Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mai tsawo har qarfe daya na dare bata yi barci ba, tana ta juye-juye ita kadai a kwance akan katifarta. Tana tunanin sai yaushe wannan babban masoyin nata zai zama mijinta su zauna tare?
.
.
Washe gari tunda sassafe Ma'aruf ya shirya ya tafi Matazzu garin iyayensa da kakanninsa. Ya samu mahaifinsa da sauran 'yan uwansa, wadanda duk sanda ya zo gidan ya kawo masu ziyara basu yi masa kyakkyawar tar6a.
.
Da ya fadawa mahaifinsa cewar ya samu aure ne yana so a je a tambayo masa iyayen yarinyar a Katsina, tun kafin ya gama sanar dashi ya ce....'
.
"to ni zaka zo ka fada mata ka samu aure don baka da kunya? Ga 'yan uwana nan kafi qarfin ka je ka same su sai ni' zaka dubi qwayar idona ka yi min rashin kunya. Rashin mutuncin da uwarka ta yi mana a nan gidan, wato ynx kaima ka girma shi ne zaka yi mana ko?"
.
Ma'aruf ya ba mahaifinsa haquri ba don ya yi masa laifin komaI ba." ya san san dama dolene sai ya sha fada da zagi indai zai zo wajen mahaifinsa. Qiyayya da gabar dake a tsakanin mahaifinsa da mahaifiyarsa ita ce ta jawo masa wannan tsanar a gidan su." mahaifiyarsa ta rasu tun yana yaro amma har xuwa ynx da Ma'aruf ya girma, mahaifinsa bai yafe mata ba, sbd tsabar riqo da zafin rai, Ma'aruf ya sake baiwa mahaifinsa haquri. Ya je wajen qannen baban nasa. Ya fada musu abin da yake faruwa. Basu yi masa jayayya ba suka amince zasu je a yi maganar auren. Ma'aruf ya yi masu jagora xuwa Katsina, ya kai su wajen mahaifin Ilham. Ba a tsaya wani 6ata lkc ba." Alh. Ayuba ya ce ya ba Ma'aruf 'yarsa, sannan kuma ya sara masa sadaki naira dubu ashirin.
.
A satin Ma'aruf ya kai kudin auren. A ka tsayar da lkcn biki. Wata biyu masu xuwa. Allah Shi ne Mai rufawa bawan sa asiri akodayaushe. Ma'aruf bai ajiye komai ba, kuma bashi da komai. amma sbd mutuncinsa da kyautatawarsa, da kuma iya zama da mutane, ya yi ta samun gudunmawa a wajen ma'aikatan da yake aikin bautar qasa a ma'aikatarsu. Da sauran mutanen da yake zaune tare dasu a unguwar su Ilham
.
Wadansu suka riqa bashi kudi, wasu turamen zannuwa wasu shaddoji da takalma, wata mata wacce ko sunanta Ma'aruf bai sani ba, a layin ta aiko masa sa sarqoqi masu tsada kala biyar, ta ce a sa a kayan lefe.
.
Ma'aruf ya ce da wanda matar ta aiko, bai san yadda akayi ta sanshi ba, har ta yi masa wannan kyautar. Mutumin da ya kawo masa sarqoqin ya ce....'
.
"Sunanta Haj. Zainab, ta ce tun sanda kazo layin nan duk sanda zata ganka sai ka gaisheta. Shi ne aka bata labarin zaka yi aure."
.
Ma'aruf ya ce ya gode...ya gode. Wani direba dake a kusa da gidan da yake zaune ya aiko masa da babban leshi guda daya. Tun sanda Ma'aruf ya ciro dansa da ya fada a cikin rami ya kawo masa shi har gida, mutumin ya yi alqawarin duk sanda ya samu hali zai yiwa Ma'aruf wani abin alkairi.....
.
.
Lp=16%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 16
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Mutumin ya yi alqawarin duk sanda ya samu hali zai yiwa Ma'aruf abin alheri indai suna tare a unguwar.
.
Ma'aruf ya ce a fada masa shima ya gode, Allah Ya bar qauna a tsakanin sa da duk wadanda suka taimaka masa, manyan abokansa su Khalid mai sayar da kati, suka hada guiwa su hudu, suka ce sun dauki nauyin duk abincin da za a ci a wajen bikin Ma'aruf. suka buga katin gayyata suka rarrabawa mutane.
.
Saura sati daya a daura auren Ma'aruf da Ilham ne ya samu gidan da zasu zauna. Wani attajiri dake a unguwar ne ya bashi gidan haya akan dubu arba'in duk shekara daya. Amma sbd kyakkyawar shaidar da Ma'aruf ya samu a wajen mutane, mai gidan ya ce ya yafe masa na rabin shekara ya zauna kawai, bayan wata shida idan ya samu aiki sai ya fara biyansa.
.
Auren ya yi albarka... Ya yi kwarjini sosai. Abin da Ma'aruf bai ta6a zato ba, bai ta6a tsammani ba." saura kwana uku a daura auren. Manajansu wanda Ma'aruf ya yi aikin bautar qasa a qarqashinsa a babban ofishin hukumar wutar lantarki ya kira shi har ofishin sa. A ranar da abin ya faru an kai sati uku da kammala bautar qasar da Ma'aruf ya yi a wajen su, har ya yi bankwana da su ya tafi.l
.
Manajan ya miqawa Ma'aruf takarda yana dariyar taya murna. Ya ce ya amsa ya karanta ya ga abin da ta qunsa. Ma'aruf ya amsa ya duba, ya dago kai cikin kaduwa da xumudi, ya ce da Manajan
.
"Ranka ya dade wannan ai (Offer) ce....' na samu aiki ne?"
.
Manajan ya gyara zama ya dubi Ma'aruf yana murmushi
.
"qwarai kuwa Ma'aruf, takardar shaidar daukarka aiki ce, daga yau kaima ka zama ma'aikacinmu, ina tayaka farin ciki. Na san ka yi mamaki, don da baka sa ran samun aiki a nan ba." to amma ina so in tabbatar maka da cewa tun xuwanka aikin bautar qasar da ka yi wajen mu, nake ta qoqarin ganin na samar maka aiki sbd kyawawan halayenka da gskyrka. Bamu ta6a zama da mutumin da muke so irin ka ba a wannan ma'aikata tamu, tun wata biyu da suka wuce wannan takardar ta fito, ta maqale ne a wani ofishi, don haka za a baka albashin wata biyu da suka wuce, ko yau kake so za a baka kudin ka."
.
Ma'aruf ya rasa abin da zai cewa Manajan, ya duqar da kai ya fara rusa kuka. Ya samu madogara a daidai lkcn da zata amfaneshi, sauran kwana uku a daura auren Manajan ya ce da Ma'aruf
.
"ba kuka zaka yi ba, ka godewa Allah ne Ma'aruf. An ce halin mutum jarinsa. Kasancewar ka mutum na-gari da kyawawan dabi'unka, su suka jagoranceka ga samun wannan aikin da ka yi, amma kamar yadda zaka gani a jikin wannan takardar ba a nan aka ajiyeka ba, a Malumfashi zaka yi aiki a ofishin mu dake a can, kaga da amarya ta zo sai ku dunguma kawai ku tare a can, ku sha amarcinku tare da sabon aiki."
.
Ma'aruf ya yi murmushi ya share hawayen dake a idonsa. .
.
A ranar ya amshi kudinsa da manaja ya fada masa na albashinsa na wata biyu da suka wuce. Ma'aruf ya qara akwatina uku na aure akan guda dayar da ya saya a baya, ya sayi duk abubuwan da bai saya ba a baya, ya hada kayan lefe cikakku, wanda ko ita kanta Ilham bata yi tsammanin samun su daga wajen Ma'aruf ba."
.
Labari ya watsu a unguwar. Cewar Ma'aruf ya samu aiki ana gab da yin aurensa. Mutane suka yi ta taya shi murna goma da goma. Ga aiki ga amarya. A ranar Ma'aruf ya aika da kayan lefe gidan su Ilham ' an kai kayan kenan an tarasu a dakin haj. Kubra, da Ilham ta shigo ta gansu bata tsaya jiran komai ba sai ta kira Ma'aruf a waya.
.
"ina son ganinka ynxn nan a gida, ka yi sauri ka zo."
.
Ma'ya zo fuskarsa cike da farin ciki, ya samu Ilham a zauren gidan su tana jiran xuwansa.
.
"ya akayi ne amarya? Saurin me kike yi ne da kike ta faman kira na?"
.
Ilham ta ce dashi cikin damuwa.
.
"na fada maka kada ka qure kanka wajen kayan lefe, ma' na san halinka ynx haka sai da ka yiwa kanka qarqaf akan sayen wadann kayan. Ka tuna fa zaman aure zamu yi ba zaman qarya ba. Idan baka bar komai a hannunka ba bayan aure me zamu ci? Gsky zan sa a dawo maka da kayan, ka sayar da guda uku, akwati daya ya isheni na gode, na san kana sona, amma bana so ka sha wahala a kaina."
.
Ma'aruf ya ci gaba da saurarenta yana murmushi. sai da ya ji ta qai qarshe. Sannan ya ce da ita.
.
"nima na gode da tausayina da kike ji Ilham, hakan yana qara mani sonki a xuciyata. Amma a wajen kayan aure bai kamata ki tsaya kina wahalar da kanki kina tausayin muqaddashin Manajan hukumar wutar lantarki a shiyyar qaramar hukuma ba." duk kayayyakin da na saya ban qure kaina ba Ilham kada ki damu. Har ynx ina da sauran kudi a hannuna, kuma sun ishemu kashewa koda bayan biki ne....!
.
Ilham ta kalleshi cikin rashin fahimta.
.
"wane ne muqaddashin Manajan da ka fada mani ynx?"
.
Ma'aruf ya ciro takardar shaidar daukarsa aiki da yazo da ita Ilham ta gani, ya nuna mata sannan ya ce da ita.
.
"na samu aiki a inda nayi (Service) Ilham, sun tura ni ofishinsu dake Malumfashi. Ki fadawa su Baba idan kin shiga gida. Su tayamu murna."
.
Ilham ta tafa hannuwanta ta yi tsalle a gaban Ma'aruf ya na kallonta yana yi mata dariya. Ta daga hannu ta yiwa Allah gdy. Ta garzaya cikin gidansu da gudu don ta fadawa 'yan uwanta da Haj. Kubra su yiwa masoyinta murna ya samu aiki. Mijin da zata aura wanda ake ta cece-kucen bashi da aikin yi, ynx ya samu madogara.
.
Da labarin ya je kunnen Haj. Kubra dama kuma tana cike da baqin cikin baqin cikin akwatuna hudu lefe da Ma'aruf ya turo, sai ta sanar 'ya'yanta halin da ake ciki. Cewar gida babu lfy. A zo a zauna a nemo mafita, don kuwa in aka xubawa Ilham idanu ga alama zata yi nasara akan su." mijin da zata aura wanda ake ta murnar bashi da komai bai wuce ya yi mata akwati daya ba. To ya samu aiki, kuma tun ynx kafin ayi auren har ya fara yi mata sha-tara ta arziqi. A haka za a sa mata ido tana tsalle tana murna ba a yi komai akanta ba?"
.
.
.
Lp=17%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 17
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
(Madugun Taska)
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
A haka za a sa mata ido tana tsalle tana murna a cikin gidan ba za a yi komai ba akan ta?"
.
Mustafa ya ce da mahaifiyarsu a fusace.
.
"ba zai ta6a yiwuwa ba." ba zamu ta6a yarda ayi wannan auren ba." bari mu je mu samu Baba idan ya dawo."
.
Da daddare sanda mahaifinsu Alh. Ayuba ya shigo gidan ne suka same shi a dakinsa su duka ukun, fuskokinsu cike da damuwa qarara. Suka fada masa abin da yake tafe da su." Auwal shi ya fara yin magana a matsayin sa na babban yayansu a gi....
"Baba mun yi kuskuren amincewa da Ma'aruf, wanda qanwarmu Ilham zata aura. Mun yi bincike mun gano tantirin mai neman mata ne, ba zamu yarda a bashi qanwarmu ya je ya kwaso cuta ya sa mata ba, don haka a fasa wannan auren a mayar masa da kayansa kawai."
.
Mustafa ya fadi tashi matsalar kamar zai yi kuka.
.
"bayan wannan ashe yana sata, sai daxu ake liissafo mana mutanen da ya satarwa kaya a unguwar nan. Kuma Baba ka san sata tana bin xuriya, ba zamu yarda qanwarmu ta auri 6arawo, 'ya'yanta su taso suna sace-sace ba, ana cewa 'yar uwarmu ta haifesu. Wannan 6ata suna ne....!"
.
Jamilu ya qara da cewa.
.
"sannan kuma majiya mai qarfi ta tabbatar mana da cewa an ganshi yana shan giya. Idan aka bashi Ilham bamu san abin da zai yi mata ba, kada ya je ya shawo, ya kamata da bugu, ya hallaka mana 'yar uwarmu. Don haka abu mafi alheri shi ne a yi haquri da auren nan, a barta ta samu wani mijin, wanda ya fito daga gidan mutunci ba irin Ma'aruf ba."
.
A karo na farko tun zamanin da aka yi suna kawowa mahaifin su duk wata shawara yana dauka, a wannan karon sai ya taso su da fada kamar zai buge su."
.
Tuntuni kun san da wannan matsalar amma kuka 6oye min baku fada ba, sai ynx da lkcn ya qure saura kwana uku a daura aur? Kuna so ne mutane su zage ni a gari? Kome yake yi dolene a daura wannan auren, kuma kome ya samu Ilham laifinku ne ku da ita, sai da na taraku itama na tuntu6eta in kun san yaron nan ba yaron kirki ba ne kada ku amince da zancen nan. Ku ka ce kun yi bincike mutumin kirki ne, ita ma tace min ta ji ta gani shi take so. Sai ynx zaku zo min da wannan tadin banzan? Ku tafi ku bani wuri sakarkarun banza marasa hankali."
.
Alh. Ayuba ya kore su, suna rige-rigen fita daga dakinsa, suna ji suna gani har ranar daurin aure tazo. Aka daura auren Ilham da Ma'aruf. Baqin ciki kamar ya kashe yayyenta. Ba ma kamar yadda suka ga mutane sun zo sun cika qofar gidansu daga ko'ina. abokan Ma'aruf ne na kusa da na nesa, da wadanda suka yi bautar qasa tare, da malaman makarantar da yake xuwa yana taimakawa a unguwar yana koyar da yaran su."
.
Mutane sun nuna masa kara, sun yi masa halacci, bayan an daura auren ya yi ta gaisawa dasu yana yi masu gdy. Da fatan kowa zai koma gidan sa lfy. Qawayen Ilham suma sun yi mata halacci da kara, sun mutunta bikinta wajen yin anko mai tsada, tare da walimar da suka dauki nauyi a aljihun su." bikin masoya ne wanda ya ba kowa sha'awa.
.
Aka dauki amarya da yamma aka kaita gidan da Ma'aruf ya kama tun sati biyu da suka wuce, kafin ya tsayar da ranar da zai tashi su koma Malumfashi inda zai fara aiki. Ilham ta yiwa yayyenta da mahaifinta bankwana, tana kuka tana roqonsu su yafe mata. Ta durqusa cikin ladabi ta nemi gafarar HaJ. Kubra. ta san ta zalunceta don ba ita ta haifeta ba." ta nuna mata banbanci da qiyayya don ba ita ta haifeta ba, amma ta yafe mata.
.
Ta yafewa duk wanda ya cuceta, kuma har abada babu wanda zata riqe da gaba a xuciyarta. 'Yan uwanta 'yan uwanta ne har abada, haka yayyenta ne....! Kafin a tafi da ita xuwa dakinta Alh. Ayuba da ke yi mata nasiha ta zauna da mijinta lfy ya ce....'
.
"muma mun yafe miki Ilham."
.
Sun zauna da ita tun tana jaririya...tun sanda aka haifeta gashi yau radar da zasu Rabe ta zo." Ilham zata tafi dakin aure. Kwanansu goma kawai a Katsina bayan biki. Ma'aruf ya dauki matarsa suka koma Malumfashi inda zai fara aiki. Burin masoya ya cika! Ilham da Ma'aruf sun zama miji da mata.
.
.
.
*** *** ***
.
.
Babi na hudu
.
.
.
Soyayyarsu bata ragu ba." qaunar da suke yiwa juna tare da matsanancin begen junansu idan basu tare duk suna nan daram a zamantakewar aurensu. Su biyu kawai suke zaune a gidan, idan Ma'aruf zai je aiki da safe sai Ilham ta biyoshi har kusa da waje kamar ta bi shi su tafi tare. Yana so Daga tana qorafin zama a gidan ita kadai, shi kuma yana yi mata dariya. Ya sha fada mata cewar:
.
"idan kika yi haquri wata rana duk wannan kadaicin zai zama tarihi Ilham. Ynx dai gamu mu biyu qwal muke zaune, inda rayuwa wata rana zamu kai mu goma ko ashirin."
.
Idan a zaure ya fada mata haka, idan ta rakoshi zai fita sai ta tsaya a jikin qofar tana hangenshi har ya yield nisa ya bar unguwar, sannan sai ta koma cikin gida.
.
Basu dade da xuwa Malumfashi ba Ilham ta saba da maqwabtansu, ta fara sada xumunci da qawance tare da matan da tazo ta samu a unguwar. Duk inda Ilham ta je da ta zauna zata fara duba agogo.
.
"bari in je gida mijina ya kusa dawowa."
.
Ko gidanta aka zo ba a wani sakewa a zauna a yi hira, sai ta fara maganar mijinta ko kuma ta dauko waya ta kira shi suyi ta hira tana dariya, ta bar baquwarta gingirin a zaune.
.
Wannan ne dalilin da yasa mata suka fara tseguminta suna cewa 'Dadi miji'
.
Da maganar ta dawo kunnen Ilham bata yi fushi ba." abin ma dariya ya riqa bata wai mutane suna jin haushinta ta cika son mijinta. To amma abin ba haka yake ba, Ma'aruf ya zame mata tamkar rumfa a rayuwarta, shi ne yake lulli6eta ta ji bata da sauran wata damuwa. A dalilin samun Ma'aruf ne da tayi a duniya ta ji cewar 'yanchi ya zo mata kamar kowacce mace. Kafin xuwansu Ma'aruf ita baiwa ce, shi ne wanda ya fara 'yanta ta daga cikin qangin bauta, damuwa da takaici. Shi ne wanda ya fara share mata hawayen da ya dade yana sartu a kumatun ta tun shekara da shekaru....tun tana qarama. Ta yaya kuwa zata 6oye jin dadin da Ma'aruf ya zo mata dashi cikin rayuwarta? Me yasa mutane zasu ga laifinta?
.
Farin cikin Ma'aruf bai wuce yaga matarsa tana cikin farin ciki ba." da zarar ta shiga damuwa kowa sai ya sani. Don kuwa Ma'aruf ya gama annashuwa daga lkcn.
.
.
.
.
Lp=18%%% FARIN CIKI SAU DAYA %%%
Page 18
.
Daga alqalamin
Shafi'u Dauda Giwa
.
.
Tare da ni
Abu ihsan Bn ishak
Madugun taska
.
"TASKAR GIDAN LITTAFI" bata amince da daukar shafin ba."
.
Farin cikin Ma'aruf bai wuce yaga matarsa Ilham cikin farin ciki ba." da zarar ta shiga damuwa kowa sai ya sani, don kuwai Ma'aruf ya gama annashuwa daga lkcn
.
A safiyar wata laraba, wata hudu da yin aurensu, Ma'aruf ya shirya zai tafi wajen aiki da safe, Ilham ta dauko farantai da kofuna da suka sha shayi zata wanke su, sai tsautsayi ya ratsa kofi daya ya su6uce mata, ya fada akan qafarta ya fashe ya yanketa a babban dan yatsan qafarta.
.
Ilham ta riqe qafar ta runtse ido, Ma'aruf ya xubar da takardun dake a hannunsa ya rugo ya kamata, ya taimaketa ya zaunar da ita a jikin bango. Inda gilashin ya yanketa ba wani rauni bane mai girma, amma da yake ana zafi jini ya dan xuba sosai a qasa.
.
Ma'aruf ya rude yana yi mata sannu. Jikinsa ba inda ba ya tsima. Tunda suke tare bai ta6a ganin Ilham ta ji rauni ba a Tarihin soyayyarsu sai a wannan karon. Ya shigo daki ya dauki bandeji, Ilham tana zaune tana kallo, tana cije baki don zafi.
.
Sannu Ilham, ki yi haquri .... Sannu Ilham."
.
Ya nannade mata dan yatsan yana bata haquri kamar qaramar yarinya. Yana nan tare da ita yana rarrashinta ne Manajan sa ya kira shi a waya. Taro zasu yi akan matsalar rashin wuta da mutane suke ta qorafi a garin, shi ake ta jira tuni kowa ya zo." duk ma'aikatan dake ofishin su sun hallara, an gayyaci masu gari da 'yan kasuwa da qungiyoyin matasa, wadanda suka kawo kuka a ofishin wutar lantarki. Manajan ya ce da Ma'aruf a waya.
.
"kai fa muke jira tun daxu Ma'aruf. Zaman me kake yi yi a gida tun daxu har ynx baka zo ba?"
.
Ma'aruf ya ce da shi murya na rawa.
.
"ba lfy manaja. Matata ce ta ji ciwo ynxn nan, bana jin zan iya xuwa wajen aiki yau, a gafarceni:"
.
Manajan ya ce....'
.
"Tana wane asibitin ne?"
.
Ma'aruf ya ce da shi.
.
"Ynxn dai muna gida tukunna' ina nan tare da ita."
.
Manajan ya kashe wayar ya dubi mutanen da suka halarci taron a can ofishin sa ya ce da su."
.
"jama'a da sauran ma'aikatan mu ina so a yi mana afuwa zamu daga wannan taron da zamu yi sai xuwa gobe ' sbd matar muqaddashina tana can bata da lfy, ynx nima zan je in ga ko a wane hali take ciki, don a yadda naji muryarsa da muka yi waya ynx lallai abin ba qarami ba ne' yana buqatar a tallafa masa."
.
Sauran mutane suka nuna damuwarsu, suka yi addu'ar Allah Ya bata lfy. Manajan ya tashi ne sai kowa ya ce zai bi shi su je a jajantawa mal. Ma'aruf, tunda dai ana tare, kuma da ace lfy da ynx haka yana nan tare da su a ofishin
.
Tawagar masu xuwa duba wacce bata da lfy suka dungumo ayari kusan mutum talatin. Duk mahalarta taron, da sauran ma'aikatan dake a ofishin su ba wanda aka bari a baya, tunda ance matarsa tana cikin wani hali da ba a sani ba."
.
Da xuwansu gidan, manaja ya shiga kai tsaye tunda larura ce, sauran mutanen suka tsaya a waje. Da ya shiga gidan ne ya samu Ma'aruf a zaune a falo tare da matarsa Ilham sun kallo fuskarsu cike da annashuwa ya dauki qafarta ya dora a jikinsa, don ji sauqin zogin raunin da ta ji.
.
Manaja ya yi masu sallama ya tsaya daga bakin qofar falon, Ma'aruf ya yi saurin amsawa, ya dauke qafar Ilham ya ajiye ta akan kujerar ya tarbi manajansa, wanda ya yi tsaye yana kallon abin mamakin da ya zo ya tarar. Ya yi zaton zai zo ya ga Ilham a kwance bata ko iya motsawa don a yadda Ma'aruf yake magana a waya, muryarsa cike da damuwa. Wani in ya ji sai ya rantse mutuwa aka yi masa.
.
Ilham ta yiwa manaja sannu da xuwa ya amsa.
.
"ya jikin naki?"
.
Ta ce
.
"da sauqi na gode."
.
Manaja ya girgiza kai cikin mamakin abin da yake damun wadann ma'aurata. Suka fita waje shi da Ma'aruf, suka tsaya a cikin falon, Ma'aruf ya bashi hannu suka gaisa. Manaja ya tambayeshi
.
"ka ce matarka bata da lfy, amma naga gata nan a zaune tana kallo' har ta warke ne?"
.
Ma'aruf ya ce da manajansa.
.
"gilashi ne ya yanketa a qafa, na tausaya mata don ba ka ga yadda jini ya riqa xuba a qafarta ba." na tausaya mata matuqa, ina so ne ta huta anjima mu je asibiti a duba qafar a gani."
.
Manaja ya kalli Ma'aruf sosai, ya tabbatar abin da yake fada masa har cikin xuciyarsa. Sbd takaici bai ce dashi komai ba, bai ce da shi yazo da tawagar mutane suna waje ba sun zo dubiyar matarsa. Ya sa kai ya juya ya fita ya bar gidan, ya ba mutanen da yazo dasu haquri, tare da sauran abokan aikinsu, ya ce ba kowa a gidan, Ma'aruf ya fita kaita asibiti idan an samu lkc zai je ya dubata. Ya janye mutanen suka koma da sauri don kada wani ya san gskyr abin da ya faru su ji kunya.
.
Sai da manaja ya koma gida ne ya fara bambami yana fadawa matarsa abin da ya faru.
.
"in banda shashanci don kawai matarsa ta yanke da gilashi zai qi xuwa aiki, a yatsanta fa ta ji raunin, ko qaramin yaro awannan ciwon ba zai hana shi yin komai ba, amma shi ga mai mata ya sa ta a gaba sun zauna a falo yana jinyar qafarta. Kai wannan sakarci na Ma'aruf Allah Ya raba mu dashi. "
.
Matar manaja ta yi dariya sosa, ta ce da mijinta.
.
"kada ka ga laifinsa don ya nuna mata irin wannan soyayyar. A irin son da Ilham take yi masa ko rabi bai nuna mata ba, ka bari wata rana tazo gidan nan idan kana ka ji da kunnenka, da wahala ta yi minti goma bata kira mijinta ta ji halin da yake ciki ba, koda a gida ta baro shi kuwa. Haka suke shi da ita, itama haka muke yi mata wannan tsiyar."
.
Manaja ya girgiza kai cikin mamaki' tun sanda Ma'aruf ya fara aiki tare da su, bai ta6a sanin wannan sirrin ba sai a ranar da wannan al'amarin ya faru. Tunanin da manaja ya fara yi a xuciyar shi shi ne....!
.
Ya wadann ma'auratan zasu kasance idan mutuwa ta dauke daya ta bar dayansu? Babu shakka faruwar hakan zai zama babban abin tausayin da ba a saba gani ba."
.
.
.
***
.
.
Zo mu zauna' zo mu sa6a, kamar yadda masu iya magana suke cewa.kamar a mafarki duk da gagarumar soyayyar dake tsakaninsu sai da wata shu'umar bazawara ta so ta shiga tsakaninsu. Hakan ya faru ne bayan kusan kimanin shekara daya da yin aurensu, a lkcn Ilham tana da cikin 'yarsu Khairat, wanda ya kai wata shida. Haka kawai wata bazawara ta qwallafa ranta akan Ma'aruf, daga kawai suna sayen naman kaji a wajenta, a can inda take kai talla a wajen aikinsu.
.
Ta riqa kiran Ma'aruf a waya babu dare babu rana, tun Ilham bata sani ba har ta san abin da yake faruwa. Ma'aruf bai san Ilham tana da zazzafan kishinsa ba sai a ranar da bazawarar ta turo masa da wani saqo ta wayarsa. Tana fada masa cewar kada ya ji komai zata iya zama da matarsa lfy, kuma ba sai ya yi mata wasu kaya ba, kome Allah Ya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment