Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gimbiya tayi kwana biyu a
kwance tana jinyar wannan rauni nata kafin ta fara
takawa saboda kyakkyawan motsi ma zai iya sawa
dinkin ya farke.Koda jin wannan batu sai ran sarki
Darwaz ya baci ainun,zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone saboda kin haushin cewar babu
dama a cigaba da wannnan tafiya a yau bare a
hanzarta cimma su Shugaba Sharwan.A daidai
wannan lokaci ne billen Sarki Darwaz ya dameshi da
zogi har ma yana digar da jini.Koda likta ya lura da
hakan sai ya shiga tsaida jinin sannan ya dubi Sarki
Darwaz a tsorace yace ya shugabana akwai bukatar
ayi masa dinki a kan wannan rauni naka.Cikin
matukar takaici Sarki Darwaz ya ce idan ka dinke
raunin zai fatar da tabonsa har abada?Jikin likitan
na rawa yace,ai har abada tabon wannan yanka
bazai taba bacewa ba daga kan fuskarka.Kafin likitan
ya gama rufe bakinsa tuni sarki Darwaz ya
11 hours ago
Abubakar Haleefah Physicist
zaro wata sharbebiyar wuka a kugunsa ya kirbawa
likitan a cikinsa,kuma ya damki makoshinsa ya daga
sama da hannu daya a lokacin da yake kakarin
mutuwa yace,kai ne mutum na karshe wanda zai
sake ganin wannan bille.Yana gama fadin hakan yayi
wurgi da gawar likitan sannan ya bude kofar dakin
ya kirawo dakaru suka dauke gawar likitan suka fice
da ita kuma aka goge jinin daya fara zuba a
kasa.Tun a wannan Sarki ya ruge fuskarsa da
rawani,idanunsa kadai ake gani.Nan take yasa aka
kawo kuyangi guda hudu wadanda zasu lura da
Gimbiya Huraisa,sannan ya fice daga cikin daki.Yana
fita ya jagoranci wadansu dakarun nasa sukayi ta
yawo a cikin gidan suna bincika cikin
dakuna,lunguna da sako-sako ko zasu ga matar
Sultan,amma shiru ko alamarta babu.Saida suka
bincike ko'ina sannan sarki Darwaz ya hakura ya
koma can falon Sultan ya zauna don hutawa.Bayan
an kawo masa abinci da abin sha yaci yayi hani'an
sai ya kori kowa daga cikin falon hatta kuyangin
dake cikin dakin suna jinyar gimbiya Huraisa kuwa
saida suka fice,sannan ya kullo kofa da kansa yaje
gaban wani katon madubi ya tsaya.A sannan ne ya
kwaye rawanin dake fuskarsa yaga billen da Sultan
yayi masa.Bille ne mai tsawo da fadi,wanda yasa
masa muni,nan take zuciyar Sarki Darwaz ta kama
tafarfasa kamar zata kone a karo na biyu har saida
kwallar takaici ta cika amsa idanu.Ba komai ne yasa
shi zubar da wannan kwalla ba face sani cewa
shugaba Sultan ya karya masa tarihin
jarumtakarsa,domin tunda yake yaki da gumurzu a
rayuwarsa ba'a taba fitar da digin jini ba a
jikinsa,amma yau gashi ma anyi masa raunin da
indai zai bar fuskarsa a bude kowa sai ya gani.Sarki
Darwaz ya tuna cewa duk wannan abu daya faru
Siyama ce silarsa tunda inda bata kashe dan'uwansa
ba da ba zai fito farautarta ba har yayi yaki da
Sultan yayi masa wannan bille.Nan take Sarki
Darwaz yaji ya kara tsanar Siyama fiye da koyaushe
kuma ya tabbatar da cewar ransa bazai taba yin fari
ba face a ranar dayaga ya sare kan Siyama kamar
yadda ya sare na abokin mahaifinta wato Sulta.Nan
take Sarki Darwaz ya kudurce a ransa cewar bazai
sawa wannan rauni masa magani ba,kum bazai
yarda a dinke shi ba saidai yayi ta ciwon da zaiyi
har ya daina son kansa yayi warkewar dole,sannan
kuma ya kudirci niyar cewa babu wanda zai sake
ganin fuskarsa saidai idan ya zama gawa hatta
matarsa da 'yarsa kuwa.Koda ya gama aiyana
hakan,sai Sarki Darwaz ya sake rufe fuskar tasa da
rawani sannan yaje kan wata doguwar kujera ya
kishingida yana kwanciya barci ya saceshi saboda
tsananin gajiya gami da tsamin jiki bisa gumurzun
da yayi da shugaba Sultan.
¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤
Al'amarin su shugaba Sharwan kuwa suna cikin
tafiya a daji a cikin ayarin nasu gaba daya sai kawai
suka ga Shamirat matar Shugaba Sultan taja
linzamin dokinta ta tsaya cak a lokacin da jikinta
gaba daya ya kama tsuma kuma kirjinta ya kama
daka kamar zuciyarta zata faso kirjin ta fado.Koda
ganin haka Sai hankalin Shugaba Sharwan,Ilela dana
Siyama ya dugunzuma suka rugo gareta aka sauko
da ita daga kan dokinta akayi mata shimfida a kasa
saboda tsammanin ko kamuwa tayi da wata rashin
lafiya.Nan fa suka shiga tambayarta inda uakeyi
mata ciwo a jikinta.Koda jin wannan tambaya sai
hawaye ya zubowa Shamirat ta dubi Sharwan
tace,sun kashe mijina,naji a jikina baya numfashi a
doron kasa.Koda jin wannan batu sai Sharwan ya
takarkare ya kurma uban ihu wanda ya tsorata kowa
a wajen sannan ya fashe da matsanancin kuka
kamar bazai daina ba.Al'amarin daya karya zuciyar
Ilele da Siyama Kenan suma suka rungume Shamirat
suka taya ta kukan.Saida shugaba Sharwan ya jima
a tsugunne bisa gwiwoyinsa yana kuka sannan ya
dago kai ya dubi Shamirat,bisa mamaki sai taga yayi
mata murmushi yace,mijinki bai mutu rago ba.Na
tabbatar da cewar kafin su Sarki Darwaz su kashe
shi saida yayi musu mummanar barna saboda nasan
irin jarumtakar abokina gami da taurin ransa.Bana
raba daya biyu,sai ya bar shaida a jikin Sarki
Darwaz.Ina son ku sani cewa zamanmu a waje daya
yana da matukar hadari,don haka zaifi kyau mu tashi
muci gaba da tafiya.Ba tare da gardamar komai ba
kuwa aka kimtsa aka cigaba da tafiya ana keta
dazuzzuka masu sarkakiya,kwazazzabai,koramai da
fadamomi iri iri suna masu tunkarar hanyar da zata
kaisu Birinin Darul Hunam.Saida suka shafe kwanaki
arba'in suna tafiya sannan suka iso wani daji mai
tsananin fadi mai cike da sahara.Iya hangen mutum
a cikin dajin babu bishiyu ko daya,babu duwatsu ko
alamar wani danshi na ruwa sai rairayi tsabarsa
tsubi-tsubi,wani rairayin ma tudunsa yakai na
tsauni.Da isowars wannan wuri sai Shugaba
Sharwan ya bada umarni aka tsaya aka yada
zango.Bayan an kafa tantuna anci abinci kuma an
huta,sai Siyama ta dubi Sharwan tace,yakai Abbana
menene dalilin da yasa ka bada izinin mu yada
zango a nan wajen?Lokacin da Sharwan yaji wannan
tambaya sai yayi ajiyar zuciya sannan ya dubeta
cikin alamun takaici yace,yake 'yata idan baki manta
ba abokina Sultan ya gaya mama cewa tsakanin
birninsa da birnin na gaba wanda ake kira Darul
Hunam tafiya ce ta kwana arba'in da daya,yau kuma
kwananmu arba'in cif muna tafiya.Kinga kenan saura
tafiyar kwana daya jal mu riski birnin Darul
Hunam.Dole ne mu tsaya daga nan mu tura dakarun
leken asiri domin su gano mana halin da garin ke
ciki.Idan an dana mana wani tako ne mu san yadda
zamu tsallakeshi.Idan kuma garin bazai shigu ba mu
nemi hanyar dazamu kewaye shi.Sa'adda shugaba
Sharwan yazo nan a zancensa sai gaba dayan
jama'ar banu Hanzar suka aminta da shawarar
tasa.Nan yake aka tashi wadansu kwararrun dakarun
sumame guda uku wadanda akeji dasu aka turasu izuwa
cikin birnin Darul Hunam.
&GUDUN TSIRA&
Littafi na hudu(4)
Part B
&A-H Physicist&
Nan take aka tashi wadansu kwararrun dakarun
sumame wanda ake ji dasu aka tura su izuwa cikin
birnin Darul
Hunam.
¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤
A can birnin marigayi Shugaba Sultan kuwa tunda
Sarki Darwaz da gimbiya Huraisa suka kama barci
basu farka ba har saida gari ya waye rana ta
take.Huraisa ce ta fara farkawa tana bude idanunta
sai ta yunkura da nufin ta mike tsaye,amma sai
wata
kuyangarta mai suna Badura tayi sauri ta dannan
kafadunta kasa ta dubeta tace,yi hakuri ya
shugabata,kiyi sani cewa likita yace kada mu bari
kiyi kyakkyawan motsi,domin yin hakan zai iya
janyi
farkewar dinkin da aka yiwa rauninki.Koda jin
wannan batu sai bakin ciki ya turnuke Gimbiya
Huraisa ta koma ta kwanta,sannan ta dubi Badura
cikin tsananin takaici tace yanzu ina mahaifina
yake?
Badura tace yana falo yana ta fama shara bacci tun
jiya bai farka ba.Huraisa tace maza ki koma
wajensa
yanzku ki gani,idan har ya tashi daga wannan
barcin
kice dashi inason na gana dashi yanzu yanzu cikin
gaggawa.Badura ta risina tace an gama ya
shugabata.Nan take Badura ta mike tsaye ta fice
daga cikin dakin ta nufi babban falon na marigayi
Sultan.Fitarta ke da wuya sai idanun Huraisa suka
kai kan wata babbar akwatin karfe dake jikin
bangon
arewa na dakin,wacce aka kulleta da wani katon
kwadon madubi.Huraisa ta dubi wata kuyanga
dabam tace,maza kije ki nemo mini makeri ina son
na cire wannan makulli domin naga abinda ke
cikin
wannan akwati,domin koma meye a ciki yana da
matukar muhimmanci ga shugaba Sultan,amma
kuma menene dalilin da yasa ya barshi anan bai
kaiwa matarsa Shamirat ta tafi dashi ba?Kuyanga
ta
risina tace an gama ya shugabata.Itama sai ta
mike
tsaye ta fice daga cikin dakin.Jim kadan da fitar
wannan kuyanga saiga Sarki Darwaz yashigo cikin
dakin kuyanga Badura na biye dashi kuma
fuskarsa
na rufe cikin rawani idanunsa kadai ake gani.Koda
Huraisa taga Sarki Darwaz a cikin wannan yanayi
sai
ta yunkura ta mike zaune,sannan ta dubi gaba
dayan
kuyangin dake dakin tace,ku bamu wuri.Take kuwa
kuyangin suka fice suka janyo kofa suka rufe.Sarki
Darwaz ya zauna a kan gefen gadon data ke
kwance,ya dubeta yace,ki gafarceni yake 'yata,daya
yau kema bazaki saki ganin fuskata ba,domin bana
son kowa yaga wannan shaida da Sultan yayi
min.Koda jin wannan batu sai Hankalin Gimbiya
Huraisa ya dugunzuma ainun ta dubeshi cikin
alamun tsananin damuwa da takaici a lokacin da
idanunta suka ciko da kwalla,tace haba yakai
Abbana ai idan har zaka boyewa kowa fuskarka bai
kamata ace ni da mahaifiyata ka biye mana
ba,saboda zamu iya zama da kai a cikin kowacce
siffa ko da kuwa fuskarka tafi komai muni a cikin
wannan duniya,tunda ba fuskar taka muke so
ba,ruhinka muke bukata ya kasance tare damu
dimun da'iman.Lokacin da Gimbiya Huraisa tazo
nan
a zancenta sai Sarki Darwaz yayi murmushin farin
ciki,yace,yake 'yata na sani cewa kuna kaunata
kamar yadda kuke son kanku.Ina so ki sani cewa
abin kunya ne kuma abin kaskanci a cikin tarihin
jarumtakata duniya ta san cewa gwamnan da yake
karkashina shine yayi mini rauni a fuskata.Idan
kika
ga wannan fuskatawa a fili to gawata ce a
kwance.Mene ne dalilin da yasa kika aika kina son
yin magana da ni yanzu?Koda jin wannan tambaya
sai Huraisa tayi ajiyar numfashi sannan tace, ba
wani abu bane yasa na aika kazo ba,sai domin na
nemi gafararka bisa sakacin danayi har Sultan ya
sami nasarar yi min rauni a kafata gashi hakan ya
haddasa matsala a cikin tafiyarmu.Kamata yayi ace
munci gaba da tafiya yanzu don karfa abokan gaba
su kara bamu tazara sosai.Na kirawo kane yanzu
domin na baka shawara,shawarar kuwa itace ku
kara
gaba kada ku tsaya jirana har izuwa gobe don ci
gaba da wannan tafiya.Ka tuna cewa idan har
wadannan abokan gaba namu suka sami nasarar
fita
daga cikin nahiyarmu shikkenan sun tsira.Lallai ya
kamata mu kure musu wannan GUDUN TSIRA da
sukeyi mu kawo karshensu.Yayin da Gimbiya
Huraisa tazo nan a zancenta sai hankalin Sarki
Darwaz ya rabu gida biyu,ya rasa hukuncin daya
kamata ya yanke..Kwatsam sai suka ji ana
kwankwasa kofar dakin.Cikin fushi sarki Darwaz ya
daka tsawa yace wane ne nan yake kwankwasa
mini
kofa?Kawai sai sukaji muryar Boka Hurgas yana
mai
cewa nine ya shugabana.Cikin hanzari Sarki
Darwaz
ya mike yaje ya bude masa kofar ya shigo.Hurgas
ya
risuna sannan ya dubi sarki cikin biyayya yace ya
shugabana zamanmu a wannan gari har izuwa
gobe
zai iya janyo mana dalilin dazamu kasa cimma
abokan gaba da tazarar kwana daya rak.Abinda
za'ayi shine,a dauki Gimbiya a sanyata cikin keken
doki a cigaba a tafiyar a haka.Koda jin wannan
batu
sai farin ciki ya lullube gimbiya Huraisa,ba tare da
sarki Darwaz yayi wata gardama ba sai ya bada
umarni nan take aka fara shirye shiryen tafiya.Kafin
abar garin saida Sarki Darwaz ya dora wani babban
hadiminsa mai suna Zukairu akan kujerar marigayi
Sultan,sannan akayi hawa aka fice daga cikin
birnin
gaba daya aka durfafi hanyar da zata kaisu birnin
darul Hunam.
¤¤¤ ¤¤¤ ¤¤¤
Lokacin da dakarun leken asiri na kabilar Banu
Hanzar suka tafi izuwa cikin birnin Darul Hunam
domin su gano halib da birnin ke ciki da kuma
sirrin
komai na birnin,Saida suka kwana suka yini basu
dawo ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalin su
shugaba Sharwan kenan suka fara tunanin ko an
kama sune,don haka suma a koyaushe za'a iya
kawo musu harin sumame.Nan da nan shugaba
Sharwan ya hada taron gaggawa domin suyi
shawara bisa abinda ya kamata ayi.Nan fa shawara
ta yawaita wasu suce kawai ayi shirin yaki a bi
sawun dakarun da aka aika guda uku.Wasu kuma
suce a sami wuri a buya a dan kara saurarawa a
gani.Saida kowa ya fadi albarkacin bakinsa san
nan Siyama ta daga hannu akayi tsit.Siyama ta
dubi
shugaba Sharwan tace,yakai Abbana inason ka
tuna
cewa dakarun sumamen da muka tura suyi mana
leken asiri a cikin wannan birni na darul Hunam
sune suka fi kowa kwarewa a aikin leken asiri a
can
birnin Kisra gaba daya,kuma sama da shekaru
goma
suke rike da wannan kambu ba'a taba turasu aikin
dasu ka kasa ba.Haka kuma sun kasance dakaru
masu tsananin karfin damtse da tsananin karfin
gudu
da iya jure wahala ta tsawon kwana uku.Bisa
wannan dalili nake ganin cewa duk rintsi ko da
mutum daya ne daga cikinsu sai ya sami nasarar
dawowa nan garemu a raye ya bamu labarin
abinda
ke faruwa,saboda haka zaifi kyau mu dan kara
musu
lokaci daga nan zuwa tsakar date ko zuwa gobe
da
safe,saboda babu mamaki ma yanzu haka suna
kan
hanyarsu ta dawowa.Lokacin da Siyama tazo nan a
zancenta sai jikin kowa yayi sanyi,aka sake yin
shiru
tsit aka rasa wanda zai soko shawarar data
kawo.Kawai Sai shugaba Sharwan yayi murmushi
ya
dubi Siyama yace,yake 'yata hakika kina da kaifin
tunani gami da hangen nesa,don haka na amince
da
wannan shawara taki.Lallai zamu ci gaba da
sauraron dawowar dakarunmu na leken asiri,daga
na har zuwa wayewar gari.Amma duk da haka
yanzu
zamu tura dakarun tsaro mutum bibbiyu izuwa
kowane bangare na wannan daji.Wato gabas da
yamma,kudu da arewam,nisan tafiyar zngo guda
domin su labe su zuba ido.Da zarar sunji wani
motsi wanda basu aminta dashi ba,ko sunga wata
zuga ta dakaru su rugo su sanar damu.Koda jin
wannan batu sai gaba dayan yan majalisar suka
mince.Ai kuwa saida dare ya raba sannan akaji
dawowar dakarun sumamen da aka aika birnin
Darul
Hunam,sun taho a guje suna yin alamarsu ta
kukan
wani tsuntsu.Dama babu wanda yayi bari a cikin
ayarin,sai kuwa kowa ya mimmike aka tarye
su.Dakarun sumamen suka iso su uku suna ta
faman haki kamar ransu zai fita.Suka zube kasa
wanwar suna numfashi da karfi kamar ransu zai
fita.Saida suka bari suka huce sosai,suka dawo
cikin
hayyacinsu sannan aka basu ruwa suka sha.Bayan
sun nutsu ne Siyama ta dubi babbansu mai suna
Hatmara tace ba mu labari yakai tauraruwa mai
wutsiya,mu kuka gano a cikin birnin Darul Human?
Sa'adda Hatmara yaji wannan tambaya sai yayi
ajiyar
zuciya sannan yace ya shugabata kiyi sani cewa
an
sanya tsattsauran tsaro a cikin birnin darul Hunam
da kewayensa.Babu ta inda mutum zai ratsa ba
tare
da ya fada hannun dakaru ba walau ta
gabas,yamma,kudu da arewa,amma duk da haka
saida mukayi amfani da kwarewarmu muka shiga
har cikin tsakiyar birnin ta cikin bututun ruwan
kwata dake karkashin kasa,amma da zamu dawo
sai
wannan hanya ta gagare mubi dole saida muka
rafke
dakarunsu guda uku a cikin daren yau mukayi
shigarsu mukayi kasadar biyo hanyar cikin gari,a
kyar da sidin goshi muka iso bakin kofar
birnin.Anan ne fa muka gane kuskurenmu saboda
saida asirinmu ya tonu aka kama mu aka kai mu
wajen shugaban masu gadin kofar.A nan ne akayi
kuskure aka shigar da mu cikin wani daki domin
gana mana azabar da zatasa mu fadi ko mu su
waye.Cikin sa'a muka bubbuge dakarun da suka
kamamu a cikin dakin,muka sumar dasu suma
mukayi shigarsu muka dawo baki kofa.Inda anan
ma
mukayi wani yakin na sumame muka bazar da
gaba
dayan masu gadin kofar kimanin mutum saba'in
sannan muka bude kofar garin muka fito muna
masu
falfala azababben gudu,har sai da muka iso nan
yanzu.Ya shugabata a cikin binciken da mukayi a
cikin birnin darul Hunam mun gano cewa aljanu
sun
kai labarin guduwar jama'armu daga can birnin
kisra,kuma gwamnan garin ya kafa doka cewa duk
dan garin daya boye irin jama'armu a cikin
gidansa
hukucin kisa ne a kansa.Yanzu shawara ta rage
garemu mu san matakin dazamu dauka amma
komai zai iya faruwa domin gwamnan birnin darul
Hunam zai iya turo dakarunsa su biyo sawunmu
su
iso har nan su riske mu gaba daya,kuma zau iya
tsayawa a bakin birninsa yayi mana mugun tanadi
na yakarmu.Babban abinda ya tayar mana da
hankali
shin yawan dakarun birnin sun ninka namu sau
uku,inda mukace zamuyi fito na fito dasu zasu iya
karar damu gaba dayanmu.Lokacin da badakare
Hatmara yazo nan a jawabinsa sai hankalin kowa
ua
dugunzuma ainun har da shugaba Sharwan aka
rasa
wanda zaice kala har izuwa tsawon yan dakiku
masu
yawa.Kwatsama sai Siyama ta dubi Sharwan
tace,zama bai kama mu ba yanzu,dole ne mu
tashi
yanzu muyi shirin yaki muje mu tari dakarun birnin
darul Hunam a kan hanya tun kafin su iso
nan.Amma yakin sunkuru zamuyi musu,kuma dole
ne mu gaggauta gamawa dasu,sannan muyi shigar
su su shiga izuwa cikin birnin muyiwa gwaman
garin juyin mulki,domin mu sami damar shiga
garin
har mu kwana,inyaso da safe mu kara guzuri mu
ci
gaba da tafiyarmu tunda bamu da wata hanya
dazamu bi face ta cikin birnin.Lallai bamu da wani
zabi wanda yai muyi kamar yadda na shirya yanzu
ni ba haka ba kuwa karshen mu ya yazo.Sa'adda
Siyama tazo nan a jawabinta sai wani babban dan
majalisa mai suna Dairuf ya dubeta yace,ai juyin
mulkin da zamuyi bashi da wani amfani tunda dai
bazamu iya sani daga cikin jama'armu ya hau
karaga ba,kuma babu wani dan gari dazai yarda ya
karbi karagar saboda tsoron Sarki Darwaz.Siyama
tace ai bukatarmu bata son karaga bane sai dan
kawai mu sami damar kwana a garin da samun
garin guzuri da ikon wuce gaba.Shugaba Sharwan
yayi ajiyar numfashi sannan ya dubi Siyama yace
na
yarda dake a kan cewa bamu da wani zabi wanda
yafi muje mu yaki wadannan mutane,amma fa
hadarin dake cikin yin hakan yana da yawan
gaske,kuma ban ga hanyoyin daza'abi a sami
nasara.Siyama tace nayi nazarin duk irin hadarin
da
kake tunani,kuma nayi tunani akan irin dabarun da
ya kamata muyi
don ganin mun sami nasara.Abinda nake bukata
kawai shine ka bani dakaru guda dari biyi kacal
daga cikin dakarunka na musamamn masu tsaron
lafiyarka,zan jagorance sumu kai ga
nasara.Sa'adda
Siyama tazo nan a zancenta sai Shugaba Sharwan
Sharwan yayi shiru yana mai sunkui da kansa kasa
ya fada cikin kogon tunani ba tare daya nemi
shawarar yan majalisarsa ba.Daga can sai ya dago
kai ya dubeta yace,yake 'yata kiyi sani cewa dalili
daya ne zaisa na yarda dake na baki dakaruna na
musamman don zuwa aiwatar da wannan aiki mai
mugun hadari.Dalili kuwa shine tun kuruciyarki
kawo
iyanzu ban taba ganin wani abu ya gagareki ba
muddin kinyi niyyar aiwatar dashi,haka kuma ban
taba ganin kin shiga hadarin da kika kasa fita
ba.Zanyi kundubala a yanzu na baki dama,amma
ina
gargadinki daki sani cewa idan har kika kasa
samun
nasara kika janyo dalilin da kabilarmu ta tarwatse
ko
kuma mukayi asarar dumbin rayuka da dukiya mai
yawa bazan taba yafe miki ba.Idan kin yarda da
wannan sharadi na baki izini ki debi dakarun anwa
yanzu ki tafi.Koda jin wannan batu na shugaba
Sharwan Sai hankalin Siyama ya dugunzuma ainun
saboda tasan abinda yake nufi bazai taba yafe
mata
ba,yana nufin cewa zai datse duk wata alaka dake
tsakaninsa da ita tamkar ma bai taba sanin
taba,amma saboda ki fadi da tashin karayar zuci
irin
ta Siyama sai taki nuna tashin hankalinta a fili
kawai
ta dubi shugaba Sharwan cikin murmushi tace na
yarda da wannan sharadi naka ya shugabana.Tana
gama fadin hakan sai ta waro wadannan dakaru na
musamman guda dari biyu tayi musu umarnin suje
su shirya cikin gaggawa.Nan take kuwa suka
sanya
bakaken tufafi suka rufe ko'ina na jikinsu
idanunsu,bakinsu da hancinsu kadai ake gani.Wani
irin talakarma suka sa a kafafunsu masu taushin
gaske,gami da duhu yadda komai suka daka baza
aji
sautin sahunsu ba sannan a jikin kowanne daya
daga cikinsu akwai wadansu kananan wukake
masu
azabar kaifi da tsini sirara guda dari.Haka kuma
suna dauke da kwari boye a bayansu mai cin
kibiya
dubu da kuma karamar baka rataye a bayansu da
kuma sharbebiyar takobi.Sudai wadannan dakaru
an
basu horo na musamman wanda yasa suka kware
ainin a wajen iya kisan mummuke.Bayan
wadannan
dakaru sun gama shirinsu sun jera akan layi sahu
biyu,sai ga Siyama ta fito daga cikin tantinta itama
tayi shiga iri daya da tasu.Al'amarin daya baiwa
kowa mamaki kenan a sansanin domin ba a taba
ganinta ba a cikin irin wannan shiga,kuma babu
wanda ya san cewa ita ma tana da horo irin na
wadannan dakaru.Nan take Siyama ta karaso
gaban
Shugaba Sharwan ta bukaci yasa nata
albarka,kuma
ya nema mata sa'a a wajen iyaye da kakanni
saboda
su dai wannan kabila ta Sharwan basu da wani
addini guda da sukyi imani dashi face iyayensu da
kakaninsu amma dai suna aiki da tsafi ko
sihiri.Nan
take Shugaba Sharwan ya dafa bayan Siyama kuma
ya sumbaci goshinta yasa mata albarka,kuma yayi
mata addua.Nan take Siyama taji wani irin
gagarumin karfin gwiwa ya shige ta.Kuma taji
dukkan tsoro ya kau daga cikin zuciyarta.Ba tare
da
bata wani lokaci ba sai Siyama taja wadannan
dakaru suka falfalwa da gudu izuwa cikin daji suna
yin wani irin gudu na ban al'ajbi tamkar giftawar
tauraruwa mai wutsiya,kafin kace wani abu tuni sun
kule uma sun bace a cikin duhun daren.Saida su
Siyama sukayi 'yar doguwar tafiya ta yan dakiku
masu yawa tana kan gaba sannan ta tsaya cak
suma
dakarun guda dari biyu sai sukayi cirko cirko a
bayanta.Siyama ta tsuguna kasa ta kara kunnenta a
kasa tayi sauraro dan kadan sannan ta mike tsaye
zumbur ta yafito dakarun su duka sukayi mata
kawanya,tayi musu radar wata magana.Nan take
dakarun sukayi wani sihiri su duka a lokaci
guda.Kawai sai kasa ta tsage suka shige cikinta
kuma kasar wajen ta koma ta hade kamar wani abu
bai taba faruwa ba a wajen.Itama Siyama ta shige
cikin kasar ta kule.Faruwar hakan keda wuya da
kimanin tsawon rabin sa'a saiga dakarun birnin
Darul Hunam su da yawa bisa dawakai dauke da
muggan makamai sun iso daidai wannan wuri.Da
isowarsu sai shugaban nasu ya daga hannu ya
tsaya.Take sauran yaran nasa ma suka ja linzamin
dawakansu,dawakan sukayi turjiya da
haniniya.Shugaban dakarun ya shaki kamshi har
sau
uku yace,tabbas zuga ta bil'adama ta tsaya a
nan.Kafin ya gama rufe bakinsa sai sukaji kasar
wajen ta kama tsagewa,dawakansu na ruftawa
ciki.Kafin dayansu yayi wani yunkuri duk an wurgo
musu wukake masu tsani sun caccake su a wuya
da
makogwaro.Nan fa suka rinka sulalewa kasa daga
kan dawakansu suna bajewa kasa matattu,kafin
kiftawar ido su duka sun zama gawa,sauran
shugabansu shi kadai a tsaye jikinsa na karkarwa
yana waige waige da dube dube,amma baiga
wanda
yayi musu wannan barna ba.Bazato ba tsammani
kuma sai yaga kasar ta kara tsagewa,sai ga dakaru
na fitowa sama daga cikin karkashin kasa su dari
biyu suna yi masa kawanya.Saida suka gama
fitowa
gaba dayansu sannan na cikon dari biyu da daya
ya
fito,kuma ba wani bane face Siyama.Kafafunta na
dira kan kasa saita durfafi shugaban wadannan
dakaru kai tsaye tana rike da sharbebiyar takobi,a
lokacin dashi kuma ya nutsu ya daina tsoron
komai
ya kura mata idanu kawai yana mai sadudar jin
kaifi
ya ratsa shi.Bisa mamaki sai yaji Siyama ta dora
fadin takobin akan kafadarsa sannan ta dubeshi
cikin
murmushin mugunta tace shin kana da iyali?
Mutumin yace kwarai kuwa inda da mace daya da
'ya daya.Siyama tayi murmushin murna tace nasan
zaka so ka koma garesu a raye,don bazasu so su
rasaka ba,kaima bazaka so ka rasa su ba.Idan
kabi
umarnina da dokokina zaka koma garesu a raye
kuma cikin koshin lafiya,amma fa idan ka sabawa
umarnina da dokokina ko
gawarka ma iyalin naka bazasu shaidata ba.A
yanzu
inason ka yi mama jagowa mu koma har izuwa
cikin
birninku kuma har cikin gidan sarautarku gaban
sarkinku a matsayin mune jama'arka ba a kashe
maka ko yaro daya ba,ka bar sauran yaranka ne a
baya.Kada ka kuskura kayi rawar baki ko ka
munafuncemu yadda asirinmu zai tonu.Idan kayi
haka tabbas a bakacin ranka.Koda gama fadin
hakan
sai Siyama ta dubi dakarun nata tayi musu
alama,nan take suka tube kayan matattun dakarun
suka sanya,kuma suka dau makamansu suke haye
kan dawakansu.Ita kuma Siyama sai tayi irin shiga
irin wannan,sannan tasa wannan shugaban
dakarun
ya hau nasa dokin itama ta hau dokin suka jera da
ita dashi.Sauran dakarun nata na biye dasu a
baya.Babu abinda zai baka mamaki a cikin wannan
hikima da Siyama tayi face yadda ta shirya
dakarun
nata girman jikinsu yazo iri daya dana dakarun da
suka kashe masu bin wannan shugaba a baya.Ita
kanta sai gashi jikinta yazo iri daya dana
mataimakinsa kai kace wancan din ne wanda aka
kashe.Karkakara Kaka.Laifin dadi karewa.Muje ga
littafi na biyar don jin ci gaban wannan kasaitaccen
labari.Sai mu hadu a 5 gobe gaba dayansa Insha
Allah.Dama kamar yadda na fada 1-5 ne ya fito.
Seriously Ina Bukatar Addu'ar ku.Don Allah a taimaka a
sakani a ciki akan Allah ya cikan wasu bukatu na.
GUDUN TSIRA
Littafi na hudu
Na Abdulaziz Sani m gini
Ebook creator:- Shuraih 99%
For more adventure hausa ebooks visits our wepsite www.shuraih.waphall.com

Domin samun wasu littatafan yaki a matsayin ebooks sai ku ziYarci shafinmu akan www.shuraih.waphall.com


˙ūGUDUN TSIRA 5
Littafi na biyar
Na Abdulaziz sani madakin gini
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani madakin gini

HAKA DAI SU SIYAMA suka ci gaba da tafiya a cikin
shigar dakarun birnin darul Hunam,har suka iso
birnin.Da isowarsu bakin kofa sai daya daga cikin
masu gadin kofar ya dauki fitila ya bude wata yar
karamar taga a jikin kofar wacce ta kasance ta karfe
ya haska.Koda yayi arba da fuskar sadauki Samhur
wanda shine ya jagoran dakarun da suka fita dazu
sai yayi murmushi ya bude kofar.Nan take su
Siyama suka kunna kai izuwa cikin birnin.Kwatsam
sai sukaga wasu dakaru masu yawa sun taso musu
sunyi musu kawanya suna masu ritsa su da
makami.Daya daga cikin dakarun ya dubi sadauki
Samhur yace,yaya dazu ka fita tare da dakaru
kimanin dubu uku,amma yanzu ka dawo da yan
tsiraru,kayi bayani mu ji idan bamu gamsu ba
yanzun nan zamu kaddamar daku.Koda jin wannan
batu sai sadauki Samhur ya dakawa mai maganar
tsawa yace kai Zambaru shin ka sami tabin
kwakwalwa ne?Ya za ayi na dawo tare da dakaruna
gaba daya alhakin harin sumame muka kai don
gamawa da yan kabilar Banu Hanzar?Ai mun isa har
can sansaninsu mun tarwatsa su sun gudu,kuma
sun bazama izuwa cikin daji.A dalilin hakane na bar
dakaruna a can suka lallabe domin idan suka dawo
su gama dasu.Yanzu na dawo ne da tsirarun yarana
domin na sanar da gwamna halin da ake ciki,saboda
asan matakin da ya kamata a dauka a gaba.Lokacin
da Zambaru yaji wannan batu

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment