Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kaddamar mata,, ki
duba tun yanxu mun zama bola?ta kada kai,
"Allah ya kaimu,,.
Washegari yana fita suna fita,direct gidan su Sa'a
sukace driver ya kaisu,.zai musu suka hayaiyako
mai,, tuni jiki na bari ya kaisu,,Suka karewa gidan
kallo,nanne Wai gidan su ma,,ciki sukai,lokacin
tana brush a gindin famfo,, da doguwar Riga ta
bacci mai silik,da Maman ta suka fara cin
karo,,da mamaki take kallon su, ganin ko sallama
sun shigo gidan,,amaryar ce mai karfin halin
tambayar "BARIKI fa??ta kuskure baki ta juyo rai
hade,, suna hada ido suka ga ta bala'in yi musu
kwarjini,,a jinin ta yake,,mudin kaso mata
wulakanci indai kuka hada ido, toh sai dai ita ta
sauke maka,Allah yai mata baiwar Kwarjini... da
niyar nadar ta suka zo ko su ci mutuncin ta,,suka
sau baki kallon ta,, mace kira kamar ita tai
kanta?ji uban gashi da fagon wani guri?hmm
lalle kam Sa'a ta wuce tunanin su,,tuni ta wayan
ce wa tayi,tuni ta sau fuska lokacin da ta gane ko
su waye su,,ta ajiye cup din tana kade brush tare
da daukar mouth wash din,," Sannun Ku da zuwa
Aunty,..Hajiyan ta kalli amarya, amarya ta kalli
Hajiya.. Hee hee... BARIKI Ake fada muku,,IYAWA,,
ta kallo mama,."ina taburmar nan?baki sake ta
nuna mata kitchen,, ta tafi tana girgiza jiki,da
kallo suma suka bita..ta dakko ta shimfida
musu,,ta kallo su da murmushi,, "ya Ku zauna
man,,tamkar wasu masu bin umarnin ta suka
dawo,, ta koma daki ta sako hijab,.ta zauna," ina
kwanan Ku Aunty?a ciki suka amsa,badan sun so
ba,,Ta kallo Maman nata,"mama, baki nane
fa,,Matan Alhj Muktar mai naci Dana ke baki
lbr...Ba suba,hatta maman tata baki sake take
kalle ta da sauri,, sukwa tuni suka gyara zama
tare da sakar fuska,, tana ganin haka ta kada kai
da murmushin mugun ta,, a ranta tana "woo ni
BARIKI.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[6/2, 6:09 PM] Feenat Ja'afar: Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
14_Sai lokacin suka gaida Maman,.da mamakin
su itama ta amsa,,ikon Allah, da ganin Matan da
rashin mutunci suka zo gidan,,amma dubi Sa'a
cikin seconds da bai wuce 3 ba har ta
shasu,,kai,al'amarin yarinyar nan ita kanta tsoro
yake bata,,Hausa sunce Wai Barewa bata gudu

danta yai rarrafe,,toh gaskiya a kanta ta
Musa,,dan ta ko'ina halin ta bai kama da na Sa'a
ba,,da de fadeela ce,,sai dai in ta tuno ance
kowacce mace da irin tata kissar a ake haifar ta,,.
Kai ta kada musu,,ta kallo Maman,,tai mata
halamar ta dan basu waje,,ta gyada kai, "ni zan
fita ma,zan leka gidan gaisuwar nan da baban Ku
yaje dazun,, ta kada" sai kin dawo,, ganan abincin
ki a flaks,fadeela tayi makaranta.. Ta dawo gun
su,"sai anjiman Ku, Ku gaida gida,,suka washe
baki,"a dawo lfy,,Kanta fita Sa'a ta tashi ta dakko
musu drinks a fridge din tsakar gidan,,da cups, ta
zauna,,"Bissmillahn Ku fa,.suka kalle ta., "anya
kuwa,sanyi da safe,tai murmushi,"toh ya akai?
nasan da magana a bakin Ku,, sukai shiru,,tai
murmushi,,zama ta gyara kamar mai Tahiya,ta
dafa kafafun su,," am Aunty,, bari na fada muku
Gaskiya,, wlh ba son Alhj nake ba,,en kuma Ku
gode Allah,, shidai yana matukar sona,,sai dai ina
lallaba shine saboda abu 1,,ta nuno su da hannu,,
"saboda Ku,,dan kune matsalar shi,,kuma nayi
alkawarin taimakon shi,,amaryar ta tabe baki,, ta
kalle ta,," amma kun San mey? Uwar gida ta
girgiza kai,,"mijin Ku na kaunar Ku,,amma kun
tsaya kishi,,Baku da aiki sai tada mishi hankali,, ni
fa mata na bani mamaki matuka,,. Kuma
musamman Matan mai arziki, a gidan shi anfi
tashin hankali,, kufa kalle Ku,, da girman Ku,,ai
wlh kun wuce wannan gurin,,Ku tsaya kuyi kishi
akan mijin Ku,. Kwatan kwacin Matan Annabi (S A
W),,Ku kanku zaku dinga rage jin haushin juna da
saukaka kishin,,nan tai ta musu,tare da sanar su
Alhj ya sanar ta kom,, kuma tana tausayin shi
Gaskiya..
"Sai dai abu 1 zan Iya muku,,suka kallo ta tare da
sauke ajiyar zuciya,,Ku gyara tsakanin Ku,,Ku
zauna lfy,,idan har kukai haka,shi kan shi Alhjn
zaiji aurena ya fita a ranshi,kunga kun taimake
ni,, kun taimaki Alhaji,. Sannan kun taimaki
kanku.. Ni kuma zanji da sauran,, tunda Alhaji ya
taba fada min,mudin mace bata son shi ta furta
bazai aure ta dole ba..
Suka sauke ajiyar zuciya,, amarya tace.
"Hajiya,wlh sai yanxu na gano matsalar gidan
mu,,Sa'adatu tai magana mai kyau,, ya kamata
mu hada kai koba auren nan,,kuma dama chan
matsalar taki ce,,da sauri ta kallo ta" matsalar ki
dai,,ni nace ki shigo da fetsara? tace"Toh ai kema
ke kika yadda girman ki,,.tuni magana zata dawo
fada Sa'a ta tsayar su,, "kunga irin ta ai,,na lura
duk din kune Baku hakuri,, ni dai in Baku gyara
hali ba,wlh zana yarda da Alhaji ya turo ne
kawai,koda bana son shi,,.Amarya ta kallo ta" ke
kuma sai an gama magana ki sako wata,,ai
munce munji,,ta daga kafada.. "Ku dauka ni banni
matsala,, Yanxu matsalar ta Ku ce kuda mijin
Ku,,in kunji bayani na kun gyara kuga mai kyau,,in
kun cigaba ta kwabe muku..toh wlh Ku zargi
kanku,ta mike,"zan shiga wanka,,suma suka
mike.." Mun tafi, sai kin jimu,,tai musu yake,"a
gaida gida,,duk jiki yai sanyi suka fice.. Dai dai
fadeela ta dawo,,ta kare musu kallo har suka fita
kan ta dawo kan Sa'a.., "su kuma daga ina kika
yayimo su?ta tabe baki,," Wai su nan da rashin

mutunci suka zo,,any way,naga sun
russuna,,aikina zai zo da sauki da halama.. "So
nake a siyasar nan nai motar kaina a wajen
Alhajin nan,,fadeela ta zaro ido" mota??tai
murmushi, "karamar Alhaki ba,,ke Wai da ina
sakar wa kana nan Yan iskan Alhazan nan da
yanxu ina da motoci wlh,,yanxu haka ina da
alkawarin gida a kasa..fadeela ta kada kai" ai ni
tsoro kike bani,,wlh wannan ba Sana'a bace
Sa'a,, ina gudun kar wataran ki hadu da dai dai
ke,ko ki samu mai lakada miki duka..tai mata
wani kallo "duka?mtsww wlh kina ban haushi,,ko
kin manta duk inda zansa kafa tare nake da
sojojin daba?? Ta waro ido.." Daba Sa'a? Tai
murmushi "lalle da sauran ki fadeela,, kin ganni
nan.. Ta nuna kanta" wlh na Iya taku na,,duk inda
nake akwai masu take min baya tun daga safe
har yamma,.a lokacin yara su karbe,,kamar yadda
ake biyan ma'aikata a wata,nima haka nake biyan
su..kuma nasan ba wanda ya sani..kema sai
yanxun..ta kada mata kai.. "Shi yasa nace tsoron
ki nake ji nima.. Sa'a akwai masu mugun
nufi,,masu jefo asiri..da sauri ta daga mata
hannu" ke ni ban son jafa'i,, na rike Allah, babu
wanda ya isa ya min komai wlh.. Tuni ta hau
jaraba tai bandaki.. Fadeela ta girgiza kai.. Sa'a
bazata gane ba,, amma tunda ta saka Allah, ta
gama komai..
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/26, 2:12 PM] Feenat Ja'afar.
BARIKI...IYAWA
15_Sai bayan la'asar Alhaji ya koma gida,,yasan
da zuwan Matan shi zuwa gidan su BARIKI a
bakin Bala driver,, sai dai da mamakin shi da ya
shigo gidan An hadu da yara ana kallon
Namamajo ana ta cin dariya,,kowacce taci
Ado,tunda yake,abinda bai taba gani ba kenan a
gidan shi anyi,,Wai a hadu,uwar gida da ya'yan ta
da amarya da Ya'yan ta a waje daya..tab lalle ya
fara ganin sauyi,,dan Babban burin shi dama
Matan su hada kai, ya samu ya'yan shi ma su
hada,,amma ina,ya kasa tsawan shekara 6,.sai
gashi a abinda baifi kwana 3 ba BARIKI ta fara
saita gidan shi,,toh ita kwa mey ta fada musu
haka?da wani harshe tai musu magana wanda
shi baiyi ba??
Ya kada kai yai sallama,, da fara'a suka amsa
yaran suka taho da gudu mishi sannu da
zuwa,tare da karbar kayan hannun shi suka ajiye
gaban iyayen,,.Matan suma suka mai,ya amsa da
kyar,,dan dole ya ga sauyawar su koba yau
ba,,yai daki,,amarya ta kallo Hajiyan,, "mu bishi
muji.. Suka ran kaya daki,,yana kokarin cire
babbar Riga suka karaso,.karba sukai dukan su
suna cire mishi,,ya tsaya baki sake yana kallon
su,,
Uwar gida tai murmushi," Alhaji muna fa sannu
da zuwa,.ya kalle su tukun ya tabe baki,, "Ku Wai
nan campaign kuke ne komai?suka kalli juna"
name Alhj? Yai murmushi "na karna auri Sa'a,,
zasui magana ya tsayar su,, " Ba abunda zai

hanani auren Sa'a in fada muku,.gobe ma za'a
kai kayan tambaya.. Da dariya suka fashe
mishi,harda tafawa., tuni ya fara muzurai,, kadde
fa sunyi wa yarinyar mutane wani abu??suka
kallo shi, "Na BARIKI manya,,inji amarya,kai kace
mana tusa mata kanka kake bamu Sani ba? Ashe
ma ba son ka ake ba.. Ya bata rai" inji wa?suka
hada baki"BARIKI.. Yai murmushi,,"eh a haka zan
aure ta,, indai zata bani farin ciki a gida na,, ya
wuce bandaki ya barsu tsaye,,zama sukai jiran ya
fito.."aha Wai Baku tafi bane?? Suka kalle shi,,
uwar gida tai gyaran murya.. "Alhaji,, ya kallo ta"
eheem,.ta gyara zama"wlh ko ba aure mun gyara
zaman mu,, kuma koda aure baza mu saba
ba,,kai hakuri, munsan mun bata ma a baya,,
amma wlh gaba bazai kara faruwa ba,,kallon ta
kawai yake ya harde hannu,,tunda suke.basu taba
sanar shi haka ba,,. Amarya ce ta katse shi,.
"Nifa dan Allah nayi,,wlh kama daina cewa dan
zaka auro wata BARIKI.. Ehe,.inma ka auro ta in
baka Sani ba Toh yanxu ka Sani,.uwar gida sai
daga mata hannu take halamar tai shiru,amma
ina,dan fa ita yar gaba gaba ce,, tace" in baka
Sani ba ka Sani"MATA UKU.. GOBARA(Na Mrs
Jabo)Ce,,ehe,,gwara ma kai Hudu,.atoh,. yace
"kun gama??uwar gida ta kada kai,"toh koh aman
Wuta ne saina auro Sa'a., tashi tai" Hajiya mu
tafi,,kai kuma Allah ya taimake ka..yace"Amin,,
Suna fita uwar gida tace"Amma kin kwafsa mana
fa,,tai kicin kicin.."Hajiya yi hakuri, wlh haushi ya
bani,, kamar muna ziga shi.. Yana jiyo su ta
daki,,.. Da dare ya samu BARIKI.. Sai murna
yake,yau kam ta biya shi,,yaga abinda bai taba
gani ba a gidan shi,,tai murmushi,"toh Allah yasa
sun gyara kenan,.yace"Amin,. Amma Sa'a, nifa da
gaske nake son ki fa,, wlh jiya da tunanin ki nai
bacci..ta kalle shi tare da yin fari da ido.."Aiya
Alhaji,, ina da tsayayye, sai dai baya kasar
nan,PHDn shi in ya dawo muna da alkawarin
aure..yai murmushi "anya Sa'a? Ya kada kai" Any
way,, yanxu dai bamu tsadan ce ba..nawa kike ga
zan baki?ta rausayar da ido,, "Alhaji masu
gari,,Ashe ana cini ki kuma daku?yai murmushi,
itama tai,..su BARIKI anso yaudara,,, tace" Ai
zamanin siyasar yanxu da abunda ke hannun Ku
manya ake kyauta ba cini ki ba.. Yanxu muna da
kamar Ku a centern nan amma Bariki bata ko
motar hawa..bare na samu ta raly..ta kanne mai
ido 1..tuni ya hau washe baki,, lalle BARIKI,harda
ke a yan campaign din namu Ashe??tace
"kai,sosai, ai partn mu daya..tuni ta hau tsara shi
tana kara kwadaita mishi kujerar da yake nema ta
senator.. Dan dadi bai San ya mata alkawarin
mota ba indai ya hau mulki.. Kamar gaske ta
kallo shi da mamaki baki sake.." Alhj daga
wasa??yai murmushi.."karki damu.,ai irin ku
muke nema,,bare gaki da mutane,.indai kuka
mana campaign yan partn mu sukai jama'a zakiyi
mota..inkwa banci ba,,akwai wani karamin gida
na a bayan layin nan,daki 2 ne,.na mallaka miki
kodan saita min iyali da kikai..Tuni
tace"Auxubillah, In Allah ya yarda ma kaci ka
gama..yai murmushi"Toh amin sa a,,"Allah dai ya
ja mana zamanin Ku Alhaji,, ni kuwa indai haka

ne,kar kaji komai, a duk arear nan kune zakui
wining..ko baku sau kaya ba..yace "A zama
musau kaya.. Kai a hannun ki ma zai sauka,ta
dafe kirji. " Allah Alhaji?ya gyada kai.,"Alkawari
ne..tai murmushi.. Bai bar wajen ba sai 9 da 15..
Da haka auren Alhj ya tabalbal ce,,in kaje gidan
shi gwanin sha'awa.. Dai dai da abinci tare
suke,,duk sun fatattaki qawayen su yan ziga..
Suda Kansu sunji dadin zaman nasu..yadai
wayance a cewar ya fasa auren Sa'a dan bata
son shi..suka hau kuwa.
Sa'a ta shiga makaranta, inda take karantar Mass
communications., lalle tana da sha'awar hakan
tun ba yau ba,, kamar yadda Alhaji ya alkarwan
ta lokacin campaign nayi saiga katuwar mota a
kofar gidan su Sa'a da sassafe,,lokacin tana ta
aikin bacci,,baban su ya shigo dakin nata.."Ke
Sa'a,.. Sa'a.. Ta tashi a kan sallaya tana mistsike
ido.."Naam baba,.ina kwana..yace"biyoni
tukunna.. Tuni ta ware.."Baba Lfy?ya fita tana
biyo shi,, turus tai a kofar daki,,ganin yadda ake
shigo da kaya..su fridge kana na,keken
dinki,keken saka..turaman Attamfa.. Buhu buhun
su shinkafa da sugar da sauran tarkacen kayan
campaign... Tace "Malam daga ina haka?ya kallo
ta. " yauwa da drivern mai gida muka zo..Alhaji
Muktar.. Shi yace a kawo miki..tuni ta sau
baki,,har ga Allah bata dauki zancen da
mahimmanci ba,asali ma ta manta da zancen
tana ta aikin karatun ta..oh baki bai ba,, yanxu
taga uban da zai koya mata campaign,,ita da ko
zabe bata taba fita ba bare campaign...tab shiga
3,kishiya maiya,, Miji Barawo..
Baban ne ya katse ta, "mey kenan haka ke nufi
Sa'a?? Ta kallo shi ta fara inda inda..ya dakatar
ta" Kinsan bazan taba yarda da wannan halin ba
koh? Siyasa a gida na?kuma Wai kece shugaba?
mamata mey kike son zama da baki zama ba?har
gida gare ki fa,,ta kallo shi,ta marai rai ce "Baba
wlh ban zata da gaske yake ba,, amma bari zan
mishi magana.. Amma koni baba mey ya kaini
siyasa anan garin..kai hakuri.. Mama da ta fito
itama ta sau baki..ganin uban kaya a gida..ya
kada kai" ni zan fita.. Ta dan duka"a dawo lfy
Baba.. Yai murmushi, "Amin,Allah muku albarka..
tai murmushi" Amin Baba..ya kallo mama.. Mu
min tafi..da baki take nuno mata Wai ta raka shi
zaure..Maman ta mata dakuwa "yar kare..kai
Sa'a.. Allah shirye ki.. Komai zage wa take ta
nunawa uwar ta..ko daki baba ya shiga in suna
waje ta dinga," mama kije man,,inkwa zai fita ta
dinga sai ta raka baba zaure..BARIKI
Duniya...Lol.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[6/2, 6:19 PM] Feenat Ja'afar: [12/26, 11:40 PM]
Feenat Ja'afar.
BARIKI...IYAWA
16_Daki ta shiga ta kunna waya,kan ta danna
calling.. "BARIKI a Baku naku daban,,tai
murmushi, "Alhaji ina kwana," lfy lau,. Ya karatu?
tace "Alhamdulillah, " ya kaya sun iso koh?ta

kada kai,"sun iso,,Sai dai fa Alhaji da matsala,,
yace"matsalar mey Sa'a?koh sunyi kadan ne a
karo miki?Tai Jim"Alhaji ba haka ba ne,,ni fa Alhj
da wasa nake,,wlh ban taba harkar siyasa
ba,,kaga kar nazo nai muku ba dai dai ba..ya
gyada kai,, "Bari zanzo anjima da yamma,,ta kada
kai" Ok,,bye..
Tai ajiyar zuciya.. Bata Iya cuta ba,bare ace ta
Saida tace tai campaign din,,gwara yazo yasan
nayi dasu..
Da misalin karfe 5 yazo,,bayan sun gaisa ya dau
waya ya kira wata mata tare da mata kwatancen
inda yake,,ba'a jima ba tazo a motar ta ita da
wata yar unguwar yar siyasa,,Ya gaba tar mata
dasu,"sune mataimakan ki,,ganan shu gabar Ku
ta unguwar nan duka,,zata tsara miki yadda ake
komai,,karki damu,ba Wai za'a fita dake
campaign bane fa,,I trust you ne kawai, so ki rike
kayan a gidan nan,,naki kawai ki bawa wanda
kika tabbatar bata da karbi,kuma tana da
kuri'a,sannan kuma zata dangwala mana,, ta
kada kai "Ok,nagode Alhaji,, ya Ciro kudi bandir
3,yaba Sa'a 1 mai motar 2,,dakyar in zamu kara
haduwa,.. Dai dai nan su Aminu sunxo wuce wa
suka tsaya,, suka fito tana ganin su ta hau fara'a,
tai sallama da Alhaji,, "Oh Aminu manyan
kasa,.yaushe a gari??oh sorry Assalam Alaikum,,
yai murmushi" Walaikum salam,," BARIKI
manya,.da sauri abokin nashi ya dago Tare da
sake kallon ta,. Da tunda yai arba da ita yaji
zuciyar shi ta tsanan ta bugawa,. Yanxun ana
kiran ta da BARIKI yaji wani damm..yai tunanin
ko ya dace da DREAM GIRL (na Deeja Abdull)din
shi,,dan yana son mace mai Aji, kwarkwasa, da
iyayi da kuma addini.. But tashin farko a kira ta
da BARIKI? Lalle bata kwarai bace..
Katse shi tai"ina yini.."BARIKI sai kin jimu,Alhaji
ya bamu numbern ki,,ta kada musu kai tare da
dagawa Alhaji hannu.. Tuni abokin Aminu ya kara
kulewa,.dan da ganin dayar kasan muguwar yar
BARIKIN asali ce,,gaisuwar da bai amsa ba kenan
yaci mur.,tamkar bai taba dariya ba,, itama bata
bi ta kanshi ba ta koma ga Aminu,, "Lalle BARIKI,
tana fa kai miki mutuniyar nan,harda Su Alhaji
Muktar yau a gidan nan??,,tai murmushi karo na
2 ta kallo abokin nashi,, tuni ya dauke kai,,ta tabe
baki,," wlh aiki na mishi,kadai gane,kuma sai ta
rufta dani,, ta wani marai rai ce mishi,,n wlh i
don't know what do?? Ganin yadda take wani
marai rai ta ta kara bawa abokin nashi haushi,.
Ya kallo Aminu, ka saman a mota,,ya kallo ta ya
watsar tare da harara yai gaba,,take itama ta
dauke shi ta yar,,harda dan tsakin ta kadan,,"ban
San ya zanyi da baba ba,,Aminu daga wasa
mutumin nan ya kawo min kayan campaign,,
yanxu fisabilillahi ina ni ina siyasa 4 God
sake,,dube ni fa,,ta fara gyara Riga, dama
doguwar Riga ce a jikin ta sai mayafi data
daura,,Aminu yai murmushi, "Yanxu da abinda zai
gagare ki dama??ta kalle shi,," no ka gane,
wannan da ban ne,en kasan bansan shudanya da
kowa,.Shima wannan lallaba shi nake ya samu
yaci ya sallame ni da mota..ya waro ido "mota
Sa'a? Ta kada kai tana mishi wani feffekara,,"

hasko ni Kaidai,,"kuma kin yadda?ta kada kai "na
yarda,.yai murmushi, "yan siyasa fa basu
alkawari, da sunci suke manta da kai," No wlh
wannan na daban ne...horn suka jiyo,,ya kallo ta
"toh sai zuwa na 2,.tace" ina Qawata?ya kada
kai,"chan muka nufa ai...tai murmushi, "da
kyau..yace" au abokina ne,,tun satin chan ya
dawo,bamu hadu ba sai yau,nasan baki san shi
ba..munxo wuce wa na ganki nace mu tsaya mu
gaisa..ta tabe baki,,Da" ganin shi dan raini ne
wlh,.kai hakuri fa,atoh.. Yai murmushi,ai afuwa?
Ke dai sai nazo karbar kaso na,ta raki shi har
bakin motar.."Ok,see yaa,.ta dago mishi yatsun
ta,, yai kwafa,,Aminu ya kallo shi,, "ya dai? Ya
tabe baki"Amma dai yarinyar nan yar raini ce
daga ganin ta? Take Aminu ya tariyo itama nata
zancen" Da ganin shi dan raini ne..sai yai
dariya,,.ya kallo shi tare da Harar shi"dariya na
baka koh?ba kaga Harar da take min bane?ya
kada kai, "na gani,,amma kai ka fara mata
ai,,Sa'a na San tsaf,in an mata saita rama.
Baka Santa bane,,amma Sa'a,, hmm ta kece raini
ce wlh,,jin shi kawai yake, amma ya kasa tan
kawa,, take yaji haushin yarinyar ya dadu,,wato
har a kira ka da sunan BARIKI alfari ne ka
amsa?? Mtsww yai tsaki,,Aminu ya kallo shi,," ya
akai kuma? Indai Sa'a ce yi hakuri, abar zancen
ta.
"Yanxu muje na kaika wajen Ummi,kaga
hadaddiyar Babyn da zan aura,,.ya kada kai,
shikam bai fiya magana ba,,Aminu ne mai surutun
tsiya.
Ummi ta fito itama duk kusan kiwon Sa'a ne,.
Dan tare suke schl yanxun,, itama akwai iyayi,sai
dai bata kai Sa'an ba.."
ya gaba tar mata da abokin shi Hafeez, da fara'ar
ta tace"a yau kam naga Hafeez,, yau she a
kasar?yai murmushi, satin chan.. Ya shirye
shirye?biki ya karato,.ta kalli Aminu ta sunkuyar
da kai kasa tana murmushi,.a toh da dan dama
dama,tunda ita tana da kunya,a ganin shi sun
ban banta da Sa'a Qawar ta, dan shi kam yana
son mace mai kunya,,.
Anyi siyasa lfy,dakyar baba yabar ta a gidan
ma,,Allah cikin ikon shi Su Alhj Muktar sunci
zabe,Shima ya samu hawa kujerar senator,, randa
za ai walima har BARIKI Matan Alhj suka
gaiyato,,.sai dai yau har wata da hawa kujerar
senator ba mota ba lbrn ta,har ta fidda
tsammani,,.
Yau bikin su Aminu saura wata 3,.su Sa'a kirjin
biki,,taje gidan su Ummi zatai mata rakiya
siyayya super market,,. Suna tsaka da zabe
zabe,tayi gefen cosmetics tana zaba Ummi na
bata basket tana zubawa, sai dariya suke dirka,,
gaba daya hankalin ta yayi kan zancen Ummi,, ta
mika hannu zata dau turare bata kula da mutum
a tsugune zai dau abuba takai hannu,,da
tsautsayi,gwan gwanin turaren role on na nevea
ya fado kanshi yana dagowa,, da sauri ta sa
hannu a baki kan tace" am really sorry pleas..tai
shiru,take ta hade rai, shi kwa ba tare da ya dago
ba yace"No,it's Ok,.."Sa'a meya far..jin an
ambaci sunan wace yake haushi,,tuni Shima ya

hade rai"kina kallon ina kike jifo min abu kai,,tuni
itama ta kankan ce ido,,"ina kallon ka ne,,yai
tsaki, "au,haka ma zaki ce? Ta tabe baki,, zata
wuce yasha gaban ta,, " na fiskanci yar rainin
hankali ce ke,,inba haka ba..."Hafeez,, mey ya
faru?Sa'a? Tuni ya ware,,"a Ummi,,ta kalle su
duka"Naam,Hafeez, ya akai ne?meya faru,,yai
murmushi, "no ba komai,,ya Aboki na,, Sa'a tace"
uhmm,ta wuce gaba,,ya bita da kallo,."Ummi zan
wuce, koh kin gama?tace"eh mun gama,bari mu
biya,,suka jera suka je wajen biya,,ya ajiye
nashi,,kan ya kalli wajen mai kirgen"nawa ne
kudin nasu?ta kalli Sa'a "tare kuke har ita,. Ta
kallo ta" wa?Allah sauka,hanyar jirgi daban ta
mota daban,, tana mai wani kallon 9 saura
kwata,tuni ya kule,,yace"da ke zan biya wa?ya
kada kai, "u must be jocking,, yai mata wani
kallon raini,, zata tanka Ummi ta sako baki" Wai
kun San juna ne hala?
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/27, 12:34 AM] Feenat Ja'afar.
BARIKI...IYAWA
17_Ta maka mishi harara kan ta koma kan mai
kirge,,"ki fadan kudi na ko na bar muku kayan
Ku,,mai kirge tai murmushi,, ganin fadan nasu
abin dariya,,ta fada mata kan ta kallo Hafeez
Shima ta fada mishi,, ta dakko kudi ta bata,. Ta
suri kayan ta zatai gaba,mai kirgen kudi
tace"hala dai fadan nan na masoya ne?? Ya kallo
ta da sauri kan ya kalli Sa'an da ta juyo "dawa?
da waccen ne masoya,,?yaja tsaki." Dan Allah
ban chanji na kan ki Sani amai,,tuni ta kullo ta
karaso.,ka kallen da kyau,,kasan ni ba irin Matar
Ku bace,,ke kuma ki Iya bakin ki, dan he's not my
type.. Ummi da tsabar takaici ya ishe ta,,ga shi
har sun soma tada musu jama'a, tuni tai waje
taja Sa'a,, da sai bambami take,,ya fito kan ya
kalli Ummin "zo mu wuce man,,ta kallo sa'a" kiyi
hakuri kizo ya sauke mu,,"kut,. Ummi,jeki,jeki
kawai, na gode da rakiya,. Amma bazan shiga
wannan akwarabar motar ba,,muka kalli mota
nida Hauwa,,Lalle Sa'a, kin so kan ki,,shikam
dariya ma ta bashi,, "Ummi,ki shigo kawai mu
tafi,,ta kalle shi, ta kalli Sa'a, in ta shiga ta shiga
3 wajen Sa'a, ganin yadda take cika da
batsewa,,." Kai hakuri Hafeez, inna barta ba
dadi,ya daga kafada.."sai gani na 2..sukai
sallama ta dawo gun Sa'a,, yazo zai wuce ya
zuge glass,, "sai a hau ta haya,.tai mai gwalo" eh
dai baza a shiga ba,.ya sauke glass ya wuce..
Tace"a sauka da nauyi..Ummi ta kallo ta,, "Sa'a,
lfyr ki kuwa yau?meye ya hada ki da haffex har
haka da zafi?wannan ai fadan yara ne wlh,..ta
dallah mata harara," Dallah rufen baki kema,,Wai
ke ga dadi saurayi,,. "Nan har hakuri na bashi,,ta
shagwabe fuska kamar mai shirin kuka.." Wayyo
haushi,, da nasan shine,da duk kayan wajen zan
rikito mishi aka,,Ummi ta kallo ta lokacin tana
tsaida mai taxi.."Toh naji muje,,zanji komai wajen
Aminu ai,,amma dai kun bar abin fada, kuma
shagon zuwan kine kinsan?tace"Toh ina ruwa na,,

inna zo kar su siyar min..ta bude mota ta shiga..
Har akaje gida bambami take.. Kai ba wanda ta
taba chachar baki dashi a girman ta sai wannan,,.
Da dare akace ana sallama da Sa'a, ta kallo
yaron da masifa, kace"Baza'a zo ba,, mama da
fadeela suka kalle ta,,tun dazo take dacin rai,,yaro
yace"kai,Aunty Sa'a,, dan bakiga waye bane,
tace"waye,,"senator fa,. Da sauri ta zabura.."Khali
ban son karya fa..yace"ba kince ince bazaki zo
ba,ta harare shi,"dallah da wasa nake,,maza kace
ina zuwa,gobe kazo in baka chocolate.., amma
kamin nan, da mota nawa yazo??yace "2,ta doka
tsalle ta dire," wayyo niii...tuni ya hau zigata
kamar yadda suka saba yi mata a unguwa.."in kin
ganta wata karama mey kyau,,ko pikanto naji ana
ce mata..,tace " Toh naji,..da sauri tai daki,ta
yayumo gyale,,ta gyara fuska.. Mama da fadeela
yan kallo..fara'a kamar gonar audiga tace"mama
bari na leka..kai kawai ta daga mata..Tana zuwa
zaure ta nutsu,,ta dan leko,,ya hakimce a wata
dalleliyar bakar jeep,ga wata karama a gefe,yana
ganin ta ya hau fara'a, ta karaso, "badai Alhaji
nake ga ba?yai murmushi, "BARIKI da kanta,,tai
murmushi kan suka gaisa,,yadda bata nuna mai
komai ba yaji dadi,.ko irin zalamar nan.." Ai
hakuri an jimu shiru,, tai murmushi, "Ku yanxu
aikun shiga sahun uziri,,Yace" haka ne,kika ji
bayani shiru.?tai murmushi.. "Alhaji name fa?yai
murmushi, wato sai an nuna mai hali?hannu yasa
a aljihu,," Ga nan alkawarin ki,tun dazu take jiran
ki,nine yanxu na iso,kan wanda ya kawo ya
tafi,,baki sake take kallon shi kamar gaske,,"Wai
Alhaji da gaske?ya sha mur,"na taba miki wasa?
mu kullin ta karba,baki sake take kallon key
in,,"Alhaji da wace kalma zan gode maka?yai
murmushi.. "Sa'adatu, gode Allah kawai,,sai dai
har yanxun na kasa fidda ki a raina,,tun ranar
chan Dana ga saurayin ki yazo na saddaqar,, ta
kada kai" Aiya Alhaji,,kai hakuri,ya girgiza mata
kai,"no karki damu,,kin burge ni da kika rike mishi
alkawari,, kodan hakan nima yasa na cika miki
naki alkawarin, dan ina son mutum mai rike
alkawari da mahimmanci,,. Sun dan jima sukai
sallama ya tafi..tana gani yai kwana ta zufa da
gudu gida..
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[12/27, 12:05 PM] Feenat Ja'afar.
BARIKI...IYAWA
18_"Wayyo Allah na, Mama, mama,tun a zaure
take kwada mata kira,,da sauri suka mike dan
sun tsorata,, tana shiga ta rukunkume
Maman,,"wayyo Allah mama maidani ciki,, wayyo
Duniya sabuwa.. Mama ta dago ta,,"Sa'a murnar
meye wannan haka? Dagowa tai harda hawayen
farin ciki,, ta miko mata mukulli tana tsalle,
"mama mota,,wallahi mota nayi sabuwa dau a
ledar ta,,da sauri Maman ta kai hannu baki ta
rufe" Sa'adatu mota??da sauri tace "mama Ku
leko kuga wlh,, fadeela da mama suka bita a
baya,,ganin motar yasa mama kusan zube wa,,ita
kam shikenan karyar ta ta kare,,acikin 2 dole da

daya,,ko dai Sa'a ta yar da mutuncin ta? Ko
kuma a yayime ya yimen ta ta kwaso dan yankan
kai,,ganin Maman tayi shiru yasa ta dauka ko
yadda ne batai ba, da sauri tace "mam ga nan
takaddun malkakar ta in baki yarda ba.. Kai ta
girgiza mata,. Kan tace"muje gida Sa'a,, ta kallo
fadeela da sai zaga motar take da murna,,suka
ran kaya gida,,dakin su taga Maman tayi suka
bita chan,,ta zauna a kan gado"mama lfy?Maman
ta sauke ajiyar zuciya, kan ta kallo Sa'an "Ku
zauna ni kam,,suka zauna, ta sake kallon su"
Sa'a, ki dubi Allah ki fadan Gaskiya, ta waro ido
"wlh mama da gaske nake fa,ta girgiza kai, " Sa'a
ba wannan ba,, kin tabbatar ba mutuncin ki kika
yar aka baki mota ba koh?da sauri
tace"Subhanallah mama,,wlh Tallahi alkawari
yamin in sunci siyasa zai sai min mota,,da akwai
aikin da na mishi,wlh mama,,ta girgiza kai,
"yanxu Sa'a bama wannan ba, mey zan cewa
Baban Ku in yazo?itama sai yanxun ta tuna da
baban su,tai shiru,,ana haka sukaji sallamar
shi,kowa yai tsam,daga inda yake y tsaya a
kofar,a tunanin shi ko bako sukai,,Maman tace ya
shigo ba kowa,,ya bude labule" lfy kukai tsumu
haka?motar waye a kofar gida?ya zauna suna
mishi sannu da zuwa,,kowa sa kallon juna
yake,sai da ya kara tambaya "munyi baki ne?
tukun fadeela tace" Baba ta Sa'a ce,, tuni ya
dauke wuta,,ya kallo Sa'an,, "Toh a ina kuma ta
samo mota? Sukai shiru,Yace" dake nake,ta hau
inda inda,, "umm..amm,ba..bani akai fa Baba, ta
wani marai rai ce mishi kamar zatai kuka,, yai
murmushi" nasan wataran sai sun fashe dake
Sa'adatu,, ta zaro ido "Mey za'a su fanshe dani
Baba?? Ya sake murmushin takaici kan ya kallo
Maman sun,," Bissmillah man,,ya tashi ya fita,,
mama ma ta bishi,ta kallo fadeela. "Mey fanshe
wa Wai take nufi fadeela? Wai kuna nufin haka
banza ba'a kyauta sai anci moriyar ka?fadeela ta
kada mata kai" ana yi Sa'a,, amma ba irin
wannan ba,,fisabilillahi a wannan marar waye zai
baka kyautar mota haka kawai?? Ta kada kai, "Ok
na gane,,wato Baku San ma abunda zan Iya¿da
wanda bazan Iya ba koh?,, tashi tai tai waje,,a
bakin kofa ta tsaya tana sallama,, Maman tace ta
shigo,,ta kalle su duk sun wani cirko cirko.. Ita
abun ma dariya ya fara bata,,"ni

Please Login or Register in order to submit comment