Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabata, tsayawa yayi shima yabita da kallo harta shige ciki, maganan da Ruka tamai dazu ya sosamai rai ba kadanba kuma deep down yasan da gaskene Zara batada ko mashinshini guda, kuma laifinshi ne yarinya batada kayan arziki tana mace kuma budurwa datake tasawa yanzu amman kayanta sunfi name abincin saidawa kodewa, hijaban ta biyu kacal da maroon dawani mai ruwan toka sun kode harsun fara ja akai tsabagen kodewa, batada wani takalmi na fita sai silifas, kullum fuskarnan nata fayau babu komi aciki yaza'ayi saurayi zai gani ya yaba, koya sami kudi yace zai mata Ruka tahana, saisa yakeson yarinya yanzu ta shirya taje wajen Babarta hutu amman yasan Ruka bazata bariba, ganin dogon tunanin dayake yasa kanshi yafar*a sarawa yasa yajuya yafita kar hawan jininshi yatashi, machine yatada yafice daga anguwan gabaki daya











💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫


_MASIFAFFIYAR KAUNA_


_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_



✍🏾 M SHAKUR


EPISODE 3️⃣
_FREE PAGE_
Koda takoma daki bataga Maman nasuba hakan yasa ta shiga dakinta ta ijiye komi taboye kudin da Baba yabata sanan tafito tatattare falon inda sukaci abinci ta share tafita da kwanukan ta wanke sanan tadawo ta kunna turaren tsinke afalon ganin ana kiran la'asar yasa tadauro alwala ta shigo tai salla sanan ta shiga dakinta ta sanya Ash color hijabin ta har kasa dan shine na islamiyyan su sanan tadauki jakar islamiyyan tafito, gaban dakin Maman su taje ta tsaya tai sallama ahankali, daga ciki maman tace "lafiya kin isheni da sallama yarinya saikace rainon mayu" batadamu da maganar ba dan inda sabo tasaba, ahankali tace "zantafi islamiyya ne Mama natafi"? Ihu tamata daga taciki tace "au so kike ubanki yazo yace nahanaki zuwa islamiyya ko uwar shairi da kinibibi wuce ki bacemin daga gaban daki, mayya mai neman rabani da mijina" juyawa tayi ahankali tafice tai waje da sauri sauri take tafiya kaman mai jiran wata, tayi nisa sosai tahango wata yarinya kana ganinsu kaga sa'oinnin juna itama tana sanye da Ash color hijabin kaman nata tana tsaye karkashin bishiya tun kafin takaraso wajen tace "wlh kika samu latti Fatima saina rama dukan lattin da za'a min ajikinki" dan dariya tayi ta bangaje mata kafada tace "dalla chan bamuyi latti ba har yanzu hudu bata cikaba" binta da sauri yarinyar tayi tace "au hakama zakice"? Murguda mata baki tayi tace "eh din" dariya yarinyar tayi tace "tokijirani sai sauri kike FatynBaba" juyowa tayi ta tsaya chak tareda rike waist dinta tace "ohkay ke Maryam dinan kin cika wayau, sabida muyi lattin kirama dukan ajikina ko saisa kike cewa najiraki" dariya Maryam tayi takaraso inda take tareda mika mata wani leda tace "gashi nakine" da sauri ta karba tabude taga sabon hijabin islamiyyan sune Ash wanan ma anyi dinkin mai hula mai kyau juyowa tayi ahankali ta kalli Maryam din dake kallonta, murmushi tayi ta bangaje mata kafada tace "ke dalla common, Babanmu nacema hijaban mu na Islamiyya sun tsufa, shine yace nazo shago anjima a aunani a dinka mana, shine naje kinsan yanada yadin hijabai masu kyau, na zaba yabama yaron shagonshi ya dinka mana dinki daya, nima bansa nawa bane sabida nasan bazaki saka naki yauba, sai gobe zamu saka mu fasa islamiyyan tareko" gyadama Maryam dinkai tayi saikuma ta rungumeta kawai, da sauri Maryam ta tureta tace "dalla ke dadina dake son jiki awaje zaki wani rungumeni sabida hijabi, har yanzu maganana nanan kikasa mukai latti saina rama dukan ajikinki" Maryam tai maganana tana dariya taredayin gaba, share hawayenta tayi ahankali sanan tabi Maryam din da sauri tace "toni kijirani" haka suka dinga tafiya suna shirme cikin ikon Allah koda sukakai ba'a fara taron latti ba hakan yasa suka wuce ajinsu direct aka fara karatu.



_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_


Karfe shida aka tashesu daga islamiyan, saidaa ta tattaro kansu Sadiq dasuka taho tareda Habib sanan suka fito Habib yay gaba da kannin nashi itakuma suna jerowa tareda Maryam suna hira har sukakai wajen bishiya suka tsaya Maryam tace "kinga yanda Malam Sani keta kallonki kuwa dakike biyamai karatu" dan hararanta tayi tace "kallo, kallon lafiya, ni banmasan anyi hakaba kin iya sa ido Maryam" murmushi kawai Maryam tayi tace "nidai kidinga saka nikabi, kyanki yay yawa yarnan" hannu takai zata kwadama Maryam din duka ta kwashe aguje tadau hanyar layinsu itakuma tacigaba da tafiya tana dan murmushi, ana magrib suka shiga gida, gaida mutanen gidansu tayi sanan tai dakinsu Mama tasamu afalo zaune tana bama Abida nono tana ganinta tace "wuce kije ki kada miyan dake wuta" dakinsu ta shiga ta cire hijabin islamiyyan ta tasaka maroon tafito zatai kitchen, da sauri Mama tamata ihu. "sokike kije ki kone a kitchen Babanki yakusa cinyeni, wuce dan ubanki kicire hijabin nan bansan ubanwa kike boyema yan kirgan dangin nan dakika faraba" cikin kunan rai Habib yace "waike Mama kullum saikin ma Ya Faty fada dawani wai kirgan dangi mehaka dan Allah, ni wlh kidena damun Ya Faty" cikin fushi ya kalli Fatima da kanta kekasa yace "Ya Faty jekiyi da hijabin ki kinji ai Malam yace bakyau mace na yawo haka ba lullubi" mugun dundu Mama takaimai abaya tace "kai dan ubanka ko ubanka bayaja da maganata balle kai yaushe aka haifeka? Duka duka shekarunka sha biyu kake gayamin magana eh dan ubanka" cikin kuka da fushi yace "to meta......" da sauri Fatyma tajawoshi taredakai hannu bakinshi ta taushe tahanashi magana dan Allah ya zuba mata son kanninta kaman me, cikin fushi Mama ta ijiye Abida kan kujeran ta tashi tace "ni uwarka kakema rashin kunya kan wanan yarinyar eh Habibu" da sauri Faty ta tura Habib din bayanta tace "kiyakuri Mama dan Allah" gauramata mahaukacin mari Mama tayi da saida yasa tai layi kaman zata fadi sanan ta fizgota da karfi ta kumata da bango tareda shake mata wuya tace "ni zaki juyawa yarana akaina? Yaran dana haifa zaki batamin su? Harda kama Habib kina boyewa a bayanki irin ga danki dinan ke uwarshi wlh yauna lahira saiya fikijin dadi" tai maganan tareda fizgo wayan TV tashiga lafta mata tun tana daurewa bata ihu tahau kuka sosai tana ihu tana yakuri Mama, Habib na tsaye gefe yana kuka sosai kaman ranshi zai fita, duka yaran harda Abida ma saisuka hau kuka ganin ana dukan yayansu ga Mama sai uban ihu take tana jibgarta kaman daman tana tikeda ita, wata makociyarsu ce dake shiri da Maman tashigo tana zuwa rike Mama tayi tace "ya isa hakanan Maman Habib" cikin kumfan baki tace "barni na kashe yarinyar nan nahuta Zainabu, yarinya tarabani da mijina, mijina saiya hanani kudi yabama wanan makiran, komi ita komi ita, yanzu kuma nema take tarabani da yarana, to wlh bata isaba saina kasheta nakashe banza taga idan da abinda ubanta zai iya yayi kuma zama daram sai yanda nayi da uban nata datake takama take tunkaho dashi" tai maganan tana haki sosai kaman zuciyanta zai fito baki, kallon Fatima dake duke tana kuka sosai tayi kanta akan guiwanta tace "kekuma tashi kibar nan kije kiyi girkin, kafin natayata kara miki algunguma mai kama da larabawan jahannama" ahankali tashiga tattaba bango tamike tsaye da kyar jikinta har kyarma yake tsabagen wayan wutan datasha sanan tawuce ta lallaba tafita daga dakin tai kitchen, saida tafita sanan matar tace "kiyakuri kedai kiyita addu'a Allah bata miji ta tattara tabar miki gidan nan ki sakata ki walada mijinki" da sauri tace "ina Allah yabata, yarinya sai bakin jini gadon uwarta, ko mashinshini batada shi" da sauri matar tace "duk kyan nan nata" da sauri Maman Habib tace "kyan dan maciji ne, tayi gadon bakin hali ina zata samu wanda zai kwasheta yakaita gidanshi amatsayin mata"? "adai dinga hakuri Maman Habibu amman dai ina bayanki kitashi tsaye karki bari tabata miki yara" murmushi tayi tace "nagode Maman Zainab, bari ta sauke abinci zan aiko miki dashi, wlh nagaji dacin shinkafa taliya kullum yau kawai nai marmarin tuwon shinkafa da miyan taushe da kan rago zai aiko miki dashi nariga nagama miyar" cikeda jin dadi har wani sude baki Maman Zainab take tace "Allah bar mana Maman Habibu kap gidan nan babu kaman ki, godiya nake, bari naje to", fita tayi tana karamata godiya, itakuma Mama ta kalli Habib dake kuka har lokacin tace "zonan" zuwa yayi yazauna agabanta shafa kanshi tayi tace "kaga kasa nadakeka a banza ina ruwanka da wanan shegiyar nace muku ba yar uwarku bace, ya isa dena kukan jedaki kadauko biredin dana ijiye muku kaci kaida kanninka" ko kallonta baiyiba yatashi ya shige dakinsu fuuuu, tabe baki tayi tadauki Abida tace "mayyar nono ungo kafin ki kashemin dodon kunne" .

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_


Taci kuka harta godema Allah sanan tai shiru, babu indabaya mata ciwo ajikinta haka adaddafe ta kada miyan ta kashe wutan tadaura miyan atray tadauka tana tafiya ahankali tawuce daki, har gaban Maman takai tukunyar ta ijiye ahankali murya chan kasa tace "Mama gashinan nagama" ko kallonta Maman batayiba hakan yasa ta dafa kujera tamike tsaye da kyar zata wuce dakinsu Mama tace "ubankine zai dawo daga wajen neman dayaje yakawo miki kwanukan daza'a zuba abincin"? Girgiza kai tayi tawuce takwaso kwanukan da Mama tazuba tuwon already, miya Mama ta zuzzuba ta mikama yaran sanan tadau kwanonta ta zuba miya kafin tadau kwanon ta wurga mata da tuwon da miyan suka bare kan hijabin ta ihu tayi sosai dan yadan tabamata jiki ta tashi tacire hijabin tana kuka sosai, hararan ta Mama tayi tace "bacemin daga gani jaka kawai mai bakin jini" dakinsu tawuce ta shiga ta ijiye hijabin awaje daya ta kwanta akan gadonta jikinta na kyarma har lokacin tana kuka ahankali, Habib najinta amman yakasa cemata komi but bakaramin tausayinta yakeji ba, tayi kuka tayi kuka ahaka bacci yay gaba da ita batai magrib ba balle ma isha'i.

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_

Wuraren goma da rabi baba yashigo lokacin duka yaran sunyi bacci lekasu yayi ganin duk suna bacci yasa yasaki labulen yawuce dakinsu zaune yaga Mama tana kullama Abida datai bacci pampers yace "kowa yaci abinci ko Ruka" fuska adaure tace "jeka tashesu katambaye su mana" murmushi yayi yace yau yan rigiman na nanne, kulanshi yaja yashiga cin abinci batare daya karace mata komiba saida yagama sanan yay yan abubuwa kafin yarage kayan jikinshi ya kashe wuta yazo yahau gadon ya kwanta yay shiru, juyowa tayi ahankali tace "kasamo wani abu?" girgiza mata kai yayi yace "duk wayanda nake tunani zasu iya bani bashin kudi basu baniba, lokaci na gudu Ruka ya zamuyi bakiji yanda kaina keciwo ba wallahi" tabe baki tayi tace "karkaje kajama kanka jininka ya buga abanza duk yanda kaddara tasamu mutum haka yake daukanta" shiru dukansu sukayi basu sake cewa komib*a kowa da abinda yake tunani aranshi......



_DAN MAGANA DANI M SHAKUR KOKUMA KARIN BAYANI KAN ADVERT A TUNTUBENI ANAN 07012181461_








💫 _DISASTROUS LOVE_ 💫


_MASIFAFFIYAR KAUNA_


_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&GNaturals_




✍🏾 M SHAKUR


EPISODE 4️⃣


_FREE PAGE_
Wuraren karfe uku wani mugun azababben ciwon ciki yatadata, da farko tazaci mafarki take amman sai taga ba mafarki bane, wani irin murda wa da cikinta da maranta sukeyi kaman ana murda hanjinta kanta na shegen sarawa, kokarin tashi tayi daga kwancen datake amman takasa sabida komi najikinta wani irin ciwo yake mata, ahankali tasaki wani wahalallan kuka mara sauti..... cikin bacci kaman daga sama Habib yaji sheshekan kuka tashi yayi yabude idanunshi, dayake yanada wata yar karaman tocula hakan yasa ya kunna ya haska Fatima dake kwance idanunta sun kumbura sunyi jajir sabida kukan datasha jiyada daddare gakuma bacci, karasawa yayi kan katifarta da sauri, murya chan kasa gudun kar Mama tajisu yace "Ya Faty menene kike kuka"? Yay maganan yana kai hannunshi saman goshinta wani irin zafi dayaji yasa da sauri yadauke hannunshi yace "innalillahi Ya Faty bakida lpy in tada Baba"? Girgizamai kai tayi, cikin muryanta da ba'aji sosai tace "dagani na zauna" hannunta datake mikamai yakama yadagata ta zauna da kyar tana share hawaye tana cizan baki, sosai yaji tabashi tausayi, yanason Ya Faty kaman ba gobe dan tamafi kulada su kan uwarda tahaifesu, tun suna yara itane komi nasu, duk in yanajin yunwa saidai in Ya Faty batada kudi amman saita bashi yaje yasai wani abin, idan basuda lpy, Mama nafita kome sukeso saita dafa musu suna gamawa su wanke tukunya ta yanda Mama bazata saniba, ganin yanda hawaye yakasa dena zuba daga idanunta yasa yakoma kusada ita ya zauna kanshi ya daura kan hannunta yafashe da kuka ahankali gudun kar ajisu murya chan kasa yace "Ya Faty kiyakuri kinji Allah na sama yana kallo wata rana sai labari, Mama batada kirki kuma batason ki amman kinga duk ranan dana girma zan daukeki daga gidan nan nasai miki wani gida nasai miki mota nasa police nace musu karsu bari Mama ta shigo balle ta dakeki kota saki kuka, I promise idan na girma ko maganan banza babu wanda ya isa yafada miki kinji, kidena kuka, bari na girma kiga abinda zai faru kidena kuka" yay maganan yana share hawayen dake zubomata, danne kukan tayi takai hannunta ta sharemai hawayen shi shima tana murmushi tace "ninasan kanina soja ne, Habib dina, nasan idan Habib ya girma ko kallon banza babu wanda ya isa yamin, Habib dina sojana toko tubambale mayen abinci" dariya yahauyi kaman bashine ke kukaba, murmushi tamai tace "jeka koma baccin ka kaji" da sauri yace "kinji sauki"? Gyadamai kai tayi alamun eh, tashi yayi yawuce ya kwanta awajen shi yace "dazaran yacigaba ki kirani kinji" Tom ta amsashi ahankali, kwanciya yayi tareda kashe toculan, sai alokacin taji ashema hiranshi rahama ne agareta wani mahaukacin ciwone yakamata dayasa taji kaman zata kurma ihu amman ta daure tarasa inda zata saka kanta taji dadi, har aka kira asubahi idanunta biyu, har aka tashi tanaji Baba yabude kofa yafita yadawo amman takasa koda motsi.
**


_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&G_


Wuraren shida nasafe Habib yaji wani irin nishi da sauri yabude ido ganin gari yay haske yasa ya kalli katifar ta da sauri ganin Ya Faty kwance tana wani irin nishi kaman wacce ake fizgema numfashi yasa yawani irin kwala ihu. "Ya Faty!!!" yatashi da gudu yay kanta, ganin jini akan gadonta yabaci jikinta yabaci Ya Faty dabaka ganinta babu hijabi amman wanan karin zaninta wuri guda, yar under skirt dinta baki iya cinyan ta ne kadai yarage ga fararen cinyoyinta sun baci da blood yasa Habib ya kwalama Mama kira. "Mama! Mama! Baba! Babaaa!!" dawani irin sauri Abba yadiro daga gado dagashi har Maman suka fito jin yanda Habib ke kwala musu kira, Abba ne yariga shigo dakin Mama biyeda shi, kafinma Abba yay magana ganin Fatima yasa yay kanta da sauri yace "innalillahi wa innailaihi raji'un, maiya sameta Habib? Ke Zara'u, Zara'una Baba"? Gabaki dayama batasan inda kanta yakeba daukanta Baba yayi yasata ajikinshi yana jijjigata yace "ke Zara'u, kallen, nine nine meke damunki"? Cikin kuka Habib yace "tun cikin dare naji kukanta, jikinta yay zafi tahanani tadaku ni bansan meke mata ciwo ba" dagokai da sauri Baba yayi ya kalli Ruka dake tsaye inda take yace "Ruka huramin wuta kisa ruwa tai wanka mutafi asibiti" hararan shi tayi tace "ai hala kasayo itace ne" da sauri yace "to saman mini awajen makota dan Allah" tsaki tayi tace "kaima kasan abinda banyi kenan rokon makota saidai ni suzo suyi maula wajena, Um ni kaga tafiyata ku karata" tawuce tasakin musu labule tai gaba abinta, rasama abinda zaiyi yayi ganin haka yasa Habib yace "bari naje wajen Maman dadi" "yauwa Habib" da sauri Habib yatashi yafita bucket yadauka yay kitchen din gidansu wajen wata mata dake kitchen yaje direct cikeda tashin hankali yace "Maman Dady dan Allah ki tsammana ruwa Ya Faty batada lpy wanka zatayi mutafi asibiti" da sauri Maman Dady tazuba mai aroba tace "ayyah Allah bata lpy" karban ruwan zafin yayi yaje bakin rijiya ya sirka ruwan yadauka yakai bayi sanan yadawo daki, lokacin daya shigo yaga har lokacin tana jikin Baba daidai tabude ido, ahankali Baba yace "meke miki ciwo Zara'u"? Murya chan kasa tace "ciki da kai" Habib daya tsaya kansu yace "Baba nakai ruwan bayi" ahankali Baba yace "zaki iya tashi tsaye ki chanza kaya"? Gyadamai kai tayi tashiga kokarin tashi da taimakon Baba da Habib tamike tsaye, zani Baba yanemo mata yasamata a hannu yace "cire kayan ki daura wanan saiki kirani zomu fita mubata wuri Habib" fita sukayi shida Habib dakin Mama ya shiga yasame ta zaune tana bama Abida nono, cikeda damuwa yace "dan Allah zoki taimakawa yarinyar nan tai wanka kinga suma taketayi Ruka" wani kallo tamai tace "gaskiya kayakuri amman bazan iyaba kuje chan ku karata" jin karan fadin abu timm yasa dagudu daga Baba har Habib sukai dakin itane tazube akasa asume tacire kayan amman bata gama daura zanin da kyau bama. "innalillahi wa innailaihi raji'un kawomin ruwa Habibu" Baba yay maganan yana daukanta yana gyaramata daurin zanin tareda fitoda ita falo, daidai Habib nakawo ruwa, shafa mata a fuska yayi ta farfado kaman zai mata kuka yace "sannu kinji, Habib biyoni da soson wanka" tama kasa tafiya daukanta Baba yayi har zuwa bakin bayi yama rude yarasa yanda zaiyi kallonta yayi yace "zaki iya wanka"? Gyadamai kai tayi idanunta dabasa buduwa da kyau, da sauri Habib yace "Baba wlh bazata iyaba kartaje tafadi tasume abayi" hayaniyan su da Maman Dady taji yasa tafito daga kitchen ta zagayo hakanan tanason Fatima sabida natsuwa da kunya da girmama na gaba da ita, tana kallon jikin mahaifinta yanda yabaci da jini tagane meke damunta tace "assha sannu Fateema, kawota nan Baban Habib bari natayaku" da sauri Baba yamika mata Fatyma, karbanta tayi ta shigar da ita bayi babu ko karfi daya ajikinta, sanan ta turo kofan tsayawa Baba da Habib sukayi suna jiransu, basu wani dadeba Maman Dady tafito da ita tace "dauketa Baban Habib zata iya zubewa Allah yasawake" da sauri Baba yadauketa yace "nagode Allah ya sakada alkhairi" wucewa da ita Baba yayi shikuma Habib yadauki bucket da so so Maman Dady tabisu da kallo bakaramin tausayin Fatyma takeji ba, daga ita har Mahaifin nata da aka gamada shi, bata shiga harkan Maman su sabida wlh zata iya mata dukan tsiya kan fatyma dan arayuwanta ta tsani zalunci, tadade tana tunani saikuma kawai tawuce ta shiga dakinta, always ta dauko tasaka a leda dawasu sababbin pant da mijinta yasayo mata na jegon Dady dabatai amfani dasuba dan sunmata kadan, kullewa tayi a bakar leda, sanan tafito tai sallama gaban dakinsu fitowa Habib yayi bashi tayi tace "gashi kabama Baban ka yabama Fatima" karba yayi yakoma ciki itakuma tawuce abinta.

Baba na kokarin zaunar da ita kan gadonsu Habib, Habib ya shigo ya mikamai ledan da Maman Dady tabashi tace "Maman Dady tace kabama Ya Faty" karba Baba yayi yabude ganin me aciki yasa yabata yace "kin iya amfani dashi Zara'u"? Gyadamai kai tayi idanunta na kukkullewa dan bata gani sosai, barinta Baba yayi akan gado yaje wajen kayanta yadauko mata wani atampan na riga da zani bakida da ruwan toka sanan yadau sabon hijabin da Maryam tabata dayagani saman kayanta ya ijiye mata komi gefenta yace "lallaba ki saka kayan kinji bari nahado miki shayi nazo" fita sukayi shida Habib yawuce uwardakan su ko kallon Ruka baiyiba yay wajen kayan shayi yadeba yazuba a kofi sanan yazuba ruwa ya yagi buredi yafito tsayawa abakin kofan yayi yace "kin gama Zara? Zara" yasake kiranta shirun dayaji yasa ya kutsakai ya shiga dakin ganinta yayi tasa pant din da pad ajikinta, tasaka riga amman takasa jan zip din ta kwanta akan gadon tana wani irin rawan sanyi kaman wacce zata mutu, rasama mezaiyi Baba yayi yace "innalillahi Zara'u karkimin haka kinji" dagata yayi jikinta kaman wuta yahada zip din yaja sanan yadau zanin dagakan gado ya daura mata sanan yazauna akan gado yana kwalama Habib dake falo kira. "kawomin shayin Habib" shigowa Habib yayi da shayin ya karba yace "sha tea kadan kidan samu karfi saimu tafi asibiti ko" girgiza mai kai tayi tareda sakinmai kuka ahankali da muryanta dabaya fita tace "Baba ni kasayo min magani allura za'amin a asibiti" murmushi yamata yace "sha shayin to mugani tukunna inkinsha da kyau sai na sayo miki magani" kai shayin bakinta yayi ta kurbi kadan ko idasa hadiyeshi bataiba sai amai bata kasan dakin tayi da aman da babu abinci aciki, tashi Baba yayi yace "bari na chanza kaya mutafi zauna da ita Habib" zama kusada ita Habib yayi yadau

Please Login or Register in order to submit comment