Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za ta gudu sai kuma ta faɗa mata yadda suka yi da Alh. Audi akan maganar auren Shamsu. Kwantar mata da hankali Nannanta ta yi ta ce ta bar komai a hannunta. Ana magariba su Shaheed suka iso gidan. Yaransa uku Yomi (Abayomi), Latifat da Muhammad sai kuma cikin na huɗu da Sariat take dashi.
Sariat na tare da yaran suna wasa a kusa da Aidan ga Jamal a gefe yana mata surutu su kuma suka koma gefe suna tattaunawa. A bayyane yake garesu cewa Jamal da Susu basu yi sata ba tunda sun san waye Alh. Audi. Abinda ya shafe tunaninsu shi ne abinda Susu ta faɗa game da mijinta. Sun barwa Tauhidat ta yi aikinta dai taje su sake magana sosai. Daga nan kuma Shaheed ya sako zancen alaƙarta da Arƙam ta baya. Kallon Haj. Manga kawai ta yi cike da kunya ta tashi ta bar wurin.
"Ga amsarka nan Shaheed" cewar Haj. Manga tana ƴar dariya "bata tsaya ta ji me zaka ce ba ma ta tashi."
"Gobe nake so a ɗaura auren Nanna." Shaheed ya ce yana kallon saitin inda Tauhida ta zauna kusa da iyalinsa,"ina tsoron kada ya gane ƙarya nayi masa ɗazu kafin goben muji ya kuma aura mata ɗansa."
Zaman Tauhidat a wurinsu Jamal ba jimawa ya tashi ya shige ɗaki. Cike da zumuɗi ya kira Arƙam ya shaida masa cewa ta dawo gidansu. Abu na farko da ya tambayeshi shi ne ina mijinta.
"Ɗan iska ashe ya saketa tun ranar da aka sanar dashi auren kafin rasuwar Baffa."
"I am not following (ban fahimta ba)." Cewar Arƙam yana jin wani abu na yi masa yawo a jiki. Dalla-dalla karatun 'yan koyo haka Jamal ya labarta masa yadda ta kasance da auren nata. Cikin wani irin yanayi Arƙam ya ce,
"So kana nufin for the past 9 years da kai da Nanna da ita ma kun san cewa bata da aure?"
"Ƙwarai kuwa. Nanna ce ta hana ni faɗa maka saboda a barta ta yi karatu." Ya amsa masa da son burgewa.
"Tayi karatun yanzu ko?"
Wannan karon a daƙile ya yi maganar sai da Jamal ya ɗan sha jinin jikinsa. A sanyaye ya iya bashi amsa da cewa ta gama har ta fara aiki. Bai sake sako zancenta ba saboda yadda zuciyarsa ke bugawa da ɓacin rai ya ce masa gobe ya zo airport ɗaukarsa da wuri don baya son jira.
"Jamal over-sabi ka shiga uku" Inji Jamal yana dukan bakinsa bayan sun yi sallama. Da jin amsar Arƙam ya san cewa ransa ya ɓaci. Tausayin kansa ne ya kama shi ya ce, "ban ga laifinka bro, kai da na yiwa gata na fada maka ban san yadda babarka za ta yi dani ba gobe idan ka iso kana cika kana batsewa."
***
Ɗaya da rabi na rana motoci uku suka shigo gidan Haj. Manga. Mota biyu Dada ce da ƴaƴanta gabaɗayansu sai kuma guda ɗaya ta Haji Lawalli da matansa biyu. Dada ta ƙara tsufa don ma ta matsa sai tazo ne. Sun zo jajanta abinda ya sami Jamal ne sai kuma aiwatar da abinda suka zanta da Haj. Manga a waya a daren jiya. Dada har kuka ta yi da taga Jamal duk da babu abinda aka yi masa a ofishin ƴan sandan. Basu jima ba kafin la'asar sai ga mutan Maiduguri harda Umma. Gida ya cika ba masaka tsinke.

Duka mazan tare suka tafi masallacin jikin makaranta bayan sun idar da sallar la'asar Shaheed ya bada auren Barr. Oluwatosin Tauhidat Abayomi ga Dr. Arƙam Ibrahim Karam wanda Haji Lawalli ya karɓa masa bayan ya biya sadaki naira dubu ɗari lakadan. Ƴaƴan Dada da na Baffa da abokan aikin Shaheed ne suka zama shaidu yayin da limamin masallacin ya shafa Fatiha. Bai iya faɗawa ƴan uwansu ba saboda saurin da suke yi ayi ayi auren. Ya tanadi dogon bayanin ban haƙuri idan ƙura ta lafa sun je gida.
Lokacin da Haji Lawalli ya miƙo sadakin Jamal ne ya fara karɓa ya ce idan da kara ai shi ne waliyin Tauhidat. Sai da kowa ya dara aka fito ana taya juna murna. Shaheed dai don farinciki ji yayi kamar an ɗauke dutse daga zuciyarsa. Tun jiya hankalinsa bai kwanta ba saboda tsoron kada ya tashi daga bacci yaji mummunan labari ya kuma afkawa ƴar uwarsa. Da gudu Jamal ya koma gida ya rike hanci yana buga ayiririiii. Nan matar Kashim ta karɓe tana yi Umma ta fito daga daki tace bata iya ba bari ta koya musu. Wato tana karkace baki da Dada ta amsa suka ɗauka tare sai da duka bakin da Nanna ta tara suka firfito falo ana ta murna. Aidan ne kawai take ɓoyo a wani ɗaki kusa da nata da ta cewa mutane store ne. Tauhidat na ciki ta gama bashi abinci ta leƙo ta sama za ta tambayi me ya faru sai ji tayi Anti Nana ta riƙota zuwa ƙasa. Bata ajiyeta ko ina ba sai a jikin Nannanta. Yau abinda basu saba ba suka gani wato matsananciyar kunya daga Haj. Manga harda rufe fuska da laffayarta. Abin sai ya bawa Tauhidat tsoro tana kallonsu tana kallonta.
"Nanna an gano gaskiyar Jamal ne?"
Ta tambaya don shi take ganin zai sa kowa murna haka. Shaheed ne ya bata amsa da cewa,
"In sha Allah wannan ranar ma zamu gani amma yau nayi amfani da matsayina na zaɓa miki abinda nake fatan ya zama alkhairi da kariya a gareki."
Jikinta ne ya yi sanyi da Haj. Manga ta kama hannuwanta a gaban kowa ta ce, "a gaban iyaye da ƴan uwana na baki amanar ɗan uwanki yayan Jamal. Idan ya iso gida a gabansu zan bashi taki amanar. Ki shirya direba ya kaiki ku ɗauko shi ya kusa sauka. Saboda idan aka ga Jamal a hanyar airport za a iya zaton guduwa zai yi." Hannuwanta biyu tasa ta riƙe fuskar Tauhidan yadda ta kanyi wasu lokutan "Allah Yasa hukuncinmu bai zama karan tsaye a rayuwarki ba."
Kuka Tauhidat ta fashe dashi ta fada jikinta. Maimakon ta bata haƙuri sai ta biye mata. Sariat ce tazo ta rabasu tana cewa Tauhidat taje ta shirya kada su isa a makare. Ɗakin Haj. Manga suka koma inda akwatin da suka taho mata dashi yake na kaya. Tana zaune jikinta na rawa ta gaza gama fahimtar yanayin da ta shiga game da auren. Sariat ta buɗe akwatin tana cewa da ta san haka lamari zai kasance da ta ɗauko mata kaya masu kyau sosai.
"Ki gode Allah Tauhidat, ban taɓa ganin mutum mai rike amana da soyayya ta gaskiya ga wanda ba jininsa ba irin Haj. Manga. Bata sati bata kirani don jin lafiyarki ba. Idan Allah Yasa ɗan nata ya karɓi aurenku kiyi iya ƙoƙarinki ki fitar damu kunyarta."
Murmushin dole Tauhidat ta ƙaƙalo, "in sha Allah Agent Anti Sariat. Gaskiya kin ƙware a iya riƙe sirri kema. Ban taɓa zargin komai ba."
Doguwar riga mai faɗi daga ciki har kasa amma ta kamata daga saman ta wani hadadden material ta bata ta saka tana dariya, "don baki ganni bane jiya da yayanki ya yi min ƙamshin mutuwa."
Kalar material din sky da navy blue ne. Santsinsa yasa bata iya ɗaura ɗankwalin ba sai ta yafa wani lallausan mayafi kamar auduga sky blue saboda kalarsa ne mafi ƙarancin adon kayan. Har ta gama shiri Sariat na yaba yadda ta yi kyau ko don amarya ce. Jikinta babu wani ƙwari sai tarin zulumin yadda za ta fuskanci Arƙam. A son ranta ta zauna a gida amma Sariat ta sanar da ita cewa dole ce fitarta saboda Alh. Audi yana hanya kamar yadda ya kira ya sanar da Haj. Manga cewa zai zo.
Flat ɗin takalmi fari da purse ta ɗauka ta fito daga ɗakin amma ta kasa sauka sai da Haj. Manga ta hawo da kanta ta fitar da ita waje. A bayan mota ta zauna kamar ruwa ya cinyeta tana zancen zuci. Basu fita daga layin ba sai ga jerin gwanon motocin Alh. Audi sun tunkaro gidan. Ƙasa ta yi da kanta da sauri suka wuce zuga guda. Motocin da ya gani a cikin gidan da aka buɗe musu gate wanda suka sa dole su sai dai suyi packing a waje yake mamaki. Yana da labarin zuwan Dada don musamman zuwan nasa saboda ita ne a yau amma sauran motocin fa? Da suka shiga harabar gidan shi da Alh. Ari ya kasa yin shiru sai da ya ce masa me akeyi a gidan ne haka?
"Ina zan sani Alhaji? Mu shiga ciki dai mu gani."
An tarbesu kadaran kadahan sannan kowa ya watse aka bar Umma da Dada sai Haj. Manga da kuma Alh. Audi da wazirinsa. Sake gaishe dasu Umma ya yi sannan ya bige da tambayar ko lafiya yaga jama'a da yawa a gidan.
"Jikana ake zargin ya yi sata irin wadda hankali ba zai ɗauka ba kaga kuwa zuwa ya zama dole" Umma ta bashi amsa fuska a haɗe.
Sunkuyar da kai ya yi cikin sigar munafunci ya ce, "Ayi haƙuri komai zai daidaita don na ɗaukar musu lawyer. Nima fin ƙarfi aka yi min sauran manyan masu hannun jari da abin ya shafa ne suka kai maganar wurin ƴan sanda."
"Uhmm" ta ce tana taɓe baki.
Dama ya tsani duk wani makusancin Baffa bare ma matarsa shi yasa ya kawar da kansa daga gareta ya fuskanci Dada. Ƙarar Haj. Manga ya kawo mata akan cewa ta gina gida kuma ta tare batare da sani ko izininsa ba. Idan akan abinda ya faru da Jamal ne kada ta manta cewa shi ma ɗansa ne kuma zai yi bakin ƙoƙarinsa wurin ganin cewa babu abinda ya same shi.
"Audi"
"Naam Dada" ya amsa yana sake kwantar da kai.
"Ka sakar min Hafsatu tun kafin nima na shigar da ƙara akanka."
Da sauri ya kalleta idanunsa, sun ƙanƙance da ɓacin rai. Oga ya faɗa masa cewa duk abinda ya faɗawa Dada da ita kanta Haj. Mangan idan yazo ba zasu iya yi masa musu ba. To me yake faruwa haka?
"Dada ke da zaki yi mata faɗa saboda na san tana jin maganarki sai ki nemi raba auren sunna?"
Shewa Umma ta yi ta tashi daga falon da bata da juriyar ganin takaici. Ba ƙaramin aikinta bane ta zazzaga masa masifa. Sai dai tashinta bai dame shi ba kamar kallon da Dada ta yi masa kafin ta ce, "kafin a gama shari'ar Jamal nima zan shigar da tawa ƙarar saboda haka ka sakar min ƴa kawai kada dukan ya zame maka biyu."
Bayan Umma tabi ya rage Haj. Manga da Alh. Audi da maganganun Dada suka ɗaure musu kai su duka. A kwanakin nan Dada tana yawan tuna batun gadon ɗanta sai dai kafin ta faɗawa kowa tunanin ke ɓacewa. Da haka zuciyarta ta amince da cewa lallai akwai wani dalili dake kawo mata mantuwar wanda baya rasa nasaba da Alh. Audin. Tashi ya yi kamar zai kifa, ko magana bai yi mata ba ya fita a fusace. Tun kafin ya shiga mota yake dannawa Oga kira yana jin kamar komai nashi ya juye a baibai.
***
Saura minti goma jirgin ya sauka Arƙam ya sake kallon agogon hannunsa yana kiyasta mintunan da suka rage ya sake saka Tauhidat a idanunsa bayan shekara goma. Jiya da maganganun Jamal ya kwana kuma ba haƙura ya yi ba da barinsa cikin duhu da suka yi ba amma kewarta ta sake dawo masa da ƙarfinta. Ji yake kamar ya karɓi jirgin ya ƙara masa sauri.
'Allah Yasa babu nisa tsakanin airport da gidan.'
Ya cewa kansa shi kaɗai. Sai kuma ya ɗanyi tsaki. Idan ma da nisa ina ruwansa? Ba kulata zai yi ba tunda boko ya fishi taje ta yi ta boko shi ma zai yi hutunsa ne ya koma bakin aikinsa. Yaƙi sosai yake yi da zuciyarsa akan Tauhidat har jirgin ya sauke tayoyinsa a filin jirgi na Nnamdi Azikiwe dake birnin tarayya ƙarfe takwas daidai na dare. Zuciyarsa sai da ta buga yaji wata zazzafar ƙwalla ta taru a idanunsa. Jakarsa ya ɗauko ya fito sanye da rigar da yafi sakawa wato turtle-neck top mai dogon hannu. Pale yellow ce ya ɗora navy blue ɗin blazer da wandonta ya yi matuƙar kyau. Da sauri sauri ya dinga saukowa daga benen jirgin yana shaƙar iskar da ya manta daɗinta. Murmushi ne ɗauke a saman fuskarsa har ya isa wurin immigration aka gama cike-cike saboda passport ɗinsa ba na Nigeria bane. Daga nan ya ɗauko sauran akwatunan kayansa guda biyu aka ɗora kan trolley ya fito.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
Tuhidat ta ce a hankali domin kafin ya gama fitowa idanunta suka sauka a kansa. Bugun zuciyarta ne ya ƙaru taji daɗaɗɗiyar soyayyar da gudun ɓatawa Nanna rai yasa ta yi ta dako da binneta a rai ta yunƙuro mata gabaɗaya. Gani take kamar a mafarki wai Arƙam ne taku kalilan a tsakaninsu. Waige waigensa yake yi saboda duk a zatonsa Jamal ne zai zo ɗaukarsa. Juyarwa da zai yi idanunsa da na Tauhidat suka sarƙe cikin na juna. Tamkar duniyar ta tsaya cak haka suka kasance suna musayar kallo da saƙwanni ta ido amma an rasa mai motsawa. So yake ta matso gareshi, ya san ba matarsa bace. Amma ko yaya ta ɗaga ƙafa ta ƙara rage tazarar dake tsakaninsu zai iya rage masa wutar soyayyar dake cin zuciyarsa da kuma sauƙaƙa masa fushinsa. Ace shekara goma a banza suka tafi tsakaninsu bayan babu shamakin da ya haramta musu kasancewa ma'aurata.
Ita ma tsayuwarta jira take ya ƙaraso. Kunya take ji da nauyi sannan bata manta cewa ɗazu ɗazun nan aka ɗaura musu aure ba. Sun rabu a airport ɗin Jidda cike da damuwar rabuwa da juna gashi sai bayan shekara goma suka sake haɗuwa. Maganar da ya faɗa mata kafin su bar Makka ce ta faɗo mata da yace yana ganin idan ya kuskura ya bar ƙasar bai aureta ba kamar wani abu zai faru. Ashe hasaahensa gaskiya ne. Daga inda yake tsaye yana kallon lokacin da launin idanunta ya sauya, ƙwalla ta taru har ta zubo a duka idanun biyu. So yake ya rungumeta amma dole ya dakatar da kansa.
Kamar daga sama muryar direban da ya kawota ta doki kunnenta inda yake tambayarta ko bata ga wanda suka zo ɗauka ba. Arƙam na kallo ta share hawayen da ya zubo akan kyakkyawar fuskarta sannan ta yi masa wannan tsadadden murmushin da bai taɓa mantawa ba.
"Gashi nan karɓo jakarsa mu tafi"
Yaji tace har sai da muryar da ta haifar masa da kasala da miƙewar tsigar jiki. Kamar mai ɗaga dutse haka ya ɗago ƙafafunsa ya karaso inda suke. Direban yana yi masa barka da zuwa amma ya kasa amsawa sai idanu da ya tsare Tauhidat dasu. Sauke nata idon yaga za ta yi da sauri ya ƙarasa gab da ita ya tsaya.
"Don't please! Look at me Cuddles." Ya umarceta.
Ita ya bari da tashin tsigar jikin harda rawa ma gabaɗaya, ta dago a hankali amma ta kasa ƙarasa kaiwa ga nasa idanun. Yana nan da wannan tsayin kamar wanda ake ja yasa mutum ya ji ya sake ƙanƙancewa a gabansa. Da tattausan muryar nan tasa ma'abociyar sanyi da daɗin sauraro ya ce,
"Ban san me nake jira ba amma for the past 10 years ban taɓa canja layi ba saboda ke. You should have called ko sau ɗaya ne."
Buɗe baki ta yi duk da bata san me za ta ce ba amma tana son kare kanta. Ko kalma ɗaya bata furta ba ya ɗaga mata hannu.
"Save it, you never cared."
Abubuwa da yawa ne suka cushe mata a lokacin. Tana son yin kuka. Tana son bashi haƙuri. Tana son yi masa bayani amma duka bai ma tsaya ba yabi bayan direban suka tafi wurin motar. Bin bayansu tayi jiki a sanyaye har suka isa bakin motar aka fara zuba kayansa a baya. Tana tsaye a jikin ƙofa bata buɗe ba sai jin alamun tsayuwarsa ta yi a bayanta. Hannunsa ya zuro ta gefenta don neman magana zai buɗe ƙofar inda take tsaye. Ɗan baya ta yi don bashi wuri ya buɗe ƙofar sosai taji saura ƙiris ta haɗe da jikinsa. Dakatawa ta yi a inda take don kada ta yi laifi tunda ta kula da rigima ya iso ƙasar. Kansa ya duƙar wurin kunnenta ya shaƙi wani ƙamshi mai sanyi da ratsa zuciya. Kasa daurewa ya yi bai san lokacin da ya ce,
"I missed you so much Cuddles"
Ya ja numfashi a hankali sannan ya ƙara da, "I wish. I wish I can..."
Juyowa ta yi wanda ya yi daidai da barinsa wurin ya buɗe gaba ya shige abinsa.
'I wish i can hug you this minute (ina ma zan iya rungumeki yanzu)' ya ƙarasa zancen da ya fara yi mata a zuci. Daga shi har ita babu wanda ya sake magana har suka isa gida inda iyaye da kakanni suka fito tarbarsa cike da murna.
[2/23, 7:34 PM] Nasma: "Kawu are you ok?"
Arƙam ya matsa kusa dashi yana ɗan bubbuga masa baya. To a tsaye yake kamar sanda ya kasa komai. Buɗe baki ya yi zai yi magana amma ya kasa cewa komai. Hasalima sai murɗawa da cikinsa yake yi. Fanna da Alh. Ari duk sun miƙe tsaye suna ta cewa Alhaji, Alhaji amma baya jinsu bare ya iya amsawa. Duk inda hannun Arƙam ya taɓa a jikinsa ji yake kamar harshen ita ce ne mai ci da wuta. Shi kuma dan shaƙiyanci bai bar buga masa bayan ba, yana mai bayyana damuwa sosai ya ce da Tauhidat,
"Cuddles get him a glass of water."
Kamar ta tsaya ta gani ko daga nan zai ƙarasa ya haɗiyi zuciya kowa ya huta, sai dai ta tafi ta ɗebo a dispencer. Kofin ya saka masa a baki ya kuwa shanye ruwan. Yana dawowa hayyacinsa ya yi saurin gyara yanayinsa daga firgici zuwa farinciki. Nan ya shiga matso ƙwallar dole yana bin jikin Arƙam yana shafawa sannan ya ɗaga hannuwa sama.
"Allah nagode Maka. Ashe zan sake saka babban ɗana a idanuna kafin na mutu? Alh. Ari ka tayani murna. Arƙam ya dawo garemu" ya ce da amininsa sannan ya sake riƙoshi ya ɗan ɓata rai "Yaushe ka dawo? Ina ka zauna tsahon shekarun nan munata nemanka ni da mahaifiyarka? Ka san irin damuwar da ka sanyamu a ciki kuwa?"
"Ni fa kun sakani a duhu" Cewar Fanna "wai kana nufin ɗan wajen Hajiya ne da ake nema? Kodayake ga kama nan amma da gaske shi ne?"
"Shi ne Anti" Tauhidat ta bata amsa da murmushi. Alh. Ari zama ya yi, jikinsa babu inda ba ya rawa saboda tsoro. Yadda abubuwa suke tunkaro Alh. Audi yanzu anya babu sa hannun Oga kuwa? Idan kuwa hasashensa gaskiya ne to kashinsa shi ma ya kusa bushewa.
Fanna sai murna kamar ta taɓa ganinsa ta dawo kusa dashi ta tsaya, "sannu da zuwa Arƙam. Ni sunana Fanna, antinka ce don bana ce kishiyar Hajiya ba. Muna zamanmu lafiya da ita."
Ta gama tambayarsa karatu ko aiki yake sannan ta ce, "Allah Sarki zuwa ka yi saboda abinda ya sami Jamal ko? Ni fa ina ganin idan an tsananta bincike za a gano wannan shegiyar ita kaɗai ta yi komai. Yarinyar bata da mutumci ko kaɗan. Kuɗi ne kawai a gabanta."
Haushi ta bawa Alh. Audi ya hau ta da faɗa, "To uwar karaɗi. Shegen baki sai zuba yake kamar ana tatsa nonon tinkiya. Kin haɗa kan ƴaƴanki kun fita ko sai na saɓa miki? Ɗana ya dawo hankalinki bai baki cewa ki bamu wuri mu zanta ba."
Kallo suka bishi da shi, yadda yake diri kamar mahaukacin kare. Sai abin ya so bata, mamaki haɗe da dariya. Amma inkiyar da mahaifinta ya yi mata yasa ita da ƴan matanta Kulsum da Aimana da sauri suka tashi zasu fita. Arƙam ya kira yaran. Sunayensu ya tambaya suka faɗa masa a ɗarare saboda kallon da Alh. Ari yake jefa musu. Da fara'arsa saboda daga su har mahaifiyarsu yaji tausayinsu na raɓar Alh. Audi ya zura hannu a aljihu ya ɗauko kuɗin da suka kasance dala, wanda yana da yaƙinin idan aka canjasu anan suna da ɗan kauri, domin be kai ga yin canji ba. Hannun Aimana ya kama yana murmushi, ya damƙa mata wai su sha sweet.
"Harda wahala haka?" cewar Fanna ta karɓe kuɗin ta bishi da godiya.
Kafin su fita daga falon ta ƙiyasta nawa ne, saboda kuɗi da canji ba baƙinsu bane. A take ta juya darajarsu a kuɗin Nigeria. Ba ƙananan kuɗi bane kuwa. Sake juyawa ta yi ta kalli Arƙam tana jinjina masa da taya Haj. Manga murnar danta ba a tsiyace ya dawo ba. Sai da suka fita ne Alh. Audi ya dena kukan gulmar ya tambayeshi yaushe ya iso kasar ya bashi amsa.
Dariyar farinciki ya yi iya leɓe yana neman ƙarin bayani domin kwanciyar hankalinsa, "tsabar ruɗewar ganinka fa da ka yi magana sai ji na yi kamar ka ce Arƙam mijin Tauhida." Ya fuskanci Shaheed "ina mijin nata?"
Haɗa baki Alh. Ari da Shaheed suka yi wurin bashi amsar cewa haka Arƙam ɗin ya ce. Zancen ya sake dukansa a karo na biyu da ƙyar ya iya ɓoye ɓacin ransa da wata irin dariya mara fasali.
"Wannan shi ake kira dakan ɗaka, shiƙar ɗaka. To amma dama kunsan juna ne ko haɗaku aka yi?"
"She is my first love."
Arƙam ya bashi amsa yana yi mata wani irin kallo with so much adoration. Kamo hannunta ya yi yana murzawa amma tashin hankalin da take gani a idanun Alh. Audi yasa ta kasa hana shi kamar yadda ta yi niyya. Ganin irin kallon da take masa sai ya soma faɗan rashin sanar dashi auren nasu tunda shi uba ne a garesu duka musamman Arƙam. So yake kawai ya buɗe ido ya dena ganinsu a gabansa, ko ya sami yin tunanin mafita. Koda kuwa samun damar yin magana da Oga ne, amma ba ya son nuna zahirinsa. Dukkansu suka haɗa baki wurin bashi haƙuri, kamar ba zai haƙura ba da farko shi a dole anyi masa laifi. Daga baya kuma ya ce,
"Haj. Manga ta san kun yi auren kuwa? Shekara da shekaru tana fushi da marayun yaran nan ba gaira babu dalili." Ya nuna Shaheed da Tauhidat "Idan kuna so nayi mata magana don kada ta kawo muku matsala a gaba kada ku ɓoye min."
"Wane maƙaryacin ne ya faɗa maka haka Alhaji?" Shaheed ya faɗa harda zaro idanu wai shi mamaki "bamu taɓa rabuwa da ita ba. Aikin da nake yi ma ita ta sama min kuma yanzu ma haka Tauhidat tana gidanta. Babu wata matsala kada ka damu don Allah."
Banda Alh. Ari ya yi saurin danne masa hannu da tashi zai yi ya shaƙe masa wuya. Shi suka rainawa hankali tsahon lokaci yana ganin ya yi nasara ashe sakarai suka mayar dashi. Bai kuma iya cewa komai ba sai yaƙe. Alh. Ari ne uban gulma ya tambayi taron me suka yi jiya aka yi sa a Tauhidat ta bada amsa daidai da ta Umma cewa jaje suka zo. Ta ƙara da cewa gobe kafin su koma zasu biyo domin yi masa ta'aziyya da jajen Shamsu. Da haka Arƙam ya miƙe tare da Tauhidat.
"Cuddles its getting late. Ki kaini na duba Shamsu ɗin."
Murya a shaƙe kamar ƙozon kwaɗo Alh. Audi ya ce musu ya riga ya bar ƙasar zuwa asibiti tun safe.
"Yarinyar nan Suwaida kanta ta cuta ba ni ba. Da kaina na kira mahaifinta na faɗa masa abinda ya faru amma har yau babu wanda yazo. Tunda taƙi yarda ki karɓi case ɗinta kuma ita ta sani."
Murmushi ta yi kafin ta sakar masa bayanin da ya sa shi haɗe fuska har suka fita. Tunda ta fara cewa sun daidaita daga ita har Jamal sun amince ta zama lauyansu yaji zufa na keto masa. Da farko ya so amfani da ita ne don ya haɗasu su duka ukun ya kawar dasu sai ya ɓoye hakan a bayan shari'a. Mutum ɗaya ya ɗauka a matsayin lauyan Shamsu da kuma mai wakiltar kamfaninsu da aka yiwa sata. Yafi shekara ashirin yana aiki kuma da wuya ake kayar dashi. Tauhidat ba komai bace a kansa. Amma yanzu da tazo tare da Arƙam ɗin da duka su biyun Oga ya gargaɗe shi a kansu sai yake jin kamar ƙabarinsa ya tona da hannuwansa. Ihu sosai ya saka bayan fitarsu ya dinga bin kayan falon yana

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment