Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu fitila Arƙam ya yi ya gyara musu rufa sannan ya fita. Ya daɗe a kwance yana tunanin waye Aidan a gareta kafin bacci ya ɗauke shi cike da mafarkinta.
***
Takwas da rabi bayan Tauhidat ta gama shirya Aidan sannan ta shiga ɗakin da su Umma suka yi masauki. Gaishesu ta yi suka tambayeta kwanan Aidan ta ce Alhamdulillah. Daga nan ta shiga ɗakin Haj. Manga ta gaisa da baƙin ciki ta sauko ƙasa. Kitchen ta wuce ta sami Haj. Manga da mutum biyu suna tayata aikin breakfast tunda babu mai aiki a gidan. Bayan sun gaisa ta nemi kama musu suka sallameta wai amarya bata aiki. Sai ta ɗauki tsintsiya ta tafi gyaran falo.
Ana kammala abincin ta dibarwa Aidan ta haye sama da sauri su kuwa aka taru harda mazan da suka iso daga masaukinsu zasu ci a falo. Cigiyarta aka dinga yi saboda shiru bata sauko ba.
"Kada dai ace Tauhida kunyarmu take ji taki saukowa cin abinci."
"Naga ta ɗebi ɗan kaɗan wanda bai fi yaron goye yaci ba ta hau sama."
Kunnuwan Arƙam suna garesu ya kasa zuba komai yaji Umma ta ce, "Arƙam jeka ka sauko da matarka nan gidan bata da suruki."
Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Ana faɗa ya tashi Jamal yana dariyar shaƙiyanci. Yana son zuwa yana jin haushin ita me yasa bata nuna damuwarta a kansa. Sai wani ɓoye kanta take yi. Jiya ba don gidan ƙato bane kowa ya yi bacci da sai ta tara masa mutane da ihunta. Idan da ta je wurinsa ai ba zai hau saman su tsorata ba. Tsayar dashi wata matar Baffa Bukar da na uku a wurin Baffa ta yi ta haɗa masa abincin a tray.
"Ka barta kafin ta gama sakewa ku ci a can."
"Baki haɗa masa da tabarma ba" cewar maigidanta.
Yana ji suna masa dariya har ya haye saman shi ma yana murmushi. Kafin ya isa ƙofar dakin Haj. Manga ta fito daga nata. Tambayarsa ta yi ina zai je ya nuna mata abincin yana mita wai shi bata bashi ba amma an aiko shi ya kawo mata. Da yake ta kula da take-takensa wai yana fushi tun jiya sai ta rabu dashi ta buɗe masa ƙofar ɗakin suka shiga tare. Aidan na jingine da gado Tauhidat tana bashi abinci. Murmushi ya yi sosai da yaga Haj. Manga ta ƙarasa gabansa ta shafa kansa.
"Good morning Aidan."
Arƙam kuma ya ce "good morning handsome."
Bawan Allah sai ya hau ɓangala dariya. Duka iyayensa babu wanda ya taɓa yaba masa a komai. Ita Susu bata son shi bata kuma damu da lamuransa ba. Shamsu kuma neman lafiyarsa yasa a gaba duka yaran basu dame shi ba. Fork ɗin hannun Tauhidat ya karɓe wadda ta duƙar da kai tun shigowarsu ya cigaba da bashi abincin.
Gefe ta koma tana cin wanda ya kawo. Haj. Manga ta faɗa musu cewa ƙarfe uku Shaheed zai zo su je gaishe da Alh. Audi kamar yadda ya buƙata. Jin sunansa ke da wuya Aidan ya soma zabura. Abincin bakinsa ma dawo dashi ya yi. Hankalinsu duka ya tashi da ƙyar aka sami kansa. Jamal aka kira yazo ya zauna dashi suka koma ɗakin Haj. Manga. Ita ta faɗawa Arƙam waye Aidan da dalilin zamansa a gidan.
"Da babarsa da Kawu basu san yana nan ba kenan?"
"Mammalo bai yiwa Tauhida bayanin komai ba ya tafi. Shi kuma yaro ba baki kaga kuwa bamu san a hannun waye rayuwarsa take cikin hatsari ba."
Jinjina lamarin yake yi a kansa yana tunanin wace hanya ya kamata yabi domin communicating dashi. Tabbas akwai abinda yaron ya sani shi yasa aka rabo shi da gidansu. Ga kuma tsoratar da ya yi da yaji sunan Alh. Audi. Bai faɗa musu tunanin da yake ba don me yiwuwa ba tsorata bane. Ƙila ma so yake ya koma gida shi yasa ya yi kukan. Zai cigaba da saka masa ido dai. Kafin uku Shaheed ya iso gidan. Wayar Alh. Audi biyu yana tuna masa cewa lallai yau su zo yaga mijin Tauhidat. Wasu kayan nata Sariat ta bashi ya taho dasu. A ciki ta sami wani lace baƙi mai ratsin adon fari da orange sabo ta saka. Haj. Manga na tsaye a kanta sai da ta yi kwalliya sosai.
"Ki dake Tauhida banda rawar jiki ko ta murya. Kada ki kuskura ya hango alamun tsoronsa a tare dake. Idan kunje ki faɗa masa cewa Suwaida da Jamal sun amince zaki wakilcesu a kotu."
"Ba zan baki kunya ba fa Nanna." Ta ce tana gyara ɗaurin dankwalinta.
"Na sani Tauhida.” Sai kuma ta canja akalar zancen zuwa kan Arkam “wancan mijin naki fa fushi yake damu akan ƙin faɗa masa aurenki ya mutu tuntuni."
Sankuyar da kanta ta yi cike da kunya. Ita kuwa Haj. Manga ta share tana faɗa mata cewa kada ta bishi idan yana shareta. Mace sai da jan aji. Ta rabu dashi da kansa zai nemi shiri. Bata da abin cewa sai murmushi. A ɗakin Arƙam kuma Jamal da Shaheed ke nuna masa yadda zai naɗe babbar riga. Da yaga abin na neman wahalar dashi ya ɗauki wani yadi mai kyau ruwan goro ya ce shi zai saka. Rigar three quarter ce mai dogon hannu da zagayeyyen wuya mai daga maɓallai daga wurin da aka yi aikin rigar har wuyansa. Baya saka manyan kaya sai sallah-sallah. Sunyi masa kyau sosai bare da ya ɗora hula zanna bukar. Jamal da aka ce ba dashi za a je ba takaici ya kama shi. Faɗi yake idan aka bari ya je zai kawo musu rahoton komai kamar a gabansu akayi. Sai da Haj. Manga ta yi masa jan ido ya haƙura.

A waje Tauhidat ta same su. Ita da Arƙam aka rasa mai yiwa ɗan uwansa magana, sai kallo kowa na yaba kyan da ɗayan ya yi. Shaheed ya dinga godiya ga Allah da yasa bai bijirewa Nanna ba ya amince da auren. Su duka kana iya ganin soyayyar juna a tare dasu, amma bayyanawa ya yi musu wahala. Duk da son da suke yiwa juna yana nan amma dole rabuwarsu ta shafi alaƙarsu yanzu. Babu yadda za ayi ace su ture waɗannan shekarun kamar basu faru ba su ɗora daga inda suka tsaya. Awkardness is to be expected. Motarsa ya nufa yana cewa daga can yana da wurin zuwa su biyo shi a motar Tauhidat. Mukullin motar yana jakarta ta fito dashi ta danna remote ɗin. Kai tsaye Arƙam mazaunin me zaman banza ya shige ya zauna ya barta da sakin baki.
"Mijinki ɗan rigima ne" cewar Shaheed yana dariya ya shige tasa motar ya tayar.
"Are you coming?" Taji Arƙam ya ce da ita.
Ƙwafa ta yi ta shiga mazaunin direba ta zauna. Motar kaɗan ta nemi yi musu ba don rashin fili ba sai don yadda zuƙatansu suke harbawa su duka. Sake shawara ya yi ko ya karɓi tuƙin sai ya fasa don bai san ko ina ba kuma bashi da experience na tuƙin Nigeria. Tura kujerar baya ya yi yadda dogayen kafafunsa zasu sake ya ce,
"You drive tunda na kawo miki breakfast da safe so consider us even yanzu."
"Fine" ta ce tana tayar da motar.
"I wish..."
"What?" ta ce tana kallonsa.
"Nothing" Ya amsa da saurinsa saboda bai san zancen zuci ya fito ba.
A hankali ta fara tuƙin har suka hau titi sannan ta saki jiki tana yin yadda ta saba. Tuƙin ganganci da kutsa kai irin na ƴan kasarmu babu wanda bata iya ba. Salonta ya burge shi sosai ya dinga kallonta kamar wanda ya sami tv. Tana jin yadda idanunsa ke yawo a kanta ta daure rawar da hannunta ke yi don kada ta saki sitiyari.
"Karam Mansion."
Arƙam ya karanta ƙaton abinda aka kafa a saman gidan mai ɗauke da wannan rubutun.
"Akwai ɗakinka kuwa a gidan nan da"
Haɗe rai ya yi tare da cewa ya barwa masu gidan suyi kiwon ɓeraye a ciki. Dariyar Tauhidat ta tsaya masa a rai ya ce, "baki canja ba Cuddles. Har yanzu kina da yawan murmushi da dariya. I wonder yadda ki ke yi a court."
"Dr. Arƙam ina gayyatarka zamana na gaba domin na baka mamaki."
"Zan zo ko babu gayyata."
Ƙwanƙwasa gilas ɗin motar Shaheed ya yi yana nuna musu cewa su fito. Takalminta mai tsini ta mayar sannan ta fito. Suna fara tafiya Arƙam ya zura yatsunsa cikin nata suna biye da Shaheed. Wata irin nutsuwa riƙon ya sanya mata bata cire hannunta ba sai a ƙofar falon Alh. Audi. Arƙam yaƙi saki sai ma matso da ita jikinsa da ya yi. A cikin falon Alh. Audi ne da Alh. Ari sai Fanna da ƴaƴanta. An shirya kayan tarbar baƙi wanda Alh. Audi ya gama shirin kalaman da zai yiwa ko ma waye mijin ya tsorata shi akan auren bayan ya nemi su bashi wuri ya gana dashi.
Alh. Ari ne ya fara hango irin riƙon da Arƙam ya yiwa Tauhidat ya ce, "kunga marasa kunya, ji wannan runguma kamar a ɗakin baccinsu."
Bakin ƙofar Alh. Audi ya kalla daidai lokacin Arƙam ya duka ya zarewa Tauhidat takalman ƙafarta saboda akwai maɗauri. Ita kanta kunya ce ta kamata musamman da taga idanuwansu a kansu kamar su cinye su.
Alh. Audi ya ce, "Shaheed ka ce bahaushe ne amma me nake gani haka ko kunya babu yana faman rirriƙeta. Anya kunyi bincike kuwa kafin ayi auren?"
Duka maganganunsa sun shiga kunnuwan Arƙam. Shekara ashirin babu yadda za'ayi su gane shi cikin sauri. Ƙarasowa suka yi kamar wasu taurari suna taku ɗaiɗai. Sai da suka iso Alh. Audi ya tashi zumbur saboda wani irin firgici da ya baƙunci zuciyarsa. Yawun bakinsa ne ya ƙafe yana son tuna ina ya san wannan fuska.
Da murmushi cikin sanyin maganarsa Arƙam ya miƙa masa hannun damansa na hagun yana cikin na Tauhidat ya ce, "its nice to see you again Kawu."
Alh. Ari ya saki baki "Kawu kuma?"
Arƙam ya dan shafa bayan kansa sannan ya ce, "forgive my manners ban yi introducing kaina ba. I am Dr. Arƙam Ibrahim Karam mijin Tauhida" ya ƙare maganar yana mata wani irin kallo kamar ya haɗiyeta a wurin.
Mutuwar tsaye Alh. Audi ya yi don gabaɗaya gaɓoɓinsa dena komai suka yi sai amsa kuwar sunan Arƙam ke dawo masa da ambaton kansa a matsayin mijin Tauhidat.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment