Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma duk
sa'adda aka gaji ko lokacin barci yayi sai a nemi wuri mai
huduwar gaske mai
hadarin gaske inda baza a taba zaton cewa wani
abu
mai rai ba zai iya shiga wajen ba,sai a shiga a
kwakkwanta.A safiyar kwana na ukun ne suka
hangi wani babban Birni wanda ake kira MADINATUL
SULTAN a can gaban dajin da suke,tazarar dabata
wuce ziri'a dari da sittin ba.Koda hango wannan
birni na Madinatul Sultan sai kowa ya cika da farin
ciki musamman Shugaba Sharwan.Nan take
Sharwan ya dubi Siyama cikin murmushi yace,yake 'yata
ki sani cewa mun iso birnin Madinatul Sultan
inda zamu iya hutawa har tsawon kwana uku a
cikin
kwanciyar hankali kuma mu kara hada guzuri mai
kyau mu ci gaba da tafiyarmu.Koda jin haka sai
Siyama tayi ajiyar zuciya sannan tace,yakai Abbana kayi
sani cewa nikam bani da kwanciyar hankali a
duk inda zamu shiga,ina mai shawartarmu damu
hakura da shiga cikin birnin Madinatul Sultan
kawai
mu kewaye ta bayan birnin mubi ta cikin daji mu ci
gaba da tafiyarmu.Yayin da Sharwan yaji wannan batu sai
ya girgiza kai yayi murmushi sannan
yace,shin kin manta ne cewar shugaban da yake
mulkin birnin madinatul Sultan abokina ne kuma
aminina?Tun muna yara kanana muka saba a daji
wajen farauta saboda shakuwar da mukayi dashi
ne ma na bashi 'yar kabilarmu guda daya ya aura a
sirrance ba tare da Sarkin Kisra ya sani ba.Akwai
amana da alkawari mai girma a tsakaninmu
dashi,ai
na tabbatar da cewa baza a hada baki dashi ba a
cutar damu ba,kuma ko me ake ciki ma ai yanzu mun
baro dakarun kisra a can bayanmu,koda an
aiko manzon sai mun rigashi isa birnin Madinatul
Sultan bare batun dakaru masu yawa wadanda
zasu
dana tarkon cutar damu.Siyama ta numfasa tace
na yarda da duk abinda ka fada ya Abbana.Bazan
hanamu shiga cikin wannan birni ba,amma kafin
mu
shiga din inason ka fara aikawa da manzo a
sirrance
yaje ya gana da Sultan ya sanar dashi duk halin da muke
ciki,idan har yace mu shigo cikin birnin nasa
sai mu shiga tunda dai mun bashi amanar
kanmu.Koda jin wannan batu sai Shugaba Sharwan
yayi murmushi yace,tabbas nima na gamsu da
wannan shawara.Nan take aka tashi wani
kwararran dan leken asiri wanda ake kira da Jamar yayi
shiga
irin ta fataken birnin Kisra aka bashi dukiya da
dakaru kimanin mutum arba'in bisa keken doki
suka
durfafi birnin Madinatul Sultan.Suma dakarun nasa
gaba daya shigar irin dakarun Birnin Kisra sukayi.Lokacin
dasu Jamar suka iso kofar birnin
Madinatul Sultan basu fuskanci matsalar komai ba
don ana ganinsu aka bude musu kofa ko cajesu ba
ayi ba suka kunna kai cikin birnin,sukayi ta tafiya
basu tsaya a ko ina ba har saida suka iso kofar
fadar birnin.Suna zuwa aka yi musu iso suka shiga cikin
fadar suke zube a gaban Sultan suka kwashi
gaisuwa.Sultan ya dubesu cikin alamun mamaki
yace yaku wadannan bakin fatake ku gabatar da
kanku domin ban sanku ba daga cikin fataken
dana
saba yin mu'amala dasu ba daga Birnin Kisra ba.Koda jin
wannan batu sai Jamar ya zura
hannunsa a cikin aljihu ya dauko wata wasika ya
bayar a mikawa Sarki Sultan.Koda Sarki Sultan ya
warware wasikar ya karantata a gaban fadawansa
sai
ya kamu da tsananin farinciki ya mike tsaye da sauri
ya rungume Jamar yana mai yi musu lale
marhaban
tamkar yaga 'yan uwansa na jini.Al'amarin daya
daurewa 'yan majalisarsa kai kenan.Nan take Sarki
Sultan yasa aka kai su Jamar masauki mai kyau aka
kawo msu abinci da abin sha mai rai da
lafiya.Kafin
ma su fara cin abincin sai ga Sarki Sultan da
kansa
yazo har cikin turakar da suke,dakarunsa na take masa
baya.Nan take ya sallami dakarun nasa yace
duk su kama gabansu su bashi wuri yana son ya
gana da bakinsa.Nan take kuwa dakarun suka fice
daga cikin gidan suka barshi tare dasu Jamar.Suna
gama fita Sultan yasa aka rufe kofar turakar da
tagoginta don kada ma iska ta dauki sautin zancen da
zasuyi takai izuwa kunnen dakarun nasa.A
sannan ne Sarki Sultan ya dubi Jamar yace,Ya kai
wakilin babban aminina,kayi sani cewa lallai
rayuwar
kabilar Banu Hanzar tana cikin tsananin hadarin
gaske domin tuni wani aljani yazo da sako daga sabon
sarki na Kisra cewar da zarar kun iso
Birnina
na sa a kamaku gaba dayanku a tsare a kurkuku
har
Sarkin yazo ya riskeku.Tuni na karbi wannan sako
kuma na tabbatar da cewar zanbi umarni a zahiri,amma
a badini nayi watsi da umarnin Sarki
Darwaz domin irin amanar dake tsananina da
Shugaba Sharwan bazata barni na bari a cutar
daku
ba.Tuni wannan aljani ya juya da nufin ya koma
wajen Sarki Darwaz ya sanar dashi cewa ya isar da
sakonsa a gareni,amma sai na tura wani babban
hadimina wanda yafi aljanin karfin damtse dana
sihiri
ya bishi a baya ya tsafanceshi ya kulleshi a cikin
wata kwalbar sihiri domin kada ya ganku akan
hanya yaje ya tona muku asiri a riskeku a kawar
daku.Yanzi ina son ku bari sai dare ya raba
sannan
kuje ku shigo da mutanenku izuwa cikin garin
nan.Hatta masu gadin kofar birnin nan zansa a
sauyasu a cikin daren nan na yau na zuba yardaddu
a kan aikinsu.Idan ku ka shigo zan rana muku
dukkan kayayyakin daya kamata domin ku saje da
jama'ata domin ku sami damar tanadar da guzurin
da kuke bukata ku kammala dukkan shirinku
sannan ki ci gaba da tafiyarku harku cimma burinku na
fita
daga wannan nahiyar gaba daya.
Ina mai tabbatar muku da cewar sai kun bar birnina da
kamar
kwana
bakwai sannan su Sarki Darwaz zasu iso kuma
duk irin binciken dasuyi bazasu taba gano cewar na
baku mafaka a birnina.Lokacin da Sultan yazo nan
a
zancensa Sai farinciki ya lullube su Jamar suka
zube kasa suna yi masa godiya.Kamar yadda Sarki
Sultan ya shirya kuwa haka al'amarin suka kasance
wato saida dare ya raba san
nan aka sauya nasu gadin birnin na Madinatul
Sultan sannan akaje aka shigo da kabilar Banu
Hanzar gaba dayansu izuwa cikin birnin a sirrance
ba tare da kowa ya sani ba bayan an yi musu shiga
irinta mutanen birnin.Siyama da mahaifiyarta da
shugaba Sharwan kuwa har cikin ainihin turakar
Sultan aka kaisu suna yin arba da juna sai Sultan
ya
ruga ga Sharwan suka rungume juna suna masu fashewa
da kukan farin cikin sake saduwa domin
rabonsu da ganin juna a kalla yakai shekara goma
sha biyar.Sultan ya janye jikinsa daga cikin na
Sharwan a lokacin daya Hango Siyama da
mahaifarta
ya dubi Siyama cikin tsananin mamaki sannan ya dubi
Sharwan yace,yanzu wannan Siyama ce ta
girma haka?Sharwan ya gyada kai cikin murmushi
yace,kwarai kuwa wanna Siyama ce rabonka da ita
tun tana da shekara uku kacal a duniya,wata rana
sa'adda ka kawo mana ziyara a lokacin da ka fito
farautarka ta karshe harka daura mata wata laya a
wuyanta kace mu adanata a jikinta har
abada.Yanzu
haka layar na jikinta tun wancan lokacin tana bata
tsananin kulawa yadda ya kamata.Koda gama
fadin
hakan sai Sharwan ya taka yaje inda Siyama take ya
zura hannunsa cikin wuyan Rigarta ya janyo wata
siririyar laya dake zagaye a wuyanta wacce akayita
da hakorin zaki guda daya.koda Sultan yayi arba
da
wannan laya sai ya kamu da tsananin farinciki sannan ya
dubi Siyama yace yake 'yata kiyi sani
cewa asalin wannan laya ta kakana ce wanda ya
haifi
ubana nima gadonta nayi kuma ubana ya tabbatar
mini da cewar duk wanda ya girma tare da layar a
jikinsa babu makiyinsa dazai taba samun nasara
akansa.Kuma duk irin tsananin rintsin da mutum
zai
shiga sai dai kawai yasha wuya.Har yau har gobe
ban haihu ba kuma bisa binciken danayi a tsafi da
wanda matsafa sukayi mini bazan taba haihuwa ba
a takaice dai har na mutu bazan sami magaji
ba.Mahaifinki yayimini abinda har na mutu bazan
iya
saka masa da komai koda kuwa zan bada raina a
matsayin fansa ga nasa,bisa wannan dalili ne na
sallama wannan laya tawa a gareki tunda kina yarinya
karama,tunda shima bashi da wani 'da a
duniya saike kadai.Rayuwarki taci gabanki har
izuwa
lokacin da zaki gajeshi shine kadai babban burinsa
a
doron kasa.Ina son mahaifinki yaga wannan rana da
idanunsa kafin ajali ya riskeshi.Koda Sultan yazo
nan a zancensa sai na take Siyama taji ta kamu da
tsananin kaunarsa don haka bata san sa'adda ta
ruga gareshi ba ta runguemshi tana mai fashewa
da kukan farin ciki domin ta tabbatar da cewa basu da
wani masoyi a doron kasa wanda yafi Sultan.Bayan
hake ne Sultan ya kirawo Matarsa wacce ta
kasance
'yar uwar Ilela mahaifiyar Siyama uwa daya uba
daya wacce ake kira da suna SHAMIRAT.Koda Shamira
ta
shiga cikin turakar tayi arba da yar uwarta Ilela sai
ta cika da tsananin mamaki gami da farinciki.Lokac
i
guda suka ruga suka rungume juna suna masu fashewa
da kukan murna suna kankame jikinsu
tamkar kara aka tsaga,kuma a danginsu su kadai
ne
suka rage.Bisa dole aure ya rabasu suna kuka
kuma
tin daga ranar da Sultan ya auri Shamirat ya dawo da ita
birnin Madinatul Sultan ita da Ilela basu
sake
ganin juna ba,kuma basu taba zaton zasu sake
saduwa ba,domin a ka'idar dokar Birnin Kisra duk
mutumin da aka bashi mukamin shugabanci na
wani Birni to shida Iyalansa shiga cikin Birnin Kisra da
dukkan dazuzzukan da suke kewayenta sun
haramta
gareshi.Saida Ilela da Shamirat suka dade a
kankame da juna suna kukan murna sannan
Shamirat ta farga da Siyama ta hangota a tsaye a can
gabansu.Da yake Siyama tana kama da
mahaifiyarta,Shamirat na ganinta ta gane cewa 'yar
suce,don haka sai ta cire jikinta daga cikin na Ilela
ta
bude hannayenta a lokacin da hawaye ya zubo
mata tana kallon Siyama tace,taho gareni yake 'yata naji
dumin jikinki kafin mu sake rabuwar karshe.Nice
kadai 'yar iwar mahaifiyarki wacce tayi saura a
doron
kasa.Koda jin wannan batu sai Zuciyar Siyama ta
karaya,nan take itama idanunta suka ciko da kwalla
ta fara zubar da hawaye bata san sa'adda ta ruga
izuwa ga Shamirat ba suka rungume juna suka
suna
kuka.A'amarin daya baiwa su Sharwan matukar
tausayi kenan suma suka ci gaba da kukan.Kamar yadda
Sultan ya tsara haka duk
al'amarin ya kasance wato saida Kabilar su Siyama
suka kwana biyu a cikin Birnin Madinatul Sultan ba
tare da wani dan garin ya fahimci hakan ba,sannan
Sultan yasa aka shirya musu guzuri mai yawan
gaske,kuma aka nuna musu hanya mafi sirri wacce zasu
fice daga cikin nahiyar gaba daya.Lokacin da
Sharwan yazo suyi bankwana da Sarki Sultan sai
duk su biyun suka kasa cewa komai suka fashe da
kuka suka rungume juna.Tsawon 'yan dakiku
suna
kankame sannan Sultan ya janye jikinsa daga cikin na
Sharwan ya dubeshi a lokacin da hawaye ya
zubo masa yace,yakai abokina kayi sani cewa
wannan rabuwa da zamuyi yanzu ina ganin cewa
itace rabuwarmu ta karshe wadda har abada baza
mu sake saduwa ba tunda zaku bar wannan
nahiyar tamu ne gaba daya,bansan ranar da zaku sake
dawowa ba.Wata kila kafin ku sake dawowa bana
raye,wannan hawaye nawa da kaga ya zubo bisa
dalili biyu ne.Dalili na farko shine na SO da
KAUNAr
dake tsakanina dakai.Dalili na biyu kuma hawaye ne
na takaici bisa zamu rabu alhalin har yanzu ban
sami damar dazan iya saka maka bisa abinda kayi
mini a baya ba.Koda Sharwan yaji wannan batu sai
nan take shima hawaye ya zubo masa yace,yakai
Abokina kayi sani cewa bana fatan naga ranar dazaka
saka mini bisa abinda nayi maka a
baya.Kuma ko a yanzu ka gama saka mini tunda
harka bamu mafaka a cikin birninka a irin wannan
lokaci wanda babu wani shugaban birnin dake
karkashin masarautar Kisra yayi kundunbalar
dakayi domin ka siyar da rayuwarka ne Domin tamu.
GÛDÛÑ TSÎRA&
Littafi Nà uku ( 3 )
Part C
&A-Haleefah Physicist&
Domin ka siyar rayuwar ka ne domin tamu.Koda
jin wannan batu sai Sultan yayi
murmushi yace ai taku rayuwar itace mafi amfani
akan tawa domin kune kadai zaku iya kawo sauyin
rayuwa a wannan Nahiya gaba daya,ku kawar da
zalunci ku shimfida adalci.Abokina idan har hakan
zata tabbata raina fansa ne akan naku.Inason ka
saurara da kyau kaji shawarar dazan baku yanzu
wacce idan karkuyi amfani da ita sai mafarkinku ya
tabbata gaskiya a wannan Nahiya.Abinda nake nufi
shine sai sauyi yazi mana an kawar sa zalunci irin
nasu Sarki Darwaz.A duk sa'adda kuka hadu da
wadansu mutane wadanda suka zo muku da wani
sabon addini to ku yarda dasu kuma ku karbi
addinin nasu.Sa'adda Sharwan yaji wannan batu
shida Siyama da Ilela sai suka cika da tsananin
mamaki.Sharwan ya dubi Sarki Sultan yace,yakai
abokina yanzu kana nufin kenan akwai wani addini
wanda shine na gaskiya wanda yafi duk Allolin da
ake bautawa a wannan Nahiya,kuma yafi tsafi da
dukkan Aljanun da akayi imani dasu?Sarki Sultan
ya
gyada kai yace kwarai kuwa kuma saduwa da
ma'abota wannan addini shine burina na
karshe.Tuni
na dade da samun labarin wannan addini a wajen
iyayena kuma suma tun suna yara suka sami
labarinsa a wajen nasu iyayen.Da zarar na sadu da
wadannan mutane zan ajiye tsafi na
rungumesu.Lokacin da Sultan yazo nan a
zancensa
sai Sharwan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye
sannan ya dubi Sultan yace,yakai abokina yanzu
yaza ayi na shaida wadannan mutane a duk
sa'adda
na sadu dasu?Sultan yayi gyaran murya sannan
yace zaka iya shaida wadanan mutane ta hanyoyi
guda biyu,hanya ta farko itace yanayin shigarsu.Ko
yaushe zaka gansu a cikin sutura ta kamala
mazansu da matansu,basu barin tsiraicinsu ya
bayyana ba.Abu na biyu kuma shine sun kasance
mutane masu gaskiya,amana gami da rikon
alkawari.Basu dauki duniya a bakin komai ba.Babu
abinda suke gudu sama da dukiya da mulki.Koda
jin
wannan batu Sai Sharwan ya girgiza kai yace,ni
kuwa zan sa ido sosai duk ranar dana sadu da
wadannan mutane zan karbi addininsu hanni
bibbiyu
domin kana fadin halayensu yanzu naji na kamu
da
tsananin kaunarsu bisa kyakkyawar
mu'amalarsu,wanda duk wani mahaluki daya dauki
irinta zai gudanar da rayuwarsa cikin kwanciyar
hankali dajin dadi na har abada.Koda jin wannan
batu sai farin ciki ya lullube Sultan ya rungume
Sharwan yana mai masa godiya sannan ya sake
janye jikinsa daga cikin nasa suka fuskanci juna ya
ce,yakai abokina kayi sani cewa tafiyar dake
gabanku da kuma hadarin dake cikinta ba kadan
bane domin kafin ku sami damar fita daga cikin
Nahiyar nan sai kunyi tafiya ta a kalla wata bakwai
da rabi,kuma akwai manyan kasashe guda uku a
gabanku.Wannan birni nawa na Madinatul Sultan
yayi iyaka da wata babbar lasa da ake kira DARUL
HUNAN.Kafin ku isa iyakar sai kunyi tafiya ta
kwana
arba'in da daya.Indai kuka ketare wannan iyaka
lafiya ba tare dasu Sarki Darwaz sun riskeku ba
kun
tsallake dukkan hadari.Ina ji a jikina cewa abune
mayuwaci ku isa har can su Sarki Darwaz basu
cimmuku ba domin nasan cewa sai sunyi amfani
da
kowacce hanya don ganin sun riskeku saboda da
zaarar sun iso nan Birnina sunga bakwa nan zasu
tabbatar da cewa kun wuce gaba.Tunda bani da
tabbacin zan tsira da rayuwata,ina son ku tafi da
matata Shamirat tunda kune kadai kuka rage mata
a
doron Kasa.Idan kuka barta anan tare dani Sarki
Darwaz zai iya kashemu tare.Koda jin wannan batu
sai Shamirat dasu Ilela suka fashe da kuka,shi
kansa
Sharwan bai san sa'adda ya kama kukan ba.Sultan
ya dubi Siyama yace,yake 'yata kiyi sani cewa sai
kin gaji da wannnan GUDUN TSIRA da kukeyi kinji
kamar ki tsaya a kasheki ki huta,amma inason ki
kasance mai juriya bisa duk irin tsananin da zaki
fuskanta,kisa a ranki cewar dukkan tsanani yana
tare
da sauki.Idan gaba dayan Kabilar Banu Hanzar
zasu
kare ya zamana cewa ke kadai kada ki sare kuma
kada ki cire babban burin dake ranki nason
dawowa
wanna kasa tamu domin kawar da zalunci.Koda
gama fadin hakan sai Sultan yayiwa Sharwan
bankwana na karshe inda matarsa Shamirat ta
rungumeshi suka fashe da matsanancin kuka na
bakin cikin rabuwa.Da kyar yar uwarta Ilela ta
janyeta daga cikinsa,ai kuwa sai Sharwan ma ya
sake rungumeshi ya fashe da kuka yana mai cewa
Abokina bazan yarda na tafi na barka basaidai na
zauna azo a kashemu gaba daya tare ko kuma mu
tafi tare mu mutu a cikin wannan GUDUN TSIRA da
mukeyi.Sa'adda Sultan yaji wannan batu na
abokinsa Sharwan sai yakamu da tsananin
tausayinsa ya dubeshi yace,na sani cewa babu
ranar
bakin ciki sama da ranar rabuwa da masoyi,to
amma babu yadda zamuyi da kaddara,haka tamu
kaddarar tazo,babu abinda zamuyi face mu
kasance
masu tunawa da junanmu tare da yiwa junanmu
fatan alkhairi har sa'adda mutuwarmu zata riske
mu,zanji dadi mutukar ka rike wannan a
ranka.Haka
dai Su Sharwan suka yiwa Sultan Sallama suka tafi
matarsa Shamirat tana waigensa tana faman rusa
kuma ana janye da ita.A lokacin Sharwan da
Siyama
ma suka yi ta waigen Sultan Suna zubar da
hawaye
zuciyarsu na kuna kamar zasu fasa yin tafiyar.A
cikin daren ne su Sharwan suka sake sulalewa
daga
cikin Birnin Madinatul Sultan suka fice suka sake
nausa cikin daji suna tafiya cikin sauri sauri gudu
gudu kamar yadda suka saba ba dare ba rana har
tsawon kwana bakwai.Duk sa'adda suka hadu da
gungun yanfashi ko wadansu mugayen dabbobin
daji sai kaga sun tarwatsasu farat daya sunci gaba
da tafiyarsu.
¤¤¤¤¤¤¤¤¤
A DAREN KWANA NA BAKWANI NE DA tafiyarsu
Sharwan,Sarki Darwaz ya iso cikin Birnin Madinatul
Sultan tare da rundunarsa ta yaki,'yarsa Husaira na
daf dashi bisa kan doki sun jera.Suna isowa kofar
Birnin saiga Boka Hurgas ya baiyana tsulum a
gaban
Sarki Darwaz yana mai kyakyacewa da dariya.Cikin
fishi Sarki Darwaz ya dubeshi yace da kana ina
muka shafe wannan doguwar tafiyar baka bayyana
ba sai yanzu alhalin kace kaine zaka yi mana
jagora
a cikin tafiyar?Yayin da Boka Hurgas yaji wannan
tambaya sai yayi murmushi yace ya shugabana ai
tunda aka fara wannan tafiya ina biye daku kuma
ina
muku jagora saidai na baku tazara mai
yawa,domin
na iso nan Birnin tun a kwanaki shida da suka
wuce.Tabbas zuwana da wuri yayi amfani domin
na
samo mana wani labari mai muhimmanci dangane
da abinda muke zargi.Ko shakka babu shugaba
Sultan yayi wadansu baki daga birnin Kisra a
matsayin yan kasuwa,wato fatake,amma a cikin
kwanaki biyu aka nemesu aka rasa acikin birnin
nan.Bisa bincikena danayi na tura wadansu
zakwakuran hadimaina na aljanu sun bi bayan
wadannan fatake basu gansu ba kuma basu ji
duriyarsu ba.Ya shugaba kasani cewa Sultan
gawurtaccen matsafi ne don sihirin tsafinsa yafi
nawa karfi,Ni abinda nake zargi shine wadannan
fatake da akace sunzo fatauci kabilar banu Hanzar
ne,kuma Sultan ne ya basu mafaka suka sauka har
tsawon kwana biyu sannna suka sulale suka bar
birnin nasa.Idan har Sultan yana son ya kubuta
daga
wannan laifi toya gaggauta fada mana inda
wadannan fatake suke ko kuma ya gaya mana
garin
da suka nufa tafi muje mu gansu da
idanunmu.Abu
na biyu shine a bisa binciken danayi kafin mu baro
Birnin Kisra na gano cewa akwai wata tsohuwar
alaka ta zumunci mai karfi tsakanin Sultan da
shugaban Kabilar banu Hanzar tun suna yara
kanana,sa'adda suke haduwa a daji wajen farauta
Kaga kenan akwai yiyuwar shugaba Sultan zai iya
taimakon Kabilar Banu Hanzar ta kowacce
Siga.Koda
Boka Hurgas yazo nan a zancensa Sai Sarki
Darwaz
ya fusata ainun har jikinsa ya kama
tsuma,zuciyarsa
kuma ta kama tafarfasa,kawai sai ya yunkura zai
sakarwa dokinsa limzani ya zabureshi da gudu
izuwa Birnin Madinatul Sultan,amma sai Boka
Hurgas ya daga masa hannu yana mai tsayar
dashi.Kawai sai Boka Hurgas ya tsugunna ya debo
kasar kofar Birnin ya shinshinata kawai yayi
murmushi ya dubi Sarki Darwaz yace,ba shakka
babu mutanen kabilar Banu Hanzar sun shiga cikin
wannan birnin gaba dayansu don haka duk inda
ma
suke shugaba Sultan ya sani domin naji kamshin
sawayensu a kan wannan kasa.Kafin Hurgas ya
gama rufe bakinsa tuni Husaira ta zare takobinta ta
sakarwa dokinta limzami ta banke masu gadin
kofar
birnin da karfin tsiya ta kunna kao cikin birnin a
fusace.Ai kuwa sai Sarki Darwaz da sauran Dakaru
suka rufa mata baya suka bar Boka Hurgas a tsaye
anan yana ta kyalkyala dariyar mugunta da
farinciki.Kai tsaye Gimbiya Husaira suka durfafi
gidan
sarautar Sarki Sultan.Bisa mamaki suna isa gidan
sarautar sai suka iskeshi a bude wanwar ko masu
gadi babu.A cikin gidan sarautar kuwa gaba dayan
dakarun suna zazzaune sun ajiye makamansu a
kas,kuma basa shirin tararsu.Koda suka iso
tsakiyar gidan sarautar inda wani badakare yake
sai
suka iske wani mutum guda daya jal a cikin
gagarumar shigar yaki.Koda suka matso daf dashi
sai sukaga ashe ba wani bane face Shugaba
SultanKoda suka zo dab dashi sai suka ja
Linzamin
dawakansu suka yi tirjiya kuma suka yi masa
KAWANYA.Cikin tsananin fushi Sarki Darwaz ya
dakawa Sultan tsawa yace,yakai Sultan kayi sani
cewa kaci amanarmu ka hada kai da makiyanmu
da
basu mafaka,idan kana son ka tsira da rayuwarka
data iyalanka to ka hanzarta sanar damu inda
kabilar
Banu Hanzar Suke.Koda jin wannan tambaya sai
Sultan ya bushe da dariya,Al'amarin dayayi
mutukar
baiwa su Sarki Darwaz mamaki kenan.Daga can
sai
Sultan yayi shiru ga barin dariyar ya murtuke
fuskarsa ya dubi Sarki Darwaz yace,ko me zai faru
bazan sanar daku inda Kabilar Banu Hanzar suke
ba
kuma matata tana tare dasu.Yakai wannan
azzalumin shugaba nawa kayi sani cewa ni bani da
sauran buri a rayuwata face guda daya jal,wanda
ko
ban cika shi ba wadda ta kashe Dan'uwanka Sarki
Ruguzan sai ta cika mini shi,wato Siyama 'yar
aminina shugaba Sharwan.Na sani cewa zan mutu
a
hannunku amma ku sani kafin a kashe Gwaggon
Biri
sai yayi muguwar barna.Sultan na gama fadin
hakan
sai ya zare takobinsa ya daka tsalle sama kamar
tsuntsu ya hau dakarun Birnin Kisra da SARA DA
SUKA a saman yana fille musu kawuna tamkar ya
kasance mai fuka fukai,yana shawagi a kansu
saboda
karfin sihirinsa.Koda Sarki Darwaz da Husaira suka
ga irin mummunar barnar da Sultan yake yi musu
sai suma suka zare takubbansu suka daka tsalle
sama suka tare shi aka ruguntsume da sabon
azababben yaki mai tsananin ban tsoro da ban
al'ajabi.
WAYE ZAI SAMU NASARA A WANNNAN
GAGARUMIN
GUMURZU TSAKANIN SU SARKI DARWAZ DA
SARKI
SULTAN?
SHIN SARKI SULTAN YANA FADUWA KASA KUWA?
A WANE HALI KABILAR BANU HANZAR SUKE CIKI?
SHIN ZASU SAMI NASARAR FITA DAGA NAHIYAR
NAN HAR SU HADU DA MA'ABOTA ADDININ
MUSULUNCI SU MUSULUNTA?
SIYAMA NA CIKA BURINTA NA DAWOWA NAHIYAR
TA KAWAR DA MULKIN ZALUNCI?
YAUSHE ZA'A YI GABA DA GABA TSAKANIN
SIYAMA
DA GIMBIYA HUSAIRA 'YAR SARKI DARWAZ,INDAN
SUN HADU ME ZAI AFKU A HADUWAR TASU?
WANE IRIN BURI BOKA HUGAS YAKE DASHI A
RAYUWARSA?
Mu hadu a GUDUN TSIRA kashi na hudu don jin ci
gaban wannan kasaitaccen labari
Amsa:
Su Sarki Darwaz ne suke samun Nasara.
Eh Sarki Sultan yana faduwa kasa.
kwarai kuwa suna samun damar fita bayan sun sha
wahala har su hadu da ma'abota addinin
musulunci.
Eh Siyama tana cika burinta,amma ba'azo gunba.
Idan Siyama da Husaira sun hadu ana tafka
azababben yaki mai tsoratarwa.
Burin Boka Hurgas ya mallaki Birnin Kisra da
Nahiyar tasu.

GUDUN TSIRA
Littafi na Uku
Na Abdulaziz Sani m gini
Ebook creator:- Shuraih 99%
For more adventure hausa ebooks visits our wepsite www.shuraih.waphall.com

Domin samun wasu littatafan yaki a matsayin ebooks sai ku ziYarci shafinmu akan www.shuraih.waphall.com


ÿþGUDUN TSIRA
Littafi na hudu
Na Abdulaziz Sani m gini
Ebook creator:- Shuraih 99%
For more adventure hausa ebooks visits our wepsite www.shuraih.waphall.com

Domin samun wasu littatafan yaki a matsayin ebooks sai ku ziYarci shafinmu akan www.shuraih.waphall.com

GUDUN TSIRA
Littafi na Hudu(4)
Part A
Lokacin da aka rungumtsume da masiffafen yaki
tsakanin shugaba Sultan dasu Sarki Darwas sai
ragowar dakarun nasu sarki Darwaz suka zama yan
kallo,suka koma kwashe gawarwakin yan'uwansu
suna koma gefe daya.Dama wadannan dakaru sun
firgita ainun da al'amarin shugaba Sultan saboda a
cikin abinda bai wuce dakika dari biyu ba ya kashe
sama da dakaru dari takwas da karfin sihirin tsafi
gami da karfin damtse da kwarewa a iya yaki.Koda
aka fara wannan baki artabu sai Gimbiya Husaira da
sarki Darwaz suka gane cewa lallai Sultan ba
karamin jan gwarzo bane,tunda gashi sunyi masa
rubdugu su biyun,amma tsawon dakika dari dayansu
ya kasa koda lakutar jikinsa.Babban abinda ya bata
musu rai mashi ne a hakan ma dada zullewa yake
yana ci gaba da saran dakarunsu yana mai ci gaba
da yin mummunar barna.Koda ganin haka sai Sarki
Darwaz da Huraisa suka kara fusata ainun suka kara
kuntata shi.Lokaci guda sai Sarki Darwaz da Huraisa
suka dubi junansu a sannan suka yi wata
alama,kawai sai suka doki kirjin Sultan da kafafunsu
lokaci guda.Saboda karfin dukan sai da Sultan ya
fado kasa tim yana aman jini,amma saboda tsananin
naci da tsananin juriya bai yarda takubban hannunsa
ba.Cikin zafin nama ya mike tsaye zumbur a daidai
lokacin da Sarki Darwaz da Huraisa suka duro kasa
gabansa aka ci gaba da gumurzu.Wohoho,wanda ya
iya ya huta.Hakika su Sarki Darwaz sun sha matukar
mamaki,domin basu taba zaton cewa Sultan yana da
jarumtaka da karfin sihiri a haka ba.Ba wai
tsagwaron karfin damtse ne da Sultan ba,amma ya
sami tsananin horo na iya yaki gami da tsananin
zafin nama,tabbas ya cika tshoho mai dakawa yara
gumba.Saida aka shafe sa'a guda da rabi cif ana
fafata kazamin yaki tsakanin Sultan dasu Sarki
Darwaz amma ya zame musu alakakai,kuma saida
ya samin nasarar fitar da jini a jikin kowannansu,duk
da cewar suma sun yanke shi,domin a kalla sunyi
masa manyan raunika guda tara.Sakamakon jinin
dake zuba a jikinsa ne jiri ya fara dibarsa ya fara
gigta.Damar dasu Sarki Darwaz suka samu kenan
suka ci gaba da kai masa sara da suka gami da
naushi da bugu da dukkan karfinsu.Nan da nan
suka sami lagonsa ya zamana cewa tun yana tsaye
saida ya durkushe kasa bisa gwiwoyinsa.Babban
abinda ya fusata Sarki Darwaz shine Sultan yayi
masa wani siririn yanka a kumatu,yayi masa billen
dole,wanda har abada tabonsa bazai bata ba.Ita
kuwa Huraisa a kan cinyarta ta hagu ya yanketa
kuma wurin yayi dan zurfi dole ne tayi jinya ta kamar
tsawon kwana uku,tsananin juriya ne da jarumtaka
tasa taki sarewa.Sultan na tsugune a kasa sai Sarki
Darwaz da Huraisa suka ci gaba da saran jikinsa
suna sukar cikinsa da takobi yana ihu,jini na
tsartuwa da fallatsi a jikinsa har saida sukayi fata-
fata da sassan jikinsa.komai rashin imanin mutum
idan yaga yadda aka daddatsa sultan sai tausayi ya
kamashi,amma duk wannan abu da akayi masa bai
mutu ba saboda taurin rai.Ana cikin haka ne Kan
Sultan ya lankwabe kasa ya daina motsi,Sarki
Darwaz da Gimbiya Huraisa suka dubi Junansu
sukayi murmushin murna bisa ganin sun sami
nasarar kashe shi.Kwatsam ba zato ba tsammani sai
suka ga Sarki Sultan ya dago kansa sama ya dubi
Sarki Darwaz yayi masa murmushin mugunta
sannan yace,ko ba komai harka mutu billen danayi
maka bazai face ba daga kan fuskarka dashi a za'a
binne ka a cikin kabarin ka.Kafin Sultan ya gama
rufe bakinsa tuni Sarki Darwaz yasa takobinsa ya fille
masa kai.Take Kan yayi tsalle can gefe daya ya rinka
mirginawa da gudu har saida bango ya tokare
shi,sannan gangar jikin nasa ma ta bingire
kasa.Cikin tsananin fushi Sarki Darwaz yaje inda kan
Sultan yake ya sunkuya ya dauka sannan ya mikawa
wani hadimi nasa yace,inason a tsire wannan kai a
daidai kofar shiga fadata ya zamana cewa,kullum sai
nayi arba dashi idan zan shiga,kuma ya zamo abu
na farko wanda baki zasu fara tozali dashi a duk
sa'adda suka zo.Hadimin ya risina yace an gama ya
shugabana.Kawai sai hadimin ya jefa kan Sultan a
cikin wata jakar fata ya kunshe.Adaidai wanann
lokaci ne Gimbiya Huraisa ta fara dingisa kafarta ta
hagu wacce ke zubar da jini,kawai kuma sai ta kasa
daukar nauyin jikinta ta fadi kasa,cikin dimauta Sarki
Darwaz ya ruga izuwa kanta ya dauke ta ya ruga
izuwa cikin gidan Sarautar Sultan yana mai bada
umarnin a je a nemo babban likitan shugaba
Sultan.Bayan likitan ya gama sawa Gimbiya Huraisa
magani kuma an dinke raunin saboda yayi zurfi;sa'a
mata yi kaifin takobin Sultan bai taba kashin cinyarta
ba.Nan take Huraisa ta kama barci akan gadon
shugaba Sultan dake tsakiyar turakarsa,sakamakon
maganin barcin da likitan ya bata ta sha.A wannan
lokaci ne likitan ya mike tsaye daga kan gefen
gadon ya dubi sarki Darwaz cikin alamun damuwa
yace,Akwai bukatar

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment