Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duba wannan al'amari babu wanda yafi karfin jarabawa irin wannan. Me zaisa don ta afka musu kowa ya juya musu baya? Wallahi har yau ana fyade kuma mace da danginta sune kadai suke fuskantar kalubale daga abinda bai zama laifinsu ba. Ina laifin wanda yake neman halak da guminsa Baffa? Maimakon a lokacin mu hada kai mu jajirce wurin kwato musu hakkinsu ta yadda gobe wani mai kudin zaiyi shayin yiwa 'yar aiki fyade sai aka juya musu baya. Wannan yana daga cikin dalilan da suke karawa duk wani mutum bata gari karfin gwiwa domin yasan indai yana da kudi idan yayi babu wanda ya isa dashi. Ko ban aureta ba a lokacin yaci ace mun tsayawa juna."

Yana magana Inna ta share hawaye tana kallon Baffa "ni dai na dade abinnan yana ci min rai amma kunya da tsoron yadda zaka dauki zancen yasa na kasa magana"

Shiru Baffa yayi kamar bazaice komai ba sannan ya nisa yace "Allah Yayi maka albarka Dahiru. Karshen mako kazo ka daukemu muje gidan Mal Fatihun"

Mamaki Dahiru yayi sosai yadda iyayensa suka yi saurin saukowa. Ya tsallake wannan saura kuma neman amincewar Mawadda ya sake tado da zancen aurensu.

Abinda bai sani ba shine duka iyayen nasa kowanne shi kadai ya dade da nadamar biyewa son zuciya akan abinda ya sami su Mal Fatihu amma sun kasa yiwa juna zancen. Batun yiwa 'yan aiki fyade wasu ma su dawo da ciki kuwa ko ba a garinsu ba suna ji sosai a makota amma har yanzu an rasa wani mataki da ya kamata a dauka domin dakile cutar da marasa karfi da akeyi.

Bayan la'asar ya sake daukar hanya cike da farinciki ya tafi. Zancen da suka yi da Inna a dakinta ya tuna yayi murmushi. Cewa tayi kada yayi gaggawar sake neman auren Mawadda har sai sunje sun fuskanci wace rayuwa tayi bayan rabuwarsu. Tado da zancen da tayi kawai yasa shi sanin cewa akwai yiwuwar amincewarsu kenan.

A gajiye sosai ya isa gida sai da yayi shirin kwanciya wurin karfe goma ya kira Mawadda.

Tana aikin hada turaren wuta saboda wasu amare biyu da zata fara yiwa gyaran jiki taji wayar. Hannunta ta goge ta dauka da sallama hade da faduwar gaba ganin mai kiran.

Amsawa yayi yana jin wata annashuwa tana ratsa shi.

"Da karfinki ki ka dawo naga alama"

Tayi 'yar dariyar da sautinta ya sake jefa shi cikin wani yanayi mai dadi "Karfi kamar wata 'yar dambe?"

Ajiyar zuciya taji ya saki har tsigar jikinta ta tashi "da gaske nake, ban san ta yaya zan kwatanta miki yadda nake ji game dake ba yanzu. Tunda na hadu dake shekaranjiya na kasa ganewa SO ne, KEWA ko duka biyun ne a tsakaninmu"

"Yayanmu!"

"Na'am"

"Kayi hakuri kada muje nan. Ni da kai yanzu wa ne da kanwarsa." Yadda tayi maganar mai ji zai fahimci akwai ciwo a tattare da ita wanda take kokarin dannewa.

Hakan ya taba zuciyar Dahiru sosai yasan tana kokarin boye damuwarta ne kawai don babu yadda zatayi "haka kika zabar mana? Mu koma wa da kanwa?"

Kai ta gyada kamar yana kallonta.

Yace "to naji amma idan mun tashi mu kara da zama abokan sirrin juna. Ke kanki kin sani abinda yake tsakaninmu mai girma ne. Kinga ina da abubuwa da dama da nake son baki labari Mawadda...Nace miki yau zan zo naji yadda rayuwarki ta kasance kema amma da ki ka ji shiru babu ko cigiya"

"To kayi hakuri"

Yasan akwai aiki a gabansa indai yana son ya dawo kamar da ko ma fi a wurinta yadda zata bada kai bori ya hau. Lallabata zaiyi a hankali ya sake cusa kansa. Ya iya hakurin shekaru takwas ma basu hadu ba bare yanzu.

Tambayarta yayi cikin sigar wasa "Gobe nazo?"

"Uhmm" ta iya cewa kawai. Saboda muryarsa idan yayi magana yanzu jinta take har ranta. Anya zata jurewa wata alaka tsakaninsu idan ba soyayya ba? Ita kanta tana mamakin yadda ya dawo cikin rayuwarta yake neman wargaza duk wani shiri da katanga da ta gina tsakaninta da maza.

"Nagode Kanwarmu Mawadda" ya fada a hankali yana jan kowane harafi.

Haka nan taji tana son yasan tayi ilimi itama yanzu shiyasa tayi masa sallama da turancin da ko lokacin da tayi firamare a garinsu yasan bata iya ba "Sweet dreams Yayanmu Dahiru"

Ai kuwa ba karamin dadi yaji ba da mamaki sai da yayi da gaske ya iya cewa "mafarki na daya ne. Naki. Kuma yanzu kin hana tunda bai kamata wa yayi mafarkin kanwarsa ba. Amma duk da haka bari na kwanta da kyakkyawar addu'a kila nayi sa'ar ganin wadda zata zama matata don aure nake so wallahi"

"La ila ha illallahu" tace tana dariya kasa kasa sannan ta kashe wayar kafin ya sami damar sake magana.

Dariya yayi ya gyara kwanciyarsa "you can't escape easily adorable Mawadda".
******

Cikin bacci yaji waya ya farka. Shadaya da kusan rabi lokacin. Ko bai gaji ba yanayin aikinsa yasa ya koyi baccin wuri. Bai gane nambar ba amma ganin wayar ta katse an sake kiransa shiyasa ya dauka. Yana kara wayar a kunne yaji ance

"Ahirin..."

Takaici ne ya kama shi yaja siririn tsaki. Mutum daya ke kiransa da wannan sunan kuma muryarta yaji. Sai dai bai ga wani dalilin komai kankantarsa ba da zaisa ta kira shi a wannan lokacin.

Cikin zakuwa Qareeba ta sake cewa "Ahirin kana jina? Safwan ne nayi ta nema ya bani number dinka da ka bashi lokacin da kazo wayarsa a kashe sai yanzu na same shi"

"Naji, naji ya akayi?"

"Hmmmm dama magana ce nake so muyi idan da hali gobe sai kazo gida ko ni nazo office dinka. Duk wanda ka zaba is okay with me"

Me kuma take nema ya tambayi kansa. Kamar yaji shi ta sake cewa ya daure yazo. Baya son jan magana da ita kawai yace yaji sai ya taso daga office.
Babu sallama ya ajiye wayar ya juya abinsa ya kwanta.

Zuwa wayewar gari ya ma manta da wayar Qareeba harkokin gabansa kawai yake yi sai tunanin Mawadda da haduwar da zasuyi anjima.
*****

"Kin tabbatar da abinda ki ke fadi kuwa Qareeba?" Cewar Dr Tani cike da doki.

"Sosai Mummy zaki ganshi ma da kanki don yace yana tasowa daga office zai zo" Qareeba ta amsa tana dariya.

Dr Tani ta jinjina kai "Allah Sarki ashe shine rabon naki lokaci ne kawai baiyi ba. Dama ance matar mutum kabarinsa. Sai ki tashi a soma hada masa abinda zaici tunda daga office zai biyo"

Hannu Qareeba tasa ta rufe fuska wai ita kunya ta tashi tayi hanyar kitchen tana kiran mai aikinsu tazo ta tayata aiki.

Dr Tani kuwa zuciyarta fes tana murna da wannan sa'a da Qareeba tayi.

Dahiru na fitowa akan hanyarsa ta komawa gida yana tsaye wurin danja Qareeba tayi ta kiransa. Kallon wayar yayi sannan ya tuna jiya yace zaije. Agogo ya kalla yaga akwai sauran lokaci zai iya lekawa gidan nasu shap-shap ya koma ya shirya yaje wurin Mawadda. Yadda ya santa da naci idan baije ba kiransa zata yi tayi kamar yadda take masa da idan zata bashi aiki Abinda baya so kenan.

A falon Dr Auwal aka jera masa komai na tarar bako don Dr Tani tace dole a karrama shi yadda ya dace.

Qareeba ce a gaba yana biye da ita zuwa falon duk yabi ya takura saboda yadda yaga abin babba ne. Taci kwalliya sosai gashi yau shine har falon maigida.

A dofane ya zauna ya kasa sakin jiki. Sai da ta zuba masa lemo a kofi ta mika masa sannan ta zauna a kujerar kusa dashi. Haka ya rike kofin shi bai sha ba shi kuma bai ajiye ba yana jiran karin bayani.

Kusan minti biyar babu wanda yayi magana. Sai Qareeba ce tayi ta mata tace

"Baka ce komai ba?"

"To me zan ce ni da ki ka kirani"

Kai ta sukunyar tana wasa da yatsunta "kayi hakuri da jinkirin da aka samu na rashin fahimtarka da nayi a wancan lokacin."

Kansa ya shiga duhu ya kasa gane inda ta dosa yace "ban fahimceki ba."

"Ka tuna wata rana da na tambayeka me ka ke kiran masoyiyarka?"

Idan ma anyi haka gaskiya ya manta amma don a sallame shi da wuri yace ya tuna.

Murmushi tayi ta sake matsowa yadda zasu fuskanci juna da kyau.
"A lokacin abinda ka fada dariya ya bani. Kace wai kana kiranta Qulqulatil Qurabati. Sai bayan ka tafi rannan nayi dogon nazari ashe dani kake ban gane ba"

Da sauri Dahiru ya daga hannu "Dakata Anti Qareeba nifa na kasa fahimtarki"

Bayani tayi masa dalla-dalla kuwa. Bayan ta nutsu tayi tunani ta gane daga sunanta ne ya kirkiri wancan suna alamu na cewa yana sonta.

"Nasan a lokacin rashin kudi da wayewa yasa ka boye min soyayyarka. Amma yanzu tunda na fahimta na amince kuma Mummy is happy da hakan" tayi fari da ido tana sunkuyar da kai.

Wannan abu yafi gaban dariya a wurin Dahiru tausayi ma ta bashi. Banda shirme irin nata wane abu ta ga yayi da zai nuna yana sonta ko kuma duk tsabar son auren ne yasa kanta toshewa irin haka.

"Anti Qareeba..."

"Ka dena kirana Anti duk da nasan mu sa'anni ne kada ka damu kusan abinda yake tashe kenan yanzu auren sa'anni"

Gani yayi idan ya barta ta cigaba da wannan tunanin lallai ya cuceta. Gara kawai ya yiwa tufkar hanci tun ba'aje ko ina ba.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰14

*Batul Mamman*💖



Nutsuwa yayi sosai ya fuskanceta hannuwansa a hade kamar mai roko yace "don Allah idan daga ranar da muka fara haduwa zuwa yau nayi misleading dinki...uhmmm idan nayi wani abu da zai nuna miki ina sonki ne kiyi hakuri ba niyata ba kenan. Ina da..."

Katse shi tayi da sauri "kada kayi tunanin nafi karfin zama da kishiya, ko kadan wallahi. Ni bani da matsala kaima shaida ne. Matarka da yaranka duk zan zauna dasu da zuciya daya."

Girgiza kai yayi don ya fuskanci abin nata na gaske ne "Anti Qareeba!"

Idanuwanta ta ware a kansa "ni dai gaskiya bana son Antin nan"

"To Malama Qareeba ki tsaya ki gane me nake cewa. Ni Dahiru bani da mata amma ina da wadda nake so. Tsakanina da mutanen gidan nan ciki kuwa harda ke bai wuce mutuntawa ba albakacin zaman da nayi daku a baya"

Hawaye ne ya soma wanke mata fuska. Ita bata san ya shiga ranta haka ba sai da ta kula nema yake yace baya sonta.
"Dashiru kada kayi min haka...duk tsahon lokacin nan da banyi aure ba ban taba kai kaina ga namiji ba gudun irin haka. Yanzu ma ni na sani kana sona tsoron yadda iyayena zasu dauki maganar kake yi ko?"

Ikon Allah. Da Hausa yake mata magana amma kamar ma tana sane take kin gane me yake nufi.
"Kinga ki kalleni da kyau nine Dahiru mai shara da wankin gidanku na da"

Daidai lokacin Dr Tani ta iso kofar falon. Ta kasa hakuri so take ta ji da kunnenta don ta fara shirin gaske 'yarta tayi miji.

Hankalin Qareeba a tashe ta zamo daga kan kujerar da take kamar zatayi masa durkusu irin na me neman taimako.

"Ni mummuna ce ne?"

Tausayi ta soma bashi ya girgiza kai.

"To ko ina da wata nakasa da ban sani ba? Don Allah ka amince Mummyna ta dena kukan rashin aurena. Wallahi zan zauna da ko mata uku ne ni dai kawai ka amince. DAHIRU...SONKA NAKE YI"

Shiru yayi ya kasa magana yayin da Dr Tani ta toshe bakinta ta bar wurin don kada su ji kukan da take yi.

Sai da yaga ta dan sami nutsuwa ya soma yi mata magana "Anti"

Harara ta galla masa yayi dan murmushi "Malama Qareeba akwai girmamawa tsakaninmu bazan iya kiran sunanki haka nan ba. Kiyi hakuri Allah zai kawo miki naki mijin. Ni ina da wadda zan aura in sha Allah nan da lokaci kankani. Ina kara baki hakuri akan kuskuren da nayi bisa rashin sani har kika yi zaton soyayya ce. Allah Ya bamu alkhairi"

Kofin da ta bashi wanda ko kurba daya bai yiwa lemon ba ya ajiye ya fita tana ji tana gani. A wurin ta kife ta shiga rera kuka. Ta rasa menene aibunta da maza suke gudunta an rasa me tsayawa magana tayi nisan zuwa kunnen iyaye ma.

Yana fita ya shiga motarsa ya furzar da iska tare da nannauyan numfashi. Haka kawai da can banda wulakanci babu abinda yake hadasu da mutan gidan musamman Mummyn tasu. Qareeba kuwa kamar wadda aka kawowa abin debe kewa da sa nishadi. Duk wata sharar shirmenta akansa take saukewa. Shine kuma yau ya zama masoyi don rainin wayo. Fita yayi daga gidan rai a bace yana ayyanawa a ransa yayi zuwan karshe kenan. Gidan Prof Abdulhadi yaje yayi rashin sa'a fitarsa kenan. Sun dan taba hira da Hajiya Mama daga nan ya fita ya tafi gida sai yayi magariba yaje wurin Mawadda.

*****
Kusan minti goma da fitarsa sannan Qareeba ta fita idanu a kumbure. A falo ta hadu da mamanta ta yi saurin sakin fuska.

Dr Tani ta daure kamar bata ji komai ba tace "yaya kuka yi har ya tafi ne?"

Ta hadiyi yawu da kyar "eh Mummy daga zuwansa duk wahalar aikin da muka yi wai yana sauri." Tana magana hawaye na zuba tana gogewa da hannu "haushi naji shine harda kuka"

Idanun Dr Tani suka ciko da kwalla ganin 'yarta tana kokarin boye mata damuwarta. Ashe Qareebanta ta girma.

"Kiyi hakuri kila aiki ya masa yawa ne. Jeki ciki ki gyara fuskarki hawaye yasa kwalliyar duk ta cabe miki"

Tana tafiya Dr Tani ta goge nata hawayen. Wane irin bakin jini ne da Qareeba ace har mai wankinsu na da, wai Dahirun da ta raina shine yake da bakin cewa baya sonta.
*****

Ta dukufa tana murjewa amaryar dake gabanta dilka Ade ta shigo dakin da suke aikin ta sanar da ita Baba yace Dahiru yana jiranta an sauke shi a falon soro.

Sunansa kawai da taji yasa jikinta yin sanyi har ta kasa samun kuzarin yin aikin yadda ta faro.

Amaryar wadda ta kasance kawarta ta Islamiyar da suke zuwa a unguwar tace cikin mamaki "Mawadda dama akwai ranar da zanji ance ana kiranki? Lallai yau akwai labari don sai na fadawa 'yan ajinmu tun wuri ma na sanar dake kada a tsokaneki kice na kai gulma"

Dariyar dole tayi "to uwar son labari dan uwanmu ne"

"Mayar dani yarinyar goye dan uwan ne zai tsaya a wancan falon bai shigo ya gaishe da kowa ba?"

Mawadda ta cigaba da murje mata jikin sai dai gaskiya aikin nasu akwai saura sosai. Ita da kanwarta ne amaren kuma basu zo da wuri ba. Kanwar aka fara gamawa har ta tafi yanzu nata baiyi nisa ba. Hannu tasa ta taya Mawadda ko fita abin baiyi ba ta dauko hijabinta ta saka. Duk yadda Mawadda tayi ta rokon ta zauna taki a cewarta taje ta saurari bakonta ita din ta gida ce gobe sai tazo da wuri tunda na sati zasu yi.

Bayan fitarta nuku-nuku Mawadda ta zauna yi har Baba da kansa ya sake magana yace taje mana. Ita gaskiya tana jin kunya don ta manta rabon da ta fita da sunan zance. Duk wanda yazo nemanta ba fita take yi ba dama Rafi'a ce mai zuwa sallamarsu.

Marwanu da Saifullahi duk basa gida yanzu. Daya yana ABU Zaria daya kuma yana Kazaure informatics da sai ta tura masa su kawai.

Ba wani shiri tayi ba ta dai gyara jikinta ta yafa mayafi ta tafi.

Innar Fatihu ta dubi Baba bayan fitarta "kada yaron nan fa yace zai sake dawowa neman aurenta a kuma komawa gidan jiya"

Iya tace "kuma na kula ita ma kanta tana son shi. Fatihu ko zaka dakatar dashi ne kada a sake fama mata tsohon ciwo a barmu da jinya"

"In sha Allah ni da kaina zanyi masa magana. Yanzu ma don naga bai dace bane daga zuwansa na dakatar dashi da gaggawa batare da sanin manufarsa ba. Ko menene ina tunanin zai sanar da ita a yau sai mu dauki matakin da ya dace"

Tausayinsu ne ya kama Ade don kuwa ta sani sarai kamar yadda Iya ta fada Mawadda har yanzu tana son Dahiru.

Daga bakin kofa yau ma ta zauna a kasa shi yana ciki akan kujera sai dai basu yiwa juna nisa sosai ba.

"Na fa jirgu Kanwarmu har na fara tunanin ko dai saurayi aka shanya ba yayan da yazo ganin kanwarsa ba" Dahiru yace yana mata murmushi.

Itama murmushin ta mayar masa "ai da saurayin ne karshenta sai dai ya gaji ya tafi gida"

Daga hannuwansa yayi "Allah Ya soni da aka yimin tayin zama yayan karfi da yaji na karba"

Wannan karon dariya Mawadda tayi sannan tace yayi hakuri yazo tana tsakar aiki ne. Ya nuna mata babu komai Yaya ta fada masa lokacin da ta kawo masa kayan ci da ke gabansa.

Mawadda ta kula ya sha kusan rabin jug din kunun ayar ta sake fuska "wato wanda na kawo rannan ne baka so shiyasa kaki shan komai"

"Kada ki fassara ni ranar ma kukan da na kula kinyi ne ya janyo. Yanzu kuwa da banci ba ai da na yiwa kaina. Wata awara naci mai dadi duk da bata dameni ba amma wannan gaskiya tayi dadi sosai"

"Kai dai Yayanmu santi kake yi. Baka san ko daga bakin titi idan kana neman gidan nan kace gidan awara za'a kawo ka ba? Tana cikin sana'ar da ta rikemu zuwa yanzu"

Kallonta yayi ita ce dai Mawaddansa amma ta chanja. Sai dai chanjin bai rage komai ba sai kara masa sonta a zuciyarsa.

"Yanzu ma aikin awarar ne ya hanaki fitowa da wuri?"

Gyara zama tayi kafin ta amsa masa "a'a ni sana'ata gyaran jiki. Idan ka tashi aure ka kawo min matarka nayi alkawarin yi mata kyauta"

Dagowa yayi sosai yace "alkawari fa, Allah Ya kaimu ko wace amaryar kice tun yanzu nasan an 'yanta ni daga kudin gyaran jiki."

Dadi kawai take ji ganinsa da magana dashi a haka. Itama tunanin tasa sauyawar take yi. Ya zama dan gayu sosai banda kamshin turarensa da ya cika falon shigarsa ma kawai ta isa ta sanya mace ta soshi.

Tayi nisa a tunani taji ya kada mata yatsunsa har sun bada sauti tayi saurin dauke kanta daga gareshi.

Shi kuwa yace "irin wannan kallon sai kisa nayi tunanin promotion na samu, har na fara murna."

Kunya taji ta jawo mayafinta ta sake rufe fuska. Shi kuwa sai dariya yace "Allah kuwa haka kawai aje a sa min rai ina dalili. Yanzu dai fara bani labarin da nake kwadayin ji"

Kasa dago kai tayi maganarsa tasa mata jin nauyinsa "labarina kayan kuka ne da bakinciki kawai a ciki"

"Assha Kanwarmu a rinka godewa Allah dubi yadda rayuwa ta koma miki fa. Ni dai ina son ji. Idan anzo wurin kuka muyi tare idan na bakinciki ne mu rarrashi juna. So nake wannan gap din shekaru na tsakaninmu mu cike shi ta hanyar sanar da juna komai. Kada ki manta na roki alfarmar zama dan uwa abokin sirrinki ne"

Ji tayi bazata iya yi masa musu ba ta soma bashi labarin tun daga shigarsu kotu na farko har zuwa yanzu. Tayi kuka sosai kafin ta gama. Dahiru kuma jijiyoyin kansa suka dago saboda bacin rai.

"Kiyi hakuri Mawadda ban so haka ta faru dake bama tare ba" yace murya na rawa saboda yadda yake ji.

Dago kanta tayi wanda ta kifa akan cinyarta ta turo baki "ni ban yarda ba yanzu kace idan abin kuka yazo tare zamuyi"

Yasan wasa take so ta sako domin sassauta musu yanayin da suka shiga sai ya biye mata.
"Kada kiso jin kukana don muryata sai ta cika gidan nan ga rashin dadin sauraro"

"Ni kam tana min dadi" tace ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Kallon da yayi mata ne yasa ta rufe baki sai kuma tace saura nashi labarin.

Tun farkon zuwansa Kano ya soma fada mata har yau da yaje gidansu Qareeba.

Sai ga Mawadda tana dariya kamar ba ita ta gama kuka ba.
"Yanzu Yayanmu mace tace tana sonka shine kake ja mata aji. Huhmm gaskiya ka koma kace ka amince kawai don ni tayi min"

Dahiru yasha kunu da gaske baya son zancen Qareeba.
"Ita ce nace miki tana kirana Ahirin ko Dashiru da farkon labarin ko baki gane ba?"

Ta kuma dariya "Ahirin na Qareeba yaushe zamu sha biki?"

Kula yayi zolayarsa kawai take yi shiyasa ya dena biye mata. Sun cigaba da tattauna abubuwa da dama yace "amma likitan da taci amanarku a kotu baku sake binciken dalilinta ba?"

"Barta ta yiwa kanta ne. Kasan ranar Baba ya fadi muka taho asibiti shiyasa komai ya dakata"

Dahiru yace "naji dadi kinyi karatu yanzu Kanwarmu. Kinsan babban abinda ake cutarmu dashi bayan talauci shine rashin ilimi. Akwai abubuwa da dama da yakamata ace an kula dasu wancan lokacin. Kamar sanar da lauyan binciken farko na asibitin Bebeji, kawo wadancan 'yan sandan shaida da sauransu. Duk da haka kada ki damu hakkin da suka dauka bazai barsu ba"

Hawaye ne ya zubo mata tace "Yayanmu bazan taba yafe musu ba. Akwai ranar da abin ya ciyoni fa na kwana dashi a raina kawai sai gani a Kaduna"

Idanu ya zaro "me???"

Da sauri ta shiga girgiza hannunta tana kallon kofa "shhhhh babu wanda ya taba sani"

Yace "to wallahi fada min yadda abin ya faru ko na tona"

Wata harara ta doka masa wadda ta shiga ransa don yadda ta kada idanun ma burgeshi yayi "naji amma wallahi amanatul amana..."

"To ya isa kada ki karasa bazan fada ba bare ta cini." Ya yamutsa fuska "kai Kanwarmu ashe baki girma ba har yanzu wai amanatul amana"

"Rigakafi nake yi don kada ka janyo min duka"

Shekara biyu kenan lokacin tana ganiyar mafarkin BB tun da barayi suka shiga makotansu akace sun kusa yiwa matar gidan fyade. Shikenan abu ya dawo mata sabo tana kwanciya take farkawa a firgice. Ranar da abin ya isheta zuciya ta raya mata wai taje Kaduna ta hadasu da 'yan sanda a koma kotu. Karyar makaranta tayi sai gata a tasha kamar wasa. Taje Kaduna ta fadi sunan unguwar amma ta kasa gane ko ina. Tana cikin yawon tambaya kamar wata mahaukaciya Baba ya kirata yace ta taho masa da maganinsa na hawan jini a lamco pharmacy. Sai lokacin ta dawo hayyacinta a gaggauce ta koma tasha. Ranar sai bayan magariba ta dawo gida ta zuga musu karyar dalilin rashin dawowa da wuri. Babu wanda ya tuhumeta tunda ansan ba yawo take ba.

Dahiru na jin labarin ya sake tausaya mata da sabon kuduri a ransa na tunanin dole ma ya aureta ya nuna mata soyayyar da zata gusar mata da tunanin wannan azzalumin mutumin.
******

BB ne ya fito daga dakin Alh Sule yana ta gunaguni don me zai ce masa sai yayi aski. Kunyar yanayin shigarsa yasa sun kasa tura shi ya gaishe da 'yan uwa ma.

Yana saukowa Yasmin ta fito daga kitchen da food flask ta yiwa yaranta girki. Haj Mara tace masu aikinta bazasu yi girki da ita ba. A nata bangaren hakan yafi mata don yadda ta kula ta sawa yaran nan ido ba abin mamaki bane ta nemi hallaka su. Anyi sa'a damuwarta gabadaya tana ga BB yanzu.

Yasmin ya hango ya taho inda take kusa da dinning table ko kula Haj Mara baiyi ba da take tambayarsa yaya sukayi da Alhaji.

"Matar Alhaji wai yaya kanen nawa suke kiranki ne ba dadi ina cewa matar Alhaji dinnan."

Yasmin tayi murmushi ganin Haj Mara ta bata rai "Mama suke kirana"

"To ai nima kawai sai nabi ayari. Ni dasu ai same to same ne...so ba wani abu kingane ai" yace yana yin gaba.

Ita kuwa kai ta gyada kawai. Bayan ya wuce Haj Mara ta tashi zata bi bayansa taji Yasmin tace "ta inda aka hau ta nan ake sauka"

Dawowa tayi ta tsaya a gabanta "me ki ke nufi"

"Nayi miki magana ne?"

Rai a bace dama neman wurin huce takaici take ta cakumi wuyan Yasmin din.
"Ki bar ganin na kyaleki idan na dawo gareki bazaki ji dadi ba. Kina tunanin kin shigo min gida ne don ki kwace komai nawa?"

Bude baki tayi zata rama taji Alh Sule ya fito sai ta soma kuka tana bawa Haj Mara hakuri. Harda cewa idan saboda zuwansu ne zasu koma Abuja nan ba da dadewa ba.

Alh Sule yana saukowa ya kamata da fada sosai da ja mata kunne babu ruwanta da iyalinsa.

Mamaki ne ya hanata magana kawai ta bi bayan BB tana hawayen zuci.
*****

Kwana biyu da zuwan Dahiru tun ranar Qareeba ta dena walwala a gidan. Dr Tani ta sami maigidanta tace lokaci yayi da zasu nema mata lafiya a ajiye boko a gefe.

"Neman lafiya wane iri?" Yace yana kallonta.

"Daddy na tabbatar Qareeba aljanu gareta irin

1 Comments On GUMIN HALAK
avatar
amina-5-7-3

9 months ago

Reply

Allah ya kara basira

Please Login or Register in order to submit comment