Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankalin sa nakan dakin da aka shiga da abokinsa.!

"Fitowar likita ne Nasir ya zo da sauri... doctor ya jikinshi...? Da fatar ba abunda ya same shi? " Zo muje office" abin da doctor ya ce mishi kenan.
"Bayan mun shiga office likita ke sanar min cewa Usman ya kamu da hawan jini (hypertension). Wannan shine abun da nasani game da Usman mama..."

**** **** **** ****
Ajiyar zuciya mama tayi! San nan ta dafa kafadar Nasir tana cewa "Nasiru samun aboki nagari yana da wuya a wannan zamanin, Allah yayi maka albarka ya kuma sa zumunci ku ya daure har abada.!
"Amin mama, Allah ya bashi lafiya."
Amin ga takardar sallama nan likita ya ba ni.

Bayan sun koma gida Nasir yayi musu sallama ya wuce gida.

After 2 days
Alhamdulillah Usman ya ji sauki sosai Masha Allah! Sai dai fushin da mama keyi dashi...
Yau bayan sallar Asubahi direct dakin mama ya wuce,ya tura kofar dakin bakinshi dauke da sallama...
Mama na kan sallaya tana lazimi
" Mama ina kwana "?
Da Kai mama ta amsa mishi gaisuwar sa"
Kusan minti biyar babu Wanda ya ce komi.

Usman nason yin magana amma bega fuska ba,a hankali ya tako har zuwa wajen ta,ya daura kansa a kafafunta ...danshin da mama taji ne,ya sa ta mai da hankalin ta wajensa. Ya mugun bata tausayi sabo da rabon da taga kukan yaron ta tun yana karami...
Su biyu Allah ya ba ta,Amina sai Usman. Tun ya na primary school mahaifinsu ya rasu,haka ta ke kula da yaranta,ta sama musu ilmin addini da na zamani,yanzu haka Amina tayi Aure, shi kuma Usman ya gama N.C.E aiki yake nema,Amma har yanzu shiru " kamar an aika bawa garinsu," tunda kasar tamu ta zama wa kasani ne waya sanka!"

Haka be sashi jiran gawon shanu ba,". Yana saro tufafi yana sayarwa.

Rike hannun ta da yayi shiya dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi...
" Mama dan Allah ki yafe min wallahi fushin ki a gare ni masifa ce! Ta ya zan yi barci mai dadi bayan uwa na fushi da danta...

" Waya ce maka uwa na fushi da danta, tana dai son danta yabar biyewa zuciyarsa ne,sabo da Kar ta Kai shi ga halaka,ba ka tunanin halin da zan shiga idan wani abu ya same ka? Amma ni ba fushi na ke yi ba!
"Oya tashi muyi magana cewa mama,bayan ya tashi zaune ta fara da cewa "Usman Aure kake so ko? Sun kuyar da kansa kasa yayi,duk da akwai fahimtar juna tsakanin shi da mahaifiyarsa,amma ya ji kunyar wannan tambayar...

"Bakomi Hausawa sun ce " shiru ma magana ce " kwanciyar ka asibiti ma ya nuna min cewa Dana ya isa Aure cikin dariya mama ta gama zancen...

" Mama ban so dan Allah kibari... Fuskarsa Asanyaye Yafadi Hakane
" To shikenan tun da ba ka so a fada amma kazama jarumi,ba abu kadan mace zata yi maka ba,kazube mana ...

" Please mama naface banso yakare maganar kamar zaiyi kuka.

" To na bari Allah ya baka mace tagari wadda taffi Hauwa...

*** **** **** ****
Da fatar kuna jindadin yadda labarin ke tafiya?

Yawan comments yawan typing...๐Ÿ–Š๏ธ


** Share
**Comments

Domin shawarwari ko gyara please๐Ÿ‘‡๐Ÿป
08144066758``` ```


































``````ASHE BA SO BA NE...๐Ÿ“š

Incomplete..๐Ÿ–Š๏ธ
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba my sisi IMAN FATIMAโค๏ธso much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya๐Ÿ‘๐Ÿป


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


โค๏ธ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU๐Ÿ‘Œ

Free Book๐Ÿ“š

Bismillahir Rahmanir Rahim

๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“
๐Ÿ“๐Ÿ“
๐Ÿ“
08
" Haka rayuwa ke tafiya,kwanaki na wuce har ankai ga satuttuka,ahankali har mukai watanni,sannu sannu mun shiga shekara ,haka kwanakin mu ke tafiya ba tare da mun farga ba."
ZAMFARA STATE
gusau

Zaune suke acikin falo kowa ransa a bace yake! Abba ne ya kalli gefen da Hauwa take zaune rike da baby'n ta a hannu tana faman kuka. " Hauwa wannan shine tambayata ta karshe da zan yi miki, meya hadinki da mijinki har yayi Miki wannan dukan ya kuma hadaki da saki!?
" Abba wallahi ban yi mishi komi ba" shikenan tashi ki tafi, ammah idan na bincika ke ce ba ki da gaskiya sai ranki ya baci!? ๐Ÿงโ€โ™‚๏ธ

" Abba gaskiya bai kamata mubar wannan maganar ba, dole ne na dauki mataki akan abin da yayi ma kanwa ta! Yaya Ahmad ne ke wannan maganar cikin fushi!
"Ahmad tunda Abban ku yace abar maganar ba sai a barta ba, saki uku fa yayi mata, ka ga kuwa aikin banza ne tsayawa cece kuce, ko wayyi nagari kansa... Allah zai saka ma ta! Kuma ba za a rike diyar sa ba, tunda abun rashin mutunci ne a mayar masa da jaririyar sai ya shayar da ita. Cewar Ummi wadda ranta bace take maganar!!!

"Haba Umminsu ai "in rai ya baci hankali ake sawa a nemo shi" abar yarinyar a wurin mahaifiyar ta, har ta cika shekarun da addini ya ce, ina ga wannan shine adalci ga jaririyar. Abba ne ka wannan jawabin...

Haka dai aka tsayar da magana,yaya Ahmad ya wuce gidansa...

A daki kuwa Aisha ce zaune rike da baby Haneefa diyar Hauwa tana jijjiga ta.
Budar bakin Aisha sai cewa tayi...
Da fatar kuna jindadin yadda labarin ke tafiya?


Yawan comments yawan typing...โœ๏ธ

**Share
**Comments

Domin shawarwari ko gyara please...
08144066758``````

























`` ````ASHE BA SO BA NE...๐Ÿ“š

Incomplete..๐Ÿ–Š๏ธ
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMAโค๏ธso much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya๐Ÿ‘๐Ÿป


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


โค๏ธ True story
Written by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU๐Ÿ‘Œ

Free Book๐Ÿ“š

Bismillahir Rahmanir Rahim

๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“
๐Ÿ“๐Ÿ“
๐Ÿ“
9-10
"Hmm...Aunty Hauwa wallahi ban san daddy'n Haneefa azzalumi bane sai yau! Fisabilillahi bayan saki har da duka dan zalinci... wallahi sai Allah ya sa ka miki sai kace ba Auren soyayya ku ka yi ba!? Duk son da kike Masa awurin Sa,ASHE BA SO BA NE...

..................................
.............................................TUNA BAYA...

Farkon Auren su sun zuba soyayya babu kama hannun yaro...
Duk abin da Hauwa ke so jiki na rawa sama'ila ke yi mata shi.
Abun da ta lura shine,ba son gaske ya ke yi ma ta ba,duk wannan abubuwan ashe jikinta kawai ya ke so!

Amma lokaci ya kure mata,tun da aikin gama ya gama sai dai tayi zaman hakuri tunda ita ta kawo shi tace shi take so...tana tuna maganar Ummi da take cewa...
" Hauwa Kinga Aure za ki yi,Ina son ki bude kunnuwan ki da kyau ki saurare ni...
Zaman Aure sai hakuri,akwai soyayya, akwai fada akwai matsaloli amma idan ku ka San yadda zaku dinga tafiyar da lamuran ku sai ya zamana duk inda matsala ta kunno Kai za ku masu mafita acikin kankanin lokaci..."

Haka Hauwa ta ci gaba da hakuri da mijinta.
*******************
************
************
Akwana atashi a sarar mai rai..."
Hauwa na da ciki wata bakwai. Wani abun da ya daga ma Hauwa hankali shine... Neman matan da mijin ta ke yi,duk da abin akwai ciwo,haka zalika tana tsoron ya kwaso musu cututtukan zamani, kullum da kuka take kwana duk tabi ta lalace; ga lalurar ciki ga kuma matsalolin gidanta, abu ya game mata goma da ashirin!"

AFTER 2 MONTHS

Allah ya sauke Hauwa lafiya ta samu baby girl. Bayan sati daya akayi suna yarinya ta ci sunan maman Sama'ila wato Sakina, amma suna kiran ta Hanifa.

Yanzu Hanifa na da wata uku a duniya.
Tayi shirin bacci amma har yanzu Sama'ila be shigo gida ba. Ta kalli agogon da ke manne a bangon falon ta, 12: 43pm na dare ,duk baccin da take ji ta kuduri tsayawa har ya dawo a yi ta takare, tun farkon aurensu, ba ta sake jin dadin zaman aure ba!
Motsin da taji ne ya katse mata maganar zucin da take yi...
Sama'ila ne ya wuce daki kai tsaye ba tare da ya ko kalli gefen da Hauwa take ba.
Da sallama ta shigo dakin,karar ruwan da taji,shi ya bata tabbacin wanka ya shiga.

Haka ta danne bacin ranta, ta zauna bakin gado tana jiransa ya fito.
Bai dauki lokaci ba, ya fito...

Ba ta ko ishe shi kallo ba...

Ta kara tausar zuciyarta, gudun kar a samu matsala.
Ahankali ta isa wurinshi yana zaune a gaban dressing mirror yana shafa lotion dinsa.

Daddyn Haneefa sannu da zuwa tana maganar ne tare da kai hannunta zata karbi lotion din ta shafa masa...
Bige hannun yayi ya cigaba da shafa man sa.
A zuciyarsa tafara magana cikin bacin rai...

"Wai daddyn Haneefa mai na yi maka? Tun da na shigo gidanka ban da kwanciyar hankali, walakancin yau daban na gobe daban, na yi hakuri na shanye duk abun da kayi min Ina tayi maka uzuri, baka cin abinci na baka zama dani ka ji damuwa ta,baka kula da yaya na tashi me nake so...
San nan ba ka sauke hakkin da Allah ya daura maka Kai ne idan ka fita tun safe sai dare kake dawowa;
Yanzu kuma ga zuria ta shiga tsakanin mu amma ba ka daina abubuwan da kake yi ba!?
Yau Ina son ka fadamin menayi maka Wanda na cancanci haka daga gareka?
Sama'ila kasan hakkin da ke kanka kuwa? Kasan bala'in da kake ciki kuwa na tauye iyali!?

"To wallahi ba zan dau wannan tozarcin ba! Na tsaya ka re kaina da mutunci ka,amma Kai kana waje kana zubar mana da mutunci! Yau a ganka da waccan gobe ma haka... Wallahi daddy'n Haneefa ka ji tsoron Allah,duk abin da ka yi wallahi zaka girbe shi...
Ta gama maganar cikin kuka da bacin rai!

"Hauwa har wuyan ki ya yi kwarin da zaki saka ni a gaba kina gaya mini magana son ranki?
To wallahi kibar dakin nan ko ranki ya yi mugun baci!!!

"Bacin rai na nawa kuma ko kana son kace min duk wadan nan abubuwan ba bacin rai ba ne?

Saukar mari ne ya hana ta karashe zancen!

"Ke har ke isa kizo gabana kina fadamin magana son ranki,anki a kula,ki zo kiyi duk abin da za ki yi!
Ai ni ban San cewa Aure takurane ba wallahi,dan haka nagaji da sa idon da kike yi min, ki tattara kayanki na sake ki saki uku!!!

"Innalillahi wainna ilaihir raji'un...!!!

"Sama'ila kasan kasan me kake cewa? Anya kana cikin hankalin ka kuwa ko dai ka fara shaye shaye ban sa ni ba!? Dan Allah in wasa kake yi ka bari banson irin wannan wasar...!

"Kin taba ganin inda akayi wasa da saki? Hausa fa nayi miki ba wani yare ba.
Kuma zagina da Kika yi wallahi bazaki ci bulus ba sai kin gane ba ki da wayo!

BACK TO
STORY

.........................................................
A jiyar zuciya ta sauke yayin da take share hawayen ta.
Tasan cewa ita ce ta damu da Sama'ila amma shi yana can yana sha'anin gabansa.

Ummi ce ta shigo dakin jikinta a sanyaye kasan cewar halin da yarta take ciki.

" Hauwa kulu mai dadin suna"

"Ummi barka da shigowa"

"Yau banji rigimar kishiya ta ba?"
Cewar Ummi

"Tana wurin Aisha,tunda naji shiru nasan bacci take yi"

"Hauwa kinsan kowa da yadda rayuwa ke zuwa mishi ko?"

"Eh ummi"

"Good, Ina son ki cire damuwa a cikin zuciyarki ... wallahi rayuwa duk dadinta da rashin dadin ta dukkan halin da kike ciki ki godewa Allah domin akwai wanda ya fi ki kuncin rayuwa,ke dai ki dinga addua cikin hukuncin Allah zaki kasance cikin mutanen da ubangiji yake so ki kasance mai hakuri a komai insha Allahu komai zai wuce."

"Nagode ummi Kuma insha Allah zan yi yadda kika ce."

"Haka nake son ji Allah ya Miki albarka"

"Ameen"

BAYAN WATA BIYAR
"Yau dawuri ta gama aikace aikacen ta, ita kadaice a gida ...
Ummi ta fita unguwa , sister's dinta Kuma su na makaranta

Tayi wa baby Haneefa wanka ,ita ma tayi nata.
Zaune take tana kallon TV amma hakikanin gaskiya hankalin ta baya wurin...
Tunanin rayuwa take yi,wata kila daba Sama'ila ta Aura ba da hakan bai kasance ba...
Usman ne ya fado mata arai,da yadda ya ke turo mata love messages duk da a social media su ka hadu,amma ya kasance mutum mai kula da damuwar ta...
Usman ya nuna mata soyayya mai tsayawa arai,ta tuna lokacin da ta Kira shi a waya irin tashin hankalin da ya shiga...
Ko wane hali ya shiga alokacin, Allah kadai ya sa ni, ita dai tayi da tasani na wasa da feeling dinsa ... Allah ka yafe min
Abin da tace kenan acikin zuciyarta."

Wayar ta jawo ,ta na chating, kasance cewar hakan na debe mata kewa sosai.

Facebook ta shiga tana scrolling sabon post na mutane,har tayi kasa sai kuma tayi sama da sauri domin tantance abun da idanuwan ta su ka gani...

DUK YADDA IYAYEN KA SUKA KAI DA TALAUCI DA KUMA CUTA BAKA ISA KA GUJE MUSU BA, KO KUMA KA WULAKANTA SU DOMIN BABU KAMAR IYAYE,YA ALLAH KABIYA MA IYAYENA BUKATUN SU NA DUNIYA DA KUMA NA LAHIRA,DA SU DA DUKKAN KULLUMIN MUSULMAI, WADAN DA KUMA NASU SUKA RIGAMU ZUWA GIDAN GSKY ALLAH YAJIKAN SU YA SA SUN HUTA. IN TAMU TAZO KA SA MUCIKA DA IMANI๐Ÿ‘Œ
Dan Allah kuyi hakuri akan rashin jina da baku yiba kwana2
Yawan comments yawan typing...โœ๏ธ
Domin shawarwari ko gudun muwa```
08144066758```

``````ASHE BA SO BA NE...๐Ÿ“š

Incomplete..๐Ÿ–Š๏ธ
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMAโค๏ธso much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya๐Ÿ‘๐Ÿป


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


โค๏ธ True story
Written by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU๐Ÿ‘Œ

Free Book๐Ÿ“š

Bismillahir Rahmanir Rahim

๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“
๐Ÿ“๐Ÿ“
๐Ÿ“
11
Picts din Usman ta gani tare da abokansa, da alama hotunan daurin aure ne na abokinsu. Sai dayan pict din Usman ne shi kadai
Yana sanye da ash shaddar ( getzner ) dinkin babbar riga wanda ya sha aikin hannu. Wani tsadadden agogo baki kirar Rolex ke a tsintsiyar hannunsa na hagu. Kafafunsa na sanye da black loafers na kamfanin Gucci. A saman kansa kuma, akwai hula mai kala ash, white da black. All in all, a gaskiya Usman yayi kyau matuka
Take Hauwa taji zuciyarta tana bugawa da karfi. Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kara kurawa hoton ido.
Usman mutum ne mai matsakaicin tsayi wanda bashi da kiba sosai. Shi kalar wankan tarwada ne wato chocolate. Yana da manyan idanu. Hancinsa dogo ne, yayin da bakinsa matsakaici ce. Sajen fuskarsa yayi yanayi da na shahararren dan film din Indian Zain Imam
Ajiyar zuciya Hauwa ta sake saukewa, ta San Usman yanzu yayi mata nisa. Amma kuma wata zuciyar na rada mata cewa ta kira shi. Sannan dayan bangaren na cewa kada ta kira shi, duba da abubuwan da suka faru a baya.
Kasancewar Hauwa yarinya ce mai son Kai, tafi amincewa da maganar zuciyarta ta farko. Sai ta kira. Tana fara ringing...

ARGUNGU
Usman yana wurin aikinsa na kamfani, kasancewar yanzu shi production manager ne na kamfanin sarrafa shinkafa ( su oo na son suji wane kamfani ne, LOL ๐Ÿ˜œ)
Wayarsa da ke aje kan desk din ofishinsa ce ta fara ringing, ya zura hannu ya dauka, lambar da ta kira ba suna. Kallo daya yayi wa lambar zuciyarshi ta buga, domin ko daga bacci ya falka ya san mai wannan lambar.
Wata zuciyar na cewa ya dauka, wata kuma na cewa kar ya dauka saboda matar aure ce fah. Amman be san meyasa zuciyarshi ta rinjaye shi da dauka ba. Sautin muryarta da yaji, take wani sanyi ya ratsa zuciyarsa. Shi kanshi wannan al'amari ya bashi mamaki, saboda a tunanin shi ya dade da binne soyayyarta daga zuciyarsa.
"Hello?" Yaji tace domin jawo hankalinsa
Ita kanta Hauwa ta fara waswasin kodai ba Usman ya dauki wayar ba? Domin dakyar zai dauka bayan abunda ya faru
Gyaran murya taji
daga dayan bangaren layin, sannan muryar Usman dauke da sallama...


***********
My dear readers, ban manta da ku ba. Ina mai baku hakuri akan dogon lokacin da na dauka ban muku typing ba, saboda wasu abubuwan da suka gifta, amma Alhamdulillah, yanzu komai ya daidaita. Zaku dinga jin na akai akai

YAWAN COMMENT, YAWAN... โœ๏ธ

Karin godiya ga sis Iman โค๏ธ tare da Saddam Kabir Magaji ๐Ÿ˜„๐Ÿ‘Œ

Domin shawarwari ko gudummawa
๐Ÿ‘‡๐Ÿป
08144066758``` ```
















``````ASHE BA SO BA NE...๐Ÿ“š

Incomplete..๐Ÿ–Š๏ธ
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMAโค๏ธso much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya๐Ÿ‘๐Ÿป


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


โค๏ธ True story
Written by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU๐Ÿ‘Œ

Free Book๐Ÿ“š

Bismillahir Rahmanir Rahim

๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“๐Ÿ“
๐Ÿ“๐Ÿ“
๐Ÿ“
12

"Sai ta amsa Sallamar sa tare da cewa, "dan Allah ina magana da Usman ne?"

"Eh kina magana da Usman ne, amma ban gane mai magana ba. Wacece dan Allah?"
Ya fada in a serious tone.

Hauwa: kana magana da Hauwa

Usman: Hauwa... Hauwa..ban gane wace Hauwa ba?

Hauwa: Wadda kuka hadu a cikin group din AMINAN JUNA?

Ta fadi hakan ne cikin mamaki, sabo da a tunaninta Usman ya manta da ita. Hakan ya sa jikinta yayi sanyi.
Usman: hello? Hello?
Muryan Usman ce ta dawo da ita daga tunanin ta.

Hauwa: Usman Yana Kara maimaitawa. Hauwa ce fah, har ka manta Dani ?

Usman: kinsan yanayin rayuwa,abubuwa sun yi wa mutum Ne yawa,wani lokacin ba komai mutum yake iya tunawa ba...

Cikin ransa wani dadi yake ji Hauwa ta kira...amma wata zuciyar na fada mishi Hauwa matar Aure ce fah,me zai sa ta kira shi?

Wannan ne ya rage farin cikin da ke zuciyar shi...

Hauwa: haka ne, gaskiya. Kwanaki da yawa,amma ban yi tsammanin zaka iya mance Hauwa daga Zamfara state ba...

"Fadar haka ya sa Usman ya gane cewa magana Hauwa ta fada mishi, cikin ruwan sanyi. Sai jikinshi yayi sanyi...

Usman: Allah sarki,Hauwa Ashe kece,ya gida ? Ya mai gidan naki? Da fatar kowa na lafiya...ban gane ki bane,ki yi hakuri sabo da nayi loosing contacts kuma kinsan ana cewa "abun da ba naka ba,kayi nesa dashi."

Hauwa: tayi shiru...San nan tace ai mun rabu da shi.

Usman: yana zaune bai San lokacin da ya Mike ba! innalillahi wainna ilaihir raji'un,meya faru? Ya rasu ne?
Hauwa: himm, Usman labari ne mai tsawo...
Dama na Kira ne in baka hakuri akan abubuwan da su ka faru a baya...
Dan Allah ka yafe min,ban San ko alhakinka ne ke bii na ba...

Usman: haba Hauwa, wannan wace irin magana ce ?
Kamar baki yadda da kaddara ba? Auren dole aka yi Miki,ba laifinki bane,dan haka ni ban rike ki da komai ba...
Hauwa: nagode sosai Usman, zuciyar ka mai kyau ce
Usman: ba komi Hauwa,sai anjima.




Duk da Usman bai so aje wa ba,yayi hakan ne sabo da tausayin ta.

*****************************
*
*
*
Bayan ya aje waya,sai kuma ya ce bari ya Kira Nasir...

Nasir: wallahi yanzu nake cewa bari in Kira ka,sabo da kwana biyu bamu yi waya ba.

Usman: Allah sarki,Nima yanzu wani albishir na Kira in fada maka...

Nasir: tasamu kenan,na dade ban jika cikin farin ciki ba... Yana maganar tare da dariya

Usman: himm...kai dai bari, ai dole kajini cikin farinciki, yanzu muka gama magana da Hauwa...


Nasir: wace Hauwa? Ko kayi sabuwar budurwa ne?

Usman: dadina dakai akwai shirme wani lokacin,wace budurwa kuma... Hauwa dai wadda ka sanni da ita Yar Zamfara.

Nasir: what! Usman kana da hankali kuwa? Matar aure ce fah,kasan zunubin yin hakan kuwa?!

Usman: easy mana,wai me ka dauke ni ne dan Allah?! Jahili ko mahaukaci? Kasanni kasan halina,be kamata kayi min wannan zaton ba!

Nasir: I'm sorry abokina ,Kai dinne naji kana wani batu na daban, please explain to me

Usman: haba ko kaifah.Dazu Hauwa ta kirani take bani hakuri akan abubuwan da suka Kai Ina ruwanka da wani Auren ta ya mutu?!
Kar dai ace min...

Ina son inga ruwan comments,hakan zai sa ni yi muku typing da sauri๐Ÿ‘Œ

Yawan comments yawan typing...โœ๏ธ
Domin gyara ko shawarwari please
๐Ÿ‘‡๐Ÿป
08144066758

Taku har kullum
Yar mutan Argungu`````` ๐Ÿฅฐ












```ASHE BA SO BA NE...๐Ÿ“š

Incomplete..๐Ÿ–Š๏ธ
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMAโค๏ธso much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya๐Ÿ‘๐Ÿป


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


โค๏ธ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU๐Ÿ‘Œ

Free Book๐Ÿ“š

Bismillahir Rahmanir Rahim



Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment