Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

keda Girki,.Amma ita a
dole dauki ko Girki batai ba,. Tun alhamis ta soya kajin ta,tana tashi ta hau
pape chicken,,Ta zuba katon flaks,,ta shirya cikin wani purple da ratsin pink
din Swiss less,. Taci make up kamar mai shirin zuwa zaben Miss Universe,,Sun
fito,fir Zahra tace bazai hau saman ba,Ya mata waya ta sakko,,.Takun ta ya fara
ji,Tuni ya zubawa stairs din ido,,harda mike wa, Rabon shi da ganin ta tun jiya
da dare,,.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
®ONLINE HAUSA WRITER'S.
BARIKI...IYAWA
54_Wannan k'ayataccen Murmushi ta sau mishi,,taku take sannu a hankali, tamkar
Tausayin Carpet din, Zahra ta dalla mata harara tare da kau da kai daga kallon
ta,Zuwa yai ya karbi kwandon hannun nata,ba musu ta bashi,ta gyara gyalen ta
tana kallon Zahra,mudin bata gaida ta ba toh sai dai su zauna haka,tai Murmushi,
"Ina kwana sis?Ba tare da ta kalle ta ba tace" Lafiya, ta kallo mutumin nata,da
kawai Murmushi yake, sosai yana yabawa Sa'a ta ko'ina,bata da girman kai,bata
la'akari da itace uwar gida,tsawan zaman su bai taba ga Zahra ta gaida ta ba,sai
dai ita ta gaishe ta,ba gajiya wa... shi yasa take kara shiga ranshi,,.Zahra tai
gaba,,yana ganin haka yai saurin zuwa gare ta,, Taja baya tana murmushi,, "Ina
kwana daga nesa,,Ya harare ta," Bana amsawa,,Dama dazu ma ina kule dake,kinsan
zan zo kika kulle kofar ki ta ciki koh??Tai Murmushi, "So sorry,,yanzu dai muje
kaga sis ta fita,,Ya kara hararar ta kan yai waje,,Suna zuwa ya danna Remote
motan ya bude,,Da sauri Zahra tai gaba tare da bude gaba,Sa'a tai Murmushi,,
Hafeez Yace" Uwar gida ke zama a gaba Zahra,,Ta kalle shi ta watsar,,"Kai ka
Santa,,nidai ba mai fitar ni nan,,Zai magana Sa'a ta Riga shi,, "No,Nama fi son
Baya Habeebi,,Sis ce ai,,No worry,,Sai ta zaga kofar gefen da zai na ganin ta ta
mirror, ita ai baya zai fiye Mata gaba,yadda zata kara bata haushi,.Da sauri ya
bude mata,,ta shiga,ya rufe,yasa kwandon a boot,kan ya shiga,aka bude mishi gate
ya fice,,Sai da ya tsaya,ya kwa saita mirrorn saitin ta,,Suna hada ido ta kashe
mishi ido d'aya,, yai murmushi,,.
Tafe suke cikin nishadi,Zahra sai kokarin tusa magana take,ganin yana murmushi
yasa ta dage,chan dai ta kula,Ashe fa sai ya kalli mirror yake murmushin,,ta

juyo baya a fusace,,Dai dai Sa'an tana mishi fari da ido kai a langwabe., suna
hada ido da Zahra ta yage mata baki,,Ta harare ta sauke kan Hafeez dake kallon
hanya kamar bai ba,,.
Da sallama Suka shiga,Da gudu Tasleem ta fito,ta kama hannun su, Zahra ta zame,"
Ni kauce min,ina Hajiya?,Sai kwa tai kan Sa'a ta kan kamo ta,, Sai ga nan
Hajiyan sun fito da Zahra daga kitchen da fara'ar ta, Sa'a na ganin ta ta maida
gyalen ta saman kai tana murmushi,,Ta zauna,Zahra ma ta zauna,yayin da Sa'an tai
kasa cikin girma mawa tana gaida ta,, da fara'a ta amsa,Hafeez ma yadan zamo
yana gaida ta,. Suna haka Abba ya sakko,.Shima fara'a fal fuskar shi,, Tuni Sa'a
ta kara dukar da kanta kasa,,Suka gaida shi,,.Suka dan taba fira dasu,Yace
Hafeez yazo zai bashi sako Suka fita,,.Hajiyan ta tashi ta koma kitchen, Sa'a
tace Tasleem ta dakko kwandon suje kitchen din,ta cire gyale ta ninke tare da
daura wa a kan jakar ta..Zahra ta tabe baki tare da gyara zama tana sauya
tasha,,.
Hajiyan ta dago,Tasleem tace"Gashi inji Aunty Sa'a,ta ajiye kwandon, Hajiya ta
kallo Sa'a, "Bakya gajiya kekam,,Tai murmushi tare da zuwa ta karbi muciyar," A
haba daga zuwa Baku ko huta ba??basshi Yan nan,na ma kusa,"A ba komai,zamu
karasa da Tasleem, Ta kada kai, " Toh,Allah dai ya muku albarka, Tace"Amin,,ta
fita a kitchen,Tasleem ta kan kamo ta "Kinji yadda kullum kika kawo abinci yadda
Hajiyan Mu ke yabon ki kuwa?.kai Aunty u r amazing,. Suka sa dariya,,Tace" Miyar
mey za ai??Tace"Miyar kubewa,,Ta kada kai, ta taimaka mata da bude Leda,,Ita
kuma tana kan kare kubewa,,Ta kunna dayan Gas din,.Ta daura ruwa,ta yanka albasa
ta zuba maggi,,Tasleem duk tana kallon ta,, ta sa Curry a tafasshen ruwan,Tana
gama gurza kubewar ta zuba aciki,,kubewar tai kyau da ita,,Ta kallo ta "Fadi kar
ta shake ki,tai Murmushi," No naga Taki miyar special, kawai albasa da maggi
kika sa,"zaki ce min baki taba gani ba,.tai Murmushi "yanxu dai na rike,.amma
haka za'a ci??Ta girgiza mata kai,tare da nuna mata flasks din" Da wannan za'a
ci,.kan 12 da wani abu sun kusa gama wa,,lekowar Hajiyan biyu,,.
Suna daki ita da Zahra, kara take kaiwa,akan yau Wai girkin tane Amma Sa'a ta
dafo abincin fi'ili,,.Ta kalle ta Hajiyan kan tai Murmushi,, "Ni Zahra na rasa
yaushe kika sauya?.Yanzu kiga fa,ina aiki daga zuwan Ku ta karba,,amma ke kinyi
zaman ki,Kar ki bari ta fiki kirki fa.
Ji tai an ruko kugun ta ta baya,ta juyo,ko Tasleem ce,sai ganin Tasleem din tai
ta fice sai Ogan ta,,Ta dan harare shi, "Sannu,nazo Taya ki ne,Tai Murmushi," Ai
ma mun gama,,Ni dai sakan ni ko ka manta inda muke?.Ya kara kan kamo
ta,,tace"Allah fa zan sa ma ihu,,Ya fara mata chakulkuli,,Tuni ta hau
dariya,.Shi ya Taya ta har tai wanke wanke Suka fito,.Tasleem ce kawai a
parlourn, nan Suka zauna su Zahra Suka fito,.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
®ONLINE HAUSA WRITER'S.
[10/2, 7:43 AM] Feenat Ja'afar: [1/25, 1:20 PM] Feenat Ja'afarBARIKI...IYAWA
55_Bayan sun gama firar Su gidan su Zahra Suka sauka,,Dakin auntyn su Suka fara
sauka,kan sukai wajen mamy,, Ta tarbe su da fara'ar su,,Sa'a kawai kallon ta
take,Mace ce mai waye wa,tasha boko,sannan daga ganin ta "Allura batai halin
ruwa ba,dan ba nuna Zahra ta'ta ce,,a yadda Mamyn ta kula itama Sa'an zatai
saukin kai,duk da yar tata na complain akan zaman su,wanda dama tasan a
Rina,,Sa'a ta fito da Chocolate na coconut parket d'aya ta bawa yaran k'annen
Zahra,,Mamy tai murmushi,a dan zaman da sukai ta gano Sa'a tafi Zahra sanin
siyasar Duniya,, Domin har wajen da yara Suka bata da ledar chocolate din Sa'an
ta share,,Lalle yarta keda gyara a gaban ta,,.Lokacin da zata shiga bandaki
alwala, akwai dan gidan Auntyn su Zahran a foo, Yace Mamyn shi ya gama,,Sa'a ta
kallo shi,," Tashi toh na wanke ma,,haka ta wanke mishi ta shiga da foo in
bandaki,,kwarai mamy da kishiyar ta sun ji dadi,.sai murmushi suke,.Sa'a kam yar
siyasa ce,,.
Gidan Aunty Maryam Suka sauka,,da sallama Suka shiga,,Habeeb yana mota a
parlourn, yana ganin su ya taho da gudu gun Sa'a,, Hafeez har mamakin sabon shi

da Sa'an yake,Da sauri ta ware mishi hannu," Oyoyo Habebee nah,,Aunty Maryam ta
fito tana musu dariya,,Sabanin Zahra da ba yabo ba fallasa,,Suka zazzauna,Hafeez
yana"Sister kodai zaki bamu Habib ne??Tai murmushi tana kallon Sa'a,, Mai D'a
wawa ne,indai zaka so nashi,toh zai so ka,, "Wa zai Iya da kiriniyar Habib
Bros?? Sa'a tace " Mukam a bamu,zamu Iya,ko Habeebe??Ya daga mata kai,, Nan Suka
gaisa,,yaran ta suka zo,kai Familyn Hafeez sun mata,kowa ka gani da fara'ar shi,
a zaton ta bazata samu tarbar nan a wajen su ba,ganin yadda akai kan tazo
gidan,amma da mamakin ta kowa yana maraba da ita yanzu,,.Yadda take son Hafeez,
dole taso Familyn shi,shi yasa a siyasan ce take siye su,.Da zasu tafi Tace su
biya zatai ma su Fodio siyayya,Yaji dadi kwarai,dan bai kawo wata siyayya a
ranshi ba,,Tasan tsofi akwai son Turaruka,.Nan ta jidar musu,Drinks ne,da sauran
kayan tsaraba,. Zahra har abin ya daina bata haushi,mamaki ya dawo bata,,wato
tana nufin ta ma fisu son dangin nasu ko mai??
Biyar Suka yada zango a Family House din su,su Fodio yai murna da ganin iyalin
Hafeez din, Kowa ba nuna waraki ya tarbe su,,Nan Suka yada zango,ta zage tare da
sakin jikin ta dasu,,Kakar su Hafeez kadai ta rage,Itama duk ta tafi,,.kwarai
sunji dadin tsarabar,duk da dama Hafeez din yana kyautata musu ta bangaren
sutura,da dan abun masarufi,,Yara suna ta murnar chocolate,.
Sai bayan Isha'i Suka nufo gida,Fir zahra taki zaman Gaba,har dariya abin ya
bawa Hafeez,.
Da mamakin Sa'a taga sun baude, Layin su ya dauka,Dan murna harda rukun kume
shi,.
By
Feenat Ja'afar
56_Da murnar ta ta Dane Maman,lokacin Baba ya dawo,,Ta dawo kan Baba,Sai dariya
suke mata da Hafeez, Tuni shagwaba ta dawo,,kan ta tashi ta dakko ma su Zahra
ruwa bayan sun gaisa,,. Basu Suka je gida ba sai 10,,a jabe Zahra ta zube a
parlourn,, Sa'a tai musu sai da safe,ta haye sama,,banta yai da kallo,kan ya
shiga dakin Zahran, itama binshi tai,yai wanka,dan lokacin zafi ne duk ya
takura,yana fitowa itama ta shiga,, yai murmushi, Sa'a, Sa'an shi, da itace toh
da tare zasu shiga,,Saman yai,lokacin tana parlourn, daga ita sai towel halamar
daga wanka ta fito,chargy take jona wa ganin NEPA,,yai murmushi, tana ganin shi
Ta sau mishi murmushi,, kamar jira yake ya karasa,.ajiyar zuciya ya saukar,idon
shi lumshe,, Sa'a itace nutsuwar ruhin sa,,idan tana kusa yakan manta komai,sai
yai da gaske ko ta nusar shi yake Iya kaman ta adalci,, yanzun ma ji tai kidan
na Neman sauya wa,,da sauri ta mai chakulkuli ya sau ta,, Ta Matsa baya,,"Good
Night,. Kai ya kada mata, sai ya bata tausayi,,Ta matso tare da riko hannun shi,
har wajen glass din ta rako shi,.Tamkar wani marayu haka Suka rabu,.Ko kadan
bata son shiga hakkin Zahra.
"Amma ya Hafeez kana sane da rashin adalcin da kake mun ina hakuri koh??Ya
kallo," Da nai mey kuma??sarauniyar yan complain? Naga randa girkin ki zai
tsaya,ba tare da kin kawo Suka ba,Tuni ta kara kuluwa harda hawaye,,"Ni in
girkin ta ne a sharp sharp kai min sai da safe ka fice,amma in nawa ne,toh fa in
ka hau sama sai na ganka,,.Ya girgiza kai., kan ya gyara pillow,, kwanciyar shi
yai,ta kara kuluwa kuwa,''Dama nasan ni Matar tushe ce,kullum ni ke laifi,yar
goal din taka bata yi,,Ya juyo,,"Yanzu toh mey kike so ayi??Tai mishi banza tana
ci gaba da kukan ta,,. "Na Sani,Allah ne ya dauran son ka,amma at least ka nunan
ko kan kani kana yi dani ma da dadi,,yai shiru, ," Zahra problem, yaga ranar da
zai zo dakin ta bata bashi sukar Sa'a ba,,dole Sa'a tana birge shi,dan fin wata
kenan,amma bata taba kawo mishi sukar Zahra ko kara ba,asali ma sai dai ta
tunasar shi adalci a tsakani,,sannan yasan indai so ne!toh Sa'a tafi Zahra son
shi, don tana komai dan faran ta mishi,matukar bai saba wa shari'a ba..
Ya sauke ajiyar zuciya, jawo ta yai,,"Toh shikenan, yanzu ki bar kukan,.Nima ina
son mata na duka Sweet Zahra,. Tuni ta fara murmushi,, a hankali da dan guntun
salon ta ta tafiyar dashi,Sai dai shi abinda ke daure mishi kai, duk tsiwar nan
ta Zahra a fagen nan kunya take,komai a kunya ce,ita ba'a sabo da ita,duk da
bata da makusa,,amma Sa'a ta daban ce,,.Yau kam tashin farin ciki akai,tun asuba
ta gaida shi,ita a dole ta samo kan Hafeez,, tai break, tare da taimakon

shi,.Bayan sun gama yai sama kiran Sa'a, nan fa ta fara cika tana batse wa,,ita
kam mey zatai wa Hafeez ya dau lokaci ba tare da ya tuna hawa saman Sa'a
ba??,koda Suka sakko tare da Sa'an yai mamakin sauya war Zahran, dan ana wasa ya
barta ya hau saman,ya girgiza kai, Zahra? Sai a barta,,.
Kamar kullum, yauma Sa'a ta gaida ta, a dakile ta amsa,Kan ta hau hada ma Hafeez
tea,,Yau da matukar farin ciki ya tashi,,dan yau kam,yasan sai kwanan saman
Sa'a, tana kula dashi,,kujerar shi na facing ta Sa'an, yayin da Zahran ta zauna
gefen shi,,Cokali take juya wa a tea in data hada,lokaci lokaci takan dan kalle
shi,, kamar mai jin kunyar shi kuma sai ta dukar da kai tana Murmushi, Sa'a mai
dubun salo,yau kuma da salon kunya ta motsa da rashin son magana,,.Ta kai Cup
bakin ta taji yana mata tafiyar tsutsa a K'afa,,ta kalle shi tai Murmushi tare
da dukar da kai,,Kafar shi ya matsar gefe,da zummar in ta kawo tata ta rasa,dan
yasan zata rama,,Ai kwa kamar ya Sani,,Kurbar tea Zahra take,,taji wani salo ana
mata a kafar data mike ta,Tuni ta kware lokacin da ta gane mai mata,Dan taga
lokacin da ta kanne mishi ido,,a zabure ta mike cike da masifa,"Nifa ban son
karuwan ci!ehee,in banda jaraba ki bari yau Ai zai dawo gare ki,sai ki cinye shi
danye ma.Da sauri Sa'a ta gintse dariyar ta, "Kai sis.,ban fa kula ba,,ta wani
marai rai ce mata harda langwabe kai gefe,,",mtsww.. Taja dogon tsaki" kyaji
dashi dai,,.Ta ture kujerar ta basu waje..Tana shiga daki Suka fasa dariya...Da
sauri ya taso ya dawo kan plate din ta,,Sai da sukai mai Isar su tukun Tace
"Amma fa baka kyauta ba,,Yanzu da ta rufe ni da duka fa???Ya kara tuntsura
dariya," Allah bansan ta kawo kafar ta ba...Ta dan harare shi, "wataran ina ga
sai kasa Zahra tamin lilis a gidan nan,I swear na tsorata,.kuma kai kaja, da
akan ka zan rama.. Yai Murmushi tare da ruko hannun ta,," Ada!.Ta zuba mishi
ido..ido cikin ido suke kallon juna,sai dai takan dan lumshe nata,sun kai a kala
5mints,kan daga bisani ta kalle shi, kamar hadin baki su furta wa juna "I Love
you,,..Suka sake kallon juna,Sai kuma abin ya basu dariya.,Ta kan kamo shi,"
Love you too sweetheart... Ya sauke ajiyar zuciya,,.
Zahra da ta fito ta sake komawa, gado ta fada,ta fara rera kuka,,"Mai Sa'a ta
fita ne a rayuwa??..
Kyau??Tasan bazata gwada mata shi ba,,..diri fa?? Sai dai ta fita kauri da cikar
muzauna,,Gashi tana da dai dai gwargwado,, tana kitso duk bayan sati,sabanin
Sa'a, da sai dai tai wash and set,,.tana kokari sosai ganin itama tana
kwalliya,,.Ance mata yan BARIKI akwai su da gyara kodan su kwace maka Miji,Toh
tasan a bayan auran su kadai kudin data kashe dan ta gyara kanta ba kadan
bane,kuma ko yau Jummai tazo da sabon da zata kawo mata,,Amma Sa'a fa,tun zuwan
su in banda Ummi da tai zuwa 2,toh bata taba ganin wata Qawa tazo mata ba,,..Toh
meye sirrin da Sa'a take da wanda ita batta dashi???Tai tunanin har ta kare bata
Gano da mey ta Gaza ba..Zahra kenan...Duba da kyau dai,am sure akwai su...
Bude kofa taji,ta juya,Hafeez ne tsaye,tashi tai tare da goge idon ta,, amma a
ranta tana wallahi Sa'a zata biya bashin nan na yau..
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[1/25, 7:08 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
57_Zama yai rarrashi, murmushi kawai take mai,wanda na mugun ta ne,,abin yi
zuciya ta raya mata,,Kallon ta yake shikam da mamaki,dan yasan da a da ne,da
Tuni Zahra ta fara complain, amma yau Murmushi take mai,,Shima sai yai murmushi,
"Zan tafi office, 9 tayi,Ta kada mishi kai,," A dawo lafiya,,.Shima ya kada kai,
Ya tashi,.ganin batta niyar tashi yasa ya girgiza kai,, Allah sarki Sa'an shi,
da yanzu itace tana manne dashi da yar shagwabar na Kar ya jima,,sannan ya kula
mata da kanshi kamar tana gani,,..Yai Murmushi har hakwaran shi Suka fito,kan
yai waje..
Yana mai daukin dare yayi yakai ga Unique din shi..
Washegari Bayan ta sallame shi ta koma sama dan ramakon baccin ta..Zahra najin
shiru,ta shiga kitchen ta hada miyar Tankwar ta,attarugu zallah,tana yi tana

dariyar mugun ta,tana gamawa ta zauna a parlour tare da daura K'afa d'aya kan
d'aya, jira take Sa'a kawai ta sakko da abinci,,ita kuma ta sau mata Bom din ta
ciki,.Da mamakin ta har 12 bata ji motsin Sa'an ba,.Tashi tai ta hau saman da
zummar tada ta..
Mafarki take Wai Hafeez na sabe da ita a baya suna kewaye parlour suna dariya,.
Murmushin take dirka wa a baiyyane,taji ana buga mata glass,,.
A firgice ta tashi tare da kallon agogo,, "Subhanallah,,past 12??..Da sauri tai
kofar,,Zahra ce,da mamakin ta tana Murmushi,," Sis,naji shiru ne,shine nace ko
bacci ya dauke ki hala,,tai Murmushi,. "Wallahi kuwa,nagode kwarai sis..Ta juya
kasa tana murmushi,, Sa'an ta bita da kallo,,kawai sai taji bata yadda da
murmushin nan na Zahra ba,dan tsawan zaman su sai dai tai wa mijin ta, ita kwa
sai dai ta bita da harara,,ta dai kada kai,ta shiga kitchen a gurguje, Allah ya
sota ta dafa markade,.
Tasan Gogan ta bai fiya son k'yali a abinci ba,shidai basshi a shinkafa, saboda
haka cikin gaggawa ta daura,ta hau soya miya,duk ta manta da wayan ta dake a
kashe da zata kwanta,.Yi take tana kallon agogo,,1pm yake dawo wa gida,ga indai
ya kwaso yunwa,toh fa tanan ake fada dashi,dan shi Sam baya jimirin yunwa da
yaji a abinci,yanzu za'a ji kanku dashi,dake ita tasan abinta Shi yasa take
karewa,, a kalla in tai latti bata gama abincin rana ba takai 1,Shima kan Ya
koma bakin aiki ne,.
1 da 20 ta sakko ta ajiye flasks dinta,har Zahra na mata sannu,,.
Komawa tai ta fara yanka cabbage da zata hada cous low,da mamakin ta shiru
Hafeez bai zo ba,har 2 na Neman yi,,kan ta gurza karas tai wajen wayan ta, kai
ta dafe,kan tai saurin kunna wayan,.Tamkar wanda ake jira sai ga kira ya
shigo,tai kitchen tana receiving,,.
"Am sorry,aiki ya kachamen,kasan kana raina,,.Yai ajiyar zuciya," na aza kin
manta ni ne?? Tai murmushi, "Da kuwa na manta kaina ma Baby,,.u know u r
special.. Yai Murmushi n jin dadi,,kan ya fara sanar ta Ya kai sako ne,sai Fodio
ya kira shi,amma Gashi nan,dan duk yunwa ta rarake mishi ciki..
Bayan sunyi sallama da gaggawa ta tattare komai,tabar cous lown takai daga
baya,,Wanka ta shiga,dan sai zufa take tai komai cikin sauri.
Zahra na ganin hawar ta tai saurin shiga kitchen,, leke take,tamkar wata muna
fuka, ta juye kusan Rabin Miyar Tankwar a miyar Sa'a, ta juya,Tuni ta hade kamar
ba'a zuba ba,da gudu ta koma kitchen har tana tun tube,,
Ta dawo Taji kamshin miyar data bude ta cika parlourn, da sauri ta dakko
freshener ta hau fesa wa,.Kallon Dining din take tana wata shu'umar dariya,,ta
kalli agogo,2:09,tasan duk inda Hafeez yake iyanzun yunwa ta ciwo shi,. Ta tuna
randa ya fara fita office datai lattin abinci ya yai mata,tamkar ya rufe ta da
duka,dan Hajiya tasha fada mata Hafeez baya jimirin yunwa,,akwai lokacin da yaji
ya zarce mata a miya,da bai ci abincin nan ba,kwana 2 yai basu dai dai ta
ba...Tai murmushin mugun ta..." Sa'adatu Yau sai Buzun ki a gidan nan,,. Zan ga
karyar BARIKIN yau.,Kai Kila ma ya kifa mata mari yadda yai lattin nan,tadan
doka tsallen murna,,Daki ta koma,tai alwala Ta hau make up..sai kuma jiran zuwan
Hafeez.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
®ONLINE HAUSA WRITER'S.
[10/2, 7:50 AM] Feenat Ja'afar: [1/26, 7:36 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
58_Da Sallama ya shigo,duk din su suna parlour, Kallo suke,sai dai duk hankalin
su ba'a Kallon yake ba,kowacce da abun da ke ranta,,duk da kowacce murmushi ke
kwance a fuskar ta,,. Ba karamin dadin ganin su yai a haka ba,,da dan gudu gudu
Sa'a ta taro shi,,.Zahra ma ta tashi,.da yar dariyar da take kunshe wa,"Sannu da
zuwa,,Ya daga mata kai,"yauwa, ya gida,.tai daki,dariya take dillikawa,nan da
yan mintina zata ji kan su,,.

Ba'ai 10mints ba Suka sakko,,Manne take a kafadar shi, tana jin su ta
fito,sabanin D'a da sai a an kira ta tana yanga,,.
Kujerar Sa'a ta ja mishi,ganin yau suna dasawa da Zahran yasa ta barshi yaci da
kanshi,,Tai serving kowa ta tura ma Zahra,,ta bashi nashi tana Murmushi, ja
yai,zai fara aka kira wayan shi,Zahra ta danne cokali,, da jin haushin wanda yai
kiran,,.
Sa'an ta zuba mishi ido,, a fada fada yake wayan,ta kuma San yunwa ne,, sai da
taga ya ajiye wayan Kan ta dau cokali d'aya bakin ta...
Da sauri ta rintse ido, dan jin wani azababben yaji da ya ziyar ci kwakwalwar
ta..da sauri ta bude ido, dan tunawa da yanxu Hafeez zai kai tashi lomar shi,ta
kuma San halin shi akan "Y'aji," baya son Y'aji a abin,,,.Sai dai ina ta
makaro,dan har Ya kaita,Furzar da abincin yai,yama rasa ina zai sa bakin shi
yaji dadi,.. batai wata wata ba tai wajen shi tare da saurin tallafar kanshi ta
hau kan dining table din ta zauna,,shishitu ya fara,idon nan Tuni har sun kada
dan azabar attarugu,,in banda kunshe dariya babu abinda Zahra take,,yau
daya,tasan sai buzun Sa'a,, dan tasan sarai bai son Y'aji,sannan gwani ne wajen
Iya masifa akan yunwa inta ciwo shi,sai dai da mamakin ta, sai ganin Sa'a tai
itama tana shshitu cikin marai rai ce fuska,,fadi take"Am so sorry Baby tana
hura mishi bakin halamar yajin ya huce,,.Zumbur Zahra ta mike,sakamakon ganin
Sa'a ta hada bakin Hafeez da nata,,Saida ta tabbatar ta kauda duk wani yaji kan
ta dago,shikwa gogan abin nema ya samu,tuni ya manta da wani yaji yahau mata
murmushi,, abincin ta jawo,sai ta dan matsar da miyar,ta kara cous lown,da
plantain din ta cigaba da bashi,,duk loma daya saita manna mishi kiss,,Ina,Zahra
har ta fara zufa dan ganin Ajab,, bashi take yana murmushi,, ita kwa sai aikin
ta take,,cokalin hannun ta ta buga akan flate din nata,,da gudu tai daki tana
kunshe kuka,,duk Sa'a na kula da ita,,.
Sassayan ajiyar zuciya ta sauke,ganin ta tsallake rijiya da baya da kyar..Sauka
tai zata tafi ya ruko hannun ta yana langwabe kai gefe,sai kace irin qananan
yaran nan"Ban koshi ba?,,Tai ajiyar zuciya kan ta kakalo murmushi,,shikwa yadda
take mishi ne bai son ta daina,,.Saida ta tabbatar ya koshi,kan ta sauka ta je
fridge tana mai gode wa Allah,, tabbas tasan wannan aikin Zahra ne,,amma tasan
ko giyar wake tasha gaba bazata kara mata haka ba..Ta dakko mishi fresh
milk,Allah ya sota akwai,Ta tsiyaya mishi dan shashe baki,,.a ranta tunani
take,wani irin attarugu Zahra ta afka mata a miya haka??..Oho,wato wannan ne
dalilin Murmushin ta na tun dazun? Ta girgiza kai, "wannan Ai dabarar yan Da ce
in banda Zahra,,tai Murmushi kan ta koma tana tsiyaya mishi,,..
Kuka take,tana da ma bata aikata hakan ba, dan Gashi a karshe ita ce da
kuka,ranar dan bakin ciki bata fito ba sai taran dare,.
By
Feenat Ja'afar
59_Washegari ta fito zata kitchen ta tarar da Sa'a ta daura K'afa d'aya kan
d'aya a kan kujerar ta,, murmushi take,wanda yasa Zahran saurin kawar da kai,,ta
tako a hankali tana rausaya, "Sis ina kwana?. Da sauri ta dago kai,dan batai
tunanin haka zata barta ba,. Murmushin dole ta kwakulo,,tare da amsawa,,.tace"
Tun jiya shiru,hope dai lafiya naga baki fito ba??. Ta dan harare ta,
"Lafiya,,.ta kada kai" Ok,.Ga nan abincin ki,,.ta juya tai sama tana mata sai ta
sakko anjima.. Da kallo ta bita,da mamakin maganar da bata mata ba ta jiya,,.
"Baby,ya juyo yana kallon ta,,. Ta tashi tare da kwanto wa cinyar shi,,.ta dan
shafo fuskar shi,," Ya roko na please, gobe date line da suka bani please,,.
Tuni ya sanja fuska,,tare da matsar da system din gaban shi,,. "Na zata na gama
da nan wannan shafin Unique??.. Bana sha'awar mata ta da aiki,bare na gidan
TV,,. Da marai rai ta ta dukar da kai da dan murmushin Neman kuka,,. Allah yaga
Babban burin ta ne ta ganta tana News,amma Gashi mutumin nan yana son kwafsa
mata,,.
Bata San guntun hawaye ya zubo a,,sai ji tai ya bar sababin ya janyo ta,,." Am
sorry,,.Ta dukar da kai kasa,,."Zan kare komai Dear,,wallahi buri na ne
hakan,please,. Ya furzar da iska,,a times Sa'a tana sashi abinda bai niya
ba,,.Yai ajiyar zuciya, "Da sharadi, Cikin zumudi ta mike dan jin sharadin,,.
Yace " Na farko,babu zuwa da gyale,,na biyu,Babu magana da kowanne abokin aiki

sai dole,,. Na karshe,aikin ki bazai shafi kula dani ba,,. Ta rukun kumo
shi,"Duk na yarda Allah,, wannan Ai masu sauki ne,,.
Washegari girkin Zahra, Yau da zumudi Sa'an ta tashi,,ta Riga kowa,kan kwa 7:30
ta shirya,. Jira take su gaisa da ogan kawai ta wuce,..Zahra ta kallo ta da
mamaki,"Wai da gaske aiki zaki fara?. Ta daga mata kai"ya fice Wai,.Ta kada kai,
"Yayi,.Tai kitchen,,. Lalle Hafeez bai ya adalci a lamarin shi,. Toh wallahi ko
sama da kasa zasu hade sai ya nemo mata itama aiki..
A wajen aiki ana ta nuna mata tsarin wajen,,Murna fal ranta, yau gata a
office,,. Bilkisu ta zo wajen ta,. " Suna na Bilkisu, kefa??. Sa'a tai Murmushi,
"Sa'adatu,,. Da fara'ar ta tai mata barka da zuwa office din su,,.
Tana tashi gida ta wuce,dan yau chan zata wuni,. Tana tuki ta dau waya," Ranka
ya dade,,Yanzun kake raina sai ga kiran ka,,. Yai Murmushi, "Ya aikin toh? Naga
first NeWS naki,very interesting, sai dai fa da matsala.. Tai karamin dariya,"
Nasan matsalar, sai an daure,,.Suna ta tadi har ta isa gida,.
Yau auren su wata (6) kenan, Matsalar da ta fara fuskan ta bai wuce samun cikin
Zahra ba, Gar da gar zata na Goran ta mata haihuwa.. Ko in sun zauna ta tsiri ko
dai Sa'a tana planning ne??.. Tun abin baya tasiri a wajen Hafeez ya fara,sai ya
fara zargin ko dan aiki Sa'a take planning,,. Duk randa Zahra tace haka takan yi
Murmushi,. Dan tasan da gaiyya take fada mata haka a gaban Hafeez kullum,.
Yau suna kwance ya riko hannun ta,,. "Unique,, ta kallo shi tare da shafo fuskar
shi,,." Please in da gaske kina planing ki taimake ni ki daina,,ina matukar son
yara,musamman su fito ta tsatson ki,,Aiki baya hana haihuwa please,.. Da mamaki
take kallon shi,dan ko kadan batai tunanin maganar Zahra zatai tasiri a ranshi
ba,,.Kallon shi take ta ma kasa cewa komai, shi kuma sai ya zata bata yarda
bane,,.
Dan haushi ma ta kasa mai maganar,. Tashi yai yana mai gaskata zancen shi, lalle
Sa'a planning take tunda bata Musa ba,indai kuwa hakane dole ya sa mata ido,.
Tun ranar Sa'a ta kasa sukuni,yau ta kudiri niyar ganin likita in ta tashi a
aiki,,.File yasa ta bude tare da bata appointment ran Friday,,. Allah Allah take
Friday tai ta gano meye matsalar ta.
Dr ya kalle ta bayan an kawo result din ta,sannan ya fidda result na
scan,."Madam (you are absolutely fine,,. The uterus is normal in size,,.But
abinda ban gane ba shine,cervix naki naga halamun rufe wa,Sannan akwai kince dan
ruwa na linking kadan,,so bazan tantance yanzu ba since kin ce this month kinyi
period, right??. Ta daga mishi kai,,. Ya kada kai,"OK, yanzu let see,PMC nakin
yazo ending, if ba wani Sign then sai muyi tackling next month,,. Don't
worry,everything will be fine,,.Kin ma yi dabara da kika zo da wuri,. Tai
Murmushi,. Ya bata result da magun guna ko da da infection ya baje,,.
A gajiye taje gida,dan ma Ta sanar shi zata biya anguwa,,Yana zaune a parlour
shida Zahra,,cikin ta har ya tasa,fi'ili ake mishi kala kala,.Sa'a tai
murmushi,, "Sannun Ku da hutawa,.Yai Murmushi,," Yauwa Unique,,

Please Login or Register in order to submit comment