Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lkc yayi xai fara shiri
yi. sannan ya iya sadaka dan dasunje yana bashi
kudi ya rabama almajirai ko yasa a asusun
masallaci. sai xumunci aduk lkcn da ahj babba
xashi xanfara yana tafiya da shi. ya tashi da san
iyayan shi matuqa bai taba sanin basu suka haife
shi ba. duk da cewan duk lkc da ya shiga gidansu
umman bashi takan cemai bafa umman kace ta
haifeka ba, nice na haifeka. riqonka muka basu. in
yaji haka sai yace allah kiyaye. sai ya baro gidan
ita kuma taita xakinsa. inya fadama umman shi
saitai murmushi ta rungume shi. ya ce aidai kece
ummata ko? ita kuma tace nice ummanka rabuda
ita kaji. abba yanada tausayi dan haka ya
taimaka ma ummanshi aikin gida. shekara sha
biyu ya sauke kur'ani.a lkcn ne ya gama pry ya
samu xuwa js1 Abba makarantan masu kudi ya
ke yi.ita kuma sahura duk yaranta ta batasu,
musamman bashir. duk lkcn da akace yaje
makaranta inyace ya gaji, saitace ya xauna kaje
gobe. ko ahj babba ya korashi sai dai ya labe
inya tafi shi kuma ya dawo. yafi san xuwa qwallo
ko shagon game. to hakama qannansa duk sun
dau irin tarbiyyan uwarsu. cikin haka wata ran
umman abba ta tashi da matsananciyan mura,
lkcn ahj babba yaje legos don taho da kaya. ahj
qarami ne yakaita asibiti bayan gwaje gwaje, an
gano ciki wata biyu da yan kwanaki. murna gun
ahj qarami tamkar yayi tsuntsuwa yaaje ikko ya
fadama ahj babba. suna isowa ya shiga gun
tsohuwa ya sanar da ita. nan take tasa kukan
murna.ita kuwa suwaiba tamkar mafarki, sai
kunya ta isheta. lkcn da ahj qarami ya fadama
sahura, sai cewa tayi um, bana an tabuka, ni dai
gani da cikin na shida amma sai yauxu ta samu
daya. ahj qarami yace kinji matsalanki, ke ba dai
kiji wani ya samu qaruwa ki taya shi murna ba,
sai dai baqin ciki. ta ja tsaki bakin cikin me
xanyi? tunda ni ga nawan. ciki mai laulayi
suwaiba ta samu, wanda duk abin da taci sai ya
dawo. wannan lamari ya daga ma ahj babba
hankali da abba, duk aikin gidan abba ke yi, ga
makaranta, ko an hanashi sai yayi.dan haka aka
dauko harira qanwar suwaiba, wanda mijinta ya
mutu. umman abba dai bata samu kanta ba saida
cikin yayi wata biyar. sannan ta samu sauki.lkcn
sahura tanada cikin wata bakwai, lkcn haihuwa ta
haifa mace, murna gurinta kamarme, dan sai
yanxu ta samu mace. safiyar talata umma ta
tashi da naquda, hankalin ahj da abba ya tashi
matuqa. duk da tsohuwa tana ta kwantar masu
da hankali, ranan abba ko makaranta bai jeba,
duk da san makarantansa, har suka dawo sallan
axahar shuru. ahj babba yace tsohuwa bari na
samo mota akaita asibiti. tace to. yana fita ba
jimawa ta haihu. ta santalo yarta mace mai
matuqan kama da ahj babba. tsohuwa tace da
abba,mai sunan mlm bi su ahj kace sudawo ta
haihu. dama harira tasa ruwan wanka lkcn da
suka xo ta fito daga wanka.nan aka wanke
yarinya yan barka sai xuwa suke amma sahura
saida aka. Sahura saida aka kwana sannan ta
shigo. ta dauki yar ta taba baki tace wannan yar
baqinqirin haka sai idanu daqwa daqwa. wata
mata da taxo barka tace ai wannan yar sak
abba,suna kama sosai. sahura ko kunya ta ce
basa wani kama da abba. da tasamu kyan abba
da tayi kyau, umma tayi ma matan alama da
haunu tai shuru. ranan suna taci sunan tsohuwa,
wato habiba, dan haka umma ke ce mata ummi.
abba yana ji da ita, saidai in yanasan tsoka nanta
sai yace dubeta ta ba ummata wahala, sai na
xaneki kika girma kika qi mata aiki. umma taita
masu dariya. tsohuwa ma naji da ita dan guta
take wuni. tunda ga kan ummi umma bata qara
haihuwa ba. abba yana aji uku suna qoqarin xana
(j.s.c.e)ya dage sai ahj ya saka shi shagon dinki.
ahj yace abba kabar batun dinkinnan ka tsaya a
karatunka. yace ahj nidai ina so kaga inna iya su
umma sun huta dakai dinkin su gidan laminde.
umma tace ka barshi yayi ahj sana an hannu ai
tanada dadi, kaga in ya gama bokon ba bai samu
aiki ba xaya riqe kanshi da sana anshi. ahj yace
to shi ke nan Ahj yace, to shi kenan, wane shago
ka ke san shiga inkai ka? yace, na can bakin titin
nan, in da kake saya na lemo. ahj yace shi kenan.
mafarin shigar abba gurin koyan sanaa kenan.
ummi ta taso da rigima, tsiwa tare da tsokana,
wanda yasa suka daina shiri da abba sam. abba
ne ya kaita makarantan boka da islamiya, kullum
yaje daukota sai ya raba fada ko ya bada hakuri.
umma kullum addua take fili da xuciya da lokutan
sallah, allah ya shirya mata ummi. ita kuma tata
kalan quruci yan kenan inta girma xata daina.
tsohuwa takance aini me sunana kingama min
komai, domin banasan ragon da, da in kai qara
gara akawo min na bada haquri. duk lkcn da tayi
wannan kalman sai sunyi fada da abba, dan cewa
yake ai dama tsohuwan nan tuni na ane kin daure
mata gindin ta siqa tsokanan yayan mutane. ita
fa mace ce ba namiji ba, shi kenan bata da aiki
sai dambe? tsohuwa takance batta tayi. tunda
ganan abba basa shiri da tsohuwa. ita kuma fati
yar sahura kamar ummace ta haifeta dan bata da
hayani. ummi kuma kamar sahura ta haife ta.
Wata rana abba ya ke cewa, umma da ace lkc
daya kuka haihu da umman bashir, allah cewa
xanyi kunyi canjin yaya. umma ta dube shi dan
me kace haka? yace sbd masifar ummi irinna
umman bashir ne, fati kuma ba ruwanta kamar
ke.dariya kawai take yi. kwanci tashi ummi ta
gama pry, lkcn abba yana shekaranshi ta qarshe
a jamia. yana karantan (mass comm)ne dan yana
san xama dan jarida. umma tasoshi da likita
amma yace baida raayi. tace kaga kai bakada
hayaniya abba aikin jarida na masu maganane.
yayi murmushi yace umma kenan. ummi ta samu
shiga aji daya a qaramar sakandare. maimakon
hankali abin nata sai gaba yakeyi. aduk lkcn da
tai laifi abba ya daketa sai tayi wani abun dan
tabashi haushi, da sunan ta rama. ahj babba ya
bude mai shago, tare da xuba mishi kekuna.
tsohuwa tace dakai wanine mai sunan mlm, saika
tafi da takwarana ta koya. abba yace ko a
kwafan shago na na ganta ba sai na karya mata
qafa ba. ummi ta murguda baki, sai daya tafi
sannan tace allah ya kiyaye inje wannan qaxamin
shagon nashi. Tsohuwa ta ce,"tafi can kema da
baki son ci gaba, in banda abinki da zaki kwantar
dakai ki koya in an tashi auranki basai a saya
miki keken ba. in kuma shi kika aura kinga
shikenan inya samo dinkin da yawa saiki taya
shi, ta ce"Allah ya kiyaye me xanyi da yaya
Abba,yayi ta cin xalina?ni bana son shi" Umma
dake gefe tana jinsu ta ce,"ke in kin samu kamar
Abban ma ai kinji dadi,shine zai ce mai zaiyi
dake? mara hali irinki." Ummi dai tayi shiru tasan
inta cika surutu kan Abba yanxun nan umma ta
doddoketa,umma tafi son Abba fiye da ita. watan
ramadan ya tsaya,duk daukacin musulmi sun
dauki azumi ranar da akai na uku Abba ya shigo
gida karfe daya saura. daga shago yake zaiyi
wanka yaje makaranta don yanada darasi karfen
biyun rana. Gidan shiru kowa na bacci,don haka
bai shiga dakin umman shi ba don baya son ya
tasheta ya shige bandaki. Da ya gama ya fito ya
nufi daki kamar ance ya kalli madafi, ummi ce
tsugunne tana cin abinci. ya tsaya yana kallonta,
dagowan da xatayi suka hada ido, yace ke! karya
axumin kika yi? ta toshe bakinta sannan nace
dan allah yaya kayi haquri. yace fito muje. ya
kaita dakinshi yasata gwale gwale. da xashi
masallaci ya kulleta ta baya. ya ce inyaso ki
tashi kafin na dawo, xan gane. yana fita tahau
binci ken abinda xata lalata mashi. ta ciro bidiyon
da yake kallo xata doka da qasa, sai taga kwalin
wani kaset tana kallon hoton jikin kwali, na
tsiraici ne. ta xare ido kicin mamaki, tace lalle
yaya abba, daman shi dan iskane? to kuwa xan
tona mai asiri. ta turashi cikin xaninta, da taji
motsin shi yana bude qofa sai ta koma inda take.
ya shigo ya kalle ta ya ce nasan kin xauna dan
kinga bananan. ya xauna bakin katifa, sannan ya
dubeta fuska daure. ummi meyasa kika karya
axumi? tace ba komai. yace tunda aka fara axumi
kike karyawa ko? tace yaune kawai yaya abba.
yace kinsan hukuncin wanda ya kasya axumi da
gangan. Tace eh an fada mana a islamiya, amma
mlm yace sai wadanda axumi ya wajaba akan su.
ya kalle ta cike da mama ki, a xuciyanshi yana
cewa, yanxu har yarinyan nan tasan akwai
wadanda axumi ya wajaba akansu? afili kuma
yace lalle ummi kina buqatan sa ido. dama
saboda bai wajaba akanki ba shiyasa kika karya?
to daga yau xansa maki ido, kuma xan fadama
umma ta sa maki ido. hakanan duk wani abu da
akeyi lkcn axumi an daina qyale ki, xaki ringa
sallar tarawi, ke har tahajjud sai kinyi shi. sannan
bayan axumi saikin rama wannan axumin. ya
xuba mata ranqwashi a tsakiyan kanta ,tare da
cewa tashi ki fita munafuka. daga dakinshi bayi
ta shige ta qara kallon kwalin, sannan ta maida
ta soke shi, tace sai na tona maka asiri. da dare
bayan angama bude baki, abba xai tafi tarawi ya
shigo dakin umma yace ina ummi? umma tace
gatanan kan kujera tayi sharkaf, wai yau taji
axumi. abba ya shiga ciki yana kallanta. yace
umma xaki yaudara ko yar rainin wayau, tafa
karya axumi daxu da rana na ganta tana cin
shinkafa. Yace shine kika xube wai ke kin sha
wuyan axumi ko? umma ta dube ta tana mamaki,
tace abincin da kike kinba almajirai da ma qarya
ne? ya dubeta yace biyu kenan ga larya axumi ga
qarya, xaki sani. tashi muje salla ko in ballaki.
umma tace allah ya shiryi halinki. abba yayi
dariya tare da cewa, kema dai umma yaxaki
amince da batun wai tac almajirai abinci, su basa
axumi ne, umma tace tunanin haka sam bai xo
min ba. saida ya sakata sahun salla, sannan ya
nufi gun maxa. bayan ya gargadeta da cewa in an
idar ta jira shi, inyaxo batanan sai ta sani. koda
aka idar da yaxo bata nan gurin ya kaure da
dambe da wata yarinya wai da suna sallah tana
bigeta. shine daga idarwa ta cakume yarinyan da
fada. bai tsaya sauraranta ba ya cire ta kalmi ya
shiga dukanta, sannan ya tasata xuwa gida. sai
da ta shige dakin tsohuwa sanna ya koma nashi
dakin. hakanan suka ta xuwa masallaci har
axumi yakai ashirin. Ahj ya kawo masu shadda
da leshi da atamfa na sallah ita da umman su
bashir da fati. ya suya masu takalma da mayafai,
abbane xai masu dinki, ran ummi baya son dinkin
abba, domin wanda take so bashi yake mata ba.
ta ce umma dan allah nidai a bani dinkina na
kaima laminde, yaya abba baya min ne kyau.
umma tace kije ki karbo da kanki. tace ai baxai
bani ba ne, xai dakeni. umma tace ai nafi san ya
dake kin, lamindan finshi dinki mai kyau tayi ne?
ummi tace nidai gara ita. tsohuwa tace ai banga
lkcn da mai sunan mlm xai faranta ma takwara
ba, kullun burinshi ya quntata mata. umma tace
tsohuwa ummi fa ba a mata gwaninta, inace dinki
in yayi mata har aro ake xuwa yi? ta dube ta
tace keda shine inya jiki kyayi biyu babu, yaqi
maki dinkin luma ya hana kayan bare kiba
laminde inga ta tsiya. qarfe dayan dare ya tura
dakin tsohuwa tana xaune a kan sallaya tana
addua, abba yayi murmushi. tsohuwannan kina
birgeni dama kina ibadan dare? ya kalla kan
gadonta, ummi taya dai dai tana ta bacci./ ZURFIN CIKI book 1 part 3 ZURFIN CIKI book 1 part 3 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:42 Ya kalla kan gadonta, ummi taya dai dai tana ta bacci. Yace, ummi ke! ummi!! tashi. tsohuwa tana yi masa alama da hannu gami da gyaran murya, wai ya bar ummi maimakon haka ma sai ya dauki wani kofi nan gefansa da guntun ruwa a ciki ya watsa mata a fuska. ta farka firgigit, yace taso, da sauri ta tashi yace dauko hija binki maxa. ta dauka suna fita tsohuwa tana sallamewa. tace kai mai sunan mlm ka lafama yarinyan nan haka, wai axumi wajaba akanta yayi da xaka tasheta da tsohon darannan xuwa masallaci? yace kema in xaki, xo muje. ya tasata suna tafiya tana hada hanya suka tafi tahajjud. sai qarfe hudu na asuba aka tashi. ummi har kuka tayi saboda tsananinjin bacci, amma tana tsoran kar ta kama bacci yaxo ya same ta. tun tana layin bacci har ta gyagije. sakamakon tashinta da matan kusa da ita keyi. kafin kwana uku ta saba da sallan dare, lkc nayi xata farka. abba yana xaune ga dinki gabanshi amma yana can tunanin bushira, yarinyan da yake matuqan so ce. amma yana shakkan fada mata,dan iyayanta sunada kudu matuqa. kuma shine yakema duk yan gidansu dinki. Ahmad abokinshi da ke gefe kuma sai yayi murmushi, yasan tunanin bushiqa ne ke damun sa, dan haka sai ya ce, abba kasan allah, abari ya huce shi ke kawo raban wani. haka kuma ZURFIN KICI, ba xai kai ka gaci ba. ka fada mata kawai. abba ya ce hum ,ina tsoron kada ta ce bata sona, dan bansan ina xansa raina ba. ahmad yace daga ganin yadda take jin kunyanka tana sanka. abba ya kalli ledan da ke dauke da dunkunan su bushiran, yace ina xatan yau xasuxo amsan kayansu, dan tun jiya nace suxo.ahmad yace to in sunxo kayi qoqari ka fada mata mana, indai ba ragon namiji kake ba. abba ya tsurama qasa ido yana tunanin in sunxo mai ce mata? kusan awa biyu sukaje sukai sallan axahar, tungan motan ta tsaya yasan tasu bushurane. shi kadaine a shagon sauran basu dawo ba. bushura ta shigo da qannansu da yarsu aisha. ya taresu da faraa, suka gaisa kan bushura na qasa, sam bata iya kallan abba tela kamar yadda suke kiranshi. Ya tura masu kayansu suka duba sunata murna dan ya masu wadda sukeso. aisha ta aje masa cikon kudinsa kan table. har sun fita yagadai baxai iya hakuri ba, yace bushura xo gashi. ta juyo tana dariya taxo. yace bushura inasan na fada maki wata magana gashi kuna sauri ko? ta kalli motan tace fada min. yace kina sona? ta xare ido sannan ta ruga da gudu. gabanshi na faduwa, bata tsaya ba sai mota. ya kwantan da kanshi akan keken yace menene maanan gudun da yarinyannan tayi? ya tambayi kansa, qarfe uku sunada lecture, amma baya xatan xashi makarantan. ahmad ya dubi abba wanda daga ka dube shi xakasan yana kin damuwa. yace wai banaga sunxo ba? ko ba motan su bane? shiya bandawo ba nakuma hana yaran dawowa dan ku sasanta. abba yace um, inaga yarinyannan gara na haqura, dan bana san insa kaina cikin tunani. ahmad yace ban gane ba, abba yace, to naga daga tambaya tana sona, saita kwasa da gudu ta shige mota. ahmad yayi yar dariya sannan yace ,amsan ta baka. tana nufin tana sonka. abba ya harare shi kada ka maidani dan iska, ina ta magana ta xabga da gudune shine tana sona? yace jeka tambayi manya .yaci gaba da cewa kaine baka mata magana da hikimaba, ka fito mata kai tsaye baka sakaya ba. abba yace, kai nifa ka sanni ba ruwana da wata kwana kwana, idan abu yayi min bana kwana, inko bai min bama haka, ni ba ruwana. Ahmad yace sai xurfin kici ko? da ya aka shawo kanka ka fada mata,abba ya mike tare da kallan agogo, yace inada lecture. gida ya nufa dan shirin xuwa makaranta, har yayi kamar ya tambayi ummanshi cewa in ka ce ma mace kana sonta taji kunya ta gudu wai alamun so ne? sai kuma ya kasa, yana jin nauyi amma in bai samu wata manufa ba dole yaxo ya tanbaye ta dan baya boye mata komai.bushura yar ahj sale ce kwamishinan gona na wannan xamani, gidansu yana karkasara. danqareran gida ne ginin xamani, sun san abba ne sanadin dinki da yayi wa wata qawansu jamila.dinkin yayi matuqan birge su dan haka suka fara kawo masa dinki, tun ranan da ya fara ganin su bushura ta kwanta mashi a rai. to ashe ita ma yamata.shiyasa yau daya furta mata take ganin kamar anmata gafara da aljanna.wata xuciyar tace ,to yanxu da kika gudu in ya xaci baki sansane fa, nan take hankalinta ya tashi har tana rayawa ga abba can da wata.dan haka taga dolene ta koma gun sa inhar tana sansa. dan tasha ganin mata na masa tayin kansu in sunxo kawo dinki.nan ta soma tunanin wace dabara ce xatayi ta fita?saiko ta warware daya siket din kayanta cikin dare.da safe ta nunama momynsu tace mata telan ya manta bai hada wannanba,dama yace xai gwada nine kafin ya hada.momy tace direba ne xai kai mashi.bushura tace momx xaifa gwadani ne muje dai xa kaini.tace to kuje, bushura ta danyi gayunta suka tafi.saidai kash! bata samu abba ba ance mata yana gida. tace gidan da nisane, aka ce mata babu nisa,dan haka ta sa aka rakata.tacema direbansu tana xuwa telan na gida.gidan ba nisa. A qofar gidan su abba ta tsaya, sai ga ummi ta sheqo da gudu tana dawowa daga aike.ta tsaya tana kallan bushura, sannan tace lafiya?bushura ta dubeta. yauwa abba yana nan?budan bakin ummi sai tace yaje kashi ya fada a masai.bushura ta dafe qirji, yaushe? ummi tace oho.sai ga abba ya futo sanye cikin shadda bulu mai duhu yana ta qamshin turare.shawara ya yanke lkcn da yake xaune a shago kan cewa yaje gidan su bushura,tunda gidan kwamishina ba boyayye bane,suka hada ido da bushura,ta saki faraa sannan ta dubi ummi,kince ya fada ina? ummi tayi ciki da gudu.ya bita da kallo sannan ya kalla bishira,me tace maki?bishira tace, ba komai.saidai dariya da maganan ummin tabata.yace tunda baxaki fada min ba xomuje ki gaida ummana.cikin muryan jan hankali tace ina jin kunya.ta bude jakanta tace kamanta baka dinke wannan siket dinba.yace mugani,yaga yadda aka warware shi aka cire xaran da kyau. murmushi yayi dan yasan ya dinka siket din,kusan shinema na farkon dinki.ya gane yaran nata qila san ganinshi take san yi. Ya dinke siket din yana cewa"to amma sai dai ayi min izini inzo gida in kawo da kaina in na gama." tace haba dai,ya za ayi in taso ka?"ya ce,"ba komai,in dai anyi min izini sai inzo," ta ce,"to in maka kwatance?" ya ce,"a'a huta kada ki bata bakinki,nasan gidanku zanzo anjima bayan tarawih." ta ce,"to." sai mun zo" tace"ku dawa? ya ce,"abokina mana,kinga zo muje gurin ummana ku gaisa." Bishira ta bishi cikin jin kunya.tun kafin su shigo daman ummi ta shiga gurin umman da gudu tace mata"umma ga budurwar yaya Abba." Umma tace budurwa kuma? tace eh ai zama su shigo.daga nan ta kara kyallawa dakin tsohuwa tana fada mata. Umma dai jim tayi dan bata da wani burin da ya wuce ta baiwa Abba ummi,kuma da tasan har zai ga wata can da wuri haka data fada masa kudurinta,sa tay 'ZURFIN CIKI' gami da nauyin baki....... sallamar Abba ce ta katse ta ta ce,"shigo Abba." ya ce Umma bakuwa ce taxo gaisheki.Umma ta fadada fara'arta tace to shigo,ba dai surukar tawa bace?" ya ce,"ai ita ce kam" Bishira ta shigo tana sunne kai,ta gaida umma Umma ta ce,"masha Allah,Allah yasa rabon muce."Abba yana dariya ya ce,amin ummana."ya dubeta,"tashi ki gaida kakata." suka nufi dakin tsohuwa,umma ta jinjina kai .tabbas Abba nason yarinyar,in ta dubi yanda yake fara'a da zumudi. a fili ta ce,"Allah yayi mana zabin alkairi."ummi na kwance kanta na cinyar tsohuwa,sai ta kalli bishira ta tuntsure da dariya,lokacin da suke gaisawa da tsohuwa. Abba ya ce,"dariyar uban me kike yi?" sai ko ummi ta sake shekewa da dariya. ya nufota ya suri kafafunta,tsohuwa ta ce haba mai sunan malam yanxu in bata yi dariya ba kuka zatayi?" ya ce,Bishira tashi muje" Tsohuwa tace to yanmata mun gode ki gaida magabatan naki,sannan kiyi ta hakuri da halin wannan miskilin." Umma ta ce,"tsohuwa kodai kishi ne?suka yi sallama,ummi wadda tunda ya shureta ta rigasu fita sai ta dauki takalmi Bishiran guda daya takai soro (zaure). don haka da suka fito suka shiga nema ummi ta kule uwar dakin umma tana ta dariya tana lekensu. Abba ya ce,"ummi! ummi!!" taki amsawa ya nufi waje da niyar dubota don yasan ita ce zata dauki takalmin,sai ga takalmi a kofar shi. Don haka ya dauko kawai ya dawo ya bata umma ta ce,"ka kaita su gaisa da umman Bashir." Abba ya ce,"a'a ba yau ba."ya rakata wurin direbansu,kusa da shagonshi sukayi sallama da alkawarin zai zo washegari. yaje kuma bishira ta fada masa lallai tana sonsa sai dai tana tunanin iyayenta ko zasu amince? ya ce,to shi dai zai turo magabatansa su nemar masa izinin zuwa zance kamar yanda yake a shari'a Bishira tace a'a ya bari tunda yanxu shekarar farko take a babbar sakandare(s.s.1)ba za a bari ya dinga zuwa ba,amma zasu dinga haduwa gidan yarta dake na'ibawa. Abba baida zabin da ya wuce ya yarda da hakan tunda tace baza a barta yin tadin ba.sai dai fargabar shi kada nan gaba sunyi zurfi cikin soyayya ace ba za'a bashi ba. ta ce,"Babana bashi da matsala,amma momy dinmu ce abin tunani."Abba ya ce,"shikenan Allah ya shige mana gaba." soyayya ce mai karfi ta kullu tsakanin Abba da bishira,wanda har ummanshi da kanta tasan cewa Abba yana son yarinyar. Domin duk lokacin da zaije gurinta tana lura da zumudin da yakeyi,kazalikain tace ka gaida surukar tawa, bakinsa baya rufuwa. Don haka sai ta tattara batun ummi ta aje a gefe addu'a ce kadai bata daina ba.ana sauran kwana uku sallah.Abba ya siyo fenti yazo da mai fentin nana ak fente gidansu ciki da bai. Da yamma kuma ya kawo dinkunan su ummi da fati,ummi tasa ihu,sam irin dinkin da ta aro gurin kawarta Amina ba shi yayi mata ba,ya zai mata dink iri daya da fati? ya ce,"kin isa ki sani in miki dinkin da kike so?ta ce to ni dai bazan sa ba umma ta rafka salati tana kallon ummi ta ce,"ummi kina da hankali kuwa? kudi kika biya ko ko Abban sa'anki ne?" tace cikin kuka to ni umma ya zai min iri daya da fati? ya dubeta a fusace,"in kin bari na dauki kayannan wallahi bazaki sasu ba." Umma ta ce,"ni da zaka daukesu ma da naso"tsohuwa ta fito ta ce,"saboda me? akan wane dalili zaka amsar mata kaya?tunda baka mata wanda take so ba sai ka kyaleta." Da hannu Umma tayi mishi alamar yayi shiru,sannan ya fita waje.Abba ya kada kai ya fita. washe gari kuma ya shiga da me fenti har cikin gidan Alhaji karami,sahura tana daki lokacin da yake nuna ma mai fenti guraren da zaya fara. Ta fito daga daki ganin Abba sai ta hade rai sannan ta ce,"mune kashin baya? ai dama ka bar shi tunda baka mai da mu wani abu ba,mu ne dai baka so din mahaifanka. Ta dalilinmu zaka shiga aljanna,ba dalilin wasu banzaye ba da sauri ya nufi hanyar fita waje don baya son yaji zagin da zata yiwa Alhaji da Ummanshi. wannan na cikin dalilin dayasa baya son zuwa gidan Alhaji Babba da Umma,sune suka ci kashi da fitsarinsa. suka bashi tarbiya da ilmi,suka ci da shi suka shayar dashi.amma sam basa yi masa abinda umman Bashir ke masa. haihuwarsa ce kadai su Alhaji babba basu yi ba,sahura tana zuwa har shago tayi masa rashin mutunci,sannan ta ce ya bata kudi,ta ce ya ba bashir kudi ko ta aiko fati. Bai taba kin bata ba,amma duk da haka bai tsira daga zagin rashin mutunci ba.ta ce ya tare a gidan ummanshi komai nashike mata,wai da kuma sam ba haka bane. Umma bata taba tambayar shi sisi ba,haka nana duk lokacin da ya bata wani abu ko ya sai mata,sai tace ina na umman Bashir? kaje itama ka bata,in ko bashi da yawa ni naci girma ka bata. Ranar sallar idi kuwa ummi koda tayi wanka kin saka sabon kayanta tayi sai na bara. Lokacin da zasuje sallar idi,Abba ya fito daga wanka ya kalleta ina kayanki sabo? ta tura baki"ni baxan sa ba." Yace,"to zanga wanda zaki bi masallacin,kuma ki kara magana saina fasa bakinki."sai ta wuce kofar dakin tsohuwa,sannan ta ce,"to ai dai nima nasan hanya,kuma sai naje."ta fada dakin da gudu. ya bita bata san yaga tsohuwa lokacin da ta shiga wanka ba,bayan fitowarsa.don haka ya ritsa ta ya kwakkwada mata mari,sannan ya rike mata kunne. zan kara fada ki fada? ta ce,"a'a kayi hakuri." ya saketa ya wuce,ta zauna tana kuka. misalin karfe hudu na rana ,bishira ta iso shagon dinkin ita da direba,shagon a rufe.don haka ta ce su karasa gidan. Can dinma baya nan,amma sai ta fito ta shigj gidan dauke da tire babba cike da kuloli. cikin kunya ta gaida umma,ta kuma bada a aje masa.umma ta ce,"to ko ina Abba yayi? kila gidan su Ahmad yaje."umma ta ce,"ke uwar gudu ina yayanki?"

Please Login or Register in order to submit comment