Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Maman Basma Allah ya bar Qauna🤍 Allah ya raya Takwara


YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING...✍️


Domin shawarwari ko gudummuwa please...
👇🏻
08144066758

Taku har kullum
Yar mutan Argungu
Ke yi muku fatar alkhari🥰❤️```






































```ASHE BA SO BA NE...📚
Incomplete..🖊️
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❤️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya👍🏻


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


❤️ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU👌

Free Book📚

Bismillahir Rahmanir Rahim
🍓🍓🍓🍓
🍓🍓
🍓
24
Cikin tashin hankali Abba ke kallon Yayansa, "Yaya kasan me kake cewa kuwa? Nema kan nema fa kenan? Kuma kasan wannan abun da kake yi ko a musulumci haramun ne, dan Allah Yayaa ka rufa mana asiri kar ka jamana abun fade, wlh ba girman ka bane yin magana biyu, kuma ya kake tunanin iyayen yaron zasu dauki wannan batu wanda babu dadin sauraro. Gaskiya daya ce, kuma in ta zo dole a fade ta, tunda babu wanda zai iya fada maka ita in ba dan uwanka ba, kuma ni dai kayi hakuri idan na fadi ba dai dai ba..." Mike wa kawu Bala yayi yana cewa "eh, lallai Adamu ya ka nuna mini iyaka ta akan iyalanka. In ba haka ba, yaushe zan zauna Ina fada kana fada akan na ce ga wanda nake son ya auri diyarka, Adamu? Amma bakomi, laifi na ne da nake saka kaina cikin lamuranka, saboda haka, yarinya dai diyarka ce, toh ka je ka aurar da ita ga wanda kake son aura mata"
"Yaya Dan Allah ka zauna, wallahi ni ba haka nake nufi ba, gaskiya ce mai daci shiyasa baka fahimce ni ba, saboda Allah, yanzu Yaya misali a ce Dan mu ne ya je neman aure kuma sun ce sun ba shi, sai kuma daga baya a ce ya zo ya karbi kayansa anyi mata miji... Meyasa tun farko ba su ce anyi mata miji ba? Kaga a nan dole mu ji haushi kuma mu dauki abun da rainin hankali..."
"Yanzu dai in na fahimce ka, kana nufin ba za ka iya fada wa iyayen Yaron ba? Toh Allah na tuba ai wannan mai sauki ne awurina dan haka Kar ka damu nizan Kira su in fada musu duk abin da ake ciki, saboda haka tashi ka tafi sai ka sake jin yadda akayi insha Allah..."
Cikin sanyin jiki Abba ya tashi ya tafi. Bayan ya koma gida ya sami Ummi ya fada mata duk abun da ya faru, ya kuma kara da cewa " Umminsu kina ganin Abin da Hauwa tayi ta kyauta kenan? Ita ta kawo Yaron Nan ba muba, balle ta ce dole akayi mata kuma in ban da shashanci kin tsaida miji toh miye na kula wani can daban fisabillahi?!!! Ita dai Ummi tagumi tayi ta tsurawa kafet ( carpet) ido ba tare da tace komai ba, tana jinjina rashin ji irin na diyarta. Sallamar Hauwa ne ya katse shirun da ya ratsa parlon, kan ta a kasa ta gaida iyayen nata, har za ta wuce Abba ya katse ma ta hanzarinta da cewa " Hauwa zonan ki zauna" Bayan ta samu wuri ta zauna Abba ya tsareta da idanuwansa yana girgiza kansa cikin Bacin rai ya ke magana... " Dan ubanki abin da ki kayi miye shi? So kike yi a dauke ni mutumin banza ko Hauwa?!! Idan ba kiyi hankali yanzu ba sai yaushe za kiyi, ke ba ki san cewa yanzu ke ba yarinya ba ce?! "Wai ba dake ake magana ba kin samu gaba kina kuka kamar wadda ake duka? Wlh Abbansu ni da zanemin ita kayi sai tayi kukanta mai tushe." Cewar Ummi . Tsawar da Abba yayi ma Hauwa ne ya sa ta fara magana. "Abba dan Allah kuyi hakuri wlh ni dama ba son sa nake yi ba, Abba na ganinsa kawai ya ce ya turo iyayensa....Marin da Abba ya kaura mata ne ya katse ma ta zancen ta, cikin fushi ya nunata da yatsa "kina nufin duk Kai da kawon nan da bawan Allah nan keyi akan ki ashe ba son sa kike yi, kuma ki ka bari har na ba shi dama ya turo iyayensa Hauwa?!!!"
"ASHE BA SO BA NE Hauwa?" Cewar Ummi.
Haka Abba ya tashi ya bar parlon tare da takaicin abun da Yayansa da diyarsa su ke son aikatawa... Abangaren Usman kuwa tun jiya ya fadawa Nasir zai raka shi Zamfara gobe insha Allah. Yau tunda safe ya samu mama ya ce za su wuce yanzu, kasan cewar ita ma tasan da tafiyar, haka mama ta hada mishi turarukan Wuta ta ba wa Usman yayi tsaraba kuma tana gaida surukarta, haka dai su ka rabu tana tsokanar sa. Bayan sun dauki hanya ne Nasir ke tambayar Usman ko Hauwa tasan da zuwan su? "Aa ba ta sa ni ba, sabo da ban son tayi ta dawainiya kasan halinta da hidima". "Kuma fa gaskiya ne" cewar Nasir yana dariya.
Haka suke fira har suka kawo Maru, San nan Nasir ya ce "ya kamata yanzu ka kirata ka fada ma ta kasan bakyau a girshi mutum, hakan bai da dadi."
"Gaskiya ne dan uwa toh bari in kirata" cewar Usman, yayin da yake Kiran number Hauwa amma ana cewa NOT REACHABLE har su ka shigo cikin Gusau maganar dayace not reachable... Haka dai su ka isa gidan su Hauwa, Nasir ya aiki wani yaro yayi musu sallama da ita. Yaron ya shiga ya fadawa Ummi ana sallama da Hauwa awaje , Ummi tace " toh ka ce ana zuwa" ta shigo daki ta samu Abba ta fada mishi, kasancewar Hauwa na Asibiti ba ta dawo ba . Haka Abba ya fita ya gaisa da su Usman, ya kuma yi musu iso har cikin parlon sa, aka kawo musu ruwa da abinci. Abba ya tambaye su ya hanya da kuma jama'ar gida? "Kowa lafiya lau Abba ,mun same ku lafiya?" Cewar Nasir "Alhamdulillah, Nasiru ko?" "Eh Abba nine."


"Toh Masha Allah, Allah ya taimaka, sai dai kuma Hauwa na wurin aiki ba ta dawo ba. "Allah sarki bakomi Abba, dama mun xo mu gaisa ne... "Toh Masha Allah naji dadi sosai, ku Kirata sai tayi muku kwatancen wurin da take zai fi. "Toh Abba " haka su ka sake trying number ta Amma still not reachable. Haka dai Abba yayi musu kwatancen Asibitin da ka ward din da take, su kayi mishi sallama da cewar daga can za su wuce, yayi ta saka musu albarka. Dawowar ta kenan daga wurin duba patient kamar a mafarki ta ga su Usman, sai da gabanta ya fadi, murmushin yake tayi musu tare da cewar " Sannunku da zuwa My Dear saukar yaushe?" Tare da gaida Nasir
"Bamu dade da zuwa ba, munje can gida aka ce kina wurin aiki..."Allah sarki toh Bismillah ku zauna tare da jawo plastic chairs, amma shine ko ka kirani ?"
"Amarya ai munyi ta Kiran wayarki amma ana cewa NOT REACHABLE, but any ways laifin Angon kine tare da yi musu dariya...
Tashi Nasir yayi domin ya basu wuri su tattauna. Bayan ya wuce Usman ya tambayi Hauwa "menayi Miki da Baki daukar wayata my Dear? Kinsan damuwar da nake shiga kuwa a duk lokacin da na Kira ban samu number ki ba ?"
"Kayi hakuri kasan yanayin aiki na yadda yadda ke,bai kamata ace kana korafi ba, tana hararar sa ta gefen ido".
Murmushi Usman yayi yana cewa " Shikenan my dear na hakura Allah ya sa ba za a sake daga min hankali ba , yana smiling so lovely...
Su na cikin firar su, kwatsam suka ga Doctor Faruq a gaban su, kamar Wanda aka jefo. Fuskarsa murtuke cikin fushi, yana kallon Hauwa, ya nuna Usman ya ce " waye wannan?" Cikin rawar murya da makarkatar jiki Hauwa ta fara inda...inda... Kafin ta ce wani abu, Usman ya Mike tsaye tare da mikawa Doctor Faruq hannu, yana murmushi yace "Wanda za ta Aura ne" Da mamaki ya juyo yana kallon Usman tun daga sama har kasa sannan yace "WHAT?! Na tabbata Kai ba mahaukaci bane, Amma look please, bana son irin wasar nan." Lokaci daya murmushin fuskar Usman ya dauke ya ce, "kamar ya ?" San nan ya juya wurin Hauwa yace ma ta, " my dear, baki fada mishi about Auren ba ne?" Cewar Usman. Cikin mamaki Doctor Faruq ya juyo yana kallon Hauwa, yayin da Usman Shima ita ya ke kallo domin jin amsar da zata ba da. A wannan lokacin kuwa Hauwa ji take yi dama ace kasa zata bude ta shige wlh da taji dadi, akan wannan kunyar da ta isheta... Karar buga kofar da taji ne ya dawo da ita daga duniyar kunyar ta. Ko da ta duba, Doctor Faruq ya shige office, yayin da Usman ya nufi kofar fita. Ta kira sunansa " Usman... Usman...Amma Ina ya ri ga ya sa Kai ya tafi. Haka ta tsaya for seconds sannan tayi tunanin gwara ta bi Doctor Faruq ta ba shi hakuri, domin shi ne idan ta rasa shi zata shiga wani hali. Da wannan tunanin ne ta bude kofar office ta shiga. Jin an bude kofar office ya sa shi juyowa, idanuwansa sun yi jaa . Hauwa ya gani tsaye ,bude Baki tayi domin fara zubo bayanan karya, amma tun kafin ta fara ya katseta....


"SANNU SANNU BA TA HANA ZUWA, SAI DAI ADADE BA AKAI BA". GSKY INA JINDADIN COMMENTS DINKU ALLAH YA BAR QAUNA🥰

YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING...✍️

Domin shawarwari ko gudummuwa please...
👇🏻

08144066758
Taku har kullum
Yar mutan
Argungu ke yi muku
Fatar alkhairi🥰❤️```

```ASHE BA SO BA NE...📚

Incomplete..🖊️
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❤️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya👍🏻


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


❤️ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU👌

Free Book📚

Bismillahir Rahmanir Rahim

🍓🍓🍓🍓
🍓🍓
🍓
25
Amma tun kafin ta fara ya katseta... Ya daga hannu daya ya ce " Dakata. HOW DARE YOU?!!! ME KI KA DAUKE NI NE?! HOW DARE YOU THINK YOU CAN PLAY WITH MY INTELLIGENCE?! SHIN KINYI TSAMMANIN BAZA NA GANO BA?! DAMN YOU HAUWA!!! DAMA NASAN BAKI DA GASKIYA TUN DA HAR ANA MAGANAR KAWOO KAYA GIDAN KU,AMMA KO SAU DAYA BA KI BARI NA JE ZANCE GIDAN KU, SAI GIDAN KAWU, AMMA NINE WAWA DA BAN BINCIKA BA. YA KAMATA TUN LOKACIN DA KIKA NUNA BA KI DA INTEREST INZO GIDAN KU, YA KAMATA INYI BINCIKE KO IN JANYE. AMMA NO, LOVE BLINDED MY REASON..."


Cikin kuka Hauwa ke cewa "doctor dan Allah ka saurareni..."
Ya katseta, murya kasa kasa yace "get out of my office".
Ahankali Hauwa ta iso wurin shi tare da hade hannuwanta wuri Daya ta ce "Doctor, please..." This time ya katseta da tsawa tare da cewa "I SAID GET OUT OF MY OFFICE!!!" Da gudu Hauwa ta fita, zuciyar ta na dukan uku uku. Tun da take bata taba shiga tashin hankali irin na yau ba. Tabbas tana jin sauran Nurses su na gulmar cewa "doctor Faruq yana da fada, amma bata taba gani ba sai yau." Sabo da tashin hankalin da take ciki, bata ma tsaya dutyn ta ya kare ba, ta kawai ta fi gida, ba ta damu da problem din da zata shiga ba, idan aka duba ba ta nan...
A bangaren su Usman kuwa... Ganin halin da Usman ya ke ciki ne ya sa Nasir saurin zuwa gurinsa, tare da bude masa mota ya shiga. Yana mamakin me ya faru da Abokin nasa, amma shi kansa ya san ko ma menene toh ya danganci Hauwa. Haka Nasir ya bude driver's side ya shiga tare da sauke ajiyar zuciya, yana yi ma abokinsa fatar ko ma menene ya zo da sauki...
Bayan sun kama hanya ne Hauwa tayi ta Kiran wayar Usman, kusan 10 missed calls, amma bai dauka ba, daga karshe ma yayi blocking number dinta. Duk wannan abun da ya ke yi, Nasir na kallon sa ta wutsiyar ido, amma bai ce mishi komai ba. Dama haka Usman ya ke idan yana fushi ba ya magana, shiyasa Nasir ya ba shi time.
Usman ya maida seat dinsa baya, ya rufe ido. Nasir kuma ya maida hankalin sa kan titi ya ci gaba da tukii, tafiyar dai ta zama so silent, har suka shiga Argungu. Nasir ya Kai Usman har gida, yayi parking motar suka fito a tare , yayin da ya mikawa Usman key din motarsa. Juyo wa Usman ya yi yana kallon Nasir, tare da karbar key din. Bayan seconds kadan yace. "Thank you, aboki." Ya juya zai tafi Nasir ya Kira sunansa, ya tako har wurin da Usman ya ke, tare da daafa kafadarsa San nan ya ce mishi "Don't despair, and never lose hope, because Allah is always by your side. Insha Allah. Ko me ke damunka na san ba shi da dadin sauraro, toh amma gobe zamu yi magana Insha Allah." Usman ya lumshe idanuwansa alamar ya gamsu da abun da Nasir ya fada ya juya ya shiga gida. Nasir ya juya ya tafi Shima...
A wurin su mama kuwa, su na jimamin yadda za su fadawa Usman cewar "Kawu Bala ya Kira su, ya basu hakuri da cewar an fasa ba wa Usman Auren Hauwa." Sallamar Usman ne ya sa kowa ya dago kansa . Ya samu wuri ya zauna , bayan ya gaisar da mama da Alh. Sanusi. Mama ce ta kara kallonsa da kyau sannan tace "Babana, har kun dawo?" Usman ya amsa da "Eh mama, mun dawo"
Bayan few seconds Alh. Sanusi yayi gyaran murya, tare da fuskantar gefen da Usman ya ke, ya fara da cewa. " Usman, menene matsayina a wurinka?" Usman ya dago kansa ya kalli Alh. Sanusi, sannan ya ce "matsayin mahaifi". Murmushi Alh. Sanusi yayi yana cewa "Alhamdulillah, naji dadin wannan maganar. San nan ina son ka bani hankalin ka da kyau, ka saurari abun da zance ." A hankali Alh. Sanusi ya warware wa Usman duk abun da ya faru a
tsakaninsa da Alh. Bala... Dago kansa Usman yayi ya kara kallon mama wadda ta tsorace ta ga reaction dinsa, san nan ya ce "Baba babu komai, ai kunyi iya kokarin ku, Allah sa haka ya fi zama alkhairi." Tare da tashi zai wuce dakinsa. Maganar Alh. Sanusi ce ta katse mishi tafiyar da ya ke yi... "Usman, zo ka zauna, akwai maganar da nake so muyi , wadda Ina da tabbacin




cewa daga Kai har mahaifiyar ka za ku ji dadi... Sabo da haka na yanke shawara zan hada ka da...

Aisha Muhammad, naji dadin comment din ki sosai, na kuma gode Allah ya bar zumunci🥰 Hauwa'u Abubakar (Tiara) gsky comment din ki ya ban dariya, amma ba komai mukama😂


YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING...✍️


Domin shawarwari ko gudummuwa please...
👇🏻
08144066758

Taku har kullum
Yar mutan Argungu
Ke yi muku fatar alkhairi🥰❤️```


































```ASHE BA SO BA NE...📚

Incomplete..🖊️
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❤️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya👍🏻


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


❤️ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan
Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU👌

Free Book📚

Bismillahir Rahmanir Rahim

🍓🍓🍓🍓
🍓🍓
🍓
26
"Yar uwarka Zainab ..." A hankali Usman ya dago kansa ya zubawa Alh. Sanusi idanuwansa, yayin da kuma ya maida kallonsa bangaren Mama, wadda farin cikin ta ba ya boyuwa..." Hamdala tayi tana kara godiya ga Ubangiji da ya ku sa cika ma ta burinta, fatar ta a kullum shine, Allah ya danta mata ta gari. Toh kuwa ga shi ya amsa ma ta."
Dama ance "Dare daya Allah kanyi Bature" kuma wani hanin ga Allah baiwa ne". Yau ya rasa wata Yarinyar, ayau kuma Allah ya musanya mishi da wata." Dama ta dade tana yi mishi kwadayin Auren Zainab saboda Yarinya ce mai tarbiya, uwa uba natsuwar ta. Tabbas babu abun da za tace wa Alh. Sanusi sai dai tace Allah ya biya shi da gidan Aljanna. "Usman kayi shiru ko ba ka yi na'am da Auren ba?" Cewar Alh. Sanusi yana kallon Usman. "Baba ban da jaa akan abin da ku ka zartar akai na , zanyi na'am ga duk abun da ku ka umarce ni matukar ba sabon Allah ba ne, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi."
Da fa kafadarsa Alh. Sanusi yayi yana cewa "Allah yayi maka albarka Dana, hakika ka nuna min ba ka zubar da tarbiyar da muka yi ma ka ba, kuma insha Allah za kayi alfahari da wannan Auren." Ya yi musu sallama ya wuce...
Bayan fitar Alh. Sanusi Mama ta kalli Dan nata, ta re da nazarinsa, tabbas akwai damuwa a tare da shi, ta kuma San damuwar sa ba zata wuce akan Hauwa ba. "Komai yayi tsanani maganin sa Allah, Ina son ka dau hakan a matsayin jarabawar ka, ba komai mutum ya ke so ya ke samu ba, akwai lokacin da abun da muke so ba alkhairi ba ne agare mu, sai kuma ya kasance wanda bamu so shine alkhairi, shiyasa ako da yaushe mu dinga barwa Allah zabi shine daidai..."
"Insha Allah Mama zan manta da past in fuskanci future, nagode da goyon bayan da ku ke ba ni ako yaushe Allah ya kara lafiya da nisan kwana."
"Ameen Babana".
"Sai kuma abu na karshe Ina son ka rike yar uwarka Zainab amana, na tabbata kamar yadda ka ji zancen nan girshi haka ita ma za taji shi, kuma nasan Zainab mai biyayya ce ba zata taba bijirewa iyayenta ba, kasani Alh. Sanusi ya zartar da wannan hukuncinne sabo da Kai, bai ji dadin abun da akayi maka ba, shiyasa nake rokonka da karike masa diyarsa da kyau, ita kadai Allah ya va shi, tashi ka tafi Allah shiy maka albarka."
Haka bangare biyu ake ta shirye shirye kasancewar Alh. Sanusi ya sa Auren kurkusa yau saura sati daya biki( one week). Su Mama sunyi kokari sosai wajen hada lefe, akwati Takwas kuma kowace cike da kaya, har Alh. Sanusi na fadan kayan sunyi yawa. Haka dai akayi abu gwanin burgewa...

"Aka ce rana ba ta karya sai dai uwar diya ta ji kunya". A yau ne dubban jama'a su ka shaida daurin Auren Usman da Zainab akan dubu Dari. Alh. Sanusi har kwallah yayi saboda tunawa da Yayansa.
Bangare Ango kuwa yana tare da Nasir su na gaisawa da abokanan su, ba za ka gane yanayin da ya ke ciki ba. A haka dai taro ya watse sai dai muce Allah ya basu zaman lafiya...
Mama ce zaune a gefen gado yayin da Aunty Amina ke zaune a Bedside, Usman kuma na ku sa da mama, tana yi mishi nasiha yana hawaye( bai taba tunanin ta sa kaddarar za ta juye haka) mama hawayen ta share tare cewa ya tashi ya tafi su Nasiru na jiransa, jiki a sanyaye yayi hugging dinta, sannan ya koma bangaren Aunty Amina ita ma yayi hugging na ta "fatar alkhairi dan uwa Allah ya sanya alkhairi". Cewar Aunty Amina yana fitowa su ka wuce. Motocin ba su zame ko ina ba sai cikin G.R.A, Horn su ka mai gadi ya bude musu. Gidan ba laifi yana da girma. Kana shigowa get din gidan zaka Mike kadan zuwa kofar parlon, idan ka shiga ciki daga hannun dama kofa ce wadda za ta Kai ka kitchen,yayin da gefen hagu kuma corridor ne wanda zai yi leading din ka zuwa da kunan bacci (3 bedroom) sai wata karamar kofar wadda zata sada ka da karamin parlor. Nasir ne ya bude taro da addua su ka yi jawabin su tare da nasiha sosai, daga baya kuma aka koma fira a tsakanin abokanan Ango da na Amarya, daga karshe su kayi sallama kowa ya kama gabansa.
Zaman Auren su zamane na jindadi da kuma girmama juna. Sun hada kansu tamkar dama Auran SOYAYYA su ka yi. Duk wanda ya shigo gidansu ba zai ce Auren hadi ba ne, sabo da yadda suke tafiyar da lamuran su gwanin burgewa tare da SOYAYYA mai tsafta, komai Zainab ke so yana yi ma ta matukar bai fi karfin shi ba. Ita ma tana gudun bacin ransa, duk abun da ba ya so toh tana kokari wajen kauce ma wannan abun...

Zamfara state
Hauwa ce kwance a gadon Asibiti, ba ta ma san inda kanta ya ke ba. Sabo da fasa Auren ta da doctor Faruq ya yi.( Son ma so wani koshin wahala😃)

Tun lokacin da doctor Faruq ya samu iyayensa ya fada musu halin da ake ciki, da kuma cewa ya fasa Auren ta, saboda binciken da yayi ya gano cewa da sadakin wani akanta, amma ta ke soyayya da shi. Bakaramin murna Ammi tayi ba, saboda tun farko ba son Auren ta ke yi ba,tafi son ya Auri diyar kawarta. Abi kuwa tunani ya ke yi meyasa ba su zurfafa bincike ba, saboda yana da kayu idan za ayi Aure ayi bincike sosai ba na wasa ba. Amma bakomi wannan ma wani sabon darasi ne a gare su ko zuwa nan gaba. Da kuma adduar Allah ya shirya mana zuri'armu da ta kullumin musulmai baki daya. Ya kuma ka re muna ƴaƴan mu daga hali irin na Hauwa...

ALHAMDULILLAH

GODIYA TA MUSAMMAN GA DUK JAMA'AR DA SUKA KARANTA WANNAN LITTAFI MAI SUNA "ASHE BA SO BA NE" ALLAH YA SAKA MUKU DA ALKHAIRI YA KUMA BAKU ABIN DA KUKE NEMA NA ALKHAIRI.

KUSKUREN DA KE CIKI ALLAH YA YAFE MIN, ABUN DA NA FADA DAIDAI ALLAH

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment