa damuwa sai Ma'aruf ya daina bata kyautar komai. Ba a dade ba watan babbar sallah ya tsaya. Mahaifin Ilham ya tambayi 'ya'yansa irin kayan da za a siyasa a dinka da sallah. Kowa ya fadi irin kayan da yake so a saya masa. Ilham ta ce da mahaifinta ita tafi son atamfar England. Mahaifinta ya ce kada ta damu zai saya mata.
.
Sun yi wannan maganar da kwana daya, da wani a cikin yayyenta ya samu labarin irin atamfar da Ilham ta ce tana so a saya mata sa sallah, sai ya yi mata kutunguila ya soke alqawarin da mahaifinta ya yi mata.
.
Alh. Ayuba ya kira Ilham ya ce da ita.
.
"gsky atamfar nan da kika ce kina so ba zaki sameta ba Ilham. sbd nayi bincike an fadi mani bata da nagarta ga kuma tsada. Ynx ki bari a samu ko leshi ne na dubu uku a saya maki, ko kuma shadda, sai ki za6i wanda kike so a cikin biyun."
.
Ilham ta ji baqin ciki ya soki xuciyarta. Ta san wani ne ya je yayi mata wannan munafurcin a wajen mahaifinta. Don ya hana a saya mata atamfar da zata sa da sallah. Ilham ta ce dashi.
.
"Baba ka barshi kawai sai wani lkcn in ina da rabo na san wata rana zaka saya mani, tunda kayi niyya ba komai."
.
Ta tashi ta tafi tana share hawaye. Ta gwammace ta wanke tsofaffin kayanta ta ci sallar dasu. Ko ya akayi har Ma'aruf ya samu wannan labarin?... Kowa ya fada masa tayi wannan badaqalar da 'yan uwanta a gida? Ita dai bata sani ba, kuma bata fadawa kowa ba."
.
Saura kwana biyu sallah Ma'aruf ya xo gidansu ya sa aka kirata. A lkcn qarfe goma na safe Ilham ta fito cike da mamakin dalilin xuwan Ma'aruf wajenta da safe haka ko lfy har yake cewa tayi sauri ta zo? Da xuwanta Ma'aruf ya ce da ita.
.
"nazo ne ina so ki raka ni wani waje, amma zamu dade ba ynxn nan zamu je mu dawo."
.
Akwai yarda...akwai amincewa tsakanin Ilham da Ma'aruf. Bata yi ko kwalliya ba, haka nan ta fito da kodaddun kayanta, ta yafa qaramin gyalenta qafarta sanye da silifas. Ilham ta ce da shi.
.
"bari in shiga gida in canza kaya in sa takalmi, kaga silifas ne a qafata."
.
Ma'aruf ya ce da ita.
.
"ba komai, mu je a haka sauri nakw yi Ilham."
.
Ta ce dashi.
.
"shi kenan mu tafi.l"
.
Sai da suka fara tafiya taga ya tunkari wata qaramar mota (Civic) wacce ke a bakin hanya sannan ta fahimci shi ne ya zo da motar. Ma'aruf ya bude motar ya shiga kafin Ilham ta bude tata qofar ne ta tambayeshi.
.
"yaushe ka yi ciniki ban sani ba Ma'aruf?"
.
Ya yi dariya.
.
"ba tawa ba ce. Ilham ta wani abokina ne da muke zaune gida daya, shima corper ne."
.
Ma'aruf ya tashi motar, ya tuqa suka tafi.l Ilham tana zaune a gefe daya ya dauki hanya suka kama hanyar fita Katsina. Da taga gudun da yake yi yayi yawa, sai ta tambayeshi cikin wasi-wasi.
.
"wai ina zamu je ne Ma'aruf? naji ka xxe ba nisa kuma kana ta gudu, don Allah ina zamu je?"
.
Ma'aruf ya yi murmushi ba tare da ya dubeta ba ya ce....'
.
"kada ki damu kano zamu je, ai ba nisa ynxn nan zamu je mu dawo."
.
Ilham ta dafe qirji cikin mamaki.
.
"kano...? Ma'aruf ya baka fada mani ba, baka ganin yadda nake? Dubi fa silifas ne a qafata, dubi kodadden gyalen da na yafa. Gsky mu koma gida in canza kaya."
.
Ma'aruf ya juye ya dubeta ya ce.
.
"indai don takalmi da gyale ne ba sai mun koma gida kin canza wasu ba." naji kamar an ce ana sayar dasu a Kano."
.
Ilham ta roqeshi cikin natsuwa.
.
"ynx duk wannan wasan mu ajiyeshi a gefe daya. Ka fada mani gsky. Me zamuyi a Kano Ma'aruf?"
.
Ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya ce da ita.
.
" zamu je mu sayi kayan sallah ne. Naji ance atamfar england kike so ki sa a wannan sallar. Shi ne zamu je ki za6i irin wacce kike so ki sa a wannan sallar a Kantin Kwari. Tun sanda labarin yadda kuka yi a gida ya sameni, na dauki alqawarin ko kaina zan sayar in samu kudi, sai kin ci sallah da irin kayan da kike so."
.
A sannan ne xuciyar Ilham ta shiga yi mata kirari:
.
Kin dace da masoyi Ilham....kin dace da mijin aure. Samun masoyi kwatankwacin Ma'aruf abu ne mai wahala a duniya.
.
.
.
Lp=12%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
PAge 12
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ilham tana hangenshi ya fito da qwallo, wasu yara manya 'yan aji shida suna biye dashi cike da murna, Ma'aruf ya jasu xuwa filin qwallon makarantar. Ya rabasu gida biyu, ya fara yi masu nasiha, sannan ya sa masu qwallon suka fara wasa, shi kuma ya zama alqalin wasa, ya riqa hura usir yana binsu a guje duk inda qwallon ta nufa,
.
Wasu yara biyu suka yi karo da suna suka fadi suna kuka. Ma'aruf ya tsayar da wasan, ya kama qwallon ya riqe ya dawo da hankalinsa kan yaran da suka ji ciwo. Ya lallabe su suka tashi, sauran yaran suka zo suka zagaye shi.
.
Ma'aruf ya duba raunin da kowanne ya ji ya riqa lallashinsu da kalamai masu dadi, sannan ya kira wani dalibin ya ce dashi ya je dasu ofishin hedimasta a sa masu magani a raunin
.
Ma'aruf yana son daliban kamar yadda suke son shi. Ilham ta sirare ta tafi, ta koma gida ba tare da ya ganta ba." a xuciyarta tana tunanin shin idan ta auri Ma'aruf, haka zai riqa kulawa da 'ya'yanta...'ya'yansu da zasu haifa? Haka zai zama uba na-gari mai adalci da tausayin 'ya'yansa? Haka zai riqa kyautata masu?
.
Sai da yamma da yazo gidansu ta ce dashi tana dariya
.
"Daxu na je makarantar da kake koyarwa, na dade ina kallon ka, baka ganni ba."
.
Ma'aruf ya ce....'
.
"kamar da gaske."
.
Ilham ta ce dashi.
.
"ka tuna lkcn da yaran nan da suke qwallo suka yi karo. Ka tsayar da wasan ka zo wajen su tare da sauran yaran da ke qwallon?"
.
Ma'aruf ya ce da ita.
.
"amma baki yi min magana ba in zo Ilham?"
.
Ta ce dashi.
.
"6oyewa nayi, dama bana so ka ganni. Na ga ka sha gudu kai da yara, ya tsamin jiki?"
.
Suka yi dariya
.
"Ai na saba, bana jin wuya a haka muke wuni muna wannan guje-gujen ni dasu."
.
Ilham ta tambayeshi
.
"kuma da gaske kyauta kake yin aiki a makarantar Ma'aruf' basu biyanka komai?"
.
Ya ce da ita.
.
"Ai ni na san kaina Ilham, ba don kudi nake yi ba, ina yi ne don in taimaki al'ummata da kuma qasata." Ilham ta bi shi da kallo, bata ce dashi komai ba." Ma'aruf ya qara da cewa. "lkc ya yi da ya kamata mutane su fahimci muhimmancin aikin taimakon kai-da-kai.... Duk a yadda ka samu kanka, to ya dace ka binciko irin baiwar da Allah Yayi maka, ka taimaki al'umma da ita ka bayar da taka gudunmawar."
.
Idan mutum ya kalli duniya zai ga cike take da kayayyakin more rayuwa, wadanda wasu mutane suka samar dasu da tunaninsu da basirarsu. Kodayaushe yana da kyau mutum ya jajirce shima ya ga ya samar da wani abu da zai amfani mutane koda qanqani ne....! Koda yaushe na kan dora rayuwata akan wata magana da na yarda sa ita wacce ke cewa."
.
"Hanya daya da zaka rayu har abada shi ne ka bar wani aiki na alheri a bayanka."
.
Ilham wacce ta qurawa Ma'aruf ido ta ce a xuciyarta
.
"Na kamu da so...na kamu da so..."
.
.
.
*** *** **
.
.
Babi na uku.
.
.
Da kowa yaga abin dai da gaske suke yi. Ilham da Ma'aruf sun riqe soyayyarsu da hannu bibbiyu, suna son junansu kamar su hadiye kansu sai Alh. Ayuba ya kira Ilham ta same shi a falonssa ya ce da ita.
.
"Ilham duk abin da ki ke ciki ke da yaron nan da yazo bautar qasa, ban ta6a cewa da ke komai ba." ina ganin lkc ya yi da ya kamata in yi magana da ke akan wannan al'amarin."
.
Ilham ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba. Alh. Ayuba dake zaune akan kujera ya ci gaba da cewa.
.
"na fahimci yadda kuka shaqu ke da shi, kuma a yadda naga alama da gaske yake yi. To amma kin kuwa tsaya kin yi tunani sosai akanshi Ilham? Kina jin idan ya aureki zai iya riqe ki da mutunci? Ki a lamarin ku na yara baku tsayawa ku ba komai lkc, kuna matuqar yanke hukunci matuqar xuqatanku suna son wani abu. Me kika fahimta a game dashi, wanda ya baki qwarin guiwar jin shi mutum ne na-gari kuma zai iya riqe ki tsakani da Allah?"
.
Ilham ta yi ajiyar xuciya. Ba tare da ta dago kai ta dubi mahaifinta ba." ta ce da shi a sanyaye.
.
"Baba kowa yana shaidar Ma'aruf a unguwar nan, ko mutane ka tambaya zaka ji ance yana da mutunci da...."
.
Alh. Ayuba ya dakatar da 'yarsa Ilham
.
"zancen shirme kenan! Don mutane sun ce yana da mutunci sai ki dogara da haka?
.
.
Lp=13%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 13
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ilham tana hangenshi ya fito da qwallo ya riqeta da hannunsa biyu, wasu yara 'yan aji shida manya suna biye da shi cike da murna. Ma'aruf ya ja su xuwa filin qwallon makarantar. Ya raba su gida biyu, ya fara yi masu nasiha, sannan ya sa masu qwallon suka fara wasa, shi kuma ya zama alqalin wasa, ya riqa hura usur yana bin su a guje duk inda qwallon ta nufa.
.
Wasu yara biyu suka yi karo da juna suka fadi suna kuka. Ma'aruf ya tsayar da wasan, ya kama qwallon ya riqeta ya dawo da hankalinsa kan yaran da suka ji ciwo. Ya lallashesu, suka tashi, sauran yaran suka zo suka zagaye shi.
.
Ma'aruf ya duba raunin da kowanne ya ji ya riqa lallashinsu da kalamai masu dadi, sannan ya kira wani dalibin ya ce da shi ya je dasu ofishin hedimasta a sa masu magani a raunin
.
Ma'aruf yana son dalibansa kamar yadda suma suke son shi. Ilham ta sirare ta tafi, ta koma gida ba tare da ya ganta ba." a xuciyarta tana tunanin shin idan ta auri Ma'aruf, haka zai riqa kulawa da 'ya'yanta..'ya'yansu da zasu haifa? Haka zai zama uba na-gari mai adalci da tausayin 'ya'yansa? Haka zai riqa kyautata masu?
.
Sai da yamma da yazo gidan su ta ce dashi tana dariya
.
"Daxu na zo makarantar da kake koyarwa, na dade ina kallonka, baka ganni ba."
.
Ma'aruf ya ce....'
.
"kamar gaske." Ilham ta ce dashi. "ka tuna lkcn da yaran nan da suke qwallo. Suka yi karo ka tsayar da qwallon ka je wajen su tare da sauran dalibai?"
.
Ma'aruf ya ce da ita. "amma ba ki yi min magana ba in zo Ilham?" ta ce da shi. "6oyewa na yi, dama bana so ka ganni. Na ga ka sha gudu kai da yara. Ya tsamin jiki?" suka yi dariya tare.
.
"Ai na saba, bana jin wuya a haka muke wuni muna wannan guje-gujen ni da su."
.
Ilham ta tambayeshi "kuma da gaske kyauta ka ke yin wannan aikin a makarantar basu biyanka komai?"
.
Ya ce da ita. "Ai ni na san kaina Ilham. ba don kudi nake yi ba, ina yi ne don in taimaki al'ummata da kuma qasata." Ilham ta bi shi da kallo bata ce komai ba, Ma'aruf ya qara da cewa. "lkc ya yi da ya kamata mutane su fahimci muhimmancin aikin taimakon kai-da-kai.... Duk yadda ka samu kanka, to ya dace ka binciko irin baiwar da Allah Ya yi maka, ka taimaki al'umma da italian ka bayar da taka gudunmawar." idan mutum ya kalli duniya, zai ga a cike take da kayayyakin more rayuwa wadanda wasu mutane suka samar dasu da tunaninsu sa basirarsu. Kodayaushe yana da kyau mutum ya jajirce shima ya ga ya samar da wani abu da zai amfani mutane koda qanqani ne....! Kodayaushe ina dora rayuwata akan wata magana da ke cewa. "Hanya daya da zaka rayu har abada ita ce ka bar wani aiki na alheri a biyanka.
.
.
.
*** ***
.
.
Babi na uku
.
.
Da kowa yaga abin dai da gaske suke yi. Ilham da Ma'aruf sun riqe soyayyarsu da hannu biyu, suna son junansu kamar su hadiye kansu, sai Alh. Ayuba ya kira Ilham ta sameshi a falonsa. Ya ce da ita.
.
"Ilham duk abin da kike ciki ke da yaron nan da yazo bautar qasa, ban ta6a cewa da ke komai ba." ina ganin lkc ya yi da ya kamata in yi magana dake akan wannan al'amarin." Ilham ta sunkuyar da kanta ba ta ce komai ba. Alh. Ayuba dake zaune akan kujera ya ci gaba da cewa.
.
"na fahimci yadda kuka shaqu ke da shi, kuma a yadda naga alama da gaske yake yi. To amma kin kuwa tsaya kin yi tunani sosai akanshi Ilham? kina jin idan ya aureki zai iya riqeki da mutunci? Ku al'amarin ku na yara baku tsayawa ku ba komai lkc, kuna gaggawar yanke hukunci matuqar dai xuciyarku tana son wani abu. Me kika fahimta a game da shi, wanda ya baki qwarin guiwar shi mutum ne na-gari, kuma zai riqe ki tsakanisa da Allah?" Ilham ta yi ajiyar xuciya. Ba tare da ta dago kai ta dubi mahaifinta ba." ta ce da shi a sanyaye. "Baba kowa yana shaidar Ma'aruf a unguwar nan, ko mutane ka tambaya zaka ji sun ce yana da mutunci da..." Alh. Ayuba ya dakatar da 'yarsa Ilham ya ce....' "zancen shirme kenan! Don mutane sun ce yana da mutunci sai ki dogarA da haka? Ke ce ai ya kamata ki lura da halayensa da dabi'unsa, ba jira zaki yi sai wani ya fada maki ba. Ke me kika fahimta a game dashi?" Ilham ta numfasa ta ce da mahaifinta. "to gsky baba nima a yadda na fahimci Ma'aruf mutumin kirki ne. Ni kaina da ban gamsu da halayensa ba, ba zan bashi damar ya riqa xuwa nan gidan ba."
.
Alh. Ayuba ya gyara zama akan kujera ya ce....' "shi kenan idan kin ga yayi maki a rai kina sonshi ni a wajena babu matsala. Wanda kika ce kina so to shi zan baki. Amma abin da bana so shi ne, kada wani abu ya je ya dawo bayan an yi auren nan, ki dawo mani da wani qorafi ko wata maganar daban, ba zan lamunci wannan ba. Shi yasa nace ki tsaya tukuna kada ki yi gaggawa, ki bari sai an dauki lkc mai tsawo, bayan kin fahimceshi sai ki yanke hukuncin da zaki yanke."
.
Ilham ta yi shiru xuwa can ta ce da mahaifinta.
.
"to baba, duk abin da ka ce ba zan iya qetare maganarka ba. amma dai ni tuni na gama yin duk wani tunani da xan yi a game da shi. Sai dai kai idan zaka yi naka binciken akan shi. Don kaima ka tabbatar da hakanl" Alh. Ayuba ya ce. "A'a, bani da wani lkc da zan yi bincike akan wanda kika kawo gidan nan kika ce kina so. Haqqina ne in za6 maki miji na-gari, sbd haka idan ya yi maki. Kin tabbatar mutumin kirki ne, shi kenan sai ki fadi masa ya turo magabatansa su zo a yi magana.
.
.
.
Lp=14%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 14
.
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Sai ki fada masa ya turo magabatansa su zo a yi magana. ni kaina nafi son ki yi auren in dai kin samu miji na-gari." Ilham ta yi shiru a zaune ba ta sake cewa komai ba, Alh. Ayuba ya ce da ita. "iyakar maganar kenan dama, ki tashi ki tafi dakin ki, idan ya zo ki ce da shi nace ina son ya turo magabatansa su zo." dadi da farin ciki suka lulli6e Ilham, ta tashi cikin kunya ta tafi dakinta da sauri. Tana xuwa ta turo qofa ta rufe ta fara tsalle tana muna...me ya fi wannan ranar a rayuwata? Mahaifinta ya amince ya bata wanda take so a xuciyarta.? Ilham ta yi rawa da murna ita kadai a cikin dakinta, sbd sabuwar rayuwa ta zo."
.
Ta rasa duk wani abu da take so a duniya. sai ynx a karo na farko zata fara samun abin da take so a Tarihin rayuwar ta.
.
A ranar Alh. Ayuba ya kira manyan 'ya'yansa uku, Auwal da Mustafa da Jamilu ya ce dasu cikin farin ciki. "Qanwarku ta samu miji zata yi aure." ya saurara sannan ya sake fada masu cewa.
"Yaron nan ne dake xuwa nan gidan, wanda yake (service) din nan. Na bata shi tunda ta ce shi take so, na ce ya turo iyayensa su zo muyi maganar aure. Na kira ku ne don in sanar da ku a matsayin ku na 'yan uwanta."
.
Su dukansu ukun sun san maganar soyayyar Ilham da Ma'aruf. Abin da yasa basu ta6a nuna baqin cikin su ba shi ne, sun san Ma'aruf bashi da komai. Baqo ne a garin, yazo bautar qasa ne kuma bai fara aiki ba." ko suturar arziqi Ma'aruf bashi da ita, sau da yawa mutanen da ya saba dasu a layin suke taimaka masa. Sun tabbatar idan ya auri Ilham a cikin wannan halin da yake, ba qaramar wahala zata sha ba." abin da zata ci ma sai ya gagareta. Wannan labarin da mahaifinsu ya kira su ya sanar dasu ba qaramin abin farin ciki bane a gare su." Auwal ya dubi Mustafa suka gintse dariya. Jamilu ya dubesu yana murmushin qeta. Ya fara yin magana ya ce....'
.
""gsky mutumin nan yana da kirki Baba. Ni dai na yaba da halayensa. Ba wanda ya cancanta a ba Ilham sai shi. Allah Ya sa alheri. Mun yi murna."
.
Auwal ya nuna farin cikinsa a fili ya ce....'
.
"Baba Ma'aruf ai ya kai mutum, kowa yana yabonsa a unguwar nan, tunda ya zo ba a ta6a rabashi da kowa ba yana da haquri' ya san mutuncin mutane. Indai shi Ilham ta za6a to ta sami miji na-gari."
.
Mustafa ya qara da cewa.
.
"Baba da iyayensa sun zo kawai a amshi maganar nan, kada ma a tsaya wani 6ata lkcn yin bincike. Ma'aruf mutumin kirki ne, zai riqe mana qanwarmu da mutunci, indai shi ta za6a da kanta, to muma shi muke so, ya yi mana."
.
Bayan Alh. Ayuba ya gama sauraren ra'ayin 'ya'yansa akan Ma'aruf sai ya ce dasu.
.
"to Alhamdulillah naji dadi sosai bisa haka, sbd kunga wannan yarinyar bata da uwa a gidan nan, kada wani abu ya sameta mutane su ce na zalunceta. To amma tunda kuna ce kuna gamsu da halayen yaron ai babu damuwa, idan magabatansa suka zo sai mu amshi maganar, Allah Ya sa alheri."
.
Su duka ukun suka ce....'
.
"amince Baba."
.
Suka tashi suka fita suka bar mahaifinsu a babban falonsa. Da fitarsu suka qyalqyata dariyar mugunta, suka tafi dakin mahaifiyarsu suka sameta tana cin abinci a zaune. Had. Kubra ta tsaya da cin abincin tana kallo su, kamar masu ta6in hankali.
.
"me ye haka kuka shigo kuna dariya bako sallama?"
.
Mustafa ya sassauta dariyar ya ce da mahaifiyarsu.
.
"wannan sokuwar yarinyar ce wai za a a wa aure. Shi ne Baba ya kira mu ynx yake fada mana."
.
Had. Kubra ta 6ata rai ta ce....'
.
"to shi ne abin ya baku sha'awa, don zata yi aure har kuke murna kuna dariya? Kuna san ko nawa Alhaji zai kashe idan wannan hidimar ta taso? To ina nan zan gani, idan har ya ce zai yi mata wasu kayan daki masu tsada fiye da na 'ya'yana da akayi masu a baya, Wallahi sai na qarqare zaman lfy a nan gidan, zan xuba ido kuma in gani."
.
Mustafa ya ce da mahaifiyarsu
.
"tsaya ki ji mama. Ai ba ta kayan daki ake yi ba." saurayin da Ilham take so bashi da komai. Kawai daga ya zo bautar qasa ta liqe masa, wa ya san ko sai yaushe zai samu aiki? Ynx don mutum yana taqamar yana da digiri a nan qasar, sai ya shekara goma bai samu aiki ba."
.
Haj. Kubra ta saki ranta ce....'
.
"YAUWA 'YAR BANZA! Ai na ji dadi, ta aureshi ya qerata ba ci ba sha, kuma bata isa ta ce zata riqa xuwa nan gidan tana kawo mana matsala ba, ba zan dauka ba."
.
Jamilu ya qara da cewa.
.
"mama ke da kin ganshi zaki san fatara da talauci sun yi mashi kanta a jiki. Idan yana cikin abokanshi ko (Pure water) sai sun sai masa, a haka ne zai iya riqe mata? Shi Baba yana murna ne 'yar lelenshi ta samu miji har yana wani kiranmu. Ki barshi kawai muna nan sai wannan yarinyar ta zama abar tausayi."
.
Haj. Kubra ta yi murmushi ta ce....'
.
"yauwa ai haka ya yi. Ba dai mu ake so a riqa takawa ba ba gidan nan? To ko uwar Ilham tana nan a gidan bata isheni ba ballantana ita wacce nake kallonta a tafin hannun.....
.
.
Lp=15%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 15
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Ballantana ita wacce nake kallonta a tafin hannuna. Da ga ni har ku 'ya'yana mun fi qarfin a takamu a gidan nan, mune gida babu wanda ya isa ya zo ya keta mu."
.
Haj. Kubra da 'ya'yanta suna cike da jin dadin ganin Ilham ta auri mijin sa bashi da komai da .zai bata. Ita kuma Ilham tana cike da jin dadin zata auri mijin da zai bata abin da ta dade tana nema bata samu ba."
.
Soyayya...kyautatawa..qauna...kulawa.
.
.
***
***
*
.
Kamar wasa!
Ilham ta fito gida cike da farin ciki tana murmushi ta samu Ma'aruf a waje yana jiranta. Da xuwanta ta fara fada masa abin da yake yi mata qaiqayi a xuciyarta
.
"Daxu Baba ya kira ni, ya ce in fada maka wai ka turo magabatanka su yi magana."
.
Ma'aruf ya kalleta cikin xumudi.
.
"da gaske kike yi Ilham?"
.
Ta yi dariya cikin kunya.
.
"kaima ai ka san ba zan fadi maka wannan maganar da wasa ba." da gaske nake yi mana. In kuma dama ba sona kake yi da gaske ba a ynx ne zan fahimta."
.
Ma'aruf ya kalleta har cikin idanunta. kallon soyayyar da ya saba yi mata idan suna tare. Ya ce da ita.
.
"bai kamata in yi karambanin fadi maki irin soyayyarki dake a xuciya ta ba, sbd harshe ma ba zai iya jure tsawon lkcn da zan dauka ba wajen fada maki ko ke wace ce a wajena ba." abin da kawai zan iya fada maki shi ne....! Ilham ke ce abin gdy da yabawar da na samu a rayuwata, wacce har in bar duniya, babu sauran wani abu da zan sake samu kwatankwacin ki. Rayuwata gi6i ce ba zata cika ba sai tare da ke Ilham. Idan har na yarda na rasa ki kamar na rasa raina ne....! Ta yaya kuwa zan amince ds gangan in rasa rayuwata Ilham?"
.
Maganar ta bata dariya...maganar ta faranta mata rai sosai. A daren maganar ta riqa tunowa. Ta dauki lkc

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment