Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutum daya ta zauna a takure.

Kujerar gefenta Dahiru ya zauna ya mika hannu ya riko hannunta daya. Jikinta taji yayi sanyi fiye da yadda taji dazu da suka hadu ko don lokacin tana tattare da fargaba ne.

"Mawaddatan wa Rahma yau gaki a gidan Dahiru a matsayin matarsa. Babban burina ya cika ina fata zamu zauna lafiya mu rike juna tsakani da Allah"

Kanta a kasa tace "In sha Allah."

Irin kararrawar nan mai sallama ce ta doka sallama a falon. Daga wajen kofar hawa saman Dahiru ya saka saboda kada a buga basu ji ba idan kofar saman a rufe take. Mike yayi yace mata yana zuwa. Fita ta ga yayi bai dade ba ya dawo rike da kwandon abinci.

"Marwanu ne ya kawo"

Hannunsa na dama ta kalla har yanzu da kumburi ga dukkan alamu yana masa ciwo ta tashi ta karbi kwandon ta ajiye a kan dinning table.

Har lokacin yana tsaye "bari na nemo plates to tunda kin karasa min wannan ladan"

"A'a barshi zan duba" tace tana dan waige. Plates ne masu kyau da cokula, kofuna da jugs a cikin kitchen cabinet din da yake manne a bango daga bayan table din komai a jere yadda ya kamata. Budewa tayi ta dauko plates biyu, da sauran kayan bukata ta ajiye.

Gani tayi ya ja kujera daya ya zauna tace "in zuba maka?"

Ya tsareta da ido ganin jikinta ya soma rawa amma tana ta kokarin boye masa "ki zuba mana dai"

"Na'am?" Tace a sanyaye tana mai fargabar kada ta fara wannan abin don tunda ya tsayaba wurin table din taji zuciyarta ta tsinke.

"Kinji me nace ko yau ma kurumtar ce ta tashi?"

Cije lebenta tayi tana karfafawa kanta gwiwar kada ta tsorata yaji babu dadi shi kuma ya kawar da kansa yana mai tuna maganar da Inna tayi masa jiya bayan daurin aure. Ita ma kuma Yaya ce ta fara yi mata bayanin yanayin da Mawadda kan shiga idan ta kebe da namiji na tsoro da firgici.

_"Dahiru kai ba bako bane game da sanin wacece Mawadda. 'Yar shawara zan baka ka sani cewa soyayya daban sha'awa daban. Duk son da take yi maka kasan kaddarar da ta afka mata a baya har yanzu tana iya tasiri a kanta. Idan kana son samun nutsuwa da kwanciyar hankali a gidanka ka fara neman kusanci da yarda daga matarka kafin ka bijiro mata da wani abu daban. Ina fata ka fahimceni. Idan kaje mata lokaci guda tana iya alakanta hakan da wannan lamari na baya ku zo kuna samun sabani"_

Wannan sune kalaman Inna gareshi kafin ya baro Tariwa. Ya gamsu da su dari bisa dari ya kuma san cewa hakan shine zai sanya shakuwa a tsakaninsu.

A plate daya ta zuba musu abincin dayan kuma ta zuba soyayyan naman kaza.

Kallonta yayi ya sake kallon abincin "kin tabbata zai ishemu? Ina jin yunwa sosai"

Bata ce komai ba ta kara musu. Tana gamawa ya sake hada komai a cikin kwandon "bari na kaiwa su Attahir"

Jin haka tayi murmushi saboda tayi wannan tunanin sai dai kuma tsoron kada ya zama kaiwar akwai takura.

Inda ya barta ya dawo ya sameta. Kujera yaja ya zauna sannan yace ta zauna ganin ta tana tsaye har lokacin.

"Matarmu kinsan me nake so dake?"

Ta girgiza kai a hankali tana jin alamun hawaye mara dalili.

"Don Allahi ki cire komai a ranki ki saki jikinki. Ban aureki domin na takura ki ba duk da nasan cewa da wahala idan kowacce amarya ba haka take yi ba. Amma kinga mu special case ne."

Yadda yake daga gira yasa ta murmushi tace "kamar yaya?"

"Kinga dai ke da rana tsaka kika tare, gashi ango ya shigo ko kullin kazar al'ada babu. Sannan kin shigo gidanki babu irin kwalliyar nan ko inji kamshiki tun daga kasa"

Kallon kayanta tayi mayafin duk ya yamutse shi kuma ya nuna mata fuskarta a jikin wayarsa ta kode idanu zuru-zuru. Ita kanta ta bawa kanta dariya wai amarya kenan.

Turbune fuska tayi cikin shagwaba "ai kasan me ya janyo hakan"

"Na sani shiyasa nace miki komai namu daban ne. Saboda haka nake so daga yau har ranar da tayi miki ki dauke ni a matsayin yayanki, kaninki ko abokinki. Duk wanda kike so ki zaba. Ni kuma zan jira ki zuwa lokacin da kanki zaki dawo dani miji."

Sunkuyar da kai tayi ya ga hawaye ya diga akan tafin hannunta.

"Kina so muyi fada ne?"

"A'a"

"Na soke kuka a gidan nan daga yau. Idan kika kuskura na kamaki kina kuka zaki sha mamakin abinda zanyi"

Goge hawayen tayi ya taso ya dagota tsaye sannan ya rabata da jikinsa ya daga waya "hoton tarihi zanyi mana"

Hannu biyu tasa ta rufe fuskarta "naki wayon wallahi bazanyi kyau ba"

"Zakiyi mana" yace yana ta daukarsu tana kaucewa har ya sami wanda duka su biyun suke dariya.

Zama suka yi cin abincin ya dauki cokali da hannun hagu yana satar kallonta "ni gashi hannun daman yana ciwo, hagun kuma ban wani iya amfani dashi sosai ba"

Sam bata kawo me yake son yi ba tace "daurewa zakayi Yayanmu nasan kana jin yunwa"

Marairaicewa yayi "sosai ma amma kinsan Annabi SAW yayi hani da cin abinci da hannun hagu"

Ajiye cokalin da ta rike tayi ta dago kai "lalura ta kori komai Yayanmu"

"Haka ne amma kinsan lalura shine idan babu yadda zakayi gabadaya. Ni kuma a misali kinga ina tare dake"

Dariya ta shiga yi ta gano me yake nufi "daga zuwana gidan nan ko awa daya banyi ba zaka bani aiki?"

"Wane ni? Wai dama ina tunanin ko a matsayin yayata ki dauki kanki sai ki daure ki bani. Kinsan idan nace kanwata kanne akwai tsiwa kila ki rinka bani ba yadda nake so ba. Amma yayye mata akwai kirki"

Da fargaba Mawadda ta shigo gidan amma yanzu Dahiru yasa ta soma sakewa batare da ta ankara ba.

Roko da magiya harda cewa zai fasa cin abincin yayi a dole ta amince zata bashi. Lomar farko sai da ta rufe ido saura kiris ta tura masa a hanci ya riko hannun. A haka dai aka ci abincin sai da ya koshi ya tashi sannan ta iya ci don ko loma daya ta kasa yi a gabansa.

******

Motsinsa take ta ji a kitchen da ya shiga bayan ya gama cin abincin. Bai fito ba har sai da ta gama sai gashi yana wani sunkuyar da kai.

"Uhmm ruwan zafi ne babu na wanka amma na kunna miki heater. Ni kuma sai na dora a kitchen saboda kada na makara sallah"

"To" ta amsa masa tana dukar da kai.

Sai da yayi murmushi sannan yace "baki fahimceni ba, ruwan yayi zafi amma kinsan saboda hannuna bazan iya saukewa na kai toilet ba"

Ji tayi kamar ta shige kasa saboda kunya maganar take bata. Dahiru kuma yasan idan yana mata haka bazai bata damar tsawaita tunani akan abubuwan da suka faru ba balle ta shiga damuwa.

Ya sake kallonta yana shagwabe fuska "in dauko bokitin ki juye min?"

Kafin ya motsa ta tafi hanyar dakunan. Na farkon ta shiga ta ga babu toilet ciki amma tasan ta ga wani a falo. Sai ta bude dayan dakin. Yana da girma yayi matukar kyau da kayan da aka jera mata. Kamar yadda ta zata akwai bandaki a ciki ta shiga ta dauko bokitin a ranta tana ta tunanin wai haka ake yiwa amare ko kuwa dai ita ce daban. Ita fa duk labaran da take ji ranar da aka kai amarya tamkar sarauniya take komawa don mulki. To ita me yasa Dahiru yake yi mata haka? Babu amsa tunda bazata iya tambayarsa ba.

Ruwan ta juye ta kai masa ta ajiye yace mata za ta iya jira na heatar bandakin yayi zafi saboda akwai wuta. Kuma wai yana gama fada sai ya fara sosa kai.

"Akwai wani abin ne naga kin tsaya ni kuma kunyarki nake ji bazan iya cire kaya na shiga..."

Rasa ma me zata ce masa tayi tsabar mamaki. Saboda Allah me tayi ko tace da zaisa ya fadi wannan magana har wani sunne kai yake yi. Kuma shi ya tsayar da ita da bayanin ta jira ruwan zafi. Kwafa tayi ta fita tana auno me zata yi masa ta rama.

Sai da ya ga fitarta ya kwashe da dariyar yadda ta kwalalo idanu da yace yana jin kunyarta. Ko babu komai tunda suka shigo gidan bai yi mata wani abu da zai bata tsoro ba sai ma tsokanarta da yake yi.
******

Tamkar Dr Tani ta zuba ruwa a kasa ta sha lokacin da Dr Auwal ya gama waya da DPO din station din da suka kai karar BB yace sunyi magana da abokan aikinsu yanzu haka BB yana Bompai station.

Babu bata lokaci ta dannawa Haj Mara call tana jin ina ma za ta iya ganin yanayin da zata shiga idan taji wannan labari.

Haj Mara tana tare da wani Agent wanda ta bawa passport dinta da na BB akan zaiyi kokarin nemo musu visa China. Duk tsiya tasan akwai kudi a hannun Babawo ga dukiyarta da ya kwashe. Lallaba shi zata yi su hada komai nasu su bar kasar. Da wane idon za ta kalli 'yan uwanta idan ta koma gida. Sannan abin takaici yaranta mata wai jiya suka taru suka zo yi mata nasiha akan ta bawa Alh Sule hakuri akan laifukan da tayi masa kuma ta fadi ina BB yake a dawo dashi. Kaca-kaca tayi musu dukkansu tace basa kaunarta.

Yau dai gashi ta bada miliyan uku cikin kudin gidan Alh Sule da ta sayar wai kudin visa da ticket.

Da murmushi ta dauki wayar Dr Tani "yau kuma an tuna dani ne ko batan kai kika yi?"

"Haj Marakisiyya kenan gaisheki na bugu yi" tace cikin gatse.

Ta san da biyu ta ce hakan ta tabe baki "Ko ma dai meye sai a dena bibiyata haka. Ni da dana shirin bar muku kasar muke yi sai ku karata ke da 'yarki. Don Allah kafin mu dawo ki aurawa Qareeba mijin kece raini"

"Adana damuwarki akan annobar danki ba Qareeba ba. Na bugu ne albarkacin amintar mu ta baya in fara fada miki BB yana hannun 'yan sanda an kama shi ya sace amarya Mawadda Fatihu ina fata baki manta ta ba."

Cikin Haj Mara ya bada wani sauti ta soma cewa karya ne barazana ce kawai Dr Tani ta bugo tayi mata. Har da karin cewa Babawo a gida ta baro shi yana bacci saboda kawai ta tabbatar.

Dr Tani dariya tayi sosai " su Mara ashe kema ki kan taba kazzibu, kodayake na tuna kin kware a wannan fannin. Mu dai munyi matukar sa'a case din za'a mika shi ga wata Alkali da ta tsani masu fyade sosai bata musu sassauci. Sai ku fara shiri irin naku na masu kudi"

Sakato Haj Mara tayi da waya a hannu kafin ta kira Alh Sule ta soma kuka ta fada masa.

"Allah Yasa sanadin shiriyarsa ne" ya bata amsa.

"Zaman gidan yarin?"

"Kinga ki rufawa kanki asiri ki bari a hukunta shi kafin lokaci ya kure. Ke bakya tsoron idan ya laluba ya rasa wadda zai saukewa rashin mutumcinsa kan wa zai dawo?"

A tsorace tace "kan wa zai dawo?"

"Nima ban sani ba" ya bata amsa a dakile sannan ya kira Dr Auwal.

Ya sanar dashi iya abinda suka ji yayi masa godiya da alkawarin a ranar zai taho Kanon. Haj Mara ma gida taje ta shirya ta kira dreba yace Alhaji yace kada ya sake janta a mota. Ta kira ta gama masifarta dole ta hakura don yaki amincewa. Wani yaro ta kira dan 'yar uwarta da kyar ya amince zai tukata zuwa Kano ta biya shi.

******

Daga masallaci bayan su Dahiru sunyi sallar la'asar Attahir ya kula da yadda yake yarfe hannu.

"Ka sake fama hannun nan ko?"

Kallon babban yatsansa yayi babu alamun sacewa ga ciwo.

"Ina jin bai gyaru bane"

"Kana sakaci dashi dai. Ko muje a sake duba maka?"

Ba don yaso ba Attahir ya matsa masa sai an sake dubawa kada ciwon ya koma wani abin daban.

"Bari na fadawa Mawadda babu waya a hannunta"

Yayi dariya "Nima ba tafiya zanyi ba banje na fadawa amaryata ba. Kasan mu ne da amarci, mai hannu daya sai dai jinya"
******

Mawadda bata jin ta taba yin wanka taji dadin jikinta kamar yau. Ta jima tana sake ruwa sai da taji mai zafin ya fara karewa ta hakura ta fito.

Ta gama shafa mai da feshe feshen turare tayi kwalliya da kayan da aka jere akan madubin ta laluba dakunan kaf babu akwatunan kayanta sai na Dahiru. Salati ta shiga yi ga dukkan alamu bayan dauketa da akayi jiya kayanta da aka ce sai za'a kaita zasu tafi dasu an mayar gida.

Ta kalli wadanda ta cire ita kanta kyamarsu take yi duk wahalar nan dasu tayi harda zama a kasan bandakin gidan da aka kaita jiya. Ga lokacin la'asar na neman wucewa har hudu rabi tayi. Da kunya ta tambayi Nawal kuma babu wayar kiran gida.

Bata da wani zabi dole taje gaban akwatunan Dahiru ta shiga daga kaya tana kallon kofa kada ya shigo sannan kayan kansu kunyarsu take ji. Wata shirt ta samu yellow da rubutun baki a tsakiya tayi sauri ta zura tana kamshinsa. Ji tayi kamar shine da kansa a jikinta tayi murmushi sannan ta cigaba da bincike. Wani wando ta samu ash kamar na sanyi a gaggauce ta saka saboda ta ji kamar motsin kofa.

A bayan kofar dakin ta labe gabanta sai faduwa yake. Yana daga labulen ya ga akwatunansa a bude duka bayan kuma ko wanda ya dauki kayan da yasa yasan ya rufe shi.

Shiga cikin dakin yayi bai ganta ba kuma kofar toilet bata rufe sosai ba yasan bata ciki. Ta mudubi ya hangota tsaye sanye da kayansa da suka yi mata burum-burum abin dariya amma kuma tayi masa kyau. Shagala yayi da kallonta har suka hada ido ta mudubin.

Ya shafa kansa da hannu daya sannan ya bita bayan kofar ya matseta babu wurin fita. Mutsu-mutsu ta soma yi tana son barin wurin saboda irin tsayuwar da suka yi motsi kadan zai kara ta fada kirjinsa.

Dukawa yayi daidai kunnenta har tana jin sautin numfashinsa tayi mutuwar tsaye yace "shhhhh kada su kama mu"

"Su wa?" Ta fada a tsorace

"Ke da na gani a bakin kofa ai ke zan tambaya"

Takaici ne ya kamata kamar tayi kuka ta tura kofar da kafarta ta kuwa koma ta kulle da kanta.

"Ya zaki tona mana asiri" yace yana waigawa kamar me neman wani abu.

"Yayanmu ni fa saboda kai na buya."

"Au, tuba nake Matarmu koma ban ganki ba" ya sake jawo kofar yadda ya ganta tana tsaye tana cika tana batsewa jin ya fara cewa "Mawadda, kina ina?"

Turo kofar ta sake yi harda guntun hawayenta ta soma shagwabar da bata san daga ina ta zo ba tana cije lebe "ni wallahi ba haka ake yi ba"

Juya fuska yayi kamar wanda ya shiga tashin hankali "ba haka ake me ba?"

Ta turo baki tana harararsa "bayan ba haka ake yiwa amare ba. Ni sai wasu abubuwa kake yi min kamar ba amarya ba"

"To Mawadda fada min yaya ake yiwa amaren nima nayi miki kinji" ya kashe mata ido.

Kunya taji ta dauko mayafinta ta yafa "ni sallah zanyi"

"Babu damuwa idan na dawo sai ki fada min yadda ake yi."

"Fita za ka sake yi?" A tsorace tayi maganar ya dago mata hannunsa mai targaden da ya gagara warkewa.

"Gyara na uku zani kuma wallahi akwai zafi. Amma bazanyi kuka ba kada Attahir ya baki labari. Daga can zamu biya mu taho miki da kayanki kada ki buda min nawa"

Ya kare da tsokana saboda yadda ya ga tana kallon hannun da tausayawa.

Hararsa ta fara yi sai kuma tayi masa addua ya fita.

Har akayi magrib basu dawo ba ta gama leken ko ina a gidan ta rasa abinyi ga wuta ba'a jona tv ba. Amarya da take tarewa da jamaa ko da daddare yadda lokacin bazai dameta ba ita ta shiga gidanta da rana tsaka gagal. Allah Ya isa ta makawa BB tana jiran ranar shiga kotu.
*****

Gyaran yau yafi na kullum ba karamar wuya Dahiru ya sha ba mutumin yayi ta masa fadan sakaci. Kasa magana yayi a mota da suka je daukan kayan Mawadda wanda har su Saifullahi sun gama loda su a tasi ko fita daga motar bai iya yi ba suka dawo dasu tasu.

Da yake tun a hanyar zuwa wurin gyaran Attahir yace masa yakamata su tsaya siyan nama kada su jewa amarensu haka shiyasa a hanyarsu ta dawowa yace su tsaya duk da Attahir din yaso su hakura.

Ba su suka koma gida ba sai takwas da rabi har anyi isha. Akwatunan Mawadda har bakin kofa Attahir ya hau masa da biyu sauran Dahiru yace sai da safe.

Tana jiyo su suka yi sallama ta tashi daga kwanciyar da tayi akan doguwar kujera ta zauna tana gyara mayafi.

Yana shigowa ta ga hannun nasa an daure da farin kyalle. Sannu ta rinka yi masa akwatunan ma ita ta ja kayanta daki.

A zaune ta dawo ta same shi yayi shiru azabar hannu ta ishe shi.

"Yayanmu ko zaka yi wanka sai ka kwanta"

Ledar naman ya mika mata yana magana da kyar saboda wani irin ciwon kai da zazzabi da suka rufar masa "bani ruwa na siyo pain reliever idan nasha sai nayi wankan"

Da sauri taje ta dauko ruwa da aka jere mata su da lemuka a kasan kitchen kafin ta samar musu wurin zama.

Yana sha ya shiga daki bai dade ba ya kirata.

"Yanzu dai nine kanin kece yayar"

"Me aka yi?"

Ya nuna kayansa "riga kawai zaki cire min "

Tace "kawai ne ma"

"Ki tausaya min bazan iya da hannun nan ba ina tsoron famawa"

Wannan daren amarcin nata dai bazata taba manta dashi ba ta ayyana a ranta. A hankali tace
"Ba ka jin kunyata to?"

Ya langabe kai "ji kai, shiyasa nace kizo a yayata. kawai don kada na fama a sake gyaran ne. Yau fa na kusa kuka don ciwo"

Runtse ido tayi ta matso kusa dashi tana cewa zata tambayi Attahir kila yayi kukan.

Kasan rigar ta kama zata fara dagawa yace "wash kiyi min a hankali"

"A hankalin fa nake yi"

"Ni dai ki bude idonki sai ni na rufe nawa. Allah idan kika fama min kuka zanyi"

Bude ido tayi suka sauka cikin nasa suka yi dariya tare. Haka akayi ya rufe nasa idon "kuma saura ki kalleni"

Mawadda ta cije leben da ya kurawa ido ta soma mitar shi da ake taimakawa shine da sharudda "haka ma zaka ce, me zan kalla ma"

Sai da ya bari ta cire masa rigar tana ta kawar da kai daga shi sai vest da dogon wando sannan yace "ki ka ce babu abin kalla a jikina ko"

"To ai kai din ne"

Gabanta ta ga yana kara matsowa ta fara ja da baya yana biye da ita har bakin gado saura kadan ta fada.

"Ko zaki karasa ladanki a matsayin Yayata tunda babu abin ganin"

A tsorace take jiki har yana rawa tace "rufa min asiri akwai abin kallo a jikinka"

Saurin matsawa baya yayi harda rufe fuska da hannu "wayyo Matarmu kinsa ni jin kunya. Nifa nufina ko zaki iya tara min ruwan wankan"

Kifta idanu ta shiga yi ba kakkautawa sannan ta yi hanyar toilet din da sauri "kaine baka fada yadda zan gane ba"

"Ah....da me kike zato ina nufi? Huhhhhhh ba dai...ba dai...." ya sanya hannunsa ya wani kare jiki kamar an bude kwaila tana wanka.

"Na shiga uku Yayanmu!" Tace tamkar ta fasa ihu "Me yasa kake min haka ne? Ni ba haka nake nufi ba"

Abin da ta saba wato cizon lebe idan tana tunani ta soma yayi murmushi "yanzu ma banyi miki irin yadda ake yiwa amare ba kenan"

Ta gyada kai bakin nan tana juya shi ita kadai tasan me take cewa.

Bata san yadda aka yi ba sai ganinsa tayi a gabanta hannunsa mai lafiya ya zagaye ta bayanta ya matso da ita daf da jikinsa.

"Kinga farkon abinda ake yiwa amare idan sun tare"

Bata ankara ba taji ya hade bakinsu wuri daya dukkansu bugun zuciyoyinsu ya karu a lokaci guda.

******

"Mummy yanzu yau ta tare matar tasa?" Qareeba ta tambayi Dr Tani.

"Allah Ya takaita mata wahala daga shegen yaron nan an samu an ganta da wuri. Har gidan nasa zamu je dake don ina so in roketa ta yafe min itama"

Qareeba ta sa hannu ta share hawaye "yanzu ni Mummy a ta biyu zanje gidan kenan? Ina ta burin nima kamar ke na zauna ni kadai da miji"

Wani wawan duka Dr Tani ta kai mata a baya ta manta bata gama warkewa ba "Dahirun zaki aura don baki da hankali?"

Ta chuno baki "to ba son sa nake ba"

Takaici ya kama Dr Tani tace "yanzu ke Qareeba bayan duk wahalar nan ko warkewa baki gama ba idan aka ce miki ga namiji sai kije koda da aure yazo?"

Ta gyara kwanciya "me zai hana?"

Jinjina kai Dr Tani tayi "anya kan nan naki kalau kuwa?"

Cikin yanayin ko in kula tace "ina laifina don ina son raya sunnah Mummy? Ba don kin wulakanta dan gidan Antin gadon kaya ba tun ina secondary da yake sona kila da yanzu ina da 'ya kamar shekara shabiyu ai"

Tagumi Dr Tani tayi tana kallonta kawai babu amsar bayarwa.
[31/01 9:36 am] Batuul Mamman: *GUMIN HALAK...*💰22

*Batul Mamman*💖



Har Dahiru ya saketa ya shige toilet yin wanka Mawadda tana tsaye ya barta da kaduwa. A hankali ta dora hannu akan bakinta daga bayanta kawai taji muryar Dahiru.

Kansa ya leko ta kofar da ya dan bude "na dawo ne kina jirana?"

Da sauri ta fice daga dakin kamar zata fadi.

Shima nasa bakin ya tsaya kallo a madubin toilet yana jin kamar ya koma gareta.

"Wai ba da zazzabi ka dawo bane" ya tambayi kansa sai kuma yayi murmushi "Dama na jin baki ne ga dukkan alamu"

Wankansa yayi ya shirya cikin kayan bacci. Falo ya fito Mawadda ko kallonsa bata yi ba ta shige dakin ta rufe kofa. Dariya ta bashi ya zauna yana jona wayoyin tv.

Itama wanka tayi har yanzu tana fama da kunya. Da ta shirya daki ya kaure da kamshin turarukan su ta nemi zani ta daura akan rigar baccinta da hijab ta sami wuri ta zauna.

Shirun da yaji ne ya biyo baya ya sameta a zaune. Zaro idanu ta fara tana ganinsa.

"Kina da mara lafiya kin dawo daki ko abinci baki bashi ba"

Mikewa tayi ta sha kunu "muje amma a yayarka"

Tana rufe baki ya matso ya rungumeta. Dama tunda ya shigo kamshin turarenta ya hargitsa masa lissafi.

Ture shi tayi "yayarka fa nace"

Ya sake riketa yana dariya "kanne ne ba'a hugging fa, amma yayye ana ganinsu ake makale musu musamman idan suna kula da kannensu"

Ta fuskanci jindadin tsokanarta yake ta sake ture shi zata gudu.

"Wash...wash hannuna"

Dawowa tayi da sauri "mu gani."

Runtse ido yayi ta yi tana masa sannu. Naman da ya kawo da juice ta zuba yanzu ma a baki ta bashi yana yi yana makale hannu. Wani lokacin sai taji kamar ba na gaske bane sai kuma ta tuna duk saboda ita yake ta fama hannun sai ta hakura.

Sun gama komai anzo kwanciya suka tsaya a gaban gadon. Ta kalle shi ta kalli gadon.

"Tare zamu kwanta ne?"

"Nayi zaton har yanzu yayata ce. Babu matsala ana haka dama mace da kani gado daya"

"Inji wa? Ni dai gaskiya..." ta turo baki.

"Assha ba sai kinyi kuka ba. Zan kwanta a kasan ko na koma falo na takure akan kujera. Hannu na nake ji dama mai gyaran yau har fada yayi min"

Pillow ya dauka ya marairaice mata "kina ganin bazan fama ba idan na kwanta a wuri mara laushi?"

Sai da tayi ajiyar zuciya tace ya kwanta ita zata koma falon yace tana fita zai bita shine namiji idan da mai hakura da gadon shine. Irin dogon pillon nan ta ajiye a tsakiyar gadon saboda a gajiye take idonta har ya soma yaji. Ta nuna masa bari daya

"Ka kwanta a can kuma kada ka wuce pillon nan"

"You are the best Yayarmu Mawadda. Sai da safe. Ki kashe fitilar bana son haske"

Kwanciyarsa yayi a barin da ta nuna masa ta lalubi makunnin fitilar ta kashe. Zata rama ne bari dai yaji saukin hannun nasa tace a ranta.

A darare ta kwanta ta takure jikinta ko hijabin bata cire ba sai zanin kawai ta kwance. Yau ita ce kwance gado daya da Dahiru a matsayin mijinta. Godiya ta yiwa Allah da Ya cika mata burin da ta fitar da tsammani daga tabbatuwarsa. Ba jimawa bacci ya fara fizgarta har Dahiru yaji sauyin yanayin saukar numfashinta.

Wani dadi ne ya kama shi ya matso ya dauke pillon ya cilla shi kasa "anyi kanekane

1 Comments On GUMIN HALAK
avatar
amina-5-7-3

9 months ago

Reply

Allah ya kara basira

Please Login or Register in order to submit comment