Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hijabinta yasaka mata shi karan kanshi saida tace "kai wanan hibajin mai hulan nan yamiki kyau sosai" daki Baba ya shiga ya chanza kaya yadau key machine dinshi sanan yajuyo ya kalli Mama yace "bari nakaita asibiti" yan dubu biyun dake aljihun wandon shi yaciro yakalla sanan yatura a aljihu sanan yawuce yafita ya gungura machine dinshi zuwa waje lokacin 8 dayan mintoci nasafe sanan yadawo ciki, dagata yayi Habib yakawo mata silifas dinta tasaka Baba yariketa tana ta karkarwa da kyar suka fita waje saida yafara daurata kan machine din sanan yahau yatada suka tafi General.


Ahankali yake gudu da ita jin yanda jikinta ke bari, saisa sukai kusan 30min kafin sukai, parking yayi inda ake parking ya sauko ahankali sanan yakamata ya saukoda ita yana tattare ta gudun karta fadi yace "sannu Zara'una, muje" riketa yayi suna tafiya ahankali tana binshi ahankali dishi dishi take ganin gabanta daidai sun shiga ciki dip tadena ganin komi daga sama sama taji muryan Babanta na ihu "ataimakamin ataimakamin jama'a".

_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&GNaturals_


Dawani irin gudu nurses suka gungunro wani gado aka karbeta daga hannun Baba suka dagata sauka daurata akan gadon akai ciki da ita, wani babban examination room suka shiga da ita Baba zai bisu aka hanashi shiga sanan daya daga cikin nurses din tafito tashiga wani consultation room saigata tafito tareda wani Dr dabazai wuce 35yrs ba yana sanye da farin glasses a idanunshi wuyanshi sanye da stethoscope, wajen aljihun Lab coat dinshi ta gaban rigan anrubuta Dr Imam, da sauri sauri gudu gudu suke tafiya daidai zasu shiga dakin Baba yarike hannunshi gam hakan yasa yajuyo tareda tsayawa ya kalli Baba yakuma kalli hannunshi da Baba yarike irin lafiya, kaman wanda yazare dakin Baba yanuna mishi cikin wata irin raunanniyar murya yace "likita y'ata ce acikin dakin, dan Allah kataimaka mata kar wani abu ya saman mini Zara'una likita" wani calm smile Dr yayi tareda karbe hannunshi daga hannun Baba yakama kafadar Baba ya zaunar da Baba kan kujeran dake wajen yace "abinda nakeso dakai Baba shine ka kwantar da hankalin ka kazauna anan kama yarka addu'a, abangarena kuma namaka alkawari zanyi duk abinda zan iya naga na ceto rayuw........." bai karasa maganan ba wata nurse tafito tace "Dr come she's convulsing" da sauri yay ciki yana yana kallon Baba yace "just stay here" da gudu ya shiga dakin ya karbi handglove din da wata nurse ke mikamai yana sakawa a hannu yana kallon patient din sanan yace "ya za'ayi tana convulsing bazaku cire mata wanan hijabin ba, ku cire mata and someone should on the AC" yafada ba wasa sanan yakarasa inda take bayan yagama saka hand glove din, ahankali yakai hannunshi yajuyo da ita, tareda karban wani kalan spoon da nurse kebashi yakama kumatunta ya matste bakinta yabude yasa cokalin abakinta gudun karta taune harshenta, zafin dayaji ajikinta saida yabashi tsoro, sanan ya karbi alluran dayasa abashi yakama hannunta yanemo jijiyanta yamata allura, ko minti daya ba'a daukaba tadena convulsing yay stabilising nata, yasake saka wani sabon alluran ya debo jininta awani a syringe din yabama wata nurse yace to the lab" sanan ya kalli wata nurse yace "send in the father" fita tayi bata jimaba suka shigo tareda Baba hakan yasa sauran nurses din suka fita shikuma yadauki wani paper da byro ya kalli Baba dayaga yaje ya tsaya akan Fatima yana kallonta yace "ya sunan yarka Baba"? batare daya kalleshi har lokacin idanunshi nakan Fatima yace "sunanta Fatima Zarah Muhammad" gyadama Baba kai yayi bayan yarubuta yace "meya sameta, meka damunta, tamaka complain wani abu namata ciwone"? Ajiyan zuciya ya sauke yace "ni jiya narabu da ita lpy kafin natafi aiki, nadawo gida wajajen goma sunyi bacci, saida safen nan kaninta yakirani nazo naganta babu lafiya, ciwon cikine na al'ada dakuma ciwon kai" rubutawa yayi sanan yace "daman haka yake mata"? Gyadamai kai Baba yayi yace "eh haka yake mata amman kusan watananni biyu dasuka wuce ko ciwon kai batayiba sai wanan watan kuma, sumanta kusan uku agida, kome taci sai amai, batada karfi ko kadan, tun dare babu aiki sai kuka" sake rubuce rubuce yayi sanan ya ijiye takardan yadauko wata paper yay rubuce rubuce sanan yamikama Baba yace "yanzu dai kafara zuwa kasayo wayan nan magungunan a pharmacy kafin result din test dinta yafito mufara treatment yanzu kawai stabilising condition dinta nayi ba'a mata komiba tukunna sai kaje kabiya kudin kati da folder abaka ka kawomin anan da magungunan."



_G&G NATURALS wato Glow and Go Skin kenan, wanan kampanin ni nakan kirasu mane da transformation dan suna saida wani Body and face scrub da idan kakai amfani* dashi ko jariri bazai nuna miki taushin jikiba, sanan yana cire dead skin, acne dakuma pimples, black spot da sauransu kiji fatarki washar gata tai wani ubaaan laushi, suna saida wani gangariyan black soap, dakuma glow oil, kikai amfani da products dinan nasu kowa ya ganki saiya yaba, me kike jira Anty na? Kira daya kacal ya isheki kisami kayansu, suna tura kaya kowani gari, zaki iya tuntubarsu ta wanan number wayar 08144513333, zaki iya following nasu a Instagram @G&GNaturals








💫 _DISASTROUS LOVE_💫


_MASIFAFFIYAR KAUNA_




✍️M SHAKUR



EPISODE 5️⃣
_FREE PAGE_


Karban takardan Baba yayi kaman mara lafiya yajuya yana tafiya ahankali yafita daga dakin yay reception, tsayawa awajen yan kati yayi yabude kati da folder, folder dubu daya, karamin kati kuma dari uku yarage duka kudin saura dari bakwai, bai karayaba yarike komi a hannunshi yawuce Pharmacy ya tsaya gaban kanta tareda mika musu takardan da Dr yabashi, gani yayi anciro gorunan ruwa, allurai daban daban dawasu magunguna ankawo gaban table anyi wani tabe tabe a computer sanan aka fitomai da wata yar takarda, namijin wajen ya mikamai yace "Baba ga takardan biyan kudi je chan wajen account kabiya kudin saika dawo mana da takardan biyan kudin saika amshi magungunan katafi" karban takardan yayi ya kalli kudin dake rubuce awajen dubu takwas da naira Dari da talatin wani irin mugun faduwa gabanshi yayi ahankali yajuyo ya kalli saurayin dahar ya juya yakoma wajen zamanshi, dan gyara muryanshi dayaji ta shakemai yayi yace "Yallabai jimana" tasowa saurayin yayi yazo yace "gani Baba" cikeda damuwa Baba yace "kaga y'ata ce ba lpy, rai a hannun Allah, duka duka yanzu chanjin hannuna basufi dari shida ba, nace kozaka bani abubuwan nafara kaima likita afara mata treatment, inyaso kafin mubar nan wajen saina biya kudin daga baya yanzu dai afara bata taimakon gaggawa" dan murmushi pharmacist din yayi yace "Baba kenan, kayakuri Baba bama haka awanan asibitin" yanamai maganan yashiga attending to wasu mutane dasukazo wajen siyan magani, gajiya da tsayuwa Baba yayi awajen kafin ahankali yadaga kafafuwan shi dayaji sunmai nauyi sosai yawuce yafita, ahankali yake tafiya haryakai wajen parking space, sabida kar mutane su ganshi yasa ya zaga ta gaban motoci yazauna kan dakalin wajen yay shiru yana kallon folder da katin daya bude mata ga sunanta ajiki baro baro, Fatima Zara'u Muhammad, yarinyar nan tun tana yarinya wahala take yanzu gashi tana ciwo baida kudin kulada ita, jiya da yafita neman kudi yaje babu wanda yasani dayabashi kudi koda sisine, Rukayya ko yasan ko Mutuwa Zara'u zatayi bazata taba cire kudin ta tabada ba, dudda yasan itama ba lallai yasamu irin wanan huge kudin a hannunta ba amman bazai rasa yarsu dubu dubu biyuba, toya fita yay bara ne? Ya tambayi kanshi, but ayanda duniya ta chanza babu wanda zai ganshi yanzu haka ya yarda yabashi kudi yayi tsaf tsaf dashi gayar shaddar shine tsaf tsaf ne za'a yarda abashi taimako, jiyayi wasu hawaye masu shegen zafi sun zubomai yakai hannu ya share amman suka kasa dena zuba hakan yasa kawai ya barsu suka slcigaba d kwarara.


Agogon hannunshi kirar iwatch dake daure a wrist dinshi ya kalla about 25min kenan Baban Patient dinan bai dawoba, dagakai yayi ya kalli yarinyar ganin har yanzu she is stable bacci take yasa yadauki stethoscope dinshi yarataya awuya ya kalli nurse din dake wajen yace "stay with her, idan her Dad yakawo magungunan call me, idan ta tashi call me" yana maganan yajuya yafita daga dakin yay hanyar fita waje batare daya kalli dumbannin mutanen dake GOPD ba, tun 4 nasafe ya shigo asibitin nan emergency baici komiba har yanzu yunwa yakeji sosai by 1 yakeso yatafi gida yahuta yay bacci, wajen parking space yakarasa yay wajen wata hadaddiyar Black suv bude motar yayi da key dinshi sanan yamika hannu yadauko wani haddedden moderate flask dake kan dayan sit din gaban mota, bude marfin flask din yayi da saurinshi sabida tsabaragen yunwan dayakeji yakai flask din bakinshi yana kwalkwalan coffee dake cikin flask din daya hada da asuba dazai fito, saida yay kusan rabin flask din sanan ya sauke daga bakinshi yana sauke ajiyan zuciyan gajiya, saida yadan huta sanan yadaga flask din zai kara komar dashi baki kaman ance ya kalli bangaren damashina ke parking ya hango wani mutumi dan magidanci dabai ganin fuskarshi da kyau zaune gaban wata mota a side dinshi rikeda folder a hannunshi yana share hawayen dake bin fuskarshi looking so confused and sad, jiyayi zuciyarshi ta tsinke dan haka Allah yayishi yanada tausayi sosai, kasa cigaba dashan coffee shi yayi dudda uban yunwan dayakeji, maida flask din yayi ya ijiye, yamaida kofan yarufe yamata key sanan yataka ahankali yana tafiya harya isa inda Baba yake zaune kanshi akasa yana share hawayen dake zubomai baima lurada wani yazoba dan hankalinshi yay nisa yana tunai. "is everthing okay Sir, mesa kazo nan kazauna kana kuka"? Wata zazzakan muryan da Baba yaji akanshi namai magana cikeda kamala hakan yasa yadago kanshi da sauri da idanunshi dasukai jajir yahada ido da Dr daya rubutamai maganin Zara, Dr na ganin Baba yaganeshi shima at a spot ai mutumin dazune Baban yarinyar dake emergency ward, ganin Baba yace "what is it Sir? Mesa kazonan kake kuka ina magungunan danace kasayo"? Dr yay tambayan yana kallon Baba yana kara nazarin yanayinshi, baki Baba yabude zaiyi magana saikuma wani irin takunkumin bakin ciki yakara tokaremai wuya wasu hawayen suka sake zubomai, kaman wanda notin kanshi ya kwance baisan lokacin daya kwaso yan chanjikan dasuka ragemai ba a aljihu yanuna ma Dr idanunshi sunyi jajir ga hawaye sun cika idanun kana ganinshi kasan he is pain yace "kagansu wanan ne kudin danake dashi gaba da baya, banda hanyan samun wasu, Zara'u na nachan kwance rai a hannun Allah an rubutamin maganinta nakasa saya sabida bandashi, bandashi, ina zansa raina? Asibitin gwamnati ma nakasa biya ba dole nazo nan na zauna ba likita" yanda yake maganan kaman ma wanda baya cikin hayyacinshi tsabagen damuwa yasa Dr yacigaba da tsayuwa a inda yake batare dayay motsi ba yay shiru yana kallonshi kawai, hawaye Baba yasake sharewa yace "Kaga Zara'u itace y'ata ta farko, tunda yarinyar nan tazo duniya bata tabajin dadi naba ni Mahaifinta, bana saya mata kaya, kaya irin nakowace yarinya budurwa datake tasowa, Zara'u bata tabamin korafi ba kokuma tace saina mata, yarinyar nan bata taba bude baki ta tambayeni abuba, kotamin korafi kotanunamin bacin rai, banmata kayan salla, bansiya mata takalmi, babu abinda nakema Zara'u sabida bandashi, yarinyar nan bata taba yimin kocemin Baba yimin kaza ba, yarinyar dake tausayin mahaifinta nake wahalarwa haka gashi yanzu ma datake rashin lpy nakasa mata komi, wlh ban cancanci zama mahaifint........" kafin Yakarasa maganan Dr ya tsugunna da sauri yakai hannunshi kan bakinshi hakan yasa Baba yay shiru yana kallon kyakkyawan fuskar Dr dake sanye da glasses, cikeda tausayi Dr yajanye hannunshi daga bakin Baba ganin yadan natsu yana kallonshi, hakanan yaji Baba ya mugun bashi tausayi, ahankali yace "Sir ba'a magana haka, Allah daya baka yarka yasan ka chanchanci zama mahaifinta ne saisa yabaka ita a matsayin y'a, sanan aganina godiya yakamata kama Allah daya baka y'a irin wanan wanda tun anan duniya take jinķanka, and just because bamu bama yaranmu abinda yakamata mubasu ba, or bamu wadatasu da kayan alatun duniya ba ba doesn't mean we are not good fathers to them, karka kara magana haka Sir, I know yarka na alfahari dakai, and stop crying, yanzu dai nawane kudin magungunan"? Ahankali Baba yace "8150 sukace" gyadamai kai Dr yayi sanan yamike tsaye yakai hannunshi bayan wandonshi wallet dinshi yaciro yabude yazaro wasu kudade yan dubu dubu dashi kanshi baisan yawansu ba ya tsugunna, hannun Baba yakama yasaka kudaden aciki yace "jeka sayo magungunan kazo mufarama yarka treatment ko" yay maganan yana sakinma Baba coolest smile dake comforting any kind of heart, wani natsuwa Baba yaji ya shigeshi tareda sake rike kudin da kyau yana kallon fuskan Dr ya nisa zai bude baki yay magana wayan Dr dake aljihun lab coat dinshi yahau ringing ciro wayan yayi yana mikewa tsaye yana gani inda ake kiranshi yatashi da sauri yajuyo ya kalli Baba yace "get magungunan now ka kawomin she's convulsing again" da gudu yajuya yabar wajen shima Baba sake damke kudin yay gam gam ya tattare su folder yatashi yay pharmacy harda gudun shi.



Da sauri yatura kofan yashiga dakin nurses kusan uku ke kanta suna kokarin tura mata wani abu abakinta sabida yanda ta taune hashenta kadan har yana jini daya daga cikinsu tace "wai where is her father da magungunan"? Karasawa inda suke Dr yayi yana kallon yanda bakinta ke jini yace "me aikinku? Ya akayi kuka bari tajima tongue dinta ciwo"? Yay maganan yana grabbing kumatunta da kyau ya karbi abin yasa abakinta sanan ya karbi alluran dasuke bashi yakara pushing a jijiyanta cikin sakan daya tadena convulsing, hakan yasa yace "are the test result not ready"? Bashi wata takarda sukayi hakan yasa ya karba ganin result dintane zai duba daidai lokacin Baba yashigo dakin da mugun saurinshi yana kallon Zara ganin jini abakinta yasa yabude baki zaiyi magana da sauri Dr ya karbi magungunan da folder daga hannunshi yana mikama nurses yace "Baba she is fine yanzu zamu fara treatment kaje waje kajiramu kaji" fita Baba yayi adimauce yarufe kofan dakin dawowa ciki Dr yayi yahada kayan yazo yamata fixing drip sanan yahada wani allura wanda shi a duwaiwai zai mata sanan yarufe yazo ya tsaya akanta, fuskanta yadan kalla wanda zai iya cewa kusan sai yanzu ne yakalleta da kyau yarinyar ko ta mugun kama da mahaifinta itama farace kall kaman shi, ahankali ya ijiye alluran sanan yakai hannayenshi yadaura kan hannunta yadan juyo da ita ahankali ta side, riganta yadan daga sama kadan idanunshi ne suka sauka akan farar fatar jikinta kaman na jaririya ga dan gashi kadan kadan sun kwanta sunyi lub, hannunshi yasake kaiwa yadan ja zaninta hade da pant dinta kadan sanan yashafa spirit kafin ahankali ya chaka mata alluran motsin dayaji tayi yasa yadan waigo ya kalli fuskarta gani yayi ta yatsine fuska cikin bacci, cire alluran yayi yamika ma nurse din ta karba tasa a bola, sanan yajuya yace "ku tsaya da ita I will be back in the next 15min" yafice daga dakin Baba na ganinshi yatashi yace "Dr yatake"? batare daya kalleshi ba yace "muje office dina" binshi Baba yayi har zuwa office dinshi zama yayi tareda nunama Baba kujera Baba ma yazauna yace "meke damunta Dr naga jini abakinta" dan murmushi yayi yace "wanan ba matsala bane taune hashenta tayi kadan, I called u ne danna fadamaka I don't think zamu sallami yarka yau, result yafito tana dauke da maleria da typhoid masu karfi wanda sune ma kesata wanan convulsion din, gakuma ciwon mara at least zamu iya riketa na kwana daya ko biyu haka" shiru Baba yayi yana kallonshi cikeda damuwa, murmushi Dr yayi yace "karka damu zanyi settling hospital bill din wanan kudin hannunka ka rike na abinci dawasu abu ko" shiru Baba yayi saikuma chan ya nisa yace "Ya sunanka likita" anatse yace "sunana Imam Naseer Marafa" girgixa kai Babba yayi cikeda gamsuwa, yace "kaidan aljanna ne Naseer, Allah yamaka albarka, Allah ya saka da alheri da taimako na dakayi, azamanin nan da wuya ake samin likitoci irinku, awanan zamin likita iyaka kabiya yay treating naka, idan baka biyaba babu ruwan shi, Allah yamaka abinda kakeso kaji Naseer" shiru yayi yana kallon Baba kafin ahankali yace "Ameen nagode sir" Tashi ahankali Baba yayi yace "bari nabaka wuri" gyadamai kai kawai yayi Baba yawuce yafita, bin bayan Baba yayi da kallo yay shiru kaman wanda ke tunani kafin ya fuzarda iska ahankali ya jingina da kujeranshi tareda lumshe ido dan yagaji sosai.

Bude kofanshi da akayi aka shigo yasa yabude ido kadan ya kalli kofar, wata female Doctor ce mace kyakkyawan gaske doguwa tana sanye da atampa golden da dige digen pink ajiki, ta yana kanta dawani pink gyale chiffon plain bakomi ajiki saikuma lab coat dinta fari kal yasha guga sai kamshi take bazawa wajen aljihun ta an rubuta Dr Zee ajiki, maida idanunshi yayi ya lumshe ganin itace, karasowa ciki tayi taja kujera tazauna tace "Dr Helper koma Dr Charity zankiraka am here i need help too pleaseDr" dan yatsine fuska yayi alamun he's not into her silly talk, murmushi tayi tace "okay joke apart Dr Imam, I just came in, namanta da stethoscope dina agida kuma idan HOD yaganni wlh zansha fada, please kindly aramin naka kaji kasan Helper is your second name right Dr nice" tai maganan tana kallonshi tana murmushi cikada tsokana, ahankali yabude idanunshi kadan yadan kalleta saikuma ya yatsine fuska yace "wai why are all this intern Doctors not serious haan"? Dan murmushi tayi, hakan yasa yadaure fuska yace "ina magana kina murmushi, alright go and find stethoscope awani wajen not here" da sauri cikin kara narkan da murya kaman zatai kuka tace "no fa, ni wlh badakai nake ba" ganin yaki kulata saima wayanshi daya ciro yana kunnawa yasa tace "kasandai idan HOD yakamani bani kadai zaiyi scolding bako dan ai yasani akasan kane" dagokai yayi ya kalleta baison surutu idan kuma akwai macen dayataba gani aduniyan nan datafi kowa surutu is this girl, baimasan mesa HOD su yasata under him ba, dan gajeren tsaki yaja strictly yace "tashi kidau stethoscope daga that drawer and get out of my office Zeenat" yay maganan yana mata pointing drawer dake facing su a other side of the office wall, tashi tayi ahankali tai wajen drawer tana kara nanata yanda yakira full name dinta yau, ahankali ta sanya hannayenta taja drawer tabude taciro wani sabon stethoscope mai kyau blue tadauka sanan tamaida drawer ta juyo ta kallai gani datayi yasake lumshe ido kaman mai bacci yasa murya chan kasa tace "thank you Dr Imam" sanan tadaga kafa tai hanyar kofa harta murda kofan zata fita sanan yace "Dr Zeenat" da sauri tajuyo tadan bude manyan idanunta da mamakinta jin yakirata, folder yamika mata yace "this my patient tana Emergency, monitor her, I've written everything anan idan time yayi push d injections ma left hand veins dinta, i repeat left hand, idan any complications arise give me a call, idan kuma condition dinta yay stabilising move her to ward, zanje gida yanzu under no condition should u leave his hospital saikinga dawowana" kaman zatai kuka da sauri tace "waimena maka daga zuwana zaka hadani da irin aikin nan, yanzu harsaika dawo zan tafi? Inada bridal shower dazanyi attending fa by 5pm" tai maganan tana batarai sosai, dauke kai yayi yashiga tattare kayanshi tana tsaye tana kunkuni, lab coat yacire yarage dagashi sai kananun kayan dake jikinshi yadau wayanshi da car key dawani folder yazo zai wuce ya watsa mata wani mugun kallo, hadiye maganan tayi tareda sunnar da kanta kasa dan jitayi yacika mata ido bazata iya kallonshi ko cigaba da korafin ba yawuce yafita yabarta tsaye anan, takai kusan 2min dukan kirjinta bai dawo daidai ba sanan tasamu tabude kofan tafita har lokacin kamshin shi takeji.*











💫 _DISASTROUS LOVE_💫




_MASIFAFFIYAR KAUNA_




✍️M SHAKUR


_Deejerh Telecommunication offer data, TV cable subcription, and much more._
_Jama'a nakawo muku wata sabuwa wato Deejarh Telecommunications suna yima mutum data, suna tayaka biyan kudin subscription na Gotv, DSTV, startime harma da nepa bill zasu iya tayaki biya basaikin je nepa office kinbi layiba da sauran su, all abinda zakiyi shine kawai ki kirasu awanan number koki musu magana a watsapp 08107705128_





EPISODE 6️⃣

_FREE PAGE_
Fita yayi direct zuwa parking lot, motarshi yabude ya shiga yatadata yawuce yafita daga asibitin, agaban wani Baban gida a GRA yay horn ko sakan biyu ba'a dauka ba aka bude gate din yasa kan motar ya shiga ciki, packing yayi zai fito mai gadi daya rufe gate din yataho dagudu yace "angaida likita, Baban ka likita, Mamarka likita sannu ka da zuwa dan Alajin naira Alaji mai mutane nakowa" cikeda gajiya yasakamai key motarshi a hannu kaman zaiyi kuka yace "Ohhh i am not in for this your kirari Musa yau, ga key nan grab my things ka kawomin side dina and lock my car" yay maganan tareda juyawa yawuce abinshi, tsayawa Mai gadin yayi yarike kugu yakai yatsarshi daya kan kanshi yana tunani saikuma chan yanisa yace "wai ni da likita yaketamin yaren nan yadauka nima likitan ne yau, memawai yake nufi" "cha yayi ka kwashe kayan daya bari amota ka kaimai flat dinshi sanan karufemai mota" da sauri yajuya jin zazzakar murya na magana wata doguwar yarinya ce dabazata wuce 19 , 20ba, tana sanye da doguwan rigan atampa kanta a tsafe bama'a tajeba daga gani tsifa ake mata, harara mai gadin yaballa mata itama ballamai tayi tace "kazami kawai" da sauri yace "wlh saina hadaki da likita" gwalo tamai tajuya takoma flat dinsu shikuma ya shiga kwashe abinda akace ya kwashe sanan yawuce yay wani flat da shikadai ne daban agidan, sallama yayi tareda bude kofa yashiga ciki, falone hadadden gaske kal kal sai kamshi yake komi na dakin off whitene, shiga ciki yayi yana kalle kalle yace "dadina da likita akwai tsafta, kaga daki kaman nakara mai da yaji akai na ci tsabagen ban sha'awa" ijiye komi yayi kan centre table din sanna yawuce yafita yana kara waigen falon.


Sosai yabata lokaci sanan yafito yana sanye dawani short H&H 3quater milk color, yasanya wata black plain t-shirt, wanan karan babu glasses akan idanunshi hakan saiya kara bayyanar da kyawun kwayan idanunshi dasuke nan farare kal kwayan idon kuma bakake kirin, silipas yasaka sanan yabude kofa yafice, Baban flat din gidan ya shiga, wasu yan matane su uku ne a falon suna zaune suna kallo, suna ganinshi kowacce ta natsu atare suka gaidashi "Ya Imam good afternoon welcome" gyadamusu kai kawai yayi yace "how come banga ku fara shirin islamiyya ba" karaman cikinsu mai 19yrs din wacce ake kira da Rayyana ce tace "Ya today is Thursday fa" gyadakai yayi yace "oh okay, where's Ammi"? Kafinma subashi amsa sukaji murya datadan manyanta ance "anya akwai randa Imam zai iya dawowa gidan nan bai tambayi maman shi ba, ai kaga abinda yasa nafiji dakai kansu wa'è" tanuna babban cikin yara matan mai suna Rahma tace "su yaran Babansu ne" dariya yayi daidai ta sauko ya rungumeta hannunta takai kan cikinshi tace "zokaci abinci oya oya, cikin nan babu abinci cikinshi" dining takaishi tazubamai abinci a plate sosai yaci abincin yay nak sanan yafara mata hira, aduniyan nan Ammi kadai yake hirada ita kaganshi awani waje zaka dauka bai magana ko dariya.
Yatsine fuska yayi yace "Amma wlh nagaji da aiki at this government hospital, narasa maisa Dad baiso nai aiki a hospital dinshi" murmushi Ammi tayi tace "ai duk Dr

Please Login or Register in order to submit comment