Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ga shi
yayi wani irin kala.
Amai a -daki? Asabe tayi tambayar cikin wani
yanayi na nuna tsananin kyama, to na rantse sai dai
ki kwashe ke da kanki, don ni bana taba amai.
Ina kwance ina jin ta ko daga ido in kalleta ban
yi ba, cikin zuciyata dai fadi nake yi dadin abin ma a
kan kayana nayi.
Babah Lantana tana jin Asabe tana ambaton
sunan amai ta rugo a guje, amai? A nan gidan yau'?
Uhum, abinda na gudanwa Mallam ke nan abinda na
gudanwa Mallam ke nan, abin da na gudanwa
Mallam ke nan, bai gudunwa kan shi ba to tunda bai
gudanwa kan shi ba kuwa ga shi nan ya same shi.
Ni kuwa babu wanda zai zauna ya renan min
cikin shege a gidan nan yauwa, don mu abin kunya

20

gudun shi muke yi saboda ba mu gaje shi ba, su dai
ina jin suna da gadonshi shi yasa nake tayi mishi
kashedi bai ji ba.
Sannan al' amarin Mallam ma ai in ka duba akwai
matsala, mutumin da bai da dangi Mallam fa ko
sunan garinsu bai kira balle ya ambaci wani dan uwa
nashi, wa ya san abin da yayi ya bar gidan?
Duk da tsananin ciwon da ke damuna sai da na
zubawa Babah Lantana ido ina kallonta.
Ta ce, Eh kalle ni da kyau ko. karya nayi muku?
Ana barin gida haka kawai ne?. ai yawanci abin
kunya a ke yi a tafi in kin ga dama ki gaya mishi
kema kin san a tafin hannuna yake.
Ta muno min cikin tafin hannun nata, ta juya tana
tafiya tana gayawa Asabe tafi can wajen tumatirinshi
ki kira min shi yazo ya gani da idonshi kar ya ce
karya nayi mishi, daganan kuma sai ya kwashe
donni da hannuna ba zan kwashe aman cikin shege
ba.
Ina kwance ina jin shigowar Babana da irin
maganar da Babah Lantana ta tare shi da ita, ai babu
abinda ban gaya maka ba kan ciwon da yarinyar nan
ke yi ba haka kawai ba ne, ciwo kwana da kwanaki
kuma mai zafi haka ai kowa ma yasan menene sai
dai a yi shiru.
Da sauri Babana ya fadi cikin dakin jikinshi sai
rawa yake yi, me ya same ki Yacuuwuna? Me ya

21

same ta ko me ya same ta kai nan sai an gaya maka
abinda ya same ta?
Yasa hannu ya daga ni a'a har da amai ki ka yi?
Yasa hannu ya nade ya fitar ya dawo, Babah
Lantana tana fadin ai gara kaga aman da idonka, kar
ka ce ko sharri a ka yi mata.
Tashi muje in kai ki asibiti, yasa hannu ya daga
ni yana rungume da ni a jikinshi muka fito daga
dakin za ka kaita a cire ne? ai binka zan yi don ba za
ku ce ku dawo kayi min karya ba tunda dai wannan
ciwon nata ai kowa ya ganta yasan ciki ne da ita.
Ina jin irin lkaduwar da jikin Babana yayi sanda
Babah Lantana ta ambata.mishi cikin nan ya dan ja
ya tsaya na yan dakiku bai motsa ba, kafin ya ci
gaba da tafiya.
A asibiti a gaban Babah Lantana da Babang
Likita ya gama duba ni ya gaya musu cewar
maleriya da yunwa ne suka kama ni. A ka sanya min
ruwa saboda ramar da nayi tayi yawa, a ka hada min
da magunguna a ka sallame mu,
Likita yana dada jaddadawa Babana lalle ne a
kula da abincina don na rasa nauyi mai yawa a tare
da ni.
A gida ina jin Asabe tana tambayar Babah
Lantana me Likitan ya ce? Ta tabe baki ta cc bai kai
ta wurin wani asibiti na gaske ba, can wurin wani

22

dan iska ya kaita da bai ma iya aikin nashi ba, wai
ciwon sauro ne da yunwa. Har yana wahi daura mata
ledan ruwa in ma hada baki suka yi ya boye ai shi
ciki dan duma ne muna nan sai ki ga ya fito mun gan
shi da idonmu.
Washegari Babana ya kawo min 'yan abubuwan
ciye-ciye da yake ganin za su taimake ni. a gabanshi
Babah Lantana ta rabe komai ta bani.abinda take
ganin shine daidai a wurinta, tana yi kuma tana fadin
"In dai cizon sauro ne lalurarta to wanene mai lafiya
ne a cikin gidan nan ba gara ita ba ma tana fita ta sha
sharholiyarta a waje, mu kam ai kullum muna ciki
muna tare da saurayen.
Inda na samu kulawa ta sosai-sosai daga wurin
Umma ne da danta sai ko Yaya Dijah da mijinta,
kusan kullum sai tayi min aike, kusan kullum din
kuma zata ce wa dan aiken ya gaya min in naji sauki
in zo tana son ganina in ce mashi to.
Na soma jin sauki ke nan Mubarak ya zo yayi
min sallama kan za su tafi Umra shi da Babanshi,
nayi addu'ar Ubangiji ya dawo da su lafiya,; ya kuma
sa suyi aiki karbab6e. Ya ce, To amin.
Ban yi miki sayayya ba saboda sanin yanda gidan
naku yake da nayi don haka ungo wannan ki rike a
wurinki ki adana kar ki bari su gani, balle su kwashe
miki duk abinda ki ke so ki saya kar ki yarda ki
zauna Cikin damuwa.

23

Na gayawa Isiyaku kullum da safe yazo yaje
miki aika ko wankinki ne ya taru ki ba shi zai yi
miki, na ce mishi to. Lokaci mai tsawo ya dauka
yana yi min kalamai na bada hakuri kan tafiyar da
zai yi a cikin dani din ko wadatacciyar lafiya ba ni
da itana ce mishi a'a babu komai.
Na dawo daki na kirga kudin da ya banin Naira
dari ne cif wato fan hamsin ke nan, a wancan
lokacin kuwa mafi yawancin sadakin yanmatan
unguwarmu da a ke aurarwa ma bai wuce tan goma
wato Naira ashirin, in yayi yawa a karbi arba'in ko
hamsin da kyar kwarai za ka ji an bada sadaki fan
hamsin Naira dari ke nan.
Mamaki ya kama ni, na in da Mubarak ya samu
irin wadannan kudin ya kuma iya bani su, ganin
kimar kudin da yawansu ya sanya ni tunanin in
kaiwa Babana su sai naga to ai in na kai mishi ma
wurin Babah Lantana zai dawo da su.
To ko in kaiwa Umma ta ajiye min? nayi maza
na canza saboda tunanin anya ya gaya mata zai ba ni
irin wadannan kudin? In bai gaya mata ba ke nan na
hada su, don haka na mike da sauri na fita na bar
gidan ba tare da na gayawa kowa ba.
Na tafi na kaiwa Yaya Dijah kudin da sauri na
dawo nazo na boye Naira goman da ta bani ta ce in
rike a wurina, saboda bukatuna.
24
Kamar yanda Mubarak ya gaya min cewar
Isiyaku zai rinka zuwa min aika hakan a ka yi, da
sassafe ya shigo ya gaida Babah Lantana kafin ya zo
in da nake na dauko kudi na bashi, na gaya mishi
abubuwan da zai kawo min yaje ya kawo ya karbi
wankina ya fita da su.
Ba a wani dade sosai ba sai gashi ya kawo min
su a goge, dadin hakan yasa na mike'da nufin in je
in yi wanka don in kara jin dadin jikina.
Naje kicin da nufin in sanya ruwan da zan yi
wankan da shi a risho don ya dan kore sanyinshi
tunda ba gama wartsakewa nayi ba. Babah Lantana
tayi maza ta ce min kar ki shigar min wurin nan ba
ki da komai a ciki in dai ba tsamar min naman miya
za ki yiba.
Na dawo da baya nasa hannu na dauki bokitin
robar da ake wanka da shi, nufina in tari ruwa a
bakin famfo in je in yi wankan a haka, nan ma ta ce
a jiye min bokitin nan tunda ba uwarki ce ta saya
min shi ba.
Na maida shi na ajiye na wuce naje na dauko
wani bokitin karfe da ke can gefe na tara shi ina
duban ruwan ta bar abinda take yi ta mike ta tsaya
tana kallona wai ba nace kar ki taba min wani abina
ba ne ko kina nemana ne da magana'?
A hankali cikin natsuwa nace mata wannan ai ba
naki ba ne kin ga ni? Bokitin Innarmu ne, abinda

25

kawai na fada kenan ta takarkare ta wanke ni da
marin da nayi matukar kaduwa.
Ba na ce ki daina ambaon min sunan shegiyar
matar nan a cikin gidan nan a? ban san lokacin da
na buda baki na ce wa Babah Lantana "Gaskiya
Innarmu ba shegiya ba ce. Sai kawai ta rufe ni da
duka.
"Ai dama na gane talke-takenki nema ki ke ki fara
zahina kiri-kiri, bayan na bayan idon da kike yi ana
gaya min ba ki kuma isa ba don ni nan ko uwar taku
ma da tana nan din ba za ta buda baki ta zage ni in
kyale ta ba, to balle ke banza a banza.
Duka iin wanda Babah Lantana tayi min bai
kwatantuwa don kuwa yi tayi sai da ta gaji ta bari
don kanta, babu wanda ya shigo gidan don kawo
min agaji, duk da irin ihun da nayi ta kurmawa.
Asabe ma tana daki a zaune ba ta ce mata komai ba.
Ina zaunc a tsakar gida bayan matsanancin dukan
da Babah Lantana tayi min ban sake komawa dakin
ba saboda abinda nake tsoro wana ke kara sa ni
zaman nakin ya faru, don haka ina zaune ne kawai a
tsakar gidan amma ban iya daina kuka ba.
Ita kuwa Babah Lantana tana ta kai-kawonta tare
da fadin "Haba an ce miki ni ina tsoron wani ne? Ni
fa da ki ke ganina bana tsoron kowa ina kyaleki ne
kawai kina iskancin ina kallonki, amma ba don tsoro
ba.

26
Yi ta zama a nan har uban naki ya dawo yazo ya
same ki in ji abinda zai ce, ina ce zaman da ki ke yi a
wurin ke nan, in kuma shi wancan dan iskan ne ina
nan ina zaman jüran dawowarshi in ga abin da zai yi
ko ni ma zai zo ya kirba min naushin ne?"
Sallau yana shigowa gida ya ganni a zaune yayi
turus ya zuba min ido yana kallona, cikin tsananin
kaduwa ya juya inda Babah Lantana ke zaune tana
sakucen naman da taci da tsinken zaburin shara.
"Dukanta ki ka yi Babah, me tayí miki? Ba ta ma
fa gama warkewa ba sannan in za ki buge ta ma
Babah wannan wane irin duka ne?
Da sauri Babah Lantana ta mike ta kifa mishi
mari mai tsananin karfi ta sake kifa mishi wani.
marin har sau uku da ya tsaya wata kila da abin yafi
haka.
Juyawa yayi ya fita, ya barta tana fadin, sakarai
matsoraci, shashasha kai kam in ba sa'a nayi
rakiya kayi wa maza zuwa duniya don duk wata
harkarka ta tsoro ce, na bugeta wanda duk ke da abin
yi yazo yayi ina nan ina zaman jiranshi, aikin banza
aikin wofi, ni za a kawowa iya shege?
Ina zaune a daki cikin matsanacin hali don wani
zazzabin ne ya sake rufe ni, ga 6acin rai don na fara
gajiya da irin wadannan al'amuran naji dawowan
Babana da bayanin da Babah Lantana ke yi na nayi

27

mata rashin kunya itama kuma tayi min hukuncin da
ya dace da ni.
Sau dubu kuma in zan mata to sau dubu itama
zata yi min in ina son zama lafiya to in kiyayeta gara
tun wuri ya jaddada min in ba haka ba kuwa to ita
babu ruwanta bai ce matakomai ba.
Washegari da safe tunda na tashi da kyar nayi
sallah na koma na kwanta saboda tsamin da jikina
yayi ina jin sanda Asabe ta sauko daga kan gado ta
take min kafata ban ce mata komai ba.
Ta dawo dakin tana sallah na ji Babah Lantana
tana ta kwala mata kira, cikin wani yanayi kamar dai
wani abu ya faru, da sauri ta:sallame ta fita sai naji
tana ce mata yi sauri ki tafi gidansu Delu ki gani ko
a can Sallau ya kwana bai dawo gida ba jiya.
Gidan su Delu kuma Baba me zai kai shi can
bayan duk wannan abinda aka yi? Yanzu haka yana
can wajen abokanshi sun sha a bar su suna ta barci.
Ke wuce kije ki duba min shi mara mutuncin
yarinya mai gardamar tsiya kuma Delun kike kira
haka gatsau babu sakayawa babu komai?
Asabe ta wuce tana kunkuni haka kawai mutum
yaje ya kwana a wurin iskancinshi za a hana ni
baccina na safe ace sai na dubo shi sai ka ce wani
dan karamin yaro.
To ko ni da aka ce Sallau bai kwana a gida ba
nayi mamaki don ba mai irin wannan halin ba ne

28
amma sai na maida lamarin kan yayi fushi ne da
abinda uwarshi tayi mishi saboda maganar da yayi
mata a kaina tunda na saba ganin yana fushin da
ita ta bashi hakuri.
Abu wasa-wasa sai ya soma neman ya zama
gaskiya kusan duk inda ake zaton ganin Sallau sai
da aka je nemanshi babu shi babu dalilin shi.
A ka wuni ranar babu Sallau, tun ana kokarin
danne hankula kar su tashi har dai abin ya gagara a
ka shiga tashin hankalin mai tsanani, nena har da
Babana a ciki don ko wurin tumatirinshi bai je ba,
har wajen yan sanda aka kai riport da kuma
asibitoci shiru babu wani motsi.
Har wajen taran dare suna zaune jungum-
jumgun a tsakar gida, yayinda ni kuma nake
kwance a daki sai naji Babah Lantana tayi magana
cikin sauri duba Asabe naji kamar an shigo zauren
gidan nan.
Asabe ta mike tana fadin ke Babah ba za ki bar
mutum ya huta ba, dazu ma fa haka ina zaman-
zamana ki ka tashe ni wai kin ji kamar an shigo
zauren gidan nan to in an shigo menene?
Wani irin mummunan ihu Asaben ta kurma a
daidai shiganta cikin zauren, abinda yayi dalilin da
Babana da Babah Lantana suka karta a guje don
ganin dalilin ihun nata.

29
Thun Babah Lantana ya biyo bayan ihun Asabe
Babana kuwa sai faman salati yake yi yana karawa
alamar abinda ya ganin yayi matukar razana shi.
Makwabta ku kawo min agaji da iyakacin
karfinta take fadin hakan sai dai babu wanda va
shigo duk da ana jin ihun nata da kuma kiran
agajin da take yi amma shiru, bata kuma daina ba
tanfar dai a ce ta mance da irin zaman da take yi
da su nasa mu jinta yayiwa kowa kashedi kan
shiga gidanta da ake yi bata so.
Bai san yanda aka yi ba naji maganar Baba
Baidu cikin zauren yana fadin, a'a bai mutu ba ai
ga wannan jijiyar tashi tana harbawa da sauran ran,
da alama dai shi Baba Baidu ya amsa kiran neman
agajin da take yi ya kawo mata.
Ihu Babah Lantana take yi tana karawa bata yi
shiru ba har Likitan da Babana yaje ya kira ya iso.
Shigo da Sallau tsakar gida da aka yi yasa na
koma ta inda nake hangensu, tabbas in dai ba
hatsarin mota yayi ba ko wata Rakkarfar dabba ta
tattaka shi to wanda duk yayi mishi wannan abin
da aka yi mishin ya tabbata mara tausayi.
Likita ya fara taba shi shima ya fara fadin na
tuba na tuba ku bar ni kar ku kashe ni, kusan awa
biyu Likita yana kanshi ana yi ana danne shi
saboda zaburar da yake yi.

30
Gaba daya jikin nashi ciwo ne wajen targade
shida ne da kuma tsagewan kashi guda biyu,
bayanin Likita ke nan. Yayi abinda zai yi ya gama
ya mike yana fadin, in hali yayi a kai shi asibiti a
kara bincike na sosai amma a yanzu dai wadannan
da muka gani mun kula da su.
Baba Baidu yayi mishi godiya' yayinda Babana
ya bi bayanshi alamar zai je ya sallame shi, ita
kuwa Babah Lantaná sai faman kuka take yi tana
fyace majina da bakin zaninta itama Asaben da ba
wani shiri sosai suke yi ba kuka take tayi.
Sannu Sallau, sannu ka ji? Sanu, Ubangiji ya
baka lafiya maganar Babana ke nan. A hankali
Sallau ya bude baki ya ce "Yauwa Baba, na gode."
Da sauri Babah Lantana ta kara matsawa kusa
da shi tana tayi mishi magana saboda ganin da tayi
ya dawo cikin hayyacinshi. Da kyar ya yarda ya
buda baki ya bata amsar tambayar da ta dame shi
da ita "Su Agogo ne. gabana yayi mummunan
faduwa jin ya ambaci sunan da Mubarak ya
ambata a matsayin wanda zai sa yayi mishi
maganin abin.
Su waye su Agogo? Ta sake bukatar sani, bai
ce komai ba sai da ta gaji da tambayar cikin
natsuwa ta soma yi cikin karaji da tashin hankali
sannan ya bata amsa ki tambayi Asabe tasan shi.
31
Da sauri Asabe ta daka mishi tsawa kai kul
kasa sunana a Cikin abin ku da waui ruba66en
bakinka.
Gaba daya kowa yayi shiru daga inda nake dai
ina jiwo mishin Sallau ba kuma san ba dadi ba ne
ya kawo hakan can cikin zuciyata kuma ina
tunanin Asabe da dan uwanta Sallau babu halin su
hadu wuri daya sai sun yi fada na tuna ni da Yaya
Dijah na ce to ko don mu ba mu da uwa ne yasa
muke son juna oho?
Zuwa can Sallau ya sake gajiya da tambayoyin
uwar ta shi ya ce, to in na gaya miki abinda yasa
Agogo suka yi min haka me za ki yi? Ba kin ce ko
sama da kasa zata hadu ba za ki daina dukan
Mairo ba, to wannan abinda a ka yi min ai ba
komai ba ne kan abin da ki ka ce, don haka gobe
ma ki sake dukanta.
Shawarar da na baki ba ki dauka ba ne yaja
min wannan wahalar gobe ma in kin sake za su
sake da har sun je sun kama mijin Babah Delu da
ki ke cewa wanki ne suka sake shi saboda ya gaya
musu babu abinda ya hada ku in ban da zaman
gidan baya, yanzu ma kuma bakwa tare don in sun
baki shawara ba kya dauka.
In ban da halin da Sallau ke ciki wata Rila da
Babah Lantana ta gwabe mishi bakinshi a dalilin

32
wannan bayanin nashi, nmaimakon haka kurma ihu
mai tsanani tayi, ta yi kuka irin na fitar hankali
bayan ta tambayi Sallau yanzu saboda wannan
shegiyar yarinyar a ka yi maka wannan azabar?
Bai musa ba bai ce mata uffan ba, to ai kuwa
ba zan daina dukantä ba, sai dai... kan ta karasa
taji ya ce mata to nuna min kawai inda dangin
ubana suke tunda shi kin ce min wai ya mutu in
dai da gaske ina da shi ai ba zai rasa dangi ba don
ni Babah Delu ta ce min duk abinda ki ke gaya
min kar..
Kan ya karasa tayi maza ta tarke shi da mari a
kan ciwon nashi, ni dama kashe ni kawai ki ka yi
da yafi min tunda dai duk wahalar da nake sha a
rayuwata ke ki ke ja min.
Wannan din ma ke ce na kuma san za ki sake ja
min wani tunda sun ce sau goma ki ka buge ta sau
goma za su rama mata a kaina, to ba gara kawai ki
nuna min in da ubana yake ba.
Ganewan da Babah Lantana tayi cewar
Mubarak ne yasa a ka yi wa danta irin wannan
matsanancin dukan duka kuma irin na rashin
tausayi, a matsayin kashe di mai karfi gareta kan
abin da take yi min na azabtarwa yayi matukar
tayar mata da hankali.
33

Ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, don bakin
ciki ta rasa me zata yi ta dauki fansa kan wannan
abinda yayi mata? Tayi kuka tayi kuka har sai da
ta kwanta ciwo wanda ban taba ganin ta kwanta da
sunan ciwo ba sai a wannan lokacin.
Kwana biyu ita ma tana fama da kanta, rannan
ta samu sauki ta fito tana zaune a tsakar gida kan
turminta ashar take durawa Mubarak tana fadin
tana nan tana jiran dawowarshi yayin da ni kuma
take ta faman tsine min albarka.
Asabe ta gaji ta ce mata, to ya dai tsaya a kan
zagin kar kije ki sake jawowa mutane wata fitinar
don ke ba kya jin shawara.
Wani abin mamaki shi ne, Asabe sai ta kwaso
kowacce irin magana ta yabawa Babah Lantana
tana kallonta ba za ta ce mata omai ba, amma
Sallau duk da kasancewarshi da namiji kuma shi
ne babba bata yi mishi lamnunin hakan.
Jinya sosai Tanimu ya kwanta yayi kwana da
kwanaki yana yi Babana yayi ta dawainiya da shi,
amma tun bai gama warkewa ba sai naji Babah
Lantana tana cewa Babana wai yana gani ana
nema a kashe mata da a kan matsiyaciyar 'yarshi
amma ya kame baki yayi gum kamar na mai cin
najasa, gum din din dai ya sake yi mata bai ce
mata komai ba har tayi ta gaji tayi shiru.

34
Duk da kudin da nakeda su a hannuna rashin
Mubarak yasa nayi matukar. takura komai zan eii
sai na saya ban saba wannan rayuwar ba, abinda
nafi sabawa dashi a kawo min ne don haka kudin
da ke hannuna bai hana ni jin yunwa ba,
musamman ma da yake wani lokaci ana sayo min
in kasa ci, don bai gamsar da ni ba tunda in yana
nan ba irin wannan din nake ci ba.
Babah Lantana tayi girki ta raba ta baiwa kowa
nashi 'ya'yanta guda biyu da Babana yayinda ita
kuma take zaune a kicin tana cin nata, na mike
naje e same ta na ce Babah a bani nawa abincin.
Ta kalle ni a lalace ta ce in ba haka ba fa a kore
ni ko a yi ya ya? Shiru nayi na tsaya.ina kallonta,
yayinda ita kuma take bayani a nemi kashe min da
a kan ki sannan in yi girki in ba ki.ai ba zai yiwu
ba.
Daga bayana Babana ya ce min to zo ki dauki
wannan nawan kici, na juyo da sauri ta biyo ni
tazo ta fige kwanukan a hannuna in gadaranka kai
ka kawo ai ni na girka, ni baiwarta ce? Bata danye
itama ta girkawa kanta ai mace ce babu kuma
abinda bata sani ba wani abin ma ta fini sanin shi.
Wannan magana da Babah ILantana tayi ta in
girkawa kaina shi ne dalilin da yasa da gari ya
waye nabi bayan Babana zuwa wurin saida

35

tumatirinshi nace ya bani kayan miya, ya zuba a
leda ya miko min.
Na kalle shi cikin natsuwa na ce, to abin da zan
dafa fa? Akwai a gida, na ce ba za ta ba ni ba, bai
ce komai ba ya ciro kudi ya bani na wuce na shiga
shago na sayi taliya guda daya na juyo na kama
hanyar zuwa gida.
Ran 'yanmata ya dade, na jiyo muryar tashi
daga bayana na kuma shaidata ta Mansur ce, bàn
waiwaya ba na dai ja na tsaya ina jiran isowarshi.
Ai rannan na hango ki kina dawowa daga
Makaranta nayi ta daga miki hannu ina haba in
babu busa babu daga hann ne? sai na lura ma ba
ki ganni ba. Nayi murmushi tare da fadin eh, ka
kyauta min kwarai da kai da kanka ka gane
ganinka ne ban yi ba.
A'a haba ai nasan ba ki da irin wannan
wulakancin ke dai kawai ganinki ne yana wuya da
yake kin riga kin zama budurwa. Na ce, kai
Mansur ke nan, barkwancinka yana da yawa, can
cikin zuciyata kuwa mamakin dabi'arshi
kanbama 'yanmatancina nake yi.
Kullum muka gamu sai ya jaddada min ni din
budurwa ce ni din mai kyau ce, ni din daba ce da
saura, abinda kuma bai taba damun Mubarak ba ke
nan. Na dan yi shiru cikin nazari da tunanin ko

36
Mubarak. sya taba gaya min ifin wadannan
kalmomin? Kai bani tuna ba.
Kar dai a ce rashin lafiya ki ka yi bai sani ba?
Na ce eh amma ba mai tsanani ba ne, ya zuba min
ido yana kallona, kina nufin abinda yayi sanadin
wannan ramar ba ma tsanani ba ne? nayi
murmushi na cé. eh, ya ce to kuwa sai muyi ta
addu'a kar mai tsananin yazo, na ce to amin.
To mu ba yaran nan ledar cefanen mana don
kar mu 6ata muşu lokaci na ce a'a babu komai
cefanena ne, kina nufin kece za:ki yi girkin da
kanki? Na ce, eh, ya ce a'a to shiga ciki kawai ina
zuwa, bari in je in kawo cefane nayi maza na ce
a'a ka bari.
Ya daure fuska ya ce, to ai ba ke ki ka roke ni
ba, na wuce shi da nufin tafiya gida, ya sake biyo
ni ran yanmata ya dade, na dan rage takun da
nake yi don nasan wata magana yake son gaya
min, kina da bukatar wani abu ne? nayi maza na ce
mishi a'a na tafi.
Ina cikin tafiya sai ga Isiyaku da saurinshi, Anti
ai nazo ki ka ce babu aika, na ce eh Isiyaku wurin
Babana naje na karbo yasa hannu ya karbi ledar da
ke hannuna muna tafiya yana bani labarin wahalar
ruwan da ake yin da yanda suma matar Babansu ta

37

sanya dokar sai mutum ya ajiye bokitin ruwa goma
kafin ta ba shi abincinshi.
Ba ki ga fa inda muke tafiya diban ruwan ba,
na ce eb to wata rana ai zai wuce Isiyaku, ya ce
haka a ke fada, nayi tunanin shima yana da irin
manina kenan, da zuciyata ke yi min a duk
lokacin da a ka gaya min haka shi ne na in tambayi
kaina to yaushe ne wata ranar zata zo?
Cikin gida na shiga shima ya biyo ni duk da
yasan Babah Lantana ta tsani shigar da yake yi
cikin gidan kullum ta ganshi a ciki sai ta tambaye
shi kai baka san nan gidan, gidan matan aure ba ne
ba? Sai ya ce ya sani ye uce ta yayi abinda zai yi
ya fita.
Na shiga cikin kicin, tayi 2za ta biyo ni karki
shigar min kicin kar ki taba min komai a wurin
nan, don ba zai yiwu ni da ke a ciki ba, in kuma ke
ma matar gida ce sai ku zo ke da ubau i ku
gaya min."
Ban tanka ba nasa hannu na dauko risho tare da
tukunya mai murfi, ba na ce kar ki taba min komai
ba, na kalle ta na ce, kin gani? Wannan ai na Inna
ne, kadan ya rage ta kifa min mari saboda ambaton
Inna da nayi a gabanta, ban san yanda a ka yi ba
sai kuma naga ta fasa.

38
To juye min kananzir din ciki ko shi ma nata
ne? naje na juye mata, ina fitowa Isiyaku da ke
biye dani yasa hannu biyu ya karba ya bar ni ina
neman wani tsohon galan da na san yana nan a
cikin kicin din.
Na fito ina kwance bakin zanina da na daure
kudina

Please Login or Register in order to submit comment