Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata gareni So, Ummi baya raina
abinda yake so da nayi zaton zubar da kima ne in
furta maki kalmar so musammam in na tuna ke
baki soma, zurfin a so bashida wani amfani don
na sha wahala.Ba zan Qara boye dimbin son da
nike maki ba Ummi ko gaban wa zan nuna kina
jina matsala? Ummi wadda ke zaton mafarki take
sai taji bakinta yana furta wayyo dadi Ya Allah
kada ka farkar dani in har bacci nike Abba yace
ciji yatsanki zakiji zafi Ummi nine Abban ki mai
sonki wanda ya reneki tun kina zanen gobe.
Hawaye suka soma zubo mata cikin muryar kuka
tace Ya Abba da gaske kana sona? Nafi zaton
tausayina yasa ka furta haka, Amma koba gaske
ba ne na gode kuma naji dadi Amma ka sani Ya
Abba ina sonka mai tsanani sai tasa kuka. Yace
ummi yi shiru, in kukan takaici ne kukan ya kare.
Nima na jima ina sonki jiya naga sakonki a wayar
umma da kike rubutawa mai dauke da nuna sonki
gareni. Sai zurfin ciki ya hanaki, don allah ummi
kada ki koma zurfin ciki a sona, ki zazzage min
duk irin sonki gareni. Ummi tace yau kam ji nake
kamar a mafarki. Sun nutsa a cikin hirar so suna
ta baiwa juna labarin halin da suke shiga a baya,
a lokacin daya ganta da wani namiji yace
hankalinsa yayi mugun tashi. Sai lokacin daya
fuskanci bashir na sonta, ita kuma Tace ta tsani
koh mace ta kira layin shi, zainab kuwa data
samu labarin ta kamar ta mutu. Tace ko bishira
bata kishi kamar yarda take kishin zainab, sunyi
nisa basu san sun kwana zance ba, sai da ummi
taji kiran sallah. Tace ya abba kaji abunda naji,
yace sallah ake kira naji, kin sani kwana zance.
Ban gaji dajin muryarki ba amarya tah. Ummi
tace gari yayi saurin wayewa kaje kayi muna
godia ga allah ta hanyar nafita, yace to matata.
Hamdala ta rikayi har bacci ya dauketa, muryar
umma taji tana cewa ummi ki tashi kiyi wanka ki
gasa jikinki. Tana zaune cikin baho wanda umma
ta zuba ruwan dimi da dettol, tsohuwa ta shigo
cikin bandakin. Ummi tace don allah tsohuwa fita,
tace don allah ja can anki a fita din, ta saka
hannu cikin ruwan wankan ummi dake gefe a
bokiti. Tace ina suwaiba? Ai karo mata ruwan
zafi, wannan ruwa yaushe zata gasa jikinta, idan
da dan tawul dauko in danna mata jikin. Ummi
tace nidai tsohuwa ki barshi don allah, sai kace
wata mai jego? Tsohuwa tace tafi can kuda baku
san darajar jikinku ba. Wannan rawar kan da mai
sunan malam keyi idan ba'a gyara kiba saiki ba
sai zance ya dawo baya, idan anyi magana ku
yan zamani kuce bamu waye ba. Alhali ku
wayewarku itace kwalliya amman jiki ba'a san a
gyara ba, umma tazo ta kara mata ruwan zafi a
cikin bokiti. Tsohuwa tace yau a sawo bagaruwa
a tafasa ruwan shigar tata da ita don tayi saurin
warkewa. Kuma ko ina zai hade, in kin koma
gidanki kin kwana biyu ki dinga hada bagaruwa
da alim kina tafasa su kina shiga.IKI novels / ZURFIN CIKI book 4 part 29
ZURFIN CIKI book 4 part 29
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:31
Umma Tace xa'asiyo tafita tabar su ummi
nacewa to tsohowa kije mana tace bantafiya sai
naga yanda xakiyi ganin ummi tabata lokaci nan
tsohuwa ta dauki tawul din tashiga nadar ruwa
tana dannama Ummi, Ummi tanacewa itadai
abata tayi da kanta. Tsohuwa tace gaddamace
daku ya'yan yau kinga duk macce dake rufe
jikinta tafita daban damasu tallar jiki. Ita macce
anfison a sameta ko yaushe da dumi a jikinta,
yawo babu takalmi ko a tsakargidane yana
ragewa mace dumi sbd sanyinda ke ratsa tafin
kafarta har ni'ima yana ragemata. Sannan zama
atantagaryar suminti shima yana rage mace, da a
ace zaku gane kunga masu saka hijabinnan da
safa? bakaramin wayo suke yimukuba. Inda za'a
banbance za a samu sunfiku ni'ima da kyau fata,
don haka sai kin dage Ummi dai tayi shiru, amma
aranta cewa take wannan tsohowa ko ina tasan
wannan duk bayanin? Filo aka ajewa Ummi ta
zauna tana karin kumallo, duk takosa taga
abbanta, koda ta tsinkayi sallamarsa tamkar
tamike ta taroshi. Amma dole yaje yagaida su
alhaji, tsohuwa tace aefa mu kuma bana munga
takanmu don nan zaka dinga likemana. Yace
dadin abundai nima nan gidan ubanane, da
uwata. Umma tana kicin tanamasu dariya. Tunda
ya zama idanunsu sunsarke da juna sun kasa ko
magana Ummi ce tayi karfin halin lumshe ido
sannan tabude tace sannu daxuwa. Tasowa yayi
ya tsugunna kusa da 'its, yajikin babyna?sunan
yamata dadi, naji sauki bari in kawomaka abun
karinka. yamika mata tafin hannunsa tasaka nata
yahadasu ya yasarke, murya kasa kasa yace
barshi na' amso. Ta kula abba mutum ne maison
wasa da tafin hannu. Ita kanta tanason hakan da
akwai wani sako da tafin hannu ke isarwa acikin
duniyar ma'abota so, kila wannan dalilin ne yasa
abba ke kashema tafin hannusa kudi da mayukan
da ke saka laushin hannu har ita mah ya
saimata. Koda umma ta shigo Ummi tayi kokarie
amshe hannunta amman abba yaki saki, kuma a
hakan ya karya. Umma kasa zaman dakin tayi
domin a baki abba yake ba Ummi abinci, umma
nafita taceels / ZURFIN CIKI book 4 part 30
ZURFIN CIKI book 4 part 30
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:33
Daren ranar duk suna kan kujera doguwa a dakin
umma ya bude mata laptop wai yana koya mata
kanta kwance a cinyarsa, umma ta shigo dakin
tsohuwa tace tsohuwa zaifi kyau mu sallami
yaran nan na gaji da ganin wannan aiki nasu ai
tasamu sauki. Tsohuwa tace suwaiba ina laifin ta
kwan goma ma, umma tace anya zasu kwan
goma nan? Gobe bakwai guda ta koma dakin ta,
tsohuwa tace shine nan. Abba yace Ummi kinfa
samu sauki ba zakizo mu koma gidan mu ba?
Tace su umma ne zasu maidani ai nima ya abba
inason in koma yace yau nan zan kwana in sunga
haka sun kuramu, Ummi tace ya abba kayi hnkr
kada ka kwana, shine yace kin yarda goma inxo
mutafi ko ba sanin su umma? Tasa dariya tace
taf inajin kunya bazan iya binka ba yace to kuwa
zan kwana a nan. Suna cikin haka umma ta leko
tace abba bazakaje gida ba yanxo fa sha biyu
saura, yace umma nima nan zan kwana. Ta rike
haba nan din lafia? Yace to umma nima ba gidan
mu bane? Ummi tace dama yafi umma kada yaje
wani abu ya rudashi, umma tace a'a abba tashi
ka tafi insha allah gobe Ummi zata koma yayi
murmushi tare da cewa nagode umma.nan dai ya
tattara yanashi yanashi ya tafi gida cike da
kewar matarshi, itama Ummi lamo tayi a gado.
Bayan umma ta gama yimata fada ta bari ta
warke taki ko, sai cewa tayi umma ni fa na
warke. Umma ta kalli Ummi cike da mamaki tace
yaran yazo saidai a barsu. Shiyasa akace idan
macce ta isa aure ayi mata a huta. Ita kam Ummi
tana ganin a barta tabi mijinta ta faranta mashi
shine abinda yafi dacewa don yanxu ba inda ya
kai mata dakinta dadi bacci. Duk da kashedin da
tsohuwa tasa abba dakinta tayi mashi na cewa
ya bar Ummi sai ta kara sati kafin yace zai
kulata da sunan auratayya, bai sa abba jin zai iya
ba. Don haka koda ta fada mashi cewa yayi kadai
da huruminki da wanda ba naki ba duk sai kin
shiga? To nidai ki lafa man haka. Ya fice a dakin.
Ita kuma tana ta fadanta tana cewa "Na shiga din
dan neman yaro, da kyar ya barta ta kara kwana
biyu ya afka mata don shi hkr sa ya kare, ta
nuna mashi ita fa tsoro take ji kada ta wahala, ya
lallasheta yace ba wani wahala. Ummi tana son
faranta ran mijinta. Don haka ta jure duk da
yarda yazo mata ba sauki, sai dai tasha albarka
kuma ta kara samun wani matsayi na
musammam a gunsa. Cikin satin ta zama yar
lelenshin kafin sati biyu ta hardace duk wani
darasi da abba yake koya mata, abba jinsa yake
kamar wannan lokacin ne ya fara rayuwar
angoncinsa. Sam ya manta yana da wata mata
uwa duniya saida Aunty ta kirashi tace lafia baya
kiran matarsa sai ga abba da girman shi ya girba
karya. Wai ya kira ya kasa samunsu Aunty ta
yanda tunda farkon tafiyarsu yana kiransu sun
gaisa da bishira tana tmbyrshi ina hibbarta? Sai
lokacin ya tuna kwana biyu bai ganta don tana
gidansu umman bashir, amman sai yace tana
lafia in yaje zai kirata taji gwarancin yar tata.
La'asar sur suka jero ita da abba don su dan
zaga kurum. Sun shigo gidan ahmad da muktar
duk basu rabu ba saida sukaji sun saba da ummi.
Don ita haka take yana da wuya kayi zaman awa
guda da ita bakaji ta kwanta maka a rai ba. Abba
yaji dadi yarda Ummi ta nuna kauna ga matan
abokanin nasa, yasan bada jimawa ba matansu
zasu zama kawaye kamar yarda yaso da bishira
amman taki. Daga can suka nufi layin su gidan
su umman bashir Ummi tace su fara shiga su
dauki muhibba abba yace bazata yarda dake ba.
Ummi tace zata yarda muje a ran abba tsoro
yake gada umman bashir ta gwasaleta Ummi, sun
sameta tana shara da sauri Ummi ta amsa ta
soma sharewa hakan ya faranta ran abba sai dai
da ya kalli umman bashir yaga tana hararar
Ummi, saida ta gama taxo ta zauna suka gaisa
abba na rike da hibba tayi kaca kaca da kunu
gashi duk ya dunkule dama ko lokacin da bishira
tana nan haka zakaga yar duk kazanta. Ummi ta
bude post dinta ta cire dari biyu guda biyu ta
mikawa umman bashir gashi umma kin sai goro
saida ta tabe baki ta amsa babu ko godia, sai dai
abba cikin jin dadi yace angode, da hibba taki
binsu Ummi tace kamal xo ka siyo wa hibba
alawa, kinga baba kamal baya nan xo muje in
sayo maki. Cikin sa'a sai taxo zasu fita sai ga
bashir dauke kai yayi tare da jan tsaki daya shiga
gidan sai ya hau umma da fada Wai ta daina
barin Ummi da wannan abba suna zuwa in ba
haka ba zasu kawo mata wani asiri. Umman
bashir tace suta zuwa ma indan ta nine mi jiya
tayi bare yau, ka gansu dari hudu yanxu ta bani
don haka bazan hana zuwa ba amma fa ina nan
yarda nake bazan canza ba, suna shiga gidan su
umma kicin ta wuce ruwan zafi ta zubu ta cude
muhibba tas, ta wanke mata kai ta chajeshi ta
shafeta da mai nan ma basu jima ba suka nufi
gida zanen umma ta ansa ta goye muhibba, shine
ya bude dakin bishira duk kayan yarinyar sun rine
da datti, Ummi dai ta zazzaba yace .ba maidata
za'ayi ba, Ummi tace ta dan kwana biyu mana.
Yace tana fitsari fa. Ummi tace kasawo muna
pampers Yace shikenan duk da ya nuna bayaso
yarinyar ta zauna gurinsu amman yaji dadi sai
lokacin bacci daya shigo ya shigo da pampers din
ta saka mata Sannan ta kwantar da ita can gefe
ta azama mata pillo guda haba guda baya, su
kuma suka kwanta a nasu makwancin suka
cigaba da soyewa. novels / ZURFIN CIKI book 4 part 31
ZURFIN CIKI book 4 part 31
Posted by Bashir Sani Fesan on 15 Dec 2016 - 14:36
Ummi tana son yara don haka hibba ta dinga
samun gata, satinta guda umman bashir ta dinga
jaraba sai an dawo da ita. Wai kwadayi ne don in
bishira tadawo ta bata tsaraba, amma koda ta
tafi da hibban yarinyar sai taqi sai kuka har dasu
amai. Dole aka dawo da ita, don alhaji karami
cewa yayi atattara mata kayanta duka inyasake
samun an maido da ita sai ya saba ma umman
bashir. Hakan da babbar sallah abba yakashe
musu kudi ita da hibba, sai dai duk abinda yasai
ma ummi to ya aje ma bishira nata. Ita kam tana
can duk addu'arta akan ummi ne, kafin ta dawo
ummi tafita, don haka data dawo da kwarin
gwuiwarta ce wa bazata samu ummi agidan ba.
La'asar sakaliya, direban gidansu ya iso da ita
gidan kamar yanda mahaifinsu ya umarce shi
cewa in ya dauko su kada yaso dasunan, ya dire
kowa agidanta. Kasancewar unguwa uku suka
soma zuwa sai anty ta taya bishira diban kaya
su shiga. Daidai kofar dakin bishiran abba na
kwance rigingine, 'yar T-shirt ajikinshi fara kar.
Dawandon jeans gajere iyaka gwuiwa. Ummi
kuma dogon wando ne irin mai kama jikin nan
dariga mai kamar singileti kanta yasha kana nan
kitso, tayi filo da kirjinshi yana bata labarin wata
mota da yake son yabada tashi yayi ciko. Ita
kuma tana ce masa ya dai je ya shawarci umma,
muhibba kuwa tana ta faman wasa da sabbin
kayan wasanta da ummi tasai mata. Ita ma cikin
'yar shimi mai kyau, kanta kuwa ummi tayi mata
kitson (3 in 1). Sororo bishira ta tsaya tana
kallonsu, sam bata tsammaci a irin addu'ar
datayi zata dawo ta samu ummi agidan ba. Basu
ganta ba saida anty tayi sallama tare da cewa, ya
naga kin tsaya? da sauri suka waiwayo duk suka
mike. Gaban ummi yayi wata muguwar faduwa,
amma duk dahaka cikin fara'a ta nufe su, bishira
ta hade rai matuqa sannan taqi ko kallon ummi
ta nufi 'yarta. Anty kam cikin fara'a suka gaisa da
ummi harta zage jakarta dake kafadarta tabawa
ummi wani dan agogo mai kyau. Nan dai ummi
tayi ta godiya shima abba ya mata godiya. Abban
ne ya shigar mata da kayan daki, ummi tana
cewa anty kin mana dawowar bazata, dakin fada
da an share miki dakin. Nan ma bata tanka ba,
ummi dai data gaji dayi mata sannu bata amsa
ba sai kurum ta nufi dakinta, zuciyarta babu dadi,
tasan yanzun ya Abba zai raba jin da yake da ita
zuwa su biyu. Bishira tayi kyam tana ta qamshi
don anty baza su barta tazauna masu da qazanta
ba, ga haqorin makka an sako ana ta qwambo.
Ranar dakinta Abba yakwana, yanda bata ga
wata rawar jiki daga gare shi ba tayi zargin ummi
tasamu lafiya. Hakan ya qara dagula mata lissafi,
tayi rabon tsarabarta daga kawayenta sai
maqota, don ko umman bashir daga zam-zam
bata qara mata komai ba. Dama tana cike da
haushin umman data bari ummi ta daukar mata
'ya gashi nan muhibba ta liqe ma ummi. Hakan
ya shaqar da umman bashir har tace amaida
mata zam-zam dinta ita bata sha. Wato don taje
makka shine zato zo ta canza hali? Ita kuma
bishira ta amsa tare da cewa, ai ba ita ta aike ni
makkan bada har sai tazabi abinda zan bata.
Ummi ko zam zam din ba abata ba, kuma ko
ajikinta. Abba kam shita kawo masa dogayen
riguna da T-shirt masu kyau, amma su anty ne
suka matsa mata sai ta saya. Ranar daya dawo
daga dakin bishira ummi tana fashin sallah gashi
yanuna yana dalarura alokacin. Sai tace ta yafe
masa yau dagobe yaje gurin anty bishira, yace
A'a tace ba haramun bane nina amince, yace
nasani. Shiba yason sai yatafi tafara damuwa ko
tazo tana jin haushinsa, tace ba komai saida
yatafin kuwa har kuka tayi don kishi. Amma
tabawa zuciyarta hakuri tasan wata rana wannan
jarumtar datayi zata zame mata alkhairi. Ita ko
bishira koda yazo mata sam bata damu ta
bincika ba, tunda taga ba girkinta ba, saima ta
hau murna yayo satar kwana ya bata musamman
dataga dayayi wanka yakoma dakin ummi, haka
washegari. Don haka sai tashiga daga hanci har
da 'yan habaice habaice, kafin tadawo tun da
dama da namiji dan uwansa yake kwana. Tana
nufin ummi bata ba tayi masa amfanin komai
wannan yasa ummi ta daura aniyar cusa mata
takaici, aranta tace tunda cinikinki labe nikuma
zansa miki hawan jini. Kamal yazo daukar abincin
da ummi ta saba sawa yau har da kunun gyada
tayi. Bishira ta kalle shi, wai kai wannan abincin
na waye kullum kake zuwa dauka? Yace na
ummarmu ne. Ta taba baki, ummar nan taku
kwadayinta yayi yawa, ko kuwa itama asirin ya
kamata ne? Kamal kuwa yaje yafada sai ga
umman bashir agidan suna zage zage da bishira,
tana ce ma bishira dadin abin gidan dana nazo
kwadayin ba gidan ubanki ba. Marowaciyar bnza
ai dama ina da cikinki, lokacin da Abba yasai
maku TV, yace ki bani naki sai ki kace gara kiyar.
Bishira tace, Eh na hana TV aiba wani shegen ya
sai minba, ubana yasai min, kuma nace mai
kwadayin yarinyar daki kace uwarta mai asiri,
menene na amsar abincinta kici banda kwadayi?
Shiyasa kika bata 'yata ashe don asami abinci
ne, umman tasa kuka ni ke ke zagi? Yau ko abba
zai zo gidan nan zai zaba ko ni ko ke. Ummi dai
tana daki tana jinsu. (aranta tace dadi na da
gobe saurin zuwa). Bishira tace dama ya darajaki
ne shine za kice haka, yazo din nace mai kwadayi
harda rainawa na baki zam zam butulu duk
abinda na miki kin manta kece kika aikeni
makkan? Umman tace, zuwa makkan naki dashi
gara babu, don nasan da kyar ne in za akarbi
wannan aikin nani ke da bakya sallah arniyar
banza qazama. Ummi harda riqe ciki don dariya,
haka dai suka yi tayi wajuna gori har dai 'yan
kallon da suka taru suka soma bda haquri,
umman bashir tayi gida cikin kuka. Tagayawa
'ya'yanta komai su bashir dasunce sai sunje sun
zaneta umman bashir din tace barta ku barta
kawai bari abban yadawo. Da dare ta ritsa shi
agidan yasha mamakin wai yau mahaifiyarshi da
bishira ne suke fada yace hakane dama duk
zamantakewar da ba'a kafata don Allha ba wata
rana sai ta rushe. Nan yayi tawa bishira fada da
cewa uwarshi sa'arta ce dazata tsaya ta dinga
gaya mata magana? Nan fa aka sake kacamewa
har abba. Yakai ga kwasa wa bishira mari,
sakamakon irin rashin kunyar data rike qugu take
tsulawa umman bashir din. Ummi ganin abin yana
tsawo ta fita taja umman bashir tana bata haquri
ta zaci zata hantare ta amma sai taji tana cewa
ba komai ummi sakayya ce tunda na nuna ina
sonta dole tamin haka. Abba yace ummi tasa
mayafi taraka umma gida, hakan ya qara qona
ran bishira gashi yanda taga Abba ya bata rai zai
iya yin komai, dole ta koma daki tana cizon yatsa
tare da tunanin mafita. Ummi kuwa ahanya sai
lallashin umman take tare dayi mata alqawarin
cewa duk abinda take so ta tambayeta zata mata
shi tarakata har gida sannan tadawo. Sabon kuka
umman bashir tazauna tanayi, takaicinta yanda
bishira ta zage ta taci mata mutunci agaban
ummi, tashare ido tare dayin ajiyar zuciya a fili
tace dani take magana. Ynzun ummi tasan kishi
fiye da baya, don ta hau turbar ma'aurata kuma
tasan muhimmancin abinda ake yiwa kishi, don
haka zatayi komai na jan hankali don ganin taja
mijinta gareta. Kuma inta lura cewa bishira ta
maqale mata aqofar daki sai tayi ta jan abba da
wasanni, don ta quntata ma me labe. Amma
hakan baisa ta daina ba, don haka ta daura
aniyai saita mata abinda zata tona kanta ha abba
yasani. Duk jumma'a abba yana dawowa gida
musamman in ranar girkin ummi ne don cin
abinci na musamman. Jumma'a biyu kenan bata
fado kanta ba sai wannan, don haka tun alhamis
taje ta yarfo kitsonta, ta biyo ta gidan su gurin
tsohuwa tazo. Don haka suna gaisawa da umma
tace gurin tsohuwa nazo. Suka shige daki tace da
tsohuwa nazo ne indan samu dan wani sirrin.
Tsohuwa tace, name ummi? Ta ce na gyaran jiki
mana. Fati tace min kwanaki kin fada mata wasu
abubuwa. Tsohuwa ta ce, ja'ira, kinga uwar bari?
Dama nace zaki same ni ina kyakkyawan zamana,
bada ina fada miki kina sharewa ba? Ummi tace
haba tsohuwa banaso aji mu yanzun dai ki bani
shawara sannan ki fada min abinda zanyi inja
hankalin mijina. Ta ce, toda farko ki dinga kula da
jikinki ta hanyar rufe shi ruf, kada kibar kofar
iska. Banda tafiya ba takalmi, iska tana shiga
tanan kuma mace narage ni'ima banda zama ba
dankwali inso samu ne hatta tsarki ki daina yi da
ruwan sanyi, ki dinga yida ruwan dumi. Sannan ki
amshi bagaruwa gurin ummarki ki dinga shiga
inkin tafasa da alif dakuma saiwar mata, sannan
inkinyi al'ada kin gama kinyi wanka toki dinga
matsa farin miski a ehem dinki. Sannan ki samu
saiwar kankana, saiwar zogale, kanunfari,
mazarkwaila dazuma amma kisa kanunfari
dayawa sai ki dafa su su dafu kullum kisha kofi
biyu safe da yamma. Sannan ki aya garinta,
kwakwa ma kiyi garinta, dabino ma kiyi garinsa,
sai ki dinga diban cokali bibbiyu ki zuba amadarar
ruwa sannan ki zuba zumarki mai kyau kisha, sai
ki samu kuma gwanda, kankana, abarba, zogale,
citta, lemun tsami, ki markada su kisha. In anan
maki katsaya yarinya zakiji ki kin cika cindum
daruwan ni'ima sai kin samu martaba ta
musamman agurin miji dan zaijiki kin fita daban
da dukkan sauran mata. Ki hada da biyayya
tsafta da kuma iya tsara girki mai dadi. Ummi
tace, toni yanzun yaya zanyi nasamu saiwoyin
nan? Tace, bari zanba matar ado dake yawan
zuwa kasuwar qauye zata zo miki dasu. Amma
su gwanda gasu nan bakin titi ko shi sai kice ya
siyo miki, zogale kuwa baki rasa shi gurin
ummarki, har da cittar da alif din da bagaruwan.
Ta ce to, ta tafi gurin umma ta amsa har taje
gida bata daina mamakin tsohuwa ba, ya akayi
tasan duk wadannan hadin matan? Amma data
tuna cewa 'yar katsina ce sai tace ba mamaki.
Tun ranar alhamis din ta soma aiwatar da
darussan da ta debo daga tsohuwa, safiyar
jumma'a ranar zai bar dakin bishira. Ya fito tana
sharar tsakar gida ta gaidashi, ya amsa da fara'a,
tare dawani kallo mai fassarar in ba keba. Cikin
muryar data adana don shi kadai tace, ya abba
ina son in je ayi min zanen fulawa. Yace jiya kin
fita yau kam a'a. amma ki aika akira mai zanen
tazo ta miki. Ta marairaice, towa zan aika yaya
abba? Yace aike ni, ina ne gidan? Tace layin su
umma ne yace to za'azo ai miki. Bishira tafito
daga daki tazabga ma ummi harara, Tare dacewa
kisisina. Abba yakalleta, kema sai tayi miki. Tace
bana bukata, aikin banza, shikam yafice. Ummi
kuwa tace gaba da aikinta, ita ko sai tasa kujera
tazauna tana sakin zantuka, eh don kwalliyar
tabanzanta tunda ba a iya biyawa miji bukata.
Allah dai yasa ya fada min komai, to ni me zai
dame ni don 'yar aiki kawai na dauki yarinya.
Tashare min gida, tayi wa mijina abinci, daga nan
fa? Saita saki shewa, ummi ta ce aranta yau zan
bambance miki. Birabiskon shinkafa tayi da miya,
ta wadata birabiskon da kayan lambu, miyar ta
dauki nama da bushasshen kifi. Sannan ta hada
musu kunun aya yaji dabino da madara, ta
aikawa ummanta lokacin da kamal yazo daukar
na ummarsu. Tasheka wanka taci doguwar rigar
shadda koriya mai duhu, ta kafe dauri tamkar yau
ne daurin aurensu. Ga fulawar da yaje ya biya
akazo aka zana mata. Tanajin rigimar muhibba
tafito tazuba mata adan kwano tazaunar da ita
akofar falon mamanta.bishira tafito kicin baki
tasaki tana kallon ummi da tazo wucewa harda
bangazar ummi, nan ko kamshi ya bude ta na
turarukan da ummi ta fesa. Abba yana yin
sallama ummi tafito da sauri, oyoyo yayana,
bishira tana daga kicin dinta tana kallon su.
Ummi ta rungume shi, sannu dazuwa sahibina.
Ta amshi ledar hannunshi dajakar, yace yauwa
sannu babyna tace inazan kai ledar? Yace akwai
ta bishira aciki ki ciro. Ta mika mishi ledar ta
wuce dajakar dakinta. Ya mika wa bishira lemo
da abarba da yayo musu tsaraba sannan ya wuce
danasu, awulakance ta aje. Yana shiga ummi
tadan karo kofar yanda bishiran zata iya lekensu
sosai ta gefen kofan. Ta cire masa hula ta aje
akan madubi sannan ta kunna fanka. Ta shirya
masa abinci, yauni zan baka har ka qoshi. Haka
suka yita baiwa juna abaki har suka qoshi.
Yakamo hannunta mai qunshi yana ta sumbata,
wai kamar kada su goge. Kumatun shi ta shafa
nima yau kamin kyau, koda yake dama kai me
kyaune, ina sonka ya abba sosai. Cikin jin dadi
ya mannota a jikinshi, nima ina sonki, ina manta
kowa da komai in muna tare, tace ina tsoron kada
wata rana ka juya min baya. Ya saqalo
hunnuwansa cikin nata ina fata in mutu kafin
lokacin. Ummi tasomayi masa wasu irin darussa
wadanda tasan yana saurin tada sha'awarshi
nanda nan kuwa tasa shi fita hayyacinsa yakama
surutai. Ummi ta tabbata bishira tana wurin ta
labe, don haka tai murmushi ta bishi suka tafi
duniyar ma'aurata. Bishira tamkar tayi hauka sai
kawai ta fado dakin tana fadin, maciya amana,
har yanzun ba afita daga lokacin girkina ba
munafiki. Abba ya tashi sannan yaja riga yasaka,
ok dama kina labewa ne kiji sirrinmu? Da taga ya
sauko da zafin rai saita gudu dakinta. Yabita
yamata tatas, kuma ya fada mata cewa tazo ta
shiga dakin ta zauna ba labe ba, yanzun zai
komane yaci gaba daga inda ya tsaya. Tayi ta
kuka gashi ba damar zuwa gurin umman bashir
dole ta tafi gidansu. Shi kam abba shareta ya yi
kosu umma bai fadawa ba. Sabuwar soyayya ma
ya balle agidan, su ci abinci tare, wanka tare, su
fita yawonsu a qafa ko amota. In yana gurin aiki
bini- bini ya kira waya, ita kuma ko yaushe cikin
kirkirar girki da kwalliya tare da dadadan kalaman
dazata fada masa take. Duk lokacin datayi masa
zancen bishira sai ya ce, don Allah ta bar ta ta
huta, ummanshi kuwa 'yar bin qwaqqwafi sai da
tabi ta gano bishira bata nan. Don haka koda ya
shiga gaisheta sai tace kada ya yarda yaje yama
bata takardarta. Ita ko tana can uwarta tace ma
mahaifinta abba sakinta yayi, shi kuma yace to
sai tazauna tunda zaman gidan take so. Amma
su sani daga abinci sai ruwan gidanshi ya amince
tayi amfani dasu sai ko gurin kwana, amma bnda
wannan ko makilin dinshi ta taba bai yafe mata
ba, wannan hukunci yayi musu tsauri. Ko wata
bata rufa ba taji gidan ya isheta don hajiya zainu
taso maidata makaranta amma yace tagama
boko. Bishira na zaune ta zuba tagumi hajiya
zainu ta shigo dakiki tace tagumin menene kuma?
Tace, su sumayyah ne wai nace suyi ma muhibba
wanka sukace Allah yakiyaye. Wai tunda nazo
dakinsu ya lalace da kazanta, hajiya zainu tace
aiba karya suka yiba, don haka ma maida
yarinyar nan za ayi ke kuma ki koma gidan
antynku ko ki tafi abuja gidan aisha. Tace
baxanje gidan aisha ba, don itama bama shiri,
gara gidan antyn amma gsky ni abarmin 'yata
kuma fakinsan bai sakeni ba. Tace, inda ubanki
yasan ba saki bne da tuni bai kora kiba? Don
haka mubarshi haka amma batun 'ya nice zan
maidata.

Please Login or Register in order to submit comment