Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naja..dan hutun farko,saida malaman
su suka zo gidan su Sa'a, dan ka'ida in anyi hutu
suna kai ziyara gidan dalibai masu ilimi,,toh
fa,akaga malaman larabawa a gidan su Sa'a,
yara suka cika,, tuni ta fara dagun kai,, tun daga
nan martabar Sa'a ta kara sama cikin yaran
arear,,wannan ne ya kara sa qaunar ta a gun
iyayen,,ita kam fadeela day take so,,nan take yi.
Tana ss1.,amma in ka ganta,zaka rantse wata
katuwar budurwa ce,,komai ya kan kama,,samari
suka fara mata cha..tuni kai ya fara gilgilwa,,basu
ke gaban ta ba,,burin ta da yawa,, musamman
kanan samari,tafi raina su,, toh wanda take nema
suma ba'a barsu a baya ba,,sai kaga Alhj babba
dashi,amma yazo yana rawar jiki wa Sa'adatu,,
ganin yadda take, yasa suke sau mata kudi,,da
taci naci,ta fatattake ka,, da kudin samari ta
kafu,, dan ita batajin nan da shekara 5 ma zatai

aure,,tun baban na taka mata burki,har yai
shiru,,yakai ya kawo kayan da Sa'a take sawa
yanxun ko yar wani mai kudin albarka., Ga BARIKI
sai abunda yai gaba,,akwai lokacin da taje super
market ita da fadeela,, suna cikin siyayya saiga
wani Alhj sunzo shida matar shi siyayya,,tunda
yaga Sa'a,ya kasa sukuni,,tuni matar ta fara tsaki
tana hararar su Sa'a,, Sa'a ta kallo ta ta
watsar,,sai a lokacin ta kula da yanayin Alhjn,,tai
murmushin mugun ta.. Tuni ta fara
kwarkwasa,tana wani yauki,,tamkar bata san
Alhjn nayi ba,,da taxo dai dai wajen shi da gan
gan ta yarda kwalin corn flakes,, tana wani fari ta
tsuguna zata dauka,da sauri Alhjn yarigata,, sai
washe baki yake,, "sanun ku yan mata,, tai wani
fari ta saci kallon matar,duk sai huci take,,tai
wani far da ido" Yauwa Alhj,, tuni fara'ar shi ta
karu,, har ya manta da matar shi na gun,,iya
wuya matar nan ta kawo.. Da karfi ta katse shi..
"Wai Alhj meye haka?ya juyo,." Mey.. mey..mey
nayi,,taja tsaki sai kaje ka biya ai,,ka wani tsaya
a gaban yar cikin ka kana bari,,ya kallo Sa'a.. Ta
sau mai wani shegen murmushi tana far fara
ido..tuni ya sake washe baki,, dan takaici kira
take"Alhj, magana nake,, amma ina,shi ya tafi,,ta
kalli su fadeela da tsabar takaici.. Tace"shegu
karuwan banza kawai., ta bangaje fadeela ta
wuce tana huci..Sa'a tana ganin ta futa ta hade
rai "Baba, mama na maka magana,,tuni yasha
mur" haba yan mata,, tai gaba tana taku zuwa
wajen biyan kudi,,da sauri ya shiga gaba.."Aa
aa.,bari zan biya duka..tai wani murmushi, kai
maza abar su,,ita duk dan matar tayi,kawai daga
ganin su zata fara ya tsina musu fuska.bata san
wace ni ba,,taja baya ya biya kudin..zata dau
ledar ya dauka har tasun ya rike,,ta kauda kai
tana dariya..suka fito daga super market din,
matar tana ganin su ta fito amota.
By
Feenat JaJa'afar
&
Hauwa Damary
[12/23, 7:49 AM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
7_Magana take amma shi hankalin shi yayi kan
Sa'a.. Tuni ta kule ta tsaida Taxi,,Sa'a ta nuna
mishi ita,,kan yai wajen tana dagawa matar yatsu
cikin shakiyanci..tuni ta kara kuluwa..tace mai
taxi yaja,,shikwa Alhj yana ganin haka ya koma
wajen su Sa'a,, "Asma'u muje na sauke ku mana,,
tai far da ido,, toh mun gode,, tuni ya hau rawar
jiki,, suna tafe yana musu tadi,,ita duk ya ishe ta,
amma ta maze,,a layin su ta nuna kofar wani
gidan kasa,.nan ne gidan mu,,yasau baki yana
kallon gidan, yace" toh sai kin ganni,,ta kada mai
kai,,har yaja mota yana daga musu hannu,ita
kam yake kawai take mishi,,yana kule wa tai
tsuka,,"ji yadda yake rawar jiki,,yan wahala.. Ita
dai fadeela binta take da kallo..suja dauka suna
tafe,,saiga wani dan unguwar su
Aminu,yace"BARIKI.. Tace"IYAWA.. Yai dariyar
keta..kai Allah barmu da BARIKI.. Tai murmushi
"Amin Aminu,,yace" Wane garan aka kara wanka,
tai fari,"kasan ku maza,,sai a hankali.. Nasan zai

dawo..zan sa yara suna min gadin kofar gidan
nan,so nake tashin farko ya bani kudin gyaran
gida..Aminu mutumin ta ne,a duk unguwar a
maza dashi kadai take hulda,,duk a dalilin qawar
ta ummi.. Yai dariya "BARIKI ba imani,,yai kuma
tanan za'a fara,tace" nagaya fiya rawar kai ne
wlh,, yace"a sassauta mana,,tai murmushi
"wanda bai kawo kanshi ba ba..sukai dariya.. Kan
chan ta wuce gida,,tuni fadeela tai gida ita
kam,,da sallama ta shiga,,aka cire gyale,,"mama
mun dawo,,ta kalle ta,," sannu,ta fara bude
kaya,,ta ware wa su mama kayan shayin da ta
siyo,ta dau nasu da kayan cosmetic,ita dai mama
kallon ta take "wai ni Sa'a na tambaye ki,,ta kallo
maman" toh,, "ina kike samo wannan uban kudin
haka?tai murmushi" mama kullum tambaya 1 kike
min,,"wlh ni ba wanda nake roka yake ban kudi,,
fadeela sheda ce,,ta girgiza kai,, "ni dai kimawa
Allah kar kice zaki saida mutuncin ki a banza,,
dan wlh koni uwar ki lamarin ki ya fara bani
tsoro.. tai wani murmushi "mama,ta kallo ta," wlh
hannu wannan, ba saurayin da yaga fuska bare
ya taban,,na kuma miki alkawari, indai nice,toh
zan rike mutunci na.. Ta kada kai "Allah ya muku
albarka,. Sukace " Amin.
Washegari kuwa sai ga Alhj yazo gidan da ta
nuna mishi jiya,,tuni dama tasa yara zaman
jira..in wannan sun gaji su bawa wannan,, ya
yafito daya,,"Nan gidan su Asma'u? Ya kada kai
"amma bata nan,bari a kira ta,,dan har sunan
karyar data bashi ta sanar da yaran,,da gudu yai
gida,sai gata ta dawo a islamiya,," BARIKI., tace
"ya akai Tj,,ya rada mata" mutumin yazo,,tai
murmushi "ku tashi toh,an jima zan neme ku,,tai
gida..tuni ta cire kayan islamiya tasa na
karya,aka mitsika powder,, ta zari gyale" mama
ina zuwa, tai waje,uwar ta girgiza kai,, Allah mai
halitta,, ta rasa Sa'a halin wa ta biyo a
duniya,,wlh bata da kaffara, ko yanxu akai wa
Sa'a aure a gidan mata 4 tsaf zata zauna..ita
kanta wani sa'en tsoron BARIKI irin na yarta
take..
"Alhj sannu da zuwa,, ya washe baki," yauwa
Asma'u, ya gajiyar ku ta jiya?tai fari,"Tabi lfy,,
"ina aunty,,yai murmushi,, tuni yaji ta kara shiga
ransa,,
Ya zamo kusan kullum Alhj sai yazo,,wahalar yau
daban ta gobe daban, Alhj har ya mallakawa
BARIKI waya,lokacin rike mai kyau sai ya'yan
manya,,ranar da ya cika sati,yazo da kudi,wai zai
bata ai gyaran gida dan zai turo manyan shi
tambaya.. Saida cikin ta yai kululu..amna ta
wayen ce..ya dakko damin kudi kuwa ya bata.
ana haka washegari suna tsaye sai ga wata yar
BARIKIN gaske ta fito a gidan,ta kalli
Sa'a"BARIKI,.. Tai mata banza,,tace" Sa'a, dake
nake fa,,tai mata kallon banza.."Bance kifita
harka ta ba ne? Alhj ya sau baki,,Sa'a kuma,.ta
kallo shi da yake"Sa'a fa,,ta daga kai, "aa ni ba
wannan bama,kamar BARIKI naji an kira ki,,ta
hade rai" eh Suna na kenan, ya hadiyi yawu..
Anya kuwa tafiyar shi zata wu davyar BARIKI? Da
gani wacce ta fito a gidan sun nan ba yar kirki
bace,,take ta kallo shi, ganin tarkon ta ya

danu"Alhj lfy?ya kada kai "a ba komai,inaga zan
tafi,, tai murmushi.." Toh nagode..yaushe zan ce
zasu zo..ya kallo ta "aa ki bari zamuyi waya.. Tai
murmushi"a gaida aunty na..koh kulata bai ba.
Tun daga nan bata kara ganin kafar Alhj ba,dan
tunda ta fuskanci da gaske yake tahada plan na
rabuwa dashi cikin sauki..saida ta sake layi kan
ta koma makaranta.
By
FeenaJa'afar
&
Hauwa Damary
[6/2, 5:59 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar.
BARIKI...IYAWA
8_Gashi har ta kammala secondary school dinta
a Mamudo..iyanxu kam, karya ta ninka ta
da,,BARIKI da Yanga da kisisina ya gaba,,
cikakken zubi kuwa ya da zati Allah ya bata,,
shekarun ta 17,amma in ka ganta,zaka zata tai
20,dan komai yaji cif cif,,kugun nan tamkar dame
shi akai,ga mazaune,, ta ko'ina tayi MashaAllah..
Shi yasa take zan zaren ta son rai,,tamkar in taje
makaranta karatun yanga da Iya tafiya, salo da
sauran su ake koya mata,, duk yan Matan
unguwar nan so suke suyi kawance da
bariki,,likafa ta ci gaba,,tun a ss2 ta bude
account,,dan a yanxun Business take,bata saye da
siyarwa ba,, no.,ta saita gidan aure,, Tunda
mazan yankin suka gane tsoron BARIKI suke,sai
su kuma suka samu abun yi..
Akwai lokacin da a wata unguwar gaba dasu,wani
dan siyasa Matan shi sun hana shi sakat,,yai
nasihar a banza,,sun maida mishi gida kamar filin
dambe,,Ranar suna office yake bawa abokin shi
lbr,,"yanxu duk dabara ta ta kare,, ya kallo
shi,kan yai dariya,"kasan mey?ya girgiza kai "ina
ga ina da dabara,,tuni ya gyara zama,," in baka
manta ba gidan Dana zauna da,ya kada kai "a
unguwar, akwai wata Yarinya,," BARIKI sunan ta,,
ita indai da kudi,toh aikin ta saita mata ne,,ya
kalle shi da halamar tambaya,, "ban fahimce ka
ba?? Yai murmushi,"a unguwar kaf,ba wanda
baisan BARIKI IYAWA ba,,yarinyar tayi,ga diri ga
kwainane,, ya harare shi" toh ni kuma mai zai
hadani da wata bariki??mtsww kai ana abin kirki
ka sako mana wani zance..yai dariya "ka jira ni
tukun,,waya ya dauka,kan yai dailing wata
number, kan yasa a hands free,," Daga chan aka
dauka,"Aboki ya akai??yai dariyar keta"kaga na
BARIKI sai yayi,,Shima ya kyalkyale da
dariya,,"kai baka mantuwa abokina,, yace"ya zan
manta,,da fatan har yanxu komai normal?? Yai
dariya,, "kai BARIKI Duniya ce wlh,banga mai
Matan unguwar nan suke tsoro har yanxu sama
da BARIKI ba,, madam dina lukus kake ji, tunda
akai wannan batu..yai dariya" Ya kamata a koma
a karawa BARIKI jari,, suka sake kyalkyale wa da
dariya..bayan sunyi sallama shi dai Muktar da
kallo yake binshi,, ya ajiye waya yana"BARIKI
BARIKI,, "tukun kasan wace BARIKI kan kaje gare
ta,, Mutumi na dan nace BARIKI ba ina nufin
karuwa ce ba,,ya girgiza kai," Tasan takan Duniya
ne,,wannan abokin nawa,shekara 1 data wuce
Matar shi ta tsuro mishi da hali iri iri,,da halama

da zigar kawaye,,ga ta kamar ta yana son ta,,tuni
ta hau iskanci irin na kowa ya samu inuwa,Wai
dole yai shanya,,har karar ta yakai wajen iyaye,
amma ba abunda ya sauya,,Ranar muka
hadu,nace yau a gidan shi zanci abinci,,bai min
musu ba muka je,, a parlour muka tarar ta ita da
qawaye,,suna firar shi abokin nawa, fadi suke"Wlh
mazan Saida haka,,in ka nuna musu bakka
mutunci anfi dai dai tawa dasu..ya kalle ni na
kalke shi baki sake,,.mukai sallama tana ganin
mu ta tabe baki,, qawaye kowa yai hanyar
sa,,tana gani mun zauna tai tsaki ko gaisuwa
babu ta tafi,, ya kallo ni duk kunya ta ishe
shi,,nan yahau kame kame,,nace"Ku nan hala
Baku San da zaman BARIKI ba? Ya girgiza kai
"wace haka?nai murmushi,, biyo ni mu fita tukun,,
tuni ya zari mukullin mota,
By
FeenaJa'afar
&
Hauwa Damary
[12/24, 12:08 AM] Feenat Ja'afar.
BARIKI...IYAWA
9_Wato a unguwar mu akwai wata Yarinya
BARIKI.. Ita aikin ta kawai a dauke ta sojan
haya., indai zataji dumus,toh fa gidan ka ya
gyaru ya gama,, yanxu wajen ta zamu,, ni zan ma
iso,akwai wani Aminu Aboki na suna dasawa
sosai,,.
Suna zuwa ya nemi Aminu a waya,,sukaci saa
kuwa tana gida,, Suka koma inuwa jiran ta,, chan
sai gata ta fito tana taku tamkar hawainiya,,baki
ya sake yana kallon BARIKI,, lalle taci sunan ta,,
Ji yadda take wani yauki,,. Ta karaso da sallamar
ta, cikin muryar nan ta masu Duniya"Sannun Ku,,
Sukai yake,,"yauwa BARIKI,, Aminu yace "ganan
Aboki na ya kawo abokin shi ai mishi gyara,,tai
murmushi, tare da kallon su da wannan kallon
nata,,sai suka zama kamar wasu sokaye a wajen
ta,, Aminu ya kallo su" Ku karan to mata, "Ni zan
wuce,ga nan bakin ki,tai murmushi, tare da daga
mishi yatsun ta 2" see you,, ya gyada kai, sukai
sallama ya tafi,,Duk abunda ke faruwa suka
karanto mata,tai murmushi,, "yane toh,, tai musu
wani kallon kasa.,tuni ya gano mai take
nufi,,rafar dubu 10 ya bata,,"ki fara da wannan,,
ta juya su tai murmushi,," bakka matsala,, "Abu 1
yanxu zaka min,ya gyara tsaiwa,," kasa min
numbern ka,,sannan duk inda zata fita,ka sanar
ni,ya gyada kai,, tai murmushi "Baka da
damuwa,,ana haka saiga wata Qawar Matar
wanda aka bada contract dinta tazo wuce wa,,da
sauri ya kallo abokin,," tafa kwabe,,ganan Qawar
ta,, suka kalli Sa'a, tai murmushi "ai tama
taimaka min wajen aiki na,,Wai salma kake nufi?
ya gyada kai,, tai murmushi," kai kamar baka
ganta ba,, sannan yau,kar kaje gida sai karfe 10
dare,, nasan daga nan,gidan ka zata..zata sanar
da Matar ka,cewar ta ganka tare da BARIKI..
Daga nan, zata fada mata koni wacece,, ina so in
ka koma,ka sauya mata fuska,,da sauri ya kallo
ta,, tai murmushi "I know what am doing,,, ok?ya
gyada mata kai,,nasan zata fara tambayar a ina
kakai dare?kasan amsar bata I guess.. Ya kada

kai" ki sanar ni dai,,tai murmushi,. Zamuyi
waya,,dan yanxun haka ina da wajen zuwa,,ni
zanji da sauran aikin..sukai kada kai tare da
mata sallama,,,.
Direct kwa salma gidan Qawar ta tayi,,da mamaki
ta bude ta shigo,dan dazun ta tafi,,"da fatan ba
mantuwa kikai ba??Tace "hmm zakiga mantuwa,,
kin San kwa ina naga mijin ki? Ta kada kai tare
da gyara zama tana zaro ido,," Toh a wajen
BARIKI,,Bakya ramin kanki sai na wata,,tuni ta
fara tunanin ina take jin BARIKI? Ta cigaba. "Ke
kinga damin kudin dake hannun ta?kuma wlh
mijin ki ne ya bata,,.ta kallo ta" kinyi shiru ina
miki magana, "ko zaki ce baki gane wa nake nufi
ba?Kin manta Nazeer saurayin Mamy da suka
hada soyayya da wata ta daga karshe ya kita ya
koma gun ta?ko zakice Baki tuna wacce tasa aka
mana A tule ba lokacin bikin Hafsa dan mamy tai
mata tsaki??Ita tuni ta hau zufa,,dan tuno da
wacece BARIKI,,tuni ta mike,,ta kade in har mijin
ta ya auro mata BARIKI,,tasan koda kwarkwasa
saita Kore ta a gidan nan,,ta zauna," Qawata
meye abun yi??ta zam,,"ki fara tada mai wuta
tukun na,,na 2,gobe yana fita muhadu muje har
gida muci mata.. Dama wlh har yanxu ina cike da
a tulen data sa aka mana. Haka ta barta kan sai
goben.
Sai 10da kwata ya shigo gidan,,kamar yadda
BARIKI Tace kuwa tana ta zarya a parlour,, da
Dane,ko 8 ya shigo tana daki a kwance,,tuni ta
yai kicin kicin ya hade rai,, tana ganin haka gaban
ta ya fadi,,kan tai magana wayar shi tai kara,ya
kalle ta a wulakance yai tsaki kan ya zauna a kan
kujera yana murmushi,, "BARIKI,.. Yai dariya
tamkar ta fada mishi wata Kalmar mai dadi,," kai
ke ai ta daban ce,,yanxun dawo wata,, yai dariya
yana Shafa haba tare da kallon yadda Matar shi
ta daura hannu aka,,"nima tamkar na dawo inajin
wannan tattausan muryar taki mai mantar min da
komai,..yai Jim halamar yana saurarar ta,,ya
kyalkyale da dariya,..tuni Matar ta sau kuka,,ya
kalle ta ya watsar,,"Dan Allah asa ranar auren
nan da wuri,,..ji yai an warce wayar hannun shi,,
ya bita da kallo,tuni ta fara ban bami "Wlh ta
Allah ba taki ba,,Banza karuwa kawai,,daga chan
tai murmushi kit ta kashe wayar..a razane ya
tashi,ya warce wayar shi,," wlh in kika kuma
zagin masoyiyata a gaba sainai mugun saba
miki,,"mey kika Iya ke in banda kullum ki bata
min?sannan na samu mai wanke min zuciya da
tattausan lafazi ki zage ta?? Kai ta girgiza mai
"Dan Allah baban Najib kai hakuri,,wlh na daina,,
ka rabani da BARIKI,, gwiwa biyu ta zauna tana
rokan sa..ya fizge rigan shi tare da wuce wa
daki..,,yana shiga ya danna sakata ya hau
dariya.. Yaushe rabon sa Aisha ta mai abu ta
bashi hakuri?? Kai ya manta,sai yau a dalilin
BARIKI.. Yana son Matar shi.. Amma duk ta
sauya hali..zai juri ganin ta a haka har yarda
BARIKI tace
By
FeenaJa'afar
&
Hauwa Damary

[12/24, 12:54 PM] Feenat Ja'afar.
BARIKI...IYAWA
10_Ya danna kira ya sanar ta ya akai,"ka barta
zuwa gobe da safe,,nasan zata ce zata zo wuri
na,,ko tasa azo,, kai mata gargadin wannan kan
ka fita,,.
Washegari ma bai sauya ba,yau Aisha harda su
gaisuwa, wanda rabon ta da yi tun Kan ta sauya
hali,, yai mata banza,,zai fita cikin sanyi tace
baka karya ba,,ya harari wajen abincin, "No zan
karya a waje,,sannan ban yarda ki daga daga nan
ba,zan Iya dawo wa kowanne lokaci.. Yai waje
yana dariyar keta,,a kujera ta zube,,tunda take
Abban Najib bai taba mata haka ba,,Wai har
abinci bazai ci ba.,ta share hawaye,Kila ma wajen
BARIKI zai ciwo,,kai amma su salma sun mata
huduba marar kyau,, gashi ta kwabe mata,, waya
ta dauka,kan ta kira salman," karki zomin
gida,munafukai kawai,,kit ta kashe wayar ta,,
yanxu ta ina zata fara?
Acikin kwana 2 duk ya sauya mata hali,Waya da
BARIKI, text kuwa ba'a magana, ranar yana
wanka ta saci numbern bariki a wayan shi,da
sauri ta fita,,sai sa ya yay kan ta kira BARIKI,, a
yangance ta dauka,, "Amm Aisha ce,,tai far "
wacce kenan?
Duk ta rasa abun fadi, dan ji tai ta mata kwarjini
tun a waya..sai kawai ta kashe,,.bashi ya dawo
ba sai azahar,, kuka ya same ta tanayi reras,,
tana ganin shi ta tashi,, dan dazun nan aka kara
karanta mata wace BARIKI yar unguwar
su,,"Baban Najib,,dan Allah ka auri kowa banda
sa'a,, kayi hakuri bazan kara ba,, ya kallo ta
kamar yai dariya.,a ranshi yana tunanin "Wai
meye da BARIKI ne da yasa mata ke tsoron ta??
Ya basar" Gaskiya bazan Iya fasa auren Sa'a ba,,
dan tun yanxu tai min alkawarin zaman lfy da
kwanciyar hankali,, bazan fasa ki koma min yar
gidan jiya ba.., tuni ta hau rantsuwa ta daina,inta
kuma ya auri BARIKI,, da wannan ya samu lfy a
gidan shi,,yace da yamma muje zan raka ka..
Yamma nayi suka je gidan su BARIKI,, a lokacin
tana gida ana drama da ita,,wani kanin kakan su
yazo daga Nguru,amma irin in za'a bi da aure
tsakani,, yazo akan lalle lalle BARIKI ta fidda
Miji,,tunda fadeela ta fitar,,tuni ta fitsare "Ni fa
banni da tsayayye,, atoh ko ina da wallahi ba
zanyi aure yanxu ba,,baki ya saki har iyayen suna
kallon ta,, dake bala'eene yahau ta da masifa,,"
kedin wa?dama duk iskancin da kike tatawa a
garin na samu lbr,toh dole ki tsaida haka ki samo
na aure,,ta kalle shi, "toh na tsaida,,yai
murmushi," ko ke fa,,a ina yake?ta hade rai,, "kai
man,, ba shiba hatta iyayen sai da suka zaro ido,,
ya tashi," ke banson iskancin banxa,,Tuni ta fara
burburwa tana kukan gaske,,"ni wlh kai nake so,,
kuma kai zan aura,,baban ta ya doka mata
tsawa,"Sa'a bama son iskanci fa,, "ta kara jiniya"
wlh shi zan aura,, ni shi nake so,,tuni tsoho ya
sau kuka,,Lalle ya yarda BARIKI ce yan nan,, kuka
yake yana"Allah ya isa saude,,ki kalle ni kice ni
zaki aura?jikar jika ta?cikin kukan karya tace"Toh
Haram ne?nidai kai za'a abani, ba shiri yai
hanyar waje yana goge kwala, "InshaAllah anyi na

karshe,,da sauri baban ya bishi," Baba kai hakuri
ka dawo,,dole ta bi umarnin ka ai,,har suka fito
kofar gida tsoho na kuka"ai ni ba ruwana da
harkar yarka daga yau,,Ashe da gaske "BARIKI ce
haka??Wai ni zata aura??Alhj Muktar suka kalli
juna,tuni dariya tazo musu,,a karshe dole baban
tasha ya raka shi ya koma inda ya fito..yana fita
ta ware tana dirkar dariya.. Ladi ta fara tafa
hannu,ta nuno ta da hannu" anya Sa'a,, ta kallo
Maman tasu,"mama mey nai? Ta kar kade jikin
ta,, ta sauke ajiyar zuciya "ba komai Sa'a,, Allah
ya shirya mana ke.,tace " Amin.tai waje wajen
kiran ta,,.
Dariya ta samu suna dirka, tana ganin shi ta gane
shi,,tuni ta hau murmushi, "yau an tuno Haj
Ahmad? Yai murmushi" Manya a Baku naku
daban,ttai wani fari,,tuni Alhj Muktar ya gyara
tsaiwa, kai shikam BARIKI ta mishi,da aure ba
contract ba.
By
FeenaJa'afar
&
Hauwa Damary
[9/13, 8:10 PM] ๐Ÿ’๐Ÿ›๐ŸฌSalma๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afarSalma๐ŸฌSalma๐Ÿฌ๐Ÿ›๐Ÿ’: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar๐Ÿ›๐Ÿ’: BARIKI...IYAWA
11_Abinda ya kawo su suka sanar mata,tai
murmushi, da gani mutumin zai sau hannu, tuni
ta yarda,Alhj yace da daddare zai dawo,sai su
tsadan ce,,tai murmushi, dan tuni ta harbo jirgin
shi,,kai ta kada,,sukai sallama tai gida,,Maman su
ta kalle ta, "Sa'a, ta zauna tana amsa wa,," In
tambaye ki man?tai murmushi, "toh mama, tace"
ke ko tsoro bakya ji wataran wata tai miki illah
akan mazan su?tai murmushi, "mama Allah bazai
bawa kowa galaba a kaina ba,,kedai kimin
adu'a,.. Ta kada kai" Yauwa, dama ina son fada
muku,makaranta zan shiga,,cikin satin nan,,
Maman ta kalle ta da mamaki,,Wai yaa ita take
wa kanta komai tamkar da namiji mai aiki,,in bata
manta ba, kwanan nan aka kawo takardun gidan
Sa'a data siya da kudin ta,, ta girgiza kai "Allah
ya kara kare mata Sa'an ta a ko'ina.
Washegari plan ya fara,Alhj Muktar ya sanar
mata Matan shi zasu walima,ya gaya mata lokaci
da venue,, tuni ta gama tsara komai,, a chan
unguwar da ke gaba dasu ne,,Bikin na manya
ne,,an ciki kowa ya zauna a kan kujera mai gaba
tar da walima kawai ake jira,,filin gidan babba
ne,yadda in mutum ya shigo sai ka kare mishi
kallo bai karaso ba,, tunda mota ta tsaya ake
kallon bakin kofar,, sanye take cikin wata bakar
Riga da ratsin purple doguwa kirar Dubai,, ankai
tela ya kara fito da shape dinta,,anyi tuntu a ka
da gashi da rabons manya,, tai nadi tamkar
balarabiyar asali,, ga wani katon glass fuskar nan
ta Gaji da make up,,hand bag dinta da wayar ta
tasa cover da takalmin ta duk iri daya,tana zuwa
wasu samari sun sha bakaken suite,da ganin su
kasan bodyguards din ta ne, da suka bude mata
motar suka bude mata gate,, daya ya bata jakar
ta ta makala a hannu, daya ya bata phone
nata,,tuni ji kake tsit waje kallo ya koma gun
BARIKI,,ta tako, suma bodyguards din suka biyo
ta,, da hannu ta musu sign dasu jira ta
waje,,wata a wajen ta zunguri daya,,"Ita kuma

wannan Matar wani Alhjn ce?kamar rada dayar ta
rada mata yadda na kusa da su zasu Iya jin
su,,"ke,in kinji ana BARIKI..IYAWA, toh wannan
ce,,Matan guda 4 dake kusa suka kara kallon
Sa'a,, Matar ta cigaba "Bazawara ce, sai dai
manyan zata aura,,Budurwar wani dan siyasa
ce,koh Alhj mukhtar naji ne??tuni 2 kusa da ita
suka juyo,,sai dai sun kasa cewa komai,, ta
cigaba, "ta taba aure,tana shiga Saida ta fidda
Matan da kissa da tsabar Iyah BARIKI,, dayar ta
kallo ta,," toh ke ina kika Santa?ta rike
haba"waye besan BARIKI ba a tsuku kun nan?ai
in kin ganta a hanya kina tafe da mijin ki ko
saurayin ki boye shi,,dan maza idon su,,idon
BARIKI,.. Ta zungure ta kamar gaske,,"yi shiru
gat nan zuwa,,in an fita zan baki komai in
details.. Suka kada kai,, Sa'a ta zauna tare da
daura kafa daya kan daya,, tuni wata ta kusa da
kujerar da ta zauna taja wani mugun tsaki,kan ta
dau kujerar ta ta sauya waje,,Sa'an ta bita da
kallo a takaice, da sauri ta sake bin Matar da
kallo,,kamar ta taba ganin ta.. Matan Alhj Muktar
suka bita da kallo,,suda suka shigo suna hararar
juna,yanxu duk sun ware jin an anbaci saurayin
wannan da kamar sunan mijin su,, wata yar
safasafa ce tazo da kujera kusa da BARIKI,,
"Shege BARIKI.. Tai wani mayaudarin murmushi,,
kan ta furta" IYAWA.. Suka tafa,,"Yayi mai gara
kan yan maza,.ana haka mai walima tazo aka hau
waazi.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/25, 12:19 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
12_Tun ana raba take away uwar gidan Alhj
Muktar taje wajen Matar nan mai tsaki, Matar
abokin mijin su ce,,suka kebe da kujera,bayan sun
gaisa take tambayar ta"Ni Maman Abba kin San
yarinyar chan ne??ta tabe baki "nasan ta,
muguwar bakar kilaki kenan,,ni ai bazan manta
fuskar ta ba,,duk da yanxu ta kara girma, tunda
ma in kina Neman karuwar hanya,toh ki nemi
waccan,ta sake kallo BARIKI, ita wayar ta
take,tana ta wani lumshe ido,, ta dawo da kallon
ta kan Maman Abba," mey ya hadaku? Tai
murmushin takaice., kan tai kwafa "akwai wani
lokaci da muka je super market nida Alhj siyayya,,
anan muka ci karo da ita,,wlh Alhj baiya kallon
mata barin a gaba na,amma yarinyar nan in kinga
kwarkwasar data dinga mishi,,ke daga karshe
mantawa yai dani,,tun daga ranar Yarinyar tai
gaba dashi,,Asma'u waya.. Waya Asma'u,, inaga
da ta gama tatike shi ta Kore shi,shine kwana 2
naji shiru,,tun daga lokacin na daina yawo da
Alhj.
Tai ajiyar zuciya, inko har da gaske Alhj ita yake
nema dole taci uban yar nan,,ta gidan ma yata
kare bare wannan yar BARIKIN?? Tashi tai ta
koma wajen ta, kan BARIKI ta fita ta rigata
fita,,tashin hankali, Wai gobarar gemu,,tabbas
wannan CRV Alhj ce,,sabuwa da ko su ba'a kaisu
unguwa a ita,,ta cije lebe" Tab, wato tun kan ta

shiga har ta fisu ikoh?ana haka Drivern su yazo,
dai dai BARIKI ta fito,, da sauri bodyguards dinta
suka zo,suka karbi Jakarta da wayan ta,, da
mamakin ta sai ta ga drivern nasu yayi wajen
BARIKI yana kwasar gaisuwa,,amarya ta fito,,taga
lokacin da Bala driver ke gaida BARIKI harda bata
abu a Leda,,ta kalli uwar gidan nata a yatsine,,
"nifa ban gane lamarin nan ba fa M Hafsa?? Ta
kallo ta da takaici,, " zaki gane in munje
gida,,sukai wajen mota amma Bala driver bai taho
ba,,tai wajen tare da doka mishi tsawa"Wai baka
ga fitowar mu bane??ya juyo da sauri,."yi hakuri
Hajiya,Alhj ne ya aiko ni gun amarya,,da sauri ta
kalli BARIKI wacce take kokarin shiga mota,,da
sauri tai wajen,, "Amaryar wa?bodyguard 1 yace
ta Alhj,,sannan kiyi hankali kar wani abu ya faru
anan,,dan ya tabbatar mana tsaron ta..taja tsaki"
Dallah rufen baki,,nida Tsohuwar yar BARIKIN nan
nake,,karon farko BARIKI ta kallo ta a
wulakance,,"eh kin San ai Alalar Gero ce,wanda
bai Iya ba ta kwabe masa,, tai mata wani kallon
banza kan ta ce ya suja ta bata da lokacin ta..
Tuni suka ja suka bar amaryar Alhj baki
sake,,magana 1 ta mata mai harcen damo,, ji tai
tamkar ta kwala ihu,,a bainar jama'a an toya
ta,,jiki a salibe tai mota,,bayan ta shiga ta kallo
Bala"mey ka bata a Leda?uwar gidan ta kallo ta,,
"kina da karfin hali Halima,,zaki kwace ne komai
ya bata?tai kwafa," lalle Alhj yaso musu
wulakanci,, har ya fifita wata akan su tun kan
aure?uwar gidan ta kalle ta,, "ki bari muje gida
muji dalili,,ko aure zaiyi,toh wlh bada wannan yar
BARIKIN ba,,dan irin wayen nan suke daura ma
hawan jini..tai kwafa..
Ana dire su a parlour suka tsaya,,yau daya suka
zauna Neman mafita,," Yanxu Hajiya meye abin
yi?ta kallo ta da mamaki,,dan rabon da ta kirata
da Hajiya tun tana amarya,,lalle BARIKI mai sa
ladabin dole..
Waya ta dauka,tace "Alhjn zamu kira,,yazo muji
ta bakin shi,,ta girgiza mata kai" kar ki kira
shi,,barshi yazo da kanshi,,ba tace BARIKI IYAWA
bace?toh mu muyi amfani da damar mu ta Matan
sa mu nuna mata kuran ta.. Tuni ta rada wa
uwar gida abinda zasu mai in ya dawo..tuni aka
manta da kishi aka hau Neman mafita.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/25, 1:32 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
13_Bai dawo ba sai kusan Tara na dare,tuni suka
kara kulewa,, yana shiga ya gansu zaune a kujera
1 suna ta huci,,ba wanda yai wa magana yai
dakin shi,,da sauri suka tsayar shi, Wai Alhj mai
kake nufi?yaci mur, "danayi mey? "Kazo ka wuce
ba ko magana, yace" ita sallamar ba magana
bace?ko kun amsa?sukai shiru,yace"Ku bani
waje..amaryar ta kara tare kofa"ai wlh sai ka
fada mana wace Sa'a a gun ka da har ta fara
shiga lamarin dangin ku,,yai mata wani kallo,,
"Sa'a kuke son Sani? Ta kada kai tare da Rike
kugu,,yai murmushi" itace wacce tasan na Gaji a

barni na huta,,ita ke maraba daku a matsayin
kishiyoyin ta da zata samu,,Sa'a, ta wuce tunanin
ki a waje na,,ta tabe baki,,
"wannan kai kasani, abu daya muka Sani, mudin
Zaka auro wannan yar BARIKIN, toh fa tafiya
zamuyi,, koh Hajiya? Ita dai uwar gida tsabar
takaici ta kasa cewa komai,,yai murmushi, " zaku
Iya yin komai, amma Sa'a kamar ta shigo ta
gama,,Hajiyan ta tare shi"Alhj bafa zan zauna da
Wannan kilakin ba wlh,,saboda tsabar wulakanci,
Wai ita zaka fifita akan mu tun yanxu? Ya harde
hannu"da akai mey?tai mai banza,,ya gyada kai
kan yai daki,,amarya ta kallo uwar gida,,"Hajiya.
Gidan su kawai zamu mu

Please Login or Register in order to submit comment