Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da fargaba.
"Shi dai ya ce bai ƙone ba amma abin cikin flask ɗin ya yanke shi a babban ɗan yatsa."
Muryar Dada taji tana cewa Jamal yazo su tafi asibitin kada ya biye masa. Yadda jini yake zuba tana ganin sai anyi ɗinki a yatsan. Maganganunta sun sake tayarwa Tauhidat hankali. Hanyar asibitin ta nufa ko su rigata ko ta rigasu isa. Can kuma a gida anata rigima da Dada da Arqam. Ya dage bai ƙone sosai ba kuma yankan ma babu girma amma ta kafe wai ya zubar da jini ya kusa lita guda. Saboda a kwantar mata da hankali Haj. Manga ta ce suje ko plasta ne a manna masa a kafar su dawo. Suna fita Arƙam ya ce ya kaishi pharmacy sai ga wayar Tauhidat. Tambayar Jamal tayi ko sun kusa isa asibitin don har ta shiga reception ance basu zo ba.
"Muje asibitin kawai kaga Tauhida tana can."
Rai a ɓace Arƙam ya ce,"faɗa mata kayi? Why?"
"Matarka ce fa, kuma kirana ta yi bani na kira don na faɗa ba" shi ma ya sha kunu. Ɗauke hanya suka yi zuwa asibitin suna hararar juna.
***
"Ka san Allah Doctor sai ka faɗa min wanda ya ce ka canja report ɗin Mubeen" cewar Shamsu yana cije baki saboda azabar ciwon da yake ji a cikinsa. A tsaye yake ya dafa bango cikin ɗakin da yasa Dr. Madaki ɓoye shi saboda kada ya bar ƙasar. Dr. Madaki yana tsoron fada masa gaskiya bai sani ba ko bakinsu ɗaya tarko ne Alh. Audi ya ɗana masa.
"Kaga ni dai idan ba zaka faɗawa Alhaji cewa baka tafi ba jiya kamar yadda ya umarta to ka bar min asibitina. Bana son wani abu ya same ni haka kawai. Abinda na gani na rubuta."
Da ƙarfi Shamsu ya ce,"ƙarya kake yi. Da idona na shaida tabbas wani ya yi raping ɗin ɗana. Kuma ga alamu sun nuna ko waye baya son duniya ta sani."
Manunin yatsansa ya kai gaban fuskar Dr. Madaki, "hatta uban da ya haifeni bai san waye Shamsu ba. Na sani ban kula da rayuwar yarana ba a baya amma ko zan rasa raina sai na gano abinda yasa ake ɓoye dalilin mutuwar Mubeen."
Gwada sa'arsa ya yi cikin dakewar murya Dr. Madaki ya ce, "Shamsu kada ka tona abinda ake son binnewa domin kwanciyar hankalin gidanku."
Mummunan kallo ya jefawa Dr. Madaki a lokacin da maganar ta soma fassara kanta a ƙwaƙwalwarsa. Jikinsa na rawa ya ce, "kana nufin Baba ya san ko waye?"
Amsar likitan bata kai kunnuwansa ba yaji cikinsa ya bala'in murɗawa. Riƙe wurin ya yi a tare suka kai kallonsu ga cikin sai ga jini ya fara naso a jikin rigar. Neman faɗuwa yake yi Dr. Madaki ya tare shi da sauri ya ɗora akan gado. Yana ɗaga rigar yaga yadda yake zubar da jini alamun an sami matsala a aikin da akayi na farko. Bai san iyakar ciwukan da suke cikin Shamsu ba saboda jinyarsa kawai aka kawo musu. A wani asibitin gwamnati akayi masa operation dmɗin kafin Alh. Audi ya canja masa asibiti. Cikin sauri ya fito daga ɗakin ya sauka neman likitan da zai taya shi aiki don ga dukkan alamu dole a sake buɗe cikinsa.

ALHAMDULILLAH
Allah SWT Ya sake kawo mu karshen kasha na biyu a cikin wannan labari. Domin jin sirrin da Alh. Audi yake ta boyewa da ma yadda za ta kaya gabadaya ku nemi kasha na uku kuma na karshe a labarin CIZON YATSA.

SonSo
Batul Mamman.
[2/23, 7:34 PM] Nasma: Ganin su Dada da iyayensa da ya daɗe rabon da ya saka su a ido yasa shi sakin jiki. Jansa kawai ake yi ta kowane ɓangare ba mazan ba, ba matan ba. Bai san ta yadda zai kwatanta farincikinsa ba. Amma a haka yayi ta raba idanu yana neman ɗan uwansa rabin jiki. Ayi faɗa a shirya duk da haka basu da kamar junansu. Ta bayansa yaji an rungumo shi da ƙarfi ana dukan kafaɗarsa.
"Big Broooo."
Ba kowa bane ya sani sai wanda yake ta nema. Haɗe rai ya yi yana cewa ya sake shi.
"Kai kuwa Arƙam yaron nan wuni ya yi yana zancen dawowarka amma shi ne kake korarsa haka. Zo nan kaji Jamal." Anti Rabi’a ta janye shi ya ɗora kansa a kafaɗarta yana yiwa Arƙam gwalo. Dariya ya bashi ya fasa mitar me ya hana shi zuwa ɗaukarsa daga airport saboda ganin wani yana masa murmushi. Kallo ɗaya ya gane shi duk da ko a hoto bai taɓa ganinsa ba.
"Brother Shaheed yau dai mun haɗu." ya ce yana miƙa masa hannu tare da mayar masa da martanin murmushinsa. Mamakin kamaninsa da Haj. Manga Shaheed yake yi ya ce masa,
"Ko a waje na ganka ni dai zan kamoka na kawo gida saboda kamaninka da Nanna."
Kamar wasu daɗaɗɗun abokai suka taɓa hira. Shaheed ya gabatar masa da iyalinsa suka gaisa da Sariat sannan ya tambayi yaran sunayensu. Gefensu an jera kujeru da tebura manya guda uku wadanda zasu dauke duka mutanen. Ga abinci ana ta jerawa domin gabatar da karamar walimar cikin gida ta murnar dawowar Arqam da aurensa da Tauhidat. Haji Lawalli ne da wannan kokarin saboda ya tunatar dasu cewa sunna ne gabatar da walima bayan ɗaurin aure. Babu zancen biki yanzu duba da yanayin da aka ɗaura auren a ciki. Abu ne na gaggawa sannan kuma idan suka yi wani abu duniya ma sai ta zagesu ace anyi rasuwa ga ruɗanin da ake ciki na batun sata da Shamsu a gadon asibiti. Dakatawar dai ita tafi.
Hannunsa Jamal yaja zuwa cikin gidan har ɗakin Haj. Manga. Suna shigowa Tauhidat ta tashi daga kan abin sallah inda ta yi sallar Isha ta fice ta basu wuri. Da ido Jamal ya bita ya koma hararar yayan nasa ko ya yi mata wani abu tunda tun jiya ya fuskanci ransa ya ɓaci. Haj. Manga ta shigo suka gaisa ta tambaye shi aiki da abokan arziƙi su Abu Usama.
"Nanna ina ne ɗakina zan yi wanka kafin nayi sallah."
Arƙam ya ce lokacin da ya tashi. Zaunar dashi ta yi ta ce akwai bayanan da take son yi masa tukunna saboda idan bata yi ba suka fita cikin ƴan uwa dole wani zai faɗa. Hankalinsa ya tattara gareta yana sauraron jawabinsu game da abinda ya faru a gidan Alh. Audi. Shi ko haka bata faru ba dama bai zo da niyar ragawa Kawun nasu ba. Abubuwan da suka faru a baya ciki kuwa harda raba shi da mahaifarsa sai ya nuna masa cewa shi ba kanwar lasa bane. Yawon da yake yi a ƙasashen da ake yaƙe-yaƙe ya daɗa buɗe masa ido da fahimtar zalunci da son zuciya na ɗan Adam. Abu na biyu kuwa rufe ido ya yi ya dinga yiwa Jamal faɗa akan shaye-shaye. A ganinsa wannan ne ya bada damar Alh. Audi ya ɗora masa abinda bai ji ba bai gani ba. Duk mai shaye-shaye ai abin rainawa ne don kuwa bashi da wani kwarjini a idon jama'a. Haj. Manga bata hana shi ba a matsayinsa na yayan Jamal. Shi kuwa sai bada haƙuri yake yi yana nanata alƙawarin ya dena. Haƙurin nasa bai burge Arƙam da zuciya ta gama cinsa ba. Ganin haka ya tashi ya fita ya barsu.
Ɗakin da Aidan yake ciki ya shiga don ya tabbatar Tauhidat tana can. Ai kuwa tausa ya sameta tana yiwa Aidan saboda mutane a gidan sunƙi fitar dashi daga ɗaki. Wani ko bai yi niyya ba zai iya faɗin abinda zai iya janyo matsala bisa kuskure. Shi yasa suka zaɓi ɓoye shi ga kowa. Dada da Umma ne kaɗai suka san yana gidan.
"Haka kawai mutum daga dawowarsa zai zo yana bamu attitude, waye bai iya faɗa ba?" Taji Jamal yace yana gunaguni.
"Yayana kai da wa?"
"Wa kuwa banda..." ya dan riƙe baki, "mijinki ne fa yanzu sai ki nuna min baki ji daɗi ba gara kawai nayi shiru."
Dariya ta yi, "fadi abinka nima kafin mu iso gida har ƙwalla sai da ya sani."
Wata muguwar dariya Jamal ya saki harda buga ƙafafgunsa, "ahh ki ce ni dake sammakal. Bari na zauna kawai muyi gulmarsa ko ma huce."
Kwatanta yadda Arƙam ya dinga yi masa faɗa ya yi suka sha dariyarsu harda Aidan. Sai daga baya Tauhidat ta ce amma dai gaskiya ya dena shan komai ko don lafiyarsa.
Taɓe baki ya yi, "ahaf ai na sani. Kare masa zaki yi tun baki kwana da aurensa ba. Nan da wayewar gari ƙarshenta sai kin tambayeni suna na ma. Gara nima dai na nemo wata Celine Dion na aura." Dariya ta yi mai isarta sannan ta tashi domin sauka ƙasa.
***
A ɗakin Haj. Manga kuma bayan fitar Jamal zancen Tauhidat ta sako masa. Ya ɗage mata gira "Jamal ya faɗa min karatu ta zauna yi da sa hannunki. Kinga Nanna mu bar zancenta bari nayi wanka jikina ba dadi."
"Oh ni wannan yaro kamar ba a gasa masa baki ba da yana jinjiri." Ta ce tana girgiza kai.
Murmushin dole tasa Arƙam, "its not too late zan gasa masa da iron."
"Naji amma kafin ku fara shirmenku ka sani cewa ɗazu aka ɗaura aurenka da Tauhidat."
Dariyar da yake mata ce ta ɗauke kamar an zare masa batir ya ce, "aure fa ki ka ce Nanna?"
Gyaɗa kai ta yi ta koro masa bayanin komai yadda zai fahimta. Rasa inda zai ajiye zancen ya yi a zuciyarsa. Ya yi murna sosai amma sauran jawaban na kutsen da Alh. Audi yake neman sake yi masa sai da ya yiwa zuciyarsa dabaibayi.
Can ya nisa ya ce, "Ta san cewa an ɗaura mana aure?"
"Ina faɗa mata na turosu ɗaukarka da direba."
"So ta sani dai?"
Bata san me yake tunani ba ta kuma cewa ta sani amma bata daɗe da sanin ba.
Da gaske ransa ya sosu ya ce, "amma shi ne taƙi faɗa min tun a can?"
"Ikon Allah, to ni ba gashi na faɗa maka ba yanzu."
Cewar Haj. Manga tana harararsa. Tunowa ya yi da yadda ya dinga yaƙi da gangar jiki da ruhinsa akan tsare mutumcinsu su biyun bai rungumeta a gaban mutane ba lokacin da idanunsa suka sauka a kanta. Shi kaɗai ya san halin da ya shiga amma don mugunta Tauhidat ta kama bakinta ta rufe. A sanyaye ya ce, "atleast da sai ta faɗa min."
"Meye marabar airport ɗin da nan ne Arƙam? Ni ba gashi na faɗa maka ba. Kunya kuma ai ado ce a wurin mace. So kayi kana fitowa tace maka sannu da zuwa maigida ko me?"
Zube mata ya yi akan gado don ya gaji da zaman ya kwanta, "that was the longest drive of my life (wannan shi ne mafi nisan tafiyar motar da na taɓa yi)."
Haj. Manga ta riƙe baki, "kai Arƙam kaji tsoron Allah. Tafiyar da bata kai awa guda ba kake cewa tafi kowacce da ka taɓa yi. Kai da a wannan ƙasar taku daga nan zuwa can sai mutum yaji kamar bangon duniya za a kaishi."
Murmushin gefen baki ya yi daga kwance, "ba zaki gane bane Nanna, you don't know how much I love her (baki san irin son da nake mata ba)."
"Ban sani ba" ta ce tana ture shi daga kan gadonta, "tashi ka fice min daga ɗaki. Ga key can kusa da jakata ka ɗauka na ɗakinka ne. Jamal zai nuna maka a ƙasa."
Fita ya yi yana murmushi bakinsa kamar gonar auduga. Bashi da kalmar da zai kwatanta wannan zuwa Nigeria din. Yaji abubuwa marasa daɗi ya kuma ji wanda ya ɗaukeshi ya ɗora a sararin samaniya saboda tsabar daɗi. Wai shi Arƙam ne ya zama mijin Tauhidat.
"Finally she is mine."
Ya furta a hankali wanda laɓɓansa ne kaɗai suka motsa da wani irin karsashi. Daga bisani kuma ya murmusa.
***
Kusan karo suka yi. Ita ta fito daga wurin Aidan da guntuwar dariyarta shi kuma daga wurin Haj. Manga. Ja da baya ta yi da sauri ya tsura mata idanu yana kallonta tare da lumshe idanu. Cikin wata irin siga yake magana kamar wanda aka yiwa duka, "raka ni ɗakina."
Da sauri Haj. Manga dake bakin ƙofar ɗakinta ta buɗe da taji abinda ya ce. A ranta tana ayyana rashin kunyar maza. Idan bata yi da gaske ba sai ya nunawa kowa bai tashi cikin masu kunya ba.
Ƙofar ɗakin ta nuna masa da hannu,"ga ɗakin naka can. Idan ka shiga falon ɗakuna biyu ne. Na cikin ne naka." Ta kama hannun Tauhidat, "ke kuma wuce muje ki shirya mu sauka. Kun barmu da yunwa dare yana ƙara yi."

Tsuke baki Arƙam ya yi ya ɗauki jakar kayansa ya sauka. Da sauri ya yi wanka ya shirya ya fito babban falon. Tare da Shaheed suka fito waje kowa yana zaune ana ta hira ga fitilu kamar rana. Tebur ɗaya iyaye maza ne, ɗaya na mata sai kuma na ukun Shaheed ne da matarsa sai Jamal da Arƙam. Daga can gefensu a ƙasa an shimfiɗa kafet mai kyau Dada da Umma sun zauna tare da yaran Shaheed. Iyabo kuma tana wurin Aidan.
Fitowar Haj. Manga da Tauhidat ce ta dakatar da hirrakin dake tashi aka fara cewa ga amarya ta fito. Baƙin pencil skirt ta saka da pink tunic top mai dogon hannu wadda ta kai mata ƙwauri. Kanta pink ɗin ƙaramin mayafi ta ɗaura sannan ta yafa baƙi da yafi shi girma ya sauko ƙirjinta kaɗan. Idanun Arƙam na biye da ita har ta ja kujerar kusa da wadda Haj. Manga ta zauna suka ji muryar Jamal,
"Ƙanwata ga wurinki nan" Ya ce yana nuna mata kujerar dake tsakanin tasa da ta Sariat.
Mugun kallon da Arƙam ya bishi dashi dama yake jira ya kwashe da dariya. Kunya ta kamata haka ta tashi da iyayen suka dage ba zata zauna cikinsu ba. Kafin ta ƙaraso Shaheed ya ja mata kujerar dake tsakaninsa da Arƙam. Ko daidaita zamanta bata gama yi ba, taji yatsun Arƙam sun ratsa tsakanin tattausan hannunta sun yiwa kansu mazauni cikin nata yatsun. Sau ɗaya ta kalle shi gabanta na matsanancin faɗuwa kamar wadda ta yi tsere, shi kuwa ya ɗauke kai. Abincin gabansa ya cigaba da ci, amma hankalinsa ko kaɗan ba a kwance yake ba. Ɗumin hannun Tauhidat da bai taɓa tunanin zai ji ba shi ne yake fizgarsa.
"Ki ci abinci mana Tauhidat ko babu abinda ki ke so a nan?" Cewar Sariat.
Bowl ɗin farfesun hanta da tumbi Shaheed ya miƙa mata don ya san tana son shi. Hannun damanta yana kurkukun Arƙam sai ta miƙa na hagun za ta karɓa. Shaheed ya ɓata rai yana cewa idan yara suka yi ta iya yi musu faɗa amma ita ta miƙo masa hannun hagu. Jin haka ta ɗan ja na daman amma sai ji ta yi Arƙam ya ƙara karfin riƙon alamun ba zai saki ba. Murmushin dole ta yiwa yayanta ta ce ya ajiye a wurin za ta ɗauka.
Gani ya yi tana satar kallon Arƙam sai ya tashi yace bari yaje wurin yara kada su hana kakaninsu cin abinci. Yana tashi Sariat tabi bayansa wai ta gaji bayanta na ciwo. Dama kuma ba kwana zasu yi a gidan ba gara su fara harama. Wuri ya rage su uku. Jamal ya dinga turowa Tauhidat abinci yana cewa ta ɗebi wanda take so. Sai dai ta amsa da to taƙi ɗago hannu. Ɗan ɗago kai ya yi daga inda yake zai leƙa wurin hannun nasu.
"Wai lafiya kike kuwa?"
Ya ce yana tashi yadda zai gani da kyau. Hanyar cikin gidan Arƙam ya nuna masa,"Get lost Jamal. (ɓace/tafi)"
"Duk abin mutum bai isa ya rabani da ƙanwata ba. Shugaban ƴan farraƙun ma muna nan sai mun soya masa aya a hannu."
Ya tashi fuskar nan babu annuri. Ya gama shirin baza kunnuwa yaji hirar masoya shi ne dan buƙulu Arƙam ya kore shi. Ita kuma wadda yake taƙama da ita ko ta ɗan tare masa don ya ƙyale shi. Shi ma kan kafet ɗin ya koma wurinsu Dada tunda buƙata bata biya ba. Yana tashi Arƙam ya sakar mata hannu shi ma ya tashi.
"Ni kaɗai zan zauna? Yunwa fa nake ji." Ta tambayeshi tana kyaɓe fuska
"Ban hanaki cin abinci ba amma ina da abinda zan yi a ɗaki kafin na kwanta."
"Amma fa kaine ka riƙe min hannu ka hanani cin abinci tare da mutane."
Murmushi ya yi wanda ya bayyana fararen hakoransa " I thought you wanted it (na zata kina so)."
Ga mamakinsa sai tayi murmushi ta ce "I do. Now please ka tayani zama naci abinci."
Yana son yin dariya yana dannewa kada tace ya damu da yawa. Idan ita bata damu dashi ba shi ma ya iya jan aji. Ƙin zama ya yi ya ce ta nemi mai zama da ita. Da ta ce za ta kai ƙarar shi wurin Nanna ya ce Bismillah. Bai yarda zata yi ba sai da ta buɗe baki ta kirata abinda ya sashi zama da sauri.
"Tauhida mene ne?"
Dariya take tana kallon yadda yake girgiza kai ta ce, "naji kamar kin kirani ne."
"Yi zamanki ba kiranki nake ba."
Abincin ta zuba daidai yadda zai isheta ta riƙe cokalin da hannun dama ta kamo hannunsa da na hagunta. Yadda ya yi mata ta yi masa itama ta kuma ɗauke kai kamar bata san yana kallonta ba. Da ƙyar take tura abincin saboda ba ƙaramin takura ta yi ba amma ta dake. Bata son yadda yake mata ɗinnan. Shekarun da yawa, za ta so suyi hira su cike gurbin da ƙaddara ta sanya tsakaninsu.
"Ya hanya" ta tambaye shi idanunta akan plate ɗin gabanta.
"Lafiya."
"Ya aiki?"
"Lafiya."
"I miss you too."
Ta ce tare da sakin hannunsa ta yi gaba. Da saurinsa yabi bayanta maganar na ratsa kowace jijiya a jikinsa. Wurinsu Dada ta tafi ta zauna bata shiga cikin gidan kamar yadda yaso ba. Shi da ya biyota sai ya rasa yadda zai yi. Dole ya sami wuri kusa da Jamal. Kujerun duka an juyasu suna fuskantar su Dada ana ta hira cikin farinciki kamar babu abinda yake damunsu. Kiransa Haj. Manga ta yi da hannu ya koma kusa da ita. Kamar yadda ta ce zata yi kuwa a gaban kowa ta ce,
"Ga ƴata nan Arƙam. Marainiyace gaba da baya. Mahaifinta ya sadaukar da rayuwarsa dominmu. Sun haƙura da cin zarafi a ɓoye da Alh. Audi ya yi musu saboda kare rayuwarmu. Ba zan iya saka musu ba, hasali ma dai alfarmarsu na sake shiga da na nema maka aurenta. Akan ce ka haifi ɗa baka haifi halinsa ba, to ni ban haifi Tauhida ba amma na san ta ciki da bai. Arƙam abu ɗaya ne nake so daga gareka, kada ka bari nayi danasanin aura maka ita. Ban ce kullum za a kwana a gado ba amma duk ranar da ku ka faɗo kan tabarma to banda ture-ture."
Arƙam ya nuna inda Tauhidat take zaune ya ce, "ni bani da problem da kwanciya akan tabarma ɗin. A Yemen babu inda bama bacci. Kawai dai ki faɗa mata kada ta shureni don nima bana yi."
Ai kuwa suka kwashe da dariya. Sariat ce kawai bata fahimta ba ta matsawa Shaheed ya fassara mata. Arƙam ya bisu da kallo don bai san me ya ce da zai saka su dariya haka ba.
"Gaskiyata na faɗa fa, or did I say something wrong?"
Dariyar suka cigaba ya soma ƙulewa. Kawu Garba ne ya tausaya masa ya ce, "Haj. Manga kin ɓatar dashi da wannan dogon jawabin. Kaga Arƙam tana nufin ka riƙe matarka amana banda rigima."
"Ohk Kawu amma kwana akan tabarmar fa yaushe ne? Har na tafi ban taɓa jin wannan tradition (al'adar) ba."
Tsabar dariya Jamal ko tsayuwa ya kasa yi da kyau. Tauhidat ce ta fara shigewa ciki tunda bai dace ta yi a gaban surukai ba. Da ɗaiɗai aka watse Shaheed ya haɗa kan iyalinsa suka wuce gida. Mazan su ma tafiya suka yi wani hotel kusa da gidan. Da yake duk an gama gajiya makwanci kowa ya nema. Iyabo ta bi su Shageed ga kuma baki a dakin Haj. Manga saboda haka Tauhidat sai ta ja akwatinta zuwa ɗakin da Aidan yake.
Gajiyar da Arƙam ya kwaso bata yi nasarar saka shi baccin da yake tunanin zai yi ba. Tauhidat ke yawo a kowane lungu da sako na zuciyarsa ta hana shi sakat. Yana gama shirin bacci dama buɗe ko ina ya yi a ɗakunan ɓangaren guda biyu neman tabarma. Bai ga komai ba a falo da ɗakinsa. Ɗayan kuma babu komai a cikinsa ko labule ba a saka ba. Hannunsa ɗaya a kugu ɗayan kuma ya riƙe haɓa yana tunanin to a ina tabarmar da zasu kwanta take? Abin haushin ma bashi da sim card na Nigeria kuma babu numbarta bare ya kirata. Gani ya yi zaman ba zai kaishi ko ina ba ya tashi lokacin shabiyu ta gota ya tafi ɗakin Jamal. Kamar ɓangarensa shi ma falon babu kaya sosai a ciki sannan ɗakin farkon babu komai. A na biyun irin nasa ya same shi kwance shame-shame yana bacci. Ɗan duka ya kai masa a baya a hankali. Da yaƙi tashi ya yi masa guda mai shiga sai gashi a zaune yana murza idanu.
"Wane ɗaki Cuddles take?"
Bubbuga ƙafa ya yi akan gadon saboda takaicin tashinsa da ya yi ,"haba don Allah sai ka tasheni don baka ganta ba. Kaje ka kwanta ƙila ta bi Shaheed."
"Bata tafi ba ina wurin ya tafi."
Da ya fara wartsakewa sai ya haɗe rai, "wa ka yiwa masifa ɗazu?"
Idan ba lallaba shi ya yi ba sai su kwana Jamal na ja masa rai, "kayi haƙuri don Allah tana ina? Na gaji sosai Jamal I just need to see her kafin na kwanta."
"Idan ka hau sama ka shiga ɗaki na uku, I repeat na uku. Idan ka shiga ɗakin Nanna ko inda su Dada suke ni babu ruwana."
Yana gama faɗa masa ya koma ya kwanta, shi kuma Arƙam ya hau saman kansa tsaye. Tauhidat ta dage sai ta bashi wahala ko tausayinsa bata ji. Haushin kansa yake ji da ya kasa haƙura ya matsu da sake ganin fuskarta kafin ya kwanta. Ƙila ta daɗe da dena son shi shi yasa bata damu ba.
A hankali ya buɗe ɗakin ya shigo da sanɗa saboda kada ya tasheta. Motsin ƙofar ya tada Aidan ya buɗe idanu tar yana kallon duhun Arƙam yana tahowa wurin gadon. Abinda kakansu ya yiwa Mubeen wanda ya saka shi kuka ya tuna. Ihu ya saka da ƙarfi wanda ya rikita Arƙam don bai san da wani a ɗakin ba. Tauhidat kuma ta taso a firgice daga kan bargon da ta shimfiɗa a gefen gadon. Cikin duhun ta kai hannu kansa shi ma Arqam ya kai nasa saboda ya fahimci kamar yaro ne. Ba dai ta haihu da Shamsu ba aka rufe masa. Hakan ba zai rage masa sonta ba amma...Muryarta yaji tana cewa,
"Shhhh Aidan nice."
"Uhmm, uhmm" ya ce cikin kuka. Hannu ta miƙa sai ta kamo na Arƙam. Ihu itama ta saki har yafi na Aidan.
"Shit! Cuddles its me" Arƙam ya ce.
Zuciyarta bata dena bugawa ba saboda ta riga ta tsorata ta ce ya kunna musu fitila. Kasa gane wurin ya yi ihunsu duk ya ruɗa shi sai da ta tashi da kanta ta kunna. Tsayuwar kallonta ya yi bata ma sani ba tana saurin komawa kan gadon. Kayan bacci ne cotton a jikinta dogon wando da riga sai hula da ta saka. Gadon ta koma ta zauna sannan ta janyo Aidan jikinta. Da ido yake ta bin Arƙam shi ma sai ya zauna daga wurin ƙafafunsa. Yana kallonsa ya gane bashi da lafiya. Tissue ɗin da Tauhidat ta ciro domin goge masa yawu ya karɓa ya goge sannan ya kama kunnuwansa yana yi masa murmushi.
"Sorry na baka tsoro."
Ya miƙa masa hannu a wayance yana son gane yanayin lalurar tasa batare da ya saka shi jin wani iri ba. Ganin bai iya miƙo nasa ba amma yana murmushi sai ya kama da kan sa.
"Ka haƙura?"
"Uhm."
"Good boy."
Sumbatar goshinsa ya yi a lokaci guda yaron na shiga ransa. Kwantar dashi ya yi akan pillow yana shafa kansa har ya soma lumshe idanu. Tauhidat sai ta jingina bayanta da gadon tana kallonsu tana murmushi. Haɗa ido suka yi da Arƙam ta yi saurin runtse nata idanun. Sun ɗauki kusan rabin awa sannan Aidan ya koma bacci. Tun Tauhidat na gyangyaɗi ta buɗe ido da ƙyar har bacci ya yi awon gaba da ita ta kwanta a gadon. Kashe

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment