Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana breakfast ”.


Juyowa yayi ya kalleta ya ce “Amma asibiti fa zan tafi "


“Bansan da zuwan naka bane zaka wani ce asibiti za ka kaga Malam in ba zaka girka ba shikenan" Zainab ke wannan maganar cikin masifa da daga murya.


Cikin sanyin Murya ya ce “Yi hakuri zanyi yanzu kuwa"

Ta tabe baki Zainab tayi ta ce “da yafi ma"

Haka ya cire coat dinshi ya fice ya nufi kitchen chips ya fara ferewa ya na soyawa ya na gumi haka har ya gama .


Ya zuba a plate ya hada tea ya kaimata har daki .


Ya na shiga hakima ko tashi bata yi ba ta na zaune ta na latsa waya yazo ya ajiye a gefenta a kan bedside ya ce “Gashi!" banza ta mashi kamar bada mutum ya ke magana ba da dutse ya ke yi.


Bai sake ce mata komai ba ya a gurgije ya fara shirya dan time ya ja ya dau briefcase nashi ya kai kofar fita kenan yaji ta ce,


“in ka dawo anjima zan jika ma underwears dina zaka wanke mun kaji ni ko?"


Ya Amsa da “toh".

A gadare ta ce “ka iya tafiya" sannan ya sa kai ya fice.


Ya na futa tasa shewa tana tafa hannayenta ta ce “Gaskiya aikin boka ya na kyau" ta yi dialing number Safiyya.....



*ASALIN DR NURA*

Asalin babansa fulanin gombe ne Alhaji Saifullahi muhammad sun hadu ne da Hajiya Halima Ahmad ita ma fulanin usul ce yan adamawa lokacin yaje wani aiki ne ya hadu da ita a lokacin sunje shopping ita da y'ar yayar mamanta shima yaje a lokacin yaji ya kamu da sonta bai yi kasa a gwuiwa ba ya sanar da ita abunda ke ranshi kuma Allah ya taimake shi da wuri ta amince ba tare da yasha wahala ba.




Haka suka ringa shan soyayyarsu babu kama hannu yaro har aka kai magana gurin manya aka yi bincike ba a samu wata matsala ba aka fara shirye shiryen biki aka sha shagali bayan an daura aure ne aka dauko Amarya daga Adamawa aka kawo ta kano gidanta da ke Sharada.




Shekarasu biyu da rabi da yin aure amma ko bata wata Halima bata yi ba ba karamin damuwa tayi kullun cikin bata baki Alhaji saifullahi yake yi kullum cikin nasiha dangin mijinta(Allah yayi wa iyayen Alhaji saifullahi rasuwa a hannun kawunshi ya girma)kuwa cikin habaici suke mata ita wai juya ce haka kullum ta ke shan kuka.



Rana daya kwatsan sai gashi ta samu ciki dangi da abokan arziki sai murna ake Alhaji Saifullahi kuwa kamar ya maidata ciki ya dauki son duniya ya daurawa cikin nan , lokacin haihuwa yayi inda ta haifi yan biyu maza murna sosai kowa sai san barka ake mata.



Yan biyu na da wata biyu cikin dare sai Hussaini ya fara wani zazzabi mai zafi haka akai shi asibiti aka kwantar dasu da asuba Allah ya karbi abun shi kafin safiya kuwa shima Hassan yace ga garinku nan.


Halima ba karamin damuwa ta shiga ba wannan karan haka, tayi tawakkali ta barwa Allah komai.


Cikin ikon Allah bayan wata tara da rasuwar yan biyu ta samu wani cikin ta haifi danta namiji inda yaci suna Nura haka Nura yayi wayo bayan ta yaye shi da shekara daya ta sake haifar diyarta mace inda taci suna Amina haka suka ringa rainon yayansu cikin so da kulawa bayan shekara biyar ta sake sullubo diyarta mace mai suna Maryam.



Haka rayuwa ta ringa ja Nura har ya gama degree dinshi a bangare likitanci ita kuma Amina tana level 2 inda take karanta mass com ita kuma maryam tana SS1 lokacin.



Rana kwatsan aka tashi Amina ta dena gani iyayensu bakaramin tashin hankalin su ka shiga ba haka aka ringa kaita asibitoci aka ce gaskiya sai an futa da ita an mata aiki da yiwuwar idanun su bude tinda ba haka aka haife ya ba.



Ranar juma'a 1/10/2018 ita ce ranar da iyalan Alhaji saifullahi suka shiga cikin tashin hankali a ranar ne Alhaji Saifullahi da Amina suka je yankar ticket din tafiya kasar da za su je domin yiwa Aminan aikin ido a hanyarsu ta komawa gida ne suka yi hatsari a ta ke Allah ya dauki ransu


Su Mama da Nura ba karamin tashin hankali suka shiga ba Mama suman ta hudu .


Haka harta futa daga takaba aka yi rabon gado bayan shekara daya Nura ya tsuro da maganar aure inda ya hadu da wata budurwashi Zainab.



Nan mama ta je gombe ta sanar da kawunshi ba tare da bata lokaci ba aka yi abunda zaayi aka daura masu aure inda aka kai Amarya gidanta dake kundila.............🖊️✍🏻






*MORE COMMENT*
*MORE TYPING..........* ✍🏻✍🏻




Taku ce har kullum

_Addeejerh❤️_


✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND* *NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*ALHAMDULILLAH* !!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.



7-8


Ango da Amarya sosai su ke buga amarcin su ba kama hannun yaro ko minti daya ba su so suyi ba sa tare aiki ma sai ya kama yake zuwa irin emergency.


Bayan wata biyu da auren na su ne Zainab ta fara kawo wasu irin halaye ta dena girki tace wai ita ko a gida bata fiye girki ba dan haka a nan ma baza tayi ba.


*CIGABAN LABARI*


*Bayan Magariba*


Khadeejatu ce a tsakar gida tana share gurin da tayi wanke -wanke aka yi sallama.


”Assalamu Alaikum"wani kamilin dattijo yayi sallamar .

Da sauri Khadeejatu ta dauraye hannunta ta na gogewa da gudu taje ta rungume dattijon ta na fadin “Oyoyo Abba na oyoyo sannu da zuwa"



Murmushi ya yi ya ce “sannun ki da gida diyar albarka" kana ya kama hannunta su ka nufi dakin inna bakinshi dauke da sallama ya shiga dakin .



Inna na zaune akan tabarma ta na cin kwadon zogalen da Umma ta kwad'a mata ta na ganinsu tana murmushi ta ce “ahh babana har kadawo".



Ya na murmushi yaje ya durkusa a gabanta ya ce “wallahi Inna na dawo da fatan na same ku lafiya tuni Khadeejatu ta kwanta a jikin Inna kamar wata mage shafa kanta inna tayi.


Inna ta kalle shi tace “Lafiya kalau ya kasuwancin da fatan an samo abunda ake nema".


Alhaji Adamu Mahaifin Khadeejatu
murmushi yayi ya ce “sai dai muce Alhamdulillah Inna"



Inna ta ce “Ahh Masha Allah haka ake so"
sai da su ka dan sha hira kana ya mata sallama ya nufi gurinsu ita dama Khadeejatu tafi kwana da Inna tun dawowar ta gidan


Sai da Umma ta tabbata da Abban Khadeejatu ya kammala cin Abincin kan ta kalle shi ta ce “Abban Khadeejatu Allah sa ba ka manta gobe zamu je gidan Yaya Halima ba?"



Dagowa Abba yayi ya ce “kashhh kuma wallahi kinsan kuwa na manta wallahi gwara ma da kika tuna mun".


Murmushi umma tayi ta ce “Ai dama shiyasa nace gwara in tuna maka".


Abba ya ce “Aiko kin kyauta Allah kaimu goben bari na ga ya za'ayi zuwa gobe da safen"


Umna ta ce “toh Allah ya kaimu , Allah taimaka , Allah kara budi".


Abba ya Amsa da Amin Amin , Allah ya maki Albarka.


*BAYAN SATI DAYA*

“Assalamu Alaikum" Mama tayi sallama .

Zainab ta na zaune a daya daga cikin kujerar hadadden falon su ta na danna waya sai taunar cingum ta ke kasss kass irin na yan tasha ta cokalo daurin ture ka ga tsiya.


Sa ke sallama Mama tayi amma ko arzikin Zainab ta amsa mata bata yi ba sai ma cigaba da latsa wayar ta da tayi .



Cikin masifa da zafin nama Mama ta ce “ke Zainab wane iri hauka ke damun ki ne ina sallama amma kamar ba yar musulma ba kinki amsa mun?".


Sai a lokacin Mama Zainab ta dago tana daddaga hanci ta kalli Mama sama da kasa kamar ta ga kashi a tijare ta ce “au Mama dama kece ni na zata ma karya ce ta shigo take haushi ta na bukatar kashi da inna gama abunda zanyi sai na dauko kashin da mu ka ci Kaza da daddare".


Da sauri “Mama ta ce “kutumar uba ni kike fadawa wannan maganar Zainab to sai dai in uwar kice karyar "


Da sauri Zainab ta tashi ta na fadin “ya haka Mama ne zaki zo ki.....kafin ta karasa sai ga Dr Nura ya fito daga shi sai singlet da boxer hannunshi rike da bokiti wanda ya wanke ma Zainab kayan bacci .


Mama dake tsaye tana kallon ikon Allah ya na zuwa kusa da ita ya ce “Mama sannunki da zuwa ina wuni ya dan risuna".


Mama ta ce “lafiya kalau ina dai fatan lafiyarka kalau na ga wajen sati kenan baka shigo ba, abokin kamal ma yace kwana biyu baka shiga aiki gashi wayarka a kashe".


Zainab na hura hanci ta ce “ni na hanashi zuwa gurin naki da asibitin ko da abun da zakiyi ne in gani"


Kul kul kul Mama ta nuna Zainab da yatsa ta ce ”wai ke Zainab kike ko mai kike dake nake magana da zaki samun baki ba da dana nake ba in kika sake mun magana tsabb zanyi kasa kasa da ke wallahi"


Kass kass Zainab din taci gaba da tauna cingum din ta ta yiwa Mama banza bayan minti daya ta ce “to naji ko shi kanshi dan naki ai sai na hana shi magana".


Hararar Dr Nura zainab tayi ta ce “dallacan dauki bokitin nan ka je ka shanya mun kaya" cikin tsawa da daga murya take maganar.


Jiki na bari Dr Nura ya dauki bokintin ya yi hanyar waje sakin baki Mama ta yi ta na kallon ikon Allah saura kiris ta fadi tayi saurin jingina da bango.


Kyallkyalewa da dariya Zainab tayi tana taunar Cingum dinta ta kalli Mama da ta bude baki ta ce “ya kika gani ?"


Mama ai kasa magana ma tayi jakarta da ta fadi garin kallon ikon Allah ta dauka ta fice ita ma.


Tarar dashi tayi ya na shanyar ta wuce ta gurin shi ya na shafa kai ya ce “Ki gaida gida a gaishe da Maryam"


A hankula Mama ta ce “Zata ji "taje ta shige motarta ta bata wuta mai gadi ya bude mata gate.


Ta na tuki mamaki duk ya cikata.


*ASALIN* *KHADEEJATU*

Asalin Mahaifin Nana Khadeejatu hausa /fulani ne dan gwarzo Alhaji Adamu Muhammad kenan mahaifiyarta kuma usulin fulanin Adamawa ce Hajiya Suwaiba Usman .



Sun hadu da juna ne ta hanyar abokantar iyayen su ne har ta kai su da yin aure su na zaune a kano unguwar dorayi



Tun bayan Aurensu Suwaiba barin ta uku ko a cikin Khadeejatu da ta samu cikin sai asibiti su ka je aka daure bakin mahaifar sannan Allah yayi da rabon Khadeejatu zata rayu ne tun daga lokacin shikenan bata sake haihuwa .



Haka khadeejatu ta ringa girma ta na wayo ba karamin shiga ran jama'a tayi ba ko wa daukarta ta yake yi masha Allah da ita asalin bafulatana


Nan zaman tare da makwabtaka tsakaninsu da gidan da ya ke kusa da gidansu wato gidansu Hafsa mahaifinta Alhaji Abdullahi Abbas suka kulla Amintaka tsakanin gidajensu su khadeejatu ma da Hafsa suka zama Amina juna har ya zamo duk inda ka ga khadeejatu za ka ga Hafsa.



A lokacin da khaddejatu ta kai 12 lokacin asalin kyawunta ya fito ita ba siririya ba ita ba yar lukuta ba tsayin ta daidai gwargwado kugunta kuwa ba karamin budewa yayi ba kamar wata babba


Tana shekara 12 Allah ya yiwa kakanta na gurin babba rasuwa bayan shekara daya Allhaji Adamu ya takura ma Inna sai ta dawo kano


Ba karamin tataburza aka sha da ita ba kafin ta dawo kullum tana manne da yar jikallenta.


Sam Khadeejatu bata da san jiki gata da tsafta da girmama na gaba da ita ga biyayya ga iyaye ga ta shagwababbiya sai dai matsalar ta bata son raini da rainin hankali.


Hafsa da khadeejatu kuwa kawance su dada karuwa yayi har a unguwa ta kai ana ce masu yan biyu ko ina su na tare.






*MORE COMMENT*
*MORE TYPING......*✍🏻✍🏻




Taku ce har kullum

_Addeejerh_ ❤️


✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.


*Muddin banga kuna commenta ba zan maida novel din na na kudi* 💁🏻‍♀️

9~10



*CIGABAN LABARI*

Yau Alhamis Khadeejatu da Hafsa sunci kwalliya da yamma su na tafiya tunda su ka taho wani saurayi a majalissa ya kafe su da ido Hafsa ta tabo Khadeejatu ta ce “Kinga waccan din chan" ta na nuna saurayin da yatsa ta ya mutse fuska ta ce “Ya kure mu da ido kamar wani maye".


Khadeejatu ta kalli Hafsa ta ce “Rabu da dan iska sai mun koya mashi hankali yan iska masu zaman kashe wando kullum sai aukin kallon mata wata rana sai idon ma ya tsiyaye ".


Hhhhhhh Hafsa ta sheke da dariya su ka tafa sai hira su ke har su ka karasa daidai Majalissar.


Wannan saurayin har su ka karaso majalissar idonsa kafe a kansu ko kiftawa ba yayi har sun dan gota shi baifi da inchi biyu ba su ka ji ya ce “Yan mata ji mana".


Sai da su ka bata wajen minti biyu irin wannan jan aji na yan mata sannan su ka juyo a tare su ka yi mashi wani irin fari da ya kusan sumar dashi.

Cikin yanga Hafsa ta kalleshi sama da kasa kana ta ce “Ya akayi ne?"


Saurayin ya sosa kanshi ya ce “Maganar bata tsaye bace ko za muje wanccan dandamalin" ya nuna wani dandamalin wani gida.


“Sai mu je din bismillah fara yin gaba muna biye da kai" cewar Khadeejatu da sai lokacin tayi magana.


Fara tafiya yayi irin shi dinnan harda wani sa hannaye a aljihu haka ya karasa kan dandamalin ya zauna.


Su ma su khadeejatu su ka zazzauna Hafsa ta kamo kunne Khadeejatu ta mata rada murmushi khadeejatu tayi .


Hafsa ce a tsakiya kusa da saurayin ta juya ta fuskance shi harda daura kafa kan daya saurayin na sai yake hakora yake kamar mai tallan closeup lol,


Hafsa na fari da ido ta ce “Ehenn muna sauraronka", sai da yayi gyaran murya kafin ya bude baki ya fara fadin “Dama nace ko........ai yawun da ya ji Hafsa ta fetsa mashi a baki shi ya dakatar da shi da maganar ya keyi bai gama dawowa hayyacin shi ba ya ji saukar ruwan sanyi a jikin shi ba ai jin sanyin ruwan nan mukut ya hadiye yawun bakinshi ba shiri.


Mai yan majalisaa za suyi in ba dariya ba dan akan idon su komai ya faru.



Da sauri su Khadeejatu su ka kwabe takalmansu su na dariya da gudu su ka arci kafar kare gudu kawai su ke basa kallon gaban su ko bayan su baram su ka banka gidan su Hafsa sai daki Umma da Mamin Hafsa fadi su ke lafiya .



Amma ina su Hafsa ko sauraransu basa yi sun baje a kasan leda sai haki su ke yi.


**********

Mama ta kalli Maryam da ta gama shiryawa ta ce “Maryam nafa ce karki kuskura kije masu gida ki na jin irin rashin mutuncin da Matar nan tayi mun ki rabu da ita kawai".


Maryam tana ta murgude murguden baki ta ce “Mama billahilzi yau dinnan sai naje gidan nai wa shegiya dan iskan duka ta taba ki ta zauna lafiya in shi Yayan ta mai dashi mijin tace to ai dani wallahi in banje Mama naci uban matar nan ba ki chanja mun suna daga Maryam ta zari jakarta da waya tayi waje ko saurarar abun da Maman zata ce bata yi ba.


Bakin gate ta fita ta fito daga layinsu ta tsallaka daya tsallaken wajen gidan man Al-ihsan domin samun Adaidaitar da za ta kaita kundila .


Ta yi wajen minti goma a wajen kafin ta samu Adaidaitar da ta dauketa.


A dai-dai wani madaidaicin gida mai Adaidaitar ya sauketa ta bashi hakkinshi.


Ta na kwankwasawa gate din mai gadin ya bude mata gidan suka gaisa kana ta nufi hanyar falon ta bude jakarta ta ciro cingum ta jefa shi a baki ta kara turo daurin ta gaba.


Bam ta banka kofar falon ta na taunar cingum kass kass ta shigo falon Zainab dake kwance a kan doguwa kujera ta na chatting zumbur ta mike ta na mamakin wane mahaukacin ne wannan.


Maryam ta gani tsaye ta na ta jijjige jijjigen jiki sai kasss kass ta ke da cingum.


Mtswww Zainab taja tsaki shekeke ta kalli Maryam ta ce “ke wai wace irin dabba ce ?"

Cikin masifa Maryam ta ce “Ai ke ce babbar dabba jaka wacce bata san matsayin iyaye ba tinkiya kawai kinga kudi kina daddagawa mutane kai kina hura wa mutane hanci mai kama da gajeren wando".


“Kutumar uba!!" cewar Zainab ka na ta ce “Mara kunya har ni zaki zo gida na ki na Zagi na dan baki da mutunci".


Maryam ta harere ta ce “Ke kike ta gida mai wannan uhumm bari dai nayi shiru tunda ko gidan ubanki ai bai kai haka ba dole ki takama da wannan da kika samu shasha kawai"


Zainab ta kalle ta a gadare ta ce “Banza mara tarbiya yar mace ita kanta mahaifiyar taku ba ishasshen tarbiya gare ta ba ballantana kuma ta baku daga ke har uwar taki baku ishe......."tass Maryam ta dauke ta da wani gigitaccen mari bata bari ta dawo daga hayyacin ta ba tass ta sake marinta a dayan kunci.


Da sauri Zainab ta dafe kuncita duka biyun ta na zazzare ido bata taba tsanmanin Maryam za ta iya marin ta ba.


Da sauri Zainab din ta nufi kitchen ai kafin ta karasa Maryam ta cire high hill din dake kafarta ta sai ci keyar Zainab ji kake kwal ta kwala mata a keya da sauri Zainab ta dafe keyar tata.

Maryam na ganin haka ta nufe ta ta daidaici kafar Zainab ji kake raff ta kwada ta da kasa ta hau kan ruwan cikin ta.


Ihu Zainab take ta kururuwa da sumbatu ta na fadin “Malam Ayuba kazo ka taimaka mun zata kashe ni wayyo Allah nashiga uku!!" Maryam kuwa sai nausarta takeyi duk ta fasa mata baki.


Sai da ta mata likis har goshin ta sai da ya kumbura cikin masifa ta na haki ta na girgiza ta kalli Zainab din shekeke ta na nuna ta da yatsa ta ce “Wallahi tallahi wannan ma kadan kika gani ki sake kara Zagin mun mahaifiya ki ga yadda zan maki".


Zainab ai baki ya mutu bata da ta cewa sai kuka ta ke yi .

Maryam ta dau jakarta ta gyara yafa mayafin ta duk a lokacin Zainab ba ta mike ba ta na ta rusgar kuka.


Kafin Maryam ta fita sai da ta kara yin ball da Zainab din kafin ta fice.

Duk abin nan da ya faru Dr Nura baya nan.



*Da daddare*

Abba ne yasa su Khadeejatu a gaba ya na masu fada tun da ya ji labarin mai su ka yiwa wannan saurayin.

Kallon su Abba yayi ya girgiza kanshi ya ce “Mai yasa ne bakwa ji ne kullum sai an kawo karar ku ne kuna girma amma sam halayyar ku kamar ta kananan yara dan Allah yayan Albarka ku gyara".

A tare su ka ce “Insha Allah Baba zamu gyara".

Abba ya ce “Allah yasa haka" ya cigaba da yi masu Nasiha.............🖊️✍🏻







*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ............✍🏻✍🏻








Ta kuce har kullum

_Addeejerh❤️_



✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.



11~12
*Washegari*

_Karfe 4:30 pm_

“Uhumm yanzu kai Nura tsabar baka da kunya dan Maryam taje gidanka sunyi danbe da matarka shine bado bado ka dauko ta ko uban mai zan maku duk da ita ma Maryam din bata kyauta ba gaskiya duk ta bani labarin mai ya faru" Mama ce ke maganar cikin kunar rai.


Dr Nura ya shafa kanshi ya ce “Amma Mama kalli fa yadda tayi mata jini da majina har hakorin ta sai da ya cire".


Maryam kuwa sai aikawa da Zainab harara take yi.


Mama kuri tayi ta zubawa Dr Nura ido ta ma rasa mai zata ce mashi duk ya cikata da mamaki chan ta ce “Amma Nura na tambaye ka yanzu kai rabon ka da zuwa gidan nan kazo ka ga lafiyar mu ehh fada mun?"


Sunkuyar da kanshi Nura yayi a hankula ya ce “kwana tara"


Mama ta kalleshi ta ce “Gwara da ka bude baki ka fadi kwana nawa rabonka da zuwa yanzu kai a ganin ka hakan da kayi ya dace?


Da sauri Nura ya girgiza kanshi ya ma kasa hada ido da Maman.


Mama ta bude bakin kenan zata yi magana..Zainab ta katse cikin rashin kunya ta na ya mutsa fuska ta ce “Ni kinga kinzo ki na cika mu da zance banxa kin kasa daukar mataki kina tsoron yaran ki bakya iya masu magana"


Mama ta rufe idonta sai zazzaga masifa take a tsawace ta ce “Ku tashi ku barmun gida daga ke har Nuran kafin in bude idona".


Zainab ta kalli Mama a wulakance tace “Aikin banza lalle a duwawu "wuce kai kuma mu ma mu tafi ta juya gurin Maryam ta nuna ta da yatsa ta ce “Wallahi ke kuma haduwar mu baza tai kyau ba, ba a banza kika taba ni ba hmmm".


Nura na tsaye bai taba ganin mama irin haka ba wata irin tsawa Zainab ta daka mashi ta na fadin “Au ba

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment