Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Oga Abdul yaci suit sai kallon agogon dake daure a hannunshi yake, yana ganinsu yataho dagudu murya chan kasa yace "kayi latti sosai sokake kasamu a amtsala" ya kalli Fateema yace "good, from now sunanki Khalid understood" gyadamai kai tayi, yace "any question dasuka miki answer them da turenci, sukaga u are educated zasu yanka miki albashi mai yawa nan da nan agama biyan bashin babanki" tasake gyadamai kai, ya shiga gabansu da saurin shi yace "let's go" jikinshi har rawa yake hakan yasa taji gabanta na dukan uku uku, shiga hotel din sukayi sukai upstairs, wani babban hall suka shiga ga security guards gardawa aciki, hall ne da aka jera kujeru hadaddun gaske, ga maza manya magidanta amman irin talakawan nan haka kusan su 100+, ga yara samari maza agefe dabazasu wuce sa'oninta ba zuwa yan 22yrs suma zaune kan kujeru adayan bangaren kusan su 63 ko morethan ma, saikan hadadden stage din da akai decorating da flowers aka zuba wasu arnayen kujeru wasu hadaddun manya manyan lawyers ne da baristoci sunci suit suna rubuce rubuce ga laptops agaban su, da printers, kallon Baba Oga Abdul yayi yace "kujirani anan lemme talk to them nazo dan ankira sunanka yafi sau uku" stage din yayi zuwa wajen wani babban Barrister dan tsoho nema dukawa yayi yamai magana a kunne sanan yadawo yaje wajensu Baba kujera yanuna musu yace "kazauna za'a kiraku" zama Baba yayi yana rikeda hannun Fatima itama ta zauna a kujeran kusada shi, saishima Oga Abdul yazauna kusada Baba yace "yanzu nan police suka tafi dawani mutumi thank God kayi tunani mai kyau da....." "Muhammad Alhasan Muhammad" shiru Oga Abdul yayi jin ankira Baba, faduwa gaban Baba yayi haka itama Fatima dan yanzu saitaji tanajin tsoro sosai dan ga dukkan alamu wanan babban organization ne baba yaci kudinsu duk azatonta tazaci is just a small something, hannun Fatima yarike sukai stage, cikeda girmamawa ya gaida lawyoyin da duk suka zubamai ido suna kallon yanda danshi yay kama dashi, yace "yallabai bangama hada kudin ba amman ga......" kafin yagama maganan Barrister ya kalli Fatima yana gyara glasses din idanunshi yace "young Man akwai turenci" gyadamai Fatima tayi ahankali, yace "whats your name" gyara muryanta tayi ba yabo ba fallasa dudda muryam baiyi kaman na namiji ba hakama baiyi kaman na mace ba tace "ahhhm Khalid Muhammad" ajiyan zuciya Oga Abdul ya sauke, Barrister yace "how old are you"? Anatse tace "i am 19yrs old" documenting sukayi sanan yace "what level are you in school" ahankali tace "I just write waec this year" gyadamai kai yayi yace "what are you good at Khalid? What can you do what are your skills?" Shiru tayi saikuma ta kalli Baba taga kanshi na kasa sanan takalli Barrister tace "only house work" da sauri Barrister yace "don't you go to work" gyadamai kai tayi tace "only school and islamiyya i go" gyadakai yayi cikeda gamsuwa dan yaga yaron na kokari turenci shi dai ba laifi normal turenci yaro dan arewa dayaje school, juyawa yayi ya karbi wani bracelet dataga anciro daga wani akwati an rubuta 65 ajiki yace "give me your hand" bashi hannunta tayi ya nada mata bracelet din sanan yakalli Baba yace "because your son is educated and can communicate da English, salary dinshi every month will be 120,000 naira, yakama zaimana aikin watanni ashirin da biyar (25) shekara biyu da wata daya kenan" ya kalli Fatima da gabanta ke wani irin mummunan faduwa yanuna mata bangaren yaran yace "go and sit there with your mate, Abdul take her luggage to the car" gana masgonta Oga Abdul yafita dashi aka nunama Abba wajen zaman manya yawuce yaje ya zauna yakasa dagokai.

Wuraren 12 suka gama, sanan aka shigo da abainci yaran aka rabamawa hadadden fried rice da chicken da salad da ruwa da juice Barrister yace "eat Boys" yara sai dadi sukeji ganin abincin da basaci agida nan da nan suka cika hall din da hayaniya sanan akai dismissing iyayen su, security guards na fitarda su suka fara fita, da sauri tadaga kai ta kalli Baba kin kallonta yayi harya fita tareda Oga Abdu yaki juyowa ya kalleta saidai yana tafiya ahankali kaman baida jini ajiki, ahankali taji hawaye yazubo mata kaman daga sama taji an rungumota takafad. "Dalla karkai kuka saikace wani mace eh guy" da sauri ta daga kanta wani saurayi tagani dabazai wuce 20 ba yana sanye da riga da wando shima kabar da hannunshi tayi cikin sabon muryanta tace "dalla malam karka kara tabani" taja kujeran ta ta matsar tabude jakan bayanta tasa takeaway aciki ta ijiye jakan akasa ta kafa fuskarta akan kafafunta kawai ta shiga kuka mai taba zuciya.




_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._








💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫


_MASIFAFFIYAR KAUNA_




✍🏾M SHAKUR



EPISODE 1️⃣2️⃣
_FREE PAGE_


Sauran yaranne sukahau dariya though not all dan wasuma sunyi shiru sun natsu daga gani suna kewan iyayensu, shikuma yaron wani hararan shi yayi yafaracin abincishi kawai, takai kusan 20min ahaka, sanan ta tashi tagoge fuskarta tas da idanunta tass, ahankali taduka tadau jakan budewa tayi tadauki takeaway ta tabude ahankali tashiga turama kanta abincin sanan ta ijiye acikin jaka duk suna zaune wajen su kadai sai hayaniya yaran suke har wajajen karfe uku sanan securities suka shigo sukace "kutashi kuyi layi masu son amfani da bayi suyi, ga bayi nan anbude muku night journey zakuyi so get ready, prepare use 10min to do everything" bayika hudu dake dankareren hall din suka bude musu, ahankali ta tashi ta goya jakanta tai hanyar bayin wasuma nabinta abaya, shiga daya daga cikin bayinka tayi tarufe harda key sanan ta tsaya ta kalli kanta really fa batada banbanci da namiji da sauri ta dauke idanunta daga madubi dan bataso tana kallon kanta, fitsari tayi kaman tasani ta soke wani pad a aljihun wando dudda bata wani heavy flow dan gobenema zata gama amman saida ta dauka wanan dataji night journey zasuyi yasa ta chanza ta gyara kanta tareda flushing old one din ta shirya tsaf sanan tafito goyeda jakanta, tana fitowa security yanunata yace "kai kagama?" Gyadamai kai yayi hakan yasa security yanuna mai kofa yace "jemota ajeraku" fita yayi ahankali ya sauka kasa tareda wasu yaran, wani babban luxurious bus tagani kaman irin nasu landstar wanan hadadden bala'i kaman ma sabo, security dake tsaye gaban mota yace "oya zoka shiga" karasawa tayi ahankali ta taka tahau motan wani sanyi ne taji motar ga dankareren tv a kunne ga sanyi ga labulaye, security dake tsaye a tsakiyan motarne yana nunama kowa inda zai zauna yanuna mata sit yace "jeka zauna achan" karasawa tayi ahankali ta zauna kusada window, wani yaro aka turo yazauna kusa da ita dan sit bibbiyune jere akowani side, kafin agama jerasu tass karfe hudu, sanan taga wanan babban lawyer dayasa mata bracelet yana magana da security dukansu su biyar yabasu kudi wrapper yan dubu guda biyu har kasa suka duka sunamai godiya suna Allah iso dasu lafiya gobe da alamu su flight zasubi sanan dukansu biyardin suka shigo motan, daya ya zauna mazaunin direba, daya adayan bangaren mataimakin direba, sai uku suka zauna a first row na bayan direba dabasu saka any of the children akaiba, sanan suka tada motar suna dagama Barrister hannu harsuka fita daga hotel din suka dauki hanyar barin kano motar yay tsit sai securities din dake hira abinsu.

Ahankali ta lumshe ido azuciyanta tace "ina zaki Fatima Zarah? Wani kasa ko gari za'a kaiki? Nazaci anan kano zanyi aikatau amman wanan damuke barin garin kano ina zamu? Yau nice nake rayuwa amatsayin namiji ina amsa sunan Khalid, yau nine nake wani wuri da babu halitta daya dana sani, nine bana tareda mahaifina ko kannaina, nine nake barin garin danake zuea wani wuri daban ma saniba, Ya Allah kaga zuciyata Alkhairi nake nufima mahaifina Ya Allah na fawwala maka al amarina da rayuwata gabaki daya Ya Allah ka kareni ka tsareni, I am so scared, har kasan zuciyana inaji dabanyi wanan abinba amman kuma har kasan zuciyana inaji zan iya mutuwa aka kullemin Baba" hawaye ta share ta kalli gefe tadan bude labulen window ta kadan tana kallon hanya, itadai tunda take da wayonta bata taba tafiya tabar kano ba amman wanan tafiyan da ake motarsu na famfala uban gudu tasan
Kano zasu bari, idanunta biyu harsuka fita daga kano suka kai zaria suka isa kaduna harsuka dauki hanyar Abuja lokacin dare yasoma yi, ganin tafarajin yunwa yasa tabude jakanta tasauki abincin taci takoshi tasha ruwa sanan ta ijiye ta gyara zama tadan saci kallon yaran dake gefenta taga shi yamayi bacci, hakan yasa ta zubama TV dake aiki a motar ido tana kallon film din da akeyi nafada, ahaka wuraren goma nadare bacci yay awon gaba da ita.




********
Wajajen takwas nasafe tafarka ahankali take bude idanunta saitaga kaman all that happen jiya amafarki ne Baba yay biyan bashi da ita xataje aikatau, tarr tabude idanun nata tana kara kallon inda take ganin tana cikin motar har lokacin yasa taga ba dream bane, ganin har lokacin suna cikin mota ana gudu yasa tafara mamakin ina zasu kafafunta taji sun mata tsami sosai cikin kambas din da suke ganin yanda taketa motsi da kafar tana yatsine fuska yasa yaron kusada ita yace "kacire takalmin kafafunka susha iska inba hakaba zasu fara maka ciwo" kallon yaron tayi yananan shima kaman ita baida jiki sosai shima kuma dan farine, dauke kai tayi tashiga cire kambas din yaron na kallonta fararen kafafunta taciro dasukadan kumbura yaron yace "jibi kafarka mai kyau kaman kafar mace"! Faduwa gabanta yayi da sauri ta maida kafar cikin takalmi, dariya yaron yayi yace "kunya kakeji akira kafarka irin na mace to kafarne ba kaushi gashi batada wani girma daga gani baka aiki agida daman gaka shagwababbe sai kiran Baba kake cikin dare dakana bacci" da sauri ta kallai, dariya yayi yace "sunana Anas Abdulmalik kaifa" ahankali batare data kalleshi ba tace "Khalid" murmushi Anas yayi yace "aiman kai dan fulanine ko dan wlh kanada kyau inda kai mace ce da anga rububi gurin maza" wani irin mugun harara tamai tace "kadenamin irin maganganun nan banso" da sauri Anas yace "kai wlh kacika masifa me awanan maganan, by the way naji kasan ina muke yanzu?" Girgiza maikai yayi tace "kaika sani"? Girgizamai kai shima yayi yace "bansani ba wlh ni bantaba zuwa nan arayuwata ba amman kuma kaman garin yarbawa muke sabida naga signboard dinsu anata rubutun yarbawa akai" shiru tayi saikuma ta kalli window tai shiru, ajiyan zuciya Anas yasauke yace "irin wajen nan yakamata mutun yasami aboki dan we are all on our own, zaka zama abokina Khalid" yanda yay maganan ahankali yasa tajuyo ta kallai shima ita yake kallo, dan murmushi yayi yace "tunda baka sona da aboki shikenan amman still zan bada labarin dake cimin zuciya, kasan menene wlh na tsani Abba na sosai, bansan ina zaniba kawai yazo yacemin nahada kayana ya kalli Maman mu yacemata zai turani biyan bashi, saida mukazo wajen nagane ashe kudin dayaci kwanakin baya yakaro aure duk kudin bashine saikace yabani anini aciki dazai kama yadauken yabiya bashin dani, aikin shekara biyu da rabi fa zanyi ni bana makaranta ni inachan wata duniyan ina aikatau Mama na kewana" duka maganganun nan dasuke ahankali suke babu mai jinsu, ganin yanda hawaye yataru a idanunshi sosai yasa yabata tausayi ahankali tace "kayakuri wata rana sai labari, duk abinda d'a zaima iyayenshi koda cutanshi sukayi bai fadiba watarana zaka gane hakan kayakuri kaji" ahankali ya goge fuskarshi da bayan hannu sanan yamata murmushi ya kalli window ganin signboard na WELCOME TO LAGOS yasa da sauri yamata pointing da hannu yace "Khalid kalla" da sauri Fatima tajuya zata kalla amman sun wuce bata ganiba tace "menene" da sauri yace "naga welcome to lagos muna Lagos" dasauri tace "Lagos, Lagos din dana sabaji ana kira" gyadamata kai yayi ajiyan zuciya ta sauke, Anas nata mata hira hakan yasa tadan saki jikinta dashi kadan, saikuma daga baya sukai shiru ganin sun shiga asalin cikin garin lagos ga titina manya dake daukan kusan motoci kusan biyar a jere, ga dogayen buildings, ga hayaniga, ga yellow danfo buses, sukahau wani titi dake kan ruwa, ga jiragen ruwa manya manya irin wanda take gani a films su titanic akan ruwa, ga boat na gudu, sunyi kusan 20min sunabin bridge din chan ta hango wani babban UBA bank building tacema Anas "kalli UBA bank, banki su Baba yanada account awajen har number account dinshi nasani" dariya Anas yayi, garin yazamema yaran abin kallo securities duk suna jinsu sai murmushi kawai suke, sanan suka shigo wani hadaden kayataccen anguwa dake dauke dawani dankareren babban gida dagawani dankareren statue din mutum akofar gidan tsaye rikeda sandar girma, gaban gidan anyi wasu rubutu manya an rubuta ILE OTUN OBA LAGOS (GIDAN WAZIRIN SARKIN LAGOS).



_MBM ENTERPRISE company ne mai zaman kanshi that are into anything computer design, graphics design, sunayin ID card, folder, files, meo, baje, sunayin jotter na biki da sauransu, sunayin customize mug da magic mug, sunayin jacket da riguna signout irin idan kun gama school, sunayin invitation card, sunayin p-caps, sunayin throw pillows da sauran su, sunayin calendar na turenci dana larabci, dakomima har kwalaye sunayi, ko'ina kake zasu maka su aikamaka dashi, suna logo creation, suna customized links, flash da souvenirs na biki na birthday na suna daza'a lika suayenku ajiki, sunayin receipt, gift box na birthday koma na menene, jama'a bari kuji indai design ne da ake amfani da kwamputa ayi to MBM Enterprise kaman sunmiki sun gama, har award sunayi, customize umbrella, key holder banda haka all services dinsu are at a very low discount rate, super affordable, idan zaki tuntubesu zaki samesu awanan number takira 07010439656 , sanan zaki samesu a watsapp ta wanan number 08106788714 kuyi saving ku musu magana ko a watsapp kokuma ku kirasu awaya._









💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫



_MASIFAFFIYAR KAUNA_



EPISODE 1️⃣3️⃣

_FREE PAGE_

Suna zuwa katafaren gate din mai kama da madubi wani babban mopol din yabude musu gate suka shiga cikin gidan, itadai tunda take arayuwanta na duniyan nan bata taba ganin hadadden gida hakaba, wani irin babban gidane naban mamaki, asalin mansion din dake compound din taga sun wuce suyi kasa nan ma wani dankareren gate ne aka bude musu suka shiga, wani babban gidane dabaikai wanchan kyau ba ga yara da sunkai su 60 suma maza a compound din suna zazzaune wasu nawasa wasuna hira, parking motar sukayi, securities dinne suka fara saukowa sanan sukace su sauko, ahankali suke saukowa aka nuna musu wani babban Palo mai kama da hall suka shiga sukai layi atsaitsaye, sanan sega wani sabon mutumi yazo da turencin shi dabata da kyau kana ganinshi kasan bayerabe ne yanuna musu toilets dasuke ajere guda 10 yace "go bath get ready" hanyan bayi sukayi, kusan 4 to 5 mutane abayi daya, tsayawa tayi tana kallo ganin anshigo da ganamasgon ta yasa tai wajen jakan security dayakawo yace "mezakayi"? Bakinta har rawa yake ganin yanda ya murtuke fuska sabida tsoro tace kayan dazan sa zan dauka, hararanta yayi yawuce yafita ahankali tabude jakan tadauko wani wando da riga, bakin wando ne shima sai bakar riga t-shirt mai zanen Paris aciki sanan ta tashi, tana ganin wani yafito daga bayi tawuce ta shiga da sauri kafin wasu set subiyota ta kullo kofa tareda saka sakata da key duka, yanda bayin ke warin jikin mazane yasa ta taushe hancinta takai kusan 1min atsaye sanan tabude boturin riganta tacie rigan tacire singlet dinma kafin ahankali ta kwance daurin silkin kirjinta, dawani irin sauri ta tsugunna tareda rike boobs dinta sabida wani mahaukacin azaban ciwo dasuke mata tadade ahaka sanan ta tashi tacire wandon ta madubi ta kalli boobs dinta sunyi jajir abunku da fara da kyar tacire wando sanan tai wanka agurguje ta shirya tsaf bayan tasake kulle kirjinta da silkin, bakaken kayan data saka sun mata kyau bakadan ba, kallon kanta tasakeyi amadubi ahankali tadaura hannunta kan saikon fatar kanta tana kallon kanta wai yanzu itace wanan, wani irin mugun tausayi tabama kanta saikuma tafashe da kuka ahankali Allah kadai yasa irin tsoron datakeji azuciyanta wani irin bubbuga kofan bayin da akayi yasa afirgice tajuyo cikin ihu security guard yace "ubanwa yace maka ana rufe bayi kai kadai ke jiran bayin bude kofarnan" da dauri ta tattare kayan data cire tarike a hannu sanan tabude kofan daya daga cikin security ne tagani tsaye gaban bayin ga yara tsaye abayanshi duk sunaso suyi wanka, cikin fushi yakai hannu zai watsamata mari da gudu ta tsugunna wani daga cikin security yarikemai hannu yace "kayakuri mana he's just a boy, baku fadamusu ga yanda ake yi ba" cikin fushi shima yace "just 30min fa aka bamu musasu su shirya su fito ya shiga bayi shi kadai ya kulle ga mutane dayawa nan basu yi wankan ba abinda mutum biyu ko uku yakamata su shiga at once" dayan security dake bashi hakuri ne ya kalli Fatima da jikinta ke rawa sosai tana tsugunne kanta akasa yace "kaikuma tashi kaje ka maida kayan daka cire jakanka kadau jakan ka maida mota sanan ka shiga cikin assembly dakukeyi awaje" tashi tayi da sauri tana goge hawayen dasuka zubo mata, wajen gana masgonta tayi tasaka kayan sanan taciro kiton da Mama ta saimata baki shima ta saka ta manna igiyan dan kafarta yagaji da kambas din jiya tasaka kambas ajakan sanan tadau ganamasgon ahankali tafita har lokacin jikinta rawa yake, wajen motarsu tayi ta shiga ta ijiye jakan sanan tafito tana kalle kalle bataga yaro ko dayaba sanan bataga inda ake assembly ba hakan yasa ta tsaya tana kalle kalle, tana cikin kalle kalle kaman daga sama taji anwani irin zubamata dorina wani irin ihu tayi da mugun kuka arude tajuyo tana kuka sosai jikinta narawa tana kallon mutumin daya zuba mata wata muguwan sharbebiyan dorina dake hannunshi da tsayinta yafi tsawon mutum. Cikin harshen turenci yace "angayamaka uban gidana uban kowa najiran mutane ne ance kaje assembly ka tsaya anan kai wayekai" yasake daga nabiyun zai shaula mata da gudu tashiga mota tana kuka sosai hartana fadi har lokacin tana sosa bayanta kaman wacce ta zare bulalan gawani mahaukacin zafi sanan ga mugun kaikayi, zai shigo motar kenan security daya ceceta dazu taga yazo harda dan gudunshi yama mutumin magana mutumin yajuya yatafi yana masifa, shigowa cikin motar yayi yana kallon yanda take kuka da hausa yace "wai ka dauka har yanzu a garinku kano kake ne? Idan baka natsu kasan mekake ba duka zaka dinga ci agidan nan harsai kadawo abin tausayi ba assembly nace kaje ba" cikin kuka sosai tana soshe soshe tace "ai ban gansu ba sunake nema" hannu yamika mata alamun tashi, tashi tayi ahankali batare data rikeshiba har lokacin tana kuka, hannunta yakama yajata suka fita daga motan tana kuka sosai sanan yay gate da ita, bude gate din yayi daya sadasu da mansion din dasuka fara wucewa kafin su shigo nan, nan taga yara dayawa basu kadai bama harda wasu another set daba yan kano ba sunyi assembly ma'aikata sai gyarasu suke, kallonta yayi yace "wuce katafi, kuma ka natsu inba hakaba anan ma wani sabon dukan zaka karaci, oya tafi" ahankali tawuce ta tafi har lokacin takasa dena kuka dan bulalan shima yaki dena mata zafi da kaikayi duk uban dukan da Mama kemata da wayan wuta bata tabajin irin wanan bulalan mai zafi da kaikayi duka at the same time ba, tana karasawa wajen wani guard yajata a tsakiyan wani layi yasata daidai ta inda tsayinta yakai sanan yawuce yatafi suna patrol suna zagaye su suna gyara duk wanda yafita daga layi, itakuma sai goge kwalla take tana kuka ahankali yaran kowa na kallonta.


Sunkai kusan 30min atasaye Sungaji ga yunwa amman anhanasu tsugunnawa, sanan sukaga an bude glass door dasukai assembly gabanshi suke facing, stairs ne dabazasufi 10 ba, sai space babba dawani katon kujera, sai glass sliding door, ga flowers masu kyau an jera awajen.
Sliding glass din akayi, gani tayi wayanan lawyers dinan na jiya da Barrister jiya dukansu sun fito suna sanye da suit bakake sunyi layi akan dakalin saikuma gawani babban mutumi daya sanya wani hadaden embroidered lace akamai, agbada ga sandar girma maikan maciji a hannunshi yana dogarawa kaman baison ya dogara yana tafiya dai dai cikeda isa dakuma iko yafito yakaraso ya zauna kan hakimin kujeran dake wajen, yadaura kafa daya kan daya yana kallonsu, guards din dake wajen ne suka fara zubewa akasa yaranma suka bisu gabaki dayansu suka zube akasa sukai kneeling kan kowa akasa. "Angaishe da Wazirin Sarki"... jin iska na bugunta tako'ina tana kuka kuma taji anyi magana duka atare sanan wajen yay tsit kaman ba'ai hallita ba yasa ta ahankali tacire hannunta dake kan idanunta tana share idanunta dasukai jajir dashi hawaye na zuba, ganin mutumi zaune ga Lawyoyin nan tsaye agefenshi duk ita suke kallo yasa da sauri itama ta tsuggana akasa kaman yanda taga sunyi tawani sake rushewa da kuka sosai dan tasan hala sai ansake mata duka dan laifi takuma yi an tsugunna an gaida sarki ita tana tsaye, ta daura hannayenta akan bakinta tana taushe bakin sabida kar sautin kukan yafito amman ko'ina najikinta rawa yake.


Batare da Wazirin ya amsa gaisuwan suba balle yabasu izinin tashi tsaye yakafe Fatima da idanu yanda ta tsugunna kanta akasa jikinta na bari tana kuka sosai ta taushe bakinta, yara 100+ ne awajen amman ita kadai ke kuka gabaki dayama ma atsorace take. "You"! Yakirata cikin cikakkiyar muryanshi da babu alamun wasa aciki ko sanyi, ko kadan batasan ita ake kiraba tadaiji ance you, wani yaro dake kusada itane ahankali gudun kar ajishi yace "Otun is calling you" da sauri ta dagokanta ta daga jajayen idanunta ta kalli inda suke, ganin ita yake kallo har lokacin ya kafeta da ido kur yasa tamike tsaye ahankali tareda share idanunta jikinta ko'ina yadau kakkarwa kaman mazari, da hannu yamata alamu tazo da sauri ta tafi gaban Mansion din hawa about 10stair case din wajen tayi sanan takai gaban kujeranshi kasa jure yanda yacikamata idanu tayi da sauri tai kneeling down ta kulle idanunta gam cikin harshen turenci tace "please i am sorry, I will not repeat my mistake again, dan Allah karkasa adakeni I am so sorry, please, please" saikuma tafashe da kuka ahankali jikinta nabari har lokacin idanunta akulle wani irin tsorone aranta bana wasaba bata taba ganin irin this set of mutane ba kokuma set of life dinan, she is not use to any of this, arayuwanta daga iyayenta sai Maryam su kadaine in her life, wanan set of people dinfa dabama tasan takamaimen menene su ba, Muslim ne ko Christian.
Gabaki daya compound din yay tsit babu abinda kakeji sai sautin sheshekan kukanta, sosai Waziri ke kallon kyakkyawan yaron da baisan mesaba amman yaron yay mugun capturing attention dinshi at a glance, dan gyaran murya yayi sanan strictly yace "open your eyes" dasauri tabude idanunta dahar sunsoma kumbura tsabagen kuka amman bata kalleshi ba kanta akasa, anatse yace "what's your name"? Ahankali cikin muryanshi bana namiji ba bakuma nq mace ba mai dadin sauraro da intonation din

Please Login or Register in order to submit comment