Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a ransh yace"ko dai ita ne?bari ta farfado in tambayeta"


Abu kamar wasa anyi kwana uku ba gan minal,cikin kwana uku nan Abdul ya rame yayi baki,umma minal ko kullum cikin kuka

IKLAS ko tashiga tashin hankali sosai,Mahmud yace"laifi nane dana bari ta je dan yanzu sun bala'in shakuwa da zaliha

Yau likita ya sallami IKLAS a asibiti suka dawo gida

'Bangaren sultan ko misallin karfe 4:pm tana zaune a kujera minal ta farka

Tana farkawa tace.....









Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

πŸ…Ώ7⃣5⃣&7⃣6⃣

Bismillahi Rahmanir Rahim

Minal na farfadowa ta fara kallon wuri,sultan ma kallonta yake

Tace"ina nike?"

Yace"a gefen titi na gan ki a sume,na kawo ki asibiti yau kwanan ki uku"

Zaro ido tayi a hankali ta fara tuna komai da ya faru

Yace"bari in kira likita"

Likita na zuwa ya duba ta allura yayi mata ya fita

Kallonta sultan yayi yace"ki kira gida a san halin da kike ciki"

Tace"ba waya hanun na"

Yace"kin san noba wani a kanki?"

Tace"eh"waya ya ciro yace"kira inji"

Nan ta fara kiran noban Abdul,yana dialling ya ga sunan Abdul ya fito kallonta yayi

Yace"minal ko?"

Cikin mamaki tace"eh ya akayi kasan suna na ne?"

Yace"ai ni cousin brother Abdul ne bikin Ku ma zani na gan ki,nine Wanda kawaye ke jira"

Tace"sultan ko"

Cigaba yayi da kiran Abdul amma yaki d'agawa

Abdul da ke kwance ba lafiya ya duba wayar yana ganin sunan sultan yace"wanan sarkin surutu,zai dame ni"

Sultan yace"bai d'aga ba"

Tace"toh kira wanan,kiran noba ummata tayi sai dai shima har ya katse bata d'auka ba"

Yace"shima ba a d'aga ba"

Na IKLAS ta bashi amma noban be je ba"

Tace"please kira wanan na karshen inba sai in hakura"

Islam dake zaune kusa da IKLAS tun dawowan su daga hospital IKLAS ke kuka tana kiran sunan minal Islam itama zaliha kuka takeyi tana cewa"laifi nane"

Islam zatayi magana wayarta yayi kara tana d'agawa sultan yayi ajiyar zuciya

Tace"hello!"jire wayar yayi a kunne ya kalla ya kuma maidaw

Yace"hello"itako Islam sanda ta dafe kirjin ta dan wani bugu zuciyarta ya farayi da Sauri

Mikawa minal wayar yayi dan haka kawai yaji baya da kuzarin magana da ita

Minal tace"hello"Islam na jin muryarta ta mike tsaye tace"minal dama kina raye?"

IKLAS na jin an kira sunan minal ta kwace wayar batayi magana ba ta saki kuka


Minal tace"meya same ki sunyi miki wani abune"

IKLAS tace"please karki kara tafiya ki barni nayi kewar ki,Abdul kamar zaiyi hauka yanzu ma fushi yake da kowa"

Minal ma hawayen takeyi tace"ku zo ku d'auke ni ina asibiti"

Da sauri IKLAS ta saka hijabi Islam tace"ina zaki ke da baki da lafiya"

Kafin tayi magana RAYHAN ya sauko yace"meke faruwa ne?kuma ina zaki?"

Tace"minal ta kira wai tana asibiti"

Yace"alhamdullilah bari inki kira Abdul mu had'u a asibiti"

Sanda ya kira Abdul sau biyu bai d'auka ba a a na ukun ya d'aga

Yace"kai baban soyyaya ai sai ka tashi muje mu d'auko minal a asibiti daga yau zaman takaba ya kare"

Da sauri Abdul ya mike yace"da gaske an ganta?"

Yace"eh yanzu ta kira Islam wai sun kira ka baka d'aga ba"wani uban yayi,Wanda RAYHAN ya cire wayar a kunna yace"kar a fasa mun kunne"

Kiran ummi Abdul yayi ya gaya mata an gan minal

Cikin murna tace"toh sai kun dawo"kicin ta shiga ta fara had'a abincin mai lafiya dan ba karya tana ji da minal kasancewar ita kad'ai ta Haifa

Lokaci d'aya suka isa asibiti RAYHAN yace"har ka iso"

Abdul yace"ba dole ba"

Suna shiga IKLAS ta ruga da gudu ta rungume minal

Abun mamaki ina sanmani ganin Abdul yana farin ciki sai na gan ya tamke fuska kamar Wanda bai tab'a dariya ba"

RAYHAN ko gaisawa yayi da sultan

Islam ko ta rakube a gefe d ya dan wani irin kallo da sultan keyi mata

Abdul na karasowa kusa da minal ya..........






Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah



🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writer,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ7⃣7⃣&7⃣8⃣

Bismillahir Ramanir Rahim

Yana karasowa ya sinka mata lafiyyayen mari,rike wurin tayi tana hawaye

Yace"me kike tunani?bakiyi tunanin halin da zan shiga ba ko umma ki,ki san irin tashin hankalin dana shiga"

Cikin kuka da zafin marin da yayi mata tace"yi hakuri naga babu lokaci ne kuma ina tausayin IKLAS dan na lura a lokacin tana da ciki shiyasa"

Yace"ni na hanaki taimako ta ne?amma miyasa baki sanar dani ba?da ansan abinyi,da a ce sunyi miki wani abu fa"

RAYHAN yace"gaskiya ne da kin fad'a mana dan da wani abu ya same ki wallahi bazan iya yafewa kai na ba"

Haranrar shi tayi tace"wa zan fad'awa kai,kai da ka zama hoto kullum cikin kuka kamar mace sai wani cewa kake matata ki dawo gareni na tuba shine kake cewa in fad'a ma"

Dariya kowa yayi shima Abdul bai san lokacin da dariya ya sub'uce me ba

RAYHAN ya susa keya kallonshi IKLAS tayi tace"gaskiya minal baki da mutunci yanzu mijina kike yiwa siya"

Minal tace"ai gaskiya na fad'a"

RAYHAN yace"oho dai ai ki sha mari"

Kallon Abdul tayi ta harare shi,zama yayi kusa da ita yace"ba inda ke miki ciwo ko?"share shi tayi

IKLAS tace"ya akayi kika fita a gidan?"

Tace"bayan mugu ya bar d'akin da suka ajiye ni dan a lokacin ya gane bake bane yana fita na kwance kaina dan dama babsy bai d'aure ni da kyau ba ina gamawa na fara niman hanyar guduwa wajen window naje kawai sai naji kara bindiga da sauri na fara girgiza karafuna jikin window,gajiya nayi na zauna ina zaune na hango wani karfe da sauri na buga shi karfen yayi gefe na hau window na yi tsalle fad'owa nayi kai na ya bugi dutse, ina fita a gidan na gan su mugu sun shiga mota ga warin gas ya cike ko ina b'oyewa nayi suna tafiya na fara gudu sai dai banyi nisa ba na gan gidan ya buga kamar tashin bomb,gudu na dingayi a daji da k'yar na iso titi tun a lokacin ban kara sanin kai na ba"

Abdul yace"sorry dear"

IKLAS ko kara rungumeta tayi tana hawaye

Minal tace"ya baby na?"

IKLAS tace"ai baby sai dai wani"

Minal tace"ban gane ba"

Tace"cikin ya b'ere ai lokacin da na gan gidan na konewa"

Tace"Allah sarki ina raye ai"

Tace"eh ai Abdul kad'ai ya yarda baki mutu ba dan har haukacewa tayi"

Kallonshi minal tayi ta hararre shi susa kai yayi yace"ai ina taji a jikina kina raye dan ko wanan hararran ne ayi tamun kafin in kashe bakin nan mai siwa siya"

RAYHAN yace"karki damu kwana nan zamu samu wani baby"

Sultan ne yayi gyran murya yace"sai soye kuke toh nima ai nayi mata"

Abdul ya zaro ido yace" waye

Yace"gata nan"ya nuna Islam da hanun"sai a sanan RAYHAN ya tuna da ita a wurin yace" ke bar nan"fita tayi sultan yace"gaskiya bana son haka"


Kallon Abdul minal tayi tace"toh ai sai kaje wajen likita ka anso mana sallama ko"

Yace"toh umma"

Sultan ya kalleshi a ranshi yace"lallai ta raina shi, babu mace da zan sakarws fuska har ta raina ni haka"

Abdul na dawowa yace"tashi muje an sallame ki"

Suna fitowa suka tarar da Islam a mota tana jiran su

Kallonta sultan yayi ya basar"


Suna isa gidan umma minal umma ta rungume minal,minal na kokarin yi mata bayani umma tace"bana son inji komai dan nasan IKLAS zata iya yi miki abin da ya fi haka"

Abinci ta basu white rice dan minal na mutuwan sonshi

Minal tace"umma ina Abba na"

Umma tace"ai yana nan tafe ina fad'a me yace gashinan zuwa ya ga princess d'inshi ya je station ne ko sun samu labarin ki "

Suna cikin cin abinci sai ga zaliha ta shigo da sallama

IKLAS tace"zauna mu ci abinci"

Tace "ni da Mahmud ne yana waje"

Minal tace" toh ta yaya ya so"

Zaliha tace"driver
Shi ya kawo mu"

IKLAS tace"ke barta kawai kullum fa Mahmud na gidan su Islam ko gidan mu ta zo sai yace "zasu zo su d'auke ta kamar ba gurgu ba soyyaya ake sha"

Minal tace"kin ma tuna min akwai wani likita mai zuwa asibitin mu kowani karshen wata shi specialist ne a irin matsalan Mahmud amma a Egypt yake,muje inyi me magana"

Zaliha tace " Allah yasa ya yarda dan da kayi me irin wanan magana sai yace"ba zai je ba wanan lalurar ita ce kaddarar shi"

Minal tace"muje dai"

Suna fita suka gan shi zaune mota

Bayan sun gaisa da minal tace"Mahmud wata shawara na kawo please kar ka ce a'a"

Yace"ina ji"

Tace"wani likita ne nayiwa maganan condition d'inka shine yace a kawo file d'ika"

Tun da Mahmud yaji likita ya canza fuska

Tace "please Mahmud kayi tunanin maganata you are still young please"

Yace"OK zanyi tunani"

Zaliha tace" baby please ka yarda"

Yace"na yarda amma sai bayan auren mu saboda mu tafi tare"

Tace"ba matsala ai"

Minal dai murmushi tayi ta shige ciki"

IKLAS na zaune a palourn umma tana ganin minal tashigo tace"ya akayi ne ya yarda ne?"

Tace"ya yarda amma said bayan auren su"

IKLAS zatayi magana wayar ta yayi kara tace......



Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.


πŸ…Ώ8⃣1⃣&8⃣2⃣

Bismillahir Ramanir Rahim

Yace"ai naji"

A ranta tace"ikon Allah"

Sanda ya gama ja mata aji yace"muje ko"

Tace"ok"

Palour ummi ta kaita shi suka gaisa

Bayan sun gaisa ummi ta shige ciki

Islam tace"muje guest palour ko garden?"

Da k'yar ya bude baki yace"garden"

Tace"ok "

Suna fita hanyan garden suka nan suka tarar da zaliha da Mahmud gaisawa tayi da mahmud,mahmud ya mika mai hanun suka gaisa

Mahmud yace"nice choice"dariya tayi shiko sultan ya had'e rai a ranshi yace"meyasa take dariya dashi?"

Zama sukayi nisa dasu tace"bari inkawo maka drinks tashi tayi bayan minti biyar ta dawo da drinks da snack a hanya zaliha tace"hmmm wanan gayen akwai miskilanci"

Murmushi tayi,tana zuwa ta siyaye me a cup

Tace"gashi"

Ya karba zama tayi

Babu wanda yayi magana shiko danna wayarshi yake ta faman yi

Bayan awa d'aya da rabe tace"kana jina?"

Shareta yayi a ranshi yace"wato bazata ce tana sona ba kenan"

Can anjima tace"ina tafi ne in ba magana"

A fusace ya juyo yace"nina ce ki tafi ne bana son raini"shiru tayi

Sakawa wayar yayi a aljihu yace"miye sunan ki?"

Tace"Islam"wow yace a zuciyar shi

Yace"sunana sultan,zan turo magabata na a saida maganan auren mu"a ranshi addu'a yake yi Allah yasa ta amince da shi

Shiru tayi na wasu mintina

Cikin tashin hankali shirun datayi ya dak'e

Yace"no zaki iya fad'i ra ayi ki in bamiki ba sai in hakura"

Tace"na amince"

Yace"toh kiyi ta saka hijabi kuma bana so kiyi ta dariya da ko wani namiji"

Tace"toh"

9:50 dai dai ya bar gidan

'Bangaren RAYHAN fushi yake yi da IKLAS ko tayi me magana baya amsawa

Tace"toh miye na fushi?tunda gani mun dawo"dakinshi ta koma tace"mijina kazo ka ci abinci"

Yace"ban ci"

Tace"zaka ji yunwa fa"shiru yayi,itako ta barme d'aki ta koma d'akinta,ta haye gado ta ja bargo

Tana bari d'aki yace"Allah yasa abincin taje kawowa ta lallashe ni,wallahi yunwa nike ji"

Shiru-shiru babu alaman dawowar IKLAS gashi ya kasa barci

Yace"wallahi ba zan iya barci ni kad'ai ba"agogo ya duba ya ga 12:52am fita yayi daga shi sai boxers

Direct d'akinta yaje kunna wuta yayi,ya ganta tana barci hankali kwance

Hayewa gado yayi tana jin shi tayi banza dashi dan itama ta kasa barci

Juyi yake yi ya kasa barci yana ta kunna bedside lab ya kashe

Dariya takeyi kasa kasa,ganewa da yayi hakan ba zai taikeshi ba yasa ya tashe ta,wanda da k'yar ta tashi yi tayi kamar mai barci

Tace"har ka gama fushin ne?"

Yace"haba wiffy yanzu ko ki bani hakuri naci abinci shine kika zo kikayi kwaciyar ki"

Tace" tun rana fa nike baka hakuri,miye ma dalili fushin ka?abinci kuma ai kai ka ce baka ci"

Da sauri yace"wallahi yanzu in kika bani zanci"

Tace"toh muje dining"

Da sauri ya sauko a gado ya bi bayanta

Suna zuwa ta ciro tuwon semo jin shi tayi da sanyi

Tace"warmer d'inan baya rike zafi bari in yi ma warming"

Da sauri yace"bani haka zan ci wallahi,bazan iya jira ba"

Serving d'inshi tayi sanda yaci Leda biyu da rabe, yayi gysa"

Dariya yayi yace"yauwa na koshi"

Zo to muyi soyyaya tace"wani soyyaya da jinin"

Yace" ai bazan iya barci ba sai na rage zafi"

Tashi yayi ya d'auke ta kamar baby ya haye sama"

Washe gari misalin karfe 8:am tace"mijina yau zan d'auko nawal"

Yace"eh ya kamata"

Tace"toh in na gama aiki zani na d'auko ta"

Yace...........


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

πŸ…Ώ7⃣9⃣&8⃣0⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Wayar IKLAS ne yayi kara tana d'agawa tace "mijina ya dai"

Yace"kalau fito muje gida"

Tace"ka bari sai gobe nayi kewar minal"

Had'e rai yayi kamar tana ganin shi yace"bana so shashanci fa"

Race"ko nadawo mai zanyi ma tunda jinin ba tsaya ba"

Yace"wai yaushe kika raina ni ne"

Tace"yi hakuri sai ka zo ka shigo ka gaida umma"

Bayan minti talatin sai gashi ya shigo,gaisawa suka yi da umma daga nan suka bar gidan

Yana tuki ya kalleta yace"dama miye nufin ki da kika ce zaki kwana?"

Tace"ba komai ina dai so ne muyi fira ne"

Yace"saboda kin gaji dani ko? "

Tace"no bahaka bane"

'Bangaren Abdul ko bayan ya koma gida yayi aski yayi wanka ya fesa tulare,bakin nan ya ki rufuwa

Sultan yace"ina zaka da yamma nan?"

Yace"wuri matsoyiyata mana"


Sultan yace"shiyasa take raina ka ai"

Abdul yace"injiwa yace"maka ta raina ni?minal na da ladabi da biyyaya ga ilimi da sanin ya kamata,sai dai Allah yayi ta da fad'a amma gaskiya bata da roko kuma wallahi ta sona "

Sultan yace"hnmm waya ce ma ana nunawa mace so,ai sai ta raina ka"

Abdul yace"hmmm ni dai ina nunawa minal so kuma wallahi baka isa ka zuga ni ba,bari ma inje nasan yanzu sai ta balbale ni da masifar marin da nayi mata a asibiti amma nasan zamu shirya"fita yayi ya bar sultan baki sake

Sultan yace"wato yariyar nan ko ta kira ni bayan ina ta nuna mata green light"

Jawo wayar shi yayi kiran Islam ya danna

Ta d'aga tace"hello waye ne?"dan ita batayi saving number shi ba

Shiko a ranshi yace"kan uba bata ma da noba na"(hmmmm kuji mun sultan)


Ta kuma cewa"hello!!"

Shiru yayi na sakoni kafin yace"hello"nan take ta gane murya

Yace"ya kike?"

Tace"fyn"

Shiru ne ya biyo baya kafin a ranshi yace"toh bazatayi magana bane"


Ganin bata da niyar magana yasa yace"address d'inku zaki bani"

Tace"toh zanyi ma text yanzu"kashe wayar yayi

Shiko yace"what disrespect"

'Bangaren IKLAS kuwa suna kaiwa gida RAYHAN ya tafi d'akin shi wai yayi fushi

IKLAS tace"hmmm dole ne ma ka sauko dan ko baka nime ni dan abinci ba zaka nime ni dan show dan nasan baka wasa da abu biyu nan"


Kicin ta shiga dan girka masu dinner


Abdul ne zaune a palourn baki su minal

Fitowa tayi cikin wani fited gown ya bala'in yi mata kyau

Abdul na ganin ta yace"uwar gida sarautan mata,uwargidana matsoyiyata daga ke ba wata,in ina ganin ki sauran mata maza ne a gabana,mata a gidan abdullahi"

Minal tayi dariya tace"Allah ko mijina"


Zama tayi tace"my dear miyesa ka bani mari a asibiti"

A ranshi yace"ai yanzu sai fad'a"

Tace"sauraren ka"

Yace"wallahi umma raina ne ya b'ace ki gafarce ni"

Tace"toh last warning bana son namiji mai duka,hakan nasa indaina respecting d'inshi,zan ma uziri dan wanan shine farko dan ba a haiyacika kayi shi ba,tunda na samu labari ka kusa zarewa dana b'ace,amma wanan ya zama karshe please my love"

Yace"toh umma"murmushi tayi tace"ashe kana sona? "

Yace"sosai ma"

Tace"nima haka"

Yace"abbana yace za a d'aga bikin next week dan ki samu lafiya"yayi maganan ne kamar zaiyi kuka

Tace"in bada abun ka kwana nawa ya rage ne"

Yace"gaskiya ni an ta kurani ni dai da anyi inje inyi jiyar matata"

Tace"wai miye na sauri ne?"

Yace"hmmmm"a ranshi yace so nake in saita bakin nan"


Hira suka cigaba da yi iron ta matsoya

8:pm sultan ya shirya ya kama hanyar gidansu Islam

Yana isa sai wani shan kamshi yake yi ya kira ta awaya wai yana waje

Da sauri ta mike jiki na rawa dan tana sonshi bata San abinda zai b'ata mai rai


Tana fita ta tarar dashi jigine a mota tace" ina wuni"

Sanda ya share wasu mintoci yace"ya kike? "a kasa makoshi

Tace" muje ciki"

Yi yayi kamar bai jiba,sanda ta maimaita

Yace..........


Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers we are the best among the rest.

πŸ…Ώ8⃣3⃣&8⃣4⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Yace"no bari in na tashi a office zan d'auko ta"

Tace"toh"

'Bangaren sultan kuwa tun da ya bar gidansu islam ba kara kiran ta ba,gashi yana son jin muryar ta amma shi gaskiya ba zai iya kiranta ta raina shi ba

Abdul ko shirye shirye auren su yake da minal hankali kwance dan ji yake kamar ya jawo kwanakin kusa

Misalin karfe 4:pm RAYHAN ya dawo gida tare da nawal,da gudu taje ta rungume IKLAS

Tace"mummy nayi fushi dake,ki barni ni kadai"

Kissing goshi ta IKLAS tayi tace"baby mummy yi hakuri kiji"

Shiko RAYHAN tsayawa yayi yana kallon su cikin so da kauna yana tuna ranar da suka had'u a kasuwa

Kallonshi IKLAS tayi tace"mijina ka dawo,ya aikin ne?"

Hararata yayi "yanzu kika ganni?ai na lura in kina tare da nawal baki tuna kowa"

Tace"no ba haka bane nayi missing d'inta ne"

Bud'e hanun yayi da sauri ta rungume shi,nawal tayi ta dariya takeyi

IKLAS tace"baby d'akin ki kiyi wasa na siya miki Sabon teddy

Haurawa nawal tayi tana murna,bayan tafiya nawal IKLAS tace"baby muje inyi maka wanka"

Yace"ok wiffy"

Bayan sunyi wanka IKLAS na zaune gaban mirror tana kwalya

Shiryawa yayi cikin 3qtr da vest itama 3qter ne a jikinta da top

Karasawa yayi kusa da ita ya rungumeta ta baya yana kallonta ta mirrow,kallonshi tayi tace"honey ya dai?"

Yace"tanks,thank you very much"

Cikin mamaki tace"for what?"

Yace"for everything ina alfari da ke"

Juyo da ita yayi ta gaba yayi pecking d'inta a goshi

Rungumeshi yayi tace"l luve you very much my husband"

Yace"really wiffy"

Tace"ofcourse dear"

Yace"then prove it"

Kissing d'in shi tayi passionately sun dade suna abu d'aya da k'yar ta ja jikinta

Suna mai da numfashi kallon juna suka yi yace"I miss you baby"

Tace"I miss you more,muje downstairs in bawa nawal abinci"

Rungumeta ya kuma yi yace"love you my angel,you are the best,nagode da kike nunawa y'a ta kauna"

Murmushi tayi tace"ai nima y'ata ce ka manta kace ka bani kyauta nawal ko cikin santi ne?"

Dariya yayi yace"lah ashe baki sume ba lokaci"

Rufe fuska tayi tana dariya,saukowa suka yi nan suka tarar da nawal na wasa a falo

Tace"baby ashe kina nan"

Nawal ta kalleta tace"mummy kinyi kyau,daddy yi mana selfie"

Selfie suke tayi RAYHAN yayi musu su biyu,yayi musu ita da nawal sai kuma yayi musu duka

Nan fa nawal ta tada rigima sai suyi mata rawa da waka tace"mummy ki fara yi kafin daddy yayi"

Murmushi IKLAS tayi tace"ni ban iya ba"

RAYHAN yace"Allah sai kinyi"

Tace"OK amma wakar India zanyi"

Yace"OK"

Wankan imran khan ta fara yi tana hawaye shima shiru tayi dan yana yawan saka wakan a program d'inshi a FM ganin tana wakan cikin kwarewa shima gyran murya yayi ya fara yi har suka gama nawal ta fara tafi shiko ya rungume IKLAS

Nawal tace"mummy saura rawa"ture hanun shi tayi tace"daddy ka fiye rungume mummy ka dinga bari tayi numfashi"

Dariya IKLAS tayi tace"gaskiya ne nawal"kallon RAYHAN tayi me gwalo

A ranshi yace"ka ji yariya da bakin ciki wallahi in ta takura ni zan maida ta wajen ummi"

Waka nawal ta saka a d v d nan shiko zama yayi yana kallonsu

Nan fa IKLAS ta fara rawa babu kunya komai na jikin ta motsi yake

Ba karami burgeshi tayi ba yace"ni ina ganin ta uztaziya ashe ta iya rawa"tashi yayi zai je ya rungumeta nawal ta rigashi rungumeta nawal tayi tace"daddy mummy na ne ni kadai"

Yace"ya salam,toh bari nima in rungumeta kinji muyi one big family"

Nawal tace"toh zo"

Bayan kwana 6 sultan ne a kofar gidansu Islam tana fitowa yace......



Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
IKLAS
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟GORGEOU WRITER FORUM🌟

🌟G.W.F.🌟

Home of gorgeous,interllingent,and expert writers,we are the best among the rest.

8⃣7⃣&8⃣8⃣

Bismillahi Rahmanir Rahim

Ya jita a kashe key mota ya d'auka ya FIFA

Yana kaiwa yayi parking ya kira ta amma still noban a kashe

Zaliha ya gani a kofar gida ita da Mahmud

Bayan sun gaisa yace"zaliha pls kira min IKLAS ta zo mu tafi gida

Tace"toh yaya"

Ciki ta shiga tana zuwa tace"yaya wai ki zo Ku tafi gida "

IKLAS tace"pls je ki ce me nayi barci kuma kin tashe ni ban tashi ba"

Zaliha tace"toh"

Tana fitowa tace"yaya tayi barci na tashe ta bata tashi ba ina ina ga gajiya ne"

Juyawa yayi ya shiga mota rai b'ace yace"yariyar nan ta raina mun hankali"

Yana zuwa gida ya zauna a palour cike da haushi idon shi ya kad'a yayi jawur yace"wallahi sai na b'ata miki rai,ni zaki bari in kwana a gidan ni kad'ai hmmmnm"

'Bangaren Islam ko kwanciya tayi tana tunanin halin irin na sultan amma gaskiya tana son shi kuma bsza ta iya rabuwa da shi ba a fili tace"kila in muyi aure zai daina"

IKLAS ko fira take hankali kwance da jama'ar gidan

Minal ko sai waya takeyi da Abdul

Umma minal ne ta shigo ta ga IKLAS a d'akin tace"ke meyasa baki tafi gida ba?"

Tace"umma ai sai gobe"

Umma tace"da izinin wa?"

Tace"ai na fad'a me"

Maryam kawan IKLAS tace"karya ne d'azun ya zo su tafi gida tace a ce tayi barci"

Umma tace"tashi ki bi mijin ki"

Tace"lah umma dare yayi fa"

RAYHAN ko kasa barci yayi in ya hau sama ya sauko yace"yariyar nan ta raina ni wallahi ta fa san bazan iya barci ba sai na rugumeta shine dan iskanci ta zauna gidan biki sai na sab'a mata"tunawa yayi da ya gan ta tana sallah azuba yace"yau ma da ya kamata ta zauna musha soyyaya shine tayi zaman ta gaskiya ta cuce ni"

Haka fa yayi ta juye juye a palour, itama IKLAS tayi kewar mijinta dan kasa barci tayi sai da dare yayi tayi da na sani kin tafiya gida

Gari na wayewa misalin karfe 7:am IKLAS ta shirya nawal cikin unifoam tace"zaliha pls taimaka ki ajiye nawal a school

Nawal ta fashe da kuka

IKLAS tace"meya faru baby?"

Nawal tace"ni bazan je da ita ba ki kai ni da kanki"

Wayar ta na yayi kara tana d'agawa tace"hello mijina"

Yace",in da gaske nine mijinki ina son in gan ki a gida nan da minti talatin"

Kafin tayi magana ya kashe wayar

Kallon minal tayi tace"minal zan tafi mu had'u a wajen dinner"

Minal tace"ban gane zaki tafi ba kince sai Friday ba"

Tace"yi hakuri wallahi yayi fushi"da gudu ta rike hanun nawal suka bar gida

Bayan ta ajiye ta a school ta tafi gida

Tana kaiwa ta tarar da shi a palour karasawa tayi Inda yake tace "ina kwana baby"zata rungume shi ya d'aga mata hanun zama tayi kusa da shi tayi

Tace" baby kayi hakuri nayi laifi ka yafe mun"

Ko kallon ta beyi ba

Tace "baby why are you quite"

Sai a sanan tace"ai basan takuraki nikeyi ba da har zaki bar ni inyi barci ni kadai"

Tace"no ba haka bane"

Yace".......




Maman
Noorul
Hudah✍✍
Luv u my fans
Pls share
[3/18, 00:43] Hubeey Kn 2: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„


Please Login or Register in order to submit comment