Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


HALIN RAYUWA

1

NA

07035586299

HAJ. HAFSAT C. SODANGI

(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)

1



Hakkin Mallaka [m]
Hakkin Mallakar littafin na Haj. Hafsat C. Sodangi ne

GODIYA
Godiyata har kullum ga Allah take Subhanahu
ta'ala mai kowa mai komai, Makadaici, Mahalicci wanda a ke nufa da dukkan bukatu gwani mai hikima wanda yayi halittarsa bisa tsari na aure wato mace da namiji.
Tsira da aminci su kara tabbata ga cikamakin
Annabawa, shugaban Manzanni Annabin karshe
Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da
wadanda suka bi ma tafarkinsa na gaskiya har zuwa
ranar karshe, wato ranar rarrabewa tsakanin karya da
gaskiya (AIkiyama), Ubangiji yasa mu dace.
Har wayau ina mika godiyata ta musamman ga
daukacin makaranta littattafaee cikin kasa da waje,
Ubangiji ya saka da alheri ya kuma kara karfafa
zumuncin da ke tsakaninmu.

Na gode, Haj. Hafsat C. Sodangi
6/7/1434

2


GODIYA

Godiya mai dumbin yawa gare ki.
Rabi'atu Faruk Jauro
(Ministry of Commerce and Industry Yola,
Adamawa State)

Da
Zainab Sunusi Kofar Gabas Danbatta
Zainab Abarshi Yawuri

GAISUWA
Gaisuwar littafin naka ne Muh'd. Kabir Sodangi
(A.T.B.U BAUCH)

3

LITTATTAFAN SODANGI:
Uwar Miji
Naga Ta Kaina
Rabon Kwado...
Cikar AIkawari
Wayyo Duniya
Yi wa Wani...
Abu Naka...
Mata Ma su Duniya
Nufin Allah
Kifi Na Ganinka..
Daga Kin Gaskiya..
Da Kamar Wuya..
Mai Uwa.
Duk Daya..
Mata Da Kicin Dinsu
Wacece Ni?
Wata Fuskar..
Mijin Ta ce
Garin Banza...
Ga ni Gare ka
Biyan Bukatar Rai
Shamaki
Hattara
Mata Masu Duniya
Kyautata
Ayi Dai Mu Gani.
Tabbataccen Al'amari

4

HALIN RAYUWA 2
Washegari da safe gaba daya mutanen gidan
kowa a cikin natsuwarsbi yake, in ban da
Babah Lantana da ke ta faman zirga-zirga
tana fadin maganganu kamar yanda dama al' adarta
take in har wani abu ya 6ata mata rai.
Haka kawai a cizan mun yarinya sannan wani
Rato ya shigo har cikin gida ya dakar min yaro, to
wane irin rashin yanci ne wannan? Ai kayi
hukuncin da za ka yikawai in gani. Lalle ne kuma
kayi hukunci me tsanani don in ba haka ba kam...
Sai tayi kwafa tare da fadin "Hanya ratatata nuna
alamar abinda zai farun ba karamin al'amari ba ne.
Koda Babah Lantana bata furta irin wadannan
kalaman ba zan kasance ne a cikin natsuwata sosai
don na saba jinta tana bada umarnin a rama cizo ko
da kuwa bayan shekara guda ne, to balle ni da nayi
cizo jiya, cizon kuma ya haifar da sakamako mai
tsanani don daga Asabe har SaHau babu wanda bai
samu kanshi cikin wani hali ba matsananci.
Asabe dai tana kwance tana fama da matsanancin
zazzabi, Sallau kuwa bai iya rufa bakinshi ya daina
kurma ihun da yake kurmawa ba, sai da aka kira
Mallam Bahago yazo ya gyara mishi targaden da aka
yi mishia kafada.
Don haka sanin a nayi Babana yana cikin gidan
nan dai shi ne abinda ya zaunar dani a cikinsh da

5

kuma ganin Asabe a kwance tana fama da kanta
nasan a haka ba za ta ce zata rarume ni don ta rama
cizon da nayi matan ba, amma duk da haka ina ganin
Babana ya dauki kwandon tumatirinshi da nufin fita.
Nima zan yunkura in bar musu gidan don ba zai
viFu in 2auna tare da su ba tunda nasan zama da su
din ba zai haifar min da da mai ido ba.
Ina cikin wannai tunanin ne na bango Babana
tsaye a tsakar gida rike da kwandon tumatirinshi a
hannu alamar zai fita kenan nayi maza na jawo
gyalena kusa da ni, don yana fita in bi bayanshi sai
kawai naji ya ce ing Yaacuwuna take?
Nayi maza na ce Gani nan Baba, na fadi daidai
lokacin da na tsuguna a gebanshi, karki sake li fita
daga gidan nan. Gabana yayi mummunan faduwa,
"Kin ji na gaya miki ko ba kiji ba?" cikin sanyin jiki
na ce mishi naji Baba.
Na mike tsaye jikina a sanyaye na koma dakin na
Zuna na jawo littafina ns karatu ina dubawa sai dai
gaba daya hankalina ba a kan shi ya ke ba.
"Kai Sallau!" Sallau ya yunkura ya fito gani
Baba, shirya ka bar min gida ka koma inda dama ka
ke, tunda ka zo kana yi min fada a gida shima
wancan din na aika a gayawa Babanshi ya gaya
mishi kar ya sake shigo min cikin gidana."
gama fadin hakan yasa kai ya wuce zai tafi.
6

Babah Lantana ta bishi da kallo irin na takaici
tare da fadin "A hau, ahau wannan shi ne hukuncin
naka? Taja wani mummunan tsaki ta juya taga
Sallau da ke tafiya da kyar yana rike da ledar
kayanshi a hannu zai bar gidan don cika umarnin da
maigidan ya ba shi.
Sai kawai naji ta daka mishi tsawa "Ina za ka da
wannan jikin naka? Maza maida ledar nan kayi
kwanciyarka ka huta, ai ko za ka bar gidan nan sai
bayan kun rama abinda a ka yi muku tukuna.
Cikina ya badasautin kulululuu! Don nasan me
maganar tata ta ke nufi
Sallau ya koma daki yayi kwanciyarshi yayinda
lia ma ta koma kan hidimominta da maganganun da
take ta yi.
Ana cikin haka ne naji wata irin murya tayi
sallama a bakin kofar shigowa tsakar gidanmu.
Muryar ta mata amma abin mamakın shi ne da sunan
maza naji Babah Lantana ta kira bakuwar.
"Nalami ne kuma har cikin gida ba za ka tsaya
daga waje ka ce ayi maka iso ba? yayi 'yar shewa
tare da 'yar dariya kafin ya ce "In ba kiyi min haka
ba ai ba ai ba ki cika 'yar halak ba, ai ba zan ce kin
amsa sunanki na Butulu' ba ko ba sunan da dama
yan gidanku suke kiranki ke nan ba? Butulu ai
dama kazo ne har gidan mijina ka ci mutuncina?
7

Yayi maza ya ce "A'a ko kadan ai darajar aure
ya shige haka komai iya shegenka in har ka samu ka
shiga karkashin inuwarshi to ka zama mai mutunci
sai a mutuntaka saboda darajar shi, don haka ba zan
ci mutuncinki a gidan mijinki ba.
To tunda ka fadi haka da bakinka muje daga
waje, ya ce a'a nan kuma daya a nan din nan zaan
zauna bau ce zan shiga dakinki ba balle kiyi tunanin
zan hau kan gadonki in kina tsoron kar mijinki ya
shigo ya ganin ne babu komai yana shigowa sai in
gyara zama in maida kaina kanin Babanki in kuma
ki ka ce za kiyi min iya shege to kema kin san ni
babanki ne a nan ma.
Ina iya zuwa har wurin 7aman nasu in yi koma1,
ai ta can na biyo an nuna min shi,don haka dauko
tabarma kawai ki shimfida min."
Ta kawo tabarmar tana shimiidawa yayinda ni
kuma zuciyata ke ta faman kai-kawo a tambayata
wane irin mutum ne wannan? Na yunkura na matsa
na kebe ta matsin kyauren dakin namu mutum har
mutum yasha babbar riga har da hula zanna sai dai
kalamanshi.
"Ashe har mazaunai ne da ke haka? yayi
tambayar daidai ya kaiwa mazaunan nata duka
gabana ya sake faduwa, tayi maza ta kars daure
fuska kafin Nalami ba ka da mutunci ya gyad zama

8
kan tabarmar ya ce, Eh komai ma kina iya gaya min
ni na zo. Ta ce to ka tafi mana ko ni na kira ka?
Ya kalleta a'a ba ke ba ce ai kin samu wurin
zama sai cin mutuncin Jama'a ki ke yi ja' ira kawai
mara tuna baya, kai bebi baki da tuna alheri.
"Dakata ka ji Nalami, na daina amsa wannan
sunan duk wani abu makaman cin wannan da ka sani
na daina shi, mijina mai mutunci ne. "
Yayi maza ya ce "Gaskiya kam gaskiya kam ai
na ganshi ruan Malamai ne da shi inda tambayar
take dai na yanda aka yi ya iya zama da ke ne."
Ta zuba mishi ido cikin takaici ai ba za ka bari
muyi magana ta gaskiya ba ke nan? Ya tsura mata
nashi idanuwan da suka fi kama da gauta saboda
kaduwarsu kafin ya ce ai ba ki da ita ne, gaskiyar
balle ayi maganarta da ke. Ta gyada kai tare da
fadin to shi ke nan naji me ya kawo ka?
A haka zan fara magana ina zuba tun ban ci
komai ba? Ai sai ki kawo min da na shar kajin da a
ka bani labarin kullum a ka zo' gidanki sai an ci.
Yana cin naman da ta kawo mishi yana magana
zuwa nayi in dangwali arzikinki tunda kin shigo
cikin inuwarshi don kuwa nima babu irin taimakon
da ban yi miki ba, sanda su sarka suke wulakantaki,
ko sanda ki ka haifiyaran nan..."
Tayi maza ta katse shi "Ba fa tarihi ka zo karanta
min ba, arziki ka ce ka zo ci." Yayi maza ya ce, "Eh

9
haka na ce, to kai duk abinda ka ke da shi bai ishe ka
ba sai ka zo wurina ni da nake zaune a dakina ko
sana' a bana yi?
To ai ku ne masu rufin asirin amma na wajen
nan menene ne a cikin abin? Kin san fa shari'ar nan
da a ke ta kafawa ta karya darajar al'amuran namu
kana
gaba daya ke dai ayi shiru kawai tunda kana
Musulmi ba zai yiwu ka buda baki ka ce ba ka ji
dadin abin ba.
Ta mike ta shiga dakinta ta fito ta mika mishi to
ungo rike wannan ko sigari ka sha, lokacin ne na
tuna farkon zuwan Babah Lantana na gidanmu har
sigari sha take ji amma yanzu kam ta daina don na
ma manta in ban da yanzu da naji ta ambata da
bakinta.
Maimakon ya karba yayi godiya kamar yanda
al'adar wanda a ka yi wa kyauta take sai kawai naga
ya harari abinda ta ba shin ya ce kyautar matsiyata
za ki yi min? ko da na ce miki ba ni da harka ai kin
san nafi Rarfin irin wannan kyautar don kin san kont
waye?
To in tsaya daga waje mana in yi bara ki bai wa
yara su kawo min sadaka, ai a sauwake abinda za ki
bani in bar gidannan bakina alaikum jaka guda ne.
Da sauri ta ce mishi a'a buhu guda ba jaka guda
ba gaka guda lafiya ce da za ka ce in baka ita ina na
ganta? Kai barawo ne? A'a to sai in gyara zama ai

10
sai kin samu, to sai in gyara zama ai sai kin samu to
ma me za ki kira ni kuma oho ni dai kin san ba Delu
ba ce da ta taimake ki ta rinka yi mii zirga-zirgar
gidajen Malamai da 'yantsubbu bayan irin wahalar
da tai tayi miki da 'ya'yanki
Sai da ki ka samu kan miji ki ka mallake shi taf
ya zama bai da katabus sai naki sannan ki ka yi mata
irin tukuicin da ki ka saba yi wa wadanda suka saba
taimakonki wanda yayi dalilin da suka rada miki
sunanki na ainihi 'Butulu' ki ka koreta ki ka ce kar
ta sake zuwa miki gidą don ba ki yarda da, ita ba."
"Ita taje ta turo ka ke nan? " kan ya bata amsa sai
naji yaro yana magana a tsakar gida wai Maryan
ana kiranta a waje."
Da sauri Nalami ya kalli Babah Lantana cikin
yanayin rage murya dama ba mu biyu ba ne a gidan
shi ne ba ki gaya min mun yi maganar a hankali ba?
Ba ki kyaufa ba Lantäna, ai wata kusar tafi wata.
Ai in da ná sani ba zan yi îrin wadannan kalaman
wani ya ji ba, na fito zan wuce in je'kiran da a ke yi
min ban sani ba ko zaman Nalamin ne ya hanata
tuna min da dokar da Babana ya. kafa mini ko kuma
don taga ita ma bata bi dokar ba ne oho, tunda nasan
tafi kowa jin an ce ana kirana a waje.
Ina fitowa muka hada ido da Nalami barin komai
yayi ya shiga bina da kallo, wani irin kallo da yafi

11
kama da na kidima, uh' uh uhhh, wacece wannan
Lantana?
Tambayar da naji shi yana yi mata kenan yayin
da ni kuma na shige cikin zaure na bar su a nan ban
jiwo amsar da ta ba shi ba' lna daga cikin zaure na
hango Mubarak a tsaye daga waje yayi kwalliya
sosai.
Karo na farko da ya taka yazo kofar gidanmu
tunda ya dawo daga Ibadan, sai ko jiya wannan
kuwa naji an ce wai Babah Sumaye ce da taji ihun
da nake yi ta aiki Almajirinta da gudu yaje ya gaya
mishi abinda ke faruwa.
Daga cikin zauren naja na tsaya ban ce mishi
komai ba, shi ya matso bakin kofar zauren ya tsaya
kina da wata matsala ne? yayi tambayar yana
kallona, na girgiza kai a hankali nuna alamar babu.
Ya miko min ledar da ke hannunshi cikin zauren
na mika nawa bhannun na karba ya juya ya tafi ba
tare da na ce mishi komai ba.
Na koma baya ta cikin lungun zauren saboda jin
ledar da nauyi ga kuma sai da na nemi wuri mai dan
kyau sannan na zauna na fito da abinda ke ciki,
gasasshiyar kaza ce katuwa tayi matukar gasuwa
gashin injin ga yaji a wata takardar ga kuma ruwan
lemo na kwali mai sanyi.
Lokacin ne na kara tuna har a wannan lokacin da
agogo ya kai kan sha biyu da rabi ban sa komai a

12

bakina ba, da bai zo ya kawo min wannan kazar ba
kuma to da ban san lokacin da zan samu abinda zan
ci ba, ko a haka kuma Babana yake ganin zan iya
tsare dokar da ya kafa min ta kar in tafi ko'ina? Oho!
Ci nayi sai da naga na koshi sannan na dora
ruwan lemon nan a kai sannan na mike na dauki
saura na nade na adana shi a cikin gyalena, na shiga
cikin gida har lokacin Babah Lantana magana take yi
da bakon nata, sai dai a yanzu maganar tasu ta dan
sauya da alamar sun dan samu daidaituwa.
Yana ganina ya saki wani lallausan murmushi
har hakoran Makkanshi suka fito guda biyu, kuma
jajaye yana ganin mun hada ido da shi yayi maża ya
sakar min signal da idanuwanshi. Nima nayi maza
na galla mishi wata irin matsiyaciyar harara na wuce
na shiga dakina.
Wasu sabbin kwanukan abincin na gani wurin
Asabe da alamun fitan da nayi ya kara bada damar
da aka sake kawo mata wani abin.
"Yanzu dai kin gani Hajiýa bani kawai abinda ki
ka ga za ki ba ni tunda ga bayanin da ki ka yi min na
halin da kike ciki in an kwana biyu ai zan dawo."
Da sauri ta ce, "A'a-a'a ni kar ka dawo min gida
in ba so ka ke ka kara min wata matsalar ba."
"A aha, ai ke halinki ke nan ki ka sani ko zuwan
nawa na alheri ne? To ta ina zuwanka zai zame
min alheri ni kuwa?" ya yi murmushi "Uhum, Babah

13

Lantana kenan, ai na daina kiran sunan naki gatsau
sai na sakaya miki shi da Baba ko kuma Hajiya. Ai
kin san shi sunan Hajiya ma mai niyya yake nufi."
"Kai dai karbi amma ni kar ka dawo min gida."
Ya karba yana kirgawa, ai tunda na ce zan dawo zan
dawo din ne kiyi fatan kawai dawowan nawa ya
zame miki alheri." Ya tashi ya tafi.
Ina zaune a gida Babana dokarshi a kaina ni
kadai take aiki, Babah Lantana da 'ya'yanta babu
abinda ya shafe su da ya dawo yazo ya samu Sallau
a gidan ma bai ce mishi kala ba, sannan da zai kafa
min dokar daina fita daga gidan sai ya manta bai
sanya ta bani abinda zan ci dole ba.
Duk da haka na bi umarnin da ya banin na in
daina fita saboda magnar da Yaya Dijah take yawan
gaya min in bi duk wani abinda zai sanya ni komai
wuyarshi, kar in ki yi mishi yayya a kai kar kuma in
lura da cewar wasa ba su yi mishi ba ni ce ya zama
wajibi a kaina in bishi ba su ba.
Ina zaune a haka cikin wani irin matsanancin hali
in ba Mubarak ne ya kawo min abinda zan ci ba
babu mai bani a hakan kuma ga barazana gami da
wulakanci da neman tsokana
Kowane lokaci a cikin maganar ake haka kawai
sai ka ci Babah Lantana ta ce ah cizo? Ai sai kin
rama a natse za ki rama kara warkewa dai kawai
karfinki ya kara dawowa jikinki."

14

Ina kallo Asabe take fitowa daga wanka ta shafa
maina tayi kwalliya da kayan kwalliyata in ta gama
ta jawo akwatin kayana ta zabi wanda yayi mata ta
daura, bana cewa komai saboda ina tsoron kar
maganar da zan yin ya zama sanadin da zamu yi
fadan da zata rama cizon.
Sannan in ta gama abinda take yin sai ta mike ta
bar komai a hakanshi sai na gyara wanda ni shi ne
ma yafi bata min rai.
Rannan da hantsi Mubarak yazo muna tsaye
muna magana sai ga Sallau yazo ya wuce mu yana
taku dai-dai, ya bishi da kallo kafin ya dawo da
kallon nashi gare ni wannan ya bai tafi ba ne? na ce
mishi ch, ya dan yi shiru jimawa kadan ya ce uhun,
wato shi Baba ke kadai yake iya hukuntawa?
Ban ce mishi komai ba sai ya sake kallona "Ba
suyi miki wani abu ba ko? Har na ce mishi Eh, sai
kuma naga to in ban gaya mishi ba wa zan gayawa?
Don haka na kwashe bayanin komai nayi mishi, ya
ce To babu laifi."
Hirarmu muke yi sosai ina daga cikin zaure yana
waje sai ga Asabe tazo zata shiga cikin gida, cikin
dace zanina ne a jikinta kuma shi ya saya min shi,
wani lalataccen kallo tayi mishi ta wuce da nufin
shiga gida, ba karamar kiyayya Asabe ke yi wa
Mubarak ba.

15
Duk sanda ta bude baki zata yi magana akanshi
munanan kalamai take yi. Ina wuni Asabe? A lalace
ta ce mishi lafiya, dan saurare ni mana minti bivu
Ta waiwayo tana yi mishi kallo na sama da kasa.
lafiya? Ta ce, bani da lokaci.
Ya ce To je ki zan aiko agogo yazo ya gaya miki
ama kafin ki ji sakon daga wurinshi kina shiga gida
ki cire wannan zanin da ke jikinki ki wanke shi ki
goge shi ki maida shi inda ki ka same shi ki ajiye. Ta
ce ai ka san don ku kadai Bature yayi iinshi, bai
tanka mata ba sai kawai ya kira wani yaro mai
kimanin shekaru sha biyar da ke can gefe.
Zo nan Isiyaku, maza haura can saman layi ko
bayan layi kaje ka kira min agogo ka ce mishi ina
nan na jiranshi yazo yanzu.
Hankalina yayi matukat daurewa saboda ganin
yanda jikin Asabe yayi matukar yin sanyi da jin an
tura a kira agogo. Me ke tsakaninta da agogo? Kuma
wancne ma agogo? Wadannan sune tambayoyin da
suka tsaya a raina.
Ga ni! Ta fadi tana mai kallonshi cikin natsuwa
ya buda baki ya ce mata, in kin shiga ki gayawa
Mamanku saboda nasan uwa ta gar tana karbar
shawara wurin danta in dai tasan shi din mai hankali
ne.
Ki bata shawarar kar ta sake saki ke ko wani ku
bugi Maryamu, kai ko da ita kanta ne kar ta sake?

16

Ku barta ta zauna lafiya a gidan ubanta don ta samu
tayi ta bin dokokin da yake saka mata."
A lalace ta kalle shi ta ce, in ba haka ba fa? Bai
kau da ido daga gare ta ba ya ce in ba haka ba ranku
ne zai fi na kowa baci, don ke da ni zan shiga cikin
lamurranki ba kadan ba, kin san babu abinda ban
sani ba a kanki zan sa a gayawa Agogo labarin
Dangana kin kuma san abinda hakan ke nufi.
Zan sa shi Agogon-ya kula min da lamarin gaba
daya, ina yi muku wannan kashedin ne saboda
kiyaye hakkin makwabtaka tunda akwai iyayenmu a
tsakani, in kuma ba ki ji ba to kuje kuyi.
Ke Maryam kar ki tsokani kowa a cikin su,
amma mugun kallo idan suka yi miki ki gaya min,
na ce to.
Ya kau da kai daga garcta alamar maganar ta
kare ta gane hakan don kanta ta wuce ta shiga gida
ba a dauki lokaci mai tsawo bayan nan ba nima na
shiga cikin gidan.
Daga shigan da nayi na gane akwai wani canji a
tare da Asabe don ban samu kayana a jikinta ba,
Babah Lantana ce dai na same ta tana huci tana
fadin, Aikin banza aikin wofi, ni kam ai rashin jini
rashin tsagawa.
Abinda zai hana ni dukan mutum bai tabo ni ba
ne kawai, amma duka ai har da na tsiya zan yi mata

17

ko ma don in ga abinda za ayi min, sai nayi na wuce
daki na barta tana maganganunta.
Asabe dai na gane ta dan ji abinda Mubarak ya
gaya mata, ana cikin haka sai ga Sallau ya shigo
gidan
"Mama ina so muyi magana da ke." Ta bar
abinda take yi ta tsaya tana kallonshi, yayinda shima
yaja ya tsaya Kerere a gabanta suna kallon juna,
"Menene ya faru? tayi mishi tambayar tare da
sauraron abinda zai gaya mata.
"Wannan yarinyar ce nake so in ce miki ki fita
hanyarta, ki bar kowa ya zauna lafiya, abinda kawai
zan gaya miki ke nan." Da sauri ta tambaye shi,
"Wacce yarinyar?" "Mero." Ya fadi sunan cikin
wani yanayi.
Kan ya gama karasa sunan ya ji saukar mari a
gefen fuskarshi tau! Da iyakacin karfinta tayi mishi
marin, a kan wannan shegiyar yarinyar ka ke yi min
wannan maganar, in ce ko dan tumurmusan da yayi
maka ne yasa ka tsorata da shi haka har yake aiko ka
da irin wadannan maganganun ka gaya min?
To na rantse sai nayi mata duka har cizon da ta yi
wa Asabe sai na sata ta rama ko in rama mata da
kaina, aikin banza aikin wofi, barazanar banza da
wofi. Ni za a kawowa iya shege?

18

Ni fa nan da ka ke ganina ni ba matsoraciya ba
ce, bana tsoron kowa duk iya shegen mutumn
kallonshi kawai nake yi, yauwa!
Ya'yan Babah Lantana sun dan shiga
natsuwarsu kadan saboda ta ki yarda suyi aiki sosai
da kashedin da aka yi musu wanda ya tsorata su,
amma duk da haka Asabe ta fita hanyar kayana ta
kuma kiyaye yi mun wulakanci. na kai tsaye. Illa
iyaka dai ba ma magana da juna.
Ina zaune a cikin gidan babu mai magana da ni in
ba Mubarak ne yazo ya kira ni ba, shi kanshi Baban
nawa gaisuwa ce kawai take hada ni da shi, amnma
bayan nan babu wani abu.
Tsananin kewa da kunci suka tarar min cikin
zuciyata, na gane babu abinda yafi mu'amalla
tsakanin mutum da mutum dadi, wanda ya rasa
abokin mu'amallah kuma to ba karamar wahala ce ta
same shi ba.
Ana cikin wannan haki na kamu da wani irin
matsanancin rashin lafiya, zazzabi mai zafi gami da
mura ga matsanancin ciwon ciki saboda lokacin
al'adata ya gabato, babu wani taimako da nake samu
daga gidan, sai dai in Babah Lantana taga ina
rarumen abinda za ayi ko zan ci, saboda yunwar da
ke yawan damuna, sai ta rinka fadin ba dai kin ce da
ni za ki yi ba? Ai mun sa kafar wando daya ke nan
ni da ke, naga wanda zai fara zare kafarshi.

19


Mubarak yazo duba ni da yamma yana daga waje
ina cikin zaure, yanzu ke kin rinka zama da ciwo ke
nan? An ce ki fito a kai ki asibiti kin ki, shi Baban
ba ya ganin irin ramar da ki ka yi ne ya bar ki a
haka?
Ban ce mishi komai ba na juya na shiga gida ina
rike da ledar sayayyar da yazo min da ita. Ina shiga
daki na zauna na bude ledar na jawo robar nono zan
sha don kuwa nasan barin da jikina ke yi bana ciwo
ba ne har da na yunwar da nake ji.
na gama shan nonon na dawo-dashi gaba daya ta
hanyar yin amai mai wani irin yawa da wari,

Please Login or Register in order to submit comment