Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cigaba da yi masa bayanin cewa ciwukan jikinta sun basu dukkan wani taimako da ya dace. Babbar matsalar shine tabon da aka yiwa zuciyarta sai sunyi hakuri kuma sai an daure. Yanzu bazasu gane girman abin ba sai taji saukin ciwukan jikinta.

Suna wannan tattaunawar ne suka jiyo ihunta. Tare suka fito da sauri tana neman fita Dahiru ya saki ledojin hannunsa ya kamota. Jin namiji ya tabata ta sandare cikin murya mai ban tausayi tace
"ka rufa min asiri BB ni ba 'yar iska bace aure za'ayi min. Kayi hakuri don Allah"

Dahiru bai san lokacin da hawaye suka zubo masa ba a yayin da Ade da Yaya suka rikota suna ta koke koke. Baffa da Inna ma abin yayi matukar shigarsu suna kallo aka mayar da ita dakin.

Ba su suka sami kanta ba sai bayan isha da aka kara mata wata allurar da magunguna bacci mai mugun nauyi yayi awon gaba da ita. Sai a lokacin suka fara batun tafiya.

Baba yace Ade tazo su tafi don yasan zuwa yanzu Iya ta sami labarin zuwanta gari gashi bata je gida ba. Shima nasa iyayen dole zasu ji daga wurinta da kuma yara da suka tura musu daga makarantar allo su zo su tada hankalin rashin sanin me yake faruwa.

Ba don taso ba sai don kara da kawaici ta bisu suka tafi.

Su Inna gida suka wuce da Dahiru yayin da Baba da Baffa suka tsaya yana yi masa bayanin yadda abin ya faru. Ade har tayi hanyar gidansu wanda iyayen Mal Fatihu da Iyarta suke ciki tare sai ta fasa. Gidan Mal Isiyaku ta wuce kai tsaye.

Ummiyo ce ta amsa mata sallama Inna ta zaga bayi. Tana fitowa tayi arba da Ade a tsakar gida tace ta shigo cikin rumfa. Dahiru yana bayansu duhu yasa basu ganshi ba. Zai shiga kawai ya ga Ade ta durkusa a kasa gaban Inna tana kuka sosai.

"Don darajar Al'Qur'ani da iyaye Innar Dahiru ki rufawa yarinyar nan asiri. Na sani maganar aure da Dahiru ko ba'a fada ba ta tashi kamar yadda nasan da wuya wani ya taba aurenta. Amma ki taimakeni ko don kada zaman garin nan ya gagaremu don Allah ki rufa mana asiri"

"Haba Sa'ade sai kace wata bare? Wannan magana nayi miki rantsuwar duk ranar da kika ji ta a waje to daga bakin wani ta fito ba ni ba. Bazan taba fadawa kowa an yiwa Mawadda fyade ba. Kinga ai bamu ma san takamaimai me ya faru ba"

Dahiru ja da baya yayi har wani jiri yake ji. Tausayi sosai Ade ta bashi. Motsin da yaji a bayansa yasa shi juyawa ko ma waye ya gudu kafin ya waigo.

Har Ade ta fito tana ta yi mata godiya. Ita dai Inna bata da niyar tozartasu amma taji dadin da kafin magana tayi nisa Ade ta gane cewa batun auren nan a barshi kawai.
****

Kusan tare Ade da Baba suka shiga gidan iyayen nasu. Iya tana daga dakin farko idan an shiga wani soro sai 'yan tumakinta. Daga soro na biyu kuma tsakar gidan iyayen Mal Fatihu ne wato wa ga Iya. Rashin jituwa da dangin miji bayan rasuwarsa yasa ta dawo gidan.

Suna sallama Innar Fatihu da Malam babansa da Iya suka taso suna tararsu da tambayoyi.

Malam yace "kun daga mana hankali yara tun dazu sun zo sun ce Mawadda ba lafiya. Tana ina yanzu? Yaushe ta dawo garin ma duka bamu da labari?"

Iya kuwa harara ta dokawa Ade "wani sabon salon kinibibin ne kika shigo garin nan sai a bakin jama'a naji wai kin fara biyawa gidan tsohon mijinki."

Baba na gaisheta kamar yadda ta saba tun rabuwarsa da Ade ta juya masa keya harda tura dankwali gaba.

Innar Fatihu ta tabe baki "ke kam zan ga lokacin da zaki girma, yaro na gaisheki kina juya keya abu duk a gwaguye"

Sanin cewa yanzu zasu fara rigima Malam ya tsawatar "bana son shirme, ance yarinya ba lafiya baku tambayi halin da take ciki ba sai rigimarku da bata karewa. Sa'ade ina kuka barota?"

Daga ita har Baba duka jikinsu a sabule ga idanunta a kumbure saboda kukan da bata san adadinsa ba a yau.

Baba ne yace duka su zauna magana mai mahimmanci zasu yi. Jin haka Iya ta kwala ihu harda zaman 'yan bori ta soma kuka haikan tana fyatar majina.

"Ni Tarasulu me zan gani, wayyo Allah mun shiga uku mun lalace."

Ade ta bata rai ganin wannan abu da mahaifiyarta take yi "Iya meye haka kuma don Allah?"

Sake fyace hanci tayi sannan ta dago "cha nake ta cika ne, na ga ke da Fatihun kamar kwai ya fashe muku a ciki gashi yace magana ce mai mahimmanci"

Malam ya girgiza kai cike da takaici.
"Fatihu ina jin ka kaji"

Kai a kasa Baba ya soma labarta musu abinda ya sami Mawadda. Kafin ya kai karshe Iya ta mike tana kumfar baka zani na neman faduwa tana kamo shi

"Qur'anin Allah Fatihu baku isa ba...tabdi yo ni na taba jin danyen aiki irin wannan ma. 'Ya'yan Haule sunje sunyi aikatau dinnan kowacce ta kai mutumci gidan miji sai tawa jikar saboda ka tsani uwarta. Idan ma wata manakisa kuka shirya ku kwance don billahillazi bazan yarda ba." Duk da fada take yi sai kuka kuma yaci karfinta. Ba karamin so take yiwa 'yan jikokinta ba musamman Mawadda abokiyar fadanta. Yarinya ba sawa ba fitarwa har haushi take bata. Ade ta riko hannunta suka zauna tana ta kuka da mita.

Malam da Innar Fatihu suma abin ya taba su. Shawara aka tsayar da safe zasu koma asibitin da kuma tsawatarwa cewa su iya bakinsu kafin magana ta fita don bazata yiwa kowa dadi ba cikinsu.

Iya ta mike tana gallawa Baba harara "da yake ba jikar da kuke son uwarta bace shine zaku ce sai da safe zaku je. To ni yanzu zan tafi. Ke kuma.." ta dungure kan Ade "kin kwaso jiki kin dawo gida har zaki iya bacci kin bar yarinya a wannan halin"

Innar Fatihu ta kada baki tace "Abin ko kara babu dadin abin nima jikata ce"

"Da nayi karar ba ga irinta nan ba. Ca nake 'ya'yan Haule har biyu a Habuja suka yi aikin. Daya a Jos dayar kuma a Fatakwal ina nan rahoto na zuwa gareni. Sai ni don an raina mu nan nan Kaduna fa aka kai min Mawadda. Ina Kano ina Kaduna banda wulakanci. Kuma ku kwana da shiri harda shi shegen gorar ya taba min ita magana bata mutu ba. Idan ana yiwa 'ya'yan mutane fyade a binne magana a bar yarinya da bugun zuciya to Yasin ni sai mun shiga kotu. Yaro ko daga gidan Karuna ya fito zamu kara ai talauci ba hauka bane."

Har ta bar tsakar gidan ana jiyo sababinta. Ade ta tashi zata bita Malam ya hana. Da kansa yaje ya sameta tana laluben jaka wai zata tafi asibiti da shirin kwana. Harda bashi sallahun ya fadawa Fatihu matarsa komai dare zata dawo.

"Tarasulu bana jindadin irin wannan halaye naki ko kadan. Kiyi hakuri zuwa goben da wuri zamu tafi. Sa'ade da Fatihu duk 'ya'yana ne ko don kaddara ta rabasu sai mu kasa hakuri komai sai mun fassara shi da cewa da gangan akeyi. Ki rinka tauna magana kin girma fa."

Shiru yaji tayi ga mamakinsa ashe kuka take yi "yaya fyade ne fa? Yarinya kamar Mawadda mai zurfin ciki ta hadu da wannan bala'i ina zata saka kanta? Wallahi ko dan uban waye yaron nan bazan barshi ba. Allah Ya isa, Allah Ya kwashewa duk wani mara imani mai wulakanta da tozarta mutumcin mata yara da manya domin biyan bukatarsa"

Kukanta ya taba masa zuciya sosai. Su kadai suka rage a gidansu basu da kamar juna. Da kyar ya lallabata ta hakura zuwa wayewar gari. Sai dai babu wanda ya runtsa cikinsu kamar yadda a asibiti ma Yaya bata yi baccin ko da awa daya ba saboda yawan tashin da Mawadda take yi tana ihu.
*****

Tara na safe a asibitin tayi musu gabadaya. Yaya tana gaishe da Iya taki amsawa sai harare harare takeyi ita ba'ayi mata adalci ba.

Ganin Mawadda duk ta kare shi yafi daga mata hankali. Tana kuka tana surfawa BB tsinuwa da Allah Ya isa.

Duka zaman jiran likita suke yi sai ga sergent Bala da Nalado sun dawo. Ba jimawa Dahiru ya shigo ya gaishe da kowa na dakin.

Rabonsa da Mawadda tun ranar da zata tafi aiki sai jiya. Yau yana dago kai suka hada ido tayi saurin rufe nata hawaye na biyo baya. Me ya kawo shi inda take bayan yanzu bata da sauran daraja da kima? Ita din yanzu abar gudu ce da kyama ta tabbatar maganar aure tsakaninsu tuni tabi iska.

'Yan sanda sun nemi ta sanar dasu yadda abin ya faru sai dai idanun jama'a yasa ta kasa sai zubar hawaye. Idanunta har wani kwarmi suka yi saboda yini kuka. Ganin haka aka sallami kowa sai Babanta da Iya wadda ta dage babu inda zata je. Ita ta rike hannun Mawadda ta fada musu abinda baki zai iya fada. Iya tayi kuka har muryarta ta dashe. Kofar dakin ta dawo ta zayyane musu halin da Mawadda ta shiga a hannun BB. Duk wanda yake wurin yaji tausayinta sosai. Dahiru zuciyarsa kamar ta buga. Ji yake inama shi din wani ne da ko ya bar BB da rai sai yayi masa abinda idan ya ga mace ko da tunkiya ce sai ya canja hanya. Abu daya ya kudurcewa zuciyarsa shine aurensa da Mawadda babu fashi. Idan da yana sonta ne yanzu kaunarta da tausayinta sun taru sunyi masa yawa a zuci. A shirye yake ya fuskanci iyayensa da duk wanda zai nemi hana shi aurenta saboda yasan hakan shine daidai. Kasancewa da masoyi a lokacin da kaddara mara dadi ta same shi shine cikar soyayya.
[03/12 23:02] Meela Adeel: *GUMIN HALAK...*馃挵5

*Batul Mamman*馃挅


Bayan dan lokaci 'yan sandan suka fito. Sun bawa Baba shawara akan cewa idan yana bukatar maka BB a kotu sai yayi shiri sosai saboda shari'a yanzu sai da kudi. Sannan zasu zo da abokin aikinsu wanda zai dauki hotunan raunukan jikinta washegari saboda kafa shaida. Mutanen sun basu tausayi musamman Mawadda. Har hakuri suka bawa Baba wulakancin da suka yi masa a ofishinsu. Godiya yayi musu shima ya raka su sannan ya dawo dakin.

Iya tana rungume da Mawadda kamar za'a kwace mata ita. Da yake sun taho da abinci Innar Fatihu ta zuba mata kunun gyada fari kal yana ta kamshi amma taki karba.

Yaya tace "Inna haka muke ta fama taki cin komai. Jiya nayi fadan nayi nasihar amma duk a banza"

Nan fa suka shiga lallabata amma da aka matsa mata ma sai tasa musu kuka
"Ku barni yunwa ta kasheni na huta don Allah"

"Ahir na kuma jin wannan zance Mawadda. Kin taba ganin bawan da yafi karfin jarabta daga Allah?" Cewar Innar Fatihu

Iya ta tsuke baki
"Ya haka ne, abin kiyi mata sannu-sannu sai fada saboda dai...."

Malam ne ya katseta "za'a sai da hali ne Ta Rasulu? To dai asibiti ne ba gida ba. Sai mu koma inda muka fito iyayenta suyi jinyarta"

Shiru tayi babu wanda ya sake cewa uffan kada Malam ya korasu gida.

Ade ta kurawa Dahiru ido yana tsaye daga gefen kofa. Tun da ya gaishe su bai sake cewa komai ba. Tana ta lura da yadda yake kallon Mawadda. Ita dai tasan batun aure babu amma ga dukkan alamu akwai dalilinsa na dawowa wurinta a yau. Cike da hikima irin na iyaye mata ta kafe Baba da ido har sai da jikinsa ya bashi tana kallonsa. Yana dagowa ta cilla idanunta bakin kofa nan ya gano me take nufi. Gajeren murmushi yayi ya riko hannun mahaifinsa yana cewa gara su fara jin nawa za'a cajesu kudin asibiti tun wuri. Malam yayi na'am da hakan suka tashi.

Bayan fitarsu kuma har lokacin Dahiru bai fita ba Ade ta dan tabo Yaya. Iya na gani ta hade rai
"Ke ni fa na lura sai wani shishshigewa Haule kike yi ko irin tsohon kishin nan baya dan motsa miki. To idan ma wata gulmar za'ayi muje ayi dani. Mawadda kwanta ina zuwa"

Yaya da Ade duka murmushi suka yi sanin halin Iya. Tana gani kuwa ta hau waka tana yadawa Yaya habaici
"kishiyata idan sararki leke-leke, leka tukunya leka langa wata rana zaki sha ita ce a gadon baya...luba lubayye 'yan mata luba lubayye luba ta girma. Ehe idan mutum so yake ya shiga tsakanina da ahalina kurwarmu kur abadan wa tutur"

Kunya kamar Ade ta nutse a kasa. Duk da Yaya ta dade da sabawa da wannan habaici tun mutuwar auren Sa'ade amma bata jindadi duk ranar da Iya ta yaba mata magana. Musamman ma ga Dahiru a dakin.

Innar Fatihu abin ya kona mata rai ta bi bayansu tana ramawa Yaya. Ade ta dafe kai daga kokarin abin arziki rikici zai kaurewa tsofaffin. Kunya kuma bazata bari ta fadi gaskiya ba duk da ita Yayan ta ma fahimta.

Dakin yayi shiru sai sautin ajiyar zuciyar Mawadda. A hankali Dahiru ya soma takowa wurin gadon wani masifaffen tsoro ya ziyarci zuciyarta. Ita kadai a daki da namiji. Yanzu idan ya rufe kofa fa? Ina su Baba suka tafi? Wace hanya zata bi ta gudu kafin ya cutar da ita? Tunani barkatai ne suke yawo a kwakwalwarta sai dube-dube take yi ko zata ci karo da makamin da za ta kwala masa.

Ganin yadda ta rude ya sashi tsayuwa a inda yake sannan cikin muryar rarrashi ya kirata da sunan da ya sanya mata tun ranar da ya fara zuwa gidansu tadi.

"Mawaddatan wa Rahma"

Kamar an tsikareta a lokacin ta dawo hayyacinta ta soma neman nutsuwa. Ita kadai take ta nanatawa zuciyarta Dahiru ne. Dahirun da kika sani wanda zaku yi aure nan da 'yan watanni. Sai kuma ta girgiza kai, wane auren kina kwance a gadon asibiti anyi miki fy....

Kasa karasa tunanin tayi ta soma kuka. Yana lura da duk wani motsinta. Kukan ne ya sake taba shi.

"Assha, assha banyi zaton zuwana zai saka ki kuka ba. Kiyi hakuri bari na tafi"

Juyawarsa tasa ta jin wani iri a ranta. Shikenan BB ya rabata da masoyinta. Dahiru matashin da 'yan matan Tariwa suke rububi saboda ya maida hankali a karatun boko har turanci yana ji. Ranar da ya fara zuwa gidansu da maganar yana sonta har rawa tayi a daki ita kadai tsabar murna da samun abin da bata yi zato ba. Yanzu shikenan mafarkinta yazo karshe ba ma shi ba wani ma bazai so aurenta ba.

"Nagode jiya ma na ga kazo. Ka gaishe da su Inna. Kuma...kuma...uhmm Allah Ya baka mace tagari"

Girgiza kai yayi yana murmushi ganin yadda take kuka. A da sai yayi da gaske take iya yi masa magana. Wato yanzu a ganinta sunyi bankwana kenan.

"Ke kin fasa aurena ne ko fatan kishiya tagari kike yi tun kafin ayi bikin mu?"

Bata fahimce shi bata ta dan dago kai mayafin ya dan karkace har fuskar da yanzu kullum take lullubewa ta dan bayyana.

"Me kace?"

"Cewa nayi kin fasa aurena ne kike min addu'ar mata tagari?"

"To ai.." sai kuma ta sunkuyar da kanta. Ko ba'a fada ba ya kamata ya san cewa yanzu maganar aure ta tashi. Don ko shi yana so bata tunanin zata taba aure a rayuwarta.

Komai nata yanzu tausayi yake bashi. Minti daya tana magana, sai kuma tayi shiru ta hau tunani ita kadai sai dai a ga yanayin fuskarta na sauyawa ko tana girgiza kai.

"Kinga mu bar wannan magana ga kunun da aka zuba miki har ya huce baki sha ba."

"Na koshi" ta amsa a takaice.

"Kin taba ganin ciwo ya warke da yunwa?"

Bata son tsawaita magana dashi saboda duk da halin da take ciki har yanzu tana son sa. Rabuwarsu shine zai fi mata alkhairi. Ita duniyar ma gabadaya ta fice mata a rai.

"Su Iya ma na fada musu su kyaleni. Gara yunwa da damuwa suyi ajalina ko na huta da wannan abin da nake ji a raina"

Kofin kunun ya mika mata taki karba sai ma kuka da ta soma mai cin rai.

Kamar zai ajiye sai ya juyo yana kallonta

"Mawaddatan wa Rahma!" Ya kirata idanunsa suna kwalla


"Idan kin manta bari na tuna miki. Da wanda ya cakawa kansa wuka, da wanda ya rataye kansa, da kuma mai shirin yiwa kansa horon yunwa da gangan duka idan suka mutu sunansu kafirai. Yanzu ke kin yarda rayuwarki ta kare a haka? Kin rayu cikin talauci, talaucin nan dai ya rabaki da inuwar mahaifanki ya kaiki inda wani bunsuru ya cutar da ke. Talaucin dai shine yasa kike kwance a wannan asibitin. Kofar dakin tana rawa kamar zata fadowa mutane ga taga babu ko kyalle. Sai an sallameki ki dawo gida da alakoron maleriya"

Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba. Dahiru yayi dariya zuciyarsa tana samun nishadi daga fara'ar da ya ga tayi.

Saurin rufe fuskarta tayi yace "ko ke fa da kin takurawa kanki da kuka. Zancen gaskiya nake miki. Ace duk wahalar da kika sha a duniya kin zabi a lahirar ma...."

Da hannu ta dakatar dashi "naji bani kunun zan sha"

Dadi ya kama shi ya mika mata. Juyar da kanta tayi ga mayafi ta rufe kai ta kafa kai bata sauke kofin ba sai da ta shanye. Ashe ba karamar yunwa taji ba. Yana ganin ta shanye yace ta kawo ya kara mata. A kunyace ta mika kofin amma har ranta tana bukatar karin nan.

Yana cikin zuba mata su Iya suka dawo. Ganin Dahiru yana zuba kunu ta rike baki.

"Iko sai Rabbani, Dahiru daga jinya kuma sai ka nemi shanye kunun mara lafiya. Banda abinka ga tuwo sabo ne ma nayi mata yau da shi ka ci. Ita saboda yanayin jiki sai da abu ruwa-ruwa"

Wayyo kunya ba Dahirun ba, ba Mawaddan ba sannan ba iyayensu ba.

Ji yayi kamar ya saki kofin a kasa ya kwasa a guje. Yadda yayu tsamo ya bawa Mawadda tausayi.

Ade ta wayance "ke dai Iya ba kya rabo da zolaya abin harda suruki kuma"

Dahiru yana tsaye da kofi ya kasa karasa zubawa sai juya dan tsohon filas din kunun da kofin yake yi.

Iya ta isa gabansa kafin Innar Fatihu ta karasa. Karbar filas din tayi tana dan yin sama da kasa dashi ta auna yawan kunun

"Ya naji ba nauyi? Da bamu shigo ba sai ka shanye ko?"

Innar Fatihu taja tsaki "wai meye haka ne Ta Rasulu? Kinsa yaro ko motsin kirki ya kasa yi"

Duk sai ya basu tausayi musamman Mawadda. Tayi karfin halin cewa "Iya wallahi ni nasha karamin zaiyi"

"Ki bari dan Manzo" cewar Iya dadi ya kama ta. Ta dan dungure Dahiru "to kuma sai kayi shiru maimakom kayi min bayani? Kai da ita ashe zani ce ta tadda muje mu. Duk taron marasa magana ne"

Ganin yayi murmushi ne yana sosa keya yasa hankalin Ade da Yaya ya kwanta.

Iya ta sake cika kofin taf ta mikawa Mawadda "ungo"

Yamutsa fuska tayi tana satar kallon Dahiru "na koshi"

"Kin ma isa?" Har zata soma fada sai kuma ta hau dariya.

"Au, auho gulmammu, ashe da gangan kike kin cin abinci kina jiran na hanun masoyi. Oh ni Ta Rasulu kun gane min fitsarar yaran zamani. Ashe fitarmu dadi tayi muku."

Kan kace meye wannan Dahiru ya fice daga dakin Mawadda ta tura kanta a cinyar Iyan da ta zauna kusa da ita don kunya. Innar Fatihu duk abinta sai da ta dara. Ade kuwa kunya ta hana. Ita kuma Yaya tana tsoron tayi a watso mata maganar da zata yi mata ciwo.
******


Yana tsaye yana jiran abin hawa sai murmushi yake shi kadai saboda nasarar sanya Mawadda cikin nishadi da yayi. Da ya tuna tijarar da Iya tayi masa kuwa hannu ya dora a ka yana dariyar halin da ta jefa shi gaban Ade da Yaya.

Bai jima ba ya sami bus ya tafi gida. Rumfar Inna ya shiga jin taku ta taso daga kishingidar da tayi

"Ummiyo ina kika je tun dazu ina nemanki?"

"Inna ni ne" ya fada yana daga labulen ya shigo ya zauna sannan ya gaisheta.

Maimakon ta amsa ta bishi da kallon tuhuma "daga ina kake? Ina ka tafi da sanyin safiya ko karyawa baka yi ba?"

"Asibiti na koma kinsan jiya kafin mu taho dinnan jikin nata ba dadi"

Rai a bace ta daga yatsa tana karkada masa alamun gargadi
"saurare ni da kyau Dahiru. Zamuyi magana mai bullewa da Baffanku amma kafin nan tun wuri ka cireta a ranka. Duk garin nan babu mai yarda dansa ya auri yarinyar da irin wannan kaddara ta sameta. To nima baza'ayi a gidana ba."

Duk da dama yayi zaton haka saboda maganar da yaji sunyi da Ade jiya amma baiji dadi ba. Sunkuyar da kansa yayi cikin tausasa harshe ya soma magana
"Inna kiyi hakuri kada kice na fasa aurenta. Kema gashi kin kira abin da kaddara ai ba kai kanta tayi ba tsautsayi ne"

Ta san za'a rina dama indai Dahiru ne sai ta tashi tsaye. Ana masa kallon shiru-shiru mai hakuri da iya zama da mutane amma a zahirin gaskiya mutum ne kaifi daya ga zafin zuciya idan ransa bai so abu ba. Idan tana so tayi nasarar raba shi da auren nadama sai ta bi a sannu.

"Shikenan ka jira mu tattauna dai kafin ka zartar da hukunci. Na fada maka ne domin ka fara dasawa zuciyarka hakuri tun yanzu."

Bai ce mata komai ba ya tashi ya fita. Yana son iyayensa kuma a shirye yake yayi musu biyayya amma fa sai inda karfinsa ya kare akan Mawadda. Abu daya ne yake masa yawo a rai shine yadda muke saurin manta alkhairin mutum da zarar kaddara mara dadi ta same shi mu guje shi. Wannan hali namu yana daga abin da yake cire mana tausayin juna. Mun mayar da kanmu mutanen da indai jifa ya wuce kansu to ya fada kan kowa ma bamu da damuwa.
******

Wani wawan duka ta sauke mata a cinya cike da al'ajabi tace
"Ke ki bari don Manzo!"

Ummiyo tayi saurin toshe bakin Rahane aminiyarta.
"To uwar karadi yi ihu kowa yaji"

Babar Rahane tana jiyo haka ta dawo bakin tagar dakin ta labe. Yo labe da leke a wurinsu ai ba komai bane. Balle kuma taji alamun gagarumin abu ne ya faru tsakanin Ummiyo da Rahanen don da ta shigo irin gaisuwar nan mike tayi mata ta wuce dakinsu Rahanen.

Mamaki sosai a fuskar Rahane baki na rawa tace "yanzu da gaske fyade aka yiwa Mawadda? Wallashi har ta bani tausai."

Babar Rahane ta ja numfashi a tsorace tare da dafe kirji tana kara kara kunne. Nan ta jiyo Ummiyo tana cewa
"Ki bar fadi mana Rahane kada a jiyo mu. Jiya Aden Mawadda har dakin Inna tazo ta roketa a rufe maganar. Da kyar na jira wayewar gari saboda na fada miki. Kuma fa Yayanmu Dahiru ya sani don ta bayansa ma na labe. Yanzu ban sani ba ko zai aureta"

"Allah Yasa kada yace ya fasa gashi kince ma tana asibiti baiwar Allah" cewar Rahane har da 'yar kwallarta saboda tausayin Mawadda.

"Don ba yayanki bane ki ke masa mugun fata? Ni dai gaskiya bana so ya aureta. Me zaiyi da 'yar iska. Rannan naji ance duk wacca aka yiwa irin haka ita ma shikenan ta zama irinsu. Kuma garin nan kinsan kowa gudunta zaiyi azo a tsani Yayanmu Dahiru. Ha'aan"

Babar Rahane tana jin haka ta janyo abin tatar koko daga igiyar shanya a zatonta mayafi ne. Makotansu ta shiga da sauri cikin dan kankanin lokaci ta labartawa matan gidan su hudu har da karin cewa Mawaddan tana asibiti an zubar mata da ciki.

Tuni gida ya dauka mata suka fara fita waje kowacce tana son kaiwa makusanciyarta labari.

Cikin abin da bai wuce awa biyu ba maganar nan tayi yawo fiye da zato. Mata da maza manya da yara da dama sun sani tunda safiya ce. Kusan ko ina zancen ake ta yi gashi a kowacce gaba labarin ya sami karin gishiri ya tashi daga fyade wasu sun kara da ciki wasu ma sun ce haihuwa tayi. Akwai wadanda suka dora da cewa dama tun tana garin ai kallonta kawai suke yi ana cewa tana da nutsuwa su kuwa sun san tana yawace-yawacenta ne kawai. Lokacin da Dahiru ya dawo ana ta binsa da kallo da yake bai kawo za'aji zancen ba ko kadan bai kula ba.

******

Ya fito da shirin tafiya gona saboda rashin samun lokaci tun ranar da Mawadda ta dawo gari bai gama cire kubewar da ya shuka ba wanda kusan duka gonar sun gama yado mai kyau. Idan ya cire Yayansa

1 Comments On GUMIN HALAK
avatar
amina-5-7-3

9 months ago

Reply

Allah ya kara basira

Please Login or Register in order to submit comment