Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nasir ya ce " ba anan garin ta ke ba."

"Allah sarki,a wane gari take?"
Ahankali Nasir ya kwashe komai ya fada wa mama...
"Tashin hankali wanda ba a sa masa rana!"

Godiya ta musamman ga mabiya littafin "ASHE BA SO BA NE . GASKIYA INA JINDADIN COMMENTS DINKU, ALLAH YA SA KA DA ALKHAIRI YA KUMA BAR QAUNA🥰

YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING...✍️

Domin shawarwari ko gudummuwa please👇🏻
08144066758
Ta ku har kullum
Yar mutan Argungu
Ke mu ku fatar alkhairi🥰```



```ASHE BA SO BA NE...📚

Incomplete..🖊️
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❤️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya👍🏻


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


❤️ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU👌

Free Book📚

Bismillahir Rahmanir Rahim

🍓🍓🍓🍓
🍓🍓
🍓
19
"Da sauri mama ta mike tsaye,ban gane ba...ita Hauwar zai kwaso mana? Duk matan da ke garin nan Nasiru ace ba wadda tayi mishi,sai ya je har Zamfara...ni ba ma zuwa Zamfara ba ne damuwa ta, yarinyar da zaije ya dauko min,amatsayin Bazaura,toh ban yarda ba, kuma ba da yawuna ba,ka ji infada maku. Kuma wallahi Nasiru ka fada mishi,ya fita daga idona in rufe!. Shiyasa kwana biyu duk ya bi ya susuce,kamar kazar da aka tsamo daga cikin ruwan zafi" toh, ku tashi kuban wuri tun ban hada da Kai ba Nasiru, yanzu inci muku mutunci!"
*** *** *** *** *** ***
Anan mama tabar su,ta shige daki ta na ta fada!!!

Hannu biyu Usman ya sa ya dahe kansa sabo da juya mishi da ya ke yi. Innalillahi wainna ilaihir raji'un ya ke nanatawa .
Nasir ne ya dafa kafadar sa,ya na girgiza mishi Kai,alamar yabi komi ahankali...dama shi tun farko ya san hakan za ta faru ,toh amma ba ya son ya sare wa Abokinsa guiwa,ya na son ako da yaushe ya zama mai ba shi kwarin guiwa. Duk da haka yanzu ma ba zasu rasa mafita ba insha Allah.
Inlow voice ya furta Aunty Amina...


ALHAMDULILLAH! INA SAMUN COMMENTS YADDA YA KAMATA👌Ni kuma insha Allah zan dinga yi muku typing akan lokaci🥰

YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING...✍️

Domin shawarwari ko gudummuwa please...
👇🏻
08144066758


Taku har kullum
Yar mutan Argungu
Ke mu ku fatar alkhairi🥰```






























```ASHE BA SO BA NE...📚

Incomplete..🖊️
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❤️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya👍🏻


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


❤️ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU👌

Free Book📚

Bismillahir Rahmanir Rahim

🍓🍓🍓🍓
🍓🍓
🍓
20
Daga falon mama,ba su zame ko ina ba sai gidan Aunty Amina...
Bayan sun shiga su ka gaisa. Ko daga ganin kamannin kanan na ta,ta San ba lafiya fa. Looks din shi sun nu na yana tattare da damuwa,har wani rama ya yi... In ma ba idonta ke yi ma ta gizo ba,kuka ya ke son yi,amma ya na kokarin dannewa .
Ta wuce kitchen ta ciko musu Tire (tray)da drinks da kuma snacks. But still idonta na kan kanenta. Sunan shi ta kira... Usman,me ke damunka,meyafaru? Duk ajere ta yi mishi tambayar. Dago kansa ya yi su ka yi ido hudu da shi... subhanallah! " Nasir wai me ke faruwa ne? Ko wani abu ya faru da mama ne? Cikin tashin hankali take magana...


Nasir ne ya kwantar ma ta da hankali akan cewa "babu abinda ya samu mama, lafiya lau ta ke."
Still Nasir ne ya sa ke kwance ma ta bakin jaaka ,bai rage komai ba...
Ahankali ta zauna a kujerar da Usman ya ke zaune,ta re da riko hannun sa...
Ta juyo da fuskarsa,ta saka tafin hannun ta,ta na goge mishi hawayen da ke zubowa...
Ahankali Nasir ya bar falon,ba tare da sun ankara da shi ba.
Fashe ma ta da kuka yayi,ya yin da ya saka dayan hannun sa,ya dahe saitin zuciyar sa,wani irin zafi ya ke ji,shikadai ya san me ya ke ji a wurin...
Duk abun da zai yi, ba za su fahimce shi ba,sai mai irin condition dinsa.
Shiyasan babu irin adduar da bai yi ba,akan Allah ya rage mishi wannan SO din,amma kamar ana kara mishi ne. Amma bakomi ya San ta shi kaddarar ce tazo a haka...

Sai da yayi kukan sa mai isar sa ba tare da ta hana shi ba. Akan ce kuka ma rahama ne...
Sannan ta dauki glass cup ta cika shi da cool water,ta mika ma sa. Nan ta ke ya karba ya shanye har da su kaari. Sai ajiyar zuciya ya ke sauke wa.
Bayan ta tabbatar da ya zama calm, sannan ta fa ra jawabi kamar haka..." Usman tun da na ke ban taba ganin ka irin yadda na gan ka a yau ba. Haka zalika tun da na ke ban taba ganin SOYAYYA a fili irin ta ka ba. Na dauka duk masu rubuta littaffai ( novels) karya su ke rubutawa,ba za a samu irin soyayyar ba a zahiri. Sai ga shi hakan ya kasance akan Dan uwana. Amma abun da ban ji dadi ba shine,rashin boye soyayyar da kake yi ma ta. Kasani su mata ba ayi musu haka,da zarar ta gane irin son da ka ke yi ma ta,toh wallahi za ta wahal sheka ne. Abu na gaba shine kabar ni da mama zan yi ma ta bayani dallah dallah yadda za ta fahimce ni...kuma insha Allah za a da ce... Kai dai kawai ka cire damuwa a zuciyar ka,gudun kar a samu matsala,kasan irin ciwon ka,kar a bata goma biyar ba ta gyaru ba."
Murmushi akan fuskar Usman, ya ma rasa irin godiyar da zai wa Aunty'nsa.
Ita ma murmushi ta mayar ma sa ta na kara ba shi tabbacin komai zai yi normal...
Sai yanzu, su ka lura da Nasir bai cikin falon...
Dariya Aunty ta yi tana cewa "Kai Nasir akwai kawaici"


Godiya ta musamman ga Aisha Abdullahi Anka tare da Farida Muhammad Bello. Ban manta da ke ba my Daughter fauziyya m Bello. Allah ya raya min Dan jikalle na 😃Wanda bai ba da kudin cefane😂


YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING...✍️


Domin shawarwari ko gudummuwa please...

👇🏻
08144066758
Ta ku har kullum
Yar mutan Argungu
Ke yi mu ku fatar alkhairi🥰❤️```







```ASHE BA SO BA NE...📚

Incomplete..🖊️
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❤️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya👍🏻


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!

❤️ True story
Written by
Fatima Zara Alhassan

Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU👌

Free Book📚

Bismillahir Rahmanir Rahim

🍓🍓🍓🍓
🍓🍓
🍓
21
Agurguje... Haka Aunty Amina ta dage wurin convincing Mama. Babu yadda Mama ta iya haka ta amince. "An ce taron yawa ya fi taron karfi😃". Mama ta fadama Kanan Baban su Usman, wato Alh. Sanusi. Bai ja zancen da nisa ba,ya ce zai Kira su ya sanar da su,nan da sati daya (1 week) su na nan tafe insha Allah."
A can Zamfara kuwa. Abba ne zaune shida yayansa Alh. Bala wanda aka fi sa ni da Kawu Bala. Bayan Abba ya koro mishi jawabin duk abun da ake ciki,har da zuwan iyayen Usman." Kawu Bala shiru yayi ya na kallon Kanan na sa. Kafin ya daura na shi jawabin da cewa... Adamu ka bude kunnuwan ka da kyau ka saurare ni.kasan halina... wallahi matukar wannan Yaron bai kwanta min arai ba,toh lallai ba zan ba shi Auren 'ya ta ba...kuma ni inso samu ne abar ita Hauwa ta fa ra aiki mana,tun da takardunta sun yi kyau. Tun da ba mararraba muke nema da ita ba...Aa Yaya dan Allah abar maganar aikin nan, idan ta yi Aure mijin ta ya ga yana da ra'ayin ta yi aiki, ai sai tayi a dakinta. Tun da yanzu kowa ne magidanci ya san mahimmancin aiki ga iyalan sa.
"Tabbas,Adamu ka nu na min iya ka ta akan 'Yar ka, toh in ba iya ka ba, miye na katse min zance na ban ga ma magana ba!".
"Ayi hakuri Yaya wallahi ni ba da wata manufa na ce haka ba,amma Allah ya huci zuciyar ka. "A toh,ni dai karka kullaceni, magana dai ce na ri ga da na fada tun farko. Allah ya kawo iyayen Yaron lafiya,in duba shi da kyau ingani,idan ba su yi min ba sai su kara gaba. Haka dai Abba ya yi sallama da shi. Amma a cikin zuciyar sa, yana Addua Allah ya sa kar asamu matsala daga wurin Yayansa." Sabo da ya san waye shi. Shi mutum ne mai mugun son Kai,da kuma nu na isa ga abun sa. Ga son kudi ,kudi kadan na iya canza maind dinshi. A wani bangare zan iya cewa Hauwa ta debo shi..."
Sai dai muce Allah ya shirya irin su,ya kuma karemu daga fadawa irin wannan hanya.
"Aka ce rana ba ta karya, sai dai uwar diya ta ji kunya." Hakan ce ta kasance a yau... A falon Alh. Bala Waziri,cike ya ke da Baki wato iyayen Usman. Bayan gaishe gaishe aka fa ra gudanar da abun da ya ta ra su...
Magabatan Usman da shirin su, su ka zo. Sun kawo kudin gaisuwa da kayan ( i see I love). Kuma su ka roki alfarmar nan ba da jimawa ba,za su dawo ayi maganar sa ka rana,sabo da ba su son aja zancen da nisa. Su ma bangaren iyayen Hauwa sun yarda.

ARGUNGU
Mama ce zaune da 'yayanta,su na farin cikin wannan rana. Yau ga Autan ta ya ku sa Aure,tana kallon su tana kara godiya ga Ubangiji da ya raya ma ta su. Ta kuma yi musu Adduar samun farin ciki har karshen rayuwar su...
Kwallace ta zubo ma ta,ya yin da ta tuna da mahaifinsu. Ba rabon ya ga wannan rana mai cike da farin ciki, ganin ta ke kamar an daura Auren ne. Usman ne ya lura da ita... hankali tashe ya ke fadin " mama meya faru?" Da sauri su ka iso wurin ta, su ka sa ta a tsakiyar. Murmushi ta yi musu ta na mai shafa kumatun su. " Kar ku damu kukan farin ciki ne,Auta ya ku sa Aure. A tare su kayi hugging dinta .
"Mama indai har yanzu ba ki son Aure na da Hauwa wallahi sai a fasa" cewar Usman yana dariya..."
Dundu ta Kai mishi...ta na murmushi ta ce "so ka ke yi abar ni da jinya ko? In ba haka ba ai sai ince a fasa mana,ta na dariya." Haka dai su ke ta barkwancin su....
Happy Family❤️🤍
Zamfara state
Yau 3 weeks da aikin Hauwa a FMC Gusau. Duk da Abba bai so hakan ba,amma ba yadda ya iya da Yayansa. Yanzu da zarar ya yi mishi magana,zai ce ya na mai iyaka da 'yayansa ne.
Duk abun nan da ke faruwa Usman kawai ne ya san da aikin Hauwa,ban da iyayensa. Kuma Shima ya yi shiru gudun kar asamu matsala. Shiyasa ko Nasir bai fadawa ba. A haka dai ya tattara komai ya aje gefe. Ya koma bakin aikinsa...


Misalin karfe biyar na yamma, Hauwa ce ke tafiya za ta je gida, kasancewar duty dinta ya kare.
Wata mota ce Black kirar G-wagon, ya fa ka agaban ta. Yayin da Glass din motar ya yi very slow wurin saukewa...

GASKIYA YAU NAYI MU KU TYPING DA YAWA,AMMA BAKOMI SON KU NE YAYI MIN YAWA😂

YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING...✍️

Domin shawarwari ko gudummuwa please
👇🏻
08144066758

Ta ku har kullum Yar mutan Argungu
Ke yi muku fatar alkhairi❤️🥰```









































```ASHE BA SO BA NE...📚

Incomplete..🖊️
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❤️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya👍🏻


Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!


❤️ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan


Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU👌

Free Book📚

Bismillahir Rahmanir Rahim
🍓🍓🍓🍓
🍓🍓
🍓
22
"Doctor" cewar Hauwa. Ya yin da ya kawata fuskarsa da Cool smile, wanda ya sa ka dimple dinsa lotsawa... cikin Deef voice ya ce "Beauty ke ce, shigo in rage Miki hanya sai ki biyani. Still fuskarsa remains smiling. "Aa Doctor nagode,yanzu yayana zai zo dauka ta." Ta ce hakane kawai dan ya kyaleta. "Beauty kar muyi haka ma na...ko tsoro ki ke ji karna gudu da ke? Yana yi ma ta dariya...
Baki Hauwa ta sa ki ta na kallon ikon Allah. Mutumin da akace miskili ne, magana ma wuya ya ke yi mishi,balle ya yi maka dariya. Lallai ta cire tuta da ma ace su Sister Merry za su ga ni, ai da sai sun sara ma ta...
Maganar shi ne ya dawo da ita hayyacin ta. "Beauty kar muyi haka da ke mana" yanayin yadda ya yi ma fuskarsa ne ya na rokonta,shiya ba ta kwarin guiwar shiga motar sa. Ahankali ya ke tuka motar kamar mai tausayin steering. Shiru ne ya ratsa ba mai cewa komi, acikin su.
Smile ya yi yana mai cewa"Beauty ko in wuce da ke gidanmu? Ya na dariya...
Ta gane me ya ke nufi,wato bai san gidansu ba. A Haka ta dinga nu na mishi har kofar gidansu.
" Godiya ta yi mishi ya yin da ta ke bude kofar mota,ta ji ta arufe. Da sauri ta mai da kallon ta gefen sa. Ido hudu su ka yi, ya yin da gabanta ke faduwa,sabo da yanayin idanuwan sa,kamar na Rotik Roshan. Sun kuyar da kanta kasa ta yi,ta na wasa da yatsun hannunta. Bude Lock din ya yi,sabo da ya ga kamar a tsorace ta ke da shi. Murmushi ya yi mai kawata fuskarsa. "Bye Beauty". Cewar Doctor
Godiya ta yi mishi ta wuce cikin gida. Shima ya jaa motarsa ya bar unguwar...
INA MASOYAN USMAN,TOH KU FITO WALLAHI INBA HAKA BA DOCTOR ZAI YI WUFF... DA HAUWA🤣ATOH,NI DAI BA RUWA NA,KARKU KULLACENI😃 ya kamata ku dauki mataki tun yanzu,sabo da kunsan halin Hauwa. Bangare daya kuma ga Kawu Bala.

YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING...✍️


Domin shawarwari ko gudummuwa please...
👇🏻

08144066758

Ta ku har kullum Yar Mutan
Argungu
ke yi mu ku fatar alkhairi🥰❤️```



























```ASHE BA SO BA NE...📚
Incomplete..🖊️
MARUBUCIYAR
**Bayan wuya...
** Ashe ba so ba ne

Ban manta da ke ba sisi my IMAN FATIMA❤️so much

Saddam kabeer magaji,na ga kokarin ka Allah ya bi ya👍🏻

Gargadi!!
Ban yadda wani ko wata su juya min littafi ba, ba tare da izinina ba!
❤️ True story
Written-by
Fatima Zara Alhassan

Na sadaukar da wannan littafi ga USMAN ARGUNGU👌

Free Book📚

Bismillahir Rahmanir Rahim

🍓🍓🍓🍓
🍓🍓
🍓
23
WAYE DOCTOR FARUK?
Dane ga shahararren dan kasuwan nan mai suna Abubakar,Wanda ake Kira papa. Mahaifiyarsa mai suna Hajiya Sakeena,(mami) macece mai ji da kanta. A bangare daya kuma mafadaciya ce sosai. Faruk Shikadai ne ga iyayensa,ya yi karatun likitancin sa a Oxford University da ke kasar England (UK). Yanzu haka ya na aiki a Asibitin Abuja NIZAMIYE a fanin NEUROSURGERY ( Likitan kwakwalwa). Amma every 2weeks ya na shigowa Zamfara domin ba da tashi gudunmuwa,ya na da taimako sosai, wannan kenan.
Doctor Faruk ya yi bincike akan Hauwa aka ce abin "duniya ba ya boyuwa" ahankali Hauwa ta fara son shi,amma duk haduwar da zasu yi, sai dai su hadu a gidan Kawu Bala. Hakan yana ba Faruk mamaki,meyasa ba ta son ya je gidan su,Amma har yau ba ta fada mishi dalili ba...
A gidan Kawu Bala, kowa yasan Doctor Faruk,kuma Kawu ya ba shi goyon baya tare da alkawarin cewa "matukar shine madaurin Auren Hauwa to ya ba shi...
Abangaren Usman kuwa,cikin kwanakin nan ya ra sa gane kan Hauwa,in sau Dubu ya kirata toh, zata ce mishi busy ta ke. Tun ya na ma ta uzuri da cewar "kila yanayin aikin ta ne,ya zo da haka,har abun ya fara damunshi. Haka ya sa damuwa ta yi mishi yawa sosai,amma ya na kokarin dannewa, saboda karsu mama su gane, idan ya ji alamun ciwonsa zai tashi sai ya shaa magani, kuma yanzu abun da ke kara daga mishi hankali,bai wuce kin daukar wayarsa da Hauwa ke yi ba. Goma ya Kira ta in har dare ne toh za ka ji number busy, baya son ya yarda da abun da zuciyar sa ke fada mishi....
Abangaren Kawu Bala kuwa ya ba wa doctor Faruk dama ya turo iyayensa, haka kuwa akayi....
Faruk ne zaune gaban Papa,ya gama yi mishi bayani . "Toh maasha Allah, hakan yayi kyau sosai, but I think it's better a fara magana tun yanzu... Muryar Mami su ka ji tace "babu maganar da za a fara Alhaji" duk su ka daga Kai suna kallonta ta karaso cikin parlon, bacin rai karara a fuskarta ta ce "yanzu ni zaka munafurta Faruk, haka muka yi da kai, toh kasani wlh idan ina numfashi a doron kasa baza ka Auri yarinyar nan ba, idan kuma kana son ganin ba daidai ba a lamarinka ka ci gaba da alaka da matsiyaciyar yarinyar, Ina zamana ka dauko min talauci a matsayin suruka,to wlh ka yi kadan gwara kayi tazama ba Auren yafi, ga yarinya mai hankali mai natsuwa na nemo maka, yarinyar kuma tayi mugun na'am da kai za ka tozarta ni ka mai dani karamar mutum a idonsu??"
Papa yace "Abin da na ke son infara fahimta anan shine, labe kike min Sakeena?" Mami ta tabe baki tace "idan ma laben nayi Allah ne yasan bani da hakkin kowa shiyasa har ya bani ikon labewan inji komai, Alhaji wato idan kasan talauci toh akan Yarinyar da iyayenta ya kare, can wani rukubebben unguwa fa suke,to idan ba tozarta mu Faruk ke son yi a idon jama'a ba Ina shi ina Bazaura dan Allah, kyan banza kyan wofii,toh gaskiya kayi min iyaka da shi, sabo da wlh zan nuna masa bacin raina, sam bazai ji da dadiba wlh, salon kawai ya cuceni shine zai kwaso muna Bazaura infita jama' a ana nunani, Dana ya Auri Bazaura Sam... Sam.. haka bazai yiyu ba ."
Papa ya girgiza Kai ya ce "Hala ma ke, ke raba talauci da Arziki Sakeena?" Mami tace " nidai ba ruwana, nasan dai muddin Ina da rai ba za ayi Auren Nan ba." Ta fita fuuu... Papa ya girgiza kansa yace " Look my son, ba ruwanka da wannan matar, ba isasshen hankali gareta ba. Am giving you my words,ka ci gaba da neman yarinyar, Allah ya shige mana gaba." "Amin Papa" ya Mike ya ce "nagode Papa " daga haka ya fita daga parlon.
Abba ne zaune a parlon Kawu Bala, kasancewar Kiran gaggawa da yayi mishi. Maganar Abba ce ta katse shirun da ya ratsa da cewa " Yaya Allah ya sa lafiya?" Mirtsitsi Kawu Bala yayi da idanuwansa ya na kallon kanen nasa, ya yin da ya girgiza kansa ya ce "Toh Adamu lafiyar ce ta sa har na ce kayi sauri kazo Ina kiranka, sabo da maganar ba ta waya ba ce, kuma naji dadi da kaxo Allah shii maka albarka, to maganar gaskiya zan Kira iyayen Yaron can wadanda su ka kawo kayan Hauwa za a mayar musu da kayansu, sabo da nayi ma ta miji daidai da tsarinta



kuma shine daidai ita ba wancan yaron ba, saboda haka nace bari in Kira ka in fitar maka da hakkin ka amatsayin ka na ubanta, Kar azo tambaya inkira ka kace ba kasan zancen ba." Abba bai San lokacin da ya zauna a kasa ba yana fifita da hularsa...


Godiya ta musamman ga Shamsiyya Bala tare da Sumaiya Adamu Anka, Saratu khamis kibar harara ta ban manta da ke ba🤪 Murja Umar Tubali naga sakon ki kuma nagode sosai Allah ya bar zumunci👌
Special godiya ga

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment