Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaki tafiya,.Baba Gashi Ba wanda ya Sani ko a gidan su
Zahran,.Zan sa hannu kawai gudun Kar abinda ake gudu ya faru,..Yace"Gashi nan
zuwa,..
Tunda ta fara wayar zahra take kallon ta tana hawaye,.Sa'a wace iri ce??..Mai
saka alkairi akan sharri??.. Tun samun cikin nan kullum sai ta mata gori akan
shi,.Ta wa Sa'a abu dayawa a zaman su,.Duk da zata rama,. Ga niyar ta ta zuwa
wajen malam.,amma Sai gashi yanzu ita ke dawainiya da ita harda hawaye,..Wani

irin kuka ta saka mai cin rai,.
Kila ma Allah ne ya kamata da hakin Sa'a, ga fitar da tai ba tare da izinin
Hafeez ba,Gashi ta kuma tsallake iyakar Allah,.
Duk da ta gude Allah da ta gudo da Kila achan ma zata mutu a gadon Boka..
Kuka take Sa'an na aikin lallashi,ita a zaton ta Zafin ciwo ne,.it a ranta tama
manta da Zahra kishiyar ta ce,gani take tamkar Fadeela ce a gaban ta a haka,ga
ciki yai sama ba halamun zai sakko kasa...Hawaye take tana lallashin ta,."Zahra
kiyi hakuri kiyi shiru,InshaAllah yanzu za'a shiga dake,.Ina tsoron sa hannu ne
alhalin babu wani Babba a kusa..
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[1/29, 2:11 PM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
65_Amma bari na fado wa Dr sai su fara shiri.,kai ta kada mata, ta bita da kallo
har ta fita,.Ba'a jima ba sai gata ta dawo,tace "Ga nan Baba a waje,.ki daure ki
samin numbern ko mutum d'aya ne a gida,Ta mika mata wayan,.Iyanzu tama daina jin
ciwo,sai Sai abinda ba za'a rasa ba,.Numbern Mamy ta bata,.Ta tashi,Kamin tai
dailing ta ruko hannun ta,." Sa'adatu, juyo wa tai kan ta amsa,,.ta kallo Nurses
din,"Dan Allah sisters Ku dan bamu waje,.Suka kada kai sukai waje,.Zama tai tana
kallon ta,. Hawaye take,."SA'ADATU dan Allah ki yafe min duk abinda na
miki,.Ashe da gaske yar uwa kika dauke ni,.Nasan hakin ki Dana Hafeez ne yake
tambaya ta yanzun,.Nasha binki da sharri kina tsallake wa,.Gashi yau har ta
kaini da aikata Babban aiki,.Wanda nasan yau inna mutu wallahi wuta zani
Sa'adatu... Kuka ta kara fashe wa dashi,Da sauri Sa'an ta ruko ta,. "Zahra ni
baki min komai ba,. Inma kinyi wallahi na yafe miki,.Amma ki Sani.,Ba'a yanke
rabo da Rahmar Allah, Kar ki kara ambatawa kan ki wuta Zahra,..
Murmushi tai wanda yafi kuka ciwo,." Sa'a meye hukuncin wanda yaje wajen Boka a
wajen Allah??.Ta kallo ta,. "Boka Zahra,.Allah yai mana tsari dasu,. Tace"
Amin,.Sa'a jiya da yau naje gun Boka, tare da taimakon shaidan da Muguwar
Qawa,.Sa'a nayi shirka wa Allah Alhalin nasan hukunci,. Sa'a Bani da sallah ta
kwanaki Arba'in,. Ga tsinuwar mala'ikun Allah dake bina har na dawo dan ban
tambayi Hafeez ba,.Taya in na mutu yau,zan ce ina Aljanna??,.Taya ya Sa'a.. Nan
ta hau bata labarin yadda sukai da Shi.,da tafiyar Jummai da gudowar ta har zuwa
Ganin da ta mata,."Allah kadai ya cece ni a yau,da Tuni na tafka kuskuren da har
na mutu bazan Iya goge wa ba.,.Kuka take kamar ba ita ke labor ba,.Da tsananin
tausayi Sa'a ke kallon ta,. "Ki gode Allah Tunda baki yarda dashi ba,.Sannan ki
gode Allah Tunda kin tuba kin kyautata niya,.Allahu Gafurur Raheem ne Zahra,.
Tabbas kin Tafka kuskure, Amma baki idda ba...
Shigo war Dr ne ya katse su,." Ga nan Baban ya sa hannu,.sannan ya kira Baban
Mai gidan,.Kar Ku damu,Lafiya za a fito da ita.., Yace Sa'a ta fita zasu kimtsa
Zahran dan wuce wa Operation Room,. Da kuka Suka rabu da Zahra,ita fa gani take
in ta shiga bazata fito ba,.Burin ta tace wa Hafeez ya yafe mata..
Tana fita Abba Yace"yanzu na kira shi Alhajn su Hafeez din, Sai Ku kimtsa,Ganan
na basu advance kan a fito da ita,dan 10k kawai gare ni a gida.., Ta kada kai
"Baba mun gode,.Bari naje gida,dan dakko kayan ta da abin bukata.. Ya kada
kai,.. A hanya Suka hadu da Mama,ta fada mata inda Baban yake.,
Tana bude gida waya ta fara sawa a chargy Allah ya so ta da wuta, Dakin Zahran a
bude,ta shiga,kaya ta debo set uku,karaf kaf ba zani sai skirt sai doguwar
Riga,. In ba shadda ba,duk dinki ita kan batta a skirt, ganan ranar zani
tazo,..Tana bude Dayan Side din ganan kayan baby duk na mata sai unisex,. Sa'a
tai murmushi,. wato itama mace take so kamar ta?..Allah basu Nagari shine
fata...Allah dai yasa Zahra ba tai tarun Banza ba..,Ta fito ta haura sama,.Kayan
ta masu Riga da zani ta dakko guda 2,ta dau pillow da sauran abin nema,.Abincin
da tai kan ta fita ta juyo duka,,.Ta Bude ma'ajiyar kudin ta ta dakko kudi,Na
Adashen da suke a office ne,jiyan nan ta dauka,tana burin rabawa 2.,ta kaiwa su
Baba,d'aya tai wa Zahra siyayya,.30k ta dauka,ta maida sauran,.Ta kulle gidan ta
fito

Chargern mota ta sauya,ta kunna wayan,.Kamar mai jira aka kira,.Hafeez ne,duk
hankalin shi a tashe,.
" Unique yau ina kuka shiga ne haka??..
Na kira Zahra wani yana dauka Wai a gidan shi ta bari!.Bata gidan ne??.Damm taji
gaban ta ya fadi,. Wato dan iskan bokan ne ya dauka??,.wace karya zata mishi dan
wanke Zahra ita kuwa a yanzu???..katse ta yayi,."Hello,.Da inda inda ta
amsa,."Amm..Dama,.Am,Tun dazu nake kiran Ka yaki shiga,.Zahran ce dama..Da sauri
ya katse ta cikin fada.."Wajen wani katon ta bar wayar tayi??..Kenan bata
gidan??.."Aa,,Dear Ka saurare ni,.ina ai ta inda yake shiga ba tanan yake fita
ba,."Dan taga bana gari ta sirki wani iskanci koh.. "Hafeez tana Theater
Room..Sit yai dan jin ta ambaci sunan shi da kuma Theater Room..Sai kuma ya dawo
ya rikice..," Mey ya same ta??..Haihuwar ce??."Eh.Amma yanzu za'a fito ma
InshaAllah,. Ka mata adu'a.., Ce mata yai ta kashe ga Abba yana kiran
shi...Katse wa tayi,,Tai ajiyar zuciya,. Hafeez akwai kishi,Tuni idon sa zai
rufe..,Tana tsoron yasan abin nan,Allah yasa Bokan nan Kar ya tona wa Zahra
asiri,Tunda ga Jaka,Takalmi,Gyalen ta duk suna gidan shi.
By
Feenat Ja'afar
&
Hauwa Damary
[10/2, 8:16 AM] Feenat Ja'afar: [1/30, 1:52 AM] Feenat Ja'afar
BARIKI...IYAWA
66_Baba mai gadi ta sanar wa abinda ake ciki,.Tana kokarin fita da mota sai ga
nan Jummai, rike da Jaka 2 a hannun ta,. Fitowa tai a motar Ganin kanta tsaye
tai cikin gida,Binta tai taga Iya gudun ruwan ta,. Kofa take ta ja taki bude
wa.."Hala da gadon Ubale a gidan nan ne Jummai??. Ta juyo baki sake tana kallon
ta,. Harde take da hannu a girji, ta hade girar sama da kasa., Sai tai mata
bala'in k'warjini,. Dan Tunda suke zuwa gidan Sa'a basu ishe kallo ba bare tai
musayar yawu dasu,.
Kai ta girgiza mata,. "Wajen Zahra nazo.. Rai hade tace"Uhmm, daga nan fa??.Duk
rashin mutuncin Jummai sai ta zama kamar wata doluwa a gaban Sa'a,. " Jakar ta
na kawo mata,.
Baba mai gadi ta kwalawa kira,cewar ya kulle mata gate ya zo kuma, Tace ta bata
jakar,.Ba musu ta miko mata,. Maimakon ta karbi ta Zahran, sai ta warce ta
Jumman,. Yayi dai-dai da zuwan Mai gadi,. Matsowa tai da zummar kwace jakar ta
taja baya.. Hannu ta nuno mata,.tare da kada mata su,.
"A'a.,ta kada mata hannu halamar gargadi," (Don't even think about it),.Tai mata
wani kallo.." Dan Kinsan Allah? kika yarda kika matso sai kin yaba wa A'ya zakin
ta a gidan nan,.. Chak ta tsaya,baki sake ta kasa magana,. Ta kallo Baba
maigadi,wanda ya dakko katuwar gorar shi,. Jira yake Tace "Ass,ya sau aiki..
" Baba in tai k'wak'waran motsi Ka bigen yar iska,.Ya kada kai "An gama Hajiya,.
Tuni ya Matsa gaban Jummai yai (ready)da sandar shi,.
Zazzage jakar tayi,kudi Suka zubo da tarikicen magun gunan ta,.Ta zuge munafukin
zip din cikin, sai ga sarkar Zahra ta fito,. Wanda akallah zatai 250,haka Abban
su Hafeez ya sa musu,.Ta makawa Jummai harara,."Macuciyar Allah ta'ala kawai,..
Jummai ta hadiyi yawu,.. Tace" Da kika boye sarkar,ce mata zakiyi dan wannan
chanjin ne kudin sarkar??.Ta girgiza mata kai.., Sa'a tai kwafa,."Allah ya so ki
baki siyar ba,da wallahi na Lahira sai ya fiki kwanciyar Hankali,."Ashawo
kawai,.Ta warce jakar Zahran tana kara hararar ta,.
Gyalen Zahran ne aciki da wayar ta, ta dago tana zare mata ido..,"Ina kudin da
ke jakar ta'ta kan kije Saida sarkar??..Da tsananin mamaki Jummai take kallon
ta, a zuciyar ta tana "Wai ina Sa'a tasan duk wannan abun?.."Tambayar ki
nake?..A yatsine tace. " wane kudi??.."Au tambaya ta ma kike?.."Eyee??.. Ni zaki
gwada wa BARIKI??.. Tai kwafa,. Kudin jakar jumman ta tattara ta mikawa mai
gadi,."Baba kirga min su da sauri..,Da sauri ya lissafa,."Dubu Asirin ne da
Bakwai da Dari uku,.Ta kada kai,. "(Good),.Baba ware min Ashirin da biyar
aciki,.Ya kada kai, tuni Jummai ta zaburo,,."Wallahi baki isa ba,Dubu ashirin ne
nata,.Toh Wai ma ina ruwan ki da harkar mu??..Sa'a tai wani murmushin mugun ta,.
Tace" Karamar Yar iska kawai,.Ba kince babu ba??..Nasan Na Zahra dubu Ashirin
ne,.Biyar din cikon na Taxi ne,.Sannan,daga rana irin ta yau, Baba idan Ka kara

Ganin kafar ta a gidan nan na baka izinin Ka karya shegiya,. Yace"An gama
Hajiya.,Jummai tai mata kallon Banza,. "Ai ba wajen ki nake zuwa ba Malama,.
Wajen k'awata nake zuwa,.Kai ta girgiza mata, tana murmushi, Da key din motar ta
ta nuno ta " Idan Jummai ta fito a cikin Uwale da halaliya,toh ki kara sako
kafar ki a layin nan ma kadai inda kiga??..
Ta dawo kan Baba,"Ka ajiye min wannan jakar,Ka bata sauran chanjin Ta,. Sannan
kan na kirga(10),Ta bace min da gani anan,.Tace"D'aya,.. Ya duk'ar da kai "An
gama Hajiya,.. Kan Jummai yai.," Maza tattara kan wa'adin ki ya cika,. Sa'a
tace"Biyu,.Kallon banza ta tsaya yi mata,."Uku,.Ba tsammani taji Baba ya rafka
mata Gora a gadon baya,Ai ba shiri ta hau tattare kaya tana Kunkuni,.Sa'a Tace
"Hudu,.. Baba ya sake sakar mata wata,.Ba shiri tai magana" Toh Ka dakata man na
hada,.Da mugun ta Sa'a tace"Biyar,. Ai kwa ya kara dagawa zai muka mata,datai
wani uban tsalle sai tai gefe,."Allah ya isa wallahi,. Sa'a tace"Shida,.Sai kwa
Baban yai kanta da gora,.Haba wa.,Jummai K'afa mai naci ban baki ba,.Sai ta
runtuma Gate a guje tana kiciniyar bude wa,. Sa'a tana dariyar mugunta Ta kwala
da karfi,."Takwas,.Ai baba ya samu moriya, tuni ya kara sau mata aka,.Ihu ta
kwala, "Wayyo,Toh Ka bude na fita man,.Harda yar kwallar ta,.Baban yace " Ba kin
tsaya taurin kai ba??..Ni dan Tauri ne,.Sa'a ta kara kwalo wa"Tara..,Dai dai
baba ya bude mata,amma da yake Shima chali-chalin kansa ne sai da ya muka
mata,.Sa'a mey zatai inba dariya ba,. Har kasa..Fadi take "Ki tsaya man,Yar
Kot'ar nan..Sai abi wani sarki kuma,..
Da Allah ya isa ta shiga Taxin da ya kawo ta,dama tace ya tsaya,..Har ta bar
unguwar tana Allah ya isa,.
Sa'a ta zo gun Baban, Shima sai Dariyar keta yake bayan fitar jumman,. Kudin ya
bata,." Kaji Min Y'a da taurin kai Hajiya..,Sa'a tai dariya,"Ai nasan bazata
dawo ba,. Dubu (2)ta ware,"Ungo Baba, kaima Allah ya sha dakai,.Bani kayan ma
kawai nakai ciki,. Ya duka baki har kunne,."Wai Wai Wai,.Hajjaju Harda mu??..Tai
murmushi,. "Toh Allah ja da kwana,.Allah ya sauki Yar uwar ki lafiya..
Tace" Amin,.Sai Lokacin ta tuna da asibiti, da sauri ta sa kayan aciki,ta boye
sarkar ta kullo tai asibiti..
By
Feenat Ja'afar
67_Tana zuwa duk yan uwan Zahran sun zo,.Su Aunty Maryam,. Suka tare ta suna
mata sannu,.Tasleem da Auntyn su Zahran Suka Taya ta debo kaya..Tambaya suke an
shiga??.Suka ce"Wai sai(9),.(In charge)din ne sai yanzu yazo,. Ta duba agogo,
(8:43)..Tai ajiyar zuciya,. "Toh Allah yasa Ai a Sa'a,. Suka ce " Amin,.
(8:55)Suka garo ta daga labour Room,. Tayi lamau,kamar mai bacci,.Cewa tai a
tsaya tukun,.Duk Suka iyo kanta,."Sannu Zahra,.Ta daga musu kai,.Sa'a take
kallo,.Kan ta ce ta duko kanta kadan,kamar mai rada tace"Sis ya Tambaye ni
koh??..Ta girgiza mata kai,. Hawaye ta fara,"Nidai kira min shi dan Allah,Nace
ya yafe ni. Sa'a ta dago,."Kiyi hakuri sis,.kinga Doctors na jira a theater
room,. Amma nayi alkawarin zan nema miki(Right now)..Ta goge hawayen ta,
"Nagode,. Allah ya kaddara haduwar mu,..Sai ta karyar mata zuciya ta fara itama
kuka,.
Kowa Kallon su yake, musamman Aunty Maryam da tasan Sa'an Basa shiri da Zahra,.
Ta rike Sa'an aka gara Zahran,. Sai fatan a fito lafiya.
Hafeez din ta kira,.duk da wayan shi biyu tun zuwan ta,. Ta Isar da sakon
Zahran,.
Suna nan zaune har kusan (11)Kamin aka garo ta,.Ba inda ke motsi a jikin ta,.
Suka basu Babyn girl din data samu,.
Zahra taje wajen Nurses din,." Ya naga bata motsi toh??..
Sukai murmushi,. "Ai an mata (Anesthesia),. Za ta Iya tashi " (any moment) …Kar
ki damu,.Ta sauke ajiyar zuciya..Tace wa su Aunty Maryam zata zauna taga tashin
ta,. Su kace taje gida.,Ga masu kwana da yawa,. Sannan gidan su ba kowa..
Aunty Ladi aka bari ta kwana da ita,.Dakyar da taimakon wayar Hafeez ta Iya
bacci,. Dan ma ta taho da Tasleem,.
Washegari sassafe ta gama komai,.Su Bahon wankan baby,ruwan zafi,.Abinci, Tun
asubar fari data tashi bata koma ba,.Bacci ne tun yana diban ta har ta daina

ji,.Akai Assalatu ta tashi Tasleem, da mamakin ta taga sai kiciniyar soye-soye
take,.Tace Ai da ta tashe ta,.
(7)Suna asibiti,.Ta tashi Alhamdulillah,Sai dai Rashin karfin jiki,. Sukai mata
sannu,,ta dau baby,mashaAllah, Babyn Mai kyau da ita jinin su Hafeez, kamar su
guda,. Tace"Umm,su Zahra, An samu abin nema,.Ganan Zankadediyar Budurwa mun
samu,.Tai Murmushi tare da kokarin a gyara ta,.
Aunty Ladi tace zata gida Tunda Sun zo,dan bata shirya ba,.Tasleem ta tafi karbo
wani result,.
Ta kallo Sa'a,. "Sis kema Allah ya baki Baby,.Tai Murmushi,. "Sis sai dai fatan
sauka lafiya,.Ido ta waro,." Kai haba??..Ta kada kai tana murmushi,. Sai yanzu
ta kula da farin Sa'an, tai wani fresh da ita,. Ga cikin duk yabi jikin ta,
musamman kasa.. Tai murna kwarai har ranta,.Tai mata fatan Rabuwa lafiya,.
Kan (11),yan uwa sun zo da daman su,.Kowa yana tai wa Sa'a son barka,dan kwarai
ta burge su,.Ga nan mai kula zai ga cikin ya dan tasa,.Aunty Maryam data kula da
cikin Sa'an taji dadi kwarai,.Tana son Sa'a, don mai son naka Ai Ka so shi.
Hafeez ya kira su ta bawa Zahran Suka basu waje,.Amma sai ta rike Sa'a,.
By
Feenat Ja'afar
68_Azahar Hafeez ya danno Asibiti, ko gida bai je ba,.Sa'a ta mika mishi baby
tare da manne mishi suna Kallon ta tare,.Zahra tuni ta fara adu'a,.Dan jin
chanji a ranta,.kai gaskiya kishi jaraba ne,.Ita Sa'a bata dauki abun wani abu
bama,.
Kwanan su 3 aka sallame su Suka tarkata gida,.Dan fa Zahra tsaf take manne kayar
ta ba ko kara,. In za'ai wanka,ta dinga"Ai hankali da idon ta,.
Koda Hafeez ya nemi ba'asin waya,Sa'a ce tace"Ai ita ta bari a despensry,.Ya
chake mata kudin ta na asibiti,.Fir tace Gudun mawar tane,.Baba ya kira yai
mishi godiya..
Sa'an shi ta daban ce.
Zahra ko ta Jummai bata yi,burin ta ta tsallake fadan Hafeez, tasan yanzu K'afa
ya daga mata.
Batun suna da ya tambayi Zahra ta bashi mamaki da tace Sa'a,. Kuma yaji dadi
sosai.
Amma tace ya rufe Kar ya fada mata sai ran suna.
Dake garau take,suna ba fashi sati nayi,. Da safe taci Ado na kece raini da Wani
less Din su da Sa'a ta din Ka musu na fitar suna,.
Kiran wayar ta Sa'an tayi kan ta same ta a stairs,. Ta kalli mudubi, komai
yaji,.Taso sarkar ta na nan yau ta Kar kwalliya,."Fashion"tasa ta fesa
turare,.Mai zama mata tace"Kayan nan sun amshe ki Zahra,. Tai murmushi tare da
fadin ta gode,.
Saman ta haura, dan amsa kiran Sa'a,.
Tana zuwa ta tarar ta taci Ado itama da Less din nasu,.Color ne kawai ya banban
ta..Ganan sarkar ta irin ta ta a dambare a wuyan ta,.Ga zobuna manya guda
biyu,.Bangles na Awarwaro manya kamar Gold,. Tasha Adon Gold, sai shining
take,.Sai ta gane kyaun les din a jikin Sa'an.. Tai murmushi, "Sis kinyi kyau
fa,. Itama tai murmushin,. Kan ta zaunar ta kan kujera,. Ta kamo hannun
Zahran,,.
"(Guess what)?.Ta bude ido da Neman Sani,."(what)??..Tai murmushi,. "Kawo hannun
ki,amma ki rufe ido,.Ta kada kai da murmushi,.. Sarkar Sa'an ta zaro a inda ta
boye,,.Ta daura mata a hannu tare da fadin,"Tan taran.., Ido Zahran ta
bude,.Aikwa Tana Ganin sarkar ta ta rukunkume Sa'an da murna..Hafeez da Tunda ya
shigo yai tsaye yana kallon su a bakin kofar,.Murmushi yake,.Komai Sa'a tai
burge shi take,.Yaji dadin ganin su kwarai a haka..
Karaso wa yai yana. " Kun dai manta dani a rayuwa Matan nan koh,.Suka cika juna
suna dariya,.
Ko Break ba wacce ta kula nayi."Ai angon karni baya yunwa,.bari (1)minutes,.
Zahra rike ta tai,."No yi zaman ki Maman twins na zubo mishi..Ta kada kai tana
kallon hafeez,. Yana Ganin ta fita ya ruko hannun ta,."Ya Zahra tasan ke Maman
twins ce?.Tai Murmushi, kawai (Guessing )ne..kai ya kada "Kai kunyi kyau fa

Allah,.. Tai murmushi tare da Ruko kumatun shi kamar Wani yaro" Mun gode,.Sunan
wa aka sa ne ni?? Yace"sistern naki naki bata baki Bayani ba??..girgiza kai,.
Dai dai shigo war Zahra da faranti a hannun ta shake da papee chicken,.Zahra ta
taro ta tare da karbar Abincin,. "Wannan fa ya miki nauyi.. Tai Murmushi,.
Hafeez yace"Baki sanar ta mai sunan Babyn ba?..Tace "Da zumudin Dana zo kenan,so
nake na fada a gaban ka,Da fatan baka rigani ba?.
Sa'a sai Kallon su take.,amma su sai ja mata rai suke., Tace"Hajiya aka sa Ai na
Sani Tunda baza Ku fadan ba,. Sukai Murmushi,. Zahra tace" Baki chan Ka ba,.Ta
rike hannun ta,. "Sunan Babyn mu, SA'ADATU Hafeez Takwarar Momyn ta..Sa'a ta
waro ido,."Ni Sa'an?. Ta nuno kanta,.Kai ta kada mata,.Basui aune ba takwa kwala
kara,tare da Doka tsalle,." Wayyo dadi Barni da raina,. Da sauri Hafeez ya nuno
ta,. "A'a,kinyi na kudin ki Unique,.Kar ki mini illah.. Tace" Sorry..
Sorry,.Murna fal ranta ta rukun kumo shi,. Ta hado Zahran ma duka tana kwarara
musu Godiya..
By
Feenat Ja'afar
[10/2, 8:19 AM] Feenat Ja'afar: BARIKI...IYAWA
69_Dariya suke tayi,farin ciki fal ran su,.Cika su tai ta ban kada cushion din
ta dakko kudi ta mika wa Zahra,."Ga nan ajiyar ki,.Ta karba,tana kallon ta da
rashin fahimta,. Ganin Hafeez a wajen yasa tai mata gwari gwari,."Cikon Sarkar
Jummai,. Zakui waya dai,.Ta Ciro 5k,"wannan kuma Tukwici ne,kan Babban
yazo,.Zahra tama rasa mey zata ce mata,.Ganan sarka ta amso mata,.Ashe harda
Kudin Boka sai da ta lale su wajen Jummai? Har ga Allah ta fidda rai da samun
su,dan tun daga ranar Jummai har yanzu bata kira ta ba,.Tai murmushi, Lalle
maganin shege,akace sai Dan Iska,.Jummai ta gamu da gamon ta,. Kawai sai ta
Rungumo ta tana zuba godiya ba adadi,.A ranta tana rokon Allah Kar ya kara kawo
ranar da zata sabawa Sa'a, dan ta mata Hallaccin da zata Iya kiran ta da YAR UWA
CE kadai mai mata ba kishiya ba,.
Haka Suka tafiyar da sunan su gwanin sha'awa, komai Sister, komai Sa'a,. Har aka
watse lafiya..,
Tabbas Zahra tasan Sa'a ta daban ce,ba yadda za ai ta hada kai da ita,.Don
Bazata Iya ba,Hakan yasa ta dau damarar janyo hakurin ta na Da,ta yarfa wa
ranta,..Takan gujewa duk wani cikas na zaman su da Sa'an, Duk da ta fara mata
karar abubuwa da dama,.Sai dai babu ta inda ta rage wa Hafeez.. Tabbas kowanne
bawa da irin baiwar da Allah yake haifar sa,.Musamman mata,kowa da irin tata
salon Iya kissar,. Tanan kam,ko ita ta sarawa Sa'a,. A hankali ta siye su da yan
uwan su Cikin hikima da Dabara,.Sai dai Abu d'aya ta Kudirta a ranta,,shine duk
yaran da zata Haifa mata,toh fa zata damkawa Sa'a su,dan ta karantar su
Darasi,Musamman na gidan Miji,.
LAIFIN DADI???..
Naufal,da Nailah ne ke ta kai kawo Cikin Sittern su a parlourn,. Twins din Sa'a
kenan,. Yaran gwanin sha'awa,bulo bul dasu,.Watan su(6).Amma in ka gansu ka
dauka yan wata (8)ne,.Danna Button din sittern Naufal ke yi yana wakar "Twinkle
Twinkle Little star,.Yayin da Nailah ke ta bangala mishi baki tana dariya tana
bubbuga tata,.
Da sallama ya shigo,.Daga chan kitchen aka amsa mishi,.Tuni ya karaso da
sararrafa wajen yaran,wanda tun sallamar shi Suka fara murna,." Ina Matan gidan
aka bar mun 2 little Angels na su kadai??..Ya cire Nailah "My little Princess,.
Papa's home,.Sama ya hulla ta ya chafe,.sai dariya take bangala wa..Ya sauke ta
ya dau Naufal,Shima ya masa,.Fitowa sukai a kitchen din zahra inda suke hada
kwanikan lunch,.
Da fara'ar su Suka fito,.Zahra dauke da karamin Cikin ta data kara Nad'a,. Jikin
shi Sa'an tai kamar yadda ta saba,.
Da sauri Zahra ta kau da kai,.Gudun zigin shedan,.Irin haka yasa take mar Marin
yin nesa dasu,dan tasan zuciya batta kashi,kuma zo mu zauna,Tabbas wataran zo mu
saba ne,gwara kazantar da bata ga ba a wajen ta tsafta ce,.
Sai dai tana tunanin rayuwar gidan da bata tare da su Naufal,Ga Naina ta saba
dasu,. Tai murmushi, dan tuna wa da Naina da aka kai yaye..Da tasan ta na nan da
Tuni tana makale dasu Naihan..
Ta kallo Sa'a, Yadda ta maida hankali kan Mijin ta,. In Hafeez na gaban ta, toh

hatta yaran ta gefe suke.,bare ita,.Tai murmushi,. Bazata kara da Sa'a ba,dan ko
ta bangaren kula da Miji ta daga mata tuta,Burin su Allah ya kara hade Kansu.
Alhamdulillah... Nan muka kawo karshen BARIKI IYAWA...Muna rokon Allah kuskuren
da mukai ya yafe mana..
SADAUKAR WA.
An sadaukar da labarin BARIKI IYAWA ga daukacin Masu karatun shi,.Da fatan an
tsinci abinda ke Cikin shi.
Nafisa
Bashir
Tanko(Feenat
Ke muku fatan Alkairi.
Luv All


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment