Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta hau kan gadon su ka fara ci ita ta na ci ta na chatting.


Yusuf ne ya dallawa Hafsa harara ita ba ma tasan ya na yi ba cikin tsawa ya ce ”Hafsa miko mun wayar nan ku dai baku son cin abincin sai afkin chatting".


Hafsa ce ta fara fadin “Yaya dan Allah na dena......"cikin fada Yusuf ya ce “Baza ki bani bane kinsan dai bana son musu ko"


Badan taso ba ta mikawa khadeejatu wayar ta mika mashi.

*************

*Washegari*


“Hmmm ai Suwaiba yadda kika ji na fada maki hakan ne ya faru "cewar Mama


Umma ta gyara Zama ta ce “Yaya Sadiya baki tunanin ko juyar masa da kaii taje akayi ba".


Mama ta ce “Naka nima yanzu nake zato shiyasa ma nace zan maki maganar da har gida ma zanso sai kuma aka kwantar da khadeejatu".


Umma ta ce ”Yaya Sadiya karki damu zanwa Abban Khadeejatu magana a kai duk yadda akayi zan kira ki in sanar maki ko ma nazo har gida"


Mama ta ce “Tom Nagode sosai bari mu koma ciki Maryam ta taho mu tafi gida"


______________

“Wai ina ruwanka dani ne Nura sai kaji inda zanje ajiye ni kayi ko kaii ubanane da har sai kaji ina zanje ".


Nura ne ya ce ”Allah baki hakuri "duk yayi kashin wuya yayi baki duk ya rame idanuwansa duk sun fito.

Ko kara kallon inda yake ba ta yi ba ta fice.


************


Zainab na tafe a hanya tana jin kida wayarta ta fara ruri ta na dubawa ta ga an sa Alhaji Bala.


Dagawa tayi ta kara kunnenta cikin kashe murya ta ce ”My Alhaji gani nan fa a hanya na kusa zuwa hotel din".


Tana karasawa hotel din tayi parking ta shiga direct daki da ya fada mata ta nufa tana murda handle din ya bude.


Wani dattijo ne a zaune akan couch ya na latsa wayarshi.


Tana karasawa gurinshi ta dena kan cinyar shi ta na sakala hannu ta a wuyan shi.......................✍🏻🖊️










*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ................✍🏻✍🏻










Taku ce har kullum
Addeejerh

09012671608



✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.


*JUMA'AT MUBARAK* 🕋 *MUSULIMS* _Allah_ _sada mu da Alkhairan_ _da ke cikin wannan rana_ _mai albarka_ , *Amin* .



21~22


*Bayan kwana biyu*

Alhamdulillah Khadeejatu ta samu sauki sosai an sallamo su soyayyar ita da Ya Yusuf baa cewa komai ko Yaushe su manne da juna a waya ko yazo gida.


”Dan Allah Zainab ki taimaka ki bani hakki na ina cutawa kinji dan Allah" Nura ne yake rokar Zainab.


“Dallah chan malam ni ka takura mun naki na baka an fada ma ni inji ce ".


Nura bai kara ce mata komai ba ya fice yana tafe kamar zai fadi kitchen ya nufa ya dauko lemon tsami a fridge wajen guda uku ya matse a cikin cup ya shanye dakin shi ya nufa.


Ya na shiga ya kwanta a kan gado ruf da ciki zirrrr sai ga hawaye ya na zubowa ta idonshi.


*Bayan sati hudu*

“Mama Yanzu gidan Ya Nuran zaki je?" cewar Maryam.

Mama ta na zira Hijab ta ce ”Ehh mana gwara naje na kai mashi wannan rubutun tunda jiya Suwaiba ta aiko su Khadeejatu gwara a kai dan malamin yace sai yayi wata daya da sati uku ya na sha".

Maryam ta ce “Hakane Allah yasa a dace ".

Mama ta ce “Amin Amin" ta dau galan din rubutun ta fita.

Sanda Mama ta isa gidan ta tarar Zainab bata nan sai Nuran shi kadai sai birgima yake.

Ungurnu ta jika ta bashi nan yadan ji dama dama .

Mama takalleshi a hankali ta ce ”Nura ".

Amsa mata yayi ya ce “Na'am Mama".

Nuna mashi galan din rubutu tayi ta ce “Ka ga wannan inaso safe da dare kasha kofi daya ina so ka fara a daren yau karka kuskura ka bari matarka ta sani kasan inda zaka ajiye".

Cikin ladabi ya ce “Tom Mama zanyi yadda kika ce nagode".

Mama ta ce “Yanzu ina matar taka take?"

Nura na shafa kanshi ya ce “Tun jiya bata nan"

Bude baki Mama tayi Amma bata ce komai kawai ta ce “Allah ya kyauta ni kaga zan wuce gida na baro Maryam" ta mike tsaye.

Shima Nura mikewa yayi ya ce “Mama bari na sauke ki a gida"

Da sauri Mama ta ce “A'a kayi zamanka kai da baka da lafiya zan hau adaidata dama a ita nazo".

Ya sosa kanshi ya ce “Tom shikenan Mama Allah tsare ki gaida Lil sis" har waje ya raka ta.


*Bayan wani* *lokaci*

Biki biki yazo yau saura sati biyu auren su Khadeejatu da Yusuf ya matso su Umma Sun fara gyara diyarsu ta ciki ta waje.


Khadeejatu ce a kwance sai juyi take tana wayar tana sakin murmushi ta ce ”Nifa Ya yusuf kana sani ina jin kunya".

Yusuf ya ce ”Kunyar mai ai gaskiya na fada nan da sati biyu iwar haka mu na tare insha Allah".

Khadeejatu tayi murmushi mai sauti tana rufe fuskarta dariya Yusuf ya kyalkyale da ya ce “Wannan kunyar tsab sai na kawar da ita".


Kawar da maganar Khadeejatu ta ce “Ya Yusuf ka san mai ?".

Da sauri Yusuf ya ce ”A'a sai kin fada Sweetheart".

Ta ce “Wallahi kwana biyun nan ne gaba na ya na yawan faduwa yau ma cikin dare nayi wani irin mafarki da yayi masifar tsorata ni wai a mafarki wani irin guri ne tal da haske kamar hasken sararin samaniya wani saurayi ne kwance a gurin cikin fararen kaya jini na zuba ta bakin shi da hanci yace mun “Nana Khadeeja dan Allah duk wanda zaki aura ki mashi biyayya dai dai gwargwado komai yace maki kiyi indai bai sabawa addinin ki ba sai kawai yayi sama kamar an daga shi". a daidai lokacin na tashi.


Cikim kwantar da Hankali Yusuf ya ce “Nana karki damu kinji insha Allah ba abunda zai faru sai alkhairi , amma in tambaye ki da kika tashi da fatan kinyi alwala kinyi sallah?(Alummar musulmai ya na da kyau indai kayi mafarki ko wane iri kayi sai ka samu kayi sallah daga raka'a biyu zuwa yadda kaga zaka iya, Allah ka ba da iko Amin).


A hankali Khadeejatu ta ce ”Eh nayi sallah ban ma koma ba sai bayan da nayi sallar Asuba".

Yusuf ya ce “Da kyau Nana ki dage da yin azkar din safiya da maraice kina addua in zaki kwanta kina kwanciya da Alwala koda bakya sallah dan alwala babbar kariya ce ga mumini Allah kasa mu cika da imani".


Khadeejatu ta amsa da “Amin Amin" nan su ka cigaba da hirarsu irin da masoya....................











*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ...............✍🏻🖊️









taku ce har kullum
Addeejerh

09012671608




✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA* *ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.


23~24


Saura kwana uku a fara biki su Hafsa an shiga kawuna su na ta zirga zirga ba wani event za'ayi bama kamu/ mothers eve za'ayi sai dinner da abokanan Yusuf su ka hada mashi.


Bayan Magariba Yusuf yazo ya kai su Khadeejatu da cousins dinsu Yan mata shan ice cream .


Wata red doguwar riga yasa wanda ta sake fito da ita gashi tayi wani haske tayi bulbul da ita kamar ka taba jini ya zubo dama gata fara da ita.


Table of 5 suka yi Khadeejatu na dayar kujerar dake gefen Ya Yusuf.


Waiter din Ya yusuf ya kirawo ya masu oder ice cream da shawarma.


Ba bata lokaci aka kawo masu oder su ka fara ci suna shan ice cream.


Dan karkatar da kujerar shi Yusuf yayi yana murmushi ya ce “Nana Khadeejatu "


Khadeejatu na murmushi ta juyo ta na kallon shi kifta mata ido yayi ya debo ice cream din ya kaii dai-dai bakinta.


Da sauri ta rufe fuskarta tana dariya ya ce “Baza ki bude ba ?ko sai na bude da kai na" ya fadi ya na dariya.

A hankalu ta zame hannunta ta na murmushi ya ce bude , a hankali ta dan bude bakinta kadan yadda cokalin hannunshi zai samu shiga bakinta ba tare da an samu tangarda ba bata yayi karas karas karas kake jin karar flash ta ko ina.

Dariya Hafsa su ka ringa yi su na ihu wasu Mata da miji ne su ka karaso gurinsu su na murmushi su ka fara tafi.

Matar ce ta ce “Nice couple "

Murmushi Yusuf yayi khadeejatu ta kifa kanta a kan table din tana dariya.


Hafsa ita ma murmushi take ta ce “Basu zama couples din ba sai nan da kwana biyu ".


Mijin ne ya mikawa Yusuf hannu su ka yi musabaha mijin yana murmushi ya ce ”Na taya ka murna brother Allah sanya alheri ni sunana Muhammad Kabeer ya nuna macen yace this is my wife sunan ta Suhailat watan mu shida da aure ko zan iya sanin sunanka da na amaryar mu mai jin kunya?".


Yusuf shima yana murmushi ya ce “Amin nagode nice to hear ni sunana Yusuf my Wife to be insha Allah sunan ta Nana Khadeeja"


Muhammad Khabeer ya ce “Nice".

Suhaila har ta sa ke da su Khadeejatu su na ta hira nan suka yi Exchanging contacts din juna...........


**********

Anyi kamu lafiya komai ya tafi bisa tsari yadda aka shirya shi .

Ranar juma'a da daddare akayi dinner a _Meena_ _events centre_

Nan kawayen Amarya su ka fito domin shigo da Amarya da ango a layi su ka jeru .

Amarya da Ango na shiga hall din dj ya sakar masu wakar nan ta Ali jita dubu rana da wata su na da haske gimbiya ta sai ke soyayyar mu har abada diridirin din kece gimbiya ta haske na zuciyata......


Su Hafsa sai dan girgizawa suke haka har suka karasa inda aka tanadar ma Amarya da Ango dan zama.


Ba bata lokaci aka yi adduar bude taro.

Nan aka kira babbar kawar amarya kuma aminiyarta Yar uwarta ta bada tarihin Khadeejatu inda aka ringa dariya ta gama aka tafa mata kana ta koma mazauninta.

Nan shima babban abokin ango Sulaiman ya bada tarihin ango .

Nan aka fara dinner ka'in da na'in nan na hango dandazon yan KHADEEJATU FANS 1&2 da ma sauran masoya su na ta zuba loma lol.


Sai sha biyun dare aka tashi.


*Washegari*

Rana bata karya sai dai Uwar diya taji kunya a yau ranar asabar da misalin karfe 10:30 na safe aka daura auren *KHADIJA ADAM* da *YUSUF SULAIMAN*
wanda ya samu hallartar dumbun jama'a a bisa sadaki dubu tamanin inda Alhaji Abdullahi mahaifin Hafsa ya zama wakilin Amarya ko wa kagani a wannan lokacin bakinsa yaki rufuwa bare mai gayyar sai gaisawa yake da Yan uwa da abokan arziki.


Amarya najin an daura sai ta fara kuka ana ta lallashin ta hafsa ma ta na kwalla cikin mutuwar jiki Khadeejatu ta kalli Hafsa idanuwa shabe shabe da hawaye ta ce “Gabana sai faduwa yake zuciyata ta na bugawa da sauri sauri".

Nan Hafsa ta ce “Insha Allah bakomai”

Nan aka gyara mata fuska domin angwayen sun zo su ka fita akayi ta hotuna kamar ba gobe.


Bayan angwaye sun koma gidansu Yusuf
suka bararraje a falon shi chan Yusuf ya tashi yace bari ya shiga daki yayi walaha.


Bayan shigar shi da minti goma wani abokinshi ya ce ”Kun gani ba ya shige ya shanya mu”ya mike ya nufi dakin ya leka ya hango shi yana sujjada nan ya koma falon ya ce masu bai idar ba.


Nan su ka cigaba da hirarsu Ahhh abu yaki ci yaki cinye wajen minti goma sha biyar still Yusuf bai fito ba.

Sulaiman ya mike ya ce “Bari dai na gano shi" ya na shiga dakin still ya na sujjadar ya ce “Shi wannan ko lafiya? nan ya fara kiran sunanshi Yusuf!! Yusuf!! Yusuf!!” shiru.


Kawai sai ya karasa gun shi ya tabo shi rijib ya fada kasa hancin shi da bakinshi na zubar da jini da karfi Sulaiman ya kwallara kara ya na fadin “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun............................










*MORE COMMENT*
*MORE TYPING..........* ✍🏻✍🏻








Ta ku ce har kullum
Addeejerh

09012671608


✨✨✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨✨✨


*LABARI/RUBUTAWA*


*KHADIJA ADAM IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*AND NOW*


✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*__________________________________*


ALHAMDULILLAH!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah kasa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai.


Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana.

Amin


25~26

Ummin su Yusuf da taho ita da kanwar ta domin kawo masu abinci jin salatin nan ya sata da sauri su ka karasa falon ba kowa gaban ta na bugawa da sauri sauri su ka shiga daki.


Abinda suka gani ba karamin firgita su Ummi yayi ba da karfi Ummi ta kwallara kara ta fadin “Innalillahi wa inna ilair rajiun" sai kuma tayi luuu zata fadi da sauri wani a cikin abokanan ya tora ta ma kasa magana sai hawaye dake zirya a idonta.


Sulaiman ne ya ce “Muyi maza mu kai shi asibiti" daya daga cikin abokanan ya ce “Ba zuwa asibiti sai dai muyi hakuri Yusuf ya riga da ya riga mu gidan gaskiya" ya na maganar ya na hawaye .


Ai jin haka Ummi ta sume kanwarsu Salma ta fashe da kuka ta na jijjiga Ummi ta na ta sumbatu ruwa aka yayyafa ta farfado tana ta kiran “Yusuf!!Yusuf!! kar ka tafi ka barni kamar yadda Yayarka ta rasu ta barni da marayun Yara, “Innalillahi wainna ilaihir rajiun".

_____________

“ Innalillahi mai naji kina cewa Innalillahi wa inna ilaihir rajiun Yusuf din ne ya rasu?" Mamin Hafsa na kuka ta ce “Wallahi kuwa yanzu kanwar mu Salma ta kira ni ta sanar dani yanxu ya za'ayi da su Khadeejatu? kinsan dole ta sani".


Nan daki ya kaure da salati Umma ma tana kuka ta ce “Ina ga kawai ace Ummin Yusuf ce zata hadasu su biyu ta masu nasiha sai a kirawo daya daga cikin abokanan sa yazo ya dauke su mu sai mubi su
a adaidaita tunda baza a barsu su tafi su kadai ba".


Mami ta ce ”Hakan yayi bari na kira Salma din".

______________

“Ya Abubakar mai ya faru ne naga motoci tunda daga farkon layin nan?" Khadeejatu ke wannan tambayar .


Da sauri Abubakar ya goge kwallar da ta zuba mashi ya kawar da kanshi cikin yake Ya ce ”Yan uwan su ne da suka zo daga Maiduguri sai abokan arziki da su ka zo".

A hankali Khadeejatu ta ce ”Toh" ba ta kara cewa komai ba.

Su na horn mai gadi ya bude masu .

Su na shiga Abokan Yusuf duk suna nan a tsaitsaye .

Su na fitowa Hafsa ta kama Hannu Khadeejatu Sulaiman tunda ya hango Khadeejatu ya fashe da wani irin kuka ya na barin gurin abokanan nasu.


Ai shigar su Falon idon Khadeejatu ya saukaa akan gawar Yusuf a matukar firgici Khadeejatu da gudu ta karasa gurin Ummi dake zaune tana laximi duk idonta ya rine yayi jawur.


Khadeejatu ta kama hannu Ummi fadi take “Ummi wane ya mutu ne ina Ya Yusuf dina?" Ummi ce ta rungumeta ta na fashewa da kuka.


Fincike jikinta Khadeejatu tayi gurin gawar ta karasa ta tsuguna ta bude likafani nin da yayi faca faca da jini .


A firgice ta tashi kamar zata yi baya sai zare ido take da sauri Hafsa ta kama ta fizgewa tayi ta tsuguna a gurin ta kurawa Yusuf ido kamar ya na murmushi hannunta na rawa ta shafa gefen fuskarshi.


Sai kuma ta dora kanta akan kirjin shi da sauri ta mike har tana bangaje Hafsa da ke rizgar kuka.


Hannun Ummi ta kamo ta na janta fadi take “Wallahi Ummi Ya Yusuf dina bai mutu ba gashi nan zuciyar shi na bugawa kizo ma kiji".


Ta figo Hannunta har gurin gawar ta kai ta tana dora Hannunta akan kirjin shi Ummi ce ta girgiza kaii ta na hawaye.


Baban Yusuf ne da wasu maza suka shigo har da Sulaiman su na dauke da makara .


Baban Yusuf ne ya kama Ummi ya rungumeta ya na shafa mata baya shima kawai dauriya ya ke Yusuf yaron kirki ne dan albarka bai taba saba masu ba.


Tsakanin su Umma ya kai ta ya Zaunar da ita .


Ya je ya banbare Khadeejatu da ga jikin gawar ta ma kasa kuka.

Mami ce tazo ta kama Khadeejatu.


Kama Yusuf su Sulaiman su kai suka sashi a makarar su ka dauke shi su ka fita.


Sai a lokacin Khadeejatu ta fashe da wani irin matsananci kuka ta nuna hanyar kofar tana sumbutu cewa take ”Ku dawo mun da Yaya Yusuf dina bai mutu ba Mami ki bisu ki ce masu bai mutu ba su dawon da mijina muyi rayuwa aure dashi yadda ya ke fadamun mu samu yara dan Alllah su dawon da miji na wasa yake yi ni nasani dan girman Allah dan Annabi a dawon dashi wasa muke wayyyo ni na shiga uku" nan ta kara fashewa da wani irin marayan kuka har muryata na dashewa .




*************



*Da daddare*


Salma ce akan Khadeejatu dake ta kuka.

Nan Sulaiman ya shigo hannunsa rike da leda yayi sallama.

Salma ta ce “An samu Yoghurt din ko ?".

Sulaima ya ce “Ehh yana mika mata ledar".

Cirowa tayi ta kalli khadeejatu ta ce ”Yauwa tashi kidan sha dan Allah kinga tun jiya da daddare rabon ki da cin abinci".


Hawaye na zirarowa ta idanuwan Khadeejatu ta girgiza kanta .


Nan Salma take ta lallaba ta .................

*Bayan sati* *uku*

“Ya yusuf dama na fada masu baka mutu ba sunki yarda gashinan yanzu kana mun magana wayyyo Ya Yusuf ka tsaya karka tafi...." Khadeejatu ce take wannan maganar cikin karaji bacci take.


Da gudu su Umma suka shigo dakinta su na fadin “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun".


Gurinta Abba ya karasa ya na fadin “Mai ya faru Khadeeja?".

Kuka ta fashe da tana fadin “Abba Ya Yusuf"nan ta fara surutai Abba ne ya kama ta ya na addua ya na tofa mata a jikin ta........✍🏼






*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .......✍🏼✍🏼




_Pls share_ 🙏🏻


Ta ku ce har kullum *Addeejerh❤️*


✨✨✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨✨✨


*LABARI/RUBUTAWA*


*KHADIJA ADAM IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*


👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨


*AND NOW*


✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨

*___________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*__________________________________*


ALHAMDULILLAH!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah kasa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai.


Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana.

Amin



*Shalelen kainuwa is back* 🚴🏻‍♀️🚴🏻‍♀️


_ALKALAMIN DA BAYA_ _RUBUTA SHIRME_ 🤟👌


*Recap* 👇🏻

Da gudu su Umma suka shigo dakinta su na fadin “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun".


Gurinta Abba ya karasa ya na fadin “Mai ya faru Khadeeja?".

Kuka ta fashe da tana fadin “Abba Ya Yusuf"nan ta fara surutai Abba ne ya kama ta ya na addua ya na tofa mata a jikin ta........


*Cigaba* 👉 27~28


“Haba dan Allah Khadeejatu ki daure ki ci abinci nan ki dena kuka Yusuf adduarki ya ke bukata insha Allah yana matsayi mai kyau ko da yadda kika ganshi fuskarshi kamar ace Yusuf ya amsa insha Allah Yusuf na matsayi mai kyau yayi mutuwar shahada bawan Allah ya na sujjada Allah ya karbi rayuwar shi yaro mai ibada mai biyayya ba wanda ya taba fadin wani aibun shi baya fada Khadeeja inason ki dauki kaddara mai kyau ko akasin haka ki zama mai tawakkali duk sanda ya fado maki a rai kiringa fadi “inna lillahi wa inna ilaihir rajiun" ba na so kina zama a guri ke kadai in kin gama idda ki fito da miji ki aurenki ki tafi gidan mijinki" Mamin Hafsa ke mata nasiha.


Khadeeja cikin kuka ta ce “Nidai mami bazan sake aure ba har abada sai dai in Ya Yusuf dina ne na dawo in ba haka ba har na mutu ba zanyi aure ba".


Mamin ta ce “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun" Mami ta fara ta hannu ta na fadin “ina haka zai faru Khadeeja kar fa kwakwalwar ki ta fara fada maki hauka ba ai kam aure ya zame maki dole kinyi zama zaki mu jika ki a ruwa musha ne kuma ki dau abincin nan ki fara ci ban son jin komai daga bakin ki".


Sai kuka Khadeeja take kamar ranta zai futa har wasu irin kashin wuya duk sun firfito mata idanuwan ta sunyi dark circles duk kayan ta sun mata yawa.


Mami ce ta kalleta ta girgiza kaii ba karamin tausayi yarinya ke bata ba janyo ta tayi jikinta ta ringa shafa mata baya cikin nasiha da kwantar da hankali ta ce ”Khadeeja ki daure kidan ci abincin nan ko cokali uku ne".



****************

*Bayan wasu lokuta*


“Kaiii Nura har ni zance kayi abu kaki yi saboda ka rainani to billahillazi baze yiwu ba ka..........tassss tasssss tasssss Nura ne ya mari Zainab.


Zainab na rike da kuncinta ta ringa kallon Nura cike da mamaki bakin ta na rawa ta ce “Nura ni zaka daga hannu ka mara?".


Cikin kunar rai da zafin zuciya Nura ya nunata da yatsa ya ce “An mara din ko da abin da za kiyi na fuskaci notukan kwaKwalwar ki sun fara kuncewa kamar bakisan darajar aure ba zaki ringa dagawa mijinki murya kamar da sa'anki kike magana to wallahi zan gyara maki zama a gidan nan ".


Bai ko saurari mai zata ce ba yayi shigewar sa daki ya barta tsaye rike da kunci.


Da kallo Zainab ta bishi ta girgiza kanta a fili

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment