Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu hana auren nan. Idan ba haka ba wane dalili zaisa ta kai har yanzu babu aure babu mijin auren a hannu"

Bayan gajeren nazari ya amince da bukatarta don shima ya gaji da gorin 'yan uwa. Abokansa ma wasu sukan yi masa maganar tun yana bada amsa har yayi shiru.

Maigadinsu suka sanarwa saboda ustazu ne. Washegari sai gashi da malami aka zo aka rinka yi mata karatu harda hayaki. Malamin gudun kada ace baiyi komai ba ya zaro bulala zai fara lafta mata wai aljanun masu taurin kai ne. Tana ganin haka ta tashi a guje ta koma ciki.

Bayan 'yan kwanaki ta sami Dr Tani har daki tace ita dai tana son aure tunda Dahirun bai samu ba su taimaka su sama mata miji.

Ranar hankalin Dr Tani ba karamin tashi yayi ba don da kyar tayi bacci. A ina zata sami mai auren Qareeba? Bata son mijinta yaji wannan maganar sam domin a danginsa zai nema daga nan su sami na gori ace gwanjonta aka yi musu. Mutum daya gareta da ta rike kawa aminiya amma sun kwana biyu ko gaisuwar kirki bata shiga tsakaninsu ba. Duk da haka gani tayi gara ta sake gwada sa'arta a karo na karshe kafin a nemi wata mafitar.

Wayarta ta dauko ta jima tana sake-sake kafin ta danna kira.

Haj Mara tana zaune yau ko wanka ta kasa abin duniya ya isheta ta mika hannu ta dauki wayarta da take ruri. Sunan Dr Tani ta gani to itama damuwa ta isheta ta dauka da sauri ta gyara muryarta tayi sallama.

Dr Tani tana amsawa Haj Mara tayi wata shewa kamar bata san waye ba sai yanzu "Tani kece don Allah? Wayyo aminiyata shiru shiru na rasa nambarki ke kuma kin dena nemana"

Dr Tani taji dadi ashe dai Haj Mara bata ya da ita gabadaya ba rashin number ne amma sai ta dan dake.
"Haba Marakisiyya idan babu waya baki san gidana bane? "

Kamar zata yi kuka tace "na sani amma tun tafiyar Babawo naga kamar kinyi fushi dani. Kuma na fada miki Alhaji ne yace gara ya bar kasar kura ta lafa"

"Har shekara takwas? Ni mu bar wannan zancen dama kira nayi mu gaisa inji lafiyarku" ga dama ta samu na son jin yaya BB amma tana gudun kada ace yayi aure.

Kamar Haj Mara ta sani tace "ina 'yata kuwa Qareeba? Nasan yanzu kila tayi yara biyu ko uku. Ba rabonmu lokacin gashi shi yaki aure har yanzu"

Kankame wayar Dr Tani tayi dadi har kasan zuciyarta
"To ai nima har yau Qareeba dai tana nan in fada miki taki kowa. Nayi fadan nayi nasihar duk a banza. Wai tunda ta rasa BB na farko ta hakura da aure ke kiji"

Wata siririyar dariya Haj Mara tayi. Ta sani sarai Qareeba babu mashinshini ne tunda takan dan bibiyi me Dr Tani din take ciki. To amma dama ce ta karshe ta samu ta yiwa Babawo aure ko ya kintsu kamar kowa.
[08/01 8:32 pm] Biebie: *GUMIN HALAK...*💰15

*Batul Mamman*💖



Tsohon kango ne wanda yaran unguwar da yake ciki ma tsoron yin dare suke a kusa dashi saboda 'yan daban da suka mayar dashi wurin sheke ayarsu. Daidai ballallen gate din BB ne zaune cikin daya daga cikin motocin Alh Sule yana yiwa shugaban 'yan daban bayani.

"An fada min kaima dan Kano ne ina tunanin nemanta bazai yi muku wahala ba"

Garwashi yace "to Yallabai ka bamu hoto da adireshi mana saboda rage wahala ko ya kace."

Sosa yamutsatstsen kansa yayi wanda yaki yarda ya aske har yau yace da yasan address din me zai kawo shi wurinsu ma. Gajeren tsaki yaja sannan yace.

"Sunanta Mawadda kauyensu yana cikin Kabeji a nan Kano"

Me Garwashi zaiyi in ba dariya ba "Kabeji kuma Ranka ya dade kwadon salak zaka yi hala?....hahahahhh zan taho maka da caras da gurji"

A fusace BB ya fito daga motar ya damki wuyansa. Yaran Garwashi suka soma tasowa ganin an kama ubangidansu. Shaka sosai BB yayi masa yana huci "ba wasa bane ya kawoni. Sati daya na baka ka nemo min inda take koda gidan miji ne zan baku 500k."

Jin haka Garwashi ya daga hannu ya dakatar da yaransa. BB ya ture shi har ya kusa fadowa ya dago kai a wahale "zamu duba amma duk da haka ka bamu wata inkiya mana yadda zamu jidadin yi maka aiki na dai fahimta garinsu a Bebeji yake ko"

Sai da ya shiga mota ya zauna sannan yace "anyi mata fyade shekara takwas da suka wuce har kotu an shiga amma basuyi nasara ba"

Zaro idanu Garwashi yayi "wane dan...."
Sai kuma yayi shiru ganin irin kallon da BB yake yi masa kafin ya bada musu kura yaja motar yayi gaba.

Yaransa da suke gefe suka marmatso yana rike da wuya yana jujjuya shi.

Na hannun damansa cikin yaran yace "Baaba ina tunanin shine fa yayi fyaden kaga ai yayi kalar eh yane. Kuma don rainin sense ya shake maka wuya a fadarka don yana takamar tsohonsa yana da maiko"

Cecekuce yaran suka soma suna nuna takaicin hanasu su far wa BB lokacin da ya shake shi.

"Ku barni dashi zamu nemo yarinyar nan duk inda take. Amma kwarankwatsa zamu nuna mata solidarity tunda 'yar uwa ce bakanuwa. Gayis (guys) mu ware gobe akwai trabilin gabanmu."

******

Mawadda na zaune gaban Baba daga gefen tabarma a tsakar gidansu. Yaya da Ade suna dakunansu haka ma Iya da Inna.

Kamar kullum nasiha da yabonta ya soma yi don baya gajiya wurin karfafa mata gwiwa akan hakuri da tawakkali.

"Ina alfahari dake sosai da yadda ki ka karbi kaddara bata sanya kin zama daga cikin mutane masu gazawa imaninsu yayi rauni ba. Ki cigaba da mika lamuranki ga Allah da sannu zakiyi ta girbar alkhairi kinji."

"In sha Allahu Baba"

"Bayan wannan Mawadda ina so kada kiji kunyata ki fada min gaskiya yaya kuka yi da Dahiru?"

Faduwar gaba taji hade da kunya a lokaci guda ta dukar da kanta sannan ta fada masa gaskiya wato maganar aure da Dahiru yayi mata sai dai bata fada masa yadda suka kare da ya zama yayanta kawai ba. Ta dai sanar dashi bata amince ba.

"Baba kada ka damu nima na san ba zanyi aure ba saboda bazan yaudari kaina ba" ta fada cikin dakakkiyar murya tana kokarin boye karayar da zuciyarta take neman yi.

Tausayinta Mal Fatihu yaji sosai "Allah ne Masani ko kina da rabon aure ko babu. Abinda nake so ki kiyaye dai bai wuce kada kisa Dahiru a zuciyarki ba. Kinga yadda abubuwa suka kasance a da bana jin yanzu zata sauya zani. Duk yadda na matsu inga kina dakinki kamar sauran 'yan uwanki bazan taba yarda kije inda ba'a bukatarki ba. Na shaida Dahiru mutum ne managarci amma aure Mawadda ba alaka bace tsakanin mata da miji kawai. Ta hada da iyaye da 'yan uwa makusanta. Duk inda kika samu matsala da daya daga ciki ko iyayen miji ko 'yan uwansa to ina mai tabbatar miki miji ko hadiyarki yake don kyautatawa sai jindadinki ya ragu musamman idan iyayensa ne."

Kasa daurewa tayi hawaye ya soma fita a idanunta "Baba zan kiyaye in Allah Ya yarda" tana kaiwa nan ta tashi ta bar wurin da sauri saboda kukan da ya taso mata. Bandaki ta shige ta rufe kofa ta shiga kuka har tsakar gidan Baba yana jiyo shesshekarta.

Shi kanshi ba don namiji bane babu abinda zai hana shi tayata kukan. Zuciyarsa ce tayi masa nauyi yana kara ganin laifinsa ne na turata aiki tun farko har haka ta faru. Amma zasu cigaba da hakuri har Allah Ya kawo musu mafita.
*****

Washegari tana gama ayyukanta na gida asibiti ta tafi. Da yake da wuri taje bata dade sosai a layi ba.

Dr Imran ya gama jin duk wani bayani nata ya nuna mata file din gabansa.

"Duk wani bayani ko gwaji daga ranar da na fara dubaki har yanzu suna cikin nan. Ina fata kin rike duka bayannan da nayi miki game da ainihin abinda ya sameki har ya janyo miki lalurar?"

"Na gane Doctor. Nagode sosai" tace a hankali tana kokarin boye hawayenta. Tun maganarsu da Baba jiya haka ta tashi sukuku. Ba wai abin mamaki bane kuma itama kafin ya fada ta riga tasan da hakan. Sai dai yanzu tausayin rayuwarta take yi kawai. Bata taba hango rayuwarta zata zama haka ba. Tuni ta gama shiri da tsara rayuwarta da Dahiru a shekarun baya sai gashi Allah Ya zartar da ikonSa ta koma mai gyara amare wadda bata da ranar ganin nata auren.

Dr Imran tashi yayi ya dawo dayar kujerar marasa lafiyan wadda take kallonta ya zauna. Yana ganin yadda ta sake tura tata baya duk da cewa akwai tazara tsakaninsu tun farko. Ya sani irin haka yana daga cikin tsoron da yake bibiyarta har yanzu. A kokarinsa na taimaka mata ta rage ne yasa idan ta shiga office dinsa yake tilasta mata rufe kofa ko bata so don ta gane ba kowane namiji bane macuci. Tun tana zama tayi ta kallon kofa tana hawaye har ya samu ta dena kukan. Yanzu gashi ta yarda dashi zata zauna ba tare da tunanin komai ba.

"Mawadda."

"Na'am Doctor"

"A ka'ida yau ne last day da zan duba ki sai dai idan wata matsalar ta taso wadda bama fata."

Godiya tayi masa amma yadda ya gama karantarta na tsahon lokacin da take zuwa asibitinsu ya san tana da damuwa a ranta.

"Ko soyayyata ce tayi miki mugun kamu kike tunanin daga yau zamu rabu? Banyi niyar barinki ba yau ko kinki ko kinso zan zo gida neman izini wurin Baba"

Kai ta dago da sauri "don Allah kada kazo. Na fada maka bazanyi auren nan ba."

"Saboda wani banzan BB yake ko wa? Ki barshi haka duk inda yake sakayyar Allah zata kama shi" Ya fada ransa yana dan baci.

Kai ta girgiza tana soma kuka "ni dai kawai"

"Ke dai kawai me? Ko dai Dahiru ki ke jira?"

Dr Imran yasan labarin Mawadda domin kuwa bata boye masa komai ba bayan ya hillaceta da dabararsu ta likitoci a kokarin taimakonta. Duk duniya babu wanda take iya fadawa abubuwan da ba kowa ya sani ba bayan iyayenta sai shi.

Yanayin da yaga ta shiga yasa shi gane ko ma meye matsalarta da Dahirun a ciki. Rarrashi da shawara ya soma bata da kanta ta fada masa dawowar Dahiru cikin rayuwarta da kuma kudurinta na kin amince masa.

Dariya yayi ya shiga zolayarta "Akwai matsala kuwa don nima ba hakura zanyi ba. In fact kince na kara zage damtse mai rabo ya dauka. Wato ciwon soyayya zai tashi shine duk naga jikinki a mace yau kamar wata mara lafiya."

Sai da ya gama sawa ta saki ranta sannan yace ta yawaita addu'a da neman zabin Allah.

"Nasan kina son Dahirun nan Mawadda bazanyi muku katsalandan ba har sai naga yadda ta kasance. Ki sani dai ni masoyinki ne mai burin kyautata rayuwarki. Ina fata zumuncinmu ya dore ba wai kawai tsakanin likita da patient ba"

Taji dadin saurin fahimtarsa don bata jin zata juri fama da maza biyu akan abinda duka babu lallai su samu. Sun jima suna hira kafin wata nurse ta shigo tace ya bar mutane suna jira fa.

*****

Hira Dahiru da Attahir suke yi suna tsara bikin Attahir din da yake gabatowa nan da wata uku.

Ango yana ta zumudi suna lissafin nawa za'a ware domin hada lefe da sauran abubuwa. Ga kama gida da yake son yi shima basu gama zabar unguwa ba.

Attahir ya nuna masa hoton wasu akwatuna masu kyau da yake son zaba cikinsu.

"Ba don ka tsaya ruwan ido ba kaga kamata yayi komai muyi tare. Akwatunan nan so nayi na saya mana iri daya amma kada a saya har su fita yayi baka tsayar da mata ba tuzurun Haj Mama"

Dahiru yayi dariya "yanzu ma ai komai taren muke yi. Mata kuma kasha kuruminka Haj Mama ta kusa dena yi min korafin rashin aure ana kirana tuzuru"

Dundu Attahir ya kai masa yana cewa yaci amanarsa tunda bai sanar dashi da wuri ba. Labarin sake haduwa da Mawadda ya bashi domin kuwa amincinsu yasa ya sanar dashi rayuwarsa ta baya. Attahir na murna da wannan al'amari Dahiru ya sako zancen Anti Qareeba. Sunci dariya musamman Attahir wanda yaso kwarai ace yana wurin
"Da na wanke 'yar rainin wayo. Ni ka tabbata mamanta likita ce kuwa ba irin dafta dinnan da ake karawa gaban suna bace don ado?"

"Baka da kirki har asibiti gareta fa"

"To ai abin nasu ne ba ko kunya, gaskiya idan ka auri Qareeba sunan 'ya'yanka sorry. Tun wuri ma ka sani irin hadin zumuncin nan bazan yarda ba kada a cuceni a hada ni da jikoki 'yan ahirin"

Yana fada ya tashi a guje don Dahiru bayansa ya bi suna dariya. Haj Mama tana shigowa taja tsaki tana girgiza kai.

"Allah nagode Maka. Kattin maza maimakon su kawo min yaransu in rinka jin hayaniyarsu ina bari bari shine da kansu suke cika min kunne. Kodayake gara kai Attahir, wani yana nan sai sayen kaya da takalma yana kwalliya."

Dahiru yayi dariya yasan dashi take. Iyalin gidan nan suna kaunarshi suna nuna masa soyayya tamkar jininsu. Attahir ne yayi mata albishir da an kusa gabatar mata da suruka ai kuwa ta washe fuska tana murna.

Bayan fitarta ya matsawa Dahiru ya kamata su je ya ganta ya kara wasa mata dan uwansa don tayi saurin amincewa.

Tagumi Qareeba ta rafka tana zaune daga ita sai zani da tayi dauri ya leko ta kasa sai wata vest da hannut daya ya sabule. Ko wanka bata yi ba tun safe. Rashin mijin nan fa yana damunta sosai.

Dr Tani ce ta shigo dakin rike da leda ta dora mata akan cinya.

"Qareeba bana son wannan damuwa da kika shiga 'yan kwanakin nan"

"Kiji Mummy fa na rasa mijin aure ya bazan damu ba? Dashiru ya gujeni saboda wulakancin da kika yi masa da." Ta kare da tura baki.

Bakin Dr Tani ta doke "shashasha karshenta ma Dashiru kika rinka kiransa a gabansa ba dole ya gujeki. Yanzu dai bude ledar nan ki duba"

Ihun murna ta saka bayan ta bude . Material ne mai matukar kyau da tsada. Kamar yarinyar da aka yiwa kyautar bazata tace
"Mummy nawa ne?"

Zama Dr Tani tayi sannan cikin murna itama tace "ki tashi kiyi wanka ki kai dinki. Next week sunday Babawo zai zo wurinki. Ya dawo kuma da maganar aure"

Sakin kayan tayi "Cabdi sai kace wata mara aji Mummy? Sai da ya gadamar dawowa za'ace yazo neman aure. To ni na wuce ajinsa wallahi Dashiru nake so ki fadawa Daddy kawai"

Ranta ya soma baci don Qareeba bata san yadda ta zubar da nata ajin bane saboda nema mata miji.
"Dahirun me, har nawa yake kuma me ya taka? Banda ma lalura shi har zai taba yin arzikin da zamu roki alfarma wurinsa ne?"

Har ranta Qareeba bata so ana fadin abu mara dadi ga Dashirunta yanzu. Daukan kayan tayi ba don taso ba ta ajiye akan gado ta shiga wanka.

Da ta shirya ta fito ma kana ganinta kasan an bata mata rai. Dr Tani bata son biye mata dama ina su ina Dahiru dan mutan Tariwa. Kawai dai taso amfani dashi ne lokacin da babu kowa. Ita ba wai kudin su Haj Mara ne ya dameta ba kamar son 'yarta tayi auren da zai bawa duka danginsu 'yan bani na iya mamaki. A yanzu ansa musu ido kamar su kadai suka fara haihuwar 'yar da ta rasa miji.
******

Yadda Attahir ya matsawa Dahiru dole ya kira Mawadda ya sanar da ita zai zo da dan uwansa su gaisa.

Tana kwance tana hutawa sanda ya kira. Taji dadin jin zaizo don kwana tayi tunaninsa da kuma tunanin maganarsu da Baba. Ya zama dole ta yaki zuciyarta ta dakatar da alakar da take tunanin zata kare a ciwon zuciya. Shawarar Dr Imran zata bi da yace ta yawaita addua amma duk da haka zata yi kokari wurin janye masa.

"Sai ana magana dake ki shiga tunani. Shirun na mene?" Dahiru ya fada don ya fara ganeta da yawan tunani yanzu.

Mikewa tayi kafin tace "tunanin saurayina, sai dai kazo zan baka labari yau zance naje"

Sai da ya fito daga falon ya iya amsawa yadda yaji wani bala'in kishi ya taso masa abin har mamaki ya bashi.

"Me kika ce?"

Muryarsa ta fahimtar da ita yadda yaji sai kuma ta soma karaya.
"Asibiti naje ba na fada maka ina zuwa checkup ba"

"Mawaddatan wa Rahma!"

"Na'am inji larabawa"

"Bana son wannan wasan don Allah da gaske zance kika je? Likita ne saurayin naki?" Yayi magana cikin cijewa.

Sosai ransa ya baci da kishin da ya rufe masa ido. Bai jira ta ansa masa ba ma ya nanata mata zuwansu yanzu ya kashe wayar.

Hannunsa yasa ya rike bakinsa da habarsa idanunsa suka kankance. Karshe ya koma ya dafe saman motar Attahir da hannuwansa biyu ya dukar da kansa yana kallon kasa.

Attahir da yaji bai dawo ba ya fito ya sameshi a haka. Kafadarsa ya dafa hakan yasa shi juyowa suna kallon juna.

"Me ya faru?" Attahir ya tambaya don kallo daya zaka yi masa ka gane baya cikin nutsuwa.

"Wai ni Mawadda zata cewa taje zance? Likitan da yake dubata saurayinta ne. Wallahi bazan iya sake rasata ba Attahir. Na sota sosai a baya amma yanzu ni bansan yadda zan kwatanta maka kaunar da nake mata ba. Ban taba son wata mace ba sai ita kaima shaida ne"

Motar Attahir ya bude suka shiga sannan ya kalli Dahiru "calm down bro, har ka manta rabonka da ita ne kake tunanin yanzu komai zai zo da sauki kamar ba'ayi ba?"

"Nayi zaton itama tana sona....na tabbatar ne ma. Baka ji yadda kalamanta suka tsaya min a rai ba"

Attahir ya jinjina kai "ashe haka kake da kishi Dahiru? Lallai Mawadda sai tayi a hankali"

Shiru kawai yayi Attahir yaja mota suka fita. Lokacin da yaji labarin anyi mata fyade abu daya ne a ransa wato aure. Sai dai yafi kowa sanin me ya jima yana dannewa har mutane suke masa kallon kamar mutum marasa damuwa a rai. Ko Mawadda baya son ta san yadda yake burin haduwa da mutumin da yayi mata fyade. Ko ranar da tace masa taje Kaduna da ya bagarar da zancen yayi ne kawai saboda yadda yaji abin zai fama masa tsohon ciwonsa. Soyayyarta da son sanyata cikin farinciki sune suke dakushe bacin ransa da kishin da yake damunsa game da kaddarar da ta sameta.

Suna fitowa daga gidan daidai lokacin Qareeba ma ta fito zata kai dinki. Dahiru ta hango jiki na rawa ta zuke glass ta soma kwala masa kira. Ganin bai ji ba yasa kawai tabi bayansu.

Attahir yana ta kwantarwa da Dahiru hankali kafin su tsaya a gidan mai ya sami nutsuwa sosai.

Ana zuba musu mai Attahir yana waje kusa da me zuban man yayin da Dahiru yake zaune ya kwantar da kansa jikin kujera hade da lumshe idanu.

"AHIRIN" Qareeba tace da karfi tana tsaye daga waje saitinsa.

A firgice ya bude ido yayi tozali da ita. Tsabar rudewa ma ya manta ina yake ya taso da karfi ya buge kansa. Dama gashi rai a bace abu ya tarar masa.

"Lahhhh Dashiru sannu kaji" tace da ya fito.

Attahir kawai ya gani a gefensu yana murmushi don tana cewa Ahirin ya zagayo ya kuma gane ko wacece.

Kin kulata Dahiru yayi Attahir yace "Anti Qareeba daga ina haka"

Habawa dadi kamar ta saka ihu ta rabe jikin mota ta rufe fuska da mayafi irin na jin kunyar nan. Dahiru kansa sai da yayi murmushi sannan yace.

"Mai kika zo sha kema?"

"A'a na fito zani wurin dinki ne na hango ku shine na tsaya mu gaisa" ta sake amsawa tana ta fari da idanu.

Attahir ya gimtse dariyarsa "ko dai dan uwana ya hure miki idon ne naga yana ta kadawa"

Dahiru ya watsa masa harara ita kuwa ta kuma sunkuyar da kai "Kai dai baka da kunya da alama. Dashiru ashe kana bawa 'yan uwanka labarina gashi har ya ganeni. Don Allah ka ajiye komai ka dawo su Mummy sun amince da soyayyarmu. Yaya sunanka ne?" Ta kalli Attahir.

Yayi dariya "Ni Attashir nake"

Sakin fuska tayi "sunanku kusan daya da My Man"

"Kut..." Dahiru yace tsabar mamaki wai my man, sai dai bai sami damar karawa ba Attahir ya sakar masa dundu a baya yana masa sannu wai ya kware. Shi kuma yana make tasa dariyar da tarin karya.

Duk ta rude "Man sannu wayyo me ya sameka haka? Attashir do something mana!"

Attahir dariya taci karfinsa Dahiru bakinciki ya turnuke shi zata tara musu mutane an fara kallonsu ya ma kasa magana sai biye masa da yayi yana duka bayan nasa.

Qareeba ranta ya baci da dariyar Attahir ta karbi purewater ta bawa Dahiru sannan tayi masa wani kallo da ya kara tunzuro dariyar tasa. Bakin gwargwado yake kokarin boyewa ta sake kallon Dahiru.

"Sannu Man ko zaka zo na mayar da kai gida. Bana jin hankalina zai kwanta idan na barka da wannan dan uwan naka. I am sorry to say amma kamar yana da matsalar brain ko?"

Yace cikin gatse "haka kike gani?"

"Sosai kuwa , ka kware amma ya rinka dariya haka. Kada ku rinka raina lalura inji Mummyna gara ku kaishi asibiti"

Dahiru ya kamo Attahir shima kamar yayi dariyar sai dai so yake kawai ta tafi "haka muke fama dashi amma gara ki tafi don daga dariyar nan abin nasa gaba zai kara. Jeki kawai zan kaishi gida"

A tsorace ta matsa gefe "akwai number din malamin da aka kira yayi min karatu kwanaki ko na baku? Ni dai an tabbatar bani da aljanu amma wannan...mtsw..akwai serious problem"

"Sai nazo zan karba" Dahiru yace ya danna Attahir a mota wanda dariya ta sa ya soma hawaye.

Qareeba na ganin ya goge ido tayi baya tana sake cewa Dahiru yayi a hankali ya kunna motar suka yi gaba. Itama juyawa tayi tana adduar Man dinta ya isa gida lafiya.

Har suka tsaya a danja dariya suke yi. Attahir sai ya kalli Dahiru yace "My Man" sai su sake kwashewa da dariya.

"Man da gaske fa idan ka auri Woman babu zancen auren zumunci tsakanin 'ya'yanmu. Wai ji ko kadan bata ma fahimci ita ce abar dariyar ba"

"Ai baka ga komai ba. Ni da na zauna a gidan nasha kallo wani abin shiru ake yi kawai"

Har suka isa gidansu Mawadda suna dariyar Anti Qareeba.
******

Yanayin da Dahiru ya amsata da ajiye waya ya tsaya mata a rai. Jiki a sanyaye ta fita falon da take sauke shi ta sami Marwanu a kwance kan kujera yana bacci yazo hutu. Tashinsa tayi tace ya kwashe kwanukan abincin da ya soma tarawa daga zuwansa.

"Bako zaki yi ne Yayata ta kaina?" Ya tambaya yana daga gira.

"Jere zamu yiwa amaryarka dai" ta bashi amsa fuskarta ba walwala.

Tattare kayan yayi harda fesa wani turare da take hadawa na daki. Yana fita ya tambayi Ade me aka yiwa Mawadda tace itama tun jiya ta kula yanayinta ya sauya. Yaya tace sun sawa 'yarta ido a barta ta sarara.

Ba dadewa Dahiru ya sake kiranta yace sun iso. Har yanzu yana jin ba dadi saboda maganarta ta dazu kuma taji hakan a muryarsa. Ji tayi kamar tasa kuka da tayi tunanin me zaiyi kuma idan ta tabbatar masa da ya dena zuwa da sunan ganinta gabadaya.

Marwanu ne shigo dasu yana ta murnar ganin Dahiru. Sai da ya fita Mawadda ta shigo ta zauna a inda ta saba , bakin kofa.

Attahir ta gaisar ta dauke kai kamar bata ga Dahiru ba. Shima wayarsa ya shiga dannawa yaki kallonta.

Attahir yayi gyaran murya kamar suna jira duka su biyun suka kalle shi hakan yayi sanadin haduwar idanunsu. Mawadda ce ta soma kawar da kai gabanta yana faduwa. Ta rasa gane wane irin so take yiwa wannan Dahirun daga sake haduwarsu. Shima a nasa bangaren neman fushin ma yayi ya rasa amma sai ya basar ya kawar da kai.

Attahir ya gyara zama yana dariya "Fushin masoya da dadin kallo bari na dauka a waya ko na sami abin kallo da nishadi"

Murmushi Mawadda tayi "ayi haka Dan uwanmu? Ka tambayar min shi dai ko nayi masa laifi ne daga wasa"

Dahiru ya tabo "ka fada min me 'yar uwarmu tayi maka daga wasa ka shigo kana wani hade rai"

"Ta fada maka wurin wa taje zance har take iya fada min nida tace na tsaya iya yayanta kawai"

Juyowa yayi ya maimaita tambayar tace cikin murya mai rauni tana shirin kuka "ni wasa nake masa kace yayi hakuri bana so mu rabu haka"

Wata irin juyowa Dahiru yayi ya kalleta kafin ya sake cewa Attahir "kaji zancen rabuwa ma take

1 Comments On GUMIN HALAK
avatar
amina-5-7-3

9 months ago

Reply

Allah ya kara basira

Please Login or Register in order to submit comment