Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fasawa kamar sabon mahaukaci. Alh. Ari ma gefe ya koma don kada a haɗa dashi.
Daga waje suna jin ihunsa sai suka ji tsit. Su ukun duka dariya suka dinga yi musamman Shaheed lokacin da Arƙam ya tambaye shi ko Alh. Audi suma ya yi da suka ji shiru. Basu yarda sun ɓata lokaci a cikin gidan ba kowa ya shiga mota suka tafi. Shaheed gidan wani abokinsa zai wuce su kuma su tafi gida.
Tafiyar tasu yanzu babu sauri saboda cushewar hanya. Rediyo ta kunna tana neman tashar da zata bar musu saboda shirun ya yi yawa. Idanun Arƙam ke bibiyarta ko kunyar kada ta kama shi baya yi. Ɗazu a tafiya dayake tuƙi take sosai tafi dauriya. Yanzu kuwa sai ayi minti goma mota bata motsa ba. Ta rasa me ya kawo wannan tsaikon ake ta tafiyar hawainiya. Tana nata tunanin shi ma da yake kallonta ransa bai huta ba. Zuciyarsa ta kasa gaskata masa cewa Tauhidat ce a tare dashi kuma a matsayin matarsa ta sunna. Gani yake kamar idan ya ɗauke idanunsa daga gareta zai iya farkawa ya ga ashe jiya da yau duka a mafarki suka faru. Zai so hakan ta kasance a ɓangaren Jamal amma akan abinda ya shafi Tauhidat inama babu abinda ya taɓa rabasu. Kusan a tare suka buɗe baki da niyyar magana sai ta yi shiru ta bashi dama ya fara.
Kada kai ya yi "ladies first."
"Na bar maka."
"Ina bukatar simcard. I need to make an important call tonight (akwai wayar da zanyi mai mahimmamci a daren yau)." Haka kawai taji wani abu ya tokare mata wuya da ta yi tunanin ko mace zai kira. Daga zuwa a tunaninta ko hutawa bai yi ba yake zancen wani sim.
"Ka bari sai gobe, wannan hold up ɗin ban san yaushe zamu fita ba kuma ga yamma."
"Zan iya amfani da taki kafin goben?" Ya ɗauki wayarta yana juyawa a hannunsa. Hannunta ta miƙa masa tana kallon titi don bata ma son ta kalle shi tace ya bata abarta. Maimakon wayar sai ya ɗora nasa hannun a kai ya dan matsa.
"Meye na bata rai ba girlfriend ɗina zan kira ba." Duk yadda taso dannewa sai da murmushi ya subuce mata. Ɗauke kai ta yi ta basar kada yaga kamar ta wani damu dashi fiye da yadda shi yake nuna tasa damuwar.
"I don't believe you are jealous Cuddles (ban yarda kishi na kike yi ba). Shekara nawa kin kasa nema na ko sau ɗaya. Abinda kika yi bai yi min daɗi ba seriously."
Dama ta san sai ya yi wannan ƙorafin. A matse take su isa gida saboda a ganinta zancen ba na mota bane. Suna buƙatar zama sosai suyi magana ta fahimta. Sai da suka isa gida tace masa, "Ka ari wayar Jamal ko Nanna kayi important call ɗin sai muyi magana akan abinda ya faru a baya idan ka gama."
"Wayar tawa sai can dare around midnight so gara muyi maganar da wuri."
Kamar ta yi masa kuka ta fita daga motar bayan ta harare shi. Idan ba mace ba wa zai kira cikin dare? Fita ta yi ta leƙo da kanta kafin ta rufe ƙofar.
"Kuma ba zan zo ba, gobe zani office da wuri zan kwanta."
Ɗage gira ɗaya ya yi cikin halin ko in kula da fushinta bayan a ransa daɗi yake ji ya ce "Na fa san inda kike kwana."
"Idan Nanna ta kamaka babu ruwana."
Ta wuce tana ƙunƙuni. Sai da ta ɓacewa ganinsa ya bi bayanta. A can wurin dinning table ya hangota tare da Nanna da Jamal tana magana. Ji akayi sun bushe da dariya su biyun sauran mutanen falon suka ce dole ayi dasu, su dawo cikinsu aji labari da kyau. Zamansa ya yi ita kaɗai ke bada labarin harda zaro idanu yadda Alh. Audi ya yi lokacin da ya gane Arƙam. Komai nata yana burge shi. Babu abinda yafi masa daɗi kamar yadda take mu'amala da danginsa. Kowa yana nuna mata so kuma itama halayenta bai ga na kushewa ba.
Bayan sun yi sallah ne yake jin cewa washegari gidan zai watse. Umma da Dada ne kawai zasu rage sai kawunnansu biyu. Ɗaya daga Kano ɗaya daga Maiduguri. Jibi zasu tafi Abeokuta tare da Haj. Manga da Shaheed akan auren da aka ɗaura ba tare da sani ko izininsu ba. A take Arƙam ya ce zai bisu Haji Lawalli ya goyi baya. Gara aje dashi su san cewa da gaske yake zai riƙe musu ƴa. Gidan zai rage Tauhidat, Aidan da Jamal sai kuma sabuwar mai aikin da zata fara gobe.
Wurin takwas da rabi na dare Tauhidat ta tafi ɗakin baƙi matar Kashim za ta yi mata kitson bare-bari. Sai da ta wanke kan ta yi steaming tunda zuwa salon bai samu ba. Ta sha gyangyaɗi kafin a gama saboda yawansa da ƙanƙanta. Bai fi biyar ya rage a gama ba ta wartsake daga baccin. Su biyu ne ido biyu kowa ya yi kwanta. Lokaci ta duba ta sake ware ido don mamaki.
"Anti shadaya fa ta wuce. Guda nawa ki ke yi?"
Anti Yakura ta yi dariya, "ban ƙirga ba amma anyi ɗari biyu ina jin. Kitson yafi kyau a irin wannan kan mai cika sosai. Ko gajiya bana yi saboda yana tafiya yadda nake so."
"Anti tsifa fa" ta shafa kan tana tausayin kanta ranar da zai tsufa.
"Mijinki aikin me yake yi, ba sai ya tsefe miki ba."
Shiru Tauhidat ta yi tana murmushi taji Anti Yakura ta ce, "gulmammu kuna so kuna kaiwa kasuwa. Leƙowarsa ɗakin nan ta yi huɗu kina bacci wai aron wayarki zai yi. An bashi amma ya ce kin rufeta. Shi ne yake ta mana sintiri ko kin farka kuma yaƙi yarda a tasheki ki bude masa."
Bata manta sun yi zancen waya ba amma ta zata zai karɓi ko ta Jamal ne shi yasa ta tafi kitson hankali kwance. Maganar da ya ce za suyi ce tasa ta so gujewa kitson Umma ta ce sai an gyara mata kai. Tana can tana tunanin ransa ya ɓaci ko bai ɓaci ba Anti Yakura tana yi mata zancen yadda zasu sha biki idan an gama case ɗin Jamal. Shaɗaya da ashirin aka gama kitson ta tashi jiki ya yi tsami. Godiya ta dinga yiwa Anti Yakura ita kuwa tana cewa yiwa kai ne. Sauri take taje tayi wanka ta samu ta kwanta saboda fitar safe gobe. Za ta fita Antin ta bata wata ƙaramar kwalba da bata fi girman ƙaramin yatsa ba mai kyau.
"Ki dinga shafawa bayan kinyi wanka da daddare, da safe ko baki saka komai ba in kin yi wanka babu ke babu warin gumi. Kina iya sake sakawa amma fa idan ba zaki fita ba. Dan kaɗan za ki dinga shafawa domin ƙarfi ne dashi." Ta kwatanta mata kaɗan ɗin da yatsa.
Sabuwar godiya ta sake yi mata sannan ta fita. Ɗakin da suke kwana ita da Aidan taje. Da tunanin yadda za ta barshi shi kaɗai ta shirya tafiya kitson sai Dada ta shiga ɗakin. Yanzu kuma da ta hau bacci ta same shi suna yi shi da Haj. Manga. Murmushi ta yi tana ƙara yabonta a ranta. Tabbas cikakken musulmi shi ne wanda baya kama wani da laifin wani nasa. Dubi yadda take kaffa-kaffa da jikan Alh. Audi kamar ba shi ne babbar matsalarta a duniya yanzu ba. A hankali ta tasheta ta tafi ɗakinta ita kuma ta shiga wanka. Bayan ta shirya cikin doguwar rigar bacci ta gama ƴan shafe-shafenta ta ɗauko turaren tabi jikinta ta saka. Ƙamshinsa akwai daɗi sai lumshe idanu take a gaban madubi tana kallon kitsonta da suka kwanta yar-yar a kan kamar da inji aka ɗora shi. Alamun taɓa ƙofa taji ta tafi da sauri ta danneta don kada a ga Aidan.
"Wa. Waye?"
Ta ce daga jikin ƙofar tana kallon agogo. Shabiyun dare lokacin. Rawar da muryarta take yi yasa Arƙam murmushi, "matsoraciya. Buɗe min ko na buga da ƙarfi kowa ya tashi."
Maimakon hankalinta ya kwanta sai rawar jikinta ta ƙaru. Me kuma ya kawo shi a daren nan ta tambayi kanta. Da taga babu mai bata amsa sai ta ce ya jira tana zuwa. Kamar ya san abin lulluɓi take son ɗauka kafin ta buɗe masa ya murɗa hannun ƙofar ya shigo. Bata kai ga ɗaukar mayafin ba ya riƙota ta baya ta faɗo jikinsa gabaɗaya sauran kaɗan su kai ƙasa. Shi ya daidaita musu tsayuwa ya duƙar da kansa daidai wuyanta yana shaƙar humran da ta shafa. Magana ya yi mata a kunne wadda duk da kusancin tsayuwarsu ita kanta da ƙyar take iya jin me yake cewa. Tamkar daga bacci ya tashi muryarsa ke fita cikin wani irin salo mai ɗaukar hankali.
"This is intoxicating (bugarwa), ina son ƙamshin sosai Cuddles."
Tsabar ruɗewar da ta yi sai cewa ta yi, "yanzu aka bani idan kana so gashi can ka ɗauka."
Lips ɗinsa taji a kasan kunnenta ya dan ciza a hankali sannan ya ce, "Ba fa turarenki nake so ba Madam..."
"To. To. Me kake so?" Ta tambayeshi gabanta na tsananta faɗuwa.
"Kinfi kowa sani."
Yanayin maganarsa ne yasa tsoronsa ya kamata. Wani abu na kusanci makamancin haka bai taɓa haɗata da wani namiji ba idan ka cire ranar da Shamsu ya far mata a ɗaki. Da ya fuskanci a tsorace take sai ya zura hannuwansa ya rungumota sosai a jikinsa har lokacin tana kallon gabanta. Kwantar da kansa kawai ya yi a tsakanin wuyan nata yana jin nutsuwa da farincikin da bai taɓa tunanin samu ba.
Muryarta can ƙasa kamar mai tsoron magana ta ce,"ka cikani kada Aidan ya tashi."
Kasa haƙuri ya yi sai da ya bata peck a gefen haɓarta wanda ya ƙarasa firgita zuciyarta da tsoro da kunya. Da gangan ya ce su tafi ɗakinsa don yaji me za zata ce. Ɗif ta haɗiye abinda za ta sake faɗa gudun kada ta tunzura shi. A yadda suke a tsayen ya kama yatsanta ya zuro wayarta ta gabanta ya ɗora a kai. Dama lock ɗin mai sensor ne na yatsan mai ita. Yana ɗorawa wayar ta buɗe. Da yatsan nata dai ya danna wasu lambobi sannan ya saketa. Kamar jira take da sauri ta faɗa kan shimfiɗarta a gefen gadon ta duƙunƙune jikinta. Tana kwanciya Arƙam ya kashe fitilar ɗakin ya dawo inda take ya zauna jingine da gadon. Kanta ya ɗora a cinyarsa yana bin kitson layi layi yana shafawa har aka ɗauki wayar. Jikinta babu inda baya rawa don firgici da wani irin yanayi da bata taba kasancewa cikinsa ba. Ba jin abinda ake faɗa sosai take yi ba amma ta gane muryar namiji ce. Cikin duhun ta saki murmushi duk da halin da ya jefata a ciki. Shi din ma ya daure ne gudun kada ya karasa tasa raunanniyar zuciyar.
Da Director Zhang yake wayar. Shi ma ya tafi China jiya. Sun taɓa hira ya tambaye shi lafiyar duka patients ɗin da ya bari a Yemen sannan ya yi masa magana akan wani aiki da suka fara kafin ya taho. Duka hirar abinda ya shafi aikinsa ne. Kusan rabin awa suna tattaunawa sannan suka yi sallama. Gefen fuskarta ya shafa bayan ya gama ya kira sunanta a hankali,
"Cuddles."
Sake matse idanuwanta ta yi a zuwan bacci take harda dauke numfashi. Da wayar ya haska fuskarta yana kallon yadda take ta sake runtse ido.
"I can't leave without saying goodnight gashi kuma kinyi bacci." Zame kanta ya yi daga cinyarsa ya dora akan pillow yana cewa zai kwanta a kusa da ita saboda kada ta farka tace bai kyauta ba. Rasa inda zata saka kanta ta yi da taji ya kwanta a kusa da ita. Kunya ce ta yi masifar lulluɓeta kamar ta tsaga kasan ta bace. Da hannu daya ya tallafi kansa, daya hannun kuma ya cigaba da haske mata fuska. Ƙara hasken ya yi yadda zai dameta ai kuwa ta yi ta ɓata fuska yana murmushi. Basu fi minti biyar ba ta buɗe idanun tasa hannu ta ture wayar daga fuskarta.
Har kin gaji kenan." Arƙam ya ce yana dora wayar a bedside drawer.
"Ni ka tashi ka tafi."
"Cuddles am I nameless to you? (Bani da suna a wurinki?)" ya ce kamar yana fushi, "ina laifi ko Maigida ki dinga kirana." Ya faɗa yana nunata da yatsa, "kuma saura kiyi dariya."
Dariyar kuwa ta dinga yi ƙasa-ƙasa kamar ya zuguta. Cikin duhun ta kalli saitin inda yake ta ce "sorry D."
"Doctor? Darling? Dear? Dolo? Daskindariɗi?"
Tauhidat bata yi ƙoƙarin danne dariyarta ba wannan karon. Banda sunan karshen harda yadda ya faɗa yasa ta dariya tana dai ta ƙoƙari kada sautin ya fito sosai. Bata yi aune ba taji ta a ƙirjinsa ya rungumeta yana mata magana a kunne.
"D for Daskindariɗi? Are you serious? Prince ɗin tatsuniyar Dada ne fa" ya ce sounding horrified. Idonta har ƙwalla ya tara don abin yafi ƙarfinta. Ta maimaita Daskindariɗi yafi a ƙirga tana dariya. Shi kuwa ji yake ba don Aidan ba da babu abinda zai hana shi kwana a ɗakin ko yasa ta bishi ƙasa. Cikin ƙanƙanin lokaci ta sake shigewa kowane ɓangare na zuciyarsa. Murmushi yake yi har ta dena dariyar ta ɗan ture shi.
"Ka zo ka tafi please kada na kasa tashi da wuri gobe?"
"I was trying to be a gentleman, kada na tafi ban yi miki sai da safe ba."
Ɗago kanta ta yi daga ƙirjin shi, "Allah Ya tashemu lafiya ni dai ka tafi."
"Ki rakani zuwa step na tsakiya sai ki dawo." Ya ce tare da tayar da ita tsaye. Don ya tafi ɗin sai ta amince. Yana riƙe da hannunta suka fito daga ɗakin. Tana tako ƙafarta ƙofar ɗakin hasken fitilar wurin ya sauka akan rigar jikinta. A gigice ta ƙwace hannunta ta turo ƙofar da suka haɗa ido taga irin kallon da yake mata. Wata shu'umar dariya ya yi wadda shi kaɗai ya san ma'anarta ya soma sauka benen.
"Arƙam daga ina haka?"
Yaji muryar Haj. Manga wadda bugun ƙofar Tauhidat ya taso ta. Sai yanzu yaji kunya da faɗuwar gaba, ya ɗaga hannuwa kamar wanda aka zo kamawa "uhmm, yes, waya ce." Don kada ya tona kansa ya gyara tsayuwa "Nanna waya na ara."
"Waya? A tsohon daren nan kuma? To a wurin wa?" Ta tambaya duk da ta riga ta san amsar kuma hakan ya faranta mata rai. Tana ta tsoron kada ya dawo ya watsa mata ƙasa a ido akan auren saboda ƙorafin da ya dinga yi.
A hankali yana sosa ƙeya ya ce, "a wurinta. Bani da sim ne kuma wanda na kira yana China, safiya ta yi a can."
Riƙe dariyarta ta yi ta harɗe hannuwa a ƙirji, "ita wa kenan?"
"Cuddles mana." Haɗe gira ta yi tana masa kallon tuhuma ya yi saurin ƙarawa da cewa, "babu abinda nayi mata fa. Daga aron waya sai ki dinga yi min wannan kallon Nanna its not fair. Da nayi wani abu ne kamar..."
Da sauri ta soma kora shi tana cewa, "Sauka ka tafi sai da safe."
Yana sauka ya ɗago suka haɗa ido ya kanne mata ido ɗaya. Daƙuwa ta dinga yi masa ya arce ya barta a wurin.
"Kaga shakiyin yaro. To duk abinka sai ka jira na shirya. Dama a gwauro ka taho sai ka ƙara haƙuri."
Ɗakinsu Tauhidan ta buɗe ita kuma a tunaninta Arƙam ne ya dawo. Daga inda take kwance ta ce "don Allah ka tafi kada Nanna ko wani ya ganka."
Haj. Manga taji inama bata fito ba. Wai don ta kashe maganar sai ta ce, "Tauhida nice."
Baiwar Allah sai ta sake rikicewa bakinta yana harɗewa ta soma bayani.
"Wallahi babu abinda ya yi Nanna. Wayata kawai ya ara ya kira wani."
Murmushi Haj. Manga ta yi mata daga bakin ƙofa, "babu komai yi kwanciyarki."
Maida kai ta yi niyyar yi kan pillow ta kwanta ta kasa. Zuciyarta ke raya mata kamar Haj. Manga bata yarda da ita ba. Tana rufe musu ƙofar ta buɗe da sauri tabi bayanta da wayar a hannu.
"Wallahi Nanna waya yazo karɓa. Kin san bashi da sim ɗin nan. Nima sai da na ce dare ya yi." Tana magana tana danna wayar ta nuno mata call log, "kin gani numbar wata ƙasa ce, ai dai kin san bani da kowa a wata ƙasar. Gashi minti ashirin da shida suka yi shi yasa ya daɗe."
"La ilaha illalahu" cewar Haj. Manga tana ɗora hannu ɗaya a ka, "ki dena rantsuwar na yarda. Ko kina da wata uwar da ta fini sanin halinki ne?"
Girgiza kai ta yi hankalinta na kwanciya amma duk da haka sai da ta ce, "kin yarda dani ko Nanna?"
"Na yarda dake Tauhidana jeki ki kwanta."
***
Daga sallar asuba bata koma bacci ba ta yi wanka. Kafin ta gama shiryawa Umma ta shigo zama da Aidan. Idan Haj. Manga ta fito sai ta yi masa wanka ta bashi abinci idan ya tashi. Da taje gaisheta sauran su Anti Nana da masu kwanan ɗakin baƙi duka suna tare an kafa hirar asuba. Tambayar abinda za ɗora na breakfast ta yi Anti Yakura ta ce kada ta damu zasu sauko su ɗora. Ta dafa koma meye iya cikinta. Banda ma dole me zai sa amarya tashin asuba ta fita aiki. Sallama ta yi musu da fatan isa gidajensu lafiya tunda zasu tafi kafin ta dawo. Ta sauko falo kenan taga kira daga Jamal. Tunanin ko zai sake tambayarta ƙarfe nawa zai je office saboda tambayoyin da zata yi masa ta yi. Tana kara wayar a kunnenta taji muryar Arƙam.
"Morning Cuddles."
Ƙaramar dariyarta yaji kafin ta ce, "Morning D, ka tashi lafiya?"
"Daskindariɗi ya tashi lafiya" Ya bata amsa da murmushi.
Jamal dake kwance bayan sun dawo daga masallaci bai san lokacin da ya yaye bargon rufarsa ba.
"Daskindariɗi? Daskindariɗi dai na assalam salam ɗan yaro?" Ya tura bakinsa jikin wayar "ƙanwata meye haka don Allah? Duk sunayen duniya ki rasa ..."
Toshe masa baki Arƙam ya yi ya fita da niyyar komawa nasa ɗakin ya ganta a tsaye ta juya masa baya. Motsin ƙofar ne yasa ta juya suka haɗa ido. Saurin kawar da nata ta yi da ta tuna yadda suka kwashe jiya. Tana kallon ƙasa ya iso gabanta,
"D for?"
"Idan na dawo zan faɗa maka wanda na zaɓa."
"Shikenan ina jira"
Ya ce kawai ya kaita zuwa wurin dinning table yaja mata kujera ya ce ta zauna kuma bai yarda ta motsa ba. Umarninsa tabi don bata so su tsawaita magana a sauko a gansu. Tana jiyo alamun yana amfani da kayan kitchen da ƙamshi ta tashi ta leƙa. Ƙwai ta tarar yana soyawa ya zare mata ido tare da nuna mata ta koma inda ya barta. Ba musu ta tafi zuciya da gangar jiki suna ƙara faɗawa soyayyarsa. Tea ya haɗo mata a mug da bread sai ƙwan da ya soya ya ajiye a gabanta. Bai tashi ba sai da ya tabbatar ta ƙoshi ya rakata har bakin mota ta shiga ya rufe ƙofar.
"Nagode" ta ce a kunyace.
"Ba godiya nake so ba. Do your best to save our bro (ki yi ƙoƙari wurin ceton ɗan uwanmu)."
"In sha Allah zanyi ƙoƙari, ka tayani addu'a kaima."
"Always Cuddles"
Ya shafa fuskarta. Kasa dauke ido ta yi daga kallon da yake mata sai da ya hura mata iskar bakinsa, "still in love with me (Har yanzu kina sona)?"
"Always D."
Tana bashi amsa ta yi ribas da motar ta fita daga gate ɗin da Maigadi ya buɗe tun fitowarsu.
***
"Ki manta da sanin da kika yi min a secondary school. Ki manta da mun taɓa auren miji ɗaya da duka abinda ya biyo baya a rayuwarmu. I am your lawyer, I need you to trust me (ni lauyarki ce, ina bukatar ki amince dani) ki faɗa min gaskiya. Idan kika ce zaki duba waɗancan abubuwan na baya ki ɓoye wani abu ina mai tabbatar miki zaki iya ƙare rayuwarki a kurkuku."
Susu kallon yadda Tauhidat ta rikiɗe tana magana babu alamun wasa ko wargi ta yi, taji ta ƙara aminta da zaɓarta da ta yi ta wakilceta. Wannan ba Tauhidan da ta sani bace, lauya ce a gabanta mai zaman kanta wadda ta san kan aikinta. Ajiyar zuciya ta yi, "[dan ban yarda dake ba ma wa ya rage min yanzu? Ban taɓa zaton zan ga rana irin wannan ba. Har yau babu wanda yazo daga gidanmu kuma na san cewa yanzu maganar nan ta zaga ko ina."
Ƙwallar da ta soma taruwa a idanunta ce tasa Tauhidat kara tausaya mata.
"Amma su kuwa me zai sa su gujeki a wannan yanayin da kike ciki? Musamman ko don baby ɗinki ina ganin kamar mamanki zata fi bata kulawa akan Nanny."
"Hmmm Tauhida kenan, iyayena basu gujeni ba, ni na guje musu."
"Saboda kin auri mai kuɗi?"
"Ɗan maikuɗi ba maikuɗi ba." Gani ta yi zata tonawa kanta asiri sai ta canja zancen da cewa ta yi mata tambayar da ta shafi case ɗin.
Ba haka Tauhidat taso ba. So ta yi ta yi maganar da ta danganci nadama domin ta tayata neman sulhu da ƴan uwanta. Abubuwan da ta yi mata a baya musamman sharrin nan yana nan manne da zuciyarta to amma idan suka tafi a haka ribar Alh. Audi ce. Yadda ta san shi zai iya amfani da abinda ta yiwa iyayenta lokacin auren Shamsu ya nuna kwaɗayinta a kotu. Jerin tambayoyin da ta tsara ta fara jero mata tana bata amsa.
"Ina son ki faɗa min duk abinda zaki iya tunawa akan Shamsu a ranar da abin ya faru."
Bakin gwargwado ta faɗa mata abinda ta tuna ta ƙara da cewa, "abu ɗaya ne ya dameni a cikin ƴan kwanaki kafin abin ya faru."
"Me kenan?"
"Yana yawan zama shi kaɗai a ɗaki da tunani. Sai kiyi ta magana ma bai ji ba. Na san cewa lokacin lalurarsa ta yi ƙarfi sosai amma duk da haka na lura akwai abinda ke damunsa bayan wannan."
"Wace irin lalura ce?" Ta tambaya ba don tana ganin amsar za ta zama da mahimmanci ba.
Abinda take ta ɓoyo yau ga sanadin faɗarsa ya taso. Nauyi taji ta ɗan duƙar da kai "yana fitsarin kwance."
Tauhidat ta ce, "zancen Shamsu muke yi ba Mubeen ba."
"Na sani. Kin yi mamaki ko? Ya ce min tun yana da shekara goma sha shida ya fara."
"What?"
Ta ce mamaki ya kusa kasheta a zaune. Sai ta tuna a wane matsayi take a wurin ta gyara maganar, "bai neman magani?"
Iya neman da ta san sunyi da wanda take yi a gefe ita ɗaya tsakanin bokaye da malamai ta dunƙule ta ce mata suna nema amma ba'a dace ba.
Rubutu tayi a ɗan littafin gabanta sannan ta ce, "to amma daga fitsarin kwance Susu sai kuma kawai ki ce ya yiwa Mubeen fyaɗe?"
Tsigar jikinta sai da ta tashi da ta tuna yanayin da ta kama shi da ɗan nasu.
"Ba sharri nayi masa ba. Abinda yasa ni bin bayansa ma wayar da ya yi ce da rana amma ban san da wa yake yi ba. Naji dai yace ana buƙatar ya gama kafin biyun dare. Ban ɗauki maganar da mahimmanci ba sai da na farka kusan lokacin naga baya ɗakin. Shi ne na bishi na gansu."
"Kina da labarin cewa report ɗin ƴan sanda ya nuna hatsari ku ka yi da kika gudu dashi wanda ya yi ajalinsa?"
Ƙaryatawa Susu ta yi kamar yadda ta yi tsammanin zata yi ɗin. Bayan waɗannan tambayoyin sai ta koma batun satar kuɗi wanda shari'arsa za a fara yi. Shi ma dai Susu ta yi rantsuwa ta ƙara da cewa bata da account a kowace ƙasa sai Nigeria. Banda kuɗaɗen da Shamsu yake bata a hannu ko transfer akwai kuma allowance da kamfanin Karam Holdings ke tura mata duk wata. Ƴaƴaanta ma kowa nada shi.
Abin ya sake zamewa Tauhidat sarƙaƙiya saboda ga shaidar saka hannun Jamal da na Susu akan takardar bankin da suka tura kuɗin. Joint account (na haɗin gwuiwa) suka buɗe ga kuma takardar yarjejeniyar idan kudin ya samu za suyi raba daidai. Agogo ta duba taga lokacin da ta bawa Jamal yaje office ya sameta ya kusa dole ta katse tambayoyin zuwa washegari ta tashi. Kiransa tayi bayan ta fito daga station ɗin taji muryarsa ba yadda ya saba yi mata magana ba. Hankalinta a take ya tashi ta soma yi masa tambayoyi.
"Asibitin Dr. Madaki zamu je. Flask ɗin ruwan zafi ne ya faɗowa Arƙam a ƙafa."
Allah Yasa bata tayar da motar ba, da ƙila ta dokawa wani saboda fargabar da ta kamata lokaci guda.
"Ya ƙone?" Ta tambaye shi a sanyaye cike

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment