Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suyi MUTUWAR KASKO.Koda
ya
kawo mata sura sai ta sunkya ta shige ta karkashin
kafafunsa ta dako gadon bayansa da kafafunta ta
baya,kawai sai ya fadi kan katakon karyayyen
wannan gado.Take wani icen gadon ya tsireshi a
ciki
ya hudo ta gadon bayansa.Sarki Ruguzan ya rinka
kwarara uban ihu da kururuwa sannan idanunsa
suka kafe,jikinsa gaba daya ya sandare ya zama
gawa.A sannan ne Siyama ta mike tsaye tana layi
sakamakon jinin dake zuba a gefen kanta saboda
 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~ 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~naushin da Sarki Ruguzan yayi mata dazu ya tsaga
mata kanta kuma har sannan hancinta bai daina
yoyon jini ba.Hakika ita kanta Siyama bata taba
zaton cewar zata tsira ba daga sharrin Sarki
Ruguzan ba,kawai ta saida ranta ne akan ko tayi
nasara kota rasa rayuwarta.Lokacin da Sarki
Ruguzan yayi mata wannan naushi a fuskar ta ta
kife
kasa ba suma tayi ba,amma ta fita daga cikin
haiyacinta saita dauke numfashinta tayi kamar
suman tayi.Damar datayi amfani da ita kenan ta
shammaceshi ta zaro wannan kashi daga cikin
aljihun wandonta cikin bakin zafin nama ta soka
masa a makoshinsa.Lokacin da Siyama ta dubi
gawar Sarki Ruguzan ta tabbatar cewar ta mutu sai
tayi murmushin farin ciki amma data juyo ta dubi
kofar gidan ta tabbatar da cewar bazata iya budeta
ta
fita ba sai hankalinta ya dugunzuma ainun sannan
ta
dubi ko ina a cikin gidan taga babu ta inda zata
iya
fita sannan ta tuno cewar idan fa aka sake jimawa
akaji shiru za a bude kofar dakaru su shigo,in
kuwa
aka shigo aka ga ta kashe Sarki itama rubdugu za
a
yi mata a kasheta kuma tabbasa sarkin yawa yafi
sarkin karfi.Kuma bayan an kasheta za a bi sawun
dukkanin jama'arsu a hallakasu.Koda tazo nan a
tunaninta sai hankalin ya kara dugunzuma fiye da
ko
yaushe ta rasa abinda ke mata dadi a duniya,nanfa
ta kama kai kawo a cikin gidan tana mai ci gaba
da
kalle kalle da tunani.Tana cikin hakane ta daga
kanta
ta kallo rufin saman gidan saita ga ashe na katako
ne.Nan take farin ciki ya lullubeta kawai saita daka
tsalle sama ta kama rufin tayi ta tafiya a kansa da
hannayenta da kafafunta tamkar kadangaruwa har
saida ta iso wani wuri inda ta dan hango hasken
wata yar karamar huda sannan tasa hannunta ta
doki
wajen take katakon daya rufe wajen ya burme.Tana
zura kanta ciki ta shigo sai gashi ta fito a saman
gidan.Cikin sauri tayi ruf da ciki akan rufin saman
domin dakaru ta hango suna takai kawo a ko ina
cikin gidan sarautar don tabbatar da tsaro.Saida ta
shafe yan dakiku a kwance a saman ginin sannan
taga dakaru sun rarrabu saura mutum daya jak a
wani sako.Cikin hanzari ta daka tsalle ta duro a
bayan wannan badakare ta murde wuyansa ya
sulale
kasa matacce,kawai sai ta jashi izuwa cikin wani
sako mai duhu ta cire kayan jikinsa tayi canji da
nata,kawai sai ta bude wani kwandon shara na
karfe
ta jefa gawar badakaren a ciki ta rufe kawai sai ta
fito
daga cikin sakon ta kunna kai izuwa hanyar fita
daga gidan sarautar gaba daya kai tsaye ba tare da
shakkar komai ba ta saje a cikin dakarun gidan
sarautar masu fita.Duk da cewar ta saje da
dakarun
zuciyarta sai bugawa takeyi da karfi domin gani
take
yi kamar a koda yaushe asirinta zai iya tonuwa a
gane ko wacece ita.Wani iko na Allah kuma ta
gaban
wannan
hadimi daya kaita inda Sarki yake ta wuce harma
suka hada idanu amma bai shaidata ba.A Wannan
lokaci hadimin ya kagu yaga Sarki ya bude kofar
wannan gida ya fito amma sai yaji shiru.A wannan
lokacin ji yake kamar ya bugawa sarki kofa amma
saboda tsoron kada yayi laifi shi yasa bai buga
kofar
ba kuma yayi tunaniin ko har a sannan sarko bai
gama more rayuwarsa ba da Siyama.Har Siyama ta
iso bakin kofar karshe ta gidan Sarautar babu
wanda
ya tareta,amma tun kafin ta iso bakin kofar taga
masu gadin su hudu sun kura mata idanu suna yi
mata kallon rashin sani da rashin yadda.Nan take
Siyama ta gane cewa lallai idan ta karaso bakin
wannan kofa baza'a barta ta fita ba sai an
binciketa,in kuwa aka binciketa sai an gano wacece
ita.Koda ya rage baifi taku uku bata riski masu
gadin
sai ta daka tsalle sama ta makesu da kafafunta su
duka hudun a fuskokinsu a lokaci guda suka zube
kasa sumammu.Ai kuwa dakarun dake bayanta
suka
hango abinda ya faru suka falfalo da gudu,itama
Siyama tana durowa kasa bisa kafafunta sai ta
falfala
da azababben gudu na ban al'ajabi ta fice gaba
daya
daga cikin gidan sarautar.A sannan ne fa dakaru
suka bita duu!suna ihu suna harba mata
kibiyoyi.Idan mutum yaga yawan dakarun da suka
bi
bayan Siyama suna son su kure mata gudu,kuma
mutum yaga irin ruwan kibiyoyin da ake yi mata
dole ne yayi rantsuwa cewa babu yadda za'ayi ta
tsira da rayuwarta.A can kofar wannan gida na
cikin
gidan sarautar wanda Siyama ta kashe Sarki
Ruguzan a cikinsa.Koda wannan hadimi yaga
dakarun gidan sarautar gaba daya sun rude suna
ihu
kuma sun ruga izuwa can kofar fita daga gidan sai
shima ya dimauce yayi zargin ko Siyama ce yabi
ta
wata hanyar daban ta gudu,don haka hannunsa na
karkarwa yasa kuba ya bude kofar yaja wadansu
dakaru masu yawa suka ruga izuwa cikin
gidan.Suna
isa inda gadon nan na sarki yake sai suka iske
gawar Sarki Ruguzan soke a jikin katakon
gadon.Koda sukayi arba da gawar sai kowa ya
firgita
ainun kuma suka cika da tsananin mamaki.Nan
take
wannan hadimi ya kurma uban ihu mai tsananin
firgitarwa ya dakawa dakarun dake bayansa tsawa
yace maza kuje ku gayawa sarki yaki cewar 'yar
shugaba Sharwan ta kashe sarki kuma ta gudu.Nan
take wadannan dakaru suka juya da baya da gudu
shi kuma sai ya fara kokarin cire gawar daga jikin
katakon da take tsire.Saida aka shafe sa'a uku da
rabi ana tseren gudu tsakanin Siyama da
wadannan
dakaru su basu cimmata ba ita kuma ba ta bace
musu ba,tun ana cikin birnin kisra har aka shiga
cikin daji.Babu abinda ya daurewa dakarun kai yayi
matukar basu mamaki face ganin yadda Siyama ta
tsallake harin ruwan kibiyoyin da ake yi mata ta
sama da kasa kai kace aikin sihiri ne.Koda aka
shiga
cikin wani daji wanda Siyama ta saba yin farauta a
cikinsa tun tana yarinya karama ta lakanceshi
ainun
sai ta fada cikin wani surkuki mai yawan
duhuwoyi,hanyoyi barkatai gami da koramai da
kwazazzabai da kuma manyan ramuka da ciyoyin
fadamomi da koramu.Tana shiga cikin wannan
surkuki sai dakarun suka nemeta sama da kasa
suka
rasata tamkar anyi ruwa an dauke.Amma saboda
naci har gari yayi duhu Dakarun basu bar dajin ba
suna ta neman Siyama a cikin kowanne sako da
lungu har cikin kogon duwatsu shiga suke suna
haska ko ina da fitilun itatuwa.A karshe dai ba
basu
ganya ba sai sukayi hakurin dole suka koma izuwa
can gidan sarautar.Suna zuwa ne suka iske gidan
sarautar a cike da mutane ana gabatar da jana'izar
sarki Ruguzan.Da yawa daga cikin mutanen garin
murna sukeyi bisa mutuwar sarki Ruguzan saboda
tsananin mulkin zaluncin da yake yi musu,to
amma
saboda tsoron dan'uwansa Yarima Darwaz wanda
shine zai gaji karagar mulkin babu wanda ya nuna
farincikinsa a fili.
Babu wanda ya nuna farincikinsa a fili.A wannan
lokaci tuni an binne Sarki Ruguzan a cikin
kabarinsa,yarima Darwaz ya kwanta akan kabarin
yana ta faman rusa kuka da ihu.Da kyar da sidin
goshi fadawa suka bashi baki suka lallabeshi ya
tashi daga kan kabarin.Yarima Darwaz da Sarki
Ruguzan sun kasance uwa daya uba daya,kuma
yarima Darwaz ya girmi sarki Ruguzan,asali ma
shine ya kamata ya hau kan karagar mulki amma
saboda tsananin son da yake yiwa dan uwan nasa
Ruguzan ya hakura ya bar masa sarautar.A takaice
dai a duniya babu abinda Yarima Darwaz yakeso a
duniya sama da Sarki Ruguzan,don haka a wannan
rana yana cikin tsananin bakin ciki wanda ba zai
iya
misaltuwa ba kuma gashi ya kasance mutum mai
bakar zuciya gami da rashin imani fiye da Sarki
Ruguzan,don haka a wannan rana hatta fadawan
kasar ma a tsorace suke dashi suna baya baya
don
gudun kada ya huce haushinsa a kansu.Lokacin da
wadannan dakaru masu wadanda suka tafi neman
Siyama suka dawo sai suka zube kasa agaban
Yarima Darwaz suka sunkui da kawunansu kas aka
rasa wanda zaiyi bayanin cewar ba aga Siyama ba
wacce ta kashe Sarki Ruguzan.Koda Darwaz yaga
haka sai ya kara fusata ainun ya yunkura da sauri
ya
zare takobinsa da nufin ya hau Dakarun da
sara,kawai sai yaji an daka masa tsawa.A fusace
ya
waiga,koda yaga wanda yayi masa tsawar sai
jikinsa
yayi sanyi ya sauke takobin tasa kasa cikin sanyin
jiki.Ba wani bane yayi masa tsawar ba face
matarsa
ZUMAIRA.Zumaira ya karaso gaban Darwaz ta
karbe
takobin dake hannunsa ta dubeshi tace,idan ka
kashe wadannan dakaru bazaka sami sakamakon
komai ba face na dadin bacin rai da bakin ciki
tunda
asarace ga masarautarmu.Tunda dai Sarkin yaki da
manyan zakwakuran dakarunsa sun bi bayan
wannan Yarinya na tabbatar da cewar sai ka yanke
mata hukuncin daya dace da laifin data tafka.Koda
Zumaira tazo nan a zancenta sai Yarima Darwaz ya
zubar da hawaye sannan ya matsa gaban kabarin
dan uwan nasa ya dafashi yace,Na rantse da
kaunar
da nake yiwa Sarki Ruguzan sai nayiwa Siyama
mugun kisan gilla irin wanda ba a taba yiwa wani
mahaluki ba a doron kasa,kuma sai na shafe gaba
dayan kabilarsu daga kan doron kasa yadda har
abada ba za a sake tunowa dasu ba.Koda fadin
hakan sai Darwaz ya sake kwantawa akan kabarin
Sarki Ruguzan ya fashe da sabon matsanancin
kuka
har saida Zumaira tazo ta tasheshi tsaye ta shiga
rarrashinsa ta jashi izuwa cikin gidan Sarautar
sannan kowa ya kama gabansa.

SARKIN YAKIn birnin kisra basu dawo daga bin
sawun Siyama da jama'ar kabilarta ba sai bayan
kwana uku.A wannan lokaci ma tuni anyi bikin
nadin
sarautar Sarki Darwaz ya hau karagar mulki amma
a
tsawon kwanaki ukun Sarki Darwaz bashi da wani
sukuni da kwanciyar hankali,burinsa kawai yaga
sarkin yaki ya dawo tare da Siyama.Da rana tsaka
su Sarkin yaki suka shigo fadar birnin kisra suna
shigowa fadar suka iske Sarki Darwaz zaune bisa
karagar ya sunkui da kansa kas,gashi ana ta tafiyar
da harkokin mulki amma shi Sarki Darwaz yayi
shiru
kamar bashi ne sarkin ba domin fadawa ne suke
zartar da komai.Koda Sarki Darwaz yaji sawun
dakaru da yawa sun shigo cikin fadar saiya dago
da
kansa da sauri amma dayaga sarki yaki akan gaba
babu Siyama a tare dashi sai jikinsa ya kama
tsuma,zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone
saboda tsananin fushi.Sarkin yaki ya zube kasa
gaban sarki Darwaz bisa guiwoyinsa yana mai
sunkui da kansa kas yace,ya shugabana munbi
sawun Siyama har izuwa sansaninsu a daji inda
muka isle babu ko kaza a wajen sun kwashe komai
nasu sunyi hijira.Mun sake bin sawunsu izuwa
cikin
dajin har tsawon kwanaki biyu amma ko duriyarsa
bamujiba domin sawunsu dana dabbobinsu ma ya
dauke.Al'amarin dayayi matukar bamu mamaki
kenan tamkar aikin sihiri.Koda sarkin yaki yazo na
a
zancensa sai sarki Darwaz ya mike tsaye a fusace
ya kwarara uban ihi wanda ya firgita kowa a cikin
fadar.Faruwar hakan ke da wuya sai ga Bokan
Garin
wanda ake kira HURGAS IBINI SALBARU ya bayyana
tsulum a tsakiyar fadar.Hurgas ya karasa gaban
Sarki Darwaz suka kurawa juna idanu sannan Boka
Hurgas ya risina yace Ya shugabana,Siyama da
sauran jama'arsu suna nan a cikin yankin kasarka
sun saje da mutane a cikin daya daga cikin
biranenka,bisa wannan dalili ne yasa ba a gano
inda
suka ba.Idan har ka bari suka fice daga cikin
wannan nahiya tofa har abada baza a dauki fansa
akansu ba kuma komai daren dadewa sai Siyama
ta
dawo kasar na ita da jama'arta ta rushe mulkinmu
sun karbi karagar kasar bisa taimakon wata
hatsabibiyar jaruma wacce zata addabi gaba dayan
sarakuna da attajiran duniya.Koda Boka Hurgas
yazo
nan a zancensa sai hankalin Sarki Darwaz ya
dugunzuma ainun fiye da ko yaushe ya dubi
Hurgas
cikin alamun tsananin damuwa yace,yakai abin
dogarona iyaye da kakanni maza ka sanar dani
birnin da su Siyama suke domin nayi shiri da
kaina
na jagoranci dakarun yaki masu yawa muke mu
shafesu daga doron kasa.Koda jin wannan batu sai
Boka Hargus yayi ajiyar zuciya cikin alamun
karayar
zuciya yace,ai nayi iya kokarina domin na gano
inda
suke amma na kasa saidai kawai na sami nasarar
ganowa cewa suna bangaren gabashin kasar
nan.Don haka ku hanzarta tunkarar dukkanin
manyan birane da suke gabas har izuwa karshen
iyakarmu.Koda jin wannan batu sai Fuskar Sarki
Darwaz ta fadada da murmushi na farinciki nan
take
ya dubi Sarkin Yaki Amzad yace maza kaje ka
shirya
mana sabuwar runduna ta mayaka dubu dari uku,ni
da kai zamu jagorancesu izuwa gabashin kasar
nan
kuma tun kafin mu tafi inason a tashi manzanni su
tafi izuwa biranen dake karshen iyakokinmu a
gayawa
shugabanninsu cewar su rufe kofofin garuruwansu
yadda ba shiga ba fita har sai na aiko da umarni.A
sannan ne fada ta watse kowa ya kama
gabansa.Har
Sarki Darwaz ya jiya zai shiga cikin gidan sarautar
saiya juyo da sauri ya dubi Boka Hurgas a cikin
alamun damuwa a karo na biyu yace,yakai abin
alfaharin birnin kisra waishin wace shu'umar
budurwar jarumar da idan ta hadu da Siyama zata
taimaketa har ta rushe mulkinmu?Koda jin wannan
tambaya sai boka Hurgas yaja dogon numfashi
gami
da ajiyar zuciya sannan yace hakika kayi tambaya
mai kyau kuma mai muhimmanci saidai a yanzu
babu isasshen lokaci wanda zai isa na baka labarin
wannan shu'umar jaruma wacce daidai take da
GUGUWAR ZAZZAGAR BALA'I ga dukkan sarakunan
duniya.Shawarar da zan baka kawai itace kayi
hakuri
zan baka labarin wannan jaruma ko da akan
hanyarmu ne ta dawowa bayan mun sami nasarar
gano inda su Siyama suke mun shafesu daga
doron
kasa.
A WANE HALI 'YAN KABILAR SU SIYAMA SUKE
CIKI?
SHIN SARKI DARWAZ ZAI CIKA BURINSA?
INA LABARIN SIYAMA DA TAKE GUDUN TSIRA?
SHIN
ZATA KOMA CIKIN KABILARTA?
A WANE HALI MAHAIFINTA DA MAHAIFIYARTA
SUKE
CIKI?
INA LABARIN ABOKAN TAFIYARTA DATA
UMARCESU
SUYI GABA,A WANE HALI SUKE CIKI?
Mu hadu a GUDUN TSIRA kashi na uku don jin
cigaban wannan kasaitaccen labari.
Da alamu littafin bai karbu ba ko Dan ba samun
comments.
Barkan ku da Sallah.Allah ya maimaita mana.Ameen.
Gudun tsira
Littafi na biyu 2
Na Abdulaziz sani m gini
Ebook creator::- Shuraih 99%
You can download more hausa novels ebooks At http://shuraih.waphall.com
Zaku iya downloading na wasu littatafan mu amatsayin ebook ta hanyar latsa wannan blue din rubutun www.shuraih.waphall.com

GUDUN TSIRA
Littafi na Uku
Na Abdulaziz Sani m gini
Ebook creator:- Shuraih 99%
For more adventure hausa ebooks visits our wepsite www.shuraih.waphall.com

Domin samun wasu littatafan yaki a matsayin ebooks sai ku ziYarci shafinmu akan www.shuraih.waphall.com

&GUDUN TSIRA&
Littafi Na Uku(3)
Part A
&A-H Physicist&
KODA JIN WANNAN BATU NA BOKA hurgas sai
Sarki
Darwaz ya dubi hurgas cikin matukar mamaki
yace,au dama tare da kai zamu tafi neman Siyama
da jama'arta?Boka Hurgas yace kwarai kuwa ai na
fika tashin hankalin idan har ban tabbatar da
mutuwar Siyama ba da jama'arta saboda in dai
wannan lokaci yazo to duk wani Boka dayake
wannan nahiyar ma sai sun kashe shi sun shafe
harkar tsafi gaba daya tamkar ba a taba yinta ba a
wannan nahiyar,duk cikin bincikena na ga wannan
al'amari.Sa'adda sarki Darwaz yaji wanann batu sai
ya gyada kai yace ai kuwa indai muka hada karfi
da
karfe mu ta kai dole ne muga bayan wadannan
makiyan namu.Yanzu zan shiga cikin gida nayi
shiri
in yaso ka samemu a can kofar fada inda zamuyi
zuga mu tafi gaba daya.Lokacin da boka Hurgas
yaji
wannan batu saiya bushe da dariya sannan yace
aini
bana bin zugar mutane saidai ku riskeni a can
gaba
ko hanya ina jiranku.Nine zan zamo mai yi muku
jagora har mu riski abokan gaba tunda nine zanfi
kowa saurin gano inda abokan gabar suke.Koda
gama fadin sai boka Hurgas ya bace bat daga cikin
fadar tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen.Koda
ganin hakan sai sarki Darwaz ya ruga izuwa cikin
gidan sarautar ya iso cikin ainihin turakarsa ya
shiga
kimtsa kansa yana sanya kayan yaki.Yana cikin
wannan haline matarsa Larisa tare da 'yarsa
gimbiya
Husaira suka shigo cikin turakar da sauri cikin
tsananin tashin hankali.Husaira ta kasance
kyakkyawar budurwa abar kwatance domin da
kadan
Siyama zata fita kyau.Ga wanda ma bai iya
tantance
kyawu ba cewa zaiyi sunyi kunnen doki.Lasira da
Husaira suka sha gaban Sarki Darwaz idanunua
cike
da kwalla suna shirin fashewa da kuka.Kawai sai
Lasira ta kama kafadun Darwaz ta rike a lokacin da
hawaye ya zubo mata ta dubeshi tace,haba yakai
mijina saboda me zaka bar karagar mulkinka ka
tafi
farautar kabilar Banu Hanzar alhalin baka da
tabbacin
ganinsu tunda sunyi hijira sun gudu.Kayi sani
cewa
zata iya yiyuwar cewa tuni ma sun fice daga cikin
nahiyar nan gaba daya.Ka tuna cewa fa kwananka
uku kacal akan karagar mulkin nan,Idan har wani
tsautsayi ya sameka a cikin wannan tafiya shike
nan
fa ka rasa karagarka nida 'yarka kuma rayuwarmu
ta
shiga cikin hadari kenan tunda ka san cewa kana
da
makiya da yawa a cikin majalisar garin nan da
cikin
jama'ar gari.Lokacin da Lasira tazo nan a zancenta
sai Sarki Darwaz ya bushe da dariya,al'amarin
dayai
matukar baiwa Larisa mamaki da haushi kenan,ta
kura masa idanu,ita kuwa Husaira sai ta sunkui da
kanta kas tana zubar da hawaye kawai.Daga can
sai
Darwaz ya tsuke bakinsa kuma ya hade fuska ya
dubi Lasira yace,yake matata yanzu ke ashe har
kina
tunanin cewa wani abu zai iya taba lafiyata a
wannan
fita da zanyi?Ashe kin manta da cewa ni mutum ne
mai tsananin sa'a da rabo bisa dukkan abinda na
sa
agabana?A iya saninki dani tun muna matasa wane
abune kika taba ganin ya gagareni?Larisa ta girgiza
kai tace duk abinda kasa agabanka sai kaga
bayansa
amma wannan karon naji a jikina cewa lallai zaka
riski matsala kasancewar mai Laya ya kiyayi
zamani.Darwaz ya gyada kai cikin murmushi
yace,ai
ko Giwa ta fadi tafi karfin karnuka su dasa mata
wawa sai a sannu.Kada ki manta cewar 'yarki
Husaira ta gadoni a jarumtaka gani da taurin
zuciya,don haka ko babu ni dole ne ayi shakkarki
saboda ita kuma itace zata gaji karagata.Ke
Husaira
mene dalilin da yasa kike zubar da wannan hawaye
daga idanunki?Shin kina tsoron kada na fita ne
wani
tsautsayi ya sameni?Koda jin wannan tambaya sai
Husaira ta dago kai ta dubi sarki Darwaz cikin
murmushi tana mai share hawayenta tace,ko kadan
ni bana tunanin akwai wani mahaluki ko wani
tsautsayi da zai sameka.Ina zubar da wannan
hawaye ne saboda kawai takaicin kace bazaka tafi
tare dani ba.Ka sani cewa a rayuwata ban taba fita
yaki ba na daukar rayukan bil'adama da
yawa.Wannan ce kadai damar da nake da ita
wacce
zan gwada tsantsar iyakar jarumtakata kuma a
yanzu
ne takobina za ta sami damar shan jini mai yawa
ta
more,amma gashi ka hana.Ina mai rokonka don
darajar iyayenka da kakanninka wadanda suka
shude kayi mini izini yanzun nan naje na kimtsa
cikin gaggawa ayi wannan tafiya dani.Ka tuna cewa
ni kaina jarumtakata ta ninka ta marigayi sarki
Ruguzan sau uku,bare kai kanka.Ai abin kunya ne
ma ace kaine da kanka zaka tari Siyama ka
yaketa,ni
ya kamata ka barni da ita a matsayina na 'ya mace
kamarta nayi mata kisan gilla na ciro kanta nazo
maka dashi.Lokacin da Husaira tazo nan a
zancenta
sai mahaifiyarta ta shara mata mari ta dubeta a
fusace tace,yanzu ke dama manufarki kenan,ashe
ban sani ba?Wato zuciyarki ta kekashe ta zama irin
ta ubanki kin gadoshi da rashin imani da tausayi
alhalin kina matsayin 'ya mace wacce nake son
tayi
aure ta bar mini zuri'ar dazanyi alfahari da ita mai
farin jini a cikin al'umma?Koda Larisa tazo nan a
zancenta sai Husaira da Sarki Darwaz suka duni
junansu suka bushe da dariya.Husaira ta hade rai
ta
dubi Larisa tace yake ummina ki sani cewa kyan
'da
ya gaji ubansa,idan mai mulki yana son ya sami
karfi da biyayyar talakawansa dole ne ya kasance
mara tausayinsu.Ni SARAUNIYAR GOBE ce wadda
take da burin dama yafi na mahaifinta don ni so
nake na mallaki duk kasashen dake nahiyar nan
gaba daya su zamo a karkashin mulkina.Koda jin
wannan batu sai Sarki Darwaz da Larisa suka
kurawa
Husaira idanun cikin tsananin kaduwa da
mamaki,daga can sai Sarki Darwaz ya bushe da
dariyar farinciki yace,tabbas yaune na san cewa
banyi haihuwar banza ba tabbas na sami irin 'yar
dana dade ina mafarkin samu.Koda gama fadin
hakan sai Sarki Darwaz ya rungume Husaira cikin
murna yana
A*H PHYSICIST
maicewa,jeki ki shirya yake 'yata
lallai tare dake zamu tafu wannan gagarumin
yaki.Kafin Sarki Darwaz ya gama rufe bakinsa tuni
gimbiya Husaira ta ruga izuwa cikin turarkata.Ita
kuwa Larisa saita durkushe a kasa ta fashe da
kukan
bakinciki.Ko kallonta Sarki Darwaz baiyi ba ya
gama
shirinsa ya zuba dukkanin makamansa na yaki a
jikinsa sannan ya fice daga cikin turakar ya bar
Larisa a zaune a kasa dirshen tana rusa
kuka.Wannan shine abinda ya faru a cikin birnin
Kisra bayan Siyama ta sami nasarar kashe Sarki
Ruguzan da kyar da sidin goshi domin ta kawo
karshen mulkin zaluncin da yakeyi a nahiyar
harma
jama'arsu su sami damar gudanar da rayuwarsu a
cikin daji a kwanciyar hankali.Abinda bata sani
bashine ALLURA TA TONO GARMA,domin babu
wani
sauki talakawa zasu samu face karin
matsawa,talauci
da fatara wacce sai sun gwammace mutuwarsu
akan
rayuwars a doron kasa.Kuma ta tsokano tsuliyar
dodon daya shafe shekara da shekaru a kwance
yana faman shara barci kuma ta kulla gabar da ba
a
san ranar karshenta ba.

AL'AMARIN JARUMA SIYAMA KUWA,lokacin da ta
samu ta fice daga cikin gidan sarautar sarki
Ruguzan
tayi ta gudu a cikin daji har ta isa inda ta bacewa
dakarun birnin Kisra,ashe cikin wata korama ta
shige
tayi nutso izuwa karshenta ashe akwai wata
barauniyar hanya a kasan koramar nan wacce ta
bulle har izuwa cikin wani kogon dutse wanda yake
a cikin wani daji daban dake nesa sosai.Koda tayi
doguwar ninkaya a kasan koramar ta tabbatar da
cewar ta iso cikin wannan kogo sai ta taso izuwa
saman ruwan ta shaki numfashi kuma ta tsaya ta
dan huta sannan ta cigaba da tafiya a cikin ruwan
har saida ta iso karshen katon kogon dutsen ta
cikin
wani dan karamin rami wanda mutum bazai taba
tsammanin cewar za'a iya ficewa ta cikinsa ba.
Tana fita daga cikin kogon ta tsinci kanta a cikin
wannan katon daji wanda tace jama'arta su
jirata.Nan take ta kama waige waige da kalle kalle
cikin tashin hankali tana zargin ko wani abu ya
sami
jama'arta ne?Nan take tayi wani irin fito na inkiyar
da sukeyi a daji a duk sa'adda suka shiga daji
farauta a yayin da suka hango dabbar da suke son
kamawa.Bisa mamaki sai taji an amsa mata da irin
fion nata sai ga wani babban hadimi na mahaifinta
ya fito daga cikin wanu surkuki daya buya ya
dubeta
cikin murna ya yafito ta da hannu.Cikin farin ciki ta
ruga izuwa wannan hadimi shima ya juya ya ruga
izuwa wani bangare dabam na dajin.Saida sukayi
tafiya mai tsawo tana biye dashi taga an shiga
wani
sakon daban wanda ma bata taba shigarsa ba sai
taga dajin ya zamo sabo a wajenta.Kwatsam sai ta
an shigo da ita wani sabon tafkeken kogon dutse
wanda ya akai girman gari guda wanda bata taba
sanin wanzuwarsa ba a cikin dajin.Shidai wannan
kogon dutse a karkashin wadansu dogayen
bishiyoyi
yake masu manya manyan ganyaye wadanda suka
lillubeshi babu yadda za ayi mutum yaga wannan
kogon dutse face ya ture ganyayyaki da
bishiyoyi.Suna shiga cikin kogon sai Siyama tayi
arba da gaba dayan mutanen kabilarsu mazansu
da
matansu,yaransu da manyansu.Shugaba Sharwan
ne
kadai a tsaye,amma kowa a zaune yake a kas sun
jeru sahu sahu kuma duk sunyi shiru tsit tamkar
babu mai rai a cikinsu.Koda aka ga shigowar
Siyama
cikin kogon dutsen sai kowa ya kamu da tsananin
farinciki.Nan take Sharwan ya ruga gareta suka
rungume juna yana mai cewa ni san cewar sai kin
dawo a raye gareni.Jikina ya bani cewar bazaki
mutu ba yake 'yata abar alfaharina.Cikin tsananin
farin ciki Siyama ta janye jikinta daga cikin na
Sharwan ta dubeshi cikin mamaki tace,yakai Abba
yaya akayi ka amince da duk abinda na umarceka
da ayi a cikin wasikata.Kuma yaya akayi kuka gano
wannan boyayyan kogo inda Dakarun Kisra bazasu
taba ganowa ba?.Koda jin wadannan tambayoyi sai
Shugaba Sharwan ya bushe da dariya sannan yace
yake 'yata kiyi sani cewa ba wani abu bane yasa
na
bi duk umarnin da kika bani ba acikin wasikar taki
ba face na yarda da kwakwalwarki gami da
tunaninki
da hankalinki baki taba shirya wani abu ba wanda
aka kasa samun nasara ba.Dalilina na biyu wanda
shine ne mafi muhimmanci shine bamu da wani
zabi na samu tsira daga sharrin Sarki Ruguzan
face
mu yanke hukuncin kashe shi kuma muyi hijira ta
zuwa wani dan lokaci kafin a sami sauyin Sarki
mai
adalci...Saidai Kash!Mun saki reshe mun kama
ganye domin sarkin daya hau karagar mulkin
Birnin
Kisra a yanzu masifarsa da bala'insa sun ninka na
Sarki Ruguzan sau goma.Samun azzalumin sarki
kamarsa a duniya sai an tona.Nidai a sanina
Sarki.Darwaz wanda ya kasance yaya ga Sarki
Ruguzan ya tafi wata nahiya dabam ya tare a cikin
daji yana farauta kuma yace bazai dawo gida ba
sai
bayan shekara ashirin,ashe ya dawo birnin Kisra
babu shiri sakamakon wata rashin lafiya da
dan'uwan sa Sarki Ruguzan yayi bara.Ina mai
tabbatar miki da cewar a duniya babu abinda Sarki
Darwaz yakeso sama da dan'uwansa Sarki
Ruguzan
don haka duk yadda zai yi yaga ya dauki fansar
ran
Ruguzan a kanmu sai yayi don haka nasan cewa
da
kansa zai jagoranci dakaru ya fito farautarmu.Dole
ne yanzu muci gaba da tafiya dare da rana babu
sassauci,kuma dole ne mu kiyaye shiga cikin
biranen kasar nan face mun tura 'yan leken
asirinmu
sun gano halin da birnin yake ciki ta hanyar batar
da
kamanninsu izuwa matsayin 'yan gari.Ba zamu
taba
samun kwanciyar hankali ba face mun ga mun fita
daga cikin wannan nahiya gaba daya.Yake 'yata
inason ki sani cewar muna cikin tsananin TSAKA
MAI WUYA dole ne muyi niyar yaki da dukkanin
karfinmu da ranmu kodai mu tsira ko kuma a
shafemu daga doron kasa gaba daya.Lokacin da
shugaba Sharwan yazo daidai nan a jawabinsa sai
hankalin Siyama ya dugunzuma ainun fite da ko
yaushe.Nan take idanunta suka ciko da kwalla
tace,yakai Abbana ka yafeni kai da dukkan sauran
jama'armu hakika na jefamu a cikin masifa.Koda
jin
wannan batu sai Shugaba Sharwan yayi murmushi
yace yake 'yata kiyi sani cewa baki da wani laifi a
wajenmu domin kokin yi abinda kikayi ko bakiyi ba
sai mun shiga cikin wannan tashin hankali da
masifa
tunda tuni Sarki Ruguzan ya jefamu a cikin wannan
tafarki.Inason ki kwantar da hankalinki kuma ki
tattauna da dukkan dakarunmu domin mu san
hanyar da zamubi mu kare kanmu harmu sami
nasarar fita daga cikin wannan nahiyar gaba
daya.Yanzu ba baku rabin sa'a kacal ku gama
dukkanin shirinku domin mu cigaba da tafiya.Koda
jin wannan batu sai Siyama ta kirawo gaba dayan
dakarun nasu suka taru a gabanta,a sannan ne
taga
su Muzaru ashe tuni sunzo sun riski su Shugaba
Sharwan.Saida Siyama da dukkanin Dakarunta
suka
shafe rabin sa'a cif sannan suka kammala
dukkanin
shirye shiryensu,nan take akayi wata dabara aka
lullube jikin kowa da koren ganya,hatta dawakai da
dabbobi saida aka lullubesu da ganyaye yanda ko
kada ba a ganin jikinsu sannan aka fito daga cikin
kogon dutsen aka ci gaba da tafiya,mata suka goya
yara kanan,su kuma tsofaffi da miskinai matasa
suka
goyasu a bayansu akayi ta tafiya cikin sauri sauri
gudu gudu.A ko yauhse dakarun da suka kware a
iya leken asiri suna kan gaba sai sunyi tafiya mai
nisa sun tabbatar da cewar babu wani mugun abu
a
gabansu sannan suke dawowa su bayar da
umarnin
a cigaba da tafiya.A bayan tawagar kuma a ko
yaushe wadansu dakarun leken asiri ne suna
bazuwa gaba da yamma,kudu da arewa don
tabbatar
da cewar ba wanda ya biyo sawunsu.Haka dai aka
ci
gaba da wannan tafiya ba dare ba rana har tsawon
kwana uku ba tare da an gamu da wani mugun
Abu b.&GUDN TSIRA&
Littafi Na uku (3)
Part B
&A-H Physicist&
Ba tare da an gamu da mugun abu ba

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment