Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaka wuce ba?"


Jiki na bari Nura ya fice Sai da Zaimab ta harari Maryam tare da yin kwafa sannan ta fita...


**********

“Kinji Abba da wani zance dazu ya kira Umma wai dazu da ya fito sun hadi da wani saurayi wai shi nan ya na sona wai dan haka da daddare zaizo" cewar Khadeejatu ta na dariya.


Hafsa ta kyalkyale da dariya ta ce “Jar uba kaji Abba da wani zance wai su nufin su da mun gama secondary za su aurar da mu ne".


Khadeejatu ta ce ”Da alamu dai kinsan yanzu ya zamuyi wa wanchan dan iskan kuwa da zaizo?".


Da sauri Hafsa tace “A'a sai kin fada dai "

Khaddejatu ta ce “Matso kiji" da sauri Hafsa ta matso kamo kunnenta ta Khadeejatu tayi ta mata magana ko mai tace mata ohooo.


*Da daddare*

Umma ce tasa Khadeejatu dole sai ta gyara fuskarta.


Sai chuno baki Khadeejatu take yi powder da lipstick kawai tasa ta zumbula hijabin ta kalar ruwan toka .


Tazo fita umma ta ce “Toh a dawo lafiya dan Allah kar ki mashi halin na san" ki ciki ciki Khadejatu ta ce ”Toh" ta fice.


Ya na tsaye a kofar gidan a jikin babur dinshi besfa tunda ta fito ya kura mata ido .


Duk da duhu amma ya kula da yadda Khadeejatu ke galla mashi harara haka dai ya share ta tana zuwa gurinshi taja burki ta tsaya bata ce mashi ko ci kanka ba.


Saurayin yace “Khadeejatu!!" ta mashi banza kamar da dutse ya ke magana ita kuma mamaki ta ke ya akayi yasan sunan ta.

Kamar yasan mai take tunani ya gyara tsayuwar shi ya ce “Nasan mamaki kike yadda na san sunanki ko? Kana ya ce “Hakan ba abun mamaki ba ne akan kasan sunan masosiyar ka saboda son da nake maki ban fara sanar maki ba sai da naje na nemi izini gurin Abba har ya aminta na rinka zuaa gurin ki zance nasan ya fada maki komai ko?".

Nan ma dai banza ta mashi amma duk da banzan da ta mashi bai fasa magana ba ya ce “Na cika ki da surutu ban fada maki suna ba , suna na Bashir da fatan na samu karbuwa a gurin wannan sarauniyar matan?"


“Kaga malam dakata ni ka ishe ni da surutu sai kace wanda ya hadiyi battery in labari kake so ai akwai gidajen radio da yawa zaka iya zuwa daya daga ciki ka basu labarin" cewar khadeejatu ta na galla mashi harara.


Kafin ya ce komai sai ga Hafsa ta karaso gunsu bakinta dauke da Sallama hannunta rike da tray mai dauke da jug da cup Bashir ya amsa mata ya na murmushi .


Hafsa ma murmushi tayi ta ce ”Sannun ka da zuwa bakonmu ga ruwa kasha"ta sunkuya ta zuba mashi ruwa ta mika mai ya karba yayi murmushi ya ce “Nagode sosai yar uwa ko zanso sanin sunanki ?".


Hafsa ta kalleshi ta ce “Sunana Hafsa"


Ya ce “Masha Allah suna mai dadi da fatan zaki tayani shawo kan gimbiya?" ya na murmushi harda shafa gemun shi.

“Insha Allah karka damu yanzu dai kasha ruwa" ta na yi ta na wani irin makirin murmushi


Ya na kurbar ruwa yayi sauri ya furzar dashi ya na fito da harshe da kyar ya iya furta “wannan....ai....ruwan.......zafi ne.....da...gishiri"


Kyallkyalewa da dariya su Khadeejatu su ka yi su na tafawa.


Khadeejatu ta kalleshi sai futo daa harshe yake kamar karen da ya ga kashi lolx, kwafa tayi ta ce “ka ma sake dawowa kofar gidannan hmmm" ta sheke da dariya su na dariya su ka shige gidansu Khadeejatu su na murmushi sun barshi kim a tsaye yayi suman tsaye..............









*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ..........









*Ta kuce har kullum* _Addeejerh_ ❤️



✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND* *NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.



13~14

Su na karasawa soro su ka sheke da wata iriyar dariya Khadeejatu dan dariya har kasa ta kai tana rike ciki.


Kallon Hafsa Khadeejatu tayi ta ce “Zo muje waje muga ko ya ja wannan mashin nashi roba roba”


Mikewa Khadeejatu tayi su ka leka har ya tafi (nikam nace wannan azaba.com ba dole ya fece ba lolx).



Ai wata yar iskar dariya Hafsa tayi ta kalli khadeejatu ta ce ”Nj wallahi mamaki ya bani shi ko kunya ya wani taho dugwui dugwui dashi jallo jallo dashi kamar iska zata dauke shi".


Khadeejatu ta ce ”Rabu da karamin mara kunya ai gwara da muka yi maganin shi gobe ya sake zuwa dan malafar uba"ta sheke da dariya


Abba da ya dawo kenan ya gansu su na dariya ya ce “Ku kuma lafiya kuke dariya?".


Tsagaitawa da dariya sukai a tare su ka ce “Lafiya sannu da dawowa Abba"


“Yauwa yayan Albarka har angama hirar ya tafi ne?"Abba ya tambaya.


Khadeejatu ta ce “Ehh Abba yanzu ya tafi "


“To mu shiga ciki sai ku bani labari yayan nawa an girma Allah yasa dai ba kuyi masa halin ba?” ya tambayesu lokacin su na shiga gida Khadeejatu ta ce “A'a Abba hira muka yi fah".



Umma na ganin su ta ce ”Ahhh ya na ganku tare kardai harta gama hirar ?" da sauri ta ce “Yi hakuri Abban khadija sannu da zuwa na cika ka da surutu".


Abba yayi murmushi yace “Yauwa sannun ki da gida shiru yau ko ?inna ta na kauye"


“Yauwa Abban khadija wallahi kuwa shiru ji nayi kamar ta shekara" Umma ta amsa tana shimfida tabarma.



Zama Abba yayi ya na dariya su khadeejatu suka zagaye shi Umma ta debo ruwan tulu mai sanyi ta kawowa Abba ita ma ta samu guri ta zauna.


Umma ta kalli su Hafsa ta hararesu ta ce “Anje anyi halinko kudai Allah ya shirya"


Abba yayi saurin katseta ta hanyar fadin ”Aa yau fa basu yi ba sunce"yana murmushi.


Umma ta ce “Hmmm Malam kenan yaran nan ne za a tashi garin Allah ta'ala a kai dare basu yi wani abun ba na janyo magana Allah dai ya kyauta".


A tare su khadeejatu su ka chuno baki wani irin zumburo baki Khadeejatu tayi kamar zata yiwa jaba kisss hhhhhhhh lolx, ta ce “Wai wai wai Umma kullum kice bamu ji kuma ni ba abun da na masa hira ma muka yi ko Hafsa?"


Hafsa na murmushi tace Ehh mana kwatsam Khadeejatu ta ce “Gashi Umma ya iya Kalamai ......”


Ko karasawa batai ba Umma ta jefo mata omon da aka siyo mata ta harare Khadeejatu ta ce ”Dan kin maidani kakarki ni zaki fadawa haka?".


Abba yayi dariya daki su Khadeejatu suka shige.


Bayan sun shiga Umma tayi murmushi ta ce “wallahi sam yayan zamanin nan basu da kunya Abban Khadeeja........"


**********

*Bayan kwana biyu*

A makaranta an fito break su Khadeejatu su na hira su kadai a ajin kowa ya futa harkar gabanshi sai ga wata daliba za tayi sa'ar su tana fadin “Khadeejatu kun san mai kuwa"


Hafsa cikin zumudi ta ce “A'a Salma shaka mana ai ke ba'a rasa story a gurinki jourailist din makarantar mu".


Wata bazawarar dariya Salma tayi ta ce “Haka yake fadi ki kara fada".


Katse ta Khadeejatu tayi tana fadin “Dallah ki fada mana kin tsaya ja mana
rai".

Salma ta ce “Nawa to zaku bani?in shaka maku" da sauri Khadeejatu ta dauko festo din da ta siya a jaka ta mika ma Salma.


Karba Salma tayi ta ce “Yanzu naji batu, toh in fada maku fada ake a field yan SS2c".


Cikin hada baki su khadeejatu su na murmushi su ka ce ”Dagaske?"


Ai kafin ta basu Amsa suka arci kafar kare sai field .


Wata ce take narkar dayar dalibai duk an zagaye su ba wanda yayi kokarin raba su kusa kai su Hafsa suka yi.


Ai su Khadeejatu bokitin mopping su ka dauko da kara suka dawo tsakiyar filin suka fara kida suna cewa a casu a casu a casu bame rabaku a zamanin nan na yanzu in ka raba ace kayi.....kida suke kamar yan bodin hhhhhhh



Nan masu fada ko wacce Zuciyarta sai tafasa take kidan na tsuma su .


Khadeejatu ce ta kalli wacce bata da karfin ta ce“ Jamila in shigar maki?" Jamila ba bakin magana ta daga mata kaii nan Khadeejatu ta shiga fadan..............



Kuyi manage banjin dadi ne







*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* .......









Taku ce har kullum
*Addeejerh* ❤️


✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND* *NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.



15~16



Khadeejatu ta ringa likidar yar mutane sai shegen karfin tsiya har wasu yan makarantar su na cewa kodai tana da Aljanu.


Sai da tayiwa yarinya dan bura uban duka ta hada mata jini da majina


Yan team Jamila sai tafawa khadeejatu suke yi sai kara fasa mata kai su ke.


Inda Jamila take tsaye nan Khadeejatu taje ta mika mata hannu ba tare da tace mata komai ba Jamila hannu na bari ta ciro naira dari a Aljihun wando ta mikawa Khadeejatu dan tasan halinta yanzu in ba ta bata wani abun ba ita ma sai ta likide ta .


Khadeejatu ta kama hannun Hafsa suka bar field din.

**********


“Mama dan Allah ki cire damuwar wanchan yar iskar matar a ranki kina kallo fa likita yace jinin ki ya hau sosai fah" cewar Maryam .


Mama ce ta bude idanuwanta da sukai mata nauyi ta ce ”Maryam ba zaki gane bane kiga yanzu kwana nawa banda lafiya amma ko yazo dubani ".


“Uhumm Mama nifa ina da zargi akan wanchan shegiyar matar dan wallahi ba haka halin Yaya Nura yake ba"


Lallabawa Mama tayi tashi zaune ta jingina a jikin Allon gadon ta kalli Maryam ta ce ”Wane irin Zargi kikeyi Maryam?".


**********

”Haba ku kuwa Yayan nan yaushe zaku shiryu ne kuyi hankali dazu muna zaune da Ummanku Hajiya Kubra tazo da yarta duk fuskarta a kumbure tana ta masifa yarinyar tace wai haka kawai suna fada Khadeejatu tazo ta shiga fadan shine tawa yarta jini da majina" cikin fada Mamin Hafsa take maganar.


Khadeejatu ce ta ce ”Toh....toh" Mami ta ce “Dallah chan ku rufen baki ku bace mun da gani tun kafin na sassaba mu ku wallahi Allah".


Su na tutturo baki gaba su ka tashi.


************


Tass tasss tasss kakeji Maryam ce ta fallawa Zainab mari zafafa guda uku da har sai da wayar dake hannun Zainab ta fadi a kasa .



Tasss ta sake faula mata wani marin wani irin gigitaccen ihu Zainab ta saki tana kuka



Maryam ta nuna Zainab da hannu tana hararar ta ta ce “Kinyi na farko kin yi na biyu da har zaki sake tunkarar uwata da nufin rashin kunya nasan baki taba tunanin zanzo ba to wallahi kika kuskura kika yi na uku wallahi sai na maki dan iskan duka da sai dai azo a samu gawar ki in kunne yaji jiki ya tsira".



Ta na gama fadar abunda zata fada tasa kai ta fice.



Gwalolo Zainab ta bita da kallo .



______________



*BAYAN SHEKARA BIYU*


A cikin wannan shekara biyun nan ne abubuwa da yawa sun faru su Khadeejatu sun gama makarantar sakandiri a halin yanzu an kawo kudin auren Khadeejatu in da zata auri wani Yusuf wanda suka hadu dashi a gidan bikin yar uwarsu Hafsa yayan Amaryar ne cousin gurin Hafsa dan yayar Mamin ta.


“Hafsa dan Allah ki taya ni zabar kayan da zansa in Yaya Yusuf zai zo anjima duk na hargitsa kaya na"


“Kinga kisa wanchan leshin namu brown mai ratsin orange" cewar Hafsa tana nuna mata leshin da Hannu.


Khadeejatu ta durkusa ta dauka leshin fuskarta dauke ta murmushi ta kalli Hafsa tace ”Wallahi yayi ni nama manta dashi ke yanzu wanne zaki saka?, kinsan yace zai kaimu shopping"


Hafsa ta ce “Nima bari kawai nasa irin shi muyi anko"


Khadeejatu ta ce “Yauwa haka ko za'ayi"


*************


Khadeejatu ce a kwance wajen sha biyu na dare bata yi bacci ba Hafsa kuwa tuni ta wuce Gusau lol,


Khadeejatu idonta kirr akan cilin din dakinsu ta na ta tunanin masoyinta Yusuf.


Wayarta ce da Yusuf din ya siya musu ta fara ringing da sauri ta duba taga ansa Yaya Yusuf har ta katse bata daga ba ita nan wai irin jan ajin nan na yanmata lol,


Wani kiran ne ya sake shigowa sai a lokacin ta daga chan yusuf ya ce


“Assalamu Alaikum ya ma'abociyar kyau da cikar kamala da fatan na same ki lafiya?"


Wani yarrr khadeejatu taji a jikinta duk tsigar jikinta tashi ta rasa mai yasa duk sanda ya mata magana take jin hakan.



Sun dau wani guntun lokaci ba wanda yace da dan uwanshi ci kanka
Chan Yusuf ya katse shiru ta hanyar cewa “Naji kinyi shiru Nanata"



Sai da Khadeejatu tayi wata sanyayyar ajiyar zuciya sannan ta amsa “Wa'alaikums salam Ya yusuf lafiya kalau ina fatan haka kaima".



*************


“Dan Allah Safiyya kiyi sauri kizo ki taimakan wani irin nake ji pls kozo na rage zafi" Zainab ke maganar tana wani irin nishi .


Daga ita sai guntuwar rigar bacci hannunta na ta yawo a kan dukiyar fulaninta da ko bra bata sa ba.



( waiyazubillah Allah ka kare mu daga sharri aika zunubi , Allah ka kare mana gabannin mu daga aikata Alfasha Amin ya rabbil Alamin.)



Ba ayi ko minti ishirin ba sai ga Saffiya ta karaso Zainab na ganinta tayi sauri ta kamo ta , taja ta daki nan ta tsige rigar barcin jikinta.


Ta cirewa Safiyya kayanta gaba daya nan su ka fara aikata Alfasha waiyazubillah..............🖊️✍🏻









*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ...........✍🏻✍🏻








Taku ce har kullum
_Addeejerh❤️_


✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA* 👩‍❤️‍👨

*AND NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na *KHADEEJATU* Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.



17~18

Su na gama aikata badalar su ko wanka ba suyi ba su ka dafa indomie su ka baje su ka ci su ka bingire bacci (waiyazubillah zama da janaba).


*************

Hafsa ce ta shigo dakin ta tana fadin “Dan Allah Khadeejatu ki zo muje chemist a maki Allura kinki gashi jikin ki yayi......"


Abun da ta gani shi ya makalar da maganar da take da karfi ta kwalla kara tana fadin “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun".


Mami ce ta shigo da sauri har ta na tuntube gurin Khadeejatu ta nufa ta fara jijjigata tana fadin “Innalillahi ki tashi Khadeejatu" amma ina ko motsi bata yi.



Da gudu Hafsa ta fita ba ko dan kwali a kanta baram ta fada gidansu Khadeejatu ba sallama ta fara kiran Umma!! Umma!! Umma!!.


Da sauri Umma ta fito a hargitse ta kalli Hafsa ta ce “Lafiya zaki zo kina mun kiran mafarauta? kinga ma yadda kika fito".


Kama Hannun Mami Hafsa tayi jikinta sai kyarma yake cikin rawar baki ta ce ”Khadeejatu!! Khadeejatu!! Umma" lu tayi kamar zata fadi.


Da sauri umma ta kamo ta tana jijjiga ta tace “Mai ya faru da Khadeejatu din?".

Kasa magana Hafsa tayi nuna hanyar futa take yi kamata Umma tayi ta rufe gidan su ka fice sai gidan su Hafsa.


Su na zuwa su ka tarar Mamin sai yayyafawa Khadeejatu ruwa take bata farfado ba .


Da sauri Umma ta karasa gurin Khadeejatu tana ta salati ( ita ba ta yarda da da abun yan fari ba)dora kan Khadeejatu tayi a cinyarta ta cire mata hijab din da tayi sallah ta zuge mata zip din rigarta ta fara mata fiffita da hijabin amma ina.


Mami ta kalli Hafsa da ke ta kuka ta ce “Yi maza ki samo mana adaidaita kawai mu wuce asibiti".

Da sauri taje ta samo mai adaidaitar har kofar gida su Umma suka dauko Khadeejatu.


Hafsa tana ta kuka haka da dauko hijabi tasa ta dau wayarta ta rufo gidan su ka wuce Asibitin.



Su na karasawa asibitin da sauri likitocin sun ka karbe ta gani halin da take ciki.


Hafsa sai zurga take ta na kuka tafiya tayi tafiya wajen awa daya sai a lokacin lokitocin su ka fito.


Da sauri su Mami su ka nufe likitan a tare su ka hada baki wajen fadin ”Doctor ya ake ciki ta farfado?".


Doctorn ya kallesu ya ce “Ku buyo ni Office" ya nufi Office ya na sharce gumin fuskar shi da hankachief Dr Musab kenan.


Su na shiga Office din su ka zazzauna.


Kallon su yayi sai da ya numfasa sannan ya ce “Hajiya sai dai hakuri"


Da sauri Hafsa ta mike tana fadin ”Innalillahi wain'na ilaihir rajiun ta mutu ko na shiga uku" ta kwallara kara.


Kamo ta Umma tayi ta zaunar .

Likitan ya ce ”A'a yan mata ba haka nake ba Zazzabi ne take mai zafin gaske da har yasa ta suma sai kuma Ulcer da ya dan kamata bawani matsala amma da ta farka amai zata yi saboda mun mata wata Allura ".


Mami ta ce “Tom Doctor mungode Allah saka da Alkhairi"


Doctor ya na cire glass din idon shi ya ce “Amin Allah bata lafiya"


“Amin Amin mungode" sai a lokacin Umma tayi magana


Sallama su kai mashi su ka fita dakin da aka kwantar da ita su ka shiga.


Da sauri Hafsa ta karasa jikin gadon ta kama hannun Khadeejatu fuskarta tayi fayau kamar wacce ta shekara tana ciwo da sauri tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo mata.


**********

Hafsa ce ta fito daga toilet Ya yusuf ta gani su Umma sun tafi gida ya na zaune a gefen Khadeejatu dake ta baccin ta.


Karasowo gurin shi Hafsa tayi ta ce “Ya yusuf sannu da zuwa"


Yusuf ya kalleta yayi murmushi ya ce “Lafiya kalau kanwata ya mai jikin?"

Hafsa ta ce “Da sauki ta zauna a gefen gadon gurin kafafun Khadeejatu"


Yusuf ya ce “Allah kara sauki"

Hafsa ta ce ”Amin Amin".



_Bayan minti goma_


Khadeejatu ta fara motsi da sauri Hafsa ta karasa gurinta ta na mata sannu daga kai Khaddejatu tayi ta na bin Hafsa da kallo.


Taimaka mata tayi ta jingina da filo a hankalin Khadeejatu ta bude baki kenan zatai magana sai ga amai.


Da sauri Hafsa ta kamata har saida ta gama aman wani koren amai tayi da sauri Hafsa taje kiran doctorn dan ya Yusuf ya fita karbo masu abinci karta farka ba abun da zata ci .


Doctorn ne yazo ya ga Khadeejatun ya yi examining dinta ya fita wata nurse ce ta taimakawa Hafsa suka gyara ta......................✍🏻🖊️









*MORE COMMENT*
*MORE TYPING* ...............✍🏻✍🏻




_Sanarwa_

Sabon littafi na da zan fara nan gaba zai zama na kudi sunanshi *KUNCIN RAYUWA*




Taku ce har kullum
Addeejerh


09012671608

✨✨✨✨✨✨✨

*KHADEEJATU*

✨✨✨✨✨✨✨



*LABARI/RUBUTAWA*



*KHADIJA ADAM* *IDRIS*
( _Shalelen kainuwa_ )


*MARUBUCIYAR*



👩‍❤️‍👨 *FANSAN RAN* *MAHAIFANA👩‍❤️‍👨*

*AND* *NOW*

✨✨✨✨✨
*KHADEEJATU*
✨✨✨✨✨


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

ALHAMDULILLAH!!!Allah na gode ma da ka bani ikon rubuta littafin nan na KHADEEJATU Allah ka sa na rubuta abun da zai amfani Alummar musulmai .




Sadaukarwa

Na sadaukar da daukacin littafin nan gareku mahaifina da mahaifiyata *Hajiya Halima Adamu* *Muhammad* da *Alhaji* *Adamu Idris* Allah kara lafiya da nisan kwana

Amin.




19~20

Rufe idanuwanta Khadeejatu tayi ta koma ta kwanta tana ta sakin ajiyar zuciya.



Kiiiiii Ya yusuf ya turo kofar ya shigo hannunsa rike da ledoji yayi sallama Hafsa ce ta amsa.


Shiko tunda ya shigo idonsa na kan Khadeejatu.



Karasawa gurin gadon yayi ya zauna akan kujerar dake gefe yana kallon Khadeejatu ya ce “Hafsa " ta ce “Na'am" ya ce ”Zo ki karba ki ajiye har yanzu bata farka ba ne?" ya kalli Hafsa.


Hafsa bayan ta ajiye kayan ta ce “A'a ta tashi, har aman ma tayi wani irin kore dashi"



Khadeejatu ta da take saurararsu ta dallawa Hafsa harara.


Hafsa ma galla mata hararar tayi ta ce ”Uwar masifa baki ma da lafiya sai kinyi masifa"


“Kaiii ya ishe ni ko ina sai kun nuna halin ku ke Hafsa kamar bakye akace kina ta kuka ba” Yusuf ne yake maganar turo baki Hafsan tayi taje chan kan couch ta zauna murmushi kawai Yusuf yayi ya maida duban shi gurin khadeejatu ita ma ta juyar da kanta tana kallon bango.


Dariya ya kyalkyale da danshi dariya suke bashi cikin dariya ya ce “Sweetheart ba ma magana?"


Khadeejatu ta ce ”Uhumm" yayi murmushi ya ce “Shikenan bari na tashi na tafi tunda ba'a son gani na".


Da sauri khadeejatu ta juyo ta na kallonshi fuskarta dauke da murmushi ta ce “Ya Yusuf ina wuni "


Wani irin niimtaccen kallo yayi mata mai nuna shaukin so a tsakanin masoya ya ce “Lafiya kalau ya jikin?"


A hankali khadeejatu ta bude dan mitsitsin bakinta mai matukar kyau a hankali ta ce “Da sauki".


Yusuf ya shafa sumar kanshi ya ce “Masha Allah haka akeso tashi ki ci abinci"


Kallon Hafsa yayi dake chatting ya ce “Hafsa zoki hada mata tea ga kayan tea nan na kawo ga chips nan sai ku ci akwai fried rice ma".


Cikin nutsuwa Hafsaa ta ce “Toh Yaya Yusuf ( wannan tarbiyar su Mami ne sam basa raina na gaba dasu) ta na tashi.


Tea mai kauri ta hadawa Khadeejatu ta mika mata ta zuba chips din

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment