Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“
πŸ“
13
Usman: Haba Nasir, mutuwar Aure fa ba dadi! Wallahi tabani tausayi!

Nasir: kar kace min har yanzu kana son waccan yarinyar?

Usman: to miye aciki idan nace ina sonta,ai dama tun farko ita ce zabina...

Nasir: kar ka soma wannan gangancin,kasan ko mama ba zata yadda ba...

Usman: Nasani,amma kasan mama na girmama maganar ka,wallahi idan kayi mata bayani zata yadda...

Usman: ka ga... Nifa baruwa na acikin wannan maganar, kuma ya za ka yi da yar' uwarka ZAINAB?

Wadda naji mama nayi maka maganar ta?

Usman: Bai da matsala, tun da shawara ce kawai mama keyi, Amma zancen bai Kai gidansu ZAINAB ba...

Nasir: to, shikenan Allah ya zabi mafi alkhairi...

Usman: Amin Dan uwa sai mun sake waya...




🍏🍏🍏🍏🍏
🍏
🍏🍎🍎🍎🍎
🍏
🍏
🍏

Kwanakin nan duk Wanda ya San Usman ya San yana cikin farinciki sosai, kasancewar firar da suke yi da sahibar shi kullum...


Mama ta ga Chanji a tattare da yaron ta kuma Autan ta. Hakan yasa ta tambaye sa,meke faru?

Amma ya ce bakomi.

Ta barshi akan bakomi din,amma ita tasan danta ya sauya...

Shiyasa ta zuba mishi ido, a tafi a hakan,tana zaune zai neme ta


**Zamfara state**

Hauwa ce cikin kitchen tana girki tana smiling. Tana sauri ta gama taje tayi waya da SAHIBIN ta

Mama ce tsaye wurin kofar kitchen tun dazu tana kallon yar ta, da ke ta famar doka murmushi ita kadai



"Himm... Suwance kodai kodai... Wannan murmushi haka, ko ansamamin Suriki ne,ban sani ba...? Tayi maganar cikin zolaya"
"Kai mama,bafa haka bane..."

"To yayane inba haka bane? Tun fa dazu ina tsaye ina kallon ki,kina murmushi ke kadai,koma dai menene Allah ya zabi mafi alkhairi"
Cikin jin kunya Hauwa tabar kitchen da sauri.

Dama ta gama girki


"Aunty Hauwa wannan wanka sai ina? Cewar Aisha


"Indon ummi mutum baya wanka sai zaya fita? Ta karashe maganar tana hararar ta"

"Hahahhh... wallahi ba haka bane, Aunty ba ki ga yadda kika yi kyau baπŸ‘Œ kamar a gudu dake...

Yauwa Aunty ni kuwa dan Allah dawa kike waya da Dare, kullum ina jinki kina waya?
Kodai Brother in-law?

"Himm...Aisha kenan, sai yau kika sa ni...ai jirgi ya barki Tasha...cikin dariya take zancen"

"Tabbas jirgi ya barni Tashaa,sisto please a dan gutsuramin mana... Tana dariya

"Mun dawo soyayya da Usman"

"This is serious? Aunty Usman fa kika ce?! Da gaske?"

"Na taba yi Miki irin wannan wasa?!

"Aunty abun ne kamar Almara,amma ya haka ta faru,Ina kika samu number sa?"

"Facebook"
Kuma na roke shi, ya fiya


"Amma yanzu kina son shi?"

"Aisha wai wannan wace irin banzar magana ce!! Ina son shi ko ban son shi ba ruwanki!!!"



"Allah ya baki hakuri,daga magana?"

"Amma Aunty dan Allah wannan karon karki biye wa son kai, idan har baki son shi ki sallame shi kawai, ato,dan wallahi wannan karon ba ruwana"

"A zuciye Hauwa ta taso,don ta make Aisha...
Da gudu Aisha tabar dakin,tasan ko giyar wake ta sha,ba zata iya da Hauwa ba, NO NONSENSE ce..."

"Tabbas ita kanta tasan ajinta ya wuce ace ta na soyayya da irin Usman,duk da ya hudu iya haduwa,kuma burin kowa ce mace a ce ta mallaki irin sa.
Amma matsalar ita ce Albashinsa, Ba zai isheta lalurar ta ba.

Amma aka ce" da babu gwara ba dadi"

NASIHAπŸ‘Œ
Kusani akwai irin Hauwa a duniya,wadan da kansu kawai suka sa ni,ba ruwansu da hadarin da Dan uwansu zai shiga. Ya kamata ace yanzu tayi karutun ta natsu. Ya kuma kamata ace yanzu ta gane kudi ba komai bane idan babu zaman lafiya,kamar yadda rayuwar ta takasance a gidan Sama'ila.

Mutane na manta cewa ba kudi kawai ne jindadin Rayuwa ba.
Mutane nawa keda kudi amma su na kwance a Asibiti?
Mutane nawa keda kudi amma Allah bai basu ya'ya ba? Tun da suna da kudi meyasa ba zau sayi ya'ya ba?
Mutane nawa keda kudi amma ba zaman lafiya?
Mutane nawa keda kudi,amma jindadin Rayuwa ya katse musu?

Kusani wallahi kudi basu ne jindadin Rayuwa ba,kamar yadda Bahaushe ke cewa "ZAMAN LAFIYA YA FI ZAMA DAN SARKI tabbas haka zancen yakeπŸ‘Œ

Wallahi akwai Talakan da idan ubangiji yayi mishi Arziki Allah kadai yasan tsiyar da zai tsula a doron kasa
Kunga Ashe wani hanin ga Allah baiwa ne

Allah yasa mu gane
AMIN

NO COMMENTS,NO UPDATE ON TIME

COMMENTS DINKU SHIKE BANI KWARIN GUIWA WAJEN YI MUKU TYPING...✍️

Domin shawarwari ko gyara please call this number
πŸ‘‡πŸ»

08144066758

Yar mutan Argungu
Ke muku fatar alkhairiπŸ₯°```





```ASHE BA SO BA NE...πŸ“š

Incomplete..πŸ–ŠοΈ
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❀️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi yaπŸ‘πŸ»


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


❀️ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGUπŸ‘Œ

Free BookπŸ“š

Bismillahir Rahmanir Rahim

πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“
πŸ“
14

Amma aka ce" da babu gwara ba dadi"
Tana da tabbacin Ko ba komai Usman zai rike mata yarta, sabo da yanzu duniya ta lalace,ba kowane ke rike dan wani ba.
Ringing din wayar ta ne ya katse mata tunanin ta...

Usman: amincin Allah ya tabbata ga sahiba ta kuma uwar ya'yana insha Allah...

Hauwa: amin tare da sahibina mai kyakykyawar zuciya...

Usman: ya kike ya gida? Da fatar kowa yana cikin koshin lafiya?

Hauwa:kowa yana lafiya. Ya mama da Aunty Amina?

Usman: lafiya lau suke,suna gaishe ki..
Hauwa: Ina amsawa.

Usman: Ina son muyi magana mai mahimmanci kamar yadda kika sa ni duk matar da aka ce Auren ta ya mutu,to mutane za su fara zargin mijin ne ko kuma suce laifin matar ne.
Amma ni agani na kamar laifin na kine...duba da cewa Auren dole aka yi miki, Ina son ki bani labarin abun da ya faru Wanda yasa kika fito daga gidan mijinki?


Wani irin takaici ne ya kama Hauwa,kenan kowa laifinta yake gani,sabo da Auren ta Ya mutu...!

Usman: Amma idan kina ganin na takura Miki,kibar shi kawai


Hauwa: bakomi a shirye nake da in fada maka komi...
Ahankali Hauwa ke yi mishi bayani dallah dallah ba tare da boye mishi komi ba...

Usman: gaskiya kam ba laifinki bane, Allah ya zaba mana abin da yafi zama alkhairi...

Hauwa: Amin my dear

Usman: kice na zama Baba,shine ba ki fadamin ba,to Allah ya raya mana baby'nmu...

Amin...

After two days

Hauwa ke yima Usman korafi akan anya ya damu da ita kuwa? Sabo da ya kamata ace sun ga junansu, kasancewar ba au taba ganin junansu ba...

Yau alhamis
Tun da safe Usman ya Kira Hauwa ya ce zai shigo Zamfara...
Murna awurin Hauwa ba a magana. Haka taje ta samu Ummi tace zata yi bako, amma gidan Aunty Maryam zata aje shi. Ummi tace ba komai Allah ya kawo shi lafiya. Ummi ta kira Abba ta fada mishi, yayi murna sosai, ya kuma yi fatar alkhairi, saboda shima baya son zawarcin nan.
Yaya Ahmad ma ya san da zuwan shi, yaje ya siyo duk abubuwan da ake bukata na tarbon future brother in-law

Kasancewar ya taso da wuri shiyasa ya isa Zamfara 2 o'clock. Ya kira Hauwa ya tambayeta wace unguwa zai zo? Hauwa tace "ka ce a kawo ka titin lalan" tare da sauran kwatancen gidan. Duk a tunaninta da motar haya ya zo, wato da babur za a kawo shi. Amma sai taga sabanin haka. Usman ne ya fito daga wata sleek black Mercedes Benz. Ba Hauwa ba, hatta da Yaya Ahmad saida Usman ya tafi da imaninsa. Yayi ma Hauwa flashing wani killer smile, tare da mika ma Yaya Ahmad Hannu, suka gaisa.
Hauwa baki har amadun kunne, saboda bata taba tunanin Usman ya kai yadda take ganinshi ba.
Haka Usman ke ya murna yau ga shi kusa da sahibarsa. Duk yadda yake ganin kyan Hauwa, ashe ma tafi kyau a fili. Bayan sun shiga gida, Usman ya gabatar da sallar da ake bin shi, aka kuma gabatar mishi da abinci kala-kala, tare da abun sha. Irirn su; biryani rice, tuwon shinkafa da miyar egusi soup, sannan peppered chicken. Bangaren drinks kuma tayi mishi mango lassi da farin sobo mai abarba
Gefe daya kuma ka snacks irin su shawarma da sponge cake wanda aka yi decorating, yayi kyau sosai. Haka kowa ya fita daga falon saboda ya samu ya ci abinci. A hankali Hauwa take serving dinsa. Yana kallonta gwanin burgewa, kamar su kasance haka har abada. Taji a jikinta kamar ana kallonta, dagowar da zata yi...

No comment,no update on time


Yawan comments yawan typing...✍️


Godiya ta musamman ga lil...iman ❀️🀍

Domin shawarwari ko gudummawa please
πŸ‘‡πŸ»

08144066758

Yar mutan Argungu ke muku fatar alkhairiπŸ₯°```
























```ASHE BA SO BA NE...πŸ“š```

```Incomplete..πŸ–ŠοΈ
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne```

```Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❀️so much```

```Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi yaπŸ‘πŸ»` `````


```Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!``````


```❀️ True story
Written by
Fatima Zara Alhassan```


```Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGUπŸ‘Œ```

```Free BookπŸ“š

Bismillahir Rahmanir Rahim```
```
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“
πŸ“```
Fiction 15
``` ```Alhamdulillah! Allah abin godiya.
"Kana naka Allah na nashi"
Komai sai Allah ya nufa. Ina rokon Allah ya ba ni ikon, gama wannan littafi lafiya...

```Dagowar da za tayi kuwa su kayi ido hudu...
Almost 10 seconds su na kallon juna, yayin da Hauwa ta sauke kanta kasa sabo da wani irin kwarjinin sa...
Ahankali ta mike zata wuce...ya tsaida ita chak ta tsaya daga tafiyar da take yi...
Wani killer smiling yake yi. A bangaren Hauwa gaban ta ke dukan uku uku(LOLπŸ˜ƒ)```
"Haka za abar bako shi kadai"?
Ta tsinkayi maganar sa ```...
A jiyar zuciya ta yi!
In ka gama zan dawo
Cewar Hauwa

"Zan fi jindadin abincin idan kina nan, yana kallon ta tare da kashe ma ta ido daya...
A hankali ta dawo ta zauna ta na murmushi...

Ya na cin abinci amma idonsa na kanta```

Ina ma ace su zauna haka har abada, da ya fi kowa ```farin ciki( ni kuma na ce anya... Usman ba ka zurma ba kuwaπŸ˜‚lol...)


After ya gama cin abinci,ta gabatar da yan uwan,a ka sake gaisawa...

Ana haka kuma sai ga cousin dinta Lubna tashigo, ita ma suka gaisa

Su ka ci gaba da fira sosai, kamar dama can sun San Usman...```
```
Kiran sallah ne yasa suka fita zuwa masallaci shi da yaya Ahmad.

```Tsarabar``` da Usman ya kawo ne suke budewa

Leda daya kayan su turaruka *ne designer's
Dayan ```kuma``` su chocolate dankare da ledar...

Kowa na taya Hauwa murna

Haka dai su ka garzaya gidan su Hauwa
Sabo da Usman zai gaisa da su ABBA```
_
Da sallama suka shiga cikin Falon,yayin da Abba ya taso yana Cewa "maraba da Dana...tare da ba shi hannu
Usma duk kunya ta kamashi, sabo da be taba zuwa gidan surukai ba* .

Abba ya zaunar dashi agefen damansa yana tambayar shi, ya hanya da kuma mutanan gida?
"Lafiya ```lau suke Abba, nasame ku lafiya, yana maganar kansa duke.

U ```mmi ce ta kawo mishi ruwa,tare da kara tambayarsa, hanya?```
"Abba ya fara ```dacewa``` "
"To Alhamdulillah naji dadi da ku ka daidaita kanku, duk da ita Hauwa bata yi muna bayani sosai ba,
Amma yanzu tunda ga ka akwai wasu tambayoyi da zan yi ma ka ,Ina fatar za ka bani amsoshin su,kasan sha'anin Aure ```sai``` da bincike``` .

" ```Hakane Abba``` "
Haka Abba ya sa Usman gaba yana yi mishi tambayoyi,daga karshe tambayar da yayi ma Usman ne ya sa kayan cikinsa suka fara yamutsewa`````` ...

INA MAI KARA BAKU HAKURI AKAN RASHIN JINA DA BAKUYI BA KWANA2

KUMA INSHA ALLAH WANNAN SHINE LAST UPDATE DA ZAN TURO MUKU, SABODA GSKY BA KWAYIN COMMENTS!!
SABODA HAKA ZAN RUFE WANNAN GROUP DIN.

ZAN DINGA TURAWA GROUP DIN DA SUKE BUKATA```

```
YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING...✍️

Domin shawarwari ko gudummawa
πŸ‘‡πŸ»
08144066758

Yar mutan Argungu
Ke muku fatar alkhairi```































```ASHE BA SO BA NE...πŸ“š
Incomplete..πŸ–ŠοΈ
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❀️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi yaπŸ‘πŸ»


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


❀️ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGUπŸ‘Œ

Free BookπŸ“š

Bismillahir Rahmanir Rahim

πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“
πŸ“
16

"Ina ku ka hadu da Hauwa, sabo da a bayanan ka, kace daga ARGUNGU kake ko"?
Garin tsoho mai daka ma yara kashi( KANTA LOLπŸ˜ƒ)
"To, Ina jinka" cewar Abba ya na murmushi

"Am...emm...A school of nursing muka hadu,a lokacin da nakai ma Abokina ziraya".
Ya fada kansa a sunkuye.

Azuciyarsa kuma yana mamakin yadda ya hada wannan zance . Zufa kawai ke karyo mishi. Bai gama maganar zuci ba,Abba ya kara jeho mishi wata tambayar, cewar "kasan Hauwa Bazaurace "?
Usman ya ce "Eh Abba,na sa ni".
Abba ya sake tambaya, "ka San kuma tana da diya?".
Usman ya kara amsawa da "Eh,duka na sa ni ,Abba".

Abba yayi murmushi sannan ya ce "Masha Allah. Miye ra'ayinka game da Hauwa?
Shin ka shirya Auren ta? Kuma gida an yarda ? "

Usman ya amsa da "Abba Auren ta zan yi" yana yi yana sosa Kai don kunya, fuskarsa na kallon kasa, sannan ya sake cewa "gida an yarda" duk da bai ji dadin yadda ya yi wa Abba karya ba,Amma bai da zabi na fadar haka.

"Toh Alhamdulillah, komai yayi kyau. Sannan Ina so idan ka tafi gida,ka turo magabatanka, ni kuma zan sanar da madaurin Auren ta,sai ku iske su". Cewar Abba.

Wani dadi ya kume / kama Usman,ya kasa rike murmushin sa,har yanzu fuskarsa a done kasa . Yace ,"insha Allah Abba, nagode. Allah ya kara lafiya da girma".

"Ameen Ameen,ai ba komai ka zama Dan gida yanzu, cewar Abba.
Haka dai yayi sallama da kowa,ya kama hanyar ARGUNGU,yana mai addua Allah ya sa Mama ta yarda,da wannan Auren....


Himm..shin kuna ganin za ayi wannan Auren?
Ko kuma akwai wata matsala,wadda zata sa a fasa Auren?
Toh,in ma akwai ta,daga wane bangare za ta fito?
Usman ko Hauwa...?



YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING...✍️


Domin shawarwari ko gudummawaπŸ‘‡πŸ»
08144066758

Yar mutan Argungu
Ke yi muku fatar alkhariπŸ₯°```















```ASHE BA SO BA NE...πŸ“š

Incomplete..πŸ–ŠοΈ
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❀️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi yaπŸ‘πŸ»


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


❀️ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGUπŸ‘Œ

Free BookπŸ“š

Bismillahir Rahmanir Rahim

πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“
πŸ“
17
Bayan Usman ya shiga Argungu,the following day ya hadu da Nasir. Ya fada ma Nasir zuwan shi Zamfara da duk abubuwan da suka faru.

Nasir kawai kura mishi ido yayi,yana mamakin wannan soyayyar da Usman ya ke yi ma Hauwa. Tun da ya ke a duniya,ko a cikin tatsuniya bai taba jin labarin SOYAYYA irin ta Usman ba...

Juyowar da Usman zai yi,sai ya ga Nasir ya zura mishi idanuwa,kallon shi kawai,yake yi,ba bu ko kyaftawa.

"Nasir lafiya ka ke kallo na haka,kamar ka ga wata halitta? Ni fa shawara na zo nemq wurin ka." Cewar Usman.
Ajiyar zuciya Nasir ya yi ya ce " Ni dai ba shawara ka zo nema wuri na ba, Usman. Tun da ba ka nemi shawara ta ba a zuwanka Zamfara,to meyasa za ka nema yanzu?"
Haba Nasir ya za ka yi min haka,Kai kasan zuwan nan ban zauna nayi planning din shi ba ,abu ne kawai ya ta so. San nan nasan ko kowa bai fahimce ni ba ,Kai za ka fahimce ni, kasan cewar ka Aminina,kuma dan uwana ,wallahi Nasir idan ba ka fahimce ni ba,to babu Wanda zai iya fahimtata. Usman ya na maganar cikin kunci!

Ganin yanayin da Usman ya ke ciki ya ba wa Nasir tausayi,kasan cewar damuwar da Usman ya ke ciki. Shi kanshi Nasir ,abun da farko haushi yake ba shi,ganin yadda friend din shi mai son was da dariya amma lokaci kadan SOYAYYA duk ta birkita shi,kamar ba shi ba.

Amma daga baya yayi understanding abokinsa sai ya dawo jin tausayin shi.
Shirun da Nasir ya yi yana tunani,shi ya sare ma Usman kwarin guiwa.
Ajiyar zuciya yayi, har ya tashi zai tafi,a sanyaye...
Motsin da Nasir ya ji shi ya ankarar da shi cewar Usman wuce wa zai yi...
Sai ya yi saurin rike...

YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING...✍️
Godiya ta musamman ga FATIMA IMAN IBRAHIM🀍


Kuna ganin har yanzu za a iya samun Aboki irin Nasir ko Usman?

Domin shawarwari ko gudummuwa please
πŸ‘‡πŸ»
08144066758

Ta ku har kullum

Yar mutan ArgunguπŸ₯°```




















```ASHE BA SO BA NE...πŸ“š

Incomplete..πŸ–ŠοΈ
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne
Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❀️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi yaπŸ‘πŸ»
Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


❀️ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan

Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGUπŸ‘Œ

Free BookπŸ“š

Bismillahir Rahmanir Rahim

πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“
πŸ“
18
Ya yi saurin rike hannun Usman,ya sa ke mayar da shi wurin zaman sa. "Haba dan uwa, mai ya yi za fi shi ba wuta ba ? Cewar Nasir. Ai bamu gama magana ba,amma shi ne za ka tafi.?"

Ahankali ya sauke ajiyar zuciya..."Da gaske za ka taimake ni?"

"Me zai hana in taimake ka,ai babu abun da za ka nema ban yi maka ba,matukar ba sabon Allah ba ne." A cewar Nasir
Usman bai san lokacin da yay yi hugging Nasir ba,ya na murmushi.

"Toh yanzu was the plan da zamu yi kafin muje wurin Mama?"
Murmushi Nasir ya yi...Kai dai akwai ka da zanzana wallahi.
Dundu Usman ya kai mishi``` ...
```Da sauri Nasir ya jaye ya na dariya.

Ni da ya kamata ace ka na lallabawa,amma don cin zali,za kazo ka yi min dundu...sai in fasa zuwa wurin Mama"
Hararar shi Usman ya yi,"ba sai ka fasa zuwan ba mugani"

Shima Nasir, hararar sa ya yi "sai ka ce zai iya zuwa shi kadai" yana danne dariyar da ke taso ma sa"...
Da sallama su ka shigo falon mama. Sun iske ta zaune tana kallon TV...
Su ka duka har kasa,su ka gaishe ta. Tun da su ka gaishe ta, Usman ya koma gefe,kasan sa a duke kamar sabon maraya...
Mama tasan akwai abun da su ke so,kuma ko wane irin abu ne toh yana da mahimmanci.

Ta san halin su tun ba yau ba,idan su na son wani abu,toh za ka gan su sumisumi kuma kan su a soke kasa...
Ta yi murmushin manya...ta ce "Nasiru ba ri in kawo maka abinci,tun da Abokin na ka miskilancin ya tashi,balle ya zubo muku abinci"

Da sauri Nasir ya ce "wallahi mama a koshe nake."
"Toh shikenan...ta koma wurin zamanta."
Tana kallon su ta gefen ido su na kuskus,ba ta dai ce musu komai ba.
Nasir ne ya katse shirun da cewa "mama dama akwai maganar da ke tafe damu...ko daga jin maganar sa kasan a tsorace yake,gudun kar asamu akasi...
"To Nasiru Ina jin ka, Allah ya sa lafiya,tun da naga Babana ya sawo ka a gaba nasan "ba za a rasa nono a rugga ba"

"Lafiya lau mama,dama kan maganar yarinyar da Usman ke so ce."
" Alhamdulillah! Masha Allah, lallai wannan babbar magana ce,ta na maganar ta na gyara zaman ta."
Ka gani ko Nasiru, Allah maji rokon Bawa ya karbi adduar mu,ya cire mishi son yarinyar can...ya ma sunanta...?
Ba Usman ba,har Nasir sai da ya dago kan sa da mugun speed jin abun da mama ke cewa...
"Ah Ina yarinyar ta ke?" Mama ta jeho mu su wannan tambayar.
Cikin karfin hali

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment