Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kunya,.
Ina,Zahra in ta cigaba da tsayuwa a tana kallon su zata Iya hawan ruwa,tuni ta
juya Tasleem ta daura bayan ta tana waiwayen wannan BARIKIN, kai ko ita ta tafi
da imanin ta wallahi,, duk ba Wai kyau tafi Zahran ba amma da gani ta fita sanin
kan ta Duniya..sai dai ba yadda za ai Yayan su ya kaso musu yar BARIKI.. Tab,
bari suje gidan.
Gidan su zahran da ba'a je ba kenan sukai gida,in banda hawaye ba abinda Zahra
take, Tasleem tayi tayi ta kasa dai nawa,. A parlour suka tarar da Hajiya,itama
ta tsunduma tunanin Wai Hafeez da mata 2,,kukan Zahra ne ya dawo da ita,,tuni ta
hau tambaya,, kan Tasleem tace komai Zahran ta amshe,tana kuka tana tsarawa
Hajiyan. " Kuma Wai yar BARIKI fa Hajiya?da sauri ta waro ido waje,,tace
"wallahi Hajiya Wai ma sunan ta" BARIKI,Tasleem tace"Hajiya kinga yadda yake
mata dariya, tamkar wacce ta mishi ishara da Aljanna.."Ni ya ishe ni haka,,ni
dama nasan yaron nan ba haka kawai yake ba,,Ashe yana chan an dauke hankalin
shi, kuma Wai Karuwa yar BARIKI?? Ta kallo Zahra,"yi shirun ki,bari baban naku
yazo,,bazata sabu ba Sam,,da hankali na bazaa auro min sirika yar BARIKI ba
wallahi..
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[10/2, 6:31 AM] Feenat Ja'afar: [1/9, 1:03 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
31_Hafeez na dira gida Hajiya ta fara sauke mishi,,da tsananin mamaki ya sauke
kai kasa,yasan bai isa wanke kanshi da Sa'a ba yau a wajen Hajiya,.."Saboda ta
dauke maka hankali har ka gagara ban bance tsakanin Aya da Tsakuwa,,Yace"Hajiya
Wallahi ba haka Sa'a take ba,,wannan sunan daban,kuma.."Rufe min baki shashasha
kawai,, in baka Sani ba toh ka Sani yanzun,Zahra kawai na Sani,ba ruwana da da
wata BARIKI,Macen kwarai ce za'a kirata da sunan BARIKI ta amsa??. Mita take har
Abba ya ritsa ta bayan ya dawo,,yana hawa ta bi bayan shi.
Hafeez ya juyo yana hararar Zahra da Tasleem,,"Yaushe na zama abin wasan Ku da
har zaku Bini a baya?? Sukai tsurutsuru,ya nuno Zahra da yatsa, "Bari ma
kiji,wannan abun bazai hanani auren Sa'a ba,sannan Gobe kisan nayi ki tattara ki
koma gidan Ku,,.Ya tashi yai daki,,ta bishi da ido,Tuni ta fara hawaye,abun
harda gori?Ita kwa mita tsinana a zaman gidan banda takaici?Bari taje gida,har
gidan Aunty salma zata,karya ne a gama ta zaman aure da wata,,.
Shikwa yana shiga daki ya jawo waya,ita kanta Sa'ar haushi take bashi,,dan dazun
suna tsaye Ali yazo,, saboda tsabar rashin so Wai tace mishi " Excuse me"?,..Tai
wajen Ali,duk da bai ji mey suke cewa ba,amma ya gano wanda suke waya dazu
ne,tuni koh ta kanta bai bi ba ya shiga mota..shine kuma yana zuwa Hajiya ma ta
sauke mishi,.Yai dan tsaki, Lalle sai ya dage,,Ashe da gaske take Wai Bai karbi
soyayyar taba?
Toh ya take so yayi??Ya fidda zuciyar shi kan Yace"Sa'adatu I luv u,komai??ya
sake tsaki,,a hankali ya furta "Sa'a matsala,..
Ita kuwa tunda taga Hafeez ya zuciya ta rasa sukuni,gashi ta kasa kiran shi, a
nata tunanin ajin ta zai zube,. Tai kwafa,amma Alin nan sai ta sa kafar wando
daya dashi zai ki yayi zuwa wajen ta, in takamar sa gidan na uban shi ne,toh
itama tana da gidan daya taka wannan na bulo ma..ta kara tsaki,,ta juya ta dau

waya kan ta tashi zaune..tai dailing numbern Hafeez din,da sauri ta katse,," Oh
God,,ta rike kai,"Wai Sa'a mey ke damun ki ne akan Hafeez??Tun farkon haduwar su
da Hafeez shine kadai Namijin da ta taba mafarki,,shine kadai wanda ta taba
chachar baki dashi dan Dabarar ta takare, shine kadai ke sawa ta bata lokacin ta
wajen tunanin shi, Shine kadai a yanzun in suna tare take jin wani nishadi kadan
kadan na shigar ta..Sannan yanxun yayi fushi ta damu,ji yadda take gwara kan
maza,manya da kana nan su,,yau 1 wanda taki jini ya hana ta sukuni.." Ya
Ilahiii", "Mey kenan hakan yake nufi??
Ta kalli agogo 9,kwanciya tai kamin ta hau Mishi text da bata San ma ta fara
ba..Da sauri ta goge na ban hakuri ta rubuta. " Shine ka tafi ba koh sallama??
Tasa halamar shagwaba.. Tai murmushi, kan ta kishingida.
Text yaji ya shigo wayan ya kara tsaki kan ya kwanta,chan ya jawo wayan,dan yana
zata koh Alert ne na contact na Zane da aka bashi,,da mamakin shi yaga
Sa'ada,.yai murmushi, take yaji kuncin shi ya yaye,tuni yai reply..
Taji text itama,tai murmushi dan tasan shine,."Munyi fada ai,, tai murmushi da
har hakwaran ta suka fito, tai rufda ciki kan ta mishi Reply.. "Ai bama
fada..Triple sorry" ..Shima yai rubda cikin yana karanta wa,,yai murmushi,,"No
banyi ba..ban Aron minti 5 naji muryan ki sai nai sorryn..ya tura..chan itama ta
bude,,tai murmushi tana duba sling,, kan ta kada kai tai reply"An baka.
Ringing 5 tai kan ta katse ta dauka da sallama,,yai Jim,,tace"koh ba'a yafe ni
ba??ya sauke wata ajiyar zuciya,, kan Yace"u know what?? Kina da dadin muryar
sosai,,Tai murmushin jin dadi,. Kan tace "kaima haka?..sai kuma ta datse harshen
ta da hakorin ta,bata ma San ta furta ba,,yai murmushi,." No,ke ai ta daban
ce,,Tace"Koh,? Yai shiru,"Sa'ada waye Ali nan ne??tai dan murmushi,, "Dan mai
gidan Baba ne,,Yace" ehm,sai mey kuma??ta kada kai "shikenan, Yace" Ba So??tai
Jim, kan tace"akwai,.tuni ya mike zaune,,sai ta kara da"Shi yake kayan shi
amma,,ya sauke wata ajiyar zuciya da taji ta,, Yace"Toh Ni fa Sa'a?? Tai shiru
tana,tace"Hafeez ne kai,Yace"ehm?Toh ana son Hafeez din?? Tai Jim,gaban shi ya
fara faduwa,,ita kwa murmushi take a hankali,. Sai da ya kara magana,"Ko har
yanzu ban karbi Son ba Sa'adatu?? Wallahi believe me,I am madly, deeply in love
with you ...Sa'a I really Love you, en u know?? Tun farkon haduwar mu na kamu da
son ki,sai dai a wancen lokacin ban San so bane Sa'ada, nasan dai ina tsananin
kishi na ganki da gyale shara shara,,sai naji zuciya ta na tafasa,,in na tabo ki
mukai ne kawai nake samun relief.. Tunowa take da lokacin, tabbas tun ganin
Hafeez na farko ta ji sauyi a tare da ita.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[1/9, 1:43 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
32_Ya cigaba, "Kin tuna ranar da na watsa miki lemon strawberries a jiki??? Tuni
ta rintse ido dan tuna wa da wannan rana,ba zata manta ba har kuka tai,,.ya
katse ta" nasan ke a zatan ki dan tsokana nai,,Ya girgiza kai, "Ganin mai shagon
nan fa nai yana ta kallon ki sai ga kin dame Riga,ga nan gyale a kafada,,shine
yasa na tashi na harare shi yana sosa kai,kan na baki baya na watsa miki,nasan
Ummi ta gani,en dole ki nemi agaji,sai kwa gashi ta baki kin suturce jikin ki da
abayar ta,,.Jin shi kawai take..ta katse shi da" Mey zakace da Marin da kamin
kuma??Ya sauke ajiyar zuciya,, "Sa'adatu.. Taji kiran har kwakwalwar ta,.," Naga
shigo war ki kina ta wani yauki,,ga kayan sun dame ki,ga wani Wai shi gyale da
kika dakko kin maka shi a kafada,baki sa maraba da wacce ta fito haka,,ga duk
kusan ke ake kallo,,amma ke na fuskan ci baya ma damun ki,haka kika kutso taron
nan kika shigo fa,,da zaki kula,da zaki gano tsabar haushin da nake ji, hararar
ki nake tayi ko zan samu saukin zugin raina,,ina fa jin wani a yan uwan su Ummin
yana cewa wani "Woow,,she's Beautiful!! Kamar na cire babbar Rigar Aminu na rufa
miki naji,.sai dai nasan ba laifin shi bane,,naki ne,. Dan na rage zugin dake
raina na koma baya,,juyo war da zanyi naji ki kusa dani,kuma kamar ki shige min
jiki,,bazan boye miki ba,a lokacin nan ji nan kamar ma na rufe ki da duka,,dan
na tsani mace mai chudanya da maza,.ban Ankara ba naji saukar sanyi a jiki
na,,...Yai shiru tare da rintse ido,,." Sa'ada ban so tuno Marin nan da na

miki,, duk da har gobe kowa yana kallon kece kika mare ni in kika cire Ummi da
Aminu,tanan kawai na gode Allah.
Tai ajiyar zuciya,, Lalle sai yanxu ta kula da kishin da Hafeez ke nuna wa,,ya
katse ta,, "Da fatan kin gamsu zaki yafen,..yaji shiru,, Ashe kudin ya kare..
Shi yana ta zuba ko warning din bai jiba,,ya dau wayan Glo ya kira..dai dai zata
kira.. Yace" kiban dama gobe nazo gida da safe,yanxun dare yayi,. Ta kada mishi
kai,,"Ok.. Yace"Mey toh zan samu??tai Jim,dan bata gane nufin shi ba,,sai
tace*Sai dai kazo gobe,,Yace"Promise?,, ta kada kai "Promise..
Haka suka sallamar kowa ya kwanta da tunanin Dan uwan shi..barin Sa'a yau da
taji duk wwani haushi ta daina ji na Hafeez,, a ganin ta ko a haka ya barta ta
gamsu da Lalle So ne ya Jawo Haka.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[10/2, 6:38 AM] Feenat Ja'afar: BARIKI...IYAWA
33_Tun safe Zahra tai niyar gida,.ko jiran Tasleem batai ba,, tana zuwa ta zube
a tsakar dakin Mamyn nasu,, Aunty Sadiya ta kallo ta,"Lfyr ki kuwa??Kinzo kin
wani zube min ba koh sallama??Tuni ta marai rai cewa Mamyn tasu tana hawaye,,
"Mamy,,Na shiga 3 wallahi,,.sai ta barke mata da kuka,,Da jin haka ta waro ido
waje,, Ta tashi ta kamo yar ta ta,tasan dai tatsuniyar gizo bata wuce ta koki,
Amma sai ta tambaye ta" Meye kin shiga 3?? Nifa ban son wautar nan taki ta yan
fari?? Ta lafe jikin shi tana kuka,,"Mamy Wai Fa Hafeez mu 2 zai aura,, kuma ya
rasa da wacce zai hadani sai yar BARIKI mamy,, Mamyn tai Jim,ita dai dama wannan
hadin na Zahra da Hafeez kwata kwata bai mata ba,,duk da Hafeez da yake a gurin
ta,amma tasan ba abunda yar tata zata tsinta a gidan shi sai ciwan rai, toh amma
ita batta da wani power a gidan,tunda itace auta a cikin gidan su kakanin Hafeez
din,, haka itama aka mata wannan auren hadin,, gashi za'a sake da yarta tilo
mace,dan duk sauran kannen Zahra maza ne,,.
Rarrashi ta fara,,"Toh meye ne abun kuka anan Zahra?Ta sake magana cikin
kuka"Mamy Abban su fa Wai ya yarda,,Hajiya ce kawai tace bata yarda ba,, Dan
Allah mamy ki Taimaken ki samu Fodio da maganar,tunda Abban yana jin maganar
shi,,.. Ta sake fashe wa da kuka"wlh mamy ban son zama da kishiya.. Da sauri ta
kwade mata baki,,ta rike bakin tana cigaba da hawaye "Wato kaddarar ki a hannun
ki take koh Zahra?Ta hade fuska mamyn,,"Da hankalin ki kike furta irin kalaman
da wanda basuyi makaranta ba kadai ke fadan shi??tai kwafa,"Sannu autar
mata,,Toh ki sata a ranki,,sannan ki daura damarar zama da ita tun yau,.Da sauri
ta kalli Mamyn nasu,, "Anya mamy kuwa tana son ta??,,Bari Abban yazo,shi zata
tsara mishi komai ya shige mata gaba,,.kamar tasan tunanin yar tata,,sai ta dawo
mata Nasiha,,kan tana saukaka kishi,dan duk yadda ka dauki Kishiya toh fa a haka
take zuwa maka,," Ki duba ni da auntyn Ku,da yawa mutane basa gane kishiya
tace,dan tsabar muna zaman mutunci da girma ma juna..ki cire wanna akidar taki
tun wuri Zahra,,Dan kin fini sanin halin Hafeez, bare akan abinda yake
so,,sannan duk Family nan suna matukar yaba dashi,hakan yasa suka zaba mishi ke
suna ga da hankalin Ku zai zama daya..kar ki fara bata rawar ki da tsalle tun
yanzun,, tai ta mata,amma ina,ita gani take Mamyn bazata gane ba,.
Karfe 9 da rabi yana gidan su Sa'a,, ita duk daukan ta wasa yake,yai katari kuwa
Baban su yana waje,,Har kasa ya gaida shi cikin girma mawa,. Da fara'a Baban ya
amsa,,Take yaji Hafeez ya kwanta mishi,dan ba kasafai yaran yanzun suka Iya
girma ma manya ba haka..Ya kalle shi da fara'a, "Hala ka wani kake nema??Ya
sunkuyar da kai kasa cikin girma mawa,, Da halamar kunya Yace"Baba dama wajen ka
nazo,,Yace" Toh mu shiga daga ciki,Ya Sosa kai,Daga zaure ya cire musu farar
kujera,suka zauna,sai leken cikin gidan yake ko zai hango sahibar shi,,Baban ya
dan kula da hakan,"Allah dai yasa lfy?Ya sunne kai kasa cikin kunya,"Amm Baba
sunan Hafeez, muna chan kasa daku kadan, dama,Amm,Sa'adatu na gani Baba,shine
nake Neman izinin fara Neman auren ta a gun ka..Baban yai murmushi, a ranshi
yana ambaton "Allahu Akbar,,Lalle zabin shi Dana Sa'an shi Yazo,,Dan duk wanda
zai cika sharudan mulunci na Neman aure Hafeez ya fara,.Bai manta zancen shi da
Sa'a ba akan Tara samari ba na aura,,bai manta amsar da ta bashi a lokacin ba,,"
Baba duk saurayin da ya fara zuwa Neman aure na wajen ka toh ya cika sharuddan

aure na,,ka shaida hakan Baba,,nasan zaka fini sanin dawa na dace Baba..Da irin
kalaman nan Sa'an take kara shiga ranshi,, ga daga gani daga gidan mutunci
Hafeez din ya fito,,Ya kada kai, "Tabbas kayi abinda ya dace Hafeez, hakan ya
nunan daga gidan da ka fito,,Allah yasa alkairi a ciki,,.Tuni ya fadada fara'ar
shi yana sunne kai,, Baban ya tambaye shi iyayen shi,ya dai gamsu da duk bayanan
shi,sai kuma bincike ya rage..
By
Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
34_Baban ya shiga dashi ciki,yai wa mama magana,,ta fito da kamalar ta,Ya dan
duka ya gaida ta, itama da fara'ar ta ta amsa,,kan tai dakin Sa'an da ta koma
bacci,,.
Ido waje take kallon shi, tunda mama tace tana da bako ta sa hijab,ta zata Ali
ne,dan tama manta da Yace safe,,ido 1 ya kanne mata,, dai dai Baba ya fito zai
tafi,yai mai sallama,, Ya dawo da kallon shi kanta,,Ta zauna tana mai mamakin
jin sallamar shi da Baba kamar sun San juna,," Ina kwana,, yai mata wani kallo,
ta kauda kai tana murmushi,,A hankali tace"Allah sa ma kai break irin wannan
sammako,,ta dan harare shi,, yai murmushi,Tare da kama ciki, halamar yunwa..Ta
make kafada,,ya marai rai ce fuska,,"Wajen Baba nazo,kuma na dace,,harma ya ban
auren ki,harda dan duko kai a hankali kamar mai rada,,Ta kara dukar da
kanta,,kan ta tashi ta debo mishi abinci,,ta zauna,,kunun gyada ne mai cous
cous, yasha madara da lemon tsami,sai Doya da kwai,,Ya kalle ta yana nuna dakin
mama,,yana yin halamar kar ta fito,,Tai dariya,,Ya dau cup din kunun yakai baki
yana kara kallon dakin mama,ita dai sai dariya take mishi,,ya rintse ido,dan jin
dadin kunun,ita kwa da sauri ta waro ido, ya bude ido a kanta,fuskar shi ba yabo
ba fallasa,zatan ko bai mishi dadi bane,Yace"Hope ke kika dama,,ta
[10/27, 12:11 PM] 💍🛍🍬Salma🍬🛍💍: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afarSalma🍬Salma🍬🛍💍: [6/2, 5:38 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar🛍💍: FEENAT JAAFAR'S MOBILE BLOG
JUST ANOTHER BLOG

BARIKI IYAWA 5

[10/2, 6:51 AM] Feenat Ja'afar: BARIKI...IYAWA
38_Ta daga mishi kai tana sunne kai,, "Tunda Baba ya sanar dani zuwan ka da
abunda kazo nema wajen shi na amince maka,,." Hafeez, buri na ka cika a gun
Abba,,Ta kallo shi," I'm inluv with you than I ever was...I love you too
Hafeez,, Da sauri ta rintse idon ta da murmushin kunya, dan jin wata kunya da
bata San tana da ita ba ta rufe ta,, Kallon ta yake yana murmushi,, kai shikam
baiga abunda Sa'a ta rage shi ga mace da yake son aure ba..
" Kunya "
"Addini:
"Class"
Kyauu "
Da Iya kwarkwasa..
Shikam ya gode Allah, Sa'a ta mishi komai da ta so shi..
"Tnks much My Unique,,Yaushe zan turo a mini Tambaya??
Baki ta fara kunshe wa tana dariya kadan kadan,Tuni ta so zautar dashi,..
Yau sun buga luv,tamkar kar su rabu, Dakyar ta samu ta gudu gida dan magriba
tayi,,Ashe haka "So" din yake??..Ashe Haka masoya suke ji amma a baya take ganin
wautar su??..ita kam indai haka ne,toh itama sai ta sarrafa zuciyar ta, dan
gujewa so mai zafi,,Ji take kamar dama ta girma ne da son Hafeez,,.
Mama ma sai da ta gano yau Sa'a na cikin farin ciki matuka,,Dan komai ta ke sai
kaga tana murmushi ita kadai,,.
Shikam daga nan wajen Zahra yaje dan cika hukuncin Hajiyan shi,Da Tasleem ta
sanar mata murna fal ranta,Wai yau Hafeez ne yazo gidan domin ta??..
Suna zaune bayan ga gaisuwa ta kasa ce mishi komai,dan jinsu take wani

iri.,Shikam kallon ta yake yaga ta ina ta Gaza,, sannan mey Sa'a ta fita?..Ya
kada kai,, "Amm Zahra magana nazo muyi ta fahimta,. Ta kallo shi fuska
sake,,.Yace"Nasan kinji maganar ba ke kadai zan aura ba,,ina fatan tun yanxun ki
rike ta yar uwar ki tun kan azo ga batun zama,,dan Sa'adatu she's simple, baki
da matsalar zama da ita..
Tuni Annurin fuskar ta ya kau,,tai tsagal ta mike," Ya Hafeez kar muyi haka da
kai,,Ban San wata Sa'adatu ba kai na Sani,,sannan ni kishiya,wallahi kishiya na
dauke ta, ba Wai yar uwa ba..akan mey an gama magana tashin farko ka watgazan
tsari..Kallon ta kawai yake yana murmushi,, Sa'an shi kawai yake tuno wa,mace
mai Iya lafazi da kawai ci,,Akallah a haihuwar kaji zai haifi Zahra,amma dan
fitsara shi ta tasamma aka tana mishi haka..Kyale ta yai sai da tai mai Isar ta
harda hawaye,kamin ya taka mata birki.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[1/14, 6:30 AM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
39_Tuni ya hade rai,, Yace"Bafa shawarar ki nazo nema ba da zakimin fitsara,aure
na da Sa'a kuwa zan Iya cewa shi yafi zame min dole,,so tun wuri kisan inda kika
dosa,dan gaba bazata mana kyau ba,,.Nan ya barta tana ta kuka,A ganin ta magana
ya fada mata, wato ita auren ta dashi bai zama dole ba??,,.Mamyn tata ta shigo
dakin ganin Ta fito daga parlour tana kuka,.Lalle yar ta tana da aiki a gaban ta
ja,don tana son tusa kanta a inda bata kwarjini, tasan tabbas kukan ta bazai
rasa nasaba da Hafeez ba,, Gashi ta nace da sauran dangi sai anyi auren nan,amma
tana tausaya wa rayuwar auren yar tata data ki jinin kishiya...
Soyayya ake yi tsaftacacciya a tsakanin Hafeez da Sa'a, a yanxun kam ya maida
gidan su Sa'a kamar gidan su, tun yana jin nauyin zuwa har ya ware,,sai dai abu
1 dake kawo musu cikas Ali,,Ali ya nace sai Sa'a,, tashin farko yazo da Baban
shi Wai a bashi Sa'a,, kai ranar tai dariya har taji ba dadi,,sai a ranar ta
kara tabbatar da Lalle Ali ba tsaran ta bane,, duk da Abban yaso tun wuri hakan
ta faru,bai rufa wa mai gidan nashi ba ya sanar shi Sa'a Nada Miji,,sai dai a
bawa Ali hakuri,,dake shi Dattijo ne mai dattako ya amince da Allah baiyi Matar
shi bace,amma shifa Ali fir yaki daina zuwa,,duk da ko yazo ba kula shi take
ba,da yaga baci ya dawo gori,inda alkawari ai Baba bazai ki bashi auren ta
ba,kodan muhallin da Abban shi ya basu,,Take Sa'an tace"Indai wannan gidan kake
wa toh ka kwantar da hankalin ka,amma aure ne ka kara lalata shi,dan ka nunan
kai ba na kwarai bane,kuma dole mubar muku gidan Ku... gori har yaje kunnen
Baba,.Tuni ta bawa mutanen da suke mata haya Notice, ta hau gyaran gida,,shi
Baban bai zata ta dau zafi haka ba,,sai ranar Laraba bayan anyi da wata tazo Wai
gobe zasu tashi,,da fari Baban dariya yake mata,sai dai ganin ta fara parking
yasa ya tsayar ta,,"Sa'adatu ba fa Ali ya bani gidan nan ba,kinga bai kamata
muyi wa Alhaji haka ba,, tace"Baba ai ko ba gori yaci karan nan ka yarda mu
shiga gidan nan, Ina da gidan zama,amma fur kunki zama ciki,sai dai nasa
haya,Baba chan gashi na zamani,nan na kasa,ya kamata inn ka samu dama Baba kai
amfane ta,,kawai ce mishi zakai tashi zakai,daga baya ni nasan abin yi...Duk da
haka Abban bai yarda ba,sai dai kamar yadda ta fada Washegari ta dakko mai
katuwar Daf, Baban baya nan aka fara kwasar kaya,sai gidan Sa'a,, gida ne mai
daki Uku,,biyu kana na,daya katon parlour, duk da baida wani girma,amma na bulo
ne,kuma na zamani,daya dakin mai bandaki a ciki nan ta jera wa su mama kayan su
da gadon ta,tasa aka sa carpet a pparlourn da manyan tuntu,,sai fridge da
Katuwar TV,,Ita kuma ta hular da katifa da sauran tariki cen ta..Lalle gaya wa
mai zuciya,bamai Dukiya ba,,,sai da kudin account dinta yai kat..
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[1/14, 11:41 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
40_Baki sake su Baba suke kallon Sa'an,basu isa musu ba,dan har kuka ta sau

musu,,Mama ta lallabi Baban,,ta kira Fadeela ita tazo,Gidan ya musu dai dai,Dan
tsakar gida ne mai dan fadi kadan,anyi mishi siminti,suna da ruwan su,komai dai
dai sauki akwai shi,Fadeela ma tai farin ciki sosai,,.
Da yamma Baba ya sanar da Alhaji cewa sun tashi,yai hakuri abinne yazo musu a
bazata,,yai mishi Allah sanya alkairi, ai gida kam nashi ne duka,zai yi duk
yadda yaso,sai yazo ganin gida,,.yaji dadin yadda ya fahimce shi kwarai,yai
mishi kwatancen inda suka koma,.kan ya dawo yana fada ma su mama yadda
sukai,Sa'a tace Baban ya bata mukullin tsohon gidan toh,za ai mishi aiki,zuciya
1 ya bata,yana mai shi musu albarka.
Tai ma Hafeez text, cewa sun tashi da address, dan tasan zai Iya zuwa bai same
su ba,,5da rabi kuwa yazo, yana ta yiwa mama murna,,da Allah sanya alkairi,, Nan
take sanar shi ai Sa'a ce ta tada ballin sai sun tashi,ba shiri,,yai murmushi,
Yace "Toh ya kikai da yan hayar cikin??Da mamaki take kallon shi, Ya akai yasan
nata ne?,Sai da suka je parlour yana yaba tsarin gidan,komai a saukake, amma da
kyau,,yadda suka zauna a Chinese carpet din ma ya kayatar shi,ya jin Gina a tun
tun,kamar wani basarake,,nan ta sanar mishi abinda Ali Yace, " Shine na basu
Notice, bawai kora na musu ba,tana murmushi, ya kada kai, "Good,kin min dai
dai,nan din tunda ba na uban nashi bane naga kafar mutum,,Tuni ta hau kunshe
baki tana dariya,,Fadeela ta shigo suka gaisa,yana mata itama Allah sanya
alkairi,..
Alhaji yazo daukan Fadeela yaga gida,,yana ta son barka,,nan yai wa Sa'a zata ga
gudun mawar shi,,.
Ko minti 3 ba ai da tafiyar Fadeela ba,Ali yazo,Baban shi ne Wai Yace yazo yaga
gida kan suzo,,Allah yasa baban baya nan,Sa'a tace ya jira ta a waje toh,,Da
dariya suka fito,da ka gansu kasan suna cikin nishadi,in ran Ali yai dubu ya
baci,,a zuciyar shi yana,,"shifa kota ya ya sai ya samu Sa'a, atoh, yama ji da
kyau,,..Ba ko magana ta mika mishi key, Ya karba yana kallon ta,,.
Hafeez Yace" Ganan keys na gidan naku,,an bar muku shi sarkin yan gori,,en ya
zamo last da zan kara ganin kafar ka a gidan nan,, dan bazata mana kyau ba,,Suka
juya Sa'a na daga mishi hannu da shakiyanci,,ya kulu Iya kuluwa,,.
Direct Baban shi ya kaima key in,,. Washegari sai gashi yazo da kanshi ba'asi,,
Baban ya kira Sa'a,ba ko dar ta korowa Alhaji bayani,kan danshi ne ya Goran ta
musu,Alhaji ya girgiza kai, "Sa'a in banda abinki, ai ni nai kyautar nan ba Ali
ba,,Ya ajiye musu kan ya basu hakuri,tare da sanar shi zai ga Alin.
Sa'a sun gama schl,sai Attachment,Zancen aure sai karfi yake,yayin da Zahra sai
baudewa take,Da son abun Sa'a take attachments din,daga dan wannan sukai
sha'awar daukar ta bayan ta gama..
Ansa bikin su zuwa Hafeez din ya gama ginin shi,,Duk bangaren kowa na shirye
shiryen biki.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[10/2, 7:13 AM] Feenat Ja'afar: [1/19, 1:13 AM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
41_Matsala 1 da ta fara fuskan ta shine kana nan maganganu da dangin Hafeez suke
a kanta,,dan sau daya da ya taba kaita ta gano basa yi da ita,,tun daga ranar ta
kudiri wani abu a ranta,burin ta kawai Allah kai Damo ga harawa.
Makarantar zama da Miji mai mata ta bazama nema,,duk wani wa'azi mai kyau da
ma'ana, mai taken mallakar Miji Sa'a Nada shi a waya,,duk wasu littattafai da
tasan tabbas zata kara Sani akan su ta neme su,, Matakin farko data fara shine
Bincika yanayin kayan Dakin da Hafeez yake da muradi,cikin wasa sukai abinsu,nan
kwa bai son satar amsa tai ba,,a haka in fira tai dadi a wasa da wasa sai da
tasan mai Hafeez yafi so na daga abinci, sutura,color, best perfumes da sauran
su,,kan ma ta shiga ta gama karantar daga A har Z.. Tanan tai wa Zahra zarra tun
kan su shiga,ita kullum batta dabara sai ta yaya zatai Hafeez ya zama nata ita

kadai??
Duk abinda aka sa mishi lokaci toh tabbas zaizo da sannu,babu wanda yakai Hafeez
da Sa'a farin ciki, duk da Zahra tana farin ciki, amma Sa'a ce ta tsokane mata
ido,,ganin har yanxun yadda yake rawar kafa a kanta,duk da tayi nasarar sanya
dangi yadda da cewa Lalle Hafeez zai auro musu karuwa,,kuma tabbas sun yarda,,.
Hakan yasa dai dai da lefen ta a dangin Hafeez din sai yan tsirirai ne suka
kai,,yai kaya na azo a gani,duk dunsu ba banbanci,,,Ware kunya Sa'a tai ta hau
gyaran kanta da kanta,,.Tsohon gidan su sukutum ta maida gidan gyaran ta,Tun
kamin sati da biki ta kammala duk wasu jeka ka dawo na hidimar ta,,ta hada
nutsuwar ta waje guda,,dan kwarai tunda taji wa'azin Malama zuwaira ta dau
darasi,,don tabbas itama ta fahimci yawancin amare basa cikin nutsuwar su ake
kaisu gidan Miji,,kenan duk wani gyara da za'a miki kadan ne zai tasiri a gare
ki,dan komai yana bukatar nutsuwa..
Kaflas din fenti babba tasa aka nemo mata madarar shanu,dan tasan takamar da
za'a gwada mata kenan su Zahra, dangin Fulani,tasha tai wanka ..,sai da tai ta
wankan amare na Lalle kullum a daura Dana madarar shanu da turaren Durot,,,Wata
kwararriya ta samu,tazo har gidan tana biyan ta,,su fresh Nonon Rakumi, Su
ganyen Tumfafiya,tai,duk wani sirri ta nemo su ta hada anyi mata,kan satin biki
yazo in ka kalli Sa'a tamkar wata yar black Indian nan masu kyau,sai shining
jikin nan yake,ga wani dan karan kamshi da laushi da fatar ta take,,kai kace
daga Maiduguri ta fito,,Dan tun kan biki tasa wata Qawar ta yi mata hanyar wani
mai hada turarurrukan mata masu kyau da kamshi,,Dan ita akwai son
kamshi,musamman na turaren wuta..
Yau Juma'a, ta kama gobe za'a dauro auren su Hafeez da Matan shi,sun shirya
kyatattiyar Dinner,, Kowa ya halatta Sa'a kawai ake jira,,in kaga ango sai wage
baki da ido yake yaga ta ina zata ratso,,Zahra an hakimce a kusa da Hafeez, an
Gaji da kyau itama,,gashin nan an zubo shi baya,duk da taiwa Hafeez din kyau
amma shi burin shi yaga Sa'an shi,,duk sunyi waya tace suna wani room ne a hotel
din 5 mint's,,.
Hargowa da fadin MashaAllah shi ya juyar da hankalin Hafeez da Zahra,,tafi ake
mata,ganin gasu Tj yan kanan Bodyguards dinta na unguwa sunyi wankan bakaken
suite, kowa yasha bakin glass,yaran sunyi kyau matuka,sun shassha kunu su a dole
masu tsaran Aunty Sa'a, sai abin ya kayatar,Ga nan Qawayen ta yan karya da wanda
sukai Turkish suma sunsha kyau,,sanye take

Please Login or Register in order to submit comment